taga dandazon mutane antaru Ana kallo
Batareda magana ba tashiga kutsawa ta tsakanin mutane har tasamu ta qaraso gaba
Wani tagani riqeda kwalar rigar Deen yana janshi yana Dariya
Jitayi ranta ya sosu ganin yadda Deen keta qoqarin kwatar kanshi amma yakasa ga su can juice data aikoshi watse a qasa
Batasan ya akayi ba Kawai sai ganinta tayi gaban mutumin tasa iya qarfinta ta tureshi
Kasancewar T.j be shiryama haka ba sai yatafi yayi baya2 Alex dake bayanshi yayi saurin tareshi, nan aka shiga kallon kallo tsakanin zee dasu tawagar master
Mutanen dake wajen yan kallo da duk aka rasa wanda zai ta6uka komai tundazu sukaji wani irin dadi ya ratsasu kasancewar dama kowa ranshi bemashi dadi da abinda ke faruwa, tsorone kawai ya hanasu motsawa, karon farko da zee tayi abinda students sukaji dadinshi
"ku wadanne irin dabbobi ne da bakusan abinda kemuku ciwoba? Me yayi muku zaku tareshi a hanya kuna shaqoshi kamar kunsamu wani dan taure?!" tafada rai a matuqar 6ace
"ke malama ki kiyaye abinda harshenki zai furta tun kafin in juyamaki fuska takoma baya yanzunnan" inji T.j da shima ranshi ya 6aci sosai
"go ahead mana! Ka juya din, dama kayi Kama da arnan dajin qarnin farko, so dan kayi hakan ba komai bane, saidai zee tafi qarfin a ta6amata Koda tip din akaifa ne duk wanda yayi gigin haka ya shiryama baquntar lahira!" tafada tana nunasu da yatsa
Alex da dama yana ciki daita ya hayyayako yace
"ke eazy fa, acikinmu uban wa kikaga yayi Kama da tsararki anan?! Ko dan kinga Ana daga miki kikeson wuce makadi da rawa, To wlh kiyi gaggawar shiga taitayinki tun kafin na lahira yafiki jin dadi" yafada yana zazzare jajjayen idanunshi
Ita yakewa warning amma mutanen wurin sukaji tsoro don sai zare idanu suke
Wani kallon uku saura kwabo ta watsamashi tace
"kai kuma daga ina? Person dey talk baboon dey answer, ko anan kaga masu irin siffarka ne?"
Alex zai sake magana master da tunda aka fara abin yazama dan kallo yayi saurin dafa kafadarshi ya dan kalleshi fuskarshi dauke da wani munafikin Murmushi yace
"Baaasar mana"
Sannan yajuyo kan zee daketa watsamasu mugun kallo tana huci shikau Deen yana bayanta ba baka sai kunne
Qarasowa yayi gabanta ya kwantar da murya yace
"Baby.. Kiyi hqr, basusan dan uwanki bane, hakan bazai qara faruwa ba"
Duk yan kallon wajen hangame baki sukayi cikin tsananin mammakin abinda yafito daga bakin master
Itakau zee Yatsine fuska tayi tana mashi kallon sheqeqe tace
"waye babyn? Kuma ba Dole sai dan uwana ba, su kingin mutanen basuda freedom akace muku? Bakuda aikin yi sai neman magana a school kun gagari kowa, kowa tsoronku yake and you're proud of that har kuna fitowa kuna nuna hakan, this school is for learning kuma saboda karatun Kowa anan ke zuwa, idan ku jagaliyanci kuka qware akai why not kutafi tasha da dandalin qauraye instead of coming here kuna harassing innocent souls" tafada kai tsaye babu ko digon tsoro a tattare daita
Daga kallon mammaki ya sauya yakoma na tsoro a fuskar yan kallo suna ganin abin kamar almara wai wata ce ke tsaye gaban the whole Master tana gayamashi irin Wannan maganar
Tare su Bash dasuka yunquro yayi da hannuwa yana Murmushi sannan yasake kallon zee dake binsu da disgusting look yace
"kiyi hqr, hakan bazata sake faruwa ba, kuma ku bata hqr" yafada yana kallonsu Alex
Alex zaiyi magana yayi mashi wani kallo yace
"kubata hqr nace!!" yafada a tsawace har saida mutane suka Girgiza including zee da Deen dashima be qaunar tsawa ko kadan
Ganin 6acin rai qarara a idanuwanshi yasasu Kama kansu suka juya ga zee dake qoqarin saita nutsuwarta daga firgicin da tsawar master ya sata suka bude baki kamar masu ciwon baki suka bata hqr zuciyarsu na tafarfasa
Wannan embarassment din dame yayi Kama? Ace su kebada hqr ga yar tatsitsiyar yarinya a bainar jama'a?
