kuka, kukan da batayi ba tun faruwar wannan abin.
Toilet tashige ta kunna shower tashiga ciki tayita kukanta har Saida muryarta ta disashe
Ko daddare ma kasa rintsawa tayi, tana Kwance lamo kamar mai barci amma ba barcin take ba
Rayuwar dasukayi da Deen kawai take tariyowa a kwalwarta From A-Z
Tayi kukan da bata ta6a yiba a wannan daren shiyasa koda ta tashi washegari idanunta sukayi suntum suka kumbura
Su mummy basuyi mammakin haka ba don sunsan kukanta mai dalili ne, gwara ma tayi ta wanko abinda ke zuciyarta da ta barshi a daskare a wajen.
Jirgin qarfe 12pm zasu bi Hakan yasa sukabar gida Tun qarfe 11:15am suka dauki hanyar airport.
Tafiya suke sunata fira cikin raha ana Dariya banda zee da idanunta ke kafe akan glass din motar na gefenta tana kallon masu wucewa, tana yiwa Nigeria kallon qarshe don ta qudura a ranta ita da Nigeria kuma sai wani ikon allah
11:30am dot suka shigo filin jirgin saman
Parking daddy yayi a parking space sannan duk suka bubbude koffofin motar suka shiga fitowa.
Zee ce qarshen fitowa.
Wani iska ne ya bugi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanunta tana shaqar iskar sannan tasake budesu
Su daddy ke fiddo trolley dinsu daga cikin motar Yayinda itakuma ke bin harabar airport din da kallo ba wai na qauyanci, A'a na bankwana, tana bankwana da her beloved country Nigeria inda zata tabar mutane masu matuqar muhinmmanci acikinta wanda bata jin zasu qara haduwa nan kusa Saidai idan su zasu bita can.
she's gone too, maybe forever, maybe not.
12 saura minti goma su Ummu batool da Zainab sukayi bankwana dasu daddy
Rungume zee su mummy sukayi in turn duk suna iya qoqarin ganin basu bayyana rauninsu ba ta hanyar xubar da hawayen dake forming a idanunsu.
Itadai zee barin nata tayi suka gangaro don bataga amfanin riqesu ba
Saida sukaji ana qara sanarwa sannan suka haqura da bankwanan suka juya Ummu batool riqe da hannun zee suka fara tafiya
Tunda suka fara tafiya zee bata qara waigowa ba har Saida suka kai daidai kofar dazasu shiga cikin inda passengers din keta shiga sannan ta waigo
Su mummy da daddy ta hanga can nesa tsaye still suna kallonta, dan murmushi tayi musu dukda batada tabbacin zasu gani saboda nisan dasuka yima juna sannan ta juya suka ida shigewa.
Mummy ce ta dora fuskarta akan kafadar daddy hawayenta na gangaro mata
Dafe bayanta daddy yayi idanunshi akan kofar da suka shige shima yana trying very hard don ganin yayi controlling emotion dinshi.
Ahankali zee kebin Ummu batool dake riqe da hannunta still suka isa inda ake tantancewa aka tantancesu suma sannan suka shige ta inda zasu bi su 6illa filin da jirgin da zasu hau yake.
Babu 6ata lokaci suka shiga jirgin suka nemi seat number dinsu suka zauna, zee na daga ciki daidai window Ummu batool na kusada ita.
Tunda ta zauna ta maida kanta baya ta jinginashi da kujerar datake akai ta lumshe idanunta
_*Xainab bazan ta6a barinki ba duk rintsi, zan jajirce a soyayyarki babu gudu babu ja da baya*_
_*I promised, I promised I'll never break your heart, never!*_
Jitayi anfara announcing akan a daura seatbelt jirgin na shirin tashi
Tana jin Ummu batool ta jawo belt din seat din nata tana dauramata Hakan yasa taki bude idanun
_*Zainab ina sonki, yanzu, da'iman, abadan*_
_*please marry me*_
_*am sorry... For everything*_
_*natafi.. Am gone.. Maybe forever.. Maybe not*_
Jin Sautin tashin jirgin ne yasata bude jajjayen idanunta Ahankali
Kallon window din gefenta tayi tana hangen waje ta nan
Dagawa jirgin yafarayi har ya ida barin qasa
Kurawa waje ido tayi tana ganin yadda suke qara yiwa qasa nisa
"bye.." tafada ahankali daidai da gangarowar wasu hawaye masu zafi
"Natafi... Maybe har abada.. Maybe not"
_safe journey ✈️_
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*DUBAI (Abu dhabi)*
Tafiyar awa bakwai sukayi kafin su iso Qasar Gamayyan Larabawa wato Dubai, a birnin tarayyar qasar wato Abu dhabi.
