Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kowannensu riqeda Littafi a hannu sun juyawa kansu bawa kowa na abinda ke gabanshi Jin kanta na neman fashewa don nauyin dayayi mata yasata maida littafin ta rufe tana dafe kan tana matse idanu Duk abinda take Deen besan tanayiba don sosai yayi nisa a duniyar karatu Juyowa tayi taga kanshi na kan Littafi bema san abinda ke faruwa ba hakan yasata dan 6ata rai tasa hannu ta fizge littafin hannunshi Firgigit yayi ya waigo don abin yazomashi a bazata, Ganin tayi saurin maida littafin bayanta yasashi shima 6ata rai "O'O! Give me my book" Maqe kafada tayi tace "anqi din, kai baka gajiya? Ni yanzu haka jin kaina nake kamar zai dare gida biyu" Daga kafadu yayi yace "then? Aike keji ba niba ko? Bani littafina" yafada yana neman amsa Maida littafin tayi bayanta tana Dariya Duk yadda yaso ya amsa qi tayi hakan yasashi hqr ba don yaso ba yace "now tell me, me zamuyi bayan karatun?" "komai ma Amma banda karatun, nagaji" tafada tana yatsine fuska "komai kamar me?" "komai dai, kamar labari da dai sauransu" "Ni ai ban iya labari ba" "wa din?" tafada tana eyeing dinshi "Ni din" yafada shima yana Dariya "hmm, gwara dakaba kanka Dariya" tafada tana harararshi "nidai ai gaskiya nafadi" yafada yana cigaba da Dariya Harararshi tayi kawai can kuma tace "ka Bani lbr, na komai ma, ko naka, kona family dinka, komai ma, qila inji sauqin nauyin kwalwa ta" Murmushi yadanyi sannan ya gyara zama yace "to bari nabaki na Ni da family dina" Itama gyara zama tayi cikin jindadi tace "yauwa, to inaji" tafada tana buga tagumi da hannu daya Murmushi yayi ganin yadda tawani nutsu ita dadi labari sai yace "Nidai sunana Deen kamar yadda mutane including you ke kirana, Amma my real name is _*KAMALDEEN MUHAMMAD*_ Amma kakata nace min _Kyakyawa na_๐Ÿ™ˆ" ya qarashe yana rufe fuska alamun jin kunya Dariya zee tayi wanda hakan yasashi leqota ta tsakankanin yatsun dake fuskarshi "waye Kyakyawan? Cemaka akayi kanada kyau ne? Ca6! Tana fada ne kawai don kaji dadi Amma dont let that get into your skull ok?" Cire hannunshi yayi daga fuska yana kumburi "cigaba" Maqe kafada yayi alamun beyi "meye kuma?" "kin Cemin am ugly" yafada yana hade gira Wara idanu tayi tace "yaushe nace hakan? Kaji tsoron allah" "ba yanzu kikace ba?" "nace you're ugly? Cewa nayi bakada kyau" "what's the difference?" "difference din shine, ugly yana nufin mummuna, marar kyau kuma yana nufin marar kyau" Yamutse fuska yayi yace "me I see no difference in these" "ni naga difference din, so cigaba" Qara Maqe kafada yayi Bata fuska tayi tace "why na?" "sai kince inada kyau" yafada yana turo baki Dan Wara ido tayi sannan tace "to shikenan kanada d'an kyau" Juya idanu yayi yace "eh babu komai, aidai inada shi ko? Keda bakidashi kwata2 fa" Harara ta gallamashi "me din?" "kyau din" ya amsa yana mata gwalo Yitayi kamar zata makamashi Littafi yayi saurin jada baya yana Dariya Kwafa tayi tana jinjina kai "in cigaba?" ya tambaya yana dan leqota Hararshi tayi tace "cigaba ba don halinka ba amma" Dariya sukayi gabadaya sannan Deen yacigaba dacewa "yauwa as I was saying, kakata na kirana kyakyawarta nikuma ina kiranta kakata.. Kakata itace komai na, my life, my happiness, my komai Tana sona sosai, komai nata is kyakyawarta, haka nima komai nawa itace Tana yin komai don ganin ta faranta mani, tana yin komai don taga ta inganta rayuwata