Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tashigo dakin cikin hijab iya gwiwa sai daurin gaba datayi da zane aciki wanda ana iya hango zanen ta qasan hijab Fuskarta da hannayenta duk a jiqe suke da alama daga wanka tafito "wai ke ina kika shiga Tundazu kinbar waya anata kira?" inji wata cousin dinta Qarasowa tayi tana yamutsa fuska "wanka najeyi part din Aunty Raliya I can't use toilet din dakinnan" Harararta yarinyar tayi tana cewa "sannu tsafttatu, nidai dalla amshi abinki an wani cika mana kunne da kira" Itama Harararta tayi sannan ta amsa tana cewa "waye?" "saiki duba ai da kanki" inji yarinyar tana kauda kai ta maida gasu Feenah dake can suna dimi bama susan abinda suke ba *D❤️* tagani Murmushi tayi sannan ta juya tafita daga dakin saboda hayaniya ta zagaya can bayan gidan inda babu hayaniya sosai tayi dialing number Ringing biyu aka daga amma sai akayi shiru "Baiby.." tafada cikin sigar tsokana "babu wani nan, don't baby me mun 6ata" Dan wara idanu tayi murmushi a fuskarta "6atawa? Meyasa?" "kinsan kira nawa nayimiki?" "yakai dari?" ta Tambaya cikin sigar jan fada "Haka ma zakice?" Dariya kawai tayi "mun sake 6atawa, hang the phone banason yin wayar dake kuma" Dariya tasake yi tace "kai kayi hanging din mana" "ai ke kika kira ke ya kamata Kiyi hanging up" "then we die here" Dariya sukayi gabadaya "gist me, kun taho?" "yanzu muka gama Gaisawa da suruki na" "suruki kuma?" "yes, ashe zai iya ganeni? Rabonmu da juna tun hospital kafin a sallameni amma tsaf ya ganeni, muka gaisa amma naji kunya 🙈" "wow! Nufinka har kun qaraso?" tafada cikin doki "yes? Gashi nanma ana shirin daura aure" injishi "wow! Ashe dai kakar tabari" "zauna nan... Bari in katse gashinan za'a fara" "na bari... Tare zaka biyo su daddy ku dawo nan?" "tambaya ma kike? Me zan tsaya yi acan?" "tsayawa Wurin anguna" "meye kuma anguna? Dama shi ya kawoni? I came to see my missing princess" Zatayi magana ya sake katseta da "gashi nan za'a fara, bye.. See you" Kittt.. Ya katse kiran Ajiyar zuciya tayi tana rollling manyan idanunta sannan tayi hanyar cikin gidan da sauri don shiryawa Koda tashigo dakin saita tararda anama Feenah wani daurin dan kwalin don harta chanza kaya zuwa wani royal blue materials Bata tsaya wani kalle kalle ba tawuce bude wardrobe din Feenah taciro kayanta dake cikin leda tafice daga dakin again Part din Aunty Raliya taqara komawa don achan ne kadai babu mutane ta bude falon da makullin hannunta tashiga ta rufo Saida tafara gabatar da sallar xuhr don dama da alwalarta tafito wanka dazu Sannan itama tafara shiri shap2 don kar Deen yazo bata gama ba Angon bikin ne tasa Atamfa mai shegen kyau taji dinkin doguwar riga wanda yayi mata dass ajiki Sannan ta zauna ta tsara makeup dinta daya dace sosai da fuskarta sannan tafara daurin dan kwali Tana cikin daurin taji hayaniya daga waje sai kuma 6uda dake tashi a can cikin gidan Murmushi zee tayi ta cigaba da daurinta acikin zuciyarta tana masu addu'ar zama lafiya. Saida tagama ta tashi ta feffeshe jikinta da turare mai sanyin qamshi sannan ta yafa yalolon gyalenta stylishly a kafada Linke kayan data cire tayi ta zuba a leda ta ajiye dakin yara sannan tafito da sauri don hayaniyar gidan sai qara sama sama take. Rufe mata gidan tayi sannan tafito tana tafiyarta kamar yadda tasaba tana duba wayarta dake vibrating "Hajiya Zainab!" Taji