Be tarar daita ba wajen Hakan yasashi zama don jiranta yasan qila wani abu tajeyi ko taje saye
Fiddo wata takarda yayi yana sake dubata
Form ne da wani maqocinsu ya samo mashi na aiki a wani company
Ga yadda maqocin nasu ya gayamashi yace suna daukar mutum da kowanne mataki na karatu kai hatta wanda iyakar shi primary suna dauka Saidai kawai banbancin albashi da za'a samu tsakaninsu
Tun jiya yabashi akan zai amsa yau idan ya cike, sosai shima Deen din yaji yana son aikin don dama yanzu hutu zasuyi gashi aikin furniture dinsu yanzu ba'a cika samu ba kasancewar yanzu damuna ce kowa ta kanshi yake duk ba'a fara fitar da amfanin gona ba bare kudi su yawaita har afara maganar aure2, dakuma ya zauna hakanan ai gwara ya jaraba wannan din ko allah zaisa a dace
Ciro pen yayi yashiga cike takarda cikin nutsuwa making extra sure beyi mistake ba ko guda
Saida yagama cikewa tsaf sannan yatsaya yana sake dubawa don tabbatar da beyi kuskure ba ko daya, Ganin komai daidai ne yasashi bude tsakiyar wani Littafi ya saqa takardar ciki ya maida ya rufe
Daga kai yayi yana kallon sararin samaniya ya hangi yadda hadari ke neman haduwa ga iska iskar daketa kadawa yanzu
Duba wristwatch dinshi yayi yaga 3 saura, yanzu aqalla yafi 30mins da zama
_to ina ta shiga ne haka?_ tambayar dayayiwa kanshi kenan
Komawa yayi jikin kujerar ya harde hamnayenshi a qirji ya cigaba da jiran tsanmmani
*ZEE*
Wani dum taji kanta yayi tayi baya baya ta zube qasa
Dafe kumatunta da takeji kamar ba nataba tayi tana jan numfashi cikin fitar hayyaci
Rankwafowa Master yayi gabanta yana cigaba da wannan dan iskan murmushin
"da kika wani yunquro, nima marina zakiyi? Eh?" yafada yana leqa fuskarta data farayin jajajaja
Dagowa tayi ta kalleshi da idanunta dasuka farayin ja hannunta still Dafe da inda ya mareta tana jan numfashi haryanzu
"gayamin, nace nima marina zakiyi?" yafada yana kai hannunshi saitin qirjinta
Bige hannun tayi tana ja da baya dakyar
Kamo hannunta yaso qarayi taqara Bige hannun tana qara ja baya tana nishi
"Go away, you brat!" tafada tana dibar qasa ta watsamashi still tana ja da baya
Saurin kauda kai yayi ganin qasar ta nufo fuskarshi Hakan yasa ta sauka a jikinshi
Sake juyowa yayi ya kalleta
"brat? Nine brat? Wato bakinki bai mutuwa ko? Dont worry, zan kashe maki shi ayau, now and forever!" yafada yana nufota
Ganin Hakan yasata saurin miqewa a gigice tayi niyyar guduwa sai kawai taji bash dake bayanta ya cafketa
Qara tasaki tashiga qoqarin kwace kanta a hannunshi amma takasa, batayi wata wataba tasa kafarta atsakiyar kaffafunshi ta dago gwiwarta
Wani mahaukacin qara bash yasaki tareda sakinta ba shiri, ya fadi yana billayi
Faduwa tayi itama daya saketa amma ko second daya batayi ba ta miqe tafara gudu cikin son ku6uta daga garesu
"kubita! Karku sake ta gudu!" inji master cikin qaraji
Da gudu su alex suka bita yayinda shikuma master din ya zube gaban bash daketa ihu haryanzu hannayenshi damqe da gabanshi ya dagoshi yana kallo
Gudu take cikin fitar hayyaci batareda tasan hanyar da takebi ba, ga wani iska mai qarfi daya taso mai tafeda duhun hadari
Iya gigicewa ta gigice don kawai jefa kafarta take inda tasamu gashi bata ganin gabanta sosai saboda iska, qarin tashin hankalinta kuma shine sautin gudunsu dataji yana qara kusantota sosai
Kafin ma tayi wani nisa suka cimmata gandu yasamata kafa tayi tuntu6e ta fadi
Jan kugu tashigayi da baya baya tana numfarfashi
Nufota suka ta cigaba da jan kugu tana girgiza kai cikin tsantsar tashin hankali, tsabar rudewa ma takasa jawo kowacce addu'a sai 6ari da duk ilahirin jikinta keyi
Take kafarta T.J yayi wanda hakan yasata sakin qarar azaba, bata gama tantance zafin wannan ba taji an damqi gashinta anfara janta qiiiii!