Agajiye suka fito daga jirgin don ba qarya sun zaunu
Dare ne a qasar don lokacin har 10 ta dan gota Saidai garin tarr yake da hasken fitilun streetlights kamar da rana, mutane sai hada hada akeyi wanda mostly Larabawa ne
Amsar trolley dinta zee tayi hannun Ummu batool dake Miqamata ta Fiddo abin ja din tashiga ja tana bin bayan Ummu batool datayi gaba waya kare a kunnenta
Tafiya take tana dan qarema Wurin kallo a fakaice tana hango tarin banbancin dake tsananin nan da qasarta Nigeria
Gashi duk wanda zakaji ya bude baki yayi magana to larabci ce ziryan ta
Cigaba da bin Ummu batool tayi har suka ida fita daga airport din wanda Hakan yayi daidai da gama wayar Ummu batool
Juyowa tayi ga zee tayi mata murmushi
"marhaban biki bintii! Welcome to Dubai, qasar farincikin ki"
Murmushi zee tayi tana Kada kai kawai
"muje can mujirasu, sunce suna dab da isowa" inji Ummy tana nufar wata rumfa daga gefensu na dama
Itama zee jan akwai ta tayi tabita abaya kamar raqumi da akala
Gwadama zee inda zata zauna Ummy tayi ta zauna sannan itama ta zauna kusada ita tana qara daddana wayarta
Karawa a kunne Ummy tasakeyi da alamu kira take
Magana tafarayi da larabci tana dan sirkawa da hausa
Hausar datake dan jefawa aciki yasa zee gane ashe kwatancen inda suke takema wanda take wayar dashi
Can sai ga wata baqar mota tazo ta paka daga dayan side din
Ummu batool na ganin motar ta gyara yafin gyalenta tana cema zee ta tashi su Abbu sun iso
Wayar Ummy tasake daukan qara Hakan yasa ta daga tana kama trolley dinta itama tayi gaba zee da itama ta miqe tsaye tabi bayanta
Tsallakawa dayan gefen sukayi suka nufi baqar motar
Kafin su qarasa aka 6alle murfin kofar mai zaman banza wata budurwa wanda bazata wuce tsarar zee tafito sanye da arabian jallabiya ta yane kanta da veil din rigar irin yanin Larabawa
Bangaren driver kuma wani babban mutum ne yafito shima sanye cikin farar jallabiya da hula tashi da qwaqwa a kanshi
Kallo daya zee tayi musu ta shaidasu, Abbu ne da batool.
Da sauri batool ta taresu ta rungume Ummy tana tsuwar murnar dawowarta tana Dariya Ummy ma na tayata
Abbu ne ya qaraso wajen shima fuska fall murmushi yana yima batool magana da larabci da alamun tsokanarta yake don nan da nan ta cinno baki Ummy kuma na cigaba da yimata Dariya
Maida kallonshi yay akan zee dake kallonsu tundazu cikin fara'a yace
"lale marhaban yayata"
Murmushi zee tayi don dama hakan yake kiranta kasancewar sunan yayarshi gareta
Dan russunawa zee tayi tana gaidashi cikin murmushin yaqe shikuma yana amsawa da fara'a yana tambayarta ya suka baro su daddy tana amsawa da lfy lau
Batool ce tasaki Ummy ta nufi zee cikin murna ta rungumeta itama tana dan tsallen murna
Dan murmushi kawai zee tayi batace komai ba
Dagowa batool tayi daga rungumarta datayi
"ashe da gaske dake za'azo? Wlh dafarko ban yarda ba na zaci jana akeyi" inji batool din cikin hausarta dake radam don dukda anan aka haifesu iyayensu basuyi sake sun bari yarensu ya kufce masu ba.