Maida kallonshi master yayi ga zee yace
"kinji sun baki hqr, kiyi hqr hakan bazata qara faruwa ba"
Yatsine fuska tayi tace
"ni sukai wa laifi daxasu bani hqr? Shi da sukayi wa laifi shi zasu ba hqr" tafada tana nuna Deen dake bayanta still
Kallon Deen master yayi sannan ya kalli su Alex yayi musu magana da ido akan suyi yadda tace
Zuciyarsu kamar zata Fashe don takaici amma babu yadda suka iya Dole suka bashi haqurin
Kafin ma su rufe baki sai ganin wani school authority sukayi tsulum cikinsu yafara tambayar ba'asi
Kafin wani ya bude baki zee tayi caraff ta amshe da
"sir yanzu abinda akeyi a school dinnan yadace kenan? Ace bakada freedom of walwala yadda kake so saboda tsirarun tsageru dasuka yiwa mutane karan tsaye suka yimusu shamaki da kwanciyar hankali?"
"meya farune?" inji school authority din
Cikin zaqalqalewa tace
"sir, Wannan mutumin ne ke tafiya yadawo daga cafteria kawai besan hawa ba besan sauka ba suka tareshi suka watsar mashi da kayan da yasiyo, kalli ka gani..." tafada tana nuna juices dake watse a qasa
"hakan be ishesu ba suka Kama mashi kwala suka shiga faffala mashi mari suna jijjigashi duk don sunsan babu mai iya takamasu burki a school din, yanzu don Allah Ahaka kukeso wasu suyi sha'awar shigowa school dinnan bayan sunajin labarin cin kashin da akewa students?" tafada cikin haqiqancewa
Kafin school authority din yasamu damar amsawa sukaji Deen nacewa
"O'O! Wannan ba gaskiya bane"
Duk juyawa akayi gareshi Ana kallonshi baki sake
Be damu da yadda akayi mashi caa da idanu ba ya cigaba dacewa
"babu kyau qarya, kakata tace qarya haramun ne don Annabi Muhammad (s.a.w) yace *Iyakum wal kazziba, fa'inal kazziba yahdi ilal fujura, fa'inal fujura yahdi ilan-narr*
Ma'ana *na haneku dayin qarya, domin ita qarya tana kaiwa ga ta6ewa, itakuma ta6ewa tana kaiwa ga wuta* don haka Mud queen kiji tsoron Allah ki daina qarya"
Waro idanu tayi sosai π³ tana kallonshi speechless
Sauran yan kallon ma Wara nasu sukayi suna kallonshi baki hangame while wasu dasuka sanshi suka san halinshi suka dafe kai cikeda takaici π€¦π»ββοΈπ€¦ββοΈ?
"mene?" tafada cikin tsananin mammaki
"cewa nayi qarya ne, basu mareni ba kuma basu jijjigani ba, kawai nine nataho ban gansu agabana ba na bangaje wancan baqin π±πΏββοΈ? wayarshi tafadi shine ya riqemin kwala yace wanene ni dazan bigeshi? Nace mashi nine Deen kuma ban sani ba na bigeshi shine yace saina biyashi wayarshi ko yayi tsirena, shine nace banida kudin biya shine ya riqemin kwala yace saina biyashi wancan mummunan π©πΎβπ¦²natayashi suna wata irin magana suna Dariya" yafada innocently cikin son kare su Alex data shirgama qarya
Duk sakin baki akayi harsu Alex din Ana kallon ikon Allah yayinda ran zee yayi mummunan 6aci
"kai ni zaka cewa maqaryaciya don na kareka?!" tafada cikin tsananin 6acin rai
"ni banyi qarya ba, ba wani Marina dasukayi ki tambayi mutanen nan ai suna wajen keda kikazo daga baya ma?" yafada cikin son kare Kanshi
"kai!!!" tafada a fusace tana yowa Kanshi
Hakan yasashi saurin 6oyewa bayan master yana cewa
"O'O!" Baki a tunzure
Duk Dariya hakan yabasu hakan yasa suka shiga yinta harda authority din daya fuskanci komai Wato ita ta kareshi shikuma ya yarfata
Ganin wurin ya kacame da hayaniya yasa authority din cewa
"ya isa! Ya isa!!"
