Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne, daukar hanyar garden din sukayi suna tafe Aysha na gyarama zee rigarta dake dan jan qasa abaya Garden din shima tarr yake da haske dake haskowa daga both kwayaye masu haske da masu kaloli anyi decorating garden din gwanin sha'awa ga fararen plastic kujerun da mutanen da aka gayyata duk suka zazzauna akai daga gaban mutanen Kuma wata royal blue kujera ce mai kyau sosai sai dan qaramin glass table daga gabanta wanda ke dauke da dan madaidaicin cake dake dauke da burning candles masu kaloli akai. mutanen wajen basuda wani yawa daga su Abbu sai su mummy sai su aymaan da Ahmad dakuma iyayen Ahmad din Ahankali suka qaraso garden din suna tafe fuskokinsu dauke da murmushi sosai kallo yadawo kan zee wadda taxama kamar tauraruwa acikinsu Ahankali take tafiya hannunta cikin na ummy dake janta fuskarta dauke da murmushi dukda bata ganin mutanen wajen sosai saboda baza bazan hularta dasuka dan karemata gani taga alamun mutanen dai nada dan yawa sautin 'masha allah' keta tashi daga bakunan mutanen wajen cikin yaba irin kyawun datayi wanda hakan kesata murmushin kunya tana qara sinne kai acan na hango aymaan dake sanye cikin wani danyen tsaddaden yadi kalar madara yaci gayunshi Inda yayi shigar milk and brown tun lokacin dasuka shigo garden din idanunshi ke kanta ya kafeta dasu babu kyaftawa dukda baduka fuskar tata yake gani ba yana hango karan hancinta da guntun bakinta dake shining saboda lipgloss datasa, yana ganin yadda yake curving beautifully idan tana murmushi da kallo yarakasu har ummy ta qarasa daita wajen da aka tanada mata don zama koda suka isa wajen bata zauna ba sai qarasowa da mutanen wajen sukayi wajenta suka fara gaisawa akunyace zee keta gaidasu don duk saitaji kanta yayi girma ganin itace centre of attraction din wajen aymaan dai yakasa ko kyafta idanu akanta duk motsinta saiyabishi da Hazel eyes dinshi jiyayi an zungureshi hakan yasashi waigowa yana dawowa daga duniyar kallonta "kallatu ance mutaso mu yanka cake" inji Ahmad cikin tsokana harararshi aymaan yayi sannan ya tashi suka qarasa wajen mutanen daduk sun koma gaban wajen ana shirin yanka cake din hada idanu Aysha tayi da aymaan yawani hade rai tareda kauda kai binshi da kallo tayi saikuma ta ta6e baki itama ta kauda kai waqar birthday suka shiga yimata suna tafi sannan da taimakon mutanen wajen ta yanka cake din tafi wajen yadauka sosai ana dariyar farinciki anan zee tashiga ciyar da makusantanta suna ramawa suma ciro wani guntun tayi tanufi bakin Aysha dake kusada ita tanata murmushi cikin murmushi Aysha ta bude bakinta tasaka mata nan ma aka dau tafi itama Aysha guntun ta dauke ta bata tana lakuta mata sauran akumatu dariya duk aka dauka ganin Abinda tayi kamar ance Aysha tadago sai suka qara hada idanu da aymaan wani mugun kallo ta jefeshi dashi ta kauda kai Dan buda idanu aymaan yayi yana kallonta saikuma ya kauda kai yana kwafa acikin zuciyarshi bayan sungama kowa yakoma mazauninshi ya zauna Inda akabar zee kadai gaban wajen zaune a maxauninta anan ne Ahmad daya ari aikin m.c yafara gabatar da mawaqin dazai danyi entertaining dinsu be ambaci suna ba Kawai dai gabatarwa yayi mashi yakuma buqaci atafa mashi tafi din kau aka dauka wanda yayi daidai da shigowar mawaqin filin sanye yake cikin wani