mudin hakan be sa6awa shari'a ba We are not rich but alhamdullilah bamu rasa komai ba. Kakata na sana'ar koko da qosai da safe nikuma ina zuwa wani workshop anytime am free, ina koyon aikin furnitures a qasan layinmu. With that muke living happily the way We can" ya qarashe yana murmushi Itama murmushi tayi cikin sha'awar simple life dinshi "mama da baba fa? Tunda muke dakai ban ta6ajin ka ambacesu ba" tafada tana kallonshi Dan jimm yayi, sai kuma yayi murmushi mai ciwo yace "basa nan, tunda na bude idanuna duniya kaka nasani, itace mamata itace babana itace komai na, amma ga yadda kaka tace accident sukayi suka rasu kuma dama nikadai suka haifa shiyasa banida siblings, kaka kuma babana ne kadai danta shiyasa we're all alone, daga ni sai ita" Tunda yafara take kallonshi cikin tausayawa, ashe maraya ne gaba da baya? Allah sarki "am.. So sorry, ban sani bane, Allah yajiqansu yayi musu gafara" tafada asanyaye Murmushi yayi mata cikin jindadin addu'ar tata yace "amin ya rabb" Shiru ya ratsa wajen inda zee tashiga saqe2, to ina dangin mamanshi? Ina dangin kaka? Yakamata ace basu kadai bane kamar yadda yace, koba komai Yakamata yayi maganar dangin mamanshi "kefa? Saura ke kibani lbrin ki" yafada shima yana buga tagumi yadda tayi dazu Dariya tadanyi tace "nawa tarihin is not as special as yours" "eh dukda haka abani" yafada yana kada kai Slight murmushi tayi tace "ni sunana zainab.. Zainab Farouq" ta tsinci kanta da kasa qarasa sunan "Dan faranshi?" inji Deen yana daga mata gira Kallonshi tayi da dan mammaki "how did you know?" Qara dage gira daya yayi yace "the paper, ko har kin manta" Dariya tayi tace "to haka yake, nima ni kadai ce ga iyayena, babana bahaushe ne, mamata kuma barumiya" "menene barumiya?" yafada cikin rashin fahimta Yar Dariya tayi "tribe ne, kai bakasan Rumawa ba? Masu tsagu biyu2 a gefen kunne?" Girgiza kai yayi alamun a'a yace "no, ban ta6a jiba" "ai dama ya za'ayi ka sani? Kai dama kifin cikin rigiya ne" tafada tana Dariya ahankali Ta6e baki yayi yace "eh babu komai, yanzu ita mum dinki ce rome din?" Dariya tayi tace "ba rome ba, Rumawa nace" "to Rumawa, amma itama tanada marks din?" "yes, kuma yana Masu kyau sosai don yawancinsu farare ne kuma kyawawa sai kuma tsagar taqara fiddosu" "wow! Kema Rumawa ce ko? Tunda Kema fara ce" yafada yana mata murmushi still be janye tagumin ba Harararshi tayi tace "barumiya zakace, mutane dayawa ne Rumawa, dummy!" Daga kafadu yayi yace "whatever" "nima barumiya ce Tunda mamata barumiya ce hakama bahaushiya ce Tunda dad dina bahaushe ne, ruwa biyu kenan" tafada tana kashe mashi ido daya Murmushi yayi yace "bawani, ke ba barumiya bace Tunda bakida marks" Xaro ido tayi tace "marks? Ca6 allah ya sawwaqe, ni dama banaso a jikina nafi sonshi a na wasu shiyasa ma naji dadi da ba'ayimin ba" "nikuma Inaso, i wish muma tribe dinmu anayi da kinga yanga" yafada yana juya eyes Dariya tayi tace "sai kuma gashi ba'ayi taar๐Ÿคช" "eh babu komai" yafada yana Hade gira "to ku wadanne tribe ne?" "hausa mana" "hausa kuma? Kana nufin kai bahaushe ne" tafada tana mashi kallon uku saura kwabo "yes, dafa?" "and you want me to believe?" tafada cikin rashin yarda "allah dagaske fa nake" Harararshi tayi bata ce komai ba "allah, wlh kinjima na rantse" yafada cikin son gamsar daita "to amma babu either of your parent ko mama ko baba dasuka hada jini da Arab?" Girgiza