Murmushi zee kawai tasake yi batace komai ba
"to ai yanzu da kika ga zahiri kin yarda ko?" inji Ummy tana yin gaba da kayanta
Saurin amsar trolley din hannun zee batool tayi da hannu guda takuma sarqaho hannun zee da dayan suma suka shiga bin su Abbu dasukayi gaba tana cewa
"eh Ummy na! Yau yaya zaisha haushi, nasamu wacce zamu dinga hademashi kai" tafada tana Dariya
"ko wacce zasu dinga hademaki kai ba" inji Abbu dake saka trolley din a booth
Dan kumbura fuska batool tayi saita juyo ta kalli zee dake sauraronsu tace
"wai ukhty zee? Aini zaki za6a ko? Akhie bayada kirki ko kadan"
Murmushi kawai zee tayi tana jin Ummy na bata amsa da
"ai ke kinada kirkin ko? Ni ki kyalemin diya tasha gajiya kina damunta da surutu, babu abinda zatayi cikinku, ku dai da kuka saba sai kuyita fama"
Tura baki batool tayi tana cewa
"kai Ummy, ke dama da kin samu wata saiki mance da ni yar gaban goshinki ce" tafada tana shigewa shiga bayan motar bayan zee Tariga ta shiga
"yaushe? Aini tuni na mayar dake bayan qeya dake da yayan naki, ga yar gaban goshi na nan" tafada tana nuna zee daketa murmushin dramarsu
6ata fuska batool tasakeyi sannan ta kalli Abbu dake qoqarin tada motar
"Abbie, kaji ko?"
Dariya Abbu yayi yana cewa
"kyaleta, Aini ko me za'ayi auta ta itace da muqamin kujeran goshi na, itace ta gaban goshi na always" yafada yana tada motar
Dariyar jindadi batool ta fashe dashi sannan ta juyo wajen zee dake kallonta tayimata gwalo wanda Hakan yasa murmushi qara su6uce mata dama tuni ba Tun yau ba tasan halin batool, drama Queen ce ta gidan gaba
"to kinji kibar wani jin dadi, nima akwai masu sona" tafada tana gwalemata idanu
Dariya duk mutanen motar sukayi banda zee datayi murmushi kawai, Abbu yaja motar suka bar harabar Airport din
Tafiyar da batakai ta minti tallatin ba sukayi suka qaraso gidansu
Horn Abbu ya danna a bakin gate din gidan nasu
Ba'ayi seconds 20 ba aka wangale masu gate din
Danna hancin motar Abbu yayi cikin gidan suka shige
Direct parking space Abbu ya nufa yayi parking a kusada wata mota dake a wajen
Bubbude koffofin motar sukayi duk suka firffito
Kallon parking space din ummy tayi sannan tace
"Aymaan bayanan ko? Naga banga motarshi na"
"hmm yana hospital, wai yau night garesu" inji batool dake gyara gyalenta
Girgiza kai ummy tayi
"workaholic kenan, ni ban ta6a ganin wanda ya tattara dukkan imaninshi yaba aiki ba kamar Aymaan"
"to yaya kikeson yayi? Yaita zaman gida kamar mace? Karki manta yadda aikin likitanci yake musanmman irin wannan bangaren nashi na gynecology, ceton rayyuka yakeyi kuma dukda albashinshi nasan yanada lada awajen allah" inji Abbu yana ciro kayan bayan booth
"dukda haka Abbu, abin yayi yawa, gana fa gani wani lokacin ba lokacin aikinshi bane amma kuma a kirashi yakuma je, wani sa'in ma baida taqamaimai lokacin kanshi idan ba weekend ba" inji ummy tana kama hannun zee suka nufi cikin gida gabadaya
"ai saboda qwarewarshi tasa ake yawan nemanshi har haka, ke ba abin murnar ki bane ace danki is a professional doctor wanda ake jidashi a daya daga cikin shaharrarun asibitocin dubai?"