ratsatsen suit fari Inda yayi shigar mai combination din fari da jaa farin wando sai jar shirt yadora coat fari asama, wuyanshi sanye da jan necktie guntu, kaffafunshi sanye da fararen half cover, yar saisayyayar sumar kanshi sai shining take abayanshi kuma managern shine kuma mai sakarmashi kida shima cikin shigar suit saidai nashi baqaqe ne da wannan kyakyawan murmushin yaqarasa shigowa wajen yana kallon mutanen wajen dake tafamashi kowa idanunshi akanshi ahankali yadanyi bowing alamun godiya still murmushi afuskarshi habeeb kau tuni yanufi wurin setting dinsu Inda zai dinga sakarmasu kida musabaha Deen yayi da Ahmad dake gaban stage din sai washe baki yake mic din hannunshi Ahmad yabashi ya amsa yana godiya sannan yajuyo yana kallon audience din tun shigowarshi bugun zuciyoyin mutane biyu suka chanza, zee da Aysha Aysha binshi Kawai takeyi da kallo cikin mammaki da bugawan zuciya mammaki take yaushe yayanta yadawo daga tafiyar harya zo nan din, saidai kuma sai take ganin kamar bashi ba duba da wasu dabi'u dayakeyi wanda kamar banashi ba, ga sumarshi yar kadan sa6anin ta yayanta dakeda yawa kuma a kwance luff zee kau bata ganshi ba don yana daga can gefe ne kuma yana facing mutane saidai zuciyarta wani irin bugu take kamar zata faso qirjinta, sosai takejinta awani yanayin da bazata iya musaltashi ahankali Deen yayi gyaran murya sannan cikin harshen turanci ya gaida mutanen wajen yakuma gabatar da kanshi ta hanyar amfani dasunan da akafi sani dashi wato *Balarabe* sannan yatayasu murnar wannan taron dasuke na zagayowar ranar haihuwar diyarsu yana kuma yin fatan allah ya maimaita Tunda yafara magana zee taqame a kujerar datake zaune kwalwarta ke birgita mata cikin kai tana jin kamar bamaa duniyar ba take wannan muryar... waye mai wannan muryar? ahankali Deen yayima habeeb alamun suje zuwa, nan take habeeb yashiga aikinshi Inda ya sakarmasu wani cool kida mai dadin gaske lumshe idanunshi Deen cikin son daidaita nutsuwarshi daya rasa Inda ta fece tun shigowarshi wannan wurin yanemi duk wata nutsuwarshi yarasa, Abinda besaba faruwa dashi ba yasaba hallarta taron daya linka wannan jama'a linki ba linki amma beta6a tsintar kanshi a irin wannan yanayin ba sai wannan karon, meyasa? Ajiyar zuciya yasauke ahankali yana iyakar bakin qoqarinshi wurin cooling down humming yafarayi cikin cool voice dinshi yana lumshe idanunshi ahankali yafara rero waqar birthday dayayi composing saboda taron sosai waqar ke tafiya cikin wata iriyar salo mai narka zuciya tsit wajen ya dauka kowa hankalinshi akanshi suna sauraron yadda yake rairo baitukan waqar cikin qwarewa da salo na daban kasa ko kyafta idanu Aysha tayi akan Deen, kallonshi Kawai take kamar tana kallon wani hallita daban yaushe akhie yazama mawaqi? Tunda yafara waqar zee tarasa awane duniyar take ciki, komai ya burkuce mata, zuciyarta, kwalwarta, ruhinta suka shiga harmutsawa takasa gane takaimaiman Abinda ke faruwa akewayenta Kawai Abinda take iya ji shine wannan muryar Deen kau a bangarenshi shima bugawar da zuciyarshi keyi yafara affecting waqarshi don sai sarqewa yakeyi akai akai duk iyakar bakin qoqarinshi naganin ya daidaita nutsuwarshi abin ya faskara, jiyake kamar zuciyarshi zata tsinke saboda gudu habeeb dake gefe yana playing piano yana lura da yanayin Deen dukda bakowa zaiyi