Suna tsaye nan cikin rashin mafita kamar daga sama sega Kasim, Abokinsa ne amma irin wanda alaqar bata da qarfi sosai. Audu ya sauke ajiyar zuciya yana yiwa ubangiji godiya daya kawo masa Kasim din. Alfarmar Baburinsa ya nema ya bashi haka aka cocciba Balaraba da sam bata cikin hayyacinta Dada ta hau bayanta suka sakata a tsakiya suka tafi Kumbotso aiko wannan abu ya qara hura wutar gori Goggo Fadi ta ringa masifa tana fadar maganganu cewar Dada batayi kara ba. Ita kuwa Dadan tsabar rudu da tashin hankali yasa sam bata san sanda ta haye mashin dinba dan gani takeyi idan wani abu ya samu Balaraba itace sila tunda babu yanda Audu beyi suje Asibiti ba tun gari nada haske.
Page 7
Cikin hukuncin Allah isarsu Asibitin babu jimawa Balaraba ta sauka sedai yar tazo babu rai wanda ko ba'a fada musu ba sun san wahalar data sha a ciki ce tayi Ajalinta ita kanta Balaraban babu yanda take hankulansu basu dan kwanta ba seda Likita ya tabbatar musu da Balaraba zata samu lafiya da yardar Allah. A nan cikin Asibitin suka kwana, da sassafe Audu ya tafi Bechi tareda gawar yarinyar can aka shiryata akayi jana'iza kafin Bilki ta hada duk abinda Balaraba zata iya buqata suka juya Kumbotso tareda Bara'atu da Mariya matar Aminu se Maimuna Amaryar Hashimu da itama tana hulda dasu Balaraban dukda mijinta baya so. Goggo Fadi data kwafe tun jiya cewa tayi ba zataje ba dan haka sula tafi. Seda Balaraba ta kwana uku Asibiti kafin aka sallamota dan ba qaramin jiki taji ba. Ta rame fiyau se haske data qara kamar mara jini duk wanda ya ganta seya tausaya mata ga rashin jaririyarta ga Yakubu baya kusa yana can nisan duniya bema san abinda ya wakana ba. Haka sukayi ta tausarta harta saki zuciyarta, kwananta Ashirin da haihuwa Dada tayi mata izinin tafiya can Rugarsu dukda yan uwanta sunzo sun dubata har sun bar mata yayarta daya ita ke kula da ita amma Dadan tace taje ta huta kota qara rage kewa a sannan tuni Audu ya koma Kano ya kuma aikawa da Yakubu wasiqa ya sanar masa da abinda ya faru.
Haka aka cigaba da lallaba rayuwa, Su Yakubu sun samu hutun shekarar farko a karatunsu ya taho gida cike da kewar matarsa da kuma Alhinin yarsa daya rasa. Tsaraba niqi niqi yayo daga ikko, kowa seda yasan da dawowarsa domin dangi kaf kowanne gida seda abin Alkhairinsa ya leqa. Yaya Baba da kansa yake cewa
"Tabbas yaran nan sun san Alkhairi, ka dubi duk abinda mukeyi musu amma basu riqe mu ba ba kuma su canza daga kyautatawar da sukeyi mana ba"
Hashimu da yayi maganar a gabansa yayi tsaki zuciyarsa tayi baqi, haka siddan shedan yake hura tsanar su Audu a zuciyarsa yana qissima masa cewar duk abinda suke samu shida yan uwansa ya kamata ace sun same shi amam basu Audun ba.
Shidin mutum ne me shige shigen zuwa gurin Malamai, a yawonsa aka binciko masa cewar Yayan Dadan suna da taurarin arziqi, yabi malamai sun fi nawa amma kamar hadin baki duk inda yaje se a ce masa su dun zasu daukaka irin daukakar da beyi zato ba, da yake yayi ammana da zancen Malaman nasa shikenan qyashi da hassada ya darsu a ransa ya kuma dage ta duk wata hanya dayake tunanin daukakar zata zo musu yake qoqarin tosheta sedai rashin sani irin nasa fadar Malaman tsibbunsa ba gaskiya bace, idan kuma anyi katari sun canki daidai to wayo ko dabararsa basu isa su canza abinda ubangiji ya qaddara faruwar iya wuya se abinda ubangiji ya qaddara ya faru.