an kira sunanta abaya Juyowa tayi sai taga wani cousin dinta ne ke kiranta Kauda kai tayi kawai bata amsa ba tana qoqarin sake dialing number Deen don shi yakira "haba Aunty zee, meya kawo fada babu gaba? Magana fa nake maki" "don kana min magana sai akace dole saina saurareka?" tafada tana qoqarin dialing number still tana cigaba da tafiya Saurin shan gabanta yayi yana cewa "tuba nake ranki ya dade, haba sisi nifa yayanki ne be kamata kina yarfani ba" Wani kallon ta makamashi na wasa tace "kaine yayan wa?" "yayanki, idan kina gardama muje mu tambayi mummy" "A'a daddy zamu tambaya ba mummy ba" tafada tana qara dialing number Deen don ba'a daga wancan kiran ba "eh muje a tambayeshi daddyn, zakiji abinda zaice. Yarinya bar ganinki haka kin wani zabge to har naman sunanki Saida naci wlh da wayau na aka haifeki" Sauke wayar tayi daga kunnenta ganin ba'a daga ba again sannan ta kalli cousin din nata tace "inyee, congratulations tunda kaci naman sunana sai kaje ka rattaba Hakan cikin littafin tarihinka Saidai ko me zakayi bazai chanza ni yayarka bace, haka kowama kecewa" tafada tana mashi gwalo "marassa hankali ba, don sun ganni da dan jiki? Su kalli fuskata dakyau zasu ga bata yau bace wlh, wadannan tamoji tamojin kadai ya ishesu amsa" Dariya tayi tace "ai alarrama anbar duba fuska yanzu, tsawo ake dubawa mallam don haka kazo mu taimaka mu sanmma tsawo" tafada tana mashi Dariya "Kutt.. Amma fa kin qoshi saura ki dora da juice, wato ni kike ma shairin tsawo ko?" yafada cikin jin haushi Juyawa tayi tafara tafiya tana cewa "niba sharri nayimaka ba, Gaski... " Maganarta ce ta maqale lokacin dasuka hada idanu dashi daga can jikin gini ya jingina da bango ya harde hannayenshi a qirji ya zubamata idanu... ✍️ Kuyi hqr jiya kunjini shiru, jiya bananan ne shiyasa ban samu zaman typing ba 👏 Ummin fasihu 8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?* *043* *THE PROPOSAL* Jitayi numfashinta yakusan daukewa saboda yadda ya tafi da imaninta Sanye yake cikin farar shadda riga da wando irin na samarin nan wanda zakaga rigar da kadan ta wuce gwiwa, anyiwa wuyan rigar siririn aiki da dark blue din zare a wuya dakuma tsakankanin qirji sai kuma saman aljihu Kanshi sanye da hular dara kalar aikin kayan sai takalmi farare sai usual agogonshi data sanshi dashi daure a hannunshi Karo na farko data fara ganinshi da manyan kaya kenan sai taji dama su yake sawa don sosai yafito acikinsu yayi wani irin breathtaking kyau "waye shi din?" taji muryar cousin din nata kamar daga sama Hakan yasa tayi saurin dawowa daga duniyar kallon Deen ta kalleshi sai kuma tasake kallon inda Deen yake "muje.. He's a friend" tafada tana wucewa Dan Jimm cousin din yayi sannan yabi bayanta suka nufi Deen din da haryanzu be Janye idanunshi ba daga kanta Qarasawa tayi gabanshi cikin murmushi, sai yaji kaso mai yawa cikin 6acin ran dayake ciki yabi iska "hey.. " tafada tana dan daga mashi yatsu Dagowa yayi daga jinginen dayake yana murmushi " hyy" "ashe kana nan, inata kiranka no response" tafada hankalinta Kwance "oops na manta ban fiddata daga silent bane, nasata a silent ne dazamu shiga masjid" yafada yana kallon cousin din zee da shima shi yake kallo kowa da irin expression dinshi a fuska Ganin wanda yake kallo yasa ta juya ga cousin dinta "Umar meet Deen.. Kamaldeen, a friend" Murmushi Umar yayi mashi dryly