Ihu ta cigaba da kwallawa tana Iya qoqarinta na ganin ta qwace amma takasa, be tsayar da ita koina ba sai a gabansu master dake duqe still gaban bash daya galabaita Iya galabaita don ba qarya ya bugu
Jefar daita yayi ta zube gabansu master tana haqi
Afusace master ya damqi gashinta har saida tayi qara ya dago kanta saitin fuskarshi yana kallonta da jajjayen idanunshi
Qalato yawu tayi ta tofamashi a fuska cikin qarfin hali
Kauda kai yayi yana rintse ido saboda yawun daya sauka akan fuskarshi, Afusace yasake juyowa ya dauketa da marin dayafi na dazu ratsa jiki
Wata wahallaliyar qara tasake fasawa ta zube awajen tana numfashi sama2
Jitayi kunnenta nayimata dumm dumm ga idanuwanta da suka fara ganin dishi2
Bayan hannu yasa ya goge yawun fuskarshi yana huci sannan ya qara nufarta ya sake damqo gashinta ya tadota zaune
Rintse idanuwanta tayi gamm, tsabagen damqa har jijjiyoyin gashinta ana gani
"ni zaki tofawa yawu a fuska? Eh?" yafada yana qara dauketa da wani marin wanda yaqara sata zubewa
Cusa fuskarta tayi cikin ciyayin wajen tana jan numfashi dakyar
Qara damqo gashinta yayi ya dagota again yana saita fuskarta saitin fuskarshi ya nufi bakinta da niyyar sumbata
Datse bakinta tayi gamm ta hanyar maida la66anta ciki ta danne tana numfarfashi masu nauyi
Cikeda mugunta yasa dayan hannun ya Kamo kumatunta ya lotsa yatsunshi a kowanne gefe cikin mugunta har saida bakin ya bude
Qara nufar bakin yayi da niyyar kiss ta dago hannunta daya dakyar ta rufe mashi fuska tana turashi
Kauda kai yake cikin son kaucema ture fuskarshi datakeyi amma taqi bari Hakan yasa ya saki gashinta da haryanzu ke a damqe a hannunshi ya Kamo hannun nata data tare mashi fuska dashi dago dayan hannun tayi shima ya cafkeshi ya hadesu a baya ya riqesu da hannu guda yasake dago fuskar da tsiya yasake nufar bakin
*DEEN*
Qara duba agogon hannunshi yayi a karo na ba adadi, wai ina ta tsaya haka? Koko ta tafi ne? Amma ai basuyi daita cewa tafiya zatayi ba, gashi kuma beson tafiya kuma ace tananan tazo ta nemeshi batanan
Kallon sama da hadari keta qara haduwa yayi ga iska daya fara qarfi
Miqewa tsaye yayi yana rungume littatafanshi a qirji yana qara kallon yadda hadarin ke qara haduwa
Ina ta shiga to? Sai yanzu yake jin haushin rashin number wayarta da bedashi daba yanzu yakira yaji ko ta tafi ba?
Ga hadari sai qara haduwa yake, yasan rufin asirinshi shine yabar school dinnan Tun yanzu kafin ruwa ya 6alle saboda yanayinshi don yanzu haka ma iskar dake kadawa yafara affecting dinshi
_maybe ta tafi gida itama_
_yes na tabbata ta tafi_ yafada ma kanshi cikin qwarin gwiwa
Da wannan tunanin yasa ya fito daga inda yake yana qara qanqame littatafanshi a qirji ya fara tafiya don barin school din.
Wani iska mai qarfin gaske yaqara tasowa wanda saida Deen yaqara qanqame jikinshi, gashi dama daga shi sai wata yar farar t-shirt mai gajeran hannu, kasancewar yau da zafi aka tashi yasashi sanyota don ko kadan be ta6a kawoma kanshi za'ayi ruwa ba
Qara saurin tafiyarshi yayi cikin zuciyarshi yana addu'ar allah ya daga ruwan nan harya kai gida don bazai manta da gargadin Dr ba a wancan attack din na ciwonshi inda ya gargadeshi sosai akan ya kiyayi shiga ruwa saboda condition dinshi don koyaya ya shiga ruwa matsala za'a samu
Wani iska mai hadeda gugguwa yasake tasowa wanda saida yakai hannunshi yakare fuskarshi ganin yadda gugguwar qasar ta nufoshi
Yanajin zubewar wasu daga cikin littatafan hannunshi amma be bude idanunshi ba saima addu'o'i daya shiga karantowa a zuciyarshi har gugguwar tawuce
Sauke hamnayenshi yayi Bayan ta wuce yayi saurin duqawa don tattare littatafanshi
Iska ake sosai wanda Hakan yasa littatafan suka bashi wuya wajen tattarosu don iskan sosai yake kadawa har littatafan na bubbudewa da kansu
Cikin hakane wani Littafi ya bude iska yashiga bubbude pages din da sauri sauri har yakai page din daya saka takardar shi na form din daya cike
Fitt! Iska ya figeta tayi sama tafara shawagi acikin iskan
"O'O!" yafada yana kallon yadda takardar ke sama ke qasa acikin iskan
Saurin ida tattara kingin littatafan yayi sannan ya miqe yafara bin takardar don kamota
Saidai kwata2 yakasa don the more yake tunkarar takardar the more iska ke qara yin gaba daita
Haka yaita binta da gudu2 sauri2 trying all his best na ganin ya kamota amma a banza
*ZEE*
Duk yadda taso qwatar hannayenta daya riqe a bayanta kasawa tayi don ba qaramin riqo yayimusu ba gashi qarfi ba daya ba
Duk yadda yaso ya lallubo bakinta kasawa yayi don sosai take amfani da iyakar qarfinta na ganin ta kwace wanda Hakan yasa taqi tsayawa wuri guda bare yasamu damar lallubo bakin
Su alex na nan still tsaye kansu suna kallon artabun da sukeyi Tundazu, suna son su shiga suma a faffata dasu amma sanin halin master yasa suka jinkirta don ga dukkan alamu shi da kanshi yakeson yafara ladaftata kafin suma su biyo sahu
Gajiya yayi da kokowar tasu Hakan yasa yakai hannunshi yakamo gaban rigarta, batayi auneba sai jitayi kyattttttt yaja yana ketata
Wani giggitaccen qara tasaki cikin dimaucewa wanda saida yayi amsa kuwa ta koina
Ido rufe ta rarumo hannunshi na dama takaimashi cafka da haqoranta ta datsa cikin cicin qarfi
Wata qarar azaba yasaki ya tureta da sauri yana yarfe hannunshi cikin azaba
Jada baya tashigayi cikin jan kugu tana kakkare qirjinta da suke awaje saboda yagan da akayiwa rigar
"help!!! Somebody help me!!.... Deen!!!"
Tashi tayi da niyyar sake guduwa Saidai samata qafa da wani yayi wanda bazata tantance fuskarshi ba saboda biji bijin da take gani yasata qara zubewa awajen tana sakin wata qarar mai qarfi
"help!!! Deen!!! Sumee!!! Somebody help me!!"
*DEEN*
Sosai ya jigata wajen qoqarin kamo takardar, gashi hadari sai qara haduwa yake Saidai yakasa haqura daita don muhommmacinta agareshi yasashi jin be iya barinta tabi iska hakanan
Dakyar yasamu ta tsaya wani wuri inda ta maqale cikin wasu qayoyi
Saurin qarasawa yayi wajen ya duqa ya daukota
Ajiyar zuciya ya sauke ganin batayi komai ba yashiga linketa neatly ya sakata aljihunshi
Qarar dayajiyo daga dan nesa da wajen yasashi waigawa da sauri
Shiru yayi ya kasa kunne amma tsit beqarajin komai ba
Ajiyar zuciya yasake saukewa har yajuya zai tafi yaqara jin wata qarar wanda tafi wancan don wannan ma kamar ta namiji ne
Sake waigawa yayi yana kallon saitin inda qarar ke tahowa
Jin wata qarar yakuma yi kamar ma magana ake Saidai bazai iya tantance abinda ake fadi ba
Shiru yayi yana kallon saitin inda qarar ke fitowa saikuma ya kalli sararin samaniya yaga yadda hadari ke qara hadewa
Wata qarar yaqara ji sama2 kuma kamar muryar mace
Tunani yafara yi, to idan ma mace ce me zai kawota nan?
Hankalinshi ne yakasu kashi biyu, daya a inda yake jin qarar dayan kuma gida
Yasan idan ruwan saman nan ya sauko to ya kade har ganyenshi Saidai kuma yarasa dalilin dayasa zuciyarshi tafi karkata ga inda yakejin qarar
Qara kasa kunne yayi yaji ko zaiji wani abin sai yaji tsit, ya dan jima yana sauraren ko zaiji wani abin Saidai beji komai ba hakan yasa ya yanke shawarar tafiya wata qila kunnuwanshi ne basu jiyemashi daidai ba
Qara rungume littatafanshi yayi yafara takawa zai tafi
Wata qarar yaji wanda tafi dazu wanda Hakan yasashi qara waigowa da sauri
Tabbas wannan qarar mutum ne kuma mace
Me mace keyi anan cikin wannan gungurmin hadarin? Ko 6acewa tayi?
Babu mai amsamashi Hakan yasashi fara bin inda yakejin qarar yana qara rungume takardunshi
The more yake qara nausawa the more yakejin muryar clearly
"Daddy!!! Mummy!!! Help!!! Taimako!!! Please Help!!!"
Jin Hakan yasashi qara sauri yana dan hadawa da gudu yana bin muryar harya bayyana a scene din
Sakin littatafan hannunshi yayi yana qara wara oily eyes dinshi ganin yadda mace ke kokowa dawani namiji bakin rai bakin fama
Macen ce akasa namiji akanta suna kokowa sai ihu Macen keyi
Besan yadda akayi ba sai kawai ganinshi yayi a wajen ya cakumo namijin ta baya ya dagoshi ya wurgar gefe sannan ya ranqwafa ya dago Macen da sauri
Qanqameshi zee tayi cikin fitar hayyaci still tana sabbatun neman taimako
Duk yadda yaso ya 6an6areta daga jikinshi kasawa yayi don Qanqameshi tayi gamm kamar her life depends on him
Babu zato yaji abu ya tunkudashi ta baya wanda Hakan yasa yayi gaba ya fadi dashi da zee din dake jikinshi
Lumshe idanunshi yayi ya budesu akan fuskarta da sai yanzu ya samu damar ganinta
Qara wara idanun yayi ganin the shock of his life
_*zainab!*_ zuciyarshi tayi exclaiming
Saurin mirginawa yayi gefe ya tashi zaune still yana kallonta da madaukakin mammaki a fuskarshi
Itakau curewa tayi wuri guda ta rungumo qaffafunta ajikinta tana kuka mai cin rai jikinta babu inda be 6ari
"kai!!!" qarajin master ya dawo da Deen daga duniyar kallon zee
Dagowa yayi ya fara binsu da kallo daya bayan daya sun jera agabansu suna kallonshi shima sai huci suke
"kai waye dazaka shigo gonarmu har ka nemi takamana burki?! Ko bakasan ko mu su wayeba?!!" inji T.J cikin qaraji
Dode kunnuwanshi yayi yana yatsine fuska
"O'O! Meyasa kake tsawa to?" inji Deen still hannunshi dode da kunnuwan
_*O'O!*_
Kamar kunnuwanta abinda suka jiyemata kenan, duk duniya mutum daya tasan yana cewa haka
_*DEEN*_
"tambaya ma kake meya sani tsawa? Wato bakama ji tsoro ba saima rainin hankali dakake neman yi?"
"ni ban raina maka hankali ba, babu kyau tsawa ne saboda Hakan yana da illa sosai, gareka dakuma mai saurarenka.
Idan kayi tsawa hakan yana iya cutar dakai domin..."
"DEEN!!!!" zee ta katseshi da fadin hakan ta rarrafo cikin sassarfa ta fada jikinshi
Wani irin kuka mai tsuma kuka tafashe dashi tana qara Qanqameshi
"wayyo Deen! Deen ina katafi ka barni? Please Help me Deen, take me out of here, zasu kasheni..." tafada cikin fitar hayyaci jikinta na rawa sosai
Dago fuskarta yayi cikin taffukan hannunshi yana bin fuskarta da kallo
"Zainab, look fuskarki ta kumbura and this.." yafada yana dangwalo jinin dake gefen bakinta ya nunamata
"meya sameki?" yafada cikin raunin murya
Fashewa tayi da wani kukan tana sake komawa jikinshi ta Qanqameshi, kafin zuwanshi tariga ta saddaqar rayuwarta tazo qarshe amma yanzu ganinshi yasama mata hope, hope na cigaba da shaqar numfashi da fitarwa, kasancewarta a jikinshi kawai ya samata jin sense of security, yasamata hope na tsira daga wadannan shaidanun
"oho? Sai yanzu na ganeka, wannan gayen ne master" inji alex yana Fashewa da Dariya
Su kingin ma Fashewa sukayi da Dariya banda master da fuskarnan ke a murtuke, ga hannunshi dayake jini sanadin mugun cizon da zee tayimashi, radadi duk ya isheshi
"silent!!" injishi cikin quluwa don shi bega abin Dariya ba anan
Tsit wajen yayi zee kau qara shigewa jikin Deen dake kallon master tayi tana rufe idanu
Takowa master yayi ya nufosu
Ganin Hakan yasa Deen miqewa tsaye da zee dake jikinshi still ganin master ya tunkarosu yasata saurin komawa bayan Deen ta lafe zuciyarta na cigaba da bugawa
Qarasowa yayi gabanshi nan aka shiga kallon kallo tsakaninsu
Qara lafewa bayanshi zee tayi tana kwantar da kanta bisa bayanshi
"kai! Maza kama gabanka" inji master kamar irin yana ma dan shekara 4 magana
Shiru Deen yayi be amsa ba kuma beyi abinda yace ba
"ko bakaji ba!" yafada atsawace yana zazzaromashi idanu
Dan jada baya yayi don sosai tsawar ta daki kunnenshi gashi idanun master beda kyan gani, sun wani rune kamar garwashi
"O'O! Meyasa kaima kake shouting? It's not good for your health kuma ka daina kallona da wadannan idanun, bana sonsu" yafada yana yamutse fuska
Sheshekar zee ce ta tsaya cak
Sai yanzu ta tuna da waye Deen, sai yanzu ta tuna da waye ta la6e a bayanshi a matsayin garkuwa
Deen ne, the timid guy, tambayar anan shine shi zai kareta daga su ko ita zata kareshi?
"kai! Kalleni dakyau kagani kaga wasa a idona? The best option for you shine ka 6acemun anan tun kafin nahada dakai da mental problem din naka nayi kaca2 daku" yafada cikin zazzaremashi idanu
Shiru Deen yayi yana kallonshi batareda yace komaiba
"baka jiba?"
6ata fuska yayi yace
"Meyasa ka daketa? Bakaga ita macece ba kuma yarinya? Abinda kayi bashida kyau" yafada cikin son nusar dashi gaskiya
"yarinya? Yarinya ce amma ta iya tsokano manya? Wannan yana nufin tana jinta daidai da manyan ne don haka ta tsokanoma kanta, saita banbance tsakanin aya da tsaguwa yau" injishi cikin huci
"kayi hqr to idan laifi tamaka amma ai ba girmanka bane ka biye mata, kai kana gaba da ita, ka dauketa a matsayin qanwarka" yafada cikin son convincing dinshi
Qara matsowa master yayi gaban Deen har suna iya shaqar numfashin juna cikin husky voice yace
"look, ni banida case dakai ko daya, da ita nakeda so karka bari nasamu case din dakai, ka miqomin ita katafi salin alin tunkafin in burkita maka wannan fuskar!" yafada yana kamo gemun Deen din yajawo fuskarshi har gab da tashi sannan ya turashi baya wanda Hakan yasa sukayi baya baya shi da zee suka fadi
Be qara bi takan Deen ba ya wuce wajen zee dake jada baya ya damqo hannunta ya miqar daita tsaye yafara janta
Qara ta kwala tana tirjewa
"Deen! Help! Please!"
Jin hakan yasa Deen saurin miqewa tsaye yayi saurin binsu
Master besan dashi ba saiji yayi an fizge hannun zee din daga hannunshi Hakan yasashi juyowa yana kallon Deen dake riqe da zee din ta wani lafe a qirjinshi
Zuciyarshi ce taqara harzuqa Hakan yasashi kaima Deen naushi a gefen kumatu wanda yasashi fadawa can gefe
Qara zee tasaki a gigice tana binshi inda ya fada din tayi saurin duqawa gabanshi
"Deen!!" tafada agigice tana qoqarin dagoshi
Dagowa zaune Deen yayi dakyar yanajin gefen kumatunshi kamar ba nashi ba
Qara damqo hannunta master yayi da niyyar sake dagota, tirjewa tashigayi tana kuka sosai tana ruqo rigar Deen da dayan hannun
Qara fusata master yayi ganin yadda suke 6ata mashi lokaci
Jawota yayi da qarfi har saida rigar Deen data damqe da dayan hannun ta yage guntun kyallen yabiyota
Tirjewa tashigayi tana kuka sosai tana miqoma Deen da keta yunqurin tashi hannu
Dakyar Deen ya taso yaqara nufarsu yanajin inda master yakaimashi naushi na yin nauyi
Qara fizge hannunta yayi daga na master ya Jawota jikinshi ya rungumeta yana jada baya yana kallon master daya juyo shima yana kallonshi
Riqe kugu master yayi yana kallon Deen cikin rashin sanin abinda yakamata yayi mashi
"ka.. Kyaleta, please" inji Deen yana maida numfashi ahankali
Cigaba da kallonshi master yayi cikin takaici sannan ya kalli su alex dake kallon duk abinda ke faruwa Tundazu
"ku takaitamin shi" yafada yana maida kallonshi akan Deen din
Kamar kau jira suke suka nufi Deen gadan2
Damqe hannun Deen zee tayi jikinta na 6ari
"Deen mu gudu, they'll kill us" tafada cikin rawar murya
Kamar kau shawarar ta yake jira sai shima yaqara damqe hannunta suka juya suka fara gudu
"kai! Mubisu karku saki su tsere!" inji master din yana binsu suma suka maramashi baya
Gudu suke da dukkan qarfinsu suna jefa kafarsu duk inda suka samu
Sosai iskan dake kadawa yanzu da qarfi yake kawomusu tirjiya a gudun nasu don kadowa yake saitinsu sai jisuke kamar zai maidasu baya
Sosai Deen kejin effect din iskan ajikinshi don qirjinshi a bude yake sanadiyar yagan da rigar ta samu dazun
Haka dai yake daurewa suke gudun da dukkanin qarfinsu batareda sunsan inda suka dosa ba
Cikin wasu ciyayi suka samu suka lafe suna maida numfashi
"Zainab... Ruwa" yafada cikin maida numfashi
Saurin rufemashi baki tayi jikinta na rawa sannan cikin muryar rada tace
"ka rufamana asiri gasunan karsu jimu, kabari musamu mu ku6uta saimu samo ruwan"
Janye hannunta yayi daga bakinshi yana cigaba da maida numfashi
"ruwa...ruwan sama, yafara sauka"
Sai a lokacin zee ta lurada anfara yayyafi
"shhh it ok, please karka bari sujimu" tafada tana qara qamewa waje guda jin tafiyar su master gab
"no, doctor yace karna shiga ruwa... Mubar nan, am sick already" yafada yana rintse idanunshi yanajin yadda sanyi ke shigarshi har cikin qashi
Cak zee ta tsaya tana binshi da kallo cikin tashin hankali, ita harga Allah ta manta shaf da lalurar Deen
'innalillahi waina ilaihi rajiun' tafada cikin zuciyarta tana kallon yadda jikinshi ke dan 6ari, jijjiyoyin kanshi na bayyana
Saurin kama damtsen hannunshi tayi tana kiran sunanshi ahankali hankali tashe
Bude idanunshi yayi ahankali ya kalleta
Gani tayi idanun sunfara chanza launi zuwa ja ga siraran jajjayen jijjiyoyin dasuka fiffito a farin qwayar idanun
"Deen are you ok?" tafada cikin tashin hankali
Lumshe idanu yayi ya sake budesu yanajin yadda yayyafin da yanzu yaqara qarfi ke sauka ajikinshi
"mu... Barnan, please" yafada yana cije haqoranshi gamm
Ganin haka yasa ta kama hannunshi ta riqe gamm
"kana iya gudu?" tafada cikin rawar murya
Qara tamke idanunshi yayi ya bude yanajin jiri2
Kada mata kai yayi cikin qarfin hali
Qara tamke hannunshi tayi sannan ta taimaka mashi suka tashi suka fara gudu
Su master daketa bulayin nemansu Suka jiyo motsi a bayansu Hakan yasasun saurin juyawa
Su Deen suka Gani suna gudu Hakan yasa suma suka maramasu baya a tamanin
Gudu suke sosai da duk qarfinsu
Tun suna ganin gabansu har takai basa gani saboda qarfin da ruwan saman yayi
Kawai gudu suke suna saka qafarsu inda suka gani
Suna cikin gudu Deen ya fadi jagwab awajen Hakan yasa zee jan burki itama
"Deen! Deen! Katashi don Allah, you can do it! Please gasunan" tafada tana girgizashi cikin fitar hayyaci jikinta sai digar ruwa yake don sun jiqe jagab
Cije lower lip dinshi yayi jikinshi na rawa sosai
Yunqurawa yayi dakyar ya miqe yana jin kamar zai sake kifewa
Saurin kama hannunshi tayi tana qara damqewa suka cigaba da gudun Saidai kana ganin Deen zaka gane baya cikin hayyacinshi kwata2
Basuyi nisaba yasake yankan jiki yafadi yana maida numfashi dakyar
Durkushewa gabanshi zee tayi tana kuka sosai
"Deen! Deen!! Get up, are you ok?"
Rintse idanunshi yayi yana sauraron yadda ruwa ke bugunshi yana tuna gargadin da Dr yayi mashi shi da kaka
_*"yakamata ku kula sosai, a wannan condition din nashi idan yaqara samun wani attack din am sorry to say komai yana iya faruwa, ciki harda rasashi, ya kiyayi abinda zai tadomashi ciwon komai qanqantarshi, ya kiyayi wanka da ruwan sanyi, idan ana sanyi sanyi ya tabbatar ya kare jikinshi gareshi ta hanyar sa kayan sanyi, idan ana ruwan sama karya sake ya fita, yanzu damuna ce don allah a kiyaye, a kiyaye duk abinda zai qara tadamashi ciwon nan, please*_
Lumshe idanunshi yayi ya qara budewa yana jin yadda numfashinshi keyin sama sama
Sama sama yakejin kukan zee da sunanshi datake kira can kuma yaji motsinsu master dasuka qaraso wajen
Sake maida idanun yayi ya rufe yana numfashi ahankali
Zagayesu sukayi suna kallo kowanne na maida numfashin gudun dasuka sha
Kifa kanta tayi ajikinshi tana cigaba da kukanta ahankali
Takawa master yayi gabansu ya fizgo zee
Qanqame Deen tayi gamm tana kuka sosai
Janta yake amma yakasa 6an6areta hakan yaqara fusata shi ya dauketa da mari
Qara tasaki tana fadawa kan Deen, qara jawo hannunta yayi da qarfi saigashi ta taho batareda tirjiya ba Saidai bata ida miqewa ba Deen da idanunshi ke rufe ruff ya riqo dayan hannunta
Ja master yaqarayi amma ya riqe gamm yaqi saki saima motsi da idanunshi keyi alamun soyake ya budesu
Afusace master ya fizgeta da qarfi daga riqon Deen din sannan ya kalli su alex cikin bada umarni yace
"ku gama mun dashi!"
Nufar Deen da har yanzu ke qoqarin tashi zaune amma yakasa sukayi alex ya cakumoshi ya miqar dashi tsaye
"No! Dan Allah karku mashi komai baida lfy, please!" inji zee dake riqe a hannun master
Wani naushi alex yakaima Deen wanda saida yazube acikin ruwan daya taru qasa
Rufar mashi suka suna dukanshi takoina
Ihu sosai zee takeyi tana roqonsu su kyaleshi Saidai kamar zugasu take, bugu suke kaimashi takoina, tun yana iya yunqurin karewa harya kasa
Saida sukayi mashi laga2 sannan suka gyaleshi suka ja gefe suna maida numfashi
Sakinta master yayi Hakan yasa ta ruga da gudu wajen shi inda yake kwance jina2 ta durqushe agabanshi
Rufe bakinta tayi tana gunjin kuka ganin yadda sukayi mashi, jini duk ya 6atamashi kyakyawar fuskarshi
"innalillahi waina ilaihi rajiun" abinda tayita maimaitawa kenan tana kallon Deen dake kwance kamar gawa ruwa sai bugunshi yake
Qarasowa master yayi ya tsugunna gefenta shima yana kallon Deen
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 81