kwazara mata kira nan ma shiru bata amsa ba.
"Wai ina wannan yarinyar ta tafi?" Ya jefawa Binta tambayar ta watsa hannu tace
"Yo ka bani ajiyarta ne da zan san inda zataje?"
"Shikenan sena dawo" ya fada daga nan ya fice yana mamakin ina zataje dan sam be kawo gida ta tafi ba tunda ai bata san abinda takardar daya bata ta qunsa ba, haka ya dawo gida da yaqinin ze tarar da ita amma wayam bata nan, ya diririce, ta tabbata gidansu ta tafi kenan amma me yasa zata tafi to? Ya jefawa kansa tambayar rainin wayo.
Bayan Isha ya shirya tsaf ya cewa Binta zeje wata unguwa, gidansu Zubaidan ya tafi zuciyarsa ta ringa tuhumarsa me ze kaishi gidan amma hakan nan ya zungura kai yaje. Malam Hassan ya rasa ina ze sakashi saboda murna bayan sun gaisa ya tambayeshi Iyali yace
"Dazun Babarsu take cewa gobe In Allah ya kaimu zata leqa ta ganota kuwa jiki yayi nauyi har tana cewa ko zata dakkota tazo gida tunda haka akeyi a Al'ada haihuwar fari"
Cikinsa ya bada wani sauti quuuu, bata zo nan ba kenan? To ina yarinyar nan ta tafi kardai fa ta hefashi a masifa in duniya ta sake shiga ai da seta bari seta zo gidansu ta gayawa Mahaifinta komai sannan seta tafi amma yanzun ta ina ze fara yi masa bayanin shima nemanta yazo?
"Aa bafa abin dole bane idan baka so ta dawo gidan se tayi zamanta dan naga fuskarka ta canza daman matane da Al'ada kasansu basa wasa da ita" Mala Hassan ya katse masa tunani a zatonsa zancen dawowarta gida ne ya canza fuskar Audun besan Al'amarin yafi gaban haka ba. Tilas ya masa sallama a gurguje ya taho bayan ya ajiye masa na goro.
A gida ma rkicewa Binta yayi da tambayar ina zasu nemo Zubaida ina ta tafi?
"Ya wuce ta koma inda ta fito ne, wai kai meye ma naka na damuwa ina ka saketa duk ma inda zataje taje mana kana da matsala da ita ne?" Ta fada cikin jin haushin yanda yake ta safa da marwa cikin damuwa. Washe gari da farar safiya ya tafi gidan Yakubu ya ringa buga musu qofa kamar za'a tashi duniya Yakubun ya fito yana ganin shine ya shiga surfa masa fada shima yana tambayar ba'asin wannan bugu kamar ya masa sata. Daya masa bayanin abinda ya kawoshi qiris ya rage Yakubun yayi dariya amma ya kanne a ransa yayiwa Allah tasbihi wato tun ba'aje ko ina ba aiko ze gane kuskurensa domin baze fada masa tana gidan ba.
"Ni meye nawa a ciki yanzu Audu? Kashedi nawa kamun akan na fita daga sabgar gidanka? Ashe da nace kayi haquri ka bar maganar nan baka daddara ba to ka saketa ta bar maka gida meye kuma abin damuwa a ciki ko daman ka dauka zata zauna ne kuci gaba da ci mata mutunchi kuna aibatata kaida matarka?" Yakubun ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki yace
"Ni bance ta zauna ba amma data tashi tafiya ai seta tafi gidansu ko amma yanU naje jiya bata can yanzu me take so na gayawa mahaifinta idan suka zo ganinta basu sameta ba?"
"Se ka gaya musu ka saketa ita kuma tana tsoron ta tayarwa da mahaifinta hankali idan ta koma gida shine ta sake shiga duniya, ni dana san wannan shirmen ne ya kawoka wlh bazan bude qofata ba haka nan ina bacci na me dadi ka daga mun hankali da bugu. Ka tafi ka nemo yarinyar mutane dai kafin iyayenta su farga, kaga daman ba'a jima nayi wani case Mata ta bata Iyayenta sukace Mijin ne ya siyar da ita yayi kudin jini AAllah ya tsareka kaima kar suce kayi kudin jinin da ita daman an fiyi da masu ciki" yana gama fada masa hakan ya maida qofarsa ya rufe ya bar Audu cikin tashin hankalin daya ninka na farko akan maganar da yayi ta karshe.
