kudi sosai, shiyasa dana shiga makaranta nafi mayar da hankali akan koyan turanci saboda idan naje ingila kinga bazan sha wahala ba na iya yarensu se daga baya na gane duk qaryace Ashe na watsar da Bokon na kama Kasuwa, amma Yayana da muka fara tare saura wata kadan ya kammala karatun Shari'a a Jami'ar Ikko"
Binta ta ringa dariya jin abinda yace, tace masa
"Wato Ingila kake so kaje, kaga ni kuwa ko yanzu naga damar shiga tikitin jirgi kawai zan yanke saboda inada katin zama yar qasa nacan"
"Haba dai?" Ya tambayeta kamar be yarda ba dan shaf ya manta da Mahaifiyar Alhaji kakarsu kenan Baturiya ce. Binta tayi murmushi tace
"Dagaske a can aka haifeni lokacin Dady yaje qara karatu kuma na zauna a gurin Mah seda ta fara rashin lafiya me muka da wo nan tare gaba daya harta rasu shekara goma kenan, idan kaima kana son zama dan qasar to ka Aurkjioieni Hawaii se Hawaiixna tafi dakai kaga shikenan zaka samu katin zama Dan Ingila"
Tuntube yaci, badan Allah ya taimakeshi wani takalmin dafaffen danqo ne sauciki a qafarsa da idan ka ganshi zaka dauka na fata bane da yasan babu abinda ze hana faratansa ficewa yau dukda haka seda yaji zafi ya dage qafar dayayi tuntuben da ita yana kada hannu Ledar daya ruqo mata ta fadi Binta ta dauke tana masa sannu, seda ya daidaita kafin sukaci gaba da tafiya, ita da bata san dalilin tuntuben nasa ba taci gaba da cewa
"Kaga shikenan ka zama baqin Bature, semuyi komawarmu can da zama dan ni daman nafi jin dadin can akan Nigeria, ko dan can nayi wayo shiyasa?"
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Rasa abinda zece mata yayi dan ya rasa zolaya ce maganar tata ko kuwa har ranta da gaske take? Idan zolaya ce to irin wannan maganar gaskiya bata dace ba domin dai sanin sa ba'a wasa da maganar Aure, idan kuma da gaske take to abune bame yuwu ba kai qarya ne ma me zatayi dashi baqauye da besan komai ba dan talakawa ita kuwa yar gata jikar Turawa gata nan son kowa qin wanda ya rasa kai wannan qanzon kurege ne kawai ba abune me yuwu ba. Zuciyarsa ta tambaye shi to idan da gaske take shin ze amince ne ko kuwa? Seya rasa amsar da ze bawa kansa dan haka yaci gaba da shiru har suka isa gida Itama da taji yayi shiru seta bar maganar, a Get ya sake zama tayi masa godiyar rakiya ta shige ciki Malam Saminu ya shiga zolayarsa yana cewa
"To kodai yar gida za'ayi da uwar masu gida da Baqon Alhaji?"
Audu ya kalleshi bedai ce komai ba Saminun yaci gaba da magana yana cewa
"Nayi mamakin yanda yarinyar nan ta shiga sabgarka, ka ganta nan sedauwar da uban suka tashi tsaye kafin ta saitu tabi hanyar kwarai farkon dawowarta saga Turai ma'aikatan gidan nan iska me dadi bama iya shaqa idan tana nan. Ta tsani Talaka a yanda take fada da bakinta ta kuma tsani duk wani abu da ze hadata da takauchi. Juma'a Juma'a Alhaji na sadaka a qofar gidan nan zaka ga an cika danqam haka zata fito ta watsa mutane tayi musu rashin mutunchi seda uban ya zaneta wata rana kuma da quruciya lokacin yanzun dai komai ya lafa dukda dai bazan ce ta bar halinta kaf ba amma ta rage sama da kaso Saba'in a ciki yanzu dai babu ruwanta damu idan kaga tayi rashin mutunchi to sabgarta ka shiga da muke taka tsantsan da ita kuwa lafiya lau ake zaune dama bata gaida mu bamu isa ba mu muke gaisheta kuma uban duk cikin Yaran yafi sonta shiyasa ma da Mahaifiyarsa ta karbi shahada ya bata irin sunan ta".