Cikin tsarabar da Yakubu yayiwo wa matarsa data qaninsa harda qananan kaya irin wanda Arna suke sakawa, a cewarsa daya kalli haram a jikinsu gara ya kawowa Balaraba ta saka masa yasan zasuyi mata kyau matuqa ya kuma hado da Bara'atu itama tayiwa dan uwansa kwalliya harda Bilki da Aisha dasu Amina ya warewa kayane riga da skirt wasu da wando irin me roba idan an saka suna kama jiki a lokacin su kansu Arnan basu fara shigar badala ta rabi tsirara suna yawo a gari ba amma dukda haka su a gurinsu irin wadannan dinma sababbin abu ne. Aiko da yar bafulatanat tasa ta saka ba qaramin kyau tayi ba, seda Audu yazo Bechi Bara'atu ta tsantsara masa kwalliya da nata kayan, yanda tayi kyau ta burge shi ya sakayi cewa Yakubun mezzo hana su fara kawo ire iren qananan kayan na Mata dana yara harda ma na Maza dan suma yazo musu da Jeans da shirts tunda yace duk akwai su kuma suna da sauqi a can.
Haka kuwa akayi Bayan Yakubu ya koma ya qullo dila guda ya aikowa Audu. Tun kafin kayan su iso daman yayi tallarsu dan haka yana bude dila bata rufe sati ba se burbudi masu siyan daidai da sari sun kwashe, yanda mata suka dinga zuwa suna siya da siyawa yaransu ya bashi mamaki, kuma a lokacin bakin Asibiti kaf shi kadai ya bude irin kayan wannan dalili yasa saya tashi turawa Yakubu kudi ya ninka wanda suka siyo da farko kamar wasa se gashi sana'ar ta karbeshi ya zama wata dilar ma idan ya kwance bata kwana dan ya dena siyar da guda daidai ma yan sari ne suke kwasa a qasa da wata shida se gashi ya kama hayar Rumfa a cikin kasuwar sabon gari inda akafi siyar da ire iren wadannan kayayyakin ya kumayi suna idan ka shiga kasuwar tun daga qofa daka tambayi shagon BECHI za'a kaika. Cikin wannan yanayi ludufi da budi yayi ta zuwar masa, be kuma tsaya kan iya kayan nan ba yaci gaba da gwada duk wata sana'a daya san zata kawo kudi, kantin da suka bude a gida kuwa kullum sake habaka yakeyi dukda kwanaki sun samu Asara an farke shagon an kwashi kaya daga baya aka kama yaran da sukayi kuma sukace Hashimu ne ya sakasu, Dada ce ta hana su daga maganar, an dai je har gaban Me gari akan ayi musu iyaka da Hashimun wanda a wanann karon Goggo Fadi kanta ta nuna masa bacin rai akan abinda yayi Audu kuma ya sake sarar kaya harma da wanda da babu a shagon ya zuba.
Tun haihuwar Bara'atu ya qudurce a ransa cewar ze kafa sana'ar siyar da fetur a Bechi, koda masu Ababen hawa da suke da buqatar Fetur din daidaikune amma abinda ya faru na rasa wanda ze taimaka masa ya kai Balaraba Asibiti yasa ya yanke shawarar ze fara Bunbutun koda kuwa ba za'a siya kullum ba wata rana tana iya daurowa a samu me siyar. Aiko ya samu wani Abokinsa Falalau da suke cewa Fala dan bakin Kasuwa ne a nan cikin Kano tare suke a bakin Asibiti kafin ya kuma bunburu da kuma siyar da kayan gyaran mota, a gurinsa ya sari Mai harda su man juye da sauran yan abubuwan buqata, anan qofar gidansu ya kafa Katako inda ya dora jarakunan Man, Baballiya na kula da shago yana kuma kula da Man shida Abdullahi kuma cikin ikon Allah da masu motocin daukar kaya suka gane da yawa basa damuwa da su shawo Mai a Kano kafin su dawo gida tunda sun san da akwai.