Dan ta6e baki ummy tayi tace
"dama ai kai ke daure mashi gindi shiyasa yake abinda yakeyi din, ku kuka sani ai, like father like son"
Murmushi duk sukayi daidai lokacin da suka qarasa shiga cikin gidan.
Dayake a gajiye suke kuma dare yayi basu wani tsaya jan zance ba ummy tasa batool ta wuce da zee dakinta da yanzu zai zama nasu su biyu akan cewa za'a biyo su da dinnersu sama.
Bankwana sukayima juna batool tayi gaba jaye da trolley din zee itakuma zee na take mata baya Yayinda ita kuma ummy tawuce tareda Abbu part dinshi
Sama suka hau inda anan sukaci karo da dakuna uku ajere
"kinga dakin ummy nan" batool tafada tana nuna dakin farko
Wucewa sukayi zuwa na tsakiya
"kinga dakinmu nan"
Sannan ta nuna na qarshe
"kinga dakin akhie, dayake farin kura ne saboda tsoro saiya za6i abarmashi na quryar yadda duk abinda zai faru saiya fara taddamu kafin ya taddoshi besan mu damuke kusa kusa da stairs ba munfi samun opportunity din guduwa idan ma abin tsoron yazo shi kafin ya 6a66aka ma mun bar layin unguwar"
Murmushi mai sauti zee tayi batareda tace komai ba
Bude kofar dakin tayi ta tura ta sannan ta koma gefe tana cewa
"welcome to the princess chamber" tafada tana bowing dramatically
Shigowa dakin zee tayi still murmushi a fuskarta tana yan kalle a dakin.
Komai na dakin pink ne yayi kyau sosai dukda bekai nata na Nigeria girma da tsari ba
"to ya kika gani?" inji batool tana daga gira daya
"fabulous" inji zee tana wuceta taje ta zauna gefen gado tadan jinginar da kanta a frame din gadon cikin gajiya
"yes! Dama nasan you'll like it, bari allah ya kaimu gobe na gwada miki na akhie sai ki tantance mana wanda yafi kyau da tsari, kullum cikin rigimar muke babu mai raba mana gardama to yau ga raba gardama nan tazo"
Zee da duk ta qoshi da surutunta ta dago daga jinginen datake tace
"where's the toilet?"
"there, me zakiyi?" tafada tana nuna mata kofar toilet din
Tashi zee tayi tsaye tana warware gyalen kanta tace
"wanka, am tired and sleepy"
"ok bari na hadamiki ruwan" inji batool tana nufar hanyar toilet din
"No please, zan hada basai kin wahalar da kanki ba" inji zee
"Karki damu, nima na baqunta zan miki don kice am nice amma kina ganina nan shegen san jiki gareni, gwara kibari nayi maki yau din don wata rana da kudinki ba zaki nemi nahada miki naqiya" tafada tana shigewa toilet din
Dan murmushi tayi tana ta6e baki sannan ta cigaba da rage kayanta
Closet din batool din ta bude ta dudduba can ta hango towel din datake nema ta dauka ta daura daidai lokacin da batool tafito daga toilet din
Bata cemata komai ba tawuce toilet din don sosai take buqatar wankan ga barcin dake idonta sosai shima
Cikin yan Mintuna tayi wankan ta fito saita tararda batool har tayi shirin barci glass cup din fresh milk a hannunta tana kur6a
Qarasowa tayi tana niyyar jawo trolley dinta ta ciro kayan barci batool ta nuna mata nata data riga ta ciro mata
Godiya tayi mata ta daukesu ta saka tayi amfani da roll on din batool sannan itama tazo ta dauki nata glass of milk din ta zauna gefen batool tashiga sha
Tasha fin rabi sannan ta ajiye lokacin batool ta fita
Bata tsaya jiran komai ba ta dauki remote din dakin ta qure a.c din sannan ta haye gadon ta jawo bargo ta lullu6e tana sauke Ajiyar zuciya
Lokacin da batool tadawo har barci yayi awon gaba daita don dama agajiye take liss
Daukar remote din batool tayi ta rage sanyin a.c din sannan itama tahau gadon ta kwanta batareda ta rufa ba, itama cikin qanqanin lokaci barci yayi gaba daita.