kai yayi alamun babu "shuwa Arab?" Nan ma Girgiza kai yayi "allah mai iko, buzaye fa ko fulani dukda bakayi kalarsu ba" Qara Girgiza kai yayi snn yace "I told you ni bahaushe ne, mutane dayawa na tambayar kaka kuma haka take cewa, both mum da dad dina duk hausawa ne" yafada innocently Kada kai tayi tana kallonshi bawai don ta gamsu ba tace "kuma fa, amma nayi mammaki amma kuma ba abin mammaki bane, ikon allah kenan" Murmushi yayi kawai suka cigaba da firarsu cikin jindadi wanda sosai yadan ragemasu nauyin da kansu yayi Saida lokacin tafiya gida yayi suka rabu, ita zee tahau motarsu shikuma ya tari adaidaita _guys are you ready for the next chapter?_ _to ku tanadi hanki ๐Ÿคง domin zaiyi yaji ๐ŸŒถ๏ธ? irin sosai dinnan_ Ummin fasihu ๐Ÿงš๐Ÿปโ€โ™€๏ธ? 8/2/21, 9:33 PM - Buhainat๐Ÿ˜: *๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™‚๏ธDEEN ๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ?* *021* ๐Ÿ˜†๐Ÿ˜†๐Ÿ˜† jiya nace ku tanadi hanki mutane sun gigice, O'O!๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™€๏ธKudai bakusan wasaba, to wasa nake muku ๐Ÿค— Ku kwantar da hankalinku kamar kunyi baqo ya sheqa๐Ÿ™„ Haka lokaci yayi ta wucewa, exams nata qaratowa Kan kowa ya dauki chaji da masu qoqarin da mashiriritan duk aka komawa allah aka rungumi Littafi Alokacin library yakoma kamar bashi ba saboda cika, duk wanda ya rungumo guntun littafinshi to library yanufa Hakan yasa su Deen chanza wurin zama suka dawo silent place dinnan bakidaya Izuwa yanzu bama ce su mr ibrahim da zee sun shirya ba Saidai babu wannan yar tsamar dake tsakaninsu ada, yanzu lafiya lau suke mu'amallantan juna irin mu'amalar tsakanin malami da dalibi, abin nasu safa safa ba yabo ba fallasa Da farko zee taso tabashi hqr a lokacin sai kuma taga zaifi tabari sugama exam don karma yayi tunanin taimakonta takeson yayi a exam din๐Ÿ˜ Hakan yasa ta qudurta cewa dasun gama exams zata bashi hqr komai ya wuce a tsakaninsu Tsakaninta dasu sumee babu yabo ba fallasa don tunda exams ya qarato kai yadau chaji haduwarsu tayi wuya, dama haka yake yawan faruwa don tun kafin ma zee tasan Deen da exams ya gabato take ajiye shiririta ciki hardasu tayi facing karatun ta don tasan idan ta biye musu ita hau zai hau don kwata2 babu ruwansu da karatu koda kuwa irin wannan lokacin ne na gabatowar exam don sunfi damqa imaninsu ga expo(satar amsa) Ita kuma dayake bata iyaba yasa duk lokacin gabatowar exam haduwarsu ke dan wuya don lokacin busy take karatu sukuma busy suke da shashanci dayaimasu yawa a brain shiyasa irin wannan lokacin basu cika hadewa ba sai ta waya ko idan an Hade a makarantar a gaisa tsaitsaye awuce To Hakan ta kasance yanzu ma, basa yawan hadewa saita waya wanda mafi yawanci su ke kiranta su gaisa, wannan kulawar dataga suna bata yasata qara jin sonsu don ita tana masu so na tsakani da allah kuma kamar yadda tace ita bata iya pretending ba, idan tanason abu to tanasonshi idan kuma beyi mata ba to 6aro2 zata nuna beyi matan ba bata tsoron bayyana Hakan Tun suna lissafin exams saura sattitika harya koma saura kwanaki har yazo ma gabadaya Sosai school din yaqara daukar serious atmosphere don wannan exam din na chanza aji ne babu mai fatan yayi repeating Hakan yasa kowa ke iya bakin qoqarinshi don ganin ya tsallake Su zee sun riga su Deen fara exam kasancewar daman ba course daya suke karanta ba kuma dama yafita da shekara