A cikin Kanon ma ya bude guri nan cikin Goron dutsen ya ajiye wani yaro yana kula masa da Man shi kuma ya tafi Kasuwa, an samu shekara daya a haka zuwa sannan Ya fara damuwa da rashin samun cikin Bara'atu domin Balaraba harta kuma samun wani cikin yanzun bayan zuwan Yakubu hutun qarshen shekara ta biyu a karatunsa na shari'a. Damuwarda Bara'atun take nunawa yasa ya danne tasa sannan kullum Dada na nuna musu cewar Haihuwa lokaci ne idan Allah ya kawo zasu samu tunda ga yar uwarsa Bilki nan me shekara biyar a daki har yau bata samu ba itama toh suyi haquri suyi addu'a ubangiji ya basu a lokacin dayafi musu Alkhairi.
Da Abokinsa ko muce Amininsa Lado ya tattauna maganar, shiya ke ce masa daman yawanci Matan matafiya basu cika samun ciki da wuri ba, Audu yace ya akayi Ita Balaraba ta samu ciki toh bayan yafi Yakubu yawan zuwa gida? Lado yayi dariya yace
"Ta yuwu lokutan da kake zuwa basu dace da irin lokutan da mace take daukar ciki ba, shi kuwa kaga idan yazo ya kanyi wata guda ko sama da haka a gida kai kuwa zuwanka a tsitstsinke ne wani sa'ilin ma baka wuce kwana biyu uku ka juyo, nima wani Abokina da yake karatun lafiya naji ya fada an musu a karatunsu cewar da akwai wani lokaci bayan gama Al'ada da kwayayen halittar mata suke nuna su shirya daukar ciki to idan anyi dace an samu tarayya a irin lokutan nan shine zakaga an samu rabo bawai yawan kwanciya da mace ne yake kawo ciki ba".
Wannan magana da sukayi da Lado ta sakashi bayan yaje Bechi ya roqi Dada akan yana so su tafi Kano tareda Bara'atu ze kaita Asibiti dan yana so a gaya musu wanne lokaci ne mahaifarta take shirya daukar ciki, Dada bata qi ba suka tafi satinta daya ya maidata bayan tasha yawo a Kano ya kaita gurare dan wannan shine karonta na farko da taje, ya nuna mata gininsu da qiris ya rage a kammala ta ringa murna kuwa tana komawa ta qyarawa Balaraba dukda Audun ya gargadeta akan karta gayawa kowa tukunna amma murnar zasu koma Kano yasa ta kasa daurewa cikin ikon Allah kuwa komawarsa babu jimawa ta fara amaye amaye ko ba'a fada ba ansan ciki ne Dada ta ringa cewa gashi nan da suna garaje harda zuwa Asibiti ashe da cikinta ma lokacin bayyanarsa ne beyi ba. Da Audu ya sake zuwa kuwa haka ya kwashe su da Balaraba sukaje Kumbotso inda take Awo akayiwa Bara'atun itama register zata fara zuwa idan cikinta yayi wata hudu a sannan watansa biyu da kwanaki. Ko tari Dada batayi ba dan ba zata so a maimaita abinda ya faru a cikin Balaraba na fari ba shiyasa ko Audu bezo gari ba ranar Awonsu tazo da kanta take tasa su gaba ta rakasu ko kuma Bilki ba kuwa qaramin surutu take sha gurin Goggo Fadi ba wai rashin kunya ce.