Daman a Bechi ana rade radin qungiyar Asiri ya shiga yayi kudi farat daya da yawa sun qaryata cewar wai sirikinsa kuma ubangidansa ne ya buda masa yake samun kudi haka? Su kance shi din har nawa ya mallaka da yake bawa Audun kudi haka? Zancen da akeyi yanzu rabi da kwatan Gonaki da filayen da suke a Bechi mallakinsa ne saboda duk wanda ya daga fili ko gona ze siyar da an tallata masa ze siya a farashi me daraja kuma shiyasa wasu ma haka nan suke siyar masa suje wani gurin su sake siya ragowar kudinsu susha shagali yanzu idan wannan magana taje Bechi ace matarsa ta bata da tsohon ciki la shakka cewa zasuyi yayi tsafi da ita kawai.
Page 23
Sati guda ya shude Audu na bulayin neman Zubaida sedai sama ko qasa babu ita babu kuma wanda ya ganta bare asan labarin inda tayi. Har Zariya sukaje da Bashir gidan daya dakkota suka tarar an tashi gidan ma gaba daya titi ya biyo ta kan hanyar haka suka juyo Kano babban abinda ya qara daga masa hankali ya bazama nemanta zuwan da Baba Zayya tayi akan taje duba Zubaidan Allah ya taimake shi yana gida ranar, daya rasa abin fada mata dole ya rangada mata qaryar Zubaidan tana Bechi, kuma daman yaso yaje ya sanar dasu tana can har se bayan ta haihu zata dawo Kano to Allah be nufa ba. Dake akwai yarda da Amana sam Baba Zayya bata kawo komai a ranta ba tunda ana hakan mace ta tafi garin su Miji haihuwa dan haka tayi musu sallama ta koma gida ta shaidawa Malam Hassan yanda akayi.
Wannan dalili ya qara zaburar da Audu ga neman Zubaidan, nadama mara amfani ta dirar masa biya hukuncin daya yanke ba tareda zurfin tunani ba. Haka ya ringa raba kudi wa malamai akan ayi masa Addu'a Allah ya bayyana Zubaidan ya kuma kareta a duk inda take. Cikin wannan yanayi Alhazai suka fara tashi, Binta taje gida tayi sallama da danginta ta dawo tana ta shirin tafiya sauke farali bacci ragagge takeyi saboda jiran ace su fito. Ita sam ta manta ma da wata Zubaida balle batun ba'a ganta ba, yanda Audun be cika nutsuwa ba a lokacin yasa ta tsahirta masa, ita kadai take ta shirinta tunda dai ya sallameta ya bata Guzuri me auki ita kam ya gama da ita se jiran ranar tashi kawai takeyi.
Acan gidan Yakubu kuwa hankali kwance Zubaida ke zamanta, tsakanin Balaraba da Yakubun ba zata tantance wanda yafi tattalinta ba. Duk wani abu da zata buqata suna mata haka nan basu barinta ta zauna shiru balle ta fada tunani ko wata damuwa a koda yaushe cikin hikima sukanyi mata nasiha akan rayuwa da qalubalen da yake tattare da ita. A dan taqin zaman ta fahimci banbance banbance masu tarin yawa da suke cikin rayuwar Haske data duhu ma'ana rayuwar da akeyinta cikin sani da wayewa ta Addini da kuma rayuwar Bidin bidima irin wadda tayi a baya ta koma dora yinta a gidan Audu.
Yakubun jajirtaccen Namiji ne wanda yake tsaye akan lamuransa dana iyalinsa. Ga daishi be tara dukiya tamkar dan uwansa ba amma rayuwar gidansa ta zamo abar sha'awa wadda duk me hankali idan aka bashi zabin kudi ko nutsuwa irin ta gidan Yakubun tabbas baze tsallaketa ba.