Saida ya samu akayi shiru sannan yace
"To yanzu koma dai menene Aliyu (Alex) baku kyauta ba tunda yace ba dagangan ya bigeku ba be kamata kuyi mashi hakaba ku dinga uzuri... Ke kuma kibar bada shaida akan abinda baki saniba, kince an mareshi an halbeshi shi yace a'a, kibari ayi abu agabanki sannan kibada shaida... Kai kuma ka dinga kallon gabanka idan kana tafiya ko ba yau ba watarana zaka iya fadama wani abin"
Kada kai Deen yayi daga abayan master dayake leqe
"To yanzu kowa ya watse, case closed, oya to your classes!" inji authority din
Watsewa aka fara yi kowa na fadin albarkacin bakinshi hakan yasa wurin daukar hayaniya
"malama kuma ku tafi, kaima wuce" yafada reffering to zee da Deen dake la6e still a bayan master
Gyara zaman jakkarta tayi a kafada ta jefi Deen da wani mugun kallo wanda yasashi saurin komawa bayan master daga leqen dayake yana tura baki sannan tajuya itama tabar wajen a fusace
Sai a sannan yafito daga bayan master din still yana turo baki ya tsintsince lemukanshi shima yaqara gaba akabar daga school authority din saisu master
Kallonsu authority din yayi cikin kulawa yace
"dan Allah ku dinga dagama yarannan qafa, yarane be kamata kuna shishige masu ba hakan zai iya jamuku raini"
"basar kawai oga, guys mutafi" yafada yana yin gaba shima su Alex suka take mashi baya
Binsu da kallo authority yayi a qasan ranshi yana musu fatan shiriya... βοΈ
Tofah Deen ya 6allo ruwaππ»ββοΈ?
Zee ma ta 6allo ruwaππ»ββοΈ?
Wa ke aruwa kusada kada cikinsu ππ
Juma'at mubaraq in advance π
Ummin fasihu π§π»ββοΈ?
8/2/21, 9:32 PM - Buhainatπ: *ππ»ββοΈDEEN ππ»ββοΈ?*
*009*
Kallon juna zee da Deen sukayi sannan suka maida kallonsu akanta
"ma'ana zaka dinga yin duk abinda tasakaka batareda musu ba har ta huce" rukky tafada tanawa zee wink
6ata rai yayi yace
"but why? Haven't I apologize?"
"you have, but it's not accepted, idan kuma kafison ta dauki mataki akai shikenan but remember sojijin sunada bindigu gashi kawunta yana sonta sosai be qaunar ata6a mashi ita gashi yanada saurin zuciya abu kadan zaisa akawomashi mutum ya harbeshi" inji rukky a yanayin tsoratarwa
Pouting din mouth yayi ππ»ββοΈ? bece komaiba
"ya? Kanason tadau matakin koko ka yarda da sharadinta?"
"yaushe zata huce din?" ya tambaya fuska a kumbure
"ranar da na huce, now tell me are you ready or not?" tafada tana zaro mashi ido
Kallonta yayi sannan ya kauda kai yace
"ok"
"me kace?" inji zee
"I said fine!!" yafada cikin dan daga murya dukda bawani amo muryar tayi ba
"hey, watch out am your boss karka qara yimin tsawa" tafada tana nunashi ta yatsa
Dan kauda kai yayi cikin murya qasa qasa yace
"I don't like her"
"kalli nan" yaji tace hakan yasashi dagowa ya kalleta fuska still a tur6une
Nuna logo din jikin rigarta tayi tace
"meye nan? *Born to rule* I was born to rule everyone, am a princess, a queen so watch out!" tafada tana kwama shade dinta
Shidai bece komaiba sai kallonta dayake acikin zuciyarshi sai nanata _I don't like her_ yake
"mutafi" tafada masu rukky sannan ta juyo ta kalleshi ta nunashi tace
"anytime I need you zan kiraka zakazo kayimin duk abinda nakeso, hope am clear" tafada tana jan kunnenta daya alamun gargadi
Kauda kai yayi sannan ya kada kai ahankali
"better" tafada tana wucewa
Su kinginma bin bayanta sukayi suna qumshe Dariya bayan nurr tabashi littafinshi dasuka fizge
Binsu yayi da kallo har saida sukayi nisa sosai sannan cikin kwala kira yace
"Mud queen!!"
