tata fama dashi don daya saka maganin abaki zaita kakari kamar zaiyi amai Dakyar ake samu ya hadiye
Yana gama sha ba dadewa barci ya daukeshi don dama cikin maggungunan harda na barci
Su kaka kau ranar sun dade kafin suyi barci, firarsu kawai sukesha cike da annushuwa kallo daya zaka masu kasan yau rana ta musanmman ce agaresu don farincikin dasuke aciki a bayyane yake a fuskokinsu
Suma sai can cikin dare barcin ya sacesu suka 6ingire
*WASHEGARI*
Tunda ta tashi bata komaba tana gama sallar asuba ta sauko tashige kitchen
Maid biyu ta iske cikin kitchen din suna hidimar dora breakfast
Sunyi mammakin ganinta by this time kuma a kitchen, shanye mammakinsu sukayi suka shiga gaidata
Amsawa tayi tana nufar abubbuwan dasuka dora tana bubbudewa
Saida tagama sannan ta rurrufe ta juyo garesu
"Akwai cow leg?" ta tambayi daya daga Maid din
"eh madam Akwai a Deep freezer, shi kikeson ci ne?" inji maid din cikin ladabi
"ciromin shi farfesu zanyi" tafada tana wucewa wajen tukwane ta dauki wata yar madaidaiciya
Yin yadda tace maid din tayi tana mammakin zee a zuciyarta don da wuya ka ganta kitchen da sunan girki sai idan mummy ta tilastata bakuma wai don bata iyaba ne kawai dai qiwuya ce da son jiki irin nata na yar hutu
Cikin qanqanin lokaci tafara hada farfesun qafar sa dinta wanda yaji citta sosai da kayan qamshi kamshi
Kan kace me? Har kitchen din dama gidan baki daya ya garame da qamshin girkinta
Koda tagama yar warmer tasamu tajuye aciki ta fita daga kitchen din tabar maids din da gulma ke cinsu a zuciya
Koda tashiga dakinta ajiyewa tayi kan mirror tayi tafada bathroom don freshen up
Kamar kullum yau ma qarfe 10 suka bar gidan don zuwa hospital din
Duk sammakon zee da zumudin dole saida tajira har lokacin da mummy tafito
Haka suka fito zuwa mota tanata cin magani don taso taje dawuri ya kasance farfesun da tayi mashi zai fara sha amma yanzu ai tasan ya riga ya karya
Haka tashiga front seat ta zauna ta dora yar warmer dinta a cinya tana cigaba da kumburi while itakuma mummy tashige baya ta zauna batama san wainar da zee ke toyawa ba
*HOSPITAL*
Mutane sosai suka tadda a dakin wadanda duk mazane yan unguwarsu
Da sallama suka shigo dakin amma kasancewar mutanen dakin nada yawa shiyasa ba duka suka lura da shigowarsu ba
Zaune taganshi bayanshi jingine da pillow hannunshi riqe da dan mug din shayi yana kur6a ahankali
Fuskarshi dauke da wannan murmushin mai karamashi kyau yana sauraron wani daga cikin matasan dasuka kewayeshi yana bashi labarin irin wahalar dasuka sha wajen nemanshi aranar da abin yafaru
Dauke idanunta tayi daga kanshi ta qarasa wajensu kaka dake masu sannu da zuwa
Wuri tasamu ta zauna tana gaidasu sannan ta tambayi lafiyar mai jiki
Duk amsa gaisuwarta sukayi kaka na tambayarta ya gajiyar jiya
Murmushi kawai tayi batace komai ba
Jin sun cigaba da magana dasu mummy yasa ta daga kai da niyyar satar kallonshi
Caraff suka hada ido dashi don tunda kunnuwanshi suka jiyomashi muryarta lokacin dasuke gaisawa dasu kaka ya maido hankalinshi kanta
Ganin ya tsareta da ido expressionless yasata dan yimashi murmushi
Kamar jira yake sai shima murmushin ya su6uce mashi
Dauke kai tayi daga gareshi fuskarta still da murmushi ta maida kan kaka da aka dage sai labari ake badawa baki washe kamar ba ita bace so moody a yan kwanakinnan ba
Bata qara kallon sashin Deen ba Amma tanajin idanun shi akanta Hakan kesa murmushi ke su6uce mata akai2 tana kauda kanta duk lokacin da ya su6uce mata cikin basarwa
Ba'a jimaba mutanen dakin suka fara ragewa don dama duk mazane yan dubiyan inda yawancinsu daga nan wajajen sana'arsu suka nufa
Matan dake dakin daga kaka sai matar mallam Nasiru sai mummy sai zee, baaba Abu ankoma gida dazu sai anjima zata dawo da kingin matan unguwa masu zuwa dubiya
Saida duk suka fice sannan ta dago ta kalli saitinshi
Hada ido suka qara yi don dama ita yake kallo
Harara ta gallamashi tana qara kauda kai
Dan wara idanunshi dasuka qara dan washewa yayi yana kallonta saikuma ya 6ata fuska
Kaka ce ta dago taganshi ahaka
"Ohni ma'u, wai haryanzu baka shanye shayin ba kasha maganin koko sai lokacin shan yawuce sannan?"