daya, ita tana level 200 zata shiga 300 shikuma yana level 300 zai shiga 400 level Sosai zee ta baje kwalwarta sosai wajen jarabawar sai gashi wannan karin maganar ta turawa na _how you spread your bed that's how you lay on it_ wato _yadda kayi shinfidarka haka zaka kwanta akai_ Sosai exams din sukazo mata da sauqi fiyeda kowane semester don tafi shirya mashi a wannan semester din fiyeda kowane Har yanzu tare suke karatu da Deen, duk wanda lokacin shiga ajinshi yayi saiya tashi yabar dayan yaje ya zana ya dawo A bangaren su sumee kau bana kasuwa batayimusu dadi ba don bana an tsamar tsaro sosai dakyar suke samu sudanyi satar amsa wanda ahakan ne aka kama rukky har Sau biyu inda duk inda aka kamata tofa tayi loosing din jarabawar don yake papern akeyi kuma bazata sake wata ba, daga baya ma sai aka wareta daga cikin students aka kawo mata kujera da desk gaban class inda ba damar satar amsa, wurin yazama wurin zamanta duk in zasuyi exam, Hakan yasa komai yaqara dagule mata don kwalwar fankoce babu komai a ciki sai dusa Suma su sumee ba'a barsu abaya ba don duk watsasu akayi a class din, kowanne da mazauninshi gashi ba damar satar amsa saboda idon da aka samasu Hakan yasa basa ta6uka komai a duk jarabawar dazasu zana, wata jarabawar ma Saidai su rubuta sunayensu su sake copying din questions din aciki suje suyi submitting hakanan Sosai suka shiga damuwa da baqinciki don fa bana ba sauqi sai wajen allah, qarin baqincikin su shine idan suka hango zee ta sadda kai tanata rubutu ko dagowa batasonyi sai suji wani qululun baqinciki ya tokaremasu maqwalato suji kamar suyi tsuntsuwa sugansu gabanta su fizge shegiyar takardar su yayyaga, oho batasan sunayi ba don abinda ke gabanta takeyi su tabari da harara cikin duhu๐Ÿ˜ก Jarabawar mr ibrahim itace kusan ta tsakiya, duk cikin Jarabawar babu wanda akafi zullumi kamar ita, wadanda basuyi barci ba ranar daren Jarabawar sunfi yawa Ciki harda mutumiyar taku wanda a lokacin Saidai Deen ya ajiye nashi karatun sukayi nata tare Kuma Hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba don sosai sukayi covering abubbuwa da dama Dayake Jarabawar monday ce sai suka hadu ranar saturday a school inda ranar ma wata Jarabawa sukayi on their own don ranar tambayoyi Deen yayta rubuta mata tana amsasu kuma tayi qoqari sosai don ta ciye rabi da kwata, kingin kuma suka farmasu harta fahimta Ranar sunday kuma kwana ta kusan yi zaune saboda karatu Hakan yasa ta tashi washegari da ciwon kai Saidai cikin amincin allah tana shan magani taji dama2 Kamar yadda kowa ya chanfa Jarabawar mr ibrahim da mugun wuya a kowanne semester haka kuma yafaru a wannan ma don wasu suna tozali da question paper din zufa yafara ketomusu Kunsan *goyon goyo?* to haka questions din suke, kowanne tambaya da goyon datayi itama goyon da nata goyon shima goyon da nashi don a question daya kana iya bata long sheet gaba da baya kodayake ga yan wahala yake Hakan don su yan baiwa (su nurr) ko gaban long sheet daya basu cika ba ga dukkan questions din tsabar gwanancewa ๐Ÿ˜† (ouch! Waya jefeni ๐Ÿฅบ) An saba duk wuyan exam iyakar gudun tsiya kayi 1hr kana yi amma wannan saida akafi awa biyu kafin afara fita Qarin gishiri cikin ciwo kuma harda mr ibrahim cikin invigilators din Hakan yasa abin yafi daukan Zokaga rikicewar students ranar Mafi yawa a cikin students din kuka sukaitayi wasu na jama mr ibrahim allah ya isa kamar yadda suka saba duk Jarabawa Sukau mutanenku sai suka zama yan kallo don su aganinsu ma kuka ai rahamane, tunda har suka samu sukayi kukan to matsalar tasu bata kai matsala ba A bangaren zee ma sosai Jarabawar ta jigatar da ita dukda dai tana saka ran samun abin kirki don ita kanta tasan tayi qoqari Haka tadawo wajen Deen gajiye ti6is Deen sai Dariya yake mata Kingin exams din ma sukazo suka wuce, inda students sukayisu cikin jindadi don dama zaffafan su suka fara zuwa Kingin kau duk yan tagajan2 ne Su zee sun riga su Deen gama Exam don dama sun rigasu farawa Lokacin da su zee suka gama su Deen saura paper uku sugama Hakan yasa take ta shan hutunta tabarshi da wahala Acikin haka ta yanke shawarar bama mr ibrahim haquri Saidai ta rasa ta wace hanya Itadai tasan bazata iya samunshi face 2 face ba hakan yasata yanke shawarar yin haka a rubuce Wata zungureriyar takarda tasamu fara tass ta zauna tafara tsara kalaman ban haquri Saida ta cika gaba da baya sannan ta linke neatly Sai a sannan kuma tafara tunanin ya za'ayi takardar takai mashi don gaskiya tana tsoron taje da kanta Haka taita saqa da warwara daga baya dole Deen ta nema don yabata shawarar yadda zatayi kuma kamar yadda yasaba samo mata mafita a matsalolinta wannan karon ma haka yayi Tare dashi sukaje parking space din malamai inda mottocinsu ne a parke a wajen Wajen motar mr ibrahim suka nufa cikin sa'a kuma sukaga daya daga cikin glass din windown motar be ida rufewa ruf ba Tanan suka lalla6a suka zura takardar tafada seat din mai zaman banza Suna ganin haka sukabar wajen da sauri kowanne zuciyarsu fall murna Mr ibrahim betashi ganin takardar ba saida ya isa gida, dauka yayi yana jujjuyata sannan ya warwareta Ganin rubutun dayawa yasashi maida wa ya ninke akan saiya nutsu sannan ya karanto Sosai yasha mammaki bayan yagama karance takardar kodayake dama yaga alamu daga gareta tun lokacin data fara zama class dinshi Saidai beyi tunanin yadda take nuna jinkai dinnan zata iya bashi haquri akan abubbuwan da duk tayimashi Maida takardar yayi ya ninke ya adanata Zee tayi tunanin zai nemeta amma Shiru takeji, data gayawa Deen yace mata ta kyaleshi kawai yanzu dama ba lallai bane yayi saurin haqura kawai tabari atafi hutu adawo saita sameshi a mutum taqara bashi haqurin Sosai ta gamsu da wannan shawarar Hakan yasa tayi amfani daita ta kyaleshi A bangaren su sumee kau sosai yanzu suke hadewa da zee don Mafi yawancin lokuta suna tare musanmman yanzu da ba komai take ba ga Deen yana busy don basu gama tasu Jarabawar ba hakan yasa suka koma suka jone kamar da dukda suna yawan hadewa da Deen din shima anytime he's free *BAQAR RANA* Yau laraba kuma yau su Deen ke qarasa paper dinsu ta qarshe Sosai ake kwala rana yau ga zafi harna innanaha Hakan yasa duk inda zaka gitta a school din Saidai kaga students qarqashin bishiyoyi suna shan iska don idan ba dole ba babu abinda zai saka zaman class Dayake duk yawancin departments sun gama Jarabawarsu sai school din yarage jama'a sosai don sai tsirarun masu Jarabawa saikuma ire irensu zee wadanda dalili kawosu Tare suke da Deen har saida lokacin shiga final paper dinsu yayi sannan suka rabu bayan yafada mata inda zasu hadu idan yafito Ta dan jima nan zaune ita kadai tana yan danne dannenta a waya Zaman kadaicinne ya dameta Hakan yasata miqewa ta sa6i jakkarta da niyyar zuwa wajensu sumee koba