Wani lokaci Audu yazo gida kamar yanda ya saba, a lokacin cikin Balaraba nada watanni takwas na Bara'atu kuma yana wata biyar. Da yammaci ta tasashi gaba da wai makani take so taci, ya rasa inda ze samoshi anyi shukar makanin amma ba'a fara kawoshi gida ba. Cikin Bara'atun irin me dan banzan tsirfa ne idan kuma ta rasa abinda take so haka zata wuni ranar tana kuka da baqin Rai haka Audu ya fita akan Sabon Mashin din daya siya saboda zirga zirgar kaisu Asibiti ya ajiyewa Baballiya, gurin Shamsu Abokinsa ya tafi yana tambayarsa inda za'a samu Makani, ya ringa tsokanarsa suka hau mashin din suka tafi gonar Usman da Shamsun yace yayi shukar makani kuma ko babu yawa za'a iya cirar wanda ya nuna. Gonar tasa tana can kusan babban titi wanda tanan zaka gangaro ka dauki hanyar shiga Bechin sun samu Usman din ya debo masa da yawa kuwa cikin wanda ya fara cirewa.
Sun fito daga Gonar suna magana hankalin Audu nakan wata mota can daya hango tsallken Titi tun shigarsu gonar ya ga motar a tsaye yanzu kuma har mutanen ciki sun fito sun bude gabanta da alama ko lalacewa tayi. Seda ya daure ledar Makanin a kan mashin kafin ya cewa su Shamsu yana zuwa ya tsallaka can gurin motar, tun kafin ya qarasa yake jiyo muryar mutumin da yake zaton shine me motar yanayiwa Driver sa fada cikin harshen turanci shi kuma se faman haquri yake bashi. Audu ya qarasa yayi musu sallama dukda bashida tabbacin Musulmaine, mutumin ya juyo ya kalle shi, tabon sallah daya gani a goshin sa ya tabbatar masa da cewar Musulmi ne. Mutumin ya amsa sallamar Audu yana qare masa kallo kamar yanda shima Audun yake kallonsa, Dattijo ne dan a qalla ze iyayin shekaru Hamsin da biyar zuwa sama fari tasa me matsakaicin jiki ya tsuke cikin Coat baqa kana kallonsa kasan ya juqu a Bako sannan motarsa zata sanar maka cewar babban mutum ne da gani.
Cikin Turanci Audu ya gaishe shi yana tambayarsa meya faru dan beyi zaton yanajin hausa ba tunda turancin yaji yana yiwa Direba ga mamakinsa se yaji ya mayar masa da Hausa yace
"Wallahi Motar muce ta tsaya, na dauka ma wani gyara ne kuma wai Ashe mai ne ya qare mana qarqaf kuma saboda shashanci wannan Direban be duba man ba kafin mu kamo hanya gashi yanzu a nan bansan yanda zamuyi ba babu kuma service din kira a nan gurin ballantana nayi waya cikin Kano a kawo mana wata motar" ya qarasa yana daga qata waya da sau daya Audu ya taba ganin irinta hannun wani Bature da yake siyan kaya a gurinsa.
Direban ya sakeyin qasa da kai yana cewa
"Kayi haquri Sir, nidai nafi zaton malejin motar ne ya samu matsala dan seda na duba komai kafin mu taso kuma naga man da muke dashi ze iya kaimu gida har yayi ragowa lokaci daya ya sauka kuma motar ta mutu"
Mutumin ya galla masa harara ba tareda yace komai ba tunda motar ta tsaya yake nanata masa maganar wai malejin ne be nuna masa daidai ba yaci gaba da daga wayarsa yana neman service yana kuma dan waige waige a fakaice dan a tsorace yake, koda yake duniya na kwance a sannan amma wannan Titi da yake shiru tun tsayuwarsu ko Keke be gifta ba balle mota se Audu daya fado musu katsaham kamar Aljani kar suje ba shi kadai bane a mamaye su ayi musu wani mugun abun.