Audu dai jinsa kawai yake sedai ko kadan be hango wani hali na rashin mutunchi da Saminun yace tana dashi ba domin kuwa tun zuwansa jiya tsaki kadai tayi masa wanda yanzu yake tunanin ma qila ba dashi take ba tunda gashi har ta nemi ya rakata guri sunje sub dawo suna hira idan da ta tsani talaka kamar yanda ya fada baya zaton ko kallo ya isheta tunda dai yasan Alhajin ya gaya musu inda ya sanshi, ya kuma kwatanta musu qauyensu to me ze saka tayi masa wasan ya aureta in har bata son talaka?
Suna nan Saminu nata bashi labaran gidan Alhaji ya dawo, Audu ya rakashi har bakin qofar falo kafin ya koma masaukinsu yayo Alwala saboda magriba da aka kira. Sanda suka zauna zaman cin abinci ya sanarwa da Alhajin gobe da safe zasu juya Kano, gaba daya mutanen gidan suka nuna rashin jin dadinsu. Alhaji yace
"Na dauka zakayi mana sati ko sama da haka? Ga tafiya da zanyi zuwa Rivers da ina cewa zamu je tare"
Audu yayi qasa da kai cikin ladabi yace
"Ai Alhaji saboda na baro abubuwa da yawa a can gidan kasan komai idan babu idon mutum ba lallai ayi yanda ya kamata ba"
"Hakane ga iyali kam an baro kodan saboda su yaci a Koma" Mama ta dora abinda ya qara dagulawa Binta lissafi kenan farko damuwar tafiyar da yace zeyi ga kuma zancen iyali da Mama tayi.
Miqewa tayi kamar jiya ta bar gurin, Alhaji ya kira sunanta ta tsaya
"Lafiya Mamana baki gama cin abincinki ba zaki tashi?" Ya fada cike da kulawa, ta kwararrabe fuska tace
"Dady kaina ne naji ya fara ciwo"
"Ke kanki baya tashi ciwo se ana maganar Audu kenan" Mama ta fada tana hararar ta, ta juya ido tana kallon Audun tace
"To ni ina ruwana dashi kawai kaina ne yake ciwo bari naje nasha magani" daga haka ta shige ciki Mama tace
"Kyaji da gulmarki dai"
Alhaji yayi murmushi yace
"Aa fa karki saka mun Mamana a gaba" ya juya kan Audu dake juya cikalo a kan farantin dayaci abinci yau tuwo akayi ya kuma san saboda su ne yaji naman kaji da man shanu yace
"Da zaka daure kayi satin da akwai dalilin da ya saka nake so ka zauna"
Audu yayi jumm, baya so yayi masa musu dan haka kawai yace
"Toh, Allah ya kaimu amma inaga zan tura Baballiya ya koma shi saboda Kasuwa"
"Hakan yayi kyau" Alhaji ya fada. Tun a daren ya cewa Baballiya ya shiya dan Asubanci zasuyi Tunde ne ze mayar dashi kamar yanda Alhaji yace. Baballiyan ya ringa qunquni ya baqin rai amma da yake babu damar wargi dole ya hada yan komatsansa yana tunanin yanda ze koma yaci gaba da kwana akan Katifarsu ta gida me kama da Dakin din sumunti idan aka hadata data gidan yan gayu. Washe gari kuwa qarfe shida suka dauki hanya Bayan Alhaji da Mama sun hada masa sha tara ta arziqi da tsarabar da ze kaiwa su Bara'atu.
Audu ya rubuta wasiqa ya bashi ya kai mata a ciki ya sanar da ita duk abinda ya faru da dalilin zamansa zuwa ranar da ze dawo. Shi yayiwa Tunde cikakken kwatancen zuwa inda yasan idan Baballiya ya gani ze iya kaisu gida kafin suka dauki hanya suna musu fatan sauka lafiya. A ranar tare suka fita da Alhaji gurin da yake aiki wato Matatar Mai ta Kaduna. Audu na zaune a office dinsa tsayin lokaci bayan Alhaji ya fita ya barshi sannan ya dawo ya same shi.
"Na barka kai kadai ko? Meeting muka yi" Alhaji ya fada yana zama akan kujera, Audu yace "babu komai ina ta kallon Talabijin ma bansan lokacin ya ja haka ba".
"Dalilin da ya saka na taho dakai saboda kaga gurin da nake aiki, ko ban fada maka ba kasan nan din ina ne, matatar Mai ce, itace Ma'aikata mafi girma da daraja da kuma kawo kudin shiga a Arewa baki tana kuma takewa ta Legas data fatakwat baya. Na so ace kayi karatu me zurfi ko da Diploma ce saboda a nan gurin takardar sakandire sedai a daukeka a matsayin lebura bawai babban Ma'aikaci amma dukda hakan bata baci ba, na dade ina so na bude gidan Mai a Kano, sedai rashin Ido ya saka ni daqile qudurin nawa amma yanzu dana hadu dakai ina ganin lokacin ne yayi ina so ka gwada harkar mai domin ana samun Alkhairi sosai da sosai a ciki"
Audu yaji abin ya masa girma, domin a sanda yake bunburutu yayi bincike cikin sabgar yaso ya shigeta da gaske amma irin maqudan da aka karanto masa wai a talauce ze zuba a matsayin jari bashi dasu baya kuma tsammanin nan da shekaru goma ze mallake su sedai kuma lamarin ubangiji babu yanda baya zuwa se gashi ya samu tayin shiga harkar daga sama duk se ya rasa abinda zecewa Alhajin. Sunyi maganganu sosai, Alhajin yace masa idan ya koma Kano ya nemi guri da yake ganin zasu fara bude gidan Man ze hadashi da wakilai da zasuje tare da zarar guri yayi za'a fara aikin ba tateda bata lokaci ba domin tuntuni ya samu lasisin yin hakan Allah ne bai nufa ba se yanzu. Suka yita hira Alhajin yana fada masa yanda harkar take, sirrikan kasuwar da yanda ake tafi da ita dashi kansa abubuwan daya mallaka a ciki da wadanda yake shirin mallakar. Se yamma lis suka koma gida cike yake da murna yana hasaso yanda zata fashe nan da wani dan lokaci Audu ze zama manajan gidan Mai.
Ya ringa hasaso nan da shekaru kadan shima ze mallaki nasa idan Allah ya yarda.
Seda yayi sati cif kafin ya shiryi tafiya Kano tareda wakilan da Alhaji ya hadashi zasuje duba gurin da za'a assasa gidan Mai, a cikin satin kullum se sun fita da Alhajin haka yayi ta sakashi cike ciken takaddu, ana gobe zasu tafin kusan raba dare sukayi a tsakar gida da Binta suna hira wadda ke cike da Alhinin rabuwa da juna. Wata irin shaquwa ce ta qullu tsakaninsu, shidai Audu a bangarensa babu wani abu face ya dauki Bintan a matsayin qanwa kuma diyar mutum mai daraja a gurinsa da yake shirin canza rayuwarsa. Sedai ita ba haka bane a bangarenta, duk yanda taso hana kanta ta kasa tilas ta amince da tana qaunar Audun kuma duk sanda ta tuna haka se taji kamar ta rufe kanta da duka tsabar takaici.
Bata san sanda haka ta faru ba, yaushe zuciyarta ta yanke mata wannan danyan hukunci dukbata sani ba kawai dai ta tsinci kanta dumu dumu a soyayyar Audu Bechi kuna ta gagara boye hakan ta nuna masa sedai sam yaqi nuna mata ya gane abinda ta ke ciki ita kuma ba zata iya karya bille ta zubda girmanta ta fada masa da fatar baki ba domin ta wuce da Ajin haka, zuciyace me aiki gaba gadi ta janyo mata ba tareda tayi shawara da ita ba koda yake bataga laifinta ba, Audun Namiji ne ingarma irin zabinta. Dukda cewar be yi wayewar Azo a gani bata tabbatar zuwa gaba za'ayi Namijin gaske musamman yanzu da ta fara hango haske a gobensa saboda yanda Dady yake tsamo tsamo cikin Al'amarinsa, a kuna dan zaman da sukayi yanda yake bata labarin Harkokin da yake tabawa ta tabbatar Gobensa zatayi kyau. A tsarinta kuma tana so ta auri Namijin da zasu ginu tare suyi Arziqi tare ta yanda babu wanda ze bigi qirji yayi mata kankanba akan sa.
