munafunci, abinda ya kaso mata aure kenan kuma ya korota daga qauyensu saboda an mata tambari duk wata Masifa data taso tsakanin kishiya da kishiya a garin In sha Allahu se kaji sunan Barira a ciki ita ta qullota kuma lafiya lau take zaune da nata Mijin tsabar yanda kawa qara da zuwa shari'a gaban me gari akanta yaqi qarewa yasa ya sallameta shine wata qawarta da ta fito Aikatau Birni ta janyota itama suka taho a gidansu Turai waccen take aiki dan haka da sukazo ita kuma tata me aikin sannan ta tafi gida se Mamarsu tace ta dauki Bariran dukda bata so ba dan bata son me aiki babba kodan irin Mazansu ido a mata amma ganin ta iya aiki kuma dai ta ganta kalar gidadawa kamar ba zata yarda da irin wannan abin ba yasa ta karbeta kuma se take jin dadin zama da ita dan Barira badai ladabi da duk cikin iya takunta.
Bi ta da Turai suka shiru sunasauraronta ita kuma ganin sun bata hankali yasa taci gaba da cewa
"Ina itace naji kunce tsohuwar kilaki?" Turai ta gyada kai alamar haka ne, Barira ta gyara zama tana buga cinya tace
"Yo Allah na tuba kwace goruba a hannun kuturu ai shiyafi komai sauqi, ai kamar yanda Hajiya tace miki ki koma gefe kihya kallo to haka zakiyi amma kafin nan se kin basa bam din da ze tayar da kowa, abu daya zafi fada da ze maida Alhaji hayyacinsa in ma cikinsa ne in ma ba nasa bane kawai kice masa kin gano da cikin ta shigo, zuwa sukayi aka kwantar dashi se yanzu da suke ganin ta dan kwana biyu aka tashe shi kina fada masa hala kija gefe kiyi zamanki kawai ki saka ido, in cikinsa nema zaki gane idan ma na wani ne kin haska masa hanya duk ma yanda akayi ze binciko"
"Amma Barira kanki yana kawo haske, to tsaya dagaske ana kwantar da cikin kar kuma mu fadi abinda ba haka ba" Turai ta fada tana jinjina tunani irin na Barira.
Barirar ta sake washe baki tace
"Kai Hajiya yo wannan har wani abun mamakine ko a nan cikin Binni ai anayi. Mu a karkarar mu kihiya tanawa kihiyarta asiri a kwantar mata da ciki se kiga Mace ta hekara goma da ciki ayita cewa Aljanune nan ba asan Asiri aka mata ya kwanta ba in ta dage da neman magani se kiga ya tahi an haife dan to haka idan Yara suka dakko abin kunya hima zuwa ake a kwantar hi se an kwana biyu a daki lissafi yayi daidai se tayar dahi kiga yarinya ta haihu qalau babu me cewa komai"
"To amma ai ita watanta takwas yanzu fa" Binta ta fada bayan data gama hada lissafi akanta. Barira ta sake sheqewa da dariya irinta shegun qauye tace
"Kai Hajiya yane muke ta maimaita magana amma kamar baku ganewa. Dama ai kintatar lokaci akeyi se a daga cikin kinga in ta haihu nan da sati ko biyu ne ai babu me cewa komai tunda ta shiga wata na tara a daki to amma idan kika bullo da wannan maganar ko shekara tayi kanta haihu kin saka kokwanto a zukatan jama'a musamman da daman tana da tambari sannan shi kansa me gidan kinga lissafin da yakeyi na cikin ai be kai asalin watannin qiyasin girmansa ba ko?"
Page 21
Rai fes Binta ta koma gidase da tayiwa Barira kautar Naira Dari biyu tukuici. Ita kadai ta ringa sakin murmushi a hanya harta koma gida nan ta tarar da Lantana rabe qofar daki tana jiranta.
"Ai nazo tuntuni ashe kin fita, Mairo ma tazo ta tafi kin santa ita ba zata iya jira ba" Lantanar ta fada bayan data karni muqullin daki ta bude mata.