*WASHEGARI*
Sosai zee taji dadin barcinta na jiya don tun bayan abinda yafaru bata qara barci irin na jiya mai dadi ba, shiyasa da safe ta tashi garass
Suna gama sallar asuba batool tajata suka sauka qasa don hada breakfast
Sosai Hakan ya burge zee don agidan basuda yar aiki ko guda sai maigadi kawai Komai su sukeyi da kansu.
Hada breakfast din suke batool nata zuba kamar radio itakuma zee na aikin sauraronta
Cikin dan qanqanin lokaci suka gama suka kuma jeresu a dining
Komawa sukayi sama sukayi taking turn Wurin yin wanka da brush sannan suka shirya
8:00am daidai suka sauko qasa don yin breakfast kamar yadda yake a al'adarsu
Lokacin suma su ummy da Abbu sun fito suma cikin shirinsu Hakan yasa duk suka hallara dining area din
Batool ce tayi serving dinsu gabadaya
Itadai zee duk cikin kayan shayi kawai ta iya sha da toast bread tabar musu kingin kayansu na larabawa
Sosai taji dadin zaman yin breakfast din don sosai suka nishadantar daita da firarsu
Itadai murmushi ne nata idan akayi abin Dariya bata tsoma bakinta sai an sakota a zance kuma Koda an sakota a taqaice take bada amsar
Ahaka suka gama breakfast din su ummy suka dawo falon sukuma su zee din sukayi clearing din table din suka dawo sukayi joining iyayen a falon aka dasa firar
Sai can wajajen 9am Abbu ya tashi don zuwa shirin fita ummy tabi bayanshi saiya rage saura batool da zee
Cigaba da ba zee labaranta da basu qarewa batool tayi zee na sauraronta can batool tayi excusing kanta wai ta manto wayarta sama zataje ta dauko tadawo
Kadamata kai kawai zee tayi tanajin dadi atleast kunnuwanta zasu huta kafin ta dawo
Ajiyar zuciya ta sauke bayan wucewar batool tana mammakin yadda komai yafaru so fast qaddara takawota nan bawai da niyyar ziyara ba ko komawa nan kusaba sai don zama na adadin lokacin da itama bata sani ba
Ajiyar zuciya ta sake saukewa sannan ta miqa hannu ta dauki wani daily magazine dake kan centre table tafara budewa tana going through dinshi.
A gajiye ya turo kofar falon yana tafe yana jan qafa alamun gajiya
Lapcoat dinshi matse a qasan hannunshi na dama briefcase kuma riqe a hannunshi na haggu
Sallama yayi ciki ciki yana yayatsine fuska alamun liss yake ya ida Qarasowa cikin falon
Hangota yayi zaune hankalinta gabadaya akan littafin dake hannunta bama tasan da shigowarshi ba
Ajiye briefcase din hannunshi yayi ya tsaya ya riqe kugu yana kallon bayanta don baya dama ta juya mashi
Cije lip din qasa yayi sannan ya ajiye Lap coat dinshi yafara tahowa cikin sanda ta bayanta
Zee batasan wainar da ake toyawa ba sai kawai jitayi fitt an fige magazine din hannunta ta baya
Kafin tayi motsi kuma aka rufe mata idanu duka biyun da hannuwa ta baya
Qara tasaki don sosai abin yazo mata so sudden takuma tsorata sosai
Duk yadda taso cire hannunshi daga idanunta kasawa tayi don ya hanata yin Hakan
Hannunta tafara miqawa tasama don lalubawa taji ko wanene, tasan dai bai wuce batool amma data kawo hannu saiya zame yana qumshe Dariya
Daidai nan batool ta fito daga daki tanufo qasa
Abinda tagani yasata Wara idanu kamar zasu fado
"Akhie!" tafada cikin tsantsar mammaki
Saurin dagowa yayi ya kalli inda yajiyo muryar batool ya ganta can tsakiyar stairs tana kallonshi baki bude
Gabanshi ne yafadi, idan wancan batool ce to wacece wannan? Abinda qwalwarshi ta tambayeshi kenan
Babu shiri yayi saurin cire hannunshi daga face din zee yaja baya yana kallonta
Kyafkyafta idanu zee tashiga tana miqewa itama tsaye
Hannu tasa ta murza idanunta yadda ganinta zai dawo sannan ta bude idanun ta juyo ta inda aka rufemata idanun
Turuss tayi ganin wanda bata ta6a expecting ba
Dan Wara idanu tayi tana kallon yadda shima ya Wara idanu yana kallonta sai kuma ta maida kallonta ga batool da itama haryanzu tana a inda take tana kallonsu... ✍️
Manage 👏
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*055*
*DR AYMAAN*
Janye idanunta tayi daga kan batool tasake maidowa akanshi
Cikin daburcewa yafara bata hqr cikin harshen larabci
Dariyar batool ce ta dakatar dashi
"batajin larabci akhie, she's hausa" inji batool tana Qarasa saukowa tana Dariya
Sake kallon zee yayi yace
"ohh, please kiyi hqr, nayi tunanin wancan ce am sorry"
Sauke idanunta kawai zee tayi batace komai ba
Batool ce ta qaraso tana cigaba da Dariya
"shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gaj..."