komai sunyi fira to whine time away Koda taje mazauninsu saita iske wajen wayam, tana niyyar juyawa taji muryar sumee a bayanta Juyawa tayi ta hangota ta taho tana daga mata hannu Hakan yasata yimata guntun murmushi ta tsaya don jiran qarasowarta Qarasowa tayi wajen tana dan sauke numfashi "keda wa kiketa sauke numfashi kamar wanda aka biyo?" inji zee Tsaki sumee taja tace "kede bari, wlh saqo naje amsowa na tararda mai kawowan ma bai isoba shiyasa na dawo har zan wuce naga wata kamar ke shine fa na biyo ki" "to? To where are others? Naga wurin wayam ko yau basu zo bane?" inji zee "sunzo mana, wazai zauna anan kina ganin yadda ray din rana ke reflecting ta koina? Wani cool waje muka samu daga bayan school, bakiji wurin ba so cool kamar karka tashi, nima dan iskan saqonnan danaje amsowa ne ya tadoni abin ban haushi kuma ashe be qaraso ba" tafada cikin nuna jin haushi Ta6e baki zee tayi tace "yanzu dai muje wajen dan allah, na gaji ga rana na kwalata i need some breeze" "ai dole, gaskiya yau ana rana, qila ruwa xa'ayimana dama andan daga mana qafa kwanan nan" inji sumee suna tafiya Tafiya suke suna firarsu suka nufi bayan school inda tunda zee take a school din bata ta6a zuwa wajen ba Saidai bata kawo komai a ranta ba don babu wata alama da zai janyo ta zargi wani abu Suna cikin Tafiya wayar sumee tayi ringing Cirota tayi ta kara a kunne bayan ta tsaya Hakan yasa itama zee tsayawa tana kallonta "wai fatima wannan wanne irin wulaqanci ne? Kince min kinzo naje na tararda bakya nan, naita jira Shiru kin shanyani cikin rana kamar yar iska" tafada a masifance Jimm tadanyi alamun magana akeyi acan bangaren can kuma taja Tsaki tace "haba wannan ai wulaqanci ne wlh, kawai saiki sani zuwa da dawowa kamar marar aikinyi bayan kinga yadda ake kwala wannan ranar? Mtcheew! Ganinan zuwa idan kuma kinga dama karki tsaya inda zanyi saurin ganinki, Mtcheew!" ta katse kiran a fusace Dagowa tayi ta kalli zee dake sauraronta Tundazu "wai kinji don wulaqanci sai yanzu taga damar zuwa, ni wlh badon saqonnan nada muhinmmaci ba da babu abinda zai sani wannan wahalar" tafada cikin fushi Dan Ta6e baki zee tayi tace "to ya kika iya? Tunda yanada muhinmmaci dolenki kau kije ki amso, ehe!" ta qarashe tana mata Dariya ganin yadda take cika tana batsewa Tsaki sumee taja tana girgiza kai tace "ko zaki rakani please" tafada tana narke fuska Harara ta gallamata tace "ca6! Wazai qara wannan uwar tafiyar yadawo? Nikam saikin dawo, ni wlh ma bansan abinda yasa kukazo nan ba, zafi kanku farau zaku shigo nan inda babu wulgin kowa? Ni tunda nake a school dinnan ban ta6a zuwa nan arear ba" inji zee tana qarewa environment din kallo "hmm wlh duk aikin su deeya ne, nima dafarko nayi wannan mitan amma danaje naji coolness din wajen kamar naita barci donma wannan yar banzar fatiman ta kofsa min" "haba wajen yayi nisa sosai, ga wurin so quiet ku bakwa tsoro?" inji zee "kede ke ganin haka, sai kinje wurin zakiga acike yake don duk can students suka ruga shiyasa kikaga basuda yawa acan cikin school din" tafada cikin son convincing dinta "to nidai bari na qarasa ranar nan tafara gasamin forehead, kije ki amshi saqon kin shanyata itama" "kyaleta itama ta dandana ai" tafada tana Dariya Wucewa zee tayi tana cewa "badai kyau mugunta" Dariya sumee tayi tajuya itama tana cewa "saina iso" ta wuce Cigaba da tafiya zee tayi hoping ta hango su deeya