Cak ta tsaya Batareda ta juyoba sai su rukky dasuka juya suna kallonshi
"skirt dinki ya yage abaya! Duba kigani!" yafada cikin daga murya kasancewar sunyi nisa dashi don har saida yasa hannu yakare baki kamar yadda mai kiran sallah keyi don suji
Takaicine yaqara qume zee hakan yasa bata ko juyoba taqara gaba tana jin yadda su sumee keta kakka6ar Dariya
Ganin sun wuce yasashi daga kafadu yana mere baki π€·π»ββοΈ? sannan ya koma ya zauna yana duba lokaci a agogon hannunshi, guntun tsaki yaja ganin sun 6ata mashi lokaci sosai, maida hankalinshi yayi a littafin hannunshi yana nazari kafin lokacin dayan lecture dinsu yayi
****
kallonsu tayi cikeda takaici tace
"wai Wannan wane irin wulaqanci ne zaku tisani agaba kunata kakka6amin Dariya" tafada cikin jin haushi
Dakyar deeya ta iya tsagaita dariyarta tace
"I swear that guy is so funny, ko yanzu kasuwa ta watse dan koli yaci riba don he made my day"
Rukky tace
"wlh nima, the guy is soo funny shiyasa nayi Wannan dubarar ko banza munsha dariya" taqarashe cikin Dariya
Guntun tsaki zee taja tace
"ni kuma wlh banga abin ban Dariya ba anan, the guy is so annoying, very irritating"
Sumee cikin Dariya tace
"wai skirt dinki ya yage... Hhhhh guess be ta6a ganin straight skirt ba"
"hakan na nuna alamun bayan hauka akwai qauyanci tattare dashi, ni am wondering ma yadda akayi yayi managing harya shiga Uni Wannan ai da kindergaten ya dace" inji zee
"Hhhhh asarar kudi ko? Kinsan wasu iyayen da iyayi Dole sai 'ya'yansu sunyi karatu, basusan mu kanmu dake normal dakyar mukesha bare ayi maganar abnormal people" inji deeya
"kedai bari, ai wasu iyayen dakwai daukar dala ba gammo musanmman ma talakawa, Wannan ai da psychiatric hptl yadace ba school ba" inji zee fuska a yatsine tana qoqarin fiddo dan memo dinta datake amfani dashi wajen jotting abubuwa masu amfani idan Ana lecture
"saidai fa he's damn handsome, wlh tunda nake ban ta6a ganin namiji mai irin kyaunshi ba, Wannan da normal yake da anga miskilanci don daya fuskanci yanada kyau haka daddaga mana hanci zai dinga yi qila ma bazamu isheshi kallo ba" inji nurr
Zee da tunda tafara magana ta tsaida abinda take tana watsama nurr wani irin kallo tace
"dan Allah kibar irin wannan maganar idan kinsan ina kusa, ya dagawa wa hanci? Ki dinga tantancewa idan zakiyi magana kibar yin jimla, ni ai ba'ayi wanda zai dagamin hanci ba duk kyaunshi kuma duk dukiyarshi, ca6! God forbid badai ni zainab din ba, kuma ku kuke ganin wani kyaunshi, ina kyau anan? Mtcheew!" ta maida hankalinta akan memo din hannunta
Duk dan ta6e baki sukayi, deeya da bata iya shiru tace
"Gaskiya don kyau yanada kyau idan za'abi ta gaskiya, saidai kunsan abincin wani guban wani"
"gwara da kika ce haka don mu ba kowanne abun dake burge kowaba ke burgemu, mu special people always want special things not cheap stuffs" tafada yana jujjuya idanunta cikin salo
Duk sake ta6e baki sukayi qasan zuciyarsu cikeda haushinta don sosai jijji da kanta ke basu haushi saidai ba damar nunawa.