Bata qarasa ba ya fincikota ya kama kunnenta
"ni tsaranki ne?" yafada cikin larabci yana qara murda mata kunnen
Qara batool tasa tana matse ido cikin jin zafi
"wayyo akhie kunnena!"
Qara twisting din kunnen yayi yana cewa
"bani kike gayawa magana ba?"
Qara da tsuwa batool taita yi tana qoqarin qwace kunnenta amma takasa
Zee tunda suka fara take jinta uncomfortable, ga qarar batool datake ji har cikin dodon kunnenta
"amm... please leave her mana" inji zee tana kallonsu
Jin abinda tace yasa ya dakatar da murdawar dayake yiwa kunnen ya tsaya yana kallonta batareda ya saki kunnen ba
Ganin Hakan yasata dauke kanta gefe
"ka sakeni mana tunda tace ka kyaleni" inji batool tana 6ata fuska
Sakinta din yayi bayan ya gallamata harara yace
"ta ceceki da yau saina cire kunnen"
Yafada yana qara satar kallon zee da bata qara kallon gefensu ba Saima zamanta datayi
Da idanu Aymaan yayiwa batool nuni da wacece wannan?
Dariya batool tayi ta koma daga gefen zee din tace
"wai kinji uktie wai gulmarki yake da idanu"
Wara idanu Aymaan yayi sai ya nufota Hakan yasa ta qara Sakin qara ta ruga shima yabita suka fara zagayen falon
Tsayawa zee tayi ta saki baki tana kallon ikon allah don ita abin nasu ma mammaki yake bata
"afuwan akhie, afwan!" inji batool tana tana zillewa
"wlh yau zaki gane kurenki, yaushe nayi gulmarta?" yafada yana qoqarin tarota
"wlh bakai bane, bakai bane" tafada tana qara zillewa
Suna haka su ummy da Abbu suka shigo falon, Abbu cikin shigarshi na suit da alamun aiki zai fita
"ya subhanallilah! Meye haka?" inji ummy
Hakan yasa suka dakata daga abinda suke
"wlh ummy kiyimashi magana" inji batool kamar zatayi kuka
"Kun fara ko? Wai yaushe ma kadawo Aymaan?" inji Ummy
Hade gira Aymaan yayi
"yanzu yanzunnan kuma wai daga zuwana saita jamun sharri Wurin wannan" yafada yana nuna zee da haryanzu ke kallonsu
Tsaki ummy taja ta qaraso falon
"Allah ya shirya ku agaban baquwarma saikun saida halin, kun girma bakusan kun girma ba" tafada tana wucewa Wurin zee
Sosa lallausar sumarshi Aymaan yayi
"baquwa mukayi ne ummy?"
Dago zee ummy tayi sannan ta juyo ta gallamashi harara
"ba baquwa bace yar gidace kana ganinta nan don yanzu tama fiku iko da gidan"
"haba dai ummy, wannan wasane ko akhie?" inji batool
Gallamata harara Aymaan yayi yace
"ni meye hadina dake da zaki tambayeni? Tafiki iko da gidan, me zakiyi?"