Audu yayi murmushi yana cewa
"Ayya lamarin qarfen nasara babu tabbas, ku jira bari na shiga cikin gari sena kawo muku Man yanzu indai shine matsalar" yana fadar haka ya juya cikin sassarfa ya tsallake titi ya koma inda su Shamsu suke jiransa. Su ukun suka hau Mashin din suka koma cikin gari. Hankalin mutumin da Driver sa ya tashi, karfa gayya zeje yayo azo ayi musu wani abun? Suka kalli juna kowanne kana iya karantar firgici a fuskarsa, ga mota taqi tashi idan sukace su kwasa da gudu kan suje ko ina su Audun zasu iya cimmasu gaba daya nadamar zuwa Taron daya kawo shi Kano ta kamashi, yana zaman zamansa qungiyarsu ta masu lasisin haqar man futur ta shirya musu taro a Kano kamar baze zo ba ashe Ajaline ya kirashi. Jiki a sabule ya shige motar ya zauna ya hada kai da kujera danya gama saddaqarwa yau kam tasa ta qare, qarar mashin dayaji tasa shi dagowa a firgice sedai ganin Audu tareda Shamsu daya rungumo Qatuwar jarka ga bututu da tiyo a hannunsa yasa shi sakin ajiyar zuciya babu shiri zufar dake keto masa ta fara qafewa har iska na fifitashi.
Fitowa yayi daga motar lokacin har Audu ya bude jarkar yana jiran Direba ya bude gida man a zuba musu shi kuma yana kallon ubangidansa cikin jiran umarni, kai ya gyada masa alamar bada dama ya bude musu, seda ya cika musu tanki taf da mai kafin ya rufe jarkarda dan ragoqar daya rage ciki yana kallon Direban yace
"To ka kunna mu gani"
Direba ya kunna mota se gashi kuwa ta tashi, fuskar Alhajin ta sake washewa yana kallon Audu yace
"Amma a ina ka samo Fetur haka?"
"Ina siyarwa ne anan cikin garinmu" ya bashi amsa. Alhaji ya zura hannu a Aljihu ya zaro kudaden da besan yawansu ba ya miqawa Audu yana cewa
"Nagode kwarai samari"
"Aa ka bar kudinka Alhaji kyaiuta na baku"
"Amma kace siyarwa kakeyi" Alhajin ya fada yana sake miqa masa kudin. Audu yayi murmushi yace
"Eh siyarwa nakeyi amma ku kyautana baku, da zan karbi kudinka tun farko zance maka ina siyarwa ka fadi na nawa za'a zuba maka"
Alhaji ya gyada kai cike da gamsuwa har sannan fuskarsa dauke da murmushi yace
"Hakane, nagode kwarai, yanda ka kaimakeni kaima Allah ya kawo maka wanda zero taimake ka a lokacin da bakayi tsammani ba" suka amsa da Amin. Ya sake saka hannu a Aljihu ya ciro wani dan kati me kyau ya miqawa Audu yace
"Ga katina, idan ka samu dama ka nemeni kaji, Nagode kwarai dagaske Allah ya saka"
Audu ya karbi katin da aka rubuta 'ZAKARIYYA PAKI AND SONS' ya jefa a Aljihu daga nan Alhaji ya shiga mota yana daga musu hannu har suka bar gurin.
Audu da Shamsu suka hau mashin Shamsun nata mita akan me Audu be karbi kudinba yace shi taimakonsu yayi saboda Allah kuma iya addu'ar da yayi masa ma ta ishe shi.
Yanayin garin lokacin sanyi ne dan haka Dada nata fama da mura me zafi wadda daman tanayinta duk sanyi har da daukewar numfashi wani lokacin take samu tun su Audu na qanana haka suka tashi sukaga tana shan wahalar nan duk sanyi shiyasa ya siya mata manyan fulasan ajiye ruwa sannan sanyi na shigowa zasu cire labule me saukin da yake a jikin qofa a saka mata jibgege haka dakin baya rabo da rushi amma dukda haka data fita tsakar gida ta shaqi hazo da sanyi haka zatayita haki tana jan numfashi. Maganin gargajiya take sha tuntuni wannan karon kuma tun zuwan Audu yake fama da ita akan suje Asibiti dan zamansa a Kano yasan cutar Asthma, akwai qanin Hayatu Magashi da yake da ita kuma duk yanayin ciwon nasa haka Dadar take fama sedai taqi yarda suje Asibi balle a dorata akan magani tace tafi gane na gargajiyar da take sha tun tana yarinyarta.