Binta ta shiga tana cewa
"Eh ai ita da yake ta fiki tunani tana kuma da abinyi a gida shiyasa ba zata zauna ba tunda babu aikin da zatayi"
"Kai Hajiya" Lantanar ta fada tana yaqe dan taji zafin maganar Bintan kullum haka take yaba mata su da tana da zuciya yaci ace yanzu ta haqura da aiki a gidan gaba daya.
Binta ta shimfide Zakariyya tana miqa tareda wash
"Ai yaci ki dena goyashi haka Hajiya kar ku ringa danne na cikin, in fita ta kama ki ringa cewa na turo miki Aisha ta mana tana tayaki da daukarsa" Lantana da bata daddara ba ta sake fada, se kuma akaci sa'a Bintan ta yarda da shawarar tace zata ringa yin hakan. Tana zaune a Falo tana ayyana yanda maganar nan zata tashi Lantana na share share sega Audu kamar an jefoshi ya fado falon, ta miqe da sauri tana tambayarsa lafiya kuwa yace
"Babu lafiya, yanzu Suleiman ya dawo daga Bechi yake shaidamun Allah yayiwa Babansu Bara'atu Rasuwa, ki shirya yanzu zamu tafi can dukda dai nasan ba zamu samu jana'iza ba amma gara muje din in yaso ma dawo gobe".
Binta taja tsaki bayan data koma ta zauna tana cewa
"Shine ka shigo a gigice har kana fadar mun da gaba na zata ma qata asarar ce ta fadawa Dukiyarmu? To Allah ya jiqan musulmi amma babu inda zani da ranar nan fatsar fatsar".
Zubaida na bacci bacci ya shiga itama ya shaida mata rasuwar, iyakar abinda ta sani kan Bara'atu tsohuwar matarsa ce ba'a fi watanni biyu bama data san itace uwargidansa ba Binta ba a bakin Mairo mewa Binta Girki ranar ta roqeta ta koya mata yanda akeyin Gero da wake shine tace ai Maman Baba ma tana son Abincin a sannan ta tambayeta wacece ita tace mata Bara'atu uwargidan Audun tayi mamaki kwarai jin har yara biyu ne tsakaninsu dan be taba gaya mata ba data yi masa zancen kuma har yajin kwanaki ya mata saboda tace be kyauta ba dakyar suka shirya bayan yaja mata kashedin babu ruwanta da sabgarsa wadda bata shafeta ba, bata san meya rabashi da Bara'atu ba dan haka karta kuskura ta tsoma kanta a ciki shiyasa kidimewar da yayi yanzun da ya gaya mata rasuwar Baban Bara'atun ta bata mamaki, matar daya cire daga rayuwarsa ita da Yayan da suka haifa tare na menene ze dawo dan ta rasa mahaifi?
Haka ta cicciba ta hada abinda zata buqata a yar jaka tana hasaso yanda yan Bechin zasu karbe ta wannan karon, bata sake zuwa ba tun bayan da aka kaita wancan Al'amarin ya faru haka suma A matan Aisha ce kadai tazo babu dadewa tana ciwon Nono Audu yace tazo Kano taga Likita ta kwana hudu a dakin Zubaidan kuma dai lafiya lau babu abinda ya hadasu har suka rabu ta koma.
Bata san banda Binta za'ajwe ba seda yaceta fito su tafi, ta kulle qofarta tana tsaye jikin dakin Tsakar gida wanda Abdullahi yake kwana ciki kafin a kaishi makarantar kwana tun daga nan kuma idan anyi hutu Bechi yake tafiya da Audu ya tambayi ba'asi yace babu komai be matsa ba ya qyale shi kuma dai be fasa yi masa komai ba tamkar yana gidansa ze aikawa da Aminu kudin komai nasa ayi masa.