A kullum da Asuba seya dorawa matarsa da Yayansa karatu haka bayan sallar Isha'i idan sun zauna a maimakon hirarrakin banza na duniya sukan yi tasu hirar ne akan karatuttukan da sukayi. Ya tambayesu su tambayeshi, hatta da Qaramin dansu Tijjani me shekaru uku a sannan Alqur'ani ya fara zama a bakinsa, haka qananan Hadisai da ake dorawa Yayinsa yana tsinta har idan Yakubun yana tambayarsu sukayi kuskure Tijjanin da suke kira da Alhaji ze gyara musu ga wayewa ta boko turanci yafi hausa Nuna a bakinsu kodan inda suke zaune yaren da suka fi amfani dashi kenan? wannan abin ya matuqar birgeta ya kuma zaburar da ita kan cewar itama bata makara ba tana da damar da zata nemi ilimi tana kuma burin abinda zata haifa ya tashi cikin irin wannan rayuwar ta ilimi ba irin ta gidan ubansa ba.
Zata iya bada shaidar Audun yana salloli na farilla kuma yana qoqarin yinsu akan lokaci kuma cikin jam'i, a zamansu daya tasamma shekara a watan Azumi kadai zata bada shaidar yana zuwa sallar Tarawi da kuma Qiyamullaili tun bayan daya shude kuma a ranakun girkinta dai bata sake ganin yayi ba bata sani ba ko idan yana dakin Binta. Dama shi bame jurar Ibadar Azumi bane domin Ramadanan ma da qyar yake kaishi, bayan Alqur'ani bata tsammaci ya karanta wani littafi ba bata taba ganinsa dashi ba haka ko a magana ba zatace ga inda ya kawo misali daga cikin Hadisi ko wani littafi na Addini ba. Ba zata manta ba akwai sanda ta taba shawartarsa shiga karatun Asuba da akeyi a masallacin dake cikin layinsu wani baqon babban Malami ne yazo yake bada karatun Fiqhu da Hadisi se Tauhidi take yace mata ai ya gama karatu, seda ya shekara biyar yana qolanta to wane karatu ya rage masa da beyi ba kuma?
Da tace ita zata ringa zuwa gurin matar Malamin da take karantar da Mata a cikin gida harya yarda bata san ya akayi ba ya dawo yace babu maganar ta tambayi dalili kuma yace babu dole ta haqura badan taso ba domin Allah ya sani tana sha'awar ta nemi ilimi shiyasa yanzun data samu wannan damar tayi amfani da ita.
Dada take ja tana biya mata karatun, dayake tasan baqi dan haka karatimu da takardar Alqur'ni be bata wahala sosai ba dukda tafi gane rubutun warshu amma da yake ta saka kanta se gashi tana ganewar in ta biya mata kuma ta ringa nanatawa kenan har seta haddace. Balaraba ce ta sameta akan ta ringa fitowa suna daukar karatun tare bayan da Dada ta sanar mata tana yiwa Inna Zubaidan qarin karatu, daga nan itama ta zama yar Aji ta kuma maida hankali sosai akan abinda ake koya mata. Irin nutsuwar da take tsintar kanta a ciki ta qara tabbatar mata da cewar tabbas akwai banbanci me tarin girma tsakanin rayuwar da akeyinta cikin sani da kuma ta jahilci.
Satinta uku a gidan wata safiya ta tashi da naquda, kafin nan sunje Asibiti har sau biyu Yakubu da kansa ya kaisu tareda Balaraba an dubata an kuma tabbatar da lafiyarta data abinda yake cikinta suka basu kwana goma daya zagayo suka koma kwanaki biyu kenan da zuwan nasu da safiyar ranar Laraba ta tashi da naquda nan da nan suka wuce Asibiti da ita, daman Yakubu yana nan ya jinkirta komawarsa Ikko saboda yana taraddadin ya zasuyi idan haihuwr tazo mata cikin dare gida babu Namiji daga ita se Balaraban dalilin daya saka ya daga tafiyarsa kenan saboda a Asibiti zuwansu na farko sun bashi tabbacin ba zata qara sati biyu nan gaba bata haihu ba gashi kuwa kwanaki goma sha biyu kenan da wanacn zuwan haihuwar tazo.
Cikin taimakon Allah bata dauki lokaci mai tsaho ba ta sauka, ta haifo wasu runtuma runtuman tagwaye wanda ko a Da guda daya aka haifi wannan tabbas se an jinjinawa wadda ta santaloshi se gashi har biyu ubangiji ya bata a sauqaqe cikin Aminci. Lokacin da aka nunawa Yakubu yaran kasa cewa komai yayi se tasbihi daya ringayi a zuciyarsa. Duk wanda yasan Ahalin gidansu baya buqatar a fada masa yaran tsatsonsu ne ze iya cewa ma ba'a taba haifar Jarirai masu kama da Mahaifinsu Malam Tijjani Kwabo da kwabo irin wadannan ba har hasken fatarsa basu bari ba abinda ya banbantasu da Audu kenan saboda shi yana da duhu kadan.