To wannan karon ciwon nata yadan ta'azzara dan dalilin daya hanashi komawa Kano kenan kusan satinsa biyu a Bechi se jikin yayi sauqi se kuma ya dawo. A daren ranar ma kwana sukayi zaune saboda yanda ta kasa bacci tana jan numfashi dakyar tun bayan data dafawa su Bara'atu makani hayaqin Karan datayi girkin dashi ya cika mata qirji shikenan numfashi ya fara sama sama washe gari kuwa da sassafe Audu ya kwasheta duk yanda take tirjewa seda sukaje Asibiti. An mata Allura an kuma rubuta mata magunguna ya siya bayan dokoki da sharuddan da likita ya kafa mata akan ta kiyaye duk wani abu daze hadata da qura ko hayaqi suka dawo gida. Wunin ranar zur a dakinta yayi shi haka qannensu da matansu duk suna nan suna hidima da Dadan da gaba daya tayi wani laushi dukda tace taji dadin Allura da maganin data sha abinda take ji a qirjinta ya yaye amma jikinta babu qarfi dama kuma likitan ya gaya musu magungunan akwai me kashe jiki yasa bacci dan haka Audu yace ta kwanta ta huta.
Page 8
Goggo Fadi ta ringa sakin maganganu a tsakar gida wai Lamarin Dada dai ta rasa ma abinda zatace akai wannan rashin kunya har ina ta ringa hawa mashin Yara na goyata sannan danbata da lafiya kamar wata jinjira ta langwabe duk se wani zuruftu yara suke akanta, lokacin da take maganar Dada ta fito Aisha ta rakata kewaye ta fito tana daura Alwala. Seda ta idar ta kalli Goggo Fadin da murmushi tace
"Yaya kenan, indai nice kin kusa ki dena ganina ballantana nayi abinda ze sakaki surutu".
Goggo Fadi ta ce
"Eh ba shakka Hafsatu wato daman naji ance zakuyi qaura Birni yo ni ai haka nake so ku tattara ku tafi ku barmin gidana yanda kuka zo kuka sameni, bari ma wannan yaron yazo kuyiwa gurin naku kudi kawai ya fiddaku shikenan wanda ya hada ya raba"
Har Dadata zura qafarta a daki ta sake waiwayawa tana murmushin da seda gaban Goggo Fadi ya yanke ya fadi haka kawai tace
"Toh ai Malam ba sauri yayi ba Fadi, zan bishi kema kuma komai dadewa zaki biyo bayanmu" daga nan ta shige dakinta tabar Goggo Fadin na sababi ita kadai.
Da dare Audu ya kawo mata Kaza gasashshiya da Madara sabuwar tatsa dan gama tafasata kenan ya karbo ko hucewa batayi ba. Dada na cin naman Baballiya na gefenta yana so yaci Audu ya hanashi Abdullahi daman tuni ya gudu gurin Bara'atu tunda yaga Audun ya shigo da ledoji kuma har Goggo Fadi seda ya miqawa. Dada taci ta qoshi ta turawa Baballiya tana cewa
"Ci ubana kaji haka kawai yabi ya takuramun kai"
"Wlh Dada ke kike dada sangarta yaron nan ya girma amma baze dena sakarci ba a haka kake cewa zakaje aikin Sojan" Audu ya fada, Dada ta kishingide tana sakace tace
"Ze dena ne, aikin Soja kuma nasan indai kana raye seka cika masa burinsa kamar yanda ka dakko hanyar cika na dan uwanka. Ina Alfahari dakai Abdulwahabu ina kuma roqon Allah yaci gaba da hada kanku ya baka ikon ji gaba da jajaircewa akan zumunchinku, ina fatan har yaya da jikoki kuci gaba da hada kanku karku yarda qata baraka ta shiga tsakanin ku, Banida haufi domin kunyo dacen mata na kwarai saboda rayuwar Namiji komai nagartarsa idan yayi kuskuren dace da macen aure anan yake samun tawaya dan haka ina horar ku cewar ko gaba koda ace kunyi sha'awar qara aure kuyi qoqari gurin zabo matar da zata tayaku kuci gaba da hada kan gidanku ba wadda zata tarwatsa muku farin cikin da kuka ginu akai ba. Sannan yan uwanku kuci gaba da haquri dasu kuna jan su a jiki da sannu wata rana zaku koma tamkar baya sanda Malam yana raye".