Haka ya tattaro ya dawo Kano, beko huta ba suka shiga neman lokashon inda za'a kafa gidan Man. A cikin kwanaki biyu aka samu, filin a bakin titi yake sukayi dace na Magada ne ana kan gabar yin rabo daman neman me siya sukeyi babu bata lokaci akayi ciniki suka karbi fili a bisa qololuwar darajarsa. Abinda ya qara bawa Audu mamaki hatta da Filin da sunansa aka yi takarda, be manta ba gidan man kansa Alhaji ya tambayeshi sunan da yake so ayi masa register dashi yace masa meze hana ya saka sunansa Zakariyya Paki amma Alhajin yace masa Aa, shiya bawa zabi daga qarshe BECHI ENERGIES akayiwa gidan man suna sannan ga fili an siya da sunan Audu.
Cikin qasa da watanni biyar aka bude gidan Man wanda ya kasance na farko a Kano mallakin mutum ba kamfani ba, dangi yan uwa da Abokai sunyi masa murna. Yan Bechi duk sunzo bude gidan Man dukda yana gayawa kowa bana sa bane na ubangidansa ne, ya kuma debi ma'aikata harda Yayan yayyensa silar barowasu Bechi kenan suma. A taqin lokacin Audu yaje Kaduna babu adadi, soyayya ce ta qullu tsakaninsa da Binta wadda besan sanda shima ya afkawa soyayyar tata ba. Abinda ze iya cewa kawai Bintan tayi daidai da tsarinsa, kuma ita ta bashi fuska shiyasa beyi shayi ko jin dar na amincewa da buqatarta ba dukda ya kanga kamar abin bame yuwuwa bane amma tabbas yana son Binta kuma in har ya samu dama ze aureta.
Page 11
Kamar da wasa magana ta qullu tsakaninn Binta da Audu, da kanta ta sanarwa da Mahaifinta wanda yayi matuqar murna da Al'amarin saboda shidai Allah ya saka masa qaunar Audub a ransa tamkar dan cikinsa haka yaje jinsa. Mahaifiyar ta dai saisa saisa, bata nuna qinta ga Al'amarin ba haka kuma batayi murna ba saboda a ganinta Audun barene. Haduwar hanya bata isa tasa Alhaji ya daukake shi haka bayan aminta dashi akan dukiyarsa kuma yace zero dauki Yarsa mafi soyuwa ya aura masa ba. Yan uwanta kuwa kaf da sukaji take suka nuna qin Amincewarsu.
"Allah ya sauwaqe, ke wace kalar wawiyace Binta? Kodai irin Asirin da yayiwa Dady duk ya rikice a kansa kema yayi miki? Daman qauyawan nan da surkulle suke wlh ban yarda da wannan Al'amarin ba Asiri yayi muku daga ke har Dadyn kuma dole mu tashi tsaye mu karya" Salima da take takewa Binta baya a fannin tsiwa ta fada aiko Bintan ta maka mata harara tace
"Idan ma Asirin ya mun meye naki a ciki? Ke zaki aure shi ko kuma ke zaki zauna dashi?
Da kika Auro Inyamuri waya ce miki qala seni da zan auri Bahaushe dan uwana. Ni bana fada muku dan ku yarda ko karku yarda bane kawai dai a matsayinku na yan uwana ya kamata ku sani Aure da Audu kuma babu fashi in sha Allahu" ta fada tana murguda baki.
Haka aka ringa dauki babu dadi, sun nuna qin Amincewarsu qarara Jalal ne kadai da yake Namiji beqi abun ba dukda be nuna dokinsa a fili ba tamkar dai mahaifiyarsu amma da yake Bintan ta kafe kuma Alhaji yayi na'am haka aka qulla magana.
A bangaren Audu kuwa sanda ya sanarwa da Yakubu da sukaje hutu maganar tashin farko shima ya nuna be yarda ba.
"Haba Audu, daga ka fara samun duniya sakayyar da zaka farayiwa Bara'atu da ita kenan ta qarin aure? Karka manta sadaukarwar da yarinyar nan tayi maka. Kwata kwata ma shekarun mu nawa da auran matan namu nawa suke? A bariki fa sa'anninsu har yanzu suna gaban iyayensu ana musu kallon qananan yara kai ko me yasa ba zaka barta taci arziqin da kuka tara tare cikin kwanciyar hankali ba?" Yakubu ya fada.