Maida kallonshi yayi akan kakan sai yaqara kumbura fuska
Dariya mummy tayi tace
"besha maganin bane?"
"hmm wannan me shegen tsoron maganin? Tundazu nake mashi magana yawani fake da shan shayi don inmance, to kar nake kallonka ka gama kwalailaitar saika shashi"
Dariya duk sukayi zee kuma ta dago ta kalleshi tana murmushi taga sai yamutsa fuska yake
"ko bejin dadin shayin? Gashi naga Tundazu yake hannunshi wataqila ma ya huce" inji mummy
"ai har wuce hucewa ma yana iyawa don tun kafin kusaran zaku zo aka bashi yayi yasha abashi maganin amma yaita jujjuyashi a hannu, da anyi magana saiya kai baki kamar shan gaske yakeyi" inji matar mallam Nasiru tana gallamashi hararar wasa
"A'a kubarshi, wataqila ba shayin yakesoba, bari mugani azubamashi kunun gyada ko zai iya sha kinsan idan mutum yatashi daga rashin lafiya bakin sai ahankali sai anringayi ana daurewa
Caraff zee tace
"mummy gama wani farfesu nan, sai inga kamar zaifi sonshi, ko?" tafada tana maida akalar tambayar ga Deen
Shiru Deen din yadanyi sannan ya Kada kai alamun eh
"to? To ai saiki zubamashi yasha yayi yasha maganin tun kafin lokacin shan yawuce inba sokake muyimaka duraba" inji matar mallam Nasiru tana Dariya
Qara hade cikakkun girarshi yayi yana kauda kai
Tashi zee tayi tana murmushi ta Fiddo wani dan bowl dake cikin yar ledar warmer din sannan ta Fiddo warmer din ta bude ta zuba acikin bowl din ta miqama kaka
"A'a kai mashi tunda yanzu yana iya komai da hannunshi sai yasha, wazai biyewa shiriritar tsantsaninshi?" inji kaka
Tashi zee tayi tawuce wajen Deen taja kujera ta zauna sannan tabashi
Saida ya harareta sannan ya amsa ahankali yana bin farfesun ciki da kallo
"kasha ko nakira wancan matar tayimaka dura yanzu" tafada qasa qasa yadda shikadai zaiji
Dagowa yayi daga kallon farfesun ya gallamata harara ta daga kafadu tana murmushi
Daukar spoon din yayi ya diba yakai bakinshi
Lumshe idanunshi yayi kunnenshi daya na motsi don dadi
Bude idanun yayi ya kalleta yaga itama shi take kallo, daga mashi gira daya tayi alamun 'ya?'