yana miqa mashi hannu Miqa mashi nashi Deen yayi shima suka shiga yin musabaha "Deen, this is Umar.. My cousin" Dan murmushi yayi na gefen baki sannan yace "ashe shine? The guy.. Nice to meet you" yafada yana yiwa Umar murmushi Shima dan murmushin yayi yace "you're welcome" Sai suka sauke hannunsu gabadaya Umar ne yajuya ya kalli zee datayi kamar wanda ruwa ya cinye don sarai tasan inda maganar Deen ta dosa "ok sisi, bari natafi, see you" inji Umar Dan murmushi zee tayi mashi tana cewa "yeah, see you" Besake kallon Deen ba yayi gaba ya barsu anan Binshi da kallo Deen yayi yana jin zuciyarshi na mashi zafi sannan yajuyo ya kalli zee Cikin basarwa zee tace "you're welcome to Ruma, so ya kaga garin?" "Amazing" yafada simply still yana kallonta Murmushi tayi tace "to muje ciki ku gaisa dasu mummy ko?" "is that necessary?" yafada still babu irin wannan walwalar tashi attatare dashi "yeah, ba kace kun gaisa da daddy ba? Bazata ji dadi ba idan taji kazo bakaje kuka gaisa ba" Kada kai yayi sai yace "muje to" Tare suka jera suka nufi cikin gidan Saidai babu mai magana acikinsu Zee ta lura fushi yake but he's trying wajen 6oye Hakan Ita Dariya ma yabata, ita wlh tama manta da wani batun cousin dinta data ta6a yimashi don dama qarya ce kawai don tabashi haushi lokacin yasa tafadi Hakan ashe shi be manta ba Da ta tuna Da ko introduction din ba zatayi ba Amma kuma a qasan zuciyarta dadi taji ganin yadda yake kishinta, tana son mutum mai kishin abinshi wanda beson wani abu ya ra6eshi ko yaya ne Hakan na daya daga signs of qauna. Wani wuri inda babu jama'a sosai suka tsaya "bari nayiwa mummyn magana" Kada mata kai kawai yayi ta juya ta wuce yabita da kallo Hannu yasa ya cire hular kanshi yadan yamutsa lallausan gashinshi sannan ya maida hular ya sake harde hannayenshi a qirji Ganinta da wani ya 6ata mashi mood sosai, kafin lokacin murna yake da doqin Ganinta amma kuma ganinta da wani har tana mashi Dariya yasa duka murnar komawa ciki yaji ya rage kuzari sosai Cigaba da jiranta yayi yana dan kalle kalle Can sai ya hangosu sun taho da mummy da zee dake dauke da sultan d'an Aunty Raliya. Ganin mummy yasa Deen qara gyara tsayuwa murmushi yana forming a fuskarshi Qarasowa su mummy sukayi, mummy na cewa "wai patient ne haka?" Cikin fara'a Murmushi Deen yayi har Saida dimple dinshi na gemu ya losta sannan ya tsugguna yana gaida mummy Sai mummy taji kanta yaqara girma "haba tashi mana kamal, yasu kaka?" Tashi yayi yana murmushi yace "Tana lfy lau mummy, tana gaidaku ma" yafada yana kasa hada ido daita Murmushi mummy tayi tace "Allah sarki, muna amsawa. Munyi rashin kirki bamu tura mata I.v ba" Murmushi kawai Deen yayi yarasa abinda zaice "to idan katashi tafiya ayimin magana please, bari nakoma na ida abinda nakeyi" inji mummy Dan russunawa Deen yayi yana cewa "to mummy, afito lfy" Murmushi kawai tayi ta juya ta tafi Saida yaga ta tafi sannan ya dago ya kalli zee dake kallonshi murmushi a fuskarta Hade rai yayi ya kauda kai gefe Dariya ne ya kufce mata ta rufe bakinta da tafin hannu tanayi, sultan din hannunta ganin tanayi sai shima ya kwaikwayeta ya rufe baki da hannu shima yana Dariya Hakan yasa Deen murmusawa sannan ya miqoma sultan din hannu Da gudu yatafi don dama shi beda kiwuya ko kadan, daka miqomashi hannu zai taho yana 6angale baki Amsarshi Deen yayi yana lakutarmashi hanci ya