Ya rasa ta ina ze fara ma, Balaraba nata murna ta kasa tsayuwa guri daya shi kuwa tunanin waze fara shaidawa zancen haihuwar yake tayi. Gadai Arziqi Allah ya basu wadannan ne tagwaye na farkoba zuri'ar gidansu amma haihuwar su tazo cikin rudani. Seda ya tabbatar babu abinda ake da buqata a Asibitin kafin yacewa Balaraba zeje ya dawo.
Can kamfanin da Audu yake ginawa inda kuma nan su Musbahu suke zama ya nufa. Yaci sa'ar tarar da Musbahun be tafi gidan Mai ba, bayan sun gaisa yace yazo ya rakashi gidansu Zubaida Amaryar Audu babu musu ya hau mota suka tafi a ransa yana mamakin meyake faruwane domin a kwanakin nan gaba daya sun lura da Baba Audu baya cikin hayyacinsa dukda be fada musu komai da yake damunsa ba amma ko gidan Mai seya kwana biyu be fito ba aikin Kamfanin ma an dakatar dayi kamar yanda ya fada yana cikin wani dan uzuri ne.
Da suka isa gidan a Mota ya bar Musbahu ya qara qofar daya nuna masa a mazaunin ta gidan Malam Hassan. Yayi sallama cikin sa'a Malam din ya fito ya amsa a shirye yake da alama wani gurin zashi, be taba ganin Yakubu ba amma jini da kamannin fuska yasa ya gane dan uwan Audu ne dan haka yayi masa iso cikin gida bayan ya saka Baba Zayya tayi musu shimfida ta kawo masa ruwa a mutunce suka gaisa suna tambayarsa iyali.
Cikin nutsuwa da kuma sanin makamar aiki irin nasa ya warwarewa Malam Hassan duk abinda ake ciki be boye masa komai ba hatta da sakin da Audun yayiwa Zubaida da zamanta a gidansa zuwa yanzun data haihu be rage komai a ciki ba. Malam Hassan yayi shiru cikin tsantsar jimami kafin yace
"Tabbas nayi zargin wani abu ya faru saboda irin zaryar da dan uwanka ya ringayi a gidan nan kuma alamu na rashin gaskiya sun bayyana tattare dashi sedai na kyautata masa zato na cewar koma menene nasan baze cutar mun da Zubaida ba na saka a raina dai wata matsala ce qila da yake jin nauyin sanar dani. Hatta zuwan da zayya tayi ni na turata domin taje ta ga halin da suke ciki qila mu iya gano bakin zare sedai ya tabbatar mata da cewar ya tura Zubaidan can garinku, tabbas wannan maganar ta tayar mana da hankali hat shaidan yaso yayi wasa da zuciyata ya darsa mun zargin wani al'amari na daban amma na yaqe shi da qarfin addu'a ban kuma gusa ba kullum cikin yinta nakeyi ina roqon ubangiji da koma menene yake faruwa ya bayyana mana ya kuma sauqaqa mana.
Na godewa Allah da Jarabawar ta tsaya iyakar haka, na kuma gode maka da kayi mun wannan arziqin na riqe Zubaida a hannunka harta haihu ubangiji ya wanketa daga zargin da dan uwanka yakeyi mata na taje masa gida da Dan da ba nasa ba. Yanzu data haihu a hannunka ze iya tantance kamanceceniyar da take tsakaninsa da abinda aka samu kuma ya iya nutsuwa yayi lissafi na kwarai sabanin idan ana nan ta haihu tunda har ya rigada ya yarda da cewar Boka ko Malamin tsubbu na iya aikata komai la shakka yace itama kamannin dake tsakaninsa da abinda aka haifa qirqirarta akayi".
"Hakane Baba ina kuma qara baku haquri akan abinda ya faru In sha Allahu ma komai ze daidaita base har Zubaida ta dawo gida ba daga can gurina zata sake komawa dakinta da yardar Allah kuma abinda yasa nazo na sanar muku da abinda ake ciki saboda ku mahaifantane kuna da haqqi akanta be kamata kuma ace mun rufeku akan babban Al'amari irin wannan ba" Yakubu ya sake fada. Malam Hassan yayi murmushin daya fi kuka ciwo yace
"Kayya yaro dena wannan magana kuma ai zancen kome babu shi Aure ya qare sedai muyi fatan ubangiji ya musanyawa kowannensu da Mafi Alkhairi a gareshi. Kamar yanda rayuwar data faru a baya ta shude muka yarda da qaddara wannan ma mun dauka, rabon wadannan bayin Allah yayi sanadiyyar wannan Auran, tsakaninmu da Abdullahi kuma har abada babu abinda zamu ce masa sedai fatan Allah ya dubeshi ya saka masa da Alkhairi kwatankwacin wanda yayi mana. Maidomun da Zubaida gida da yayi ya isheni komai a duniya wlh kuma wannan al'amari daya faru baze goge tarin Alkhairinsa na baya a idona ba, wata Jarabaqar ce daga ubangiji kuma idan munyi haquri zamu cinyeta".
Yakubu be ja maganar da nisa ba yayi masa sallama bayan ya roqi Baba Zayya data shirya su tafi Asibiti tare ya kuma sake roqar Malam din da maganar ta zama sirri tsakaninsu. A hanya Baba Zayya ta samu bakin zazzage masa buhun bala'in da bata iyayi gaban Malam Hassan ba kai kace shine Audun, shidai be tanka mata ba domin sunada duk wata dama ta suyi fada dan an bata musu.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
AUDU
Shirye shirye suke tayi saboda a daren ranar suke saka ran tashin su Binta. Gaba baya ta hargitse gidan ta hada faggon jakunkuna tamkar me zuwa yawon bude ido ba Ibadah ba. Addaba masa tayi akan seya qara mata kudi,
"Kaga fa a can nake so nayi siyayyar kayan haihuwar nan, dan abinda ka bani me naci a ciki me nayo tsaraba sannan duk ciki kake so nayi siyayyar kayan jaririn?" Binta ta fada tana matse fuska sanda yake jaddada mata sisi baze qara mata ba.
Kudade masu kauri ta karba a hannunsa, banda guzurinta ga wanda Babanta ya bata amma a haka take hanqoron se ta sake waftar wasu a hannunsa ya rasa bala'in son kudi irin na Binta kuma ba abin Mamaki bane taje ta dawo daga ita se jakar hannunta dan ya dade da gane Binta bata iya tsinanawa kanta ko waninta da komai a zamansu daga kan sutura zuwa wani abin amfani na gida sabo sedai idan shi ya siyo ko kuma aka mata daga gidansu amma a karan kanta batayi ya kan tuna Bara'atu zamansu duk Azumi zatayi yan kaye kaye ta fitar da tsoffin kayan amfaninta ta maida sababbi banda Bintan.
Data ishe shi da surutu shi kuma ya rantse sile baze qara mata ba se kawai ya shirya ya fita, Gidan Mai ya tafi, mamaki ya kamashi yanda yaransa suke ta yi masa barka da Arziqi Allah ya raya bayan sun gaisa haka ya shige ofishinsa ransa fal da mamakin barkar me ake masa.
Sallama Musbahu yayi ya bashi izinin shiga bakin nan nasa kamar ze taage saboda fara'a ya gaida Audun kana yace
"Yanzu naje na gano yan tagwaye, wlh Baba kamar kayi kaki ka ajiye, duk yaran gidan nan ni banga wanda ma yayi kama da kai kwabo da kwabo kamar su ba".
Kallon Musbahun ya ringayi kamar be fahimci abinda yake fadi ba, so yakeyi ya tambayeshi waya haihu amma kuma ya qiyin hakan a maimakon haka seya miqe yana cewa
"Muje na gano su"
Maganar tasa ta bawa Musbahu mamaki dukda daman yanda ya ganshi tamkar be san da zancen haihuwar ba ya bashi mamaki sannan ya sake shiga duhu akan lamarin, tabbas akwai abinda yake faruwa tun daga daukarsa da Baba Yakubu yayi sukaje can gidan Malam Hassan bayan nan sukaje Asibiti a can din yayi tsammanin tarar da Baba Audun ko matarsa amma yaga akasin haka Inna Balaraba ce kadai se Baba Zayya da suka tafi da ita tare.
Shidai bece komai ba har suka isa Asibitin wanda shi yake tuqi yana gaba Audu na biye dashi a baya har suka isa dakin da aka kwantar Zubaidan tana hutawa. Wani tsalle zuciyar Audu ta buga lokacin da idonsa yayi arba da jinjiri a hannun Baba Zayya tana jujjuyashi, idonsa fes akan yaron ya shiga cikin dakin sosai se ganin mutum sukayi sangangan akan su. Balaraba ta buga tsaki kamar zata tsinke harshenta kafin ta miqe tana cewa Baba Zayyan
"Bari na zagaya"
"Nima bari na biki nasha iska warin magani duk ya cika mun ciki" daga haka ta ajiye jaririn hannunta Musbahu yayi zuruf ya daukeshi suka fice suka barsu a dakin.
Idanu Zubaidan ta rufe tana qara gyarawa yaron data gama shayarwa kwanciya a jikinta, Audu na tsaye tamkar wanda aka sarewa guiwoyi ya kasa gaba ya kasa baya jinin jikinsa ya tsinke haka bugun zuciyarsa ya qaru kamar wanda yake kusa dashi ze iya sauraro. Musbahu ya ajiye yaron hannunsa bayan daya gaka jujjuyashi bakin nan yaqi rufuwa ya fita ganin kamar suna da buqatar sirri. Fitar Musbahun ta dan saukar masa da qwarin guiwa har ya qara taku biyu ya isa gaban gadon sosai yana kallonta tareda yaran da kunyarsu tayi masa lullubi.
Ko a rufa ido aka shafa fuskarsa aka shafa ta yaran an sana halitta dayace balle a kalle su ido biyu, bayan kamannin fuska qirar jiki da kammani na jini duk sun bayyana tattare dasu, ya kai hannu ze sauki wanda Musbahu ya ajiye a ba zata yaji ta daka masa tsawa tace
"Akul ka tabamun yara" ta fada har tana nuna shi da yatsa. Yanda tayi maganar cikin sauti me nuna bacin rai matuqa hakan kuma ya nuna a idanunta tilas ya janye hannunsa daga daukar yaron da ya bude ido yana kallonsa tamkar ya sanshi. A sanyaye kai a qasa tamkar ba Audu uban yan Izza ba ya matsa dab da ita cikin karyayyen sauti yace
"Kiyi haquri ki yafe mun, wlh sharrin shaidan ne".
"Babu wani shaidan face kai da Annamimiyar matarka, ni yanzu babu wani abu daya rage tsakanina dakai ubangiji ya gama mun komai daya wankeni daga zargin da kake neman laqabamun, ciki dai gashi na haifeshi watanni goma sha daya a gidanka cikin qudura ta ubangiji kuma ya bani Yaya masu kama da kai kaga duk iya sharrinku da kaida matarka baku isa ku barranta wadannan yayan da Ahalinku ba, fatana kar Allah yasa su gado mugun hali irin naka. Wlh nayi dana sanin Auranka Audu, da ace na san haka can cikin zuciyarka yake baqiqqirin da ban amince da kai ba.
Ka gwada mun hali me kyau, ka yaudareni da Kyakykyawar Dabi'a. Nayi tsammanin na samu Bangon da zan jingina, jigon da ze tallafi rayuwata ya gyarani ashe kai kayi shirin qarasa tarwatsa rayuwa tane. Rayuwata ta baya ta zama tariyi kai kuma ka niyyati shafamun baqin fentin daya fi na baya muni, shin bakayi tunanin halin da mahaifina ze shiga ba idan yaji wannan mummunan abun daka zargeni dashi?
Anya kai ko da zuciya a qirjinka Audu? Me yasa baka tunani da kwakwalwarka ka sakarwa zuciyarka Linzami?
To wlh ka farka tun kafin lokaci ya qure maka, wannan rayuwar da ka dauka ta rashin tunani babu inda zata kai ka illah Nadama da dana sani mara amfani.
Ita kuma matarka ka gaya mata tabi a sannu, ina tausayawa rayuwar da zatayi a gaba haqqi dabaibaye da ita. Se yanzu na fahimci yanda kuka taru kaka kassara rayuwar Bara'atu kuka laqa mata mata mugun qazafi to wlh haqqinta kadai ya isheku a duniya idan har baku nemi yafiyarta ba ina kuma fatan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 32