Murmushi kawai yayi ya kuma diban farfesun yana hadawa da naman wanda aka yankasu qananu qananu daidai ci yakai baki yana tauna ahankali
Acan bangaren su kaka mummy ce tace
"ya naga kamar baya magana? Naga Tundazu beyi magana ba"
"hmm ai haka yake idan ciwon ya tashi, kai ko sanyi yadan bugeshi yanzu zakiji muryarshi ta chanza ta shaqe bare mai gabadaya, wancan atak (attack) din ma saida yayi kwana uku muryarshi bata fita lokacin a makaranta ma ne yasamu atak din wai wata shegiyar yarinya ta watsamashi abu mai sanyi ajiki, wlh bakiga yadda ya burkuce ba. Lokacin ina gida nagama dan wanki na akashigo aka cemin ga Kamal can asibiti, hankali tashe naje na taddashi a wani yanayi numfashi ma kanshi Dakyar yake ja, kai allah dai yakawomana qarshen wannan ciwon don wlh yana wahalar dashi, yanzu sai ahankali ahankali muryar zata dawo" inji kaka
Tunda kaka tafara magana murmushin fuskar zee yafara daukewa harya dauke dab
Bata qara fuskantar kingin magangganunsu ba saima kalmar
_wai wata shegiyar yarinya ta watsamashi abu mai sanyi_ dayaita eoching a kunnenta
Wacece yarinyar?
_*ni?*_ tabaiwa kanta amsa
Citayi zuciyarta ta quntata Bawai don taji haushin kalaman kaka ba don Gaskiya tafada, the bitter truth
Kalaman kaka sun tunasar daita cewa ta ta6a kwantar da Deen gadon jinya akan dalilin da haryanzu idan ta tuna saita ji kunya
Yamata alhairi ita kuma ta sakamashi da sharri, ta sakamashi da kwanciya jinya
Halau kuma taqara da6awa, taqara kwantar dashi, ta tadomashi ciwonshi tadowar datafi wancan Halau a dalilin taimakonta, is she that wicked?
Deen da tun lokacin da yanayin fuskarta ya chanza ya kafeta da ido babu ko kyaftawa
Yasan abinda takeji, yasan abinda take tunani shima duk sai yaji ba dadi
Ahankali yakai hannunshi ya dora akan nata dake kan hannun kujerar datake akai
Bata dagoba kamar yadda yakeso kuma bata motsaba
Dan damqar hannun yayi yana son yayi magana amma yakasa
Wani abu taji ya tsirgamata ajiki Hakan yasa tayi saurin zame hannunta daga nashi ta miqe tsaye
Wucewa tayi ta nufi kofa da sauri zata fita taji mummy na tambayarta ina zata
Daga mata wayar hannunta kawai tayi alamun zata amsa waya ta maida wayar ta kara a kunne tafice
Binta da kallo Deen yayi harta fice
Maida kallonshi yayi kan farfesun gabanshi cikin wani yanayi, shiru yayi yana kallon bowl din kamar yana ganin wani abu aciki saikuma yadanyi slight murmushi ya sake daukan spoon din ya cigaba dasha
Yasha sosai sannan ya ajiye, Ganin Hakan yasa kaka tasowa da ledar magani a hannunta tana wani cin magani don ma karya kawomata wasa
Kamar yadda yasaba yanzu ma Dakyar ya iya Hadiye maggungunan sai wani kakari yake
Komawa yayi ya kwanta yana maida numfashin shan maganin dayayi yanajin matar mallam Nasiru namashi tsiya
Maida idanu yayi ya rufe Saidai ba barci ba yake
Shiru zee bata dawoba tun mummy na jiran dawowarta don su tafi harta Fiddo waya ta kirata
Basu dade da gama wayarba ta dawo dakin
Bude idanu Deen yayi jin ta dawo ya cigaba da Binta da kallo Saidai ko kadan taqi yarda su hada ido bama dashi kadai ba da duk yan dakin
Tashi mummy tayi tayimasu sallama akan sai anjima insha allah sannan taqara yima Deen fatan warwarewa
Daukan basket din abincin jiya daddadare dasuka kawo zee tayi itama tayimasu sallama tafito batareda ta yarda ta kalli side din Deen ba dukda kau yadda takejin idanunshi akanta.
Maida idanun Deen yayi ya lumshe bayan fitarsu yana jin ba dadi sosai, ahaka har wani barcin yasake daukanshi... ✍️
Juma'at mubaraq in advance✨?
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*027*
Wunin ranar haka ta qarasheshi rai a jagule
Kwata2 batada walwala aranar tabi ta tsagwami kanta ga sense of guiltiness datake ji duk lokacin da ta tuna
Da daddare da mummy ta aiko akan tafito sutafi dojewa tayi ta hanyar kawo qabali da ba'adi Hakan yasa mummy tayi tafiyarta ita kadai
A bangaren su Deen kau haka sukayi Wunin yau da shige da ficen yan dubiya
Mutane sunzo sosai most especially yan unguwarsu
Duk wanda zaka gani da farinciki a fuskarshi yana yimasu barka da arziqi
Kaka yau baki be hutaba, wuni tayi 6a66atu saboda yan dubiya Saidai Hakan sam be dameta ba don sosai taji dadin yadda aka damu da dan kyakyawanta ana nuna mashi kulawa don har riqe wadanda sukazo takeyi a kwanya tana lissafin wadanda basuzo ba kuma tana zuba ido taga ko zasu zo don Gaskiya wanda bezo yaga dan jikallenta ba yayi mata barka ba to zata qullaceshi akan Hakan don aganinta abin azo aimata barka ne dan jikanta ya leqo lahira ya dawo
A bangaren Deen kau yau yini yayi murmushi don haryanzu muryar shi sai a slow
Fara'ar nan tashi mai qaramashi kyau yawuni daita, yana tarbar kowanne daita
Saidai a qasan zuciyarshi tunaninta ne maqale a wajen
Shi besan metayi ba, fushi tayi koko jin badadi akan abinda kaka tace
Yasan dole taji ba dadi Amma ai Gaskiya kaka tafadi kuma Batasan itace ba da bazata fadi agabanta ba, kodayake beda tabbacin idan tasan itace zata cigaba da washemata 36 dinta don duk wanda ya ta6ashi batayin wata2 wajen jefashi blacklist dinta
Tunawa yayi da yadda yasamu Dakyar yashawo kanta wajen haqura da zancen wancan karon don ita da a dole saita bishi makarantar taga wace hegiyar gorar take niyyar sheqemata jika, Dakyar yasamu ta haqura da Hakan bayan ya laftamata qaryar shi bema iya ganeta don dama karo sukayi abin hannunta mai sanyi ya zubarmashi ajiki Hakan yasa ta haqura ba don taso ba takuma gargadeshi akan ya dinga kulawa
Haka suka cinye Wunin yanata looking forward to dare don yaganta
Saidai me? Sai gani yayi mummy ce kawai tazo
Yanajin kaka na tambayarta ina aminiyar tata don haka take cemata wani sa'in kasancewar takwarar baaba Abu ce
Mummy ta amsa da yau batajin dadi ne shiyasa batazo ba
Nuna alhini kaka tayi takuma yimata fatan samun sauqi tana cewa ai tanama qoqari, wannan zirga zirgan ita kanta tana iya jawo wani abin gwara ta huta
Sosai ran Deen yaqara jagulewa, sai duk zumudinshi na ganinta yakoma ciki
Hakan na tabbatar da dagaske fushin tayi, to amma fushin me? Shi bega abin fushi anan ba
Har lokacin tafiyar mummy yayi ta tafi ranshi a jagule yake.
Yauma saida kaka ta tilasta mashi maganin yasha Dakyar sannan yakoma ya kwanta ba don yana jin barcin ba
Ya dade idanunshi biyu kafin can barcin ya sadado ya daukeshi
A bangaren zee kau sai bayan tafiyar mummy taji kuma tana danasanin rashin Binta
Haka kawai taji babu abinda take son gani kamar shi
Haka taita daurewa tayi wanka ta kwanta da niyyar yin barci amma takasa
Idanunta biyu lokacin da mummy tadawo don shigowar motarsu a kunnenta taji
Tashi tayi daga kwancen datake Tundazu ta leqa ta window tana hangen mummy data fito tayo gaba bala na biye daita da basket din abincin safe da suka kai
Sakin labulen tayi bayan shigewarsu ta dawo kan gadon ta zauna tana jingina da jikin gadon
Haka kawai takejin haushin rashin zuwan datayi don jitake ajikinta kamar tayi missing din wani abu
Itama ta dade tana karatun jaki sannan itama barci ya sadado ya dauketa
*WASHEGARI*
Yau Deen ya tashi da qwarin jiki sosai don da kanshi ma yashiga toilet din ward din yayi freshening up
Sosai farinciki ya kama kaka na cigaban da akasamu don har magana yana dan yi dukda muryar ba fita take sosai ba
Yau ma yan dubiyan da basu samu zuwa jiya ba sukaita zuwa
Tun Deen na baza ido don ganin ta inda su zee zasu 6illo har yakai da tambayar kaka ganin har sha biyun rana tayi shiru
Dariya kaka tayi tace ai dama bada wuri suke zuwa ba ranar juma'a sai nan da bayan antaso sallar juma'a zuwa la'asar zasu zo
Kada kai kawai yayi yayi shiru yana jin komai bemashi dadi
*4:30pm*
Zaune yake kan gadonshi ya zuro qaffafu qasa hannunshi riqe da plate din faten doya yana diba da cokalin hannunshi yana ci cikin sanyinshi
Agefe kuma kaka ce da wasu mata zazzaune ana maida yadda akayi
Knocking din kofar d'a kayi ya katse firarsu kaka
Murda kofar akayi aka shigo da sallama
Dakatar da spoon din abincin da yayi niyyar kaiwa baki yayi jin muryoyin da yayi
Dagowa yayi ya kallo kofar sai idanunshi suka sauka ana zee dake bayan mummy riqe da basket din abinci
Ga mammakin zee sai taga ya kauda kai ya cigaba da cin abincinshi
Sai jitayi wani abu marar dadi ya tsirgamata a zuciya, ba haka tayi tsanmmani daga gareshi, tasaba da kallonshi ta kuma sanshi da kallo don rabin communicating dinshi da idanu yakeyi saikuma murmushi
Yadda taji tana missing dinshi dinnan tayi tunanin yafita, tayi tunanin idan yaganta zai kafeta da idanu kamar yadda yasaba babu ko kyaftawa
"Aminiya, jiki yayi sauqi kenan?" inji kaka
Murmushi tadanyi tana ida qarasowa wajensu
"aikaudai kaka, ina yini? Ina yininku?" tafada tana kallon kingin matan dakin bayan ta gaida kaka
Duk amsawa sukayi da lafiya lau kaka na dorawa da
"ya jikin kuma? Mamanki tace bakiji dadi ba"
Murmushi tayi cikin jin kunya, ta rasa dalilin dayasa tun farkon haduwarsu da kaka taji tana jin kunyarta
"alhamdullilah kaka, ya mai jiki?" tafada tana dan satan kallon Deen daketa aika abincinshi kamar ma besan abinda akeyi ba
"kai ai jiki alhamdullilah, jiki sai qara kyau yake don yau dakanshi yaje yayi alwala yakumayi sallar asuba atsaye gakuma magana anfara kinga kau ai ana samun sauqi"
Jin kaka tace yana magana yasa ta dago ta kalleshi shima daidai ya kallota
Suna hade ido yaqara kauda kai yana hade gira
"kai masha allah! Haka akeso ai allah yaqaro sauqi, naji dadi sosai wlh" inji mummy cikin farinciki
Itama zee kauda kai tayi daga kanshi ta kalli kaka da murmushi a fuskarta tace
"masha allah, Allah yaqara sauqi"
Kaka da duk dadi ya isheta ganin yadda suma sukayi farinciki da Hakan tace
"amin amin, ai dole mu godewa allah da ni'imarsa dayaimana, da haka da haka zakuga ya warke tass kamar beyi ciwoba"
"to allah ya amince ai muma fatan mu kenan, allah yaqaro afuwa" inji mummy
Duk amsawa mutanen dakin sukayi da amin
Sai a sannan kaka ta dago ta kalli Deen daketa cin abincinshi hankali kwance
"kyakyawa na, bakaga su Zainabu sunzo ba? Kaida Tundazu ka dameni da yaushe zasu zo kuma yanzu kayi kamar bakasan sunzo ba"
Dago kai yayi yana dan kumburi
"O'O! Ni ban tambayeki itaba mummy na tambaya" yafada cikin muryarshi dabata fita sosai
Duk Dariya mutanen dakin sukayi kaka tace
"ikon allah, yo da ita da mummyn ba duk daya bane? Nima ai dama ba ita nace ba, su nace"
Kauda kai yayi yana qara hade gira sannan ya kalli mummy dake kallonshi tana murmushi yace
"mummy ina wuni?"
Cikin fara'a tace
"lfy qalau son, ya jikin? Jiki yayi sauqi ko?"
Murmushin nan nashi dake lo6ar da tsakiyar gemunshi yayi yace
"eh mummy, alhamdullilah"
"to allah yaqaro sauqi, ana dai shan magani ko?" tafada cikin sigar tsokana
6ata fuska yadanyi jin an ambaci maqiyinshi Hakan yasa duk mutanen dakin suka sa Dariya banda zee dake murmushi Tundazu
"wannan din? Ai yau ma saida muku sha fama, wai mutum yasan fa maganin amfanin kanshi ne amma yaita wulaqanci, wlh da don tashi ne da Saidai ya dawwama ahakan besha"
Daya daga cikin matan dakin tace
"haba kai kuwa? Kamar ba namiji ba? Ai mata aka sani da tsoron magani da allura"
"hmm to kindai gani, gwara gwara ma allurar bejin tsoronta amma magani? Dama an ambaceshi zakiga ya 6ata rai irin an ambaci maqiyinshi dinnan, don dai ma ni jar wuyace duk abinshi haka zan tusashi gaba saiya shanyesu, yo to idan na kyaleshi haka za'a tafi bazai shaba, kuma ina akaga sauqi ba'a shan magani, in don ta shine haka zamu dawwama a asibitin bayada asara" inji kaka
Duk Dariya suka sakeyi wannan karon harda zee datayi chuckling tana dan rufe baki tana kallon yadda Deen keta cika yana batsewa
"A'a yanada asara tunda ai jikinshi ne zai gayamashi" inji wata mata cikin matan dakin
"ba sai yasan ciwon jikinshi ba din? Daya sani ai bazai kawo wasa kwata2 akan harkar samun lafiyarshi, ni kuma fa? Allah kadai yasan cinikin da ya wuce ni cikin yan kwanakinnan" ta qarashe tana buga tagumi cikin jimami
Dariya dakin ya sake dauka
"aikuwa kamar kinsan kullum sai anta zirga2 gidanki dasafe, duk mun saba dake kwata2 bama jin dadin saye wani Wurin" inji dayan matar
"yo to nima ai ba dadin ba nakeji, ina dadi a zama waje guda ba shige da ficen 'yan aninnai? Amma ahakan ja'irin ke neman qara zaunar damu" tafada tana hararar Deen dake kumburi Tundazu
"A'a kaka, yafa isheku haka, yaya zaku tisa d'ana agaba kuna mashi tsiya? Da kanshi zaiji ko surutunku? Kedai kawai kice rashin shige da ficen yan aninnan naki ne damuwarki bawai rashin shan maganin ba kuma ai Son jarumi ne tunda gashi cikin kwana biyu sauqi yafara samuwa sosai don haka abar takuramana hakanan" inji mummy cikin sigar wasa
Wani dadi Deen yaji Hakan yasashi murmusawa ya kalli kaka yayi mata gwalo Hakan yasa duk aka qara kecewa da Dariya
Cigaba dayimashi tsiya kaka tayi mummy na kareshi
Wannan dramar yasa duk damuwarsu ta yaye sunata Dariya
Dagowa Deen yayi ya kalli zee daketa Dariyar dramar su kaka
Samun kanshi yayi da kasa daina kallonta don sosai Dariyar ta dace da fuskarta
Sai jiyayi shima farinciki ya mamaye zuciyarshi ya shiga murmushin da besan yanayi ba idanunshi still kanta
Kamar ance ta kalloshi saikau suka hada ido
Tsuke fuska yayi ya kauda kai irin na fushin nan
Murmushi tayi kawai ta cije lower lip dinta tana cigaba da kallonshi
Sake juyowa yayi da niyyar satar kallonta suka sake hada ido
Harararta yayi Hakan yasa zee dan waro idanu, ta nuna kanta alamun da ita yake?