Kumbura fuska tayi kamar zatayi kuka
Dariya Abbu dake sauraronsu Tundazu yayi yace
"Allah ya shirya ku, nidai karku koyawa yayata wannan halin naku, tana yar saliharta itama ta koma burkakka"
Dariya duk sukayi itakuma zee ta sauke kai tana dan murmusawa
Matsowa Aymaan yayi kusada Abbu cikin rada yace
"Abbu wai wacece?"
Murmushi Abbu yayi yace
"ai dole ka tambaya, kaida bakasan kusan mafi yawa cikin danginka ba.
To Zainab ce ta gidan daddy, daddyn Nigeria"
Wara idanu Aymaan yayi saikuma ya qara kallon zee da bashi take kallo ba
"you mean diyar Daddyn Nigeria?"
Kada mashi kai Abbu yayi in affirmation
"wannan yar yarinyar? Yaushe ta girma haka?" inji Aymaan cikin mammaki
Dagowa zee tayi jin abinda yace sai suka hada ido
Hararar da batasan tayi ba ta gallamashi don sosai taji haushin kiranta da yar yarinya dayayi
Ganin Hakan yasashi kauda kai yana Sosa qeya bakinshi dauke da murmushi
Dariya duk aka dauka falon ummy tace
"ba dole kayi mammaki ba? Yaushe rabonka da Nigeria? Almost 6years ba dole ta chanza maka ba?"
Qara satar kallonta yayi yaga bama gefen shi take kallo ba
"hmm ai zanje kwanan nan" yafada yana wucewa dining
"kamar duka kenan" inji ummy
"Allah kau ummy, bari aiki ya dan lafa, zan baku mammaki" yafada yana jan kujera daya ya zauna
"hmm allah yasa" inji ummy
"Amin dai ummy" batool ta amsa
Dagowa Aymaan yayi ya watsamata mugun kallo
"ba na hanaki sakamin baki a magana ba?"
Turo baki tayi ta koma bayan ummy
"bazaki zo Kiyi serving dina ba?" yasake fada yana huro hanci
Qara turo baki tayi sannan tazo ta wuce kitchen
Binta da kallo yayi sannan yayi kwafa ya juyo sai caraff suka hada idanu da zee, da sauri ta kauda kanta tana dan ta6e baki
"Daga zuwa sai cin abinci baka freshening up" inji ummy da tayi gaba jaye da hannun zee
"zanyi idan nagama, darabanil ju'i" yafada yana shafa cikinshi fuska a marairaice
"acici" inji ummy tana jan hannun zee suka nufi wajen Abbu
"muje mu raka Abbu kinji 'yata"
"to ni natafi, ma'asallama" inji Abbu
Fatan tsari Aymaan yayi mashi sannan suka fice gaba daya, Abbu a gaba ummy da zee abaya
Binsu da kallo yayi har suka fice sannan yadan daga kafadu
Batool ce tafito da kayan break wanda dama an fidda mashi nashi an ajiye incase idan yadawo
Zuwa tayi tana jerawa still fuskarta a kumbure
"tazo nan hutu ne?" inji Aymaan
"wa?"
"baquwar" ya amsa yana kallonta
Daga kafadu tayi tace
"kusan haka amma zata dan jima kadan"
Daga girarenshi yayi yace
"masha allah, kice mun qara yawa amma naga kamar bata magana, meyasa?"
"bari tadawo na tambayar maka ita"
Yiyayi kamar zai maketa tayi saurin ja baya da serving spoon a hannunta tana Dariya
Kwafa yayi kawai yajawo abincinshi yayi basmallah yafara ci
Acan waje kau har mota su ummy suka raka Abbu
Sallama sukayi da zee tana mashi fatan dawowa lafiya sannan ta juyo ta dawo ciki tabar ummy can tareda Abbu suna magana
Da sallama tasake Shigowa falon
Dago kai Aymaan da yanzu saura shikadai a falon yayi yana kallonta ya amsa
Kallonshi itama sukayi suka hada ido saita kauda kai
Stairs tanufa batareda ta yarda ta qara kallon gefenshi ba dukda yadda takejin idanunshi akanta
Binta da kallo yayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 81