din amma sai qara nausawa take babu su babu alamun su don ko wulgin mutum bata ganiba Gajiya tayi ta ja ta tsaya tana riqe kugu Izuwa yanzu wani iska iska akeyi mai shige da na hadari don dama kamar yadda sumee tace wannan zafin na yau da walakin Tsaki zee taja cikin quluwa, in banda ma hauka mezai kawoka nan duk da sunan shan iska? Wayarta ta ciro daga cikin jakka tashiga lalubar number su Saidai babu ta wanda ke shiga, Hakan ba qaramin qara quleta ba yayi Hakan yasa tayi kwafa ta kashe wayar tajuyo da niyyar tafiya sai jitayi ta bangaji abu har wayar hannunta na faduwa Baya2 tayi tasamu dakyar tayi regaining din balance dinta sannan ta dago don ganin menene ta bangaje Gabanta ne ya yanke ya fadi ganin wani tsaye agabanta ciggarete a hannunshi yana aikamata wani dan iskan kallo da jajjayen idanunta Dan jada baya tayi Saidai motsin dataji a bayanta yasata saurin Juyawa nanma taga wani Da guda guda taga sunata fitowa har suka gama fitowa suka zagayeta ya zamana tana tsakiyarsu Da guda guda tafara binsu da kallo gabanta na faduwa, gabanta ne yayi wani mummunan bugawa datayi tozali da master dayayi pocketing din hannunshi yana kallonta da jajjayen idanunshi dan guntun murmushi dauke a gefe bakinshi Cigaba tayi da kallonsu da daidaya zuciyarta na mugun bugawa, dakyar ta tattaro yawun bakinta ta hadiye sannan tayi qoqarin aro nutsuwa ta yafa ta duqa da niyyar daukar Wayarta sai gani tayi na kusada ita ya taketa har saida tayi qarar fashewa sannan yayi ball daita tafada can cikin wasu ciyayi Dagowa tayi gabanta na cigaba da racing tana kallon wadda ya take wayar, cikin qarfin hali tace "wai malamai lfy? Ku su waye?" tafada cikin muryar dataji kamar ba nata ba Wata mahaukaciyar Dariya suka kece daita wanda Hakan yaqara farashin tsoronta don wannan Dariyar daga jinta ta tsantsar mugunta ce "baa baa! Kaji wai qarin bayyani takeso" inji gandu yana qara fashewa da Dariya "wai dagaske kike baki ganemu ba? Harda nima" inji T.J yana nuna kanshi yana Dariya "haba baby? Kin iya mari amma baki iya tantance mutane ba?" inji Alex dake gefen damarta shima yana Dariya Gabanta ne yayi mummunan bugawa da jin haka _ya ilahi! What am I into_ tafada a cikin zuciyarta "ya isa!!" inji master yana daga hannu wanda hakan yayi daidai da daukewar dariyarsu "baby bata ganeku ba, qilama bata sanku ba tana neman qarin bayani, koba haka ba baby?" yafada yana kallonta tareda kashe mata ido daya Kasa magantuwa tayi sai kallonshi datake speechless "karki damu, ni zan fahimtar dake, ai ke ranki shi dade ce dole sai ana hadawa da tuni" yafada yana tunkarota Bugun zuciyarta ne yaqara qaruwa tafara ja da baya cikin tsananin tsoro shikuma yana tunkarota haryanzu dauke da wannan murmushin Duk takunshi daya na tunkararta daidai yake da nata daya na ja da baya, haka sukaitayi har tajita gab da bash dake bayanta, saurin Juyawa tayi tana kalleshi ta kuma kalli master dake daff daita, cikin kidima tasa hannu da niyyar ture master daya kusan Hade jiki da ita ta gudu Saidai caraff ya cafke hannun, kafin ta tantance komai taji an dauketa da wani giggitaccen mari... โœ๏ธ Ummin fasihu ๐Ÿงš๐Ÿปโ€โ™€๏ธ? 8/2/21, 9:34 PM - Buhainat๐Ÿ˜: *๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™‚๏ธDEEN ๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ?* *022* *DEEN* Yana fitowa daga exam hall yanufi inda sukayi da zee zasu hadu

Chapter 14 of 81