Kada mata kai yayi yana sake Harararta, sosai hararar tashi tabata Dariya amma saita danne ta kauda kai tana 6ata fuska tana ta6e baki kamar mai shirin kuka
Sake juyowa tayi ta kalleshi still fuskar a kwa6e sai taga shima ita yake kallo
Ganin ta kalloshi yasashi qara hade gira ya kauda kai yana satar kallonta da wutsiyar ido
Qara ta6e baki tayi tana kallonshi ☹️
Qara juyowa yayi ya kalleta sai gani yayi ta dagomashi yatsarta ta qarshe 🤙🏻 alamun su shirya
Dan kauda kai yayi yana Rungume hannuwa a qirji yana fuming😠
Qara daga mashi yatsar tayi tana qara kwa6e fuska
Dan maqe kafada yayi yana qara Rungume hannuwa a qirji
Dariya yake bata sosai amma batasonyi Hakan yasa take dannewa, abin mammaki sai jitayi kamar sunawa juna magana da zuciya
Idan yana body language dinshi saitaji kamar tana jin muryarshi a zuciyarta
Sauke idanu tayi qasa tayi kalar tausayi 😔
Murmushi yadanyi yana kallonta yana jiran ta dago
Kamar ta sani saita dago tadan kalleshi
Dan huro hanci yayi sannan shima ya daga yatsarshi ta qarshe alamun 'to mu shirya'
Harararshi tayi tareda murguda mashi baki ta kauda kai acikin zuciyarta tana cewa _it's my turn nima , zakaga jan aji_
Dan wara idanu yayi ganin murguden datayi mashi saikuma yakai hannunshi yana dan yamutsa sumarshi
Tana jin idanunshi akanta amma taqi kallonshi tayi kamar su kaka take sauraro saida ta wajigashi sannan ta dago ta kalleshi
Kamar kau jira yake yayi saurin dago yatsarshi yana marairaice fuska
Duk yadda taso danne dariyarta saida ta murmusa Hakan yasa shima murmusawa yana qara dago yatsar
Saida tadan harareshi sannan tashiga dago yatsar nata kamar zatayi kamar kuma zata chanza shawara Hakan yasashi kafeta da idanu ba kyaftawa
Yamutsa fuska tayi ta kalleshi tadan turo baki sannan ta dago mashi
Cikin jindadi yaqara dago nashi sukayi kamar sun qulla Deen na raba tsakiya
Saikuma suka bawa kansu Dariya zee tashiga qumshe tata yayinda Deen yasaki murmushi mai sauti wanda yasa su kaka juyowa suna kallonshi
Saurin maida hankalinshi yayi ga abincin gaban shi da sai yanzu ya tuna dashi yashiga ci batareda murmushin yabar fuskarshi ba
Haka suka qare zamansu yayinda su kaka ke firarsu acan gefe kuma zee da Deen ke nasu firar ta kurame wanda idan ba sa ido kayi ba baka ta6a ganewa, fuskarsu sai tashin murmushi suke
Ahaka har lokacin komawansu gida yayi
Ba don sun so ba suka rabu dukda zee bata nuna a fuska ba kamar shi Saidai acan qasan zuciyarta jitake kamar su dawwama ahakan
Haka sukayi sallama dasu suka fito
Har suka kawo gida akwai kingin murmushi a fuskarta dakuma ta tuna wani abin saita rufe bakinta tana qumshe Dariya
Haka ta qarashe wannan yinin ashiririce ga yawan murmushin da takeyi every now and then
Shima Deen Hakan take a bangarenshi, kallo daya zaka mashi kasan yau he's very lively don fara'ar yau tasha banban data kullum, annurin dake fita a fuskarshi yau na dabanne
Saturday and sunday sunzo sun wuce lfy, Deen jiki sai qara kyau yake don masha allah yanzu sosai yake recovering speedly
A bangaren alaqarsu da zee kuwa sai abinda yaci gaba
Sosai suke jin dadin kasancewa tare don har aqage suke suga juna
Da lokacin Zuwansu yayi haka zakaga yana daga kai yana duban agogon dakin akai2, hankalinshi be kwanciya sai yaga shigowarsu
Itama a 6angarenta dataga lokaci yakusa zataita zumudi, bata qaunar abinda zai 6atamasu lokaci ko yaya ne
Saidai duk zumudin son ganin junan maganar dake shiga tsakaninsu idan suka hadun be wuce ta tambayeshi ya jikin ba shikuma ya amsa daga nan zasu ja bakinsu su tsuke sai body language ko kallon kallo
*MONDAY*
Yau ake fara zaman kotu akan case dinsu master da zee
Qarfe 10:00am ake fara zaman amma su zee suna wajen tun 9
Saida 10 takusan da yan mintuna sannan aka fara shiga kotun ana zazzaunawa
10am daidai alkali yashigo dakin shara'ar wanda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 81