Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a subject din don naga kamar kina fargabar faduwa sai nayi maki tayin Hakan kuma kika kar6a hannu bibbiyu, anan kuma naqara tabbatar da rashin girman kanki" "ahankali ahankali naita fuskantar halayenki wanda sai nakusa dake kawai zai san su saina fuskanci kyawawan halayenki sunfi marasa kyan yawa Daga baya kuma na fuskanci ashe rashin qawayen kirki yasa kike wasu abubbuwan ganin daga baki shawara akan gabarki da mr ibrahim kika nuna damuwarki kema akai kika kuma nuna kinason ku shirya, Hakan ya tabbatar min cewa eh daga qawayen ne don a dan lokacin damukayi tare naga kamar su babu ruwansu da karatu, they're not serious at all shiyasa nima na kawar da hankalinki daga kansu ta hanyar baki lokacina da gudunmawa gwargwadon ikona don ganin kinyi nasara" Dakatawa yayi ya dago yana kallonta yaga itama shi take kallo babu ko kyaftawa "Bansan sadda nafara sonki ba, abinda nasani shine kina burgeni amma bansan sadda Hakan ya rikide zuwa so ba. Na fuskanci Hakan ne a zamanmu na asibiti, a lokacin nasan na kamu da makauniyar sonki, a lokacin da aka sallamemu Sainaji kamar Kada a sallamemu kamar muyi ta zamanmu a asibitin muddin zaki dinga zuwa sau biyun nan ina ganin ki, ranar da aka sallamemu sosai jikina yayi sanyi, najini so empty kamar wanda kika tafi mashi da wani abu mai matuqar muhinmmanci...." Cigaba yayi da bata labarin yadda yayi missing dinta kamar yadda nakawo a last page har kawo ranar datazo gidansu da yadda beji dadin yanayin datazo dashi ba da kuma fasa niyyar amsar number ta dayayi, ya gangaro zuwa kiran dayasa kaka taita yiwa mummy don yaji muryarta har zuwa lokacin da akace tayi tafiya har zuwa lokacin resuming dinsu da abinda yafaru har zuwa kawo yanzu dasuke zaune. Shiru yadanyi saikuma ya saki Ajiyar zuciya "Zainab, am not begging love From you, nasan bazan ta6a samuba saboda bankai matsayin Hakan ba, Kiyi hqr naci amanar abota, kin riqeni a matsayin aboki nikuma na chanza tawa manufar gareki" "meyasa kake ganin bakakai matsayin ba?" inji zee karo na farko tunda suka zauna "saboda ta koina akwai banbanci atsakanina dake" "meye banbancin?" inji zee again "zee, ke diyar masu kudi ce, you're born with a sliver spoon in your mouth, nifa?" Dan murmushi tayi sai ta kada kai tace "bayan wannan fa?" Shiru yayi yana tunani saikuma yace "family, kinada families masu sonki sosai, nifa? Kaka ce kawai" "kakan ba family bace? Kaka kawai ce? Soyayyar kaka ba soyayya bace?" Shiru yayi yana kallonta Ajiyar zuciya ta sauke tace "tunda muka zauna nan kake fadamin dalilan dayasa kafara sona mun dauki kusan 30mins kana lissafosu dakuma bayyana yadda kakeji aranka game dani amma dakazo akan dalilan da zaisa ka haqura dani sai naga ko minti daya bakayi ba, hasalima duka dalilai ne guda biyu kacal, marassa tushe" Shiru yayi still yana kallonta batareda ya iya cewa komai ba "miye banbanci na dakai? Meye banbancin mai kudi da talaka, atsakaninmu mu yan Adam ke akwai banbanci amma a wajen Allah fa?" Girgiza kai yayi sannan ahankali yace "babu... Sai wanda yafi tsoron allah" Murmushi tayi sannan tace "families kuma, dama kasan wasu families dinane banida labari? A tunanina mummy da daddy kawai ka sani koko don kai bakadasu kake jin kamar bakadasu? Daga sama ka fado? Kaima dole kanada baba da mama kuma sun rasu, ba Haka kaceba? Yakuma za'ayi kace bakadasu? Ina kaka? Ita ba family