Hade goshinsu yana girgiza kai yana mashi Dariya shima sultan din na 6angalar Dariya Zee dake kallonsu cikin sha'awa takama murmushi acikin zuciyarta tana hasko Deen dauke da baby dinsu yana mashi/mata wasa Yatsa sultan yasa a kwarin gemunshi yana cigaba da Dariya Murmushi Deen yayi mashi yana jin qaunar yaron har cikin ranshi don shima allah ya yishi da mugun son yara ko don shima shi kadai ne? Dagowa yayi ya kalli zee dake kallonsu itama murmushi a fuskarta Harararta yadanyi sannan yasake kauda kai Murmushi tadanyi tana dan girgiza kai sannan tace "let's go" Dagowa yayi ya kalleta kamar zaiyi magana saikuma yafasa yabita suka fara tafiya sultan sai gwaranci yara yake mashi shikuma yana biyemashi Part din Aunty Raliya suka wuce, a balgony ta ajiye musu kujeru biyu farare sai tashiga ciki ta dauko daya daga stools dake gefe gefen kujerun Aunty Raliya ta fito Zuwa tayi zata ajiye yayi saurin amsar mata ya ajiye inda yaga zata ajiye yana wani qara hade cikakkun girarshi Murmushi tayi kawai. Daidai nan wata yarinya tashigo gidan bazata wuce yar shekara 13 ba, itama tasha ankonta na bikin Da sallama yarinyar tashigo hannunta dauke da tray an rufeshi da wani white clean sheet Amsawa sukayi gabadaya suna kallonta Gaidasu duk tayi suka amsa sannan tazo ta dora tray din bisa stool din zee na taimaka mata Miqama sultan dake bisa kafan Deen hannu yarinyar tayi Saurin lafewa yaron yayi ajikin Deen yana 6ata fuska Dariya Deen da yarinyar sukayi zee kuma tayi murmushi "shikenan, zamu hade ne, zaka gane ni kayiwa kiwuya" inji yarinyar tana Juyawa ta tafi Bayan fitarta zee ta yaye farin kyallen tray din saiga snacks da drinks sun bayyana Dago glass cups dake kife tayi ta bude drink din ta tsiyaya masu ta ajiye mashi nashi gabanshi ita kuma ta dauki nata tafara sipping ahankali Shiru ya biyo baya idan ka cire gwarancin sultan daketa yima Deen qiriniya akan qafa sai tumurmusa mashi shadda yake shikau Deen ko ajikinshi saima murmushin dayake mashi. Dagowa yayi ya kalli zee yaga drink dinta take sipping ahankali idonta akan waya "kinyi kyau" yafada ahankali Dagowa tayi daga wayar hannunta ta kalleshi taga still fuskarshi babu walwala kamar ma bashi yayi maganar ba "thanks, kaima haka" tafada tana qara kai kofin a baki "nima me?" yafada yana kallonta "yadda kace" tafada tana juya ido Dan murmushi yayi "ni ai Gaskiya nafada bawai nafada ne kawai don kiji dadi ba" "nikuma don kaji dadi na fada? Nima Gaskiya nafada" "haba dai, kina nufin nayi kyau?" Murmushi tadanyi mai sauti sannan ta Kada kai kawai Daga kafadu yayi yace "amma ai ban kaishi haduwa ba" yafada yana dan ta6e baki Dagowa tayi ta kalleshi "wa kenan?" "kin fini sani... *your man*" yafada yana qara ta6e baki Murmushi kawai tayi batace komai ba shikuma ba abinda yakeso ba kenan soyake tafadi wani abu dazai dan sanyaya mashi zuciya daga zafin kishin dayakeji a zuciya "shi ai naga har Dariya kike mashi nikau sai shan qamshi kike min" yasake fada yana kauda kai Dariya yabata sosai Hakan yasata yin murmushi mai sauti kawai batace komai ba, Hakan yasake quleshi "kuma wajen introducing dina wajenshi wai *my friend* amma shi kin iya kiranshi *my boyfriend*, adai dinga tsoron allah" yafada yana daukar cup din gabanshi a fusace yana sha Sauke kai qasa zee tayi tana Dariya marar sauti "ko banza nafishi tsawo, wani dunqul dashi" Dariyar zee ce tafito fili tashiga yi Babu kakkautawa Qara tamke fuska yayi ya kauda kai yana sipping din juice din cikin kofin "am smelling something here... Jealousy" tafada tana Dariya Harararta yayi "it's not funny" "it is, jealousy!" "babu komai, ai so ke kawo kishi amma ni na lura ma ni kadai ke haukana babu wani sona dakike" yafada yana kumburi Murmushi tayi tace "haka dai kace" "haka dai ne, ba gashi ba kina kula wani babu ruwanki da halin da zan shiga" yafada yana kauda kai don sosai abin yayi mashi zafi don dai shi ba gwanin fushi bane koma gwanin fushin ne bejin yana iya yimata "dan uwana ne fa" "kuma boy friend dinki ba" "wai wa ya gayamaka shine? Bashi bane wannan" "wato haryanzu akwai wancan din kenan kuma haryanzu boy friend din naki ne" "my goodness! Dama haka kake?" "nafi Hakan ma Indai akanki ne " yafada yana kauda kai Murmushi kawai tayi tace "nidai banida wani boy friend, inka yarda Amma" Saurin juyowa yayi ya kalleta ya marairaice "kice wlh, wlh bakiji yadda zuciyata ke zafi ba" Dariya tayi "wlh ba abin Dariya bane, wlh bakiji yadda naji ba danaga kina washe mashi baki" Dariya tasakeyi tace "he's only my cousin, sokake naita zare mashi idanu? Afterall me zanyi da guntu bayan inada iroko tree" Harya fara washe baki Amma jin tace iroko tree saiya tsuke fuska "nine iroko din?" Dariya tashiga yi tana rufe baki da hannu "tsawon iroko ai marar kyau ne, ni banaso" "to ai naga irin tsawon gareka?" "wa? Ni? God forbid, kinsan yadda iroko tree yake kuwa, siriri sai mugun tsawo? Allah ya kiyaye" Murmushi mai sauti kawai tayi "nidai don Allah ki fita harkar shi please, ba don ni ba please" yafada yana sake marairaicewa "ai na gayamaka, me zanyi da gajere?" "babu, wlh ko guntu ne ga hancinshi kamar gajeren wando, qofofin hancin kamar kofar durbi, with that tiny tiny eyes nashi kamar na yan china" Dariya sosai zee keyi ganin yadda ya daddage yana kushe bawan allah, imagining take da agabanshi yake fadin haka da kau sun kwashi yan kallo "Allah Gaskiya nake fadamiki, Is better you choose wisely karki za6i wanda zai saki haihuwar masu zubin emmanuella" Dariya tasakeyi tana girgiza kai "Allah Deen bakajin magana" "Gaskiya na fadamiki ai, ato" Murmushi tayi sannan ta nuna mashi snacks din da be ko ta6a ba "Sai kince kin daina kula kowa sannan" "dama ai ba kula kowa nake ba kaidai ke ganin haka Afterall da wane zuciyar zan so wani bayan ni kaina banida iko daita sai yadda akayi daita" tafada tana ta6e fuska Wani farinciki ya ratsa zuciyarshi nan take murmushi ya gauraye fuskar "dagaske?" Murmushi kawai tayi tasake turamashi snacks din gabanshi batareda tace komai ba Daukar daya daga cookies din gabanshi yayi ya dan gutsira still yana murmushi "thank you" yafada yana mata winking Kauda kai tayi tana murmushi kawai Cigaba sukayi da firarsu kamar babu abinda yafaru kowanne fuskarshi da annushuwa shikau sultan wasanshi kawai yakeyi abinshi Sosai Deen yaci snacks din don shi dama bejin kunyar cin abinci ko a ina ne, idan dai kaga yaqi Sakin jiki yaci abinci sosai to be yarda da tsaftar abincin bane shiyasa ko a school yafi mu'amala da snacks, biscuit, chips e.t.c Basu sake jimawa ba suka tashi don tafiya yace zaiyi don 4 saura kuma kaka tariga tayi warning dinshi akan kar yayi dare Tare suka qara jerowa Deen riqe da sultan dake barci a kafadarshi Duk inda suka bi sai anbisu da ido