saurin fahimtar uneasiness din nashi ba amma shi yagane don yasan Deen yasan yadda yake aikinshi, dole akwai Abinda yake damunshi dukda Deen nadan kallon gefen zee saidai baya wani tsayawa kallonta don shi kanshi ba Acikin nutsuwa yake ba bare har yatsaya kallon wani abin aymaan duk Abinda ake idanunshi nakan zee yana lura da halin data shiga ahankali yaga tamiqe tsaye daga kujerarta tana kallon Deen daya juya mata baya shima Deen sai akayi daidaitoni ya juyo side dinta cikin waqar yana ambaton birthday girl sauke idanunshi yayi kanta tana atsaye tana kallonshi shima wani irin bugu zuciyoyinsu sukayi lokaci guda dukda basu tantance juna ba don zee bata hangenshi sosai saboda hular kanta shima bega fuskarta ba sosai saboda boye rabin fuskar da hular tayi ahankali ya cigaba da waqar yana kallonta zuciyarshi na lugude _Happy Happy birthday... to... you..._ yaqarashe baitin da daddaya lokacin da zee tasa hannu tazame hular kanta tafada baya cak numfashin su biyu ya dauke na wucin gadi kallon juna suke kamar idanunsu zasu fado Babu mai iya kwakwarar motsi acikinsu tsit wajen ya dauka kowa idanunshi akansu jikin Deen ne yafara rawa yadago hannu yana nuna zee da yatsarshi dake rawa lips dinshi ma na rawa as well "Z... Zainab?.." yafada cikin wata iriyar murya ko motsi zee batayi ba Kuma ko kyaftawa idanunta dake kanshi basayi ahankali yafara kusantota still yana nunata jikinshi na rawa har lokacin "Zainab.." ahankali kowa yafara tashi daga saman seat dinshi kowanne idanunshi akansu harda habeeb shima da besan meke faruwa ba ahankali zee tafara takawa tanayin baya baya ganin yana kusantota kallo daya zakayiwa su biyun kasan babu wanda kecikin hayyacinshi "Zainab.. stop, please" yafada ganin tana qara nisantarshi "stop!" yafada yana nufota da sauri kamar mahaukaci saurin juyawa tayi kamar wanda abin tsoro yabiyo tana tattare rigarta tayi hanyar barin garden "No! Zainab!" inji Deen yana maramata baya "Balarabe!" inji habeeb yana takema Deen baya shima ------ saukowa yayi daga cikin motar ya maida kofar yarufe hannu yasa ya gyara red guntun necktie dinshi sannan ya zagayo ta dayar 6aren motar bude back seat yayi yadan zira jikinshi ciki can saigashi yafito riqeda abu ahannunshi maida kofar yayi yarufe yama kulle motar gabadaya sannan yajuyo dago abin hannunshi yayi yana kallo qaton bunch of flowers ne mai glass vase daga qasa wajen mariqinshi misalta kyawun flowern 6ata bakine saidai masu karatu suyi hasashe da kansu saidai kallo daya xakayi mata kasan tsaddadiyace ta qarshe murmushinshi na gefen baki ya su6ucemashi lokacin dayakai hancinshi jikin flower din ya sinsina qara riqeta yayi dakyau sannan yafara takawa cikin takunshi ta qasaita ya nufi Inda yake kyautata zaton nan ake taron tafe yake yana saqe saqen yadda zata kaya tsakaninsu don yasan akwai chakwakiya agaba yana cikin saqe saqenshi yaji kamar hayaniya na kusantoshi dagowa yayi wanda yayi daidai da bangajeshi da akayi baya baya yayi cikin ikon allah kuma yasamu ya tsayar da kanshi saurin juyawa yayi yabi figure din daya wuce dagudu da kallo dukda wulgin mutum Kawai yagani amma yagane itace juyowa yayi yaga meya biyota saidai kafin yayi hakan yaji anqara bangajeshi again wanda hakan yayi sanadiyar su6ucewar flowern hannunshi ta fadi aqasa jikake tassss! tayi qarar fashewa cikin zafin nama ya damqi gefen rigar wanda ya bangajeshin ya maidoshi baya daqarfi daga yunqurin yin gaba dayakeyi dagowa sukayi atare suka kalli juna lokaci guda oily eyes dinsu na sarqewa ana juna....