Audu ya karkace, shi fa a yanzu Jin Binta yake kamar daga sama aka yo masa wahayinta tsabar so. Ba wai ya dena son Bara'atu bane Aa, yanda Bintan ta iya magana da tattala Namiji idan yaje Kaduna har ya dawo Kano yayi satittika kafin ya sake komawa cike yake da bege da shauqin kalaman data ciko shi dasu. Ga tarin wasiqu datake rubuta masa masu dauke da kalamai masu gigita tunani, haka ze ringa dauka kullum yana karantawa idan sun qara ya ringa maimaitawa har se yaje ta sake hadoshi da wasu ya dawo yaci gaba da tisa karatun kalaman soyayya. Irin wadannan abubuwan yasa ya fara ganin baiken Bara'atu wadda bata san komai ba bata kuma iya komai ba se abinda ya koya mata ko ya nuna mata.
Ya kasa gane banbancinta da Binta wadda ta kereta a shekaru, sannan ta bangaren wayewarsu babu hadi Binta haihuwar cikin Turawa girman Kaduna zagaye take da gogaggun yan Boko yan uwa da qawaye baya ga haka ita din tana cikin mutane da Allah yayi masu dan banzan wayo da iya magana. Duk dakiyar mutum tana iya canza masa akala a cikin ruwan sanyi yayi abinda take so ba tareda ya ankare ba. Tana da wayo kamar me, ga kissa kamar rainon Tsofaffi da wadannan halayen ta sake kanainaye shi yanda take nuna masa yafi kowa a duniya ya kai matsayin da shi da kansa yasan qaryane be kai dinba kambama shi kawai take amma da yake shi mutum nr me Izza da kuma son a girmamashi a yabe shi hawa yake ya zauna kan duk abinda ta fada baya ko tunanin Izgilanci take masa domin ta fishi ta kowacce fuska amma take nuna masa ita din banza ce akan sa.
Gyara zama yayi ya kalli Yakubu da yayi shiru cikin mamakin abinda Audun yazo dashi yace
"To amma da farko akwai haramci a cikin abinda nazo dashine? Naga qarin auran nan halal ne. Dafa ba'a qara aure da ba'a haife mu ba domin mahaifiyarmu a ta biyu taje gidan Baban mu sannan ita Bintar nan ka san komai game da Alkhairin da mahaifinta yayi mun. Kana kallon laimar Arziqin daya lulluba mun a cikin watanni kadan na damu abinda na shekara goma ina fafutuka ban samu ba meye aibu idan na karbi tukuicin auran yarsa wanda ita tayi mun tayin haka da kanta baka tunin zan zama butulu mara godiyar Allah idan nace zan qita?
Tunda har su basu dubi matsayinsu da nawa ba suka amince zasu bani auran yarsu aikuwa ni bai kamata nace Aa ba kaima kuma be kamata kaqi abin ba domin Alkhairin da yake tattare dashi ba iyakar kaina ze tsaya ba gaba daya ya shafe mu. Kuma ni Bara'atu bani da matsala da ita, mun samu fahintar juna domin ban boye mata komai ba tun farkon maganar kuma ta amince dan haka yanzu abinda ya rage kawai zamuje can Bechi mu sanar dasu Yaya Baba idan yaso se a saka rana da zakuje ku nema mun auran. Ni yanzun duk bama wannan ya dameni ba, tunanin gurin da zan ajiyeta nakeyi".
Duk yanda Yakubu yaso fahimtar da Audu abu yaci tura dole ya haqura tunda dai kamar yanda Audun ya fada abinda yake shirin yi ba haramun bane sedai shima ba qarin auransa ne baya so ba, Audu qaninsa ne kuma Aboki koma yace Amini, duk wani sirrin junansu sun sani yasan da cewar Audu baze iya zama da mace daya ba kuma irin Bara'atu saboda tayi masa kadan sannan a tsari na halitta har yanzu bata kai cikar da yake fata ba amma yaso ace idan ma auran zeyi ya nemo daidai dashi ko a can gida ko a nan cikin Kanon amma dai ya samu yarinya yar Talakawa irinsa da zasu yi zaman lafiya ba irin wannan aure daya gingimo ba. Shi gaba daya ma gani yake abin kamar da wani qulli ciki, tayaya mutum daga haduwar hanya ze ringa masa irin wannan hidima haka sannan har ya dauki ya ya bashi Aure bayan matsayinsa be wuci na me gadi ko share sharen gidansa ba.