ana wondering waye wannan tareda zee A inda yajira dazu tayima mummy magana yasake tsayawa Amsar sultan din zee tayi Deen nacewa tabi ahankali kar taji ciwo don jiyake da yana iya shiga daya kai mata shi har cikin gidan Batace mashi komai ba tajuya ta wuce cikin gidan Can ba'a jima ba sosai yaga mummy da zee sun fito Sauke idanunshi yayi qasa yana dan murmushi har suka qaraso wajen "Kamal har zaku tafi?" Cikin girmamawa yace "eh mummy naga marecen yafara kuma kakata tace karna kai dare" "aikau dai babu kyau tafiyar dare, to bari na kira rabi'u yazo ya kaika" "laa mummy, da kin barshi zan dan biya kasuwa ne sannan na wuce tasha saina hau motar acan" "to basai ya biya dakai ba? Zai Mafi sauqi" Shiru yayi don besan abinda zaice kuma ba " ga wannan ka kaima kaka, kace ina gaidata" Nauyin ta dayakeji yasa ya amsa yana mata Godiya don yasan ko yaqiya saita tilastashi Cema zee tayi ta hada shi da rabi'un saiya wuce dashi sannan sukayi sallama mummy ta koma ciki Kallon juna sukayi sukayi murmushi sannan suka taho "muje ka gaisa da amarya?" Wara idanu yayi yace "No please, please mutafi mutane sunyi yawa Wurin" Daga kafadu tayi suka wuce Basu sha wahala ba sukaga rabi'u kuma dama mummy takirashi ta gayamashi so babu 6ata lokaci kawai suka wuce mota. "yaushe zaki dawo?" "Nan da just 1 week" Wara idanu yayi yace "one week! Lokacin na mutu da kewarki kenan" "daidai kenan" "nidai please yaushe zaki dawo kinga ga school you'll miss alot" "zan dawo very soon insha allah tunda ai anyi abinda ya kawomu sai yan ide iden da ba'a rasaba" Bude murfin gaba yayi amma be shiga ba yace "ok allah ya maidoku lfy and please, don Allah karki kula kowa, please" Murmushi tayi "insha allah" "inso samu ne ma karki je dinner nan" "saifa naje" "to kije but please karki kula kowa please" Rolling idanunta tayi tace "to" "promise?" "promise" Murmushi yayi mata sannan ya shiga motar yaja murfin ya rufo Ganin Hakan yasa rabi'u dake cikin mota Tundazu tada motar Dagama juna hannu suka shiga yi Alamu yayi mata da saisun yi waya ita kuma tayi murmushi kawai, rabi'u yaja suka fice daga gidan Ajiyar zuciya ta sauke bayan taga firarsu daga gidan sannan ta dawo ciki. Lokacin data sake komawa dakin da amarya take Saita iske Aunty Feenah ma bata ciki sai yanmatan amarya daketa maida yadda akayi wasu kuma nata sallar asr Ganinta yasa sukayi mata caa suna tambayarta waye suka ganta tare dashi Qin basu amsa tayi saima biyemasu datayi sunata chafta kafin daga baya ma ta baro masu dakin takoma can part din Aunty Raliyar tayi ta kauda abubbuwan dasukayi amfani dasu dazu ta dauro alwala itama ta gabatar da sallar asr Tana zaune bisa sallaya bayan tagama sallar ta Fiddo wayarta ta kunna tashiga gallery, tashiga wani folder nan take hotunan Deen cikin shigarshi ta dazu suka bayyana Murmushi tayi tafara binsu daya bayan daya tana kallo Dik aciki babu wanda ya nuna alamar yasan an daukeshi Duk yawancinsu hankalinshi nakan sultan dake hannunshi suna Dariya sosai Bïñ hotunan taitayi da kallo don ba qarya sun dauku dukda a sace akayi daukar kuma duk babu na banza aciki Murmushi tayi sannan tafita daga gallery din tashiga message tayi mashi short safe journey sms ta tura mashi sannan ta tashi ta fita *7:30pm* Gida fa ya hargitse duk inda kayi hayaniya ce kawai na mutane yan zuwa dinner. Duk wanda zaka gani cikin shigar anko din