Wata firar suka jawo suka shiga yi zee na dan tsoma masu baki jefi2 don kusan duka hankalinta nakan memo din hannunta tana nazarin abinda aka koyamusu dazun
Sukau su sumee firarsu suke hankali kwance babu abinda yasha musu kai da yin koyi da abinda zee keyi sai firarsu suke suna Dariya hankalinsu a kwance
Suna ahaka lokacin second lecture dinsu yayi suka tashi suka nufi aji don daukar darasin.
Qarfe biyu Deen yafito daga second lecture dinsu, kai tsaye massalacin school din yanufa ya gabatar da sallar zuhr sannan ya wuce gida kasancewar bayada wani lecture din
Su kau su zee sai 3pm suka fito daga last lecture dinsu inda kai tsaye itama motarta ta nufa don har bala yazo, tashige bayan sunyi bankwana dasu sumee suka fice daga school din.
***
Cin abinci suke amma tana lura da yanayinshi, tunda ya dawo daga school dama taga kamar yanada damuwa don kadan kadan saiya turo baki ya hade gira
"kyakyawa na..."
Dagowa yayi ya kalleta yana dakatar da lomar dazaikai baki
Murmushinta dake kwantar mashi da hankali tayi tace
"yau baka bani labarin abinda yafaru a makaranta ba"
Jin haka yasashi 6ata fuska tareda turo baki, hakan ya tabbatar da hasashenta na a can school din aka ta6oshi
"meya faru kyakyawa na?" tafada cikin tsantsar kulawa
Qara hade girarshi dake cike da gashi yayi yana kumburi yace
"kaka bana sonta"
Dan Wara idanu kaka tayi tace
"wacece?"
"Wannan Mud queen din mana" yafada yana qara cika
"wacece hakan?"
"Wannan wanda tayimin tsawa na saketa tafada chakwali"
Qara wara idanu kaka tayi tace
"tofah dama ba musulma bace naji sunanta wani iri?"
"musulma ce mana, haka dai naga tasa a bayan rigarta, nidai bana sonta" yafada yana yatsine fuska
"me kuma yafaru? Ba kabata haquri ba?" kaka tafada tana jin zafi a ranta don bata qaunar abinda zai ta6amata jikanta
"ai tun ranar batazoba sai jiya, na gayamata banason tsawa amma sai taita qarawa kuma tace idan ban..." saikuma yayi saurin dafe baki yana mazurai don yariga ya manta da yace bazai gayawa kaka ba don yasan halinta tana iya jin haushi tace zata bishi har school din kuma Mud queen ranta yaqara 6aci tagayawa kawunta azo a tafi dashi
"kayi shiru kuma, idan bakayi meba?" tafada tana tsareshi da ido
6ata fuska yayi yace
"wai idan ban fita daga harkarta ba sai tasa an kamani" yafada cikin chanza abinda yayi niyyar fada da farko
"yo dama kai harkarta kake shiga ne?" tafada cikin Jin haushi
"A'a fa, ni babu ruwana da ita tunda na bata haquri ban qara tanka mataba" yafada yana kai loma baki
Ganin kaka ta kafeshi da idanu yasashi sauke nashi yana rarrabasu a qasa yana taunar tuwon bakinshi
"gayamin gaskiya, me tace maka?" tafada still tana kallonshi
Bata fuska yayi yace
"O'O! Nifa kaka gaskiya nake fadamiki"
Tallabe mashi keya tayi tace
"ja'iri! ahakan kake fadin gaskiyar sai rarraba idanu kake? Ko angayama zaka iya layyancemin ne? Koma dai menene karka qara shiga harkarta kuma duk sadda tasake ta tankamaka ka gayamin zan bika har school din inji dalili"
"To" kawai yace yacigaba da cin abincinshi
"kayi sauri kagama muyi tatarnan kar dare yayi mana kaga har tara saura" inji kaka tana miqewa don ita tuni tagama cin nata
Da to ya amsa yana kallon inda suke rataye matacin qullun kokon yana tuna gyallen zee
Be 6ata lokaci ba yagama ya kai kwanon kitchen dinsu ya dawo suka Kama da kaka suka fara tatar.
Koda suka gama saida suka Kauda komai na rufewa suka rufe sannan suka daura alwalla kamar Koda yaushe suka shige dakunansu bayan sunyima juna saida safe.