Haka ta ringa masu nasiha me shige da wasiyya, Baballiya na gama cin kazarsa ya sheme a gurin ita da Audu sukaci gaba da yar hira har ta fara gyangyadi kafin ta hau gadonta yaja mata abin rufa bayan ya shafa mata man zafi a tafin qafarta ta saka safa. Seda ya zubo toka me zafi a babban kaskon da ake ajiyewa a dakin yayi masa mazauni me kyau saboda gudun tsautsayi kafin ya tashi Baballiya ya gyara kwanciyarsa yaja musu qofar ya fita jikinsa a sanyaye saboda maganganun da Dada ta fada masa, yanda take nanata masa hadin kan Iyalinsa kamar wadda take hango wani abu a gaba haka ya shiga dakinsu Bara'atu har tayi bacci ya raba gefenta ya kwanta sedai be jima da kwanciya ba bugun qofar gida ya farkar dashi.
Da mamakin wayake musu bugu cikin dare ya dauki fitila ya fita, seda ya tambayi waye, muryar Yakubu dayaji ta sakashi bude qofar da sauri ya rabe ya shigo ganin yanda yake rawar Dari dan rigar jikinsa bata da nauyi haka nan kansa babu hula ga dare ya tsala dan haka gari yayi sanyi qarara. Yakubun na goye da Jakarsa medan girma kana kallonsa ko baa fada maka ba zaka san yasha wuyar tafiyar da yayiwo ya wuce ciki Audu yabi bayansa zuciyarsa na bugawa abinda ya fara zuwar masa Yakubun ya samu matsala da karatunsa ne. Yana so ya tambayeshi daga ina haka cikin dare ba kuma ya so hayaniyarsu ta tayar da Dada ko Goggo Fadi ta samu abin sharri dan haka yabi Yakubun daya doshi dakin Dada kai tsaya ya tura qofar ya shiga Audu yabi bayansa.
Tana kwance tana bacci hankalinta kwance ya kai hannu ze tayar da ita Audu ya riqeshi yana cewa
"Haba dai ya zaka tayar da ita tana bacci"
"Na kasa nutsuwa saboda ita na baro Ikko babu shiri me ya samu Dada kullum cikin tunaninta nak abin kuma har ya zarce misali?" Yakubun ya fada yana duban Audu, Audu yayi waje yana cewa
"Babu abinda ya sameta kaje ka kwanta kaga dare yayi da safe se muyi magana" suka wuce, seda yayita kwankwasa qofar barinsu kafin Balaraba ta taso a dan rikice da alama tana baccin itama bugun ya riske ta, ganin Yakubu ne kuma se fuskarta ta washe da murna suka shiga suka maido qofa se sannan Audu ya shiga dakinsu zuciyarsa fal da wasi wasin abinda ya taso Yakubun haka koda yake ya sani shidin me qulafucin uwa ne ta yuwu rashin lafiyar Dadan ce ta taba shi har ya kasa zama ya taho ya ganta haka ya ringa juyi a gado sedai sam bacci ya qauracewa idonsa dan haka ya tashi ya dauro Alwala ya shiga Nafila Bara'atu dai tayi daidai abinta a gado dan cikin nata irin me baccin nan ne da se a iya sace mutum sedai ya farka ya ganshi a wata Nahiyar.
Asubar Fari kururuwar Baballiya ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 32