dinner zaka ganshi pink and blue Koina ya cakude motoci sai daukar mutane suke zuwa dinner Can na hango zee tafito tana zuge wata guntuwar jakkarta mai shape din heart pink colour, itama taci adonta cikin doguwar rigarta ta anko din gyalenta a sagale da hannu, kan nan yasha daurin head. Saurin qarasawa jikin wata mota tayi don dama ita kadai suke jira ta bude back seat tana basu hqrin bata masu lokacin datayi ta shiga ta zauna sannan ta rufo, nan da nan aka tada motar suma sukabi ayarin motocin dake fita daga gidan zuwa dinner Dinner tayi dinner, ansha shagali sosai a dinner ba qarya inda amarya da ango suka fito suka zama taurari acikin tarin al'umman wajen. Zee kau samari ne suka yimata caa kowa burinshi yasamu shiga amma kamar yadda tayiwa Deen alqawari babu wanda ta kula acikinsu haka sukayi suka gaji suka barta Ba'a wani dade sosai ba a dinner don 10:00pm nayi aka tashi, motoci suka shiga jigilar mutane zuwa gida Itama amarya gida aka maidota badon ran Auwal yaso ba don shi da so samune abashi amaryar shi a lokacin suyi tafiyarsu amma ya ya iya dole ya hqr tunda da yau da gobe duk daya ne. Washegari ranar kai amarya dakinta Sai wajajen 5pm motocin daukar amarya suka iso Saiga amarya daketa cika bakin ba zatayi kuka ba da kuka sha6e sha6e, dakyar aka 6an6areta daga jikin Umma dake hawaye itama aka fita daita su kawunnanta sukayi mata fada sannan aka shiga daita mota Su zee dama an riga an shishige mota fitowar amarya kawai ake jira Ajere motocin suka fita suka wuce gidan amarya. Masha allah, gidan amarya yayi kyau sosai, ba wani babban gida bane sosai amma an tsarashi gwanin burgewa ga jeren Aunty Feenah ya mugun dacewa da sanfarin gidan Hakan yasa gidan yaqara badawa Saida su zee suka gama zagayen gida suna santi sannan tabi su Aunty Raliya suka dawo gida duk kuwa da yadda Feenah tayi tayi daita tabari sutaho da qawayenta dake jiran zuwan ango amma taqi, tabi su Aunty Raliya tana Dariyar Feenah dake cewa zasu Hade ne zatasan ita tayiwa rashin mutunci. To amarya fatan mu dai allah yabada zaman lfy yakawo dattin daki. Saida su zee suka qara kwana biyu a garin sannan suka dawo gida. Zokaga murna wajen Deen don dama duk lokacin da sukayi waya sai yayi mata complain din ta tafi ta barshi cikin kewa. Dawowar zee yasake bude wani fage na soyayyarsu da Deen Soyayya suke nunama juna tsantsarta suna jin idan babu daya daga cikinsu dayan bazai iya rayuwa ba. Ana haka suka shiga watan masoya wato february na watan bature inda aciki ke akwai ranar masoya wato VALENTINE DAY Tunda aka shiga watan kowanne masoya suka shiga tanadi wa wannan ranar ciki hardasu Deen, wadanda basu ta6a celebrating din ranar ba sai a wannan karon. Kowa shirye shirye yake wa ranar suna looking forward to ranar cikin doqi. *14th FEBRUARY 20...* Yau takama ranar laraba, ranar da duk wasu masoya ke dakon zuwanta. Ranar da kowanne keson gwadama masoyiyarshi ko masoyinta matsayinshi ko matsayinta a zuciyarsu. Hakan take a wajen su Deen ma Zaune suke a usual Wurin zamansu dake very quiet sai tsuntsayen daketa kai kawo a wajen Zaune suke suna facing din juna kowanne sanye cikin kaya jaa da fari Zee na sanye cikin wata english gown A shape wanda akayi slashing */* gaba rigar, bangaren dama kalar fari na haggu kuma jaa sai gyalen data yafa a kanta fari, takalmi ma Hakan. Shikuma Deen sanye yake

Chapter 33 of 81