*WASHEGARI*
kasancewar yau lecture din 12pm ke gareshi yasa sai 11am yabar gida.
Koda yazo school din har sha daya da rabi takusa.
Be zarce koina ba sai wajen zamanshi inda yasaba zama shikadai yayi karatun shi.
Deen beda aboki ko guda, he's the type that cherish lonely life, baida hayaniya haka zalika bayason hayaniya shiyasa yaza6i yayi rayuwarshi shi kadai.
Idan ka ganshi da mutum to lokacin lecture ne a aji ko sun hade a hanya kuma gaisuwace zata shiga tsakaninsu saidai ko su tsokaneshi yabisu da Murmushi idan kuma yaga abinda be mashi ba ya maganta
Sanadin rashin son hayaniyarshi yasashi samun Wannan quiet wurin inda zai zauna shikadai yayi nazarin karatun shi, idan kaga yabar wajen to ko class zai shiga ko gida.
Be dade da zama ba yaji ana cewa
"Helloo"
Dagowa yayi daga littafin dayake kallo ya sauke idanunshi akan deeya da rukky dake kallonshi shima fuskarsu dauke da Murmushi
Bata rai yayi ya Kauda kai sannan cikin murya qasa2 yace
"Hi"
Kallon juna deeya da rukky sukayi Dariya marar sauti sannan suka maida kallonsu akanshi
"ya? Karatu kake?" inji deeya
Kada kai kawai yayi bece komaiba kuma be kallesu ba
"amma yanzu kazo ko? Munzo dazu bakanan" inji rukky
Dagowa yayi ya kallesu fuska ba walwala yace
"eh"
Qara satar kallon juna sukayi suna dagawa juna gira daya sannan rukky tace
"To kazo inji zee"
Dagowa yaqarayi yana musu kallon rashin fahimta yayunda can qasa kuma yana jin haushin yadda sukazo suna 6ata mashi lokaci
"wanene haka?" ya tambaya yana hade girarshi
"wanene haka ko wacece haka? To boss dinka nake nufi" tabashi amsa
"boss kuma?"
"eh, ko nufinka har ka manta? Hmm fatan dai baka manta da kawunta ba da sojojinshi?"
Sake 6ata rai yayi yace
"me kuma nayi yanzu?"
"mefa? Kawai cewa tayi akiraka qila wani abin zaka mata ko ka manta da deal dinku ne?"
"amma kunga ai karatu nake ko?" yafada yana nuna musu handout din hannunshi
Dariya suka sa, deeya tace
"haba? Ashe karatu kake? To me kake karantawa?"
"me fa? Kawai bin rubutun yake da kallo wondering yaya akayi typing dinsu"
Dariya suka sake sawa, ganin hakan yasashi ta6e baki ya maida ga handout din
"kaifa muke jira" inji deeya
"nace fa karatu nake kuma mun kusan shiga class" yafada cikin qosawa
"class ko? Muje deeya, da rabon wani yajishi a cell yau" tafada tana kamo hannun deeya suka juya suka tafi
Binsu da kallo yayi ganin sunyi nisa yasashi rufe handout din yana turo baki ya dauki kingin littatafan ya miqe yabi bayansu rai a6ace
Tun daga nesa suka hangosu sun taho sai Deen dake bayansu yana cika yana batsewa
"zee kalli mutuminki" inji sumee tana ta6ota while nurr tasa dariya
Kallon wajen tayi ta dauke kai tana ta6e baki
"ca6! Da alamu dai afusace yake ji yadda yake hura hanci" inji nurr tana Dariya
"yo ba doleba, yaga ana neman takura mashi"
"Hmm ai kadan ma yagani, I'll make sure I teach him a good lesson" inji zee tana qara Kauda kai ganin sun qaraso
Zazzaunawa su rukky sukayi yayinda shikuma ya qame a tsaye yana mazurai
Ganin babu mai niyyar tankamashi yasashi cewa
"gani... What's it?"
Banza tayi dashi don ko kallonshi batayi ba sai su rukky taketa xabga Murmushi suna jiran ganin yadda za'a kaya
"Mud queen!"
Saurin Juyowa tayi tana watsamashi mugun kallo tace
"what did you just call me?"
"Mud queen, isn't that your name?" yafada yana Kauda kai bakinshi agaba
"kull! Kar inqara Jin Wannan sunan abakinka, my name is Zainab, call me zainab" tafada tana wani zazzare mashi manyan idanunta kamar irin tanama danta fada
"O'O! Banason wadannan idanun!" yafada yana yamutse fuska
Dan Wara idanu zee tayi tace
"baka sonsu? To saika kwakulesu yadda zansan baka sonsu" tafada cikin quluwa
Yamutse fuska yasakeyi yace
"uhun, ni bazan iyaba besides idan na kwakule zaki koma skull with ugly forhead"
Dariyar dasu sumee keta dannewa tundazu tafito fili suka shiga kyakyatawa
"ni kake cewa ugly skull with forhead?!" tafada a qule
Kauda kai yayi bece komaiba sai hura hanci dayakeyi
Kwafa tayi tana kada kai
Ganin bata qara tanka mashi ba yasashi cewa
"intafi? Munada class in the next 15mins" yafada yana kallon yar agogonshi dake maqale da hannunshi
"eh tafi din" tafada cikin gatse tana harararshi
Dadi yaji ya kamashi yayi saurin juyawa zai tafi
"au tafiyar zakayi?!" tafada a fusace
Kasancewar tayi maganar a tsawace yasashi Saurin Juyowa a tsorace yana cewa
"O'O!"
"O'O! Nabi O'O dagudu, wai tsaya wama yasaka a university bayan ga kindergaten nan birjik a gari? Meye ma sunanka wai?" tafada tana Girgiza kasancewar ta tunda tafara ta miqe
Banza yayi ya kyaleta yana kumburi
"ok bazaka fadi ba? Sumee bani wayata inkira kawu"
"Deen..." yafada a kumbure
"mene?" tafada tana yatsina fuska
"I said Deen!" ya fada da dan qarfi
"kutt... Ni kakewa tsawa?" tafada tana nuna kanta cikin zare ido
Banza yayi ya kyaleta sai hucin dayake
"Dakyau! Amshi kaje ka siyomin ruwa" tafada tana miqa mashi 1k
Juyowa yayi ya dan kalleta sannan ya amshi kudin yajuya yana cika da batsewa
Su rukky da cikinsu harya fara ciwo don dariya ta kalla taja guntun tsaki sannan ta zauna tana huci
"Allah dai zee, wlh you guys are so funny!" inji rukky
"I swear, wlh kunfi tom & jerry ma" inji nurr itama cikin Dariya
Tsaki tasake ja tace
"kuke ganin funniness dinshi, mtcheew! he's so annoying"
"Bawan Allah, I wonder how handsome guy kamar shi yake haka, gaskiya solu6ancinshi ba qaramin qwararshi yaiba" inji sumee
"wlh kau, dama ance mutum tara yake be cika goma ba, shi nashi tawayan kenan" inji deeya
Zee bata sake tankamasu ba tacigaba da danne dannenta a waya
Deeya ce ta ta6o sumee tana gwada mata Deen daya taho kinkime da ledar pure wata daya
Wara idanu sumee tayi tana toshe baki sannan ta ta6o nurr dake kusada ita ta gwada mata itama waro ido tayi tana qumshe Dariya, dama rukky tunda deeya ta ta6o sumee itama ta ankare
Zee batasan wainar da ake toyawa ba don hankalinta nakan wayarta harya qaraso sai jitayi ya dire mata ledar pure water din agabanta yana miqomata chanji
Bin ledar pure water din tayi da kallo sannan ta maido Kanshi cikin alamun rashin fahimta
"ga chanjin" yafada yana miqamata
Qara maida kallonta tayi ga ledar ruwan tace
"meye Wannan?"
"pure water din dakikace asiyo mana" yafada yana hade gira
"ni nace ka siyomin Wannan? Wannan ne pure water? How is it pure kana ganin abu kamar ruwan toilet? Nufinka ni zansha Wannan?" injita tana kallon ruwan a wulaqance
"but you said I should buy you water, wane ruwane kuma bayan Wannan" yafada cikin qosawa
"ce maka akayi kowama nashan qazantar dakuke sha ne? Swan water nake nufi, dummy!" tafada tana harararshi
Gani tayi beko motsaba hakan yasata qara cewa
"kafa dauke Wannan abin daga gabana ka kawomin abinda nace"
Bece komaiba sai duqawa dayayi ya dauki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 81