✍πŸ? *please masu kirana ina typing kuna maidomin aiki baya, koyaya nadaga kafin nagama wayar Abinda narubuta ya fece shiyasa ma bana dagawa, please ku dinga yin haquri tunda ku ma kunsan inamuku iya qoqarina* Ummin FasihuπŸ§šπŸ»β€β™€οΈ? 8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *πŸ™πŸ»β€β™‚οΈDEENπŸ™πŸ»β€β™‚οΈ?* *084* *THE REUNION* wani irin jada baya su biyun sukayi kamar wadanda aka tura da force mai qarfi alokaci daya suka sake wara oily eyes dinsu akan juna suna kallon juna kamar suna ganin wata hallita daban ne ba mutum ba wani irin rawa inner part dinsu ya dauka zuciyoyinsu na wata iriyar halbawa kamar zata faso qirjinsu habeeb ne yafara qarasowa wajen saidai babu shiri yaja wani irin mugun burki lokacin dayayi tozali da Deen guda biyu suna kallon juna dauke numfashinshi yayi yana wani irin kwalalo idanu waje kamar zasu fado daga socket dinsu daidai nan kingin jama'ar suka qaraso wajen Inda suma sukaci karo da the same scene suma anan suka taka burki suna kallonsu kowanne speechless wani irin gasping Aysha tayi mai sauti tana yin baya baya aymaan dake bayanta yayi saurin tarota daga faduwar datayi niyyar yi tafado jikinshi "Hey.." inji aymaan yana kallon yadda take farfar da idanu mummy ce data lura dasu tayi saurin qarasowa wajensu itama takama Aysha din da kejin kanta na juyamata ganin hakan yasa itama umman Ahmad matsowa sai aymaan ya sakarmasu ita ahankali Mussadiq yaqara jabaya still idanunshi dasuka fara sauya launi akan Deen, komai na jikinshi rawa yake ga jijjiyoyin kanshi dasuka fito rad'o rad'o cikin kidima da fitar hayyaci yasa hannu yazaro wata qaramar pistol from nowhere ya nuna Deen da haryanzu yakasa motsi daita yadda jikinshi ke rawa haka hannunshi dake riqeda bindigar keyi don saima yitake kamar zata silale dukda iyakar qoqarin dayakeyi na riqeta sosai "w..who are you?" yafada cikin wata iriyar murya dake rawa sosai duk buda idanu mutanen wajen sukayi suna kallonsu cikin kidima "speak or I shoot!" inji Mussadiq cikin qaraji jikinshi na rawa sosai yana qara nuna Deen da bindigar, kallo daya zakamashi kasan baya cikin hayyacinshi don ko cewa akayi ya danna kunamar bindigar baya iyawa saboda rawan da ilahirin jikinshi keyi shikau har lokacin Deen kasa ko kwakwarar motsi yayi Kawai yana tsaye ne yana kallonshi kamar gunki rolling idanu aymaan yayi cikin zuciyarshi yana cewa 'ai dama nace wannan mutumin mahaukaci ne' "mu..Mussadiq" "speak!" Mussadiq ya katse Ahmad daya fara magana "Mussadiq calm down.." "go away!" yafada yana maida akalar bindigar kan Ahmad "listen son.." "who are you? kusu wanene!" yaqara fada yana pointing dinsu duka yana jabaya, sosai alamun gigita ta bayyana ajikinshi ahankali bindigar ta su6uce a hannunshi dake karkarwa ya cigaba da kallon Deen yana haki "calm down son.. calm down, this is your twin.. Mujaheed" inji Abbu dake qoqarin calming dinshi down dago rinnanun idanunshi yayi ya kalli abbu "yes, Mujaheed.. your lost brother" "No.." inji Mussadiq cikin muryar mai kama da rad'a "yes.." "he's dead" yaqara fada "he's alive" "No" "calm down" "No.. No!" yafada yana dafe