Sanda yayiwa Balaraba zancen yanda ta firgice seka rantse ita aka ce za'a wa kishiyar, ta ringa masifa tana Bala'i wa Bara'atu daga qarshe dai dole ta barta tunda ita da za'ayiwa kishiyar ko a jikinta ina dalilintana daukar dumi?
A can Bechi ma haka Bilki ta ringa fada akan me Audu ze qara aure me Bara'atu tayi masa, amma tunda dai duk basu za'ayiwa kishiyar ba kuma me zama da ita tace taji ta gani dole suka haqura suka zubawa sarautar Allah ido.
Anje an tambayowa Audu Aure, Yaya Baba, Hashimu da Aminu se Yakubu sukaje Kaduna bisa jagorancin Audu. Tarba ta mutunchi akayi musu, basu taso ba seda aka tsaida ranar Aure watanni uku masu zuwa suka dawo kowa na jinjina gidan da Audu yaje neman auran. Hashimu ya ringa yawo a gari yana cewa Auran kwadayi zeyi tunda gashi tun be aureta ba ubanta ya gina gidan mai ya bashi gaba kuma ba'asan me zeyi masa ba. Takanas ya samu Baban Bara'atu akan seya tursasawa Audu ya sakar masa yarsa domin qarshe boyi boyi zata zama a gidan daya auro wannan yar Attajiran Azabatar masa da Ya kawai zasuyi hankalin Inna Hajara ya tashi sanda ta samu labarin irin Amaryar da ake shirin yiwo wa yarta, takanas ta tashi qanwar Bara'atun ta turata tace idan ta samu sarari tazo Bechi tana son magana da ita.
Haka kuwa akayi ta gayawa Audu yayi mata shiri kamar yanda ya saba duk sanda zataje gida ta tafi, Innarta ta ringa nuna mata qalubalen dake cikin auran da yake shirin yi amma se tayi murmushi tace
"Duk hasashe kukeyi Inna kuma Audu yana qaunata na tabbata babu wata mace da ze aura da zata zarceni a zuciyarsa sannan ita kanta da kuke magana tana da kirki. Tun yanzu bakiga yanda duk sanda yaje seta hadoshi da abin Arziqi ya kawowa yara ba dani kaina kuma ya fada mun sam bata da matsala dan haka kuyi mana Addu'a kawai Allah ya bamu zama lafiya" da haka ta kashe bakin Innarta da duk wani dake shirin saka mata rudu a zuciya.
Ba kuma wai bata damu ko kuma bata kishin Auran da Audun yake shirin yi ba, ta damu kwarai dan tana son mijinta, irin rawar qafar da yakeyi akan Amaryar tasa na daga mata hankali amma ta yarda da cewar Damuwarta ba zata saka a fasa abinda Allah ya hukunta ba sannan meye ribar ta tayar da hankali ta rasa mutunchinta da qimarta a gurinsa kuma daga qarshe yayi auran su zauna? Shiyasa ta maida komai ga Allah shi take roqo kullum dare da rana akan duk fitinar dake cikin aura Allah ya kade musu ita ya sanya zaman lafiya da fahimta a tsakaninsu kuma wannan haqurin da tayi da ake mata kallon wawiya ko yarinta ce take damunta ya saka Audun ya mayar da ita Abokiyar shawara akan duk wani abu da zeyi ko yake shirin yi. Daidai da zancen muhalli ita ya tuntuba akan yanda take ganin za'ayi.
"Gurin saukar baqin gidansu kadai duk unguwar nan babu gida me kyau da tsaruwarsa, gaba daya abinda ya dameni kenan yanzu inda zan ajiyeta saboda kinga ko a shari'ance be kamata ace ka dauko Mace daga cikin daula ka muzguna mata a bangaren muhalli ku sauran buqatu ba" Audu dake faman lissafin kayan lefe ya fada, Bara'atu ta hadiye yawu tace
"Gaskiya idan hakane kuwa ya kamata ace kayi mata tanadi na musamman domin nasan ba zata iya zama a cikin gidan nan ba"
"A ina ma zan ajiyeta toh?"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 32