bace? Ko bata kai matsayin a kirata da Hakan ba?" Shiru yayi nan ma yana jin zuciyarshi na wani iri "soyayya babu ruwanta da mai kudi, marar kudi, mai kyau, marar kyau, yare, qabila, addini... Babu ruwanta Makauniyace, marar dan jagora duk abinda tasamu kaimashi wafta take ta damqe gamm Mai so na asali bazaiyi fargaba akan banbancin komai ba tsakaninshi da abinda yake so zai soshi ne yakuma tsaya tsayin daka akan Hakan no matter what Amma tunda abotarmu ne bakason ya wargaje, fine mu tafi a Hakan, Abokai" tafada tana murmushi Saita fara yunqurin tashi, saurin rigarta tashi yayi yana cewa "yes, yes nagane, nagane Hakan Zainab, I was so stupid to think of that, a lokacin babu abinda nake hasasowa idan na tunkareki sai rabuwa, rabuwa na har abada kuma Hakan shine abu na qarshe da zanso yafaru damu because... I LOVE YOU" Dagowa tayi tana kallonshi "yes I love you, I love you! I love you!! Please give me a chance, give me a space no matter how tiny it is in your heart, please love me back, give me a chance... Please" Tunda yafara take kallonshi babu kyaftawa tanajin zuciyarta na kumburi don shauqi Kallon pleading face dinshi tayi data koma abin tausayi saita miqe ta dauki jakkarta da wayarta ta rataye jakkar Binta da kallo yayi tayi zuciyarshi na bugawa da qarfin gaske Dagowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo babu kyaftawa "idan ban baka space ba a zuciyar tawa fa?" "zan roqi kibani dama nayi jaraba kutsawa har nasamu nasarar yin Hakan watarana" yafada ahankali "idan nabaka kuma fa?" "zanfi kowa farinciki a duniya" yafada still yana kallonta zuciyarshi kuma bata bar bugu ba Wani kayattacen murmushi tayi sannan tace "Go ahead, kafi kowa farinciki a duniya" Saita juya ta nufi hanyar fita Dan yamutsa fuska yayi cikin rashin fahimta Yafi kowa farinciki kuma? Wani abu ya gifta mashi a qwalwa Yace zaifi kowa farinciki a duniya idan ta amince dashi Kuma tace yafi kowa farincikin Kenan? Ta amince? Dagowa yayi saurin yi saigani yayi harta fice "OMG! Ta amince! Ta amince!!!"... ✍️ Ummin fasihu πŸ§šπŸ»β€β™€οΈ? 8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *πŸ™πŸ»β€β™‚οΈDEEN πŸ™πŸ»β€β™‚οΈ?* *042* *DEEZEENπŸ’ž* Saurin tashi yayi ya fita Saidai ya waiga ta koina babu ita. Duba agogon hannunshi yayi sai yaga har 1pm ta dan gota kuma dama tanada lecture qarfe 1 Murmushi yayi ya saka hannu yana dan yamutsa gashin kanshi ya nufi hanyar department dinsu. Tun daga nesa ya hango alamun class din karatu ake amma dukda Hakan be hqr ba ya zagaya ta dayan side din class din yafara bin bango ahankali kamar wani qwararren dan F πŸ˜’ Koda yazo wajen window saiya leqo ta gefe ahankali yana scanning din iya inda yake iya hangowa amma be ga ko wulginta ba Hakan yasashi yin qasa ya rarrafa don kar aganshi ta window yawuce dayan windown sannan ya miqe ahankali ya jingina da bango yasake leqawa ahankali ta gefen windown Qara bin iya inda zai iya gani da ido amma be ganta ba Har zai qara gaba sai kuma yaga windown gaba ai na masu zama baya ne kuma ya tabbata Zainab bata zama baya Hakan yasa yaqara dan leqawa yana dan wurwurga idanu ta koina Saikau gashi ya ganta a row din tsakiya zaune Littafi kan desk dinta ta buga tagumi da hannu daya tana taunar gindin biron hannunta hankalinta akan lecturer din Murmushi ne ya su6uce mashi saiya qara gyara tsayuwa yana cigaba da leqenta Jin wannan feeling din tayi wanda takeji idan yana kallonta Saidai bata wani maida hankali akai ba don tasan bayanan Tunani tayi ko ya gane hausarta dazu? Sai kuma tayi murmushi tana cigaba da taunar biron hannunta, allah yasani yau tana cikin farinciki, farinciki marar musaltawa Kamar ance ta waigo ta windown gefen damarta sai taga kamar abu na leqowa yana komawa Hakan yasa ta kurawa wajen ido Shikuma ganin ta kallo wajen yasashi dan qara leqowa sosai yadda zata ganshi Wara idanu tayi ganin shine sai kuma tayi saurin kauda kai tana kallon lecturern dake koyar dasu Lallai ma Deen, baya tsoron ko aganshi ma? Tambayar da tayiwa kanta kenan Haka aka cigaba da lecture din rabin hankalinta akan lecturer rabi kuma akan Deen Duk lokacin da zata juyo ta kalloshi sai taga yamata murmushi ya daga mata hannu saita kauda kai kuma Ahaka har lecture din ya qare lecturern ya fita Ganin Hakan yasashi zagayowa da sauri shima don tarbonta Zee daketa sauri ta fito itama taci karo dashi a waje "har kun gama?" yafada yana qarasowa yana mata murmushi Murmushi kawai itama tayi mashi tana lura da yadda wasu ke kallonsu "kai zan tambaya, harka gama la6en?" tafada tana nufar hanyar fita Shima Binta yayi suka jera yana cewa "eh, amma fa nasha wuya, bayana ciwo" yafada yana 6ata rai Ta6e baki zee data kasa hada ido dashi tun dazu tayi tace "dakyau" "hakama zakice?" yafada yana marairaicewa Murmushi kawai tayi ta kauda kai, shi bemasan kunyarshi take jiba Tare suka nufi masjid don har ankusan kabbarawa Kowa nashi nashen yayi, basu dade da shiga ba aka tada iqama Kusan tare suka fito don Deen na fitowa itama tana fitowa Tare sukaje cafteria sukayi siyayyar abinda zasu dan ci kowa daidai aljihunshi sannan suka wuce usual Wurin zamansu idan basa library Zama sukayi Deen yafara bude masu ledar chips dinshi suka shiga ci tare Shiru wajen ya dauka na wani lokaci bakajin komai sai sanyayar iska dake kadawa sai kukan tsintsaye dake kai kawo Deen daga kai yayi yana kallon wasu balbelu dasuka zo suka wuce ta gabansu "look" yafada yana nuna mata da yatsa BΓ―Γ±su da kallo itama tayi "suna tayamu murna suma" yafada yana murmushi Itama saita tsinci kanta da murmusawa "the birds are also singing, suma suna tayamu murna... Kalli can" BΓ―Γ± inda ya nuna tayi da kallo sai taga yan moli moli ne guda biyu mace da namiji bisa kan wani reshen bishiya "A good example of us, right?" yafada yana kallonsu yana murmushi Itama su take kallo fuskarta dauke da murmushi, ahankali tace "so beautiful" "yes, love is beautiful and amazing" yafada sannan ya maido kallonshi akanta Hakan itama yasa ta juyo tana kallonshi shima "Nagode Zainab, Nagode da kika bani damar jan ragamar zuciyarki, I promised you bazaki ta6a danasaniba. Zan jagora agareki, jagora dazai jagoranceki zuwa duniyar farinciki, zan iya sadaukar da komai akanki zee na, komai" "promise" inji zee ahankali "promise you'll never let me down, no matter what" tafada tana kallonshi tanajin hawaye na neman taruwa a idanunta Kama hannunta yayi cikin nashi ya matse "nayi, nayi alqawari my zee, I'll never let you down insha allah don letting you down is equal to letting myself down, down to grave" " If I could chose between loving you and breathing I would use my last breathe to say I LOVE YOU." Sai kuma yayi interlocking din yatsunshi da nata ya dago hannun yana kallo Itama kallonsu tayi dukda tasan be dace ba Amma takasa hanashi Murmushi yayi ya kalleta, itama shi ta kalla not saying anything "yanzu nagane dalilin space dake a tsakanin yatsu na da naki Anyisu ne don yatsunmu su maye gurbinsu, kamar haka" yafada yana dan daga hannayen nasu Murmushi tayi sosai tanajin wani dadi na ratsa zuciyarta, Gaskiya soyayya dadi gareta musanmman kaso aka soka, wayyo dadi 😍 Zame yatsunta tayi daga nashi ta duqa zata dauki juice din gabanta Saurin riganta yayi ya dauko mata ya miqamata "ki dinga fadamin duk abinda kike so idan ina kusa, kibar wahalar da kanki, feel free wajen sakani komai, dama ni errand boy dinki ne" Murmushi tayi kawai ta amsa ta dan kur6a don harya bude mata Haka sukaita zama wajen Deen nata tarairayarta, wasu abubbuwan ma har mammaki yake bata don batasan ya sansu ba, a ganin ta babu abinda ya iya a faggen love, batasan yan shiru shiru dinnan akwai iya buga loveπŸ₯° Suna ahaka har drivernta yazo Saida ya rakota har motar, kafin bala yama zagayo shi ya bude mata kofa, babu abinda ya dameshi ko lura da kallon da daidaikun mutane ke masu beyi ba Shiga zee tayi ya sunkuya ya maida mata yar jelar rigarta da bata ida shigewa ba sannan ya rufo mata kofar ahankali Bala daya saki baki yana kallon ikon allah ya lalla6a yakoma cikin motar gulma fall ranshi Sunkuyowa yayi jikin glass din Hakan yasata wining din glass din qasa Murmushi suka yima juna "bye.. Ki kulamin da zuciyata" Murmushi tayi sannan tace "nima haka" "kema me?" Blushing tayi tana dauke kai tace "yadda kace" Murmushi yayi "to shikenan, qila maganar ke miki wuya amma na gane ai, zan kula miki daita sosai and please.. A taimaka a daga wayata yau.. Please" Kallonshi tayi taga yadda yawani marairaice Murmushi kawai tayi tafara wining din glass din motar sama tace "bye" "bye.. Godiya nake" Jin an tada motar yasa yadanja da baya yana kallonta dukda baya hangenta amma yasan itama shi take kallo Ganin xa'aja motar yasashi fara daga mata hannu yana murmushi har motar ta daga ta nufi hanyar gate Bebar daga hannun ba har Saida suka fita daga school din Ajiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyarshi sakwat kamar an rabashi da wani mai nauyi aka, tabbas ya yarda zee ce farincikinshi kuma idan yana tareda ita zaiji dadi da sallamar zuciya da ruhi. Ajiyar zuciya itama zee tayi sai takoma jikin kujerar motar ta lafe tana murmushi, murmushin dayaqi barin fuskarta tun jiya Wani irin dadi takeji marar musaltawa, she can't believe yau ita Deen ke furtawa kalaman soyayya, she can't believe yanzu Deen natane Dama kenan shima yana sonta tuntuni shine baya gwadawa kwata2? Kai amma ya gama daita, duk wannan sleepless nights din da damuwa ashe wanda takeyi don shi shima tana can a ranshi? Dakau tasan da Hakan da ba zata ta6a damun kanta ba irin haka, amma nevertheless yanzu ma alhamdullilah, ta godewa allah daya kawomata abin da sauqi, dama wannan itace babbar matsalar wato kaso aqi sonka amma muddin soyayyar ta kowacce bangare ce to duk abinda zai biyo baya mai sauqi ne. Ahankali ta dago hannunta tana kallo _*yanzu nagane dalilin space dake tsakanin yatsu na da naki*_ _*anyisu ne don yatsunmu su maye gurbinsu, kamar haka*_ Murmushi tayi tareda runtse hannun ta lumshe idanunta cikin jindadi A bangaren Deen ma bata dade da tafiya ba shima yafito feeling himself on top of the world Be dade ba yasamu abin hawa suma suka shilla Koda ya dawo gida kaka tayi mammaki sosai ganin yadda kai kawo cikin nishadi, murmushi yaqi barin fuskarshi sa6anin dasafe daya fita kamar yayi kuka yana komai sumi sumi Koda ta tambayeshi lfy? Ko tsintuwa yayi? Sai yakama Dariya kawai yana cewa eh tsintuwa yayi, a zuciyarshi kuma yace *Tsintuwar soyayya ba* Haka wadannan bayin allahn suka qarasa Wunin su cikin nishadi da annushuwa kowanne Saida aka ganemashi a gida don fara'ar yau ta dabance πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– "wow! Wow!! Wow!! Dole na kwaso shokiiiπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ" inji saqon Feenah via whatsapp Dariya zee tayi afili sannan tayi typing "kai Aunty, yaushe kika zama motar yansanda?πŸ˜†" "har tarakta ma ina iya zama, wayyo dadi πŸ’ƒ amma na tayaki murna πŸ₯°" Murmushi zee tayi sannan tace "thanks Aunty 😍" "shikenan kuka yaqare ko 😏" "dama wani ke kuka 🀨" "qaniyarki, shegiya kin manta lokacin da kike kuka hawaye da majina kina wlh Aunty idan be soni ba mutuwa zanyi😩 yar rainin hankali kawai πŸ˜’" "😳kai Aunty yaushe akayi haka? Wlh adai dinga tsoron allah 😫" "kyaji dashi... Yanzu shikenan harkin amince? Bawani jan aji ba komai?πŸ˜’" "shi ajin wani kalan abinci ne πŸ™„" "😦 kinci bashi yarinya 😠" "babu komai na biya idan muka hadu😜 ina alarrama yaya Auwal?" "waya bashi muqamin alarramancin πŸ˜’" "ai basai anbashi ba, alarrama ne πŸ˜† alarrama ango ba🀣🀣" "kutt! Ni tsarar wasanki ce 😬" "😝😝😝" "zaki gane bakida wayau ne 😠" "πŸ‘πŸ‘tuba nake uwata ta kaina" "zamu Hade ne zaki fadamin yaushe muka fara wasan jika da kaka dake 😠" "haba Aunty ta ta kaina, ai babu mai jin kanmu insha allahπŸ₯°" "πŸ˜’πŸ˜’ayi kema azo a aurar dake don naga wani tashen balaga kikeji kwanan nan" "can't wait πŸ˜πŸ’ƒπŸ’ƒ" "😳marar kunya?" "πŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ˜„" "😞Allah ya shirya" "Amin summa amin Aunty ta 😜" Kira taga ya shigo wayarta *D❀️* taga ansa Hakan yasata dan murmusawa Daidai nan message din Aunty Feenah yasake Shigowa "ai yanzu tunda hankali ya kwanta dole ki nunama kowa kin qoshi" Murmushi tayi sannan tayi saurin typing "eh babu komai😜, Saida safe" "tun yanzu?" "shine yakiraπŸ™ˆ" "yar isss lamiyaπŸ˜’" Dariya tayi ta kashe datarta lokacin har kiran ya tsinke amman nan take wani kiran ya shigo Murmushi tayi Saida takusan tsinkewa sannan ta daga, saita tsinci kanta da kashe murya wajen yin sallama Wata nannauyar Ajiyar zuciya Deen ya sauke daga dayan bangaren sannan ya amsa sallamarta sannan ya dora da "nayi tunanin har kinyi barci wlh" Murmushi tayi "kamar kaza?" "who knows" Murmushi tayi ta janyo pillow qirjinta ta rungume tace "ina kaka ta?" "tayi barci nasan takai kaduna yanzu" Yar Dariya tayi tace "bakada kirki, a gaban aminiyar tata kake fadin haka?" "oh haka ne fa ashe ku aminan juna ne" "sosai ma" inji zee Murmushi taji yayi sannan yace "banida lfy, ko ki kira kiji ya nake" ga yanayin dayayi magana tasan kumbura fuska yayi Dan wara idanu tayi tace "bakada lfy? Meke damunka?" "kewa" Dan daga gira tayi sannan tace "kewa? Kewar wa?" "Kewar wa? Banda ke" Murmushi tayi "duka yaushe muka rabu" "duka yaushe ma zakice? Tunfa 3" "3 din, duka awa nawa?" "O'O! Kenan ni bakiyi missing dina ba" yafada a marairaice Yar siririyar Dariya tayi tace "nayi amma kadan" "babu komai, what matters shine kinyi, zan taimaka miki nazo school gobe dawuri don ki ganni kiji sanyi a ranki" yafada cikin sigar tsokana "wasa ma kenan, dani dakai wa zai ga wani yaji sanyi?" "dani dake" Sai sukayi Dariya atare Hira suka shiga yi mai cikeda nishadi da raha Sai gashi wasa wasa har sukafi mintuna talatin sai anan kudin Deen suka kare Bugamashi zee tayi ita kuma don Saida firar ta dauko sugar katinshi ya qare Sai gashi sune har 12 dare suna fira kwata2 sunma mance a wace duniyar suke kawai basa tunawa da kowa da komai sai kansu Tun zee na iya qoqarin bude idanunta idan suna rurrufewa alamun barci har barcin ya saceta batareda ta farga ba Jin saukar numfashinta yasashi sanin tayi barci Saidai kuma yaqi kashe wayar saima ya danna recording yana daukar saukar numfashi a zuciyarshi kuma yana hasasota tana barcin, yasan barci zai mata mugun kyau, zaiso ganinta idanunta Lumshe bata komai sai sauke numfashi ahankali, yasan sosai fuskarta zata qara Fiddo cuteness dinta Katse kiran yayi ba don ya gaji ba sai don tunawa dayayi kudinta ne ke qonewa a banza Koda ya katse kiran kasa barcin yayi sai juye juye yakeyi Firarsu yake sake yin bitarshi a zuciyarshi yana jin wani shauqin sonta na qara fizgar zuciyarshi Ahaka har shima barcin ya daukeshi batareda ya shirya ba. ❀️❀️❀️❀️❀️❀️❀️❀️❀️❀️ Soyayya sukeyi tsaftattaciya wanda ya kunshi kulawa da tarairaya a kowanne bangare Zee bata bar soyayyar ta zama boring ba ta hanyar yin dunkum, itama tana nuna mashi kulawa da soyayya tsantsa dukda ba wai rawar kai takeyi ba, komai tana yinshi ne stylishly da kuma class. A school tun ana zargin soyayya suke har suka tabbatar da Hakan don a relationship dinsu babu batun wani 6oyo ko kunya, don wani lokacin ma zee ce ke dan jin kunya amma shi baya kunyar nuna mata kulawa a koma inane. Duk inda kaga daya to dayan na wajen except idan daya yashiga class yabar dayan Idan suna tafiya Deen ne ke Rataya jakkar zee ita kuma ta rungume littatafanshi Da farko daya fara amsa jakkarta hanawa take don cewa take tayaya zai daukar mata jakka kamar wata mijin Hajiya Amma nacinshi dakuma cewan dayake dama ai mijin hajiyan zai zama yasata dinga bashi itakuma saita amshi littatafanshi ta rungume A fannin waya kau ba dama Bata ta6a tunanin Deen ya iya waya ba sai a dan wannan lokacin don sa6anin da da idan sunyi gudun tsiya suyi wayar five minutes to yanzu wayar awanni suke kuma su rabu bawai don firar ta ishesu ba Deen ke fara bugowa sai sun cinye katinshi sannan ita ta bugo su ida wayar. A fannin text messages kau zee har tasan lokutan shigowar text dinshi a wayarta Idan ta farka da asuba da text dinshi take fara tozali, idan ranar akwai school kafin ta fito sai yayimata na fatan isowa lfy, idan kuma suka rabu daga school saiya daidaici sun isa gida zai mata na fatan sauka lfy, da daddare ma haka Itama tana yimashi Saidai ba kamar nashi ba barkatai, tana yimashi daya kowacce safiya, sai ranar juma'a kuma tayimashi na barka da juma'a bayan an taso daga sallar juma'a Zee bata yarda da yin dunkum ba a soyayya kamar yadda Mafi yawan yanmata keyi Idan be kira ba ita tana kiranshi, idan suna fira tana co-operating itama batayi mashi shiru Daga eh sai A'a sai hmm Tana Sakin jiki suyi labari na raha Saidai kuma tana matuqar kama kanta sosai wajen ganin bata bar wata 6araka tashigo a soyayyarsu ba Akwana a tashi saigashi bikin Feenah sai qara matsowa yake, kowanne bangare an shiga hidima ka'in da na'in Amarya sai shan gyara take ciki da bai taqara fitowa tass fess kamar ka wanke hannu kafin ka ta6ata Mummy da zee sai biki saura kwana hudu suka wuce Ruma Anan zee taita santin kyaun da Feenah tayi tana tsokanarta da itama wacce tayi mata gyaran zatamata itakuma saita hau masifar ta rainata ta maidata kakarta Bikin ba'ayi wani bidi'a ba sai dinner daza'ayi ranar daurin aure da daddare Washegarin ranar da suka isa zee da qawayen Feenah data shige cikinsu tsamo tsamo dukda duk sun girme mata suka wuce saloon Idan ka ganta cikinsu sai kayi zaton tsararraki ne don kusan babu mai girman jiki sosai cikinsu gashi ta iya mu'amalla da mutane musanmman yan gayu irinta shiyasa suma suka jiki sosai daita don tun a ganin farko yanayinta da gayunta yayi musu Daga saloon suka wuce shopping bags da shoes dazasuyi amfani dashi da yan abubbuwan da ba'a rasaba. Daga nan suka dawo gida Ranar daren biki kuma masu qunshi sukazo gidan inda aka yini ana yin qunshi, ita amarya dama mai qunshinta ta musanmman ce don ita kadai dama zatayi mawa Haka aka xauna a garejin gidan kasancewar yanada girma sosai aka baje anama amarya da qawayen amarya qunshi sai fira ake ana shewa na irin wayyayun mata Qawayen Feenah kau sai tsiya suke mata ganin yadda Auwal ya addabeta da kira, bini bini sai ya kira Hakan yasa wata qawarta ta amshe wayar daya sake bugowa cikin barkwanci tace allah idan yasake damunsu saisu fasa bashi amaryar su riqe abinsu Dariya yayi yana cewa tuba yake kanshi abisa wuya, idan suka hanashi ita ai Hakan daidai yake da hanashi numfashin shaqa, ya tuba bazai qara ba sannan yace to don Allah abata yaqara jin muryarta yayi alqawarin daga wannan bazai qara takura musu ba Dariya dik sukayi sannan qawar tata ta karama Feenah da duk ke jinsu wayar a kunne kasancewar hannunta duk qunshi ne Suka danyi magana wanda babu wanda yaji abinda suke cewa Saidai dariyar datake ahankali sannan sukayi sallama ya katse kiran Zee daga inda take zaune ana zana mata na qafa jaa take kallon dramarsu cikin burgewa Sai yanzu taqara gano hikimar Feenah na amincewa da Auwal don ko yanzu ka santa dashi to saika lura da tsananin so da kulawar dayake nunamata kuma tana ji ajikinta insha allah zata soshi don yana kyautata mata kuma zuciya kowacce iri ce tana tsananin qauna da ganin girman mai kyautata mata Hakan yasa ta tuna da Deen dinta, basu dade da gama waya ba yana complaining shi ta tafi tabar shi cikin kewarta tana mashi Dariya akan cewa ba gobe zaizo ba (dayake ta gayacceshi daurin aure, Aunty Feenah da kanta tabada katin I.v din abashi don tsakani da allah mutumin yayi mata kuma muddin kaji Feenah ta yabi abu to karka bincika abin yayi πŸ’―) Dakyar tasamu sukayi sallama bayan ta fadamashi qunshi za'ayi mata Basu suka gama qunshin ba gabadaya sai can da marece liss kowanne sai santin nashi qunshin yake don ba qarya masu qunshin qwararru ne *WASHEGARI* Rana bata qarya... πŸ’ƒ Yau su Hajiya Feenah za'a amarce Gida ya cika maqil ya cinkushe takoina, duk wanda zaka gani is very busy musanmman su mummy da matan kawunnan zee. Su Umma ana bedroom dinta an qame bisa gado tasha dakakkiyar shaddarta dataji aiki ajiki ga daurin dan kwalin da zee ta dotsana mata mai kyau, anci gayu ansha lalle tsohuwa ta fada kwata, kukau bikin auta guda? πŸ˜† A bangaren Amarya kau tana dakinta dake cike da qawayenta da yanuwa yanmata Kowa sai shiri yake don an kusan daura auren Amarya ana gefen gado taci kwalliyarta itama cikin ankon bikinta, fuskar nan tasha makeup ga wani dauri mai shegen kyau da aka murzamata sai hasketa masu daukarta hotuna keyi da flasher. Zee ce

Chapter 32 of 81