"Ba tare da Maman Zakariyya zamuje ba?" Ta tambayeshi jin yace suje,
"Badani za'aba uwar azagwai" Binta dake tsaye kan Baranderta ta turo dauri gaba irin wanda Zubaidan takeyi ta fada kome ta tuna kuma se tayi saurin sakin fuska ta matso kusada ita tana cewa
"Yauwa kar in manta, idan kun dawo daga Qauyen nan akwai taimakon da zakimun. Wlh in gaya miki qanwar qawatace Ibtila'i ya hauta wani shege ya dirka mata ciki, to kuma ta samu Miji Aure nan da wata biyu wannan abu ya faru shine nace ko zaki taimaka ki kaimu inda kuke zuwa a kwantar muku da ciki a samu asiri ya rufu ayi Auran nan idan yaso intayi wata kamar biyar a tayar dashi ko kinga sahu a likafa babu me cewa wani abu".
Sak Zubaidan tayi tana kallonta har ta kai qarshe yanda take doka murmushi kadai ya isa yasa ka gane babu Allah a ranta makirci ne zallah ta hado, waiwayawa tayi ta kalli inda Audu yake tana fatan ace ya rigada ya fita beji wannan maganar da Bintan takeyi ba amma se taga yana tsaye ya zuba mata ido tamkar yanda Bintan take kallonta tana murmushi.
"Kinyi shiru baki ce komai ba" Bi ta ta sake fada har tana dafata fuska dauke da murmushin makirci se ta saka hannu ta tureta tana cewa
"Bani da lokacin Amsa shirmenki"
Binta tayi shewa harda rangada guda tace
"Allah nawa Annabi na uwata, yarinya ba kecw bakida lokacin amsani ba nice bani da lokacinki, kuma shirme da kikace a tsakaninmu za'a tantance wadda take shirme kwanannan, kiyiwa Bara'atu gaisuwa injini kinji Allah ya jiqan Babanta" daga haka ta juya tana kada Mazaune tana waqa abinta.
Zubaida na tsaye inda take ta kasa motsi har seda Audu yayi mata magana kafin ta shiga daga qafa dakyar har suka fita. Seda suka dauki hanya sosai motar shiru babu me cewa qala kafin ya yanke shirun ta hanyar yi mata maganar data saka qirjinta bugawa dam kamar ze fashe.
"Sanda kikace kin zubar da ciki dagaske kike ya fita ko kuwa qaryarku ta yan bariki kikayimun?"
A razane ta kalleshi, hankalinsa na kan titi fuskar nan a hade tam kamar ta shanu. Shiru tayi zuciyarta na tsinkewa, takalarta yakeyi da masifa ita kuma bata shiryawa hakan ba bata da kalaman da zata kare kanta dasu a yanzu ta tabbatar matarsa ta rigada tayi masa famfo shiyasa ta tayar da wannan maganar a gabansa qila kuma ta rigada ta fada masa abinda take so ta fada wannan da tayi fami ne ta barbadawa ciwo gishiri.
"Ba magana nake miki ba kin mayar dani dan iska kinyi shiru" ya fada cikin masifa harda buga sitiyari, Zubaidan ta zabura saboda tsawar ta shigeta amma a maimakon tayi magana se kawai ta fashe da kuka. To me zata ce masa dan Allah?
Kwafa yayi be sake ce mata komai ba har suka isa Bechi, sun tarar da Anyi Jana'izar Babansu Bara'atu, a qofar gidan suka tsaya daman ya fice ya barta a motar ya tafi gurin Maza masu karbar gaisuwa Tilas ta fita ta shige qofar dataga Mata na shige da fice. Bata san kowa ba dan haka ta tsaya tana raba ido,
"Ashe tare kuke" taji an fada daga bayanta ta waiwaya ganin Aisha yasa ta saki ajiyar zuciya a qalla taga wanda ta sani.
"Muje ciki" ta sake fada mata se tabi bayanta suka ratsa matan dake zaune ta gaishe su tareda yi musu ta'aziyya kafin suka dangana da Rumfar Inna Hajara.
Anan taga Bara'atun tana rakube gefe ta sake zama fiyat da ita ga tashin hankalin mutuwar data riskesu ta farat daya idan ka ganta gwanin tausayi. Aisha ce ta gabatarwa da Bara'atu da ita. a matsayin Amaryar Audu, suka sake gaisawa kafin Aishar tace su koma tsakar gida dan yafi iska. Bayan su. Zauna Bara'atu da kanta ta fito ta kai mata ruwa da Kunun Tsamiyar da aka kawo na sadaka tace
"Ki dan sha wannan kafin a sauke abinci"
"Nagode" Zubaidan ta fada a sanyaye badan zata iya sha ko cin wani abu ba dan jiki da zuciyarta gaba daya batajin dadin da zata iya saka wani abu a bakinta a halin yanzu. Sunyi jugum jugum Aisha tace
"Itace matar Yaya Audu ta farko, Makircin Binta ne ya fitar da ita daga gidan ta qulla mata sharrin wai ta kashe mata Jariri ranar suna"
Qirji Zubaidan ta dafe tana zare idanu, tuna a inda suke yasa ta saisaita kanta cikin kaduwa tace
"Kashe jariri?"
"Wlh fa, kuma sharri tayi mata dan wlh ko kiyashi Bara'atu ba zata kashe da gangan ba balle mutum sahun barawo ta taka yaron dama ya rasu shikenan suka liqa mata sharri daga shiga dakin shi kuma Yaya Audu babu binciken komai ya yanke hukunci dalilin mutuwar Auranta kenan shekara Uku yanzu".
"Uhm" kawai Zubaida ta iya cewa, wato ashe nata tuggun da take shirin qulla mata me sauqi ne akan na Bara'atun kisan kai fa kuma na rashin Imani ace Jariri ka kashe wannan ai tayi mata tambarin da ba kowanne Namiji ne ze iya dauke kai ya aureta ba wadda ta iya kashe dan Jinjiri babu tausayi ai kisan babban mutum qaramin abu ze zama a gurinta.
Haka ta ringa jimanta maganar jikinta ya qarayin sanyi qalau da Al'amarin gida Audu, taga Babangida da Babannan sun girma Masha Allah musamman da suna da garin jiki irin na gidansu se suka tashi kamar yan biyu sedai duk su biyun suna nan a hargitse yaran qauye dai sak to uwarsu bata da nutsuwar zuciya balle ta iya samun damar kulawa dasu yanda ya kamata, Manema uku ta samu bayan rabuwarta da Audu biyu duk ba yan garin su bane amma da sunyi zuwa daya biyu za'a samu wani annamimin da zeje ya soke maganar sedai taji shiru ba zata sake jin duriyarsu ba wannan abin yasa ta shiga damuwa matuqa ga tunanin Audu da soyayyarsa data qi barin zuciyarta sedai ta sani ya mata nisa bama ta yiwa kanta fatan komawa gidansa Addu'arta daya ce a kullum ubangiji ya warware mugun qullin da Binta tayi mata ya wanketa a idon Audu da duk wanda ya yarda da sharrin da aka mata.
Se Yamma Aisha da Zubaida suka bar gidan rasuwarz babu motar Audu a waje hakan ya tabbatar musu ya wuce gida dan haka ta rakata can kafin ta wuce gidanta itama dan Magriba ta kawo kai.
"Kace badan wannan rasuwar ba qila da sedai kuzo kawo mana Jariri ko Jinjira" Goggo Fadi ta fada sanda Zubaidan ta shiga dakinta gaisheta ta tarar da Audu a ciki. Bece komai ba itama bata amsa ba se kanta data qara yin qasa dashi.
"Ya kamata ka ringa qoqartawa Iyalanka suna zuwa gida akai akai cikin dangi, kaga dai Amarya rabonmu da ita tun randa aka kawota kuma kai kana zuwa koda ba ka kwana yaci karinga tahowa dasu a haka za'a saba sosai ai" Goggo Fadin ta sake fada se sannan Audun yace
"Za'a gyara in sha Allah, bari naje an fara kiran sallah" ya miqe ya fita Zubaidan ma fita tayi ta dauro Alwala tayi sallah nan dakin Goggo Fadi Saude ta kawo mata tuwo bayan ta sauke ta dan tsakura saboda yunwa ta fara sakadarta tana nan zaune Goggo Fadi na janta da hirarraki duk a takure take ta gaji tana so ta kwanta amma bata san inane masaukinta ba bataga kayanta a dakin Goggo Fadi ba balle tace a nan zata kwana shi kuma tunda ya fita be dawo ba balle ta tambayeshi.
Be shigo gidan ba se da goma ta gota lokacin ta gaji ta kwanta a dan gadon Goggo Fadi da take tayi mata tayin tun da taga tana gyangyadi daga zaune amma taqi hawa tana kwanciya kuwa bacci ya kwasheta se ji tayi yana tashinta sukayiwa Goggo Fadin sallama tana biye dashi har bangaren dake gefe wanda aka kaita randa sukazo Bechi tana Amarya. Daki daya ya bude ya shiga tabi bayansa, dakin da aka sauketa ne wancan lokacin se yanzu ta kalleshi da kyau cikin dakin ba zakace a qauye kake ba tamkar Dakunansu na Kano Bango yasha Fenti haka qasan dakin Malale da Kafet ga bandaki a ciki har wayarin din ruwa da akwai.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Fita yayi ya barta a dakin, ta shiga bandaki tayi uzurin da zatayi ta fito ta bude jakarta data gani ta canza kaya kafin tabi Lafiyar Katifa bata sake motsawa seda aka fara kiraye kirayen sallah ta farka ta ganta ita kadai Babu Audu a dakin yanayin gurin kwanciya kuma ya tabbatar mata da ita kadai ta kwana kan katifar dan babu shaidar an kwanta daya barin to Ina ya kwana? Data tuna da wani dakin a gurin seta bar zancen a ranta tana jinjina wato lamarin yayi tsamarin da baze kwana daki daya da ita ba kenan ai shikenan. Tayi wanka bayan da tayi sallah ta shirya tsaf abinta be shigo ba seda gari yayi haske lokacin har Saude ta kai mata abin Kari Ruwan shayi a fulas se wainar kwai da qaton Burodi ta fita kawo mata Madara da Bonbita ya shiga dakin yana wani cin magani ta gaishe shi ya amsa a daqile yana gaya mata tayi sauri da wuri zasu tafi.
Haka suka kamo hanya bayan sun biya gidan Rasuqar sun sake musu gaisuwa, tana zaune cikin mota tana leqensa suna tsaye da Bara'atu daya saka aka masa magana da ita, bata san me suke cewa ba hankalinta yafi tafiya ga Yaran da suka zagaye shi amma daga nesa kowanne ya tsaya irin suna son zuwa gunsa amma babu shaquwa ko fuskar yin hakan se taji wani iri a ranta, to su kenan ma da aka rabasu da ubansu ta qarfi da yaji inaga ita da Ake shirin sheganta abinda zata haifa ta yanda ma baze samu ko Alfarmar kiran kansa jininsa ba?
Kwalla ta ziraro mata tayi saurin dauketa ganin ya nufo motar, taga sanda ya bawa Bara'atun Kudade masu kauri amma ta girgiza kai taqi karba kana taja yaranta suka shige cikin gida da alama wannan abun ya sake tunzurashi dan motar kanta fizgarta yake kamar zasu tashi sama ita dai ta qanqame jikinta har sukaje gida babu wanda yacewa dan uwansa qala.
AUDU
Tunda suka baro Kano abin duniya ya taru yayi masa yawa haka nan maganganun Binta suka samu matsuguni a zuciyarsa dukda ba kaitsaue tayi magana dashi ba amma se ya ringajin kamar saqo ta bashi, girman Cikin Zubaidan ya jefashi a kokwanton da sam be taba shiga ba se yanzu da Binta ta soko wannan maganar sannan tambayar da yayi mata akan Cikin datace masa ta zubar a baya da shirun datayi ya sake jefashi cikin rudani wannan tasa bayan sun Isa Bechi yabkasa zama har seda ya nemi qarin bayani akan Kwantar da ciki da tayarwa da yaji a zancen Binