canza ra'ayi ta karbe girki ita ta gaya mata ainin dalili amma shi se tace masa saboda Bara'atun ta huta ne hidima tayi mata yawa ga yara ga girki gara Mairo ta ringayi gaba daya tubda dai biyanta akeyi kuma dama kullum se tazo ko ba rabar girkin Bintan bane ire iren abubuwan da suke qara dagula zamansu kenan, shi tunda kunnene kawai se abinda yaji ba ruwansa da bin ba'asin ya akayi cikin kissa zata tunzuro shi ya dauki fushi da ita yanzu kuma da taso qulla wani abun shine zatace ya bata kudin cefanen abincin suna dan ta tabbata ba Alkhairi ya saka Bintan yin hakan ba.
Mairo taje ta samu tace ta duba kayan, data tambayeta me za'a dafa toh tilas ta koma ta sake tambayo Bintan tace mata Shinlafa da tuwo kawai zasuyi sauran abubuwan ta bayar da aikatau wannan yasa ta dan samu nutsuwa qila abincin iya jama'ar Bechi za'a bawa shiyasa ta barshi a hannunta. Tun rana suka fara rage aiki, su Bilki da Aisha da matansu Aminu ne suka yo gaba sauran dangi se gobe suna haka suka tasata gaba da tsiya harta rasa inda zata tsoma ranta wai daga dawowa harta tsomare a qauyen ma tafi kyan gani ta bari tsoron kishiya yayi tasiri a ranta.
Har an idar da Isha suka karbi baquncin mutanen Ikko, Yakubu da iyalansa Bara'atu ta rasa ina zata tsoma ranta saboda murnar ganin Balaraba. Suka rungume juna cike da kewa, Balaraba tayi kyau ta qara zama wata babbar Mace fata se walwali takeyi ita kuwa Bara'atu abin se godiyar Allah kawai. Daga gefe Aisha dake kallonsu tace
"Wato kwanciyar hankali duniyace, ku kalli dai idan daula da jin dadi ne Yaya Bara'atu tafi Yaya Balaraba samunsu amma kalle su ki gani banbancin kamar sama da qasa kowacce da ka ganta base an gaya maka matsayin da take a cikin gidanta ba"
"Aisha kenan kedai da Allah yasa kike ke kadai a gun Mijinki kici gaba da gode masa domin ba zaki gane qalubalen me Kishiya ba se kina da ita duk abinda zaki fada ko ki bada shawara akai hasashe ne kawai tunda baki san ya ainihin matsalar take ba" Sauda Amaryar Aminu ta bata amsa.
Bara'atu kuwa a dakin Audu ta sauki Balaraba, ta fita ta kawo mata ruwa da abin tabawa tace
"Bari na dora muku abinci wannan bazata haka ace zakuzo ko Yaya Audu be sani ba"
"Wai injiwa? Audun da shi yaje ya dauko mu daga filin jirgi" Balaraba ta fada. Bara'atu ta gwale ido tace
"Filin jirgi? A jirgi kuka zo?"
Balaraba ta harareta tana dariya tace
"Ji yanda kika gigice kamar wnada nace miki da fiffike mukazo, jirgi muka hawo mana abin Allah in gaya miki yau se ga Balaraba a jirgi qiris ya rage na haihu saboda tsoro" suka kwashe da dariya gaba daya. Bara'atu ta sake cewa
"Amma shine be gaya mun zaku zo ba?"
"Ba zata yayi miki gashi ai kinfi yin murna da muka zo yanzun, ke ni ba wannan ba ya naganki gaka qashi da fata ko laulayi kikeyi?" Balaraba ta fada tana kallon Bara'atun, seta miqe kawai tana cewa
"Bari naje na dora abincin"
"Karki wahalar da kanki seda muka ci abinci muka taho tafiya a jirgi kamar wanda Aljanu suka ragewa hanya? Ni banma san minti nawa mukayi ba kedau Allah ya qara mana arziqi me amfani Allah kuma yasa badi mu lula muyi tafiya me nisa a Jirgin muje mu sauke farali" cewar Balaraba.
Dukda haka Bara'atu taqi zama tace to bari taje su gaisa da Yaya Yakubu daga haka ta tsere, bata so ta zauna tunda Balaraba ta fara zancen ta rame ko ciki ne da ita tasan yanzu magana zata sake dagulewa sedai tana fita Bilki ta shige ta samu Balaraban ko kyakykyawar gaisawa basuyi ba dan tana sallah suka shigo yanzun taje ta gaida Yakubun kuma jira taje Audu ya matsa ra kwashe duk abinda ya faru da wanda yake faruwa ta gaya masa amma bari ta fara da Balaraban.
Tas ta labarta mata komai daya faru basa nan,
"Yanda kika san sallamammiya Bara'atu, na fada mata da nice wlh tun daga kan ginin nan gayyar zata watse. Hauka ma akeyi suci Talauci tare sannan dadi yazo ace ta zama yar kallo itafa da Boyi boyin gida babu banbanci. Idan anyi magana tace to ya zatayi? Na gaya mata taci abu ta kazan Yaya Audun tunda shi yake daurewa Bintan qugu tana mata iskanci kafin ta gangara kanta, ko Iskar qarya tayi ta musu rotse wlh duk zasu kiyayeta amma mata kamar Kazar da ruwa ya daka salaf salaf sedai tayita kuka in sun mata abu tana rama a haka fa kin ganta da kyan gani dalilin tajr Bechi kusan watanta biyar a can da ana gyaran gidan dawoqarta ne tayi wannan zabgewar to in aka cigaba a haka wata rana sedai azo a kwashi sauran qasusuwanta ai damuwa ta cinye tsokar tasa" Bilki ta fada cikin kumfar Baki.
Tsabar baqin ciki da takaici Balaraba kasa cewa komai tayi se qafa da take girgizawa, a haka Bara'atu ta dawo ta tarar dasu tana ganin Bilkin kuma ta tabbata ta gama kwaza komai. Fada Balaraba ta ringa mata kamar zata daketa da tayi tayi kuma seta koma banbaki da lallami dan lamarin Bara'atun ta rasa wannene ma zeyi amfani a ciki.
Banda kuka babu abinda takeyi ita kuma, haka suka kwana ko baccin kirki Balaraba bata iyayi ba, data rufe ido abin ze mintsineta ta tashi ta fara surfawa Bara'atun masifa can kuma tayi qasa tana lallashinta tareda bata dabarun kwatar yanci.
"Audu yana sonki, da ace baya sonki a yanda take wannan abun da ba zakiyi qarkon kawowa yanzu a gidannan ba. Wayo da dabara ne baki dasu, idan ta nuna miki wayewar Birni seki nuna mata ta qauye, akan me zaki ringa yiwa Kishiya kuka kin nuna mata kina tsoronta a fili ba dole ta takaki yanda taga dama ba, ai ko a ranki kina tsoronta ki dake idan ta fada ki mayar mata kar ki ganta wata zabgegiya kiji tsoron karta dake ki ai qarfi ba'a jiki bane idan kika qarfafa zuciyarki tsaf wlh zaki kaita qasa idan ma ta kaiku da dokuwa sannan shima karki raga masa tunda be dauki tsagin gaskiya ba. Wlh ki tashi ki kwatarwa kanki yanci idan ba so kike ki bata quruciyarki ki kashe kanki da kanki ba".
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Washe gari.
"Nifa wlh Ji nake kamar na rufeki da duka Bara'atu" Balaraba ta fada kafin taci gaba da cewa
"Banda tsabagen abin haushi Bintar me? Me akayi akayi wata Binta da zaki zauna ta shigo gidanki ta mayar dake yar kallo bayan ke kika ci wuyar Audun kika zauna dashi tun bashi da ko sisi har ya zama mutum ta ganshi ta aura na tabbata wlh a rayuwar da kikayi dashi Binta ko a me wanke mata kaya ba zata dauke shi ba. Amma shine kika zauna kika barta take zuba miki mulki a gida kin zama yar kallo jibeki dan Allah yanda kika qwanjale kika fita hayyacinki tamkar me wani ciwo ita kuwa tana walwala da farin ciki Miji na hannunta wlh tun wuri idan zaki farka gara, ki amshi Mijinki da matsayinki, ke kika sha wuya dashi dan haka yanzu kamata yayi duk wadda zataji dadinsa to a bayanki take".
"Kema dai kya fada Yaya Balaraba" Aisha ta tsoma musu baki taci gaba da cewa
"Koni da nake zaune a qauye wlh bazanyi sokoncin da Yaya Bara'atu takeyi ba banga wata kishiya da zanji tsoro ba, ba daga Kaduna ba ko daga Ingila ya aurota qarewar Bariki sena gwada mata nawa wayon qauyen dukda shima Yaya Audu da laifinsa ko nace ma yafi kowa laifi. Wancan zuwan da sukayi da Yaya Ummaru ya masa magana akan abinda tayi lokacin auran Saleh cewa yayi wai ayi haquri shi baya iya mata fada saboda idan ya duba yaga komai ya samu yanzu a rayuwa Ubanta ne sila kuma shi uban a duniya babu abinda yake so kamarta shi yasa yake mata lamuni kiji wani rainin hankali fa se kace wata diyar Qaruna ko kuma yanke Talauchi suka bashi".
Balaraba taja tsaki kamar zata tsinke harshenta kafin tace
"Saboda ubanta ya masa silar arziqi se akace tafi kowacce Mace ko yaya? Rabonsa ne a jikinsu kuma ko zasu bashi su haukace se yaci kawai tsabar mugun hali ne irin na maza matar da aka sha wuya tare da ita bola wadda zata diro rana daya itace abokiyar cin arziqi kuma wlh Audu ya bani mamaki a irin yanda kowa yasan yana qaunar Bara'atu ban taba tsammanin ko Gimbiya Elizaabeth ya auro ze fifitata akan Bara'atu ba"
"Abin ne nake ga kamar harda Asiri" Aisha ta sake fada Balaraba ta harareta tace
"Aikin kenan kullun ace Asiri, shin maza basa isakanci dole se an musu Asiri da yawa da haka suke fakewa ayita daukar Alhakin matan da basu ji ba basu gani ba ace asirce su sukayi, shidai Audu daman halinsa ne be fito ba se yanzu daman kuma kinsan kudi shi yake nuna ainihin kalar mutum ita kuma Binta tayi amfani da wannan damar take zuba sharafinta tunda shi ya bata qofa. Ni da Allah tashi kije ki karbo musu idan ba haka ba kuma naje da kaina" ta qarashe tana kallon Bara'atu data sunkuyar da kai idonta ya tara kwalla dalilin maganganun da sukeyi. Tun jiya Balaraba take mitarzancen nan, babu wanda ze fuskanci halin da take ciki kowa sedai yace mata wawuya ko sakarya ta kasa kwatar yan cin kanta ta sakarwa Kishiya ragamar gidanta daga zuwa to dan Allah base ta samu kwarin guiwa da Adalci daga gurin wanda ya ajiye su ba?
"Bari kiga na tashi" Balaraba ta sake fada tana yunqurawa dakyar saboda tsohon cikin dake jikinta nan Bara'atu ta zabura ta miqe tana cewa
"Bari naje, ni magana ce ban so wlh da kun barni yanzu se a dora musu wani tunda dai ta bamu iya rabon mu" da haka ta fice daga dakin tana jin Balaraban na zaginta. Yan Bechi na ganinta sukayi mata caa suna cewa
"Yawwa Hajiya Bara'atu, tun dazu muke jira a qaro abincin kinga yara se kukan yunwa suke wasu ko karin safe ba suyi ba muka fito". Da wani yanayi tace musu
"Kuyi haquri yanzu za'a kawo" ta fice daga falon zuciyarta na bugawa cike da taraddadin abinda ze biyo baya idan taje tace a qara musu abincin, dukda cewar su sukayi wahalar dafashi ita da wasu daga cikin yan uwan Audu da suka fara yowa gaba tun ana jibi suna. Seda suka dafe shinkafa kwano goma sha biyar, dambu kwano bakwai ga tuwon safe na kwano bakwai amma banda su Waina, Funkaso Alale da sauran tarkacensu irin na yan gayu da suka kai akayo musu daga waje amma a ciki tuwo Malmala goma suka basu se shinkafar da bata fi rabin kula madaidaiciya ba tun hantsi be gama dagawa ba kuma suka kusa cinye shi saboda ba'a karya ba duk suna jiran a kammala abinci sannan ga ma'aikatan da suka tayasu duk a ciki ta debar musu suka tafi dashi gidajensu gaba daya yan uwan Bintan suka lode abincin a Kuloli suka kai daki.
A hankali take gifta matan dake zaune tsakar gidan yan suna, wasu maqwaftansu ne wasu kuma qawayen Binta da matana Abokanan Audu wanda suke hulda da ita kadai duk kuma rukunin data wuce zata musu sannu wasu su amsa wasu suyi mata banza harta dangana da qofar falon Binta,
"Maman Baba" taji an kirata ta waiwaya fuskarta ta fadada da murmushi ganin Maman Kabir ce maqociyarta guda daya da suke sabgar Arziqi gaba daya sauran Binta ta kwace su ko tace sun koma gurin Bintan.
"Se yanzu zaki shigo mana" ta fada tana jan kumatun Kabir dake hannunta ya kuwa janye ya lafewa mamansa tayi dariya tace
"Maquyacin kawai"
"Tun safe naso na leqo baqi nayi wlh se yanzu suka tafi" Maman Kabir din ta fada. Bara'atu tayi murmushi tace
"Na sani tsokanarki nakeyi dazu Shamsiyya ta shigo ai tace Yayan Baban Kabir ne yazo, qarasa ciki to yanzu zanzo abu zan karbo gurin Binta".
"Ai gara na biki nima naga Jinjiri kafin na zauna" Maman Kabir ta fada hakan yasa suka shiga falon Bintan tare. Yayyenta na tsaitsaye a falon sun hada kai suna magana sallamar su Bara'atu ta sakasu zabura tamkar marasa gaskiya, Yaya Salima ta qaqalo fara'a ta yabawa fuskarta tana kallon Bara'atu tace
"Aa uwargida an leqo? Sannunku fa da aiki"
"Uhm" Bara'atun tace kafin kanta a qasa cike da taraddadi tace mata
"Daman yan Bechi da suka zo yanzu ne Abinci be isa ba shine nace ko za'a dan qaro musu"
"Aikin kenan abinci Abinci koda yake ba a saba ci ba, banda jaraba ma suna amma anyo gayya kamar wani Bikin fari wato za'azo aci banza to babu kowa ya nade yunwarsa ya koma da ita" Munira wadda take autarsu Bintan amma ta rigata aure ta fada cikin Fitsara se Yaya Saliman tayi saurin tareta tana cewa
"Haba ke kuwa Munira Abinci dai Allah na tuba abin aci ayi kashi kuma fa mutanen nan dangin me gidan ne idan ba'a basu ba to su za'a bawa? Barta dan Allah Bara'atu shiga ciki ki gayawa yar uwartaki se muji kamar Adadin da za'a zuba musu" ta qarasa tana nuna mata qofar dakin Bara'atu.
Maman Kabir da takaici ya quleta, ba abin tayi magana ba ta jawa Bara'atun ta juya kawai ta fita tana ce mata
"Bari naje an jima kan na tafi ma gaisa da ita" Bara'atu kuwa a sanyaye ta tura qofar dakin Bintan da sallama wanda tun zuwanta gidan shekara guda sau daya ta taba takashi randa aka kawota, ko ranar da zata haihu a qofar falo suka hadu ta taimaka mata suka tafi Asibiti. Zuciyarta duk babu dadi ta shiga, ita abincinma ko kalarsa bata dandana a harshenta ba da suka gama girkin shayi ta kada tasha saboda yanda ta gaji sannan duk taron Jama'ar da suke iqirarin sunzo cin banza Jininta biyu ne a ciki Hadiza wadda dama tare suke zama se Ubaida data biyo yan zuwa suna saboda taga Yan uwan nata ragowar dukfa Dangin Audu ne, qanne da yayyensa da Matan yan uwansa se Maman Kabir Qawarta tilo da ta shigo yanzu wadda tana da tabbacin harta fita be zama lalle ko ruwan fanfon gidan tasha ba.
Bata tarar da Binta a dakin ba motsin da taji a Bayi yasa ta ankare da tana ciki, Jinjirin daya ci sunan Babanta Binta Zakariyya na nade cikin showel ta matsa inda yake yanda aka kwantar dashi yayi kusa da bakin gado sosai, dukda cewar jinjirine amma ze iyayin motsi me qarfin da ze fado hakan yasa ta dagashi ta maidashi can tsakiyar gadon yana ta sharar bacci abinsa daidai nan taji muryar Binta akanta tana cewa
"Waye wannan? Uban me kikeyiwa Dana?"
"Gyara masa kwanciya nayi, naga an barshi a bakin gado" Bara'atun ta fada kanta a qasa. Binta ta galla mata harara ganin itace kafin tace
"Akan me zaki shigo mun har quryar daki me kike nema?"
"Daman maganar Abinci ce yan Bechi sun qaraso wanda aka bayar kuma ya qare shine nace ko zaki saka a qara musu"
"Babu, gayyar yunwa nace babu abincin ko kuwa ni na ce suzo balle na basu abinci?" Bintan ta fada cike da masifa. Bara'atu ta kalleta tace
"Yan uwan Yaya Audu ne fa ba wasu daban ba"
"Yana sama ai seki hau ki gaya masa ya sakko ya girka musu suci tunda yan uwansa ne ko kuma ke ki je ki sake dora wani amma ni abinci na ban dafa saboda wasu yan qauye ba na baqin dana gayyato ne dan haka malama maza fitarmun daga daki tun ranki be baci ba"
Kafin Bara'atu ta sake cewa wani abu burum Yaya Salima ta fado dakin kamar wadda ta labe daman tana jiran lokaci yayi ta shiga. Inda jinjirin yake ta nufa ta dauke shi tana cewa
"Bari a fita dashi mutane nata zuwa ganinsa se kuma ta zare ido ta kalli Binta data cire dankwalin kanta zata canza kaya tace
"Ke zo ki gani wane irin bacci yaron nan yakeyi haka qirjinsa baya dagawa alamar numfashi?"
tana rufe bakinta Babbar Yayarsu Anty Sakina ta shiga dakin ta kallesu sunyi cirko cirko tace
"Lafiya kuwa meya faru?"
Salima ta miqa mata Babyn tana cewa
"Yawwa dubashi kiga Anty se naga kamar baya numfashi" da yake ita malamar jinya ce, nan ta tattaba yaron tayi salati tace
"Wannan ai ya rasu".
Maganar ta taja hankalin Bara'atu da har ta kai qofa ta tsaya, Binta ta finciki yaron daga hannun Yayarta tana duba qirjinsa babu alamar yana dagawa, ta kai kunnenta zuciyarsa bayan ta saka hannu a hancinsa bata ji dumin numfashi ba nan ma shiru seta sake shi Yaya Saliman tayi azamar tarewa kafin ya kai qasa kamar qiftawar Ido Binta ta dira gaban Bara'atu ta cakumeta tana cewa
"Kashe shi kikayi? Na rantse da girman Allah se kin bishi" nan ta shiga kai mata duka kamar me casar gero kururuwarta da ihun Bara'atun ya janyo hankalin sauran dake falo shigo gaba daya, tuni gida ya dauki hayaniya magana ta fasu Bara'atu ta kashe jinjiri gashi can Binta ta riqeta itama tace seta kasheta. Binta ko dukan Bara'atu take babu ji babu gani tamkar ma bata hayyacinta fadi kawai tace
"Wlh sena kasheki, sena bi kadin haqqin dana" ta shiga jibgarta tamkar Mahaukaciya ta kama yaron da yake tsokanarta saboda rashin Imani kuma yan uwanta kaf dake tsaye aka rasa wadda zata kwaci Bara'atun daga inda suke tsayen suke ce mata wai ta qyaleta ga gawar Jaririn a Hannun Anty Sakina.
Ihun Bara'atu na neman ceto da kururuwan Binta tana fadin seta kasheta ne ya janyo hankalin Yan suna. Hankali tashe yan Bechi suka duru darin, su suka taru suka danne Bintan har Bara'atu ta samu ta kubuta daga hannunta tayi mata jina jina fuska ta haye dan duka tasha ta ko ina.
"Meye haka? Kinyi hauka ne Binta zaki kama ta da duka?" Audu da suka sakko da gudu shida Jama'arsa da suka zo mata suna ya fada cikin tashin hankali.
"Wlh ban gama dukanta ba, idan anga na haqura to na kasheta kamar yanda ta kashe mun Da" Bintan ta sake fada tana zaburowa yan uwanta suka riqeta. Cikin rashin fahimta Audun yace
"Wace magana kikeyi haka? Wane dan aka kashe?"
Bayan wasu Awanni.
Ihun kuka da hargowar Binta kawai ake ji a falon,
"Na rantse da girman Allah yanda ta kashe shi itama seta bishi babu uban daya isa ya hanani daukar mataki akan wannan abun" taci gaba da sheqa kuka. Dazun da akayi jana'izar yaron sanda aka zo fita dashi qaramin hauka ta tayar ta riqeshi qam dakyar Maza suka bambareta ta ringa doke doke qarshe se a daki a ka kulleta se yanzun bayan Isha Audu yaje ya budeta da kansa ya tasa qeyarta zuwa samansa inda Yakubu yace ya tattaro su gaba daya aji abinda ya faru. Babu tsoron Allah ko tunanin bayan wannan rayuwar da akwai wata Munira da Salima suka bada shaidar Bara'atu ce ta kashe jaririn dan Munira cewa tayi ta leqa dakin ta hangota zaune an showel dinsa bata dai tsammaci yana ciki ba seda Salima ta shiga ta tarar da ya mutu.
Sakina dai tayi shiru, har ranta bata so abinda sukayi ba, magana ta gaskiya yaron ya rasu tun kafin Bara'atu ta shiga dakin, qus qus din da ta tarar dasu sunayi na taraddadin yanda zasu fada mata ne suma basu san menene silar mutuwarsa ba haka nan suka lura da babu rai tattare dashi shine suka shimfide mata shi a kan Gado ita kuma Bara'atu ta taka sahun barawo kuma tana shiga Salima ta kitsa ai kawai suce itace kuma har yanzun basu fadawa Bintan ainihin abinda ya faru ba.
Yakubu ya kalli Bara'atu data zama wata abar tausayi, fuskarta a kumbure ga duka ga uban kukan datasha. Cikin tausayawa yana kallonta yace
"Bara'atu menenr gaskiyar abinda ya faru?"
"Wallahi Allah shine shaidata ko taba yaron nan banyi ba. Ni daga haihuwarsa ma sau daya na taba riqeshi a Asibiti, sanda na shiga dakin na tarar dashi sun kwantar dashi a gefen gado abinda ya saka na matsar dashi tsakiya saboda naji tsoron karya motsa ya fado shine Binta ta fito ta ganni ko ita idan zata fadi gaskiya a tsaye ta ganni ban zauna mata a daki ba ga yan uwana nan a tambaye su da fitata daga daki zuwa sanda abin ya faru ya isa ace na zauna akan Jariri ya mutu har jikinsa yayi sanyi?" Bara'atun ta fada cikin dasashshiyar murya me ban tausayi. Yakubu ya gyada kai cike da aminta da zancenta ya kalli Audu yace
"Kaji daga kowanne bangare se kayi alqalanci bisa Adalci"
"Alqalanci? Shi ne ze yanke mun hukunci akan kadin ran dana da aka dauka? To billahillazi huwarrahamanu ba'a isa ba, ku barni na kasheta da hannuna ko kuma gobe na tafi kotu, ina da qwararan hujjojin da zasu saka a zaman farko Alqali ya saka a gillewa muguwa kai ta bishi, wlh ran dan baze tafi a banza ba" Binta ta sake zaburowa tana fada.
"Ya isa kiyi shirunki babu wanda yace ran danki ze tafi a banza" Audu ya fada, kafin ya kalli Bara'atu yaci gaba da cewa
"Dama ai kinyi furucin se kin ga bayan ta ita da abin cikinta. Allah be baki nasara ba tun yana ciki baki haqura ba seda kika aiwatar da shirinki yanzun ko Bara'atu yaushe kika zama muguwa me baqar zuciya haka? Ina tsoron Allan ki da har zaki iya zama akan Jinjirin kwana bakwai har seda ya daina numfashi me ya tsare miki a duniyar daya saka kika kauda shi?"
Shiru ne ya gifta gurin kamar kowa ya mutu koda yake da yawa daskarewa sukayi basa ma numfashi tsabar mamakin Kalaman Audu, Yakubu har zamewa yayi daga kan kujera yana leqen fuskar Audun ya kuma gaza furta komai. Audu yaci gaba da magana yana cewa
"Na gaji da wadannan mugayen halayen naki Bara'atu, daman simi simin mutum da yawanku mugayene, zuciyarku cike take da mugunta fal gashi kuwa kin fara fito mana da ita. Yau kin kashe Zakariyya, qila gobe Kan Bintan zaki juya idan aka kwana biyu kuma ki hau kaina na mutu ki gaje abinda na tara dake da yayanki ko ba haka ne shirinki ba shiyasa bakya so Binta ta haihu saboda ya zama yayanki kadai suke da gadona to bazan jure ba, ai se da igiyoyin aurena akanki ne idan na mutu zaki ci gado na ko? To kije kawai Allah ya hada kowa da rabonsa na Alkhairi na sawwaqe miki igiya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 32