kai "Mussadiq.." inji Abbu again yana qoqarin kusantoshi "No, don't come closer.. don't" yafada yana jada baya duk tsayawa sukayi suna kallonshi saurin juyawa yayi cikin sassarfa zai bar wajen sai gani sukayi timm yafadi aqasa gasping mutanen wajen sukayi sukayi saurin nufarshi dagoshi sukayi sukaga kamar ma baya motsi "aymaan quick kawo mota" inji Abbu juyawa aymaan da be motsa daga Inda yakeba tundazu yayi yanufi parking space Ahmad kuma yanufi Deen dahar lokacin baya motsi kamar wanda aka dasa "Deen" yafada yana ta6a kafadarshi saidai beko dago bayan bare ya kalleshi, idanunshi nanan kyar akan Mussadiq habeeb ma yana daga baya kusan shima suman tsayen yayi don yakasa motsawa daga Inda yake saidai ya kalli wannan ya kalli wannan atsakanin Deen da Mussadiq aymaan ne ya qaraso da motar wajen yafito da taimakonshi aka daga Mussadiq aka sakashi abayan mota tareda Aysha da itama tuni tasuma aymaan yashiga front seat dashi da Abbu yayinda Ahmad yaja hannun Deen suka nufi motarshi shima yasakashi a front seat habeeb yayi saurin binsu yashiga backseat shikuma Ahmad yazagaya mazaunin driver ganin hakan yasa su kingin suka shiga wata motar Inda akabar ummy datace zata tsaya tareda zee agidan ajere motocin suka fita daga gidan suka halba titi *** dagudu zee tayi hanyar stairs tana hayewa da bibbiyu bibbiyu ba don allah ya tsareba data sha qasa yadda rigar keta tadeta tana kawo mata tirjiya a gudun nata bata ja burki akoina ba sai dakinsu Inda tashiga ta maido kofar tarufe ta danna sakata sannan tanufi toilet dagudu shima tabude tashige tarufo harda murza makulli. komawa tayi ta jingina da kofar tana maida numfashin gudun datayi _Deen_ _Deen dinta tagani_ _Deen dinta_ hannu bibbiyu tasa ta toshe bakinta dasu tareda silalewa qasan tiles wani irin kuka yazo mata mai tsuma zuciya tashigayi hannunta toshe da baki dukkan ilahirin jikinta na gab gab kuka take da dukkanin zuciyarta jikinta na rawa sosai, she can't believe yau idanuwanta Deen suka gani, Deen dinta, her timid, silly boyfriend. wanda ta yanke qauna dasake sakashi a ido. zuciyarta takasa yarda, kwakwalwarta takasa dauka. bugun kofar dataji ne yasata dan tsagaitawa daga kukan datake kofar dakin ake bubbugawa ana kiran sunanta data saurara saitaji muryar ummy ce sosai take bubbuga kofar tana kiranta tazo ta bude maida kanta zee tayi jikin kofar ta lumshe idanu wasu hawaye nasake gangaro mata tanajin ummy nata haukan bubbuga kofar da kiran sunanta amma takasa koda motsi ne bare ta iya tashi ta budemata *** tsaye yake yana kallon Mussadiq dake kwance bisa gado ta glass kofar dakin a gefe guda kuma yana sauraron Dr dakemusu bayyanin cewa yanzu komai normal dama shock ne kuma lokacin dazai farka zai sakeshi komai zai koma daidai haka ya tsaya yana kallon photocopy dinshi dake kwance ko kyaftawa babu kwakwalwarshi ta hargitse ta yamitse yarasa wane tunani ma zaiyi "Balarabe" muryar habeeb tadawo dashi daga duniyar kallon Mussadiq dagowa yayi ya kalleshi saikuma ya maida kallonshi akan mutanen wajen yana binsu da kallo one after the other mutane biyu Kawai ya iya shaidawa acikinsu, daddy da mummy yarasa meke faruwa, meyasa yake gane gane, wane irin mafarki ne wannan harmutsatse? dafarko yaga Zainab, macen da yasan qila harya mutu bazai qara ganinta ba yazo kuma yaga wani mai irin kammaninshi sak yadda kasan kanshi yake kallo a madubi yanzu kuma mummy da daddy wadanda shidai a Nigeria yasansu, to meke faruwa ne? wannan wane irin birkittacen mafarki ne mai dogon zango? yaushe zai farka? yakamata mafarkinnan yaqare hakanan tunkafin kwalwarshi tayi bursting suma shi suke kallo cikin tausayawa halin dayake aciki don kallo daya zaka mashi kasan tsabar taurin rai ne Kawai yakeyi mammaki ma suke yadda shi ya iya jurewa be suma ba, idanma sumar ne aishi ya cancanci yayita tunda shi kwata2 besan komai ba, everything just came at sudden ne, besan yanada yan uwa ba, besan shi twin bane, besan yanada iyaye bayan wadanda yasan sun rasu ba sa6anin su Mussadiq dasuka san dashi maida kallonshi akan habeeb dake kallonshi yasan mafarki be dakatuwa harsai yaqare amma bazai iya dauka ba kuma soyake ya farka ko ya bar wannan page din na mafarkin ahankali ya matsa kusada habeeb yakama hannunshi yariqe gamm yana kallonshi "habeeb ka fiddani daga nan, ka kaini wajen kaka" shike maganar amma saiyaji kamar bashi ke motsa bakin ba, ganin komai yake amafarki shiru habeeb yayi yana kallonshi yama rasa Abinda zaice mashi "habeeb wani irin mafarki nakeyi, don allah ka tasheni ko ka fiddani daga nan" tasake fada yana Jin kanshi soo empty wani irin tausayinshi ya tsirgama mutanen wajen suna kallonshi cikeda tausayawa "nima mafarkin nake Balarabe, wai ka rabe gida biyu" inji habeeb cikin yin qasa da murya, kallo daya zakamasu kasan they're totally confused "nima, nima naganni agabana, gani tsaye gakuma wani nidin agabana, kuma.. kuma naga Zainab.. Zainab dita, mubar nan habeeb... kwalwata zata fashe" "Kamal" muryar mummy ta katseshi juyowa sukayi suna kallonta babu ko kyaftawa harta qaraso gabansu idanunta sun duri ruwa sosai tausayinshi ke tsuma zuciyarta "Kamal ba mafarki ba kake, this is real"tafada tenderly kallonta yakeyi Babu ko kyaftawa "mummy?" yafada ahankali kamar maison jingina dagaske ita dince kada mashi kai tayi hawayenta na gangarowa "eh son, mummy ce. mummyn Zainab. it's real...taho taho ka zauna" tafada tana jan hannunshi tanufi kujera binta yashigayi kamar rakumi da akala har ta zaunar dashi sai binta da ido yake "Kamal this is real, ba mafarki bane, nice.. mummyn Zainab, wancan kuma daddy, ka tuna? kuma dagaske kaga Zainab kuma dagaske ku biyu ne masu irin kammaninka, kai tagwaye ne" kafeta yayi Kawai da idanunshi yana kallonta confused "iyayenka basu rasu ba, mahaifinka ne Kawai yarasu amma mahaifiyarka nanan, tana nan da ranta, wancan kuma twin dinka ne, kaine Hassan shine Hussain, bayanshi kuma kanada qanwa Aysha duk suna nan Dubai ne, kaima saceka akayi tun kana qarami aka kaika Nigeria amma kai ba dan Nigeria bane, kai Balarabe ne, Dan saudia, mahaifinka mutumin saudiya ne mahaifiyarka kuma yar misra, Kaka ba kakarka bace bakada alaqa daita, ga danginka nan suna nan, saceka akayi.." kuka ne yaci qarfin mummy tashigayi da dukkanin zuciyarta bama ita kadai ba babu wanda babu kwalla a idanunshi idan ka cire Deen daketa kallon bakin mummy tunda tafara magana cikin kuka mummy tace "Deen ba sunanka Kamaldeen ba sunanka Mujaheed.. Mujaheed Al-hassan shikuma twin dinka Mussadiq Al-hassan, kai Balarabe cikkaken Balarabe ne Kamal" batool datakasa jurewa ta rungume umman Ahmad dake kusada ita batareda tasani ba ta cigaba da rusa kukanta kamar ranta zai fita "eh Deen, kai asalinka Balaraben saudiya ne, duk acan mahaifanka suke, acan aka haifeka dakai da Dan uwanka Mussadiq saidai shekararka uku aka saceka aka kasheka ashe baka mutu ba, qila Kawai wucewa dakai akayi aka nuna an kasheka saigashi ankaika Nigeria. mahaifinka yarasu amma mahaifiyarka nanan tana cikin garin nan yanzu haka" inji Abbu shima cikin kwantar da murya bin Abbu shima Deen yake da ido Kawai becewa komai Kawai kallon motsin bakinshi yakeyi "daga baya muka gane hakan, wannan dalilin yasa muka quduri aniyar hadaka da danginka, shine ma dalilin zuwanmu Nigeria lokacin daka fara ganinmu, babu wani aikin daya kaimu, kai ka kaimu Deen kuma bawai saboda aiki yasa muka gayyatoka nan ba mun gayyatoka ne don hadaka da ahalinka da bakasan dasu ba" inji Ahmad da shima idanunshi suka rine aymaan sai kallon Deen yake shima da jajjayen idanunshi yakasa cewa komai saida Deen yagama sauraronsu tsab sannan ya maida kallonshi kan mummy da har lokacin hawayen idanunta sukaqi tsayawa "Kaka..." yafada ahankali kamar mai rad'a "ku kaini wajen Kaka don allah" yafada yana kallonsu cikin wani yanayi hawayen mutanen yakasa tsayawa ganin yadda yake magana so confused kamar dan shekara biyun daya 6ata tsakiyar hanya yana gantali Abbu zaiyi magana aymaan ya katseshi "No Abbu.. zaku fasamashi kwalwa, don't stress his brain futher, yana buqatar hutu, idan kuka takura za'a samu matsala" saikuma ya kalli Deen "kanason zuwa wajen Kaka?" saurin kadamashi kai Deen yayi kamar qaramin yaro "taso to, taso nakaika" yafada yana miqamashi hannu Dan tsayawa yayi yana kallonshi saikuma ya miqamashi hannu ya tadashi aymaan yayi gaba jaye da hannunshi suka fice daga wajen wani kukan batool taqara rushewa dashi, bama ita kadai ba harda sauran matan dakin, mazan nema masu dan tauri taurin rai iyakarsu hawaye kowa jikinshi yayi sanyi lakwas jikin daddy yafi nakowa yin sanyi, ganin Deen a irin wannan yanayin ba qaramin sanyayamashi jiki yayi ba, yarasa Inda zai tsoma ranshi yaji sanyi habeeb dai haryanzu bece komai ba saidai alamu sun nuna shi ya gamsu da bayyanansu don they make sense to him don shima yadade yana zargin Deen ba bahaushe bane, komai nashi sak na larabawa dukda hasken fatarshi ba irin fauu dinnan bane irin na kajin jikin kajin turawa amma dai daka ganshi kaga ruwan Arab haka suka zauna jigum har aymaan yadawo duk dagowa sukayi suka kalleshi "anyi mishi allurar barci to settle his brain" Abinda Kawai ya iya fadamasu kenan duk Ajiyar zuciya suka sauke kowa najin zuciyarshi da ruhinshi badadi daga baya ne suka yanke shawarar yakamata wasu sukoma gida wajensu ummy Abbu da umman Ahmad da abban Ahmad suka tafi sukabar mummy, daddy, batool data maqale sai aymaan da Ahmad suka kwana a asibitin. πŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’œ ahankali yafara bude idanunshi dasukayi mashi mugun nauyi dafarko biji biji yafara gani kafin daga baya ganinshi yafara yin clear ahankali yake bin dakin da kallo cikin son tuna inane wajen shikadai ne kwance adakin, ganin yanayin dakin yasashi gane a asibiti yake ahankali yakai hannu yadafa kanshi dake mishi ciwo ahaka yasamu ya lalla6a yamiqe zaune cigaba da bin dakin yake da kallo cikin son tuno Abinda yafaru ahankali abubbuwan dasuka faru jiya suka shiga dawomashi tiryan2 shiru yayi confused, abin tambaya anan shine dukkan wadannan abubbuwan mafarkine ko dagaske yafaru, idan mafarkine meya kawoshi asibiti harya kwanta? yana cikin wannan saqe saqen aka bude kofa aka shigo dagowa yayi ya kalli kofar sai suka hada idanu da mummy wani sanyayyan murmushi ta sakarmashi tana qarasowa ciki nan kingin mutanen suka ida shigowa da daddaya yake binsu da kallo yaga duk mutanen jiya ne, kenan hakan na nufin ba mafarki ba yake? "sannu.. ya jikin?" inji mummy tana masa murmushi tenderly shima murmushinshi yayimata asanyaye sannan ahankali yace "alhamdulillah" aymaan ne yashigo Ahmad biye dashi sai habeeb abayansu duk da idanu yabisu yana tuna every bit of conversation dinsu na jiya saurin qarasowa wajenshi habeeb yayi cikin murnar ganin ya farka "Balarabe" yafada yana kallonshi Dan murmushi Deen yayimashi shima yana kallonshi "ya jikin?" ya tambaya "alhamdulillah" ya amsa mashi shima asanyaye qarasowa aymaan yayi wajenshi shima "sannu..akwai Abinda ke damunka ko kemaka ciwo" ahankali ya girgiza kai "No, just a slight headache" "sannu.. zai daina insha allah..mummy adan bashi wani abu" inji aymaan da to mummy ta amsa nan da tashiga hadamashi tea duk shi suke kallo kamar t.v harta gama hadawa tabashi amsa yayi yana godiya sannan yafara sha yasha sosai sannan ya ajiye, nan ya buqaci yin sallah habeeb ya rakashi bakin toilet yayi alwala yafito sannan yahau sallayar da har an shimfidamashi ya rama sallar asuba don lokacin har gari yawaye don takwas ma tawuce duk fita sukayi lokacin dazaiyi sallar yarage saura habeeb Kawai da Ahmad yana nan zaune ya idar da sallar aka bude kofar atare duk suka dago suka kalli kofar don ganin mai shigowa Aysha ce tsaye abakin kofar batool abayanta hada idanu sukayi da Deen dake kan sallaya har lokacin kafe juna sukayi da idanu yayinda bugun zuciyoyinsu ya tsananta ahankali hawaye suka taru a kumburrarun idanun Aysha tana kallon yayan nata dasu shima dai Deen kallonta Kawai yakeyi yana Jin wani feeling na alaqa mai qarfi gameda ita a zuciya da gangan jikinshi "come in Aysha, come in and say hi to your brother" inji Ahmad dake kallonsu dagowa tayi ta kalli Ahmad saikuma tasake kallon Deen dashima ita yake kallo har lokacin dafa mata kafada batool tayi cikin qarfafa gwiwa hakan yasa Aysha fara takawa kamar wadda kwai ya fashemawa aciki ta nufi Inda Deen yake tana kallonshi saida ta qaraso gabanshi ta tsaya suna kallon juna saikuma tayi qasa ta durqusa cikin daidaita tsayinsu tana kallonshi still sake kafe juna da idanu sukayi na wani lokaci ahankali Deen yasakarmata guntun murmushi bin dimple din tsakiyar gemunshi Aysha tayi da kallo babu kyaftawa "what's your name?" yafada ahankali dagowa tayi tana kallon eyeball dinshi "A..Aysha" tafada cikin rawar murya hawayen idanunta na gangarowa "meyasa kike kuka?" ya tambayeta da harshen turanci saurin goge hawayen tayi tana girgiza kai "n..na daina" tafada cikin muryarta dake a disashe murmushi yayi shima idanunshi na chanza launi miqomata hannu yayi kallon hannun tayi saikuma ta dago hannunta ahankali tasaka acikin nashi ya riqe gamm wani feeling na jini na yawo ajikinsu "dagaske ke qanwata ce?" ya tambaya ahankali yana kallonta wasu hawayen suka gangaromata tana kadamashi kai dasauri "dagaske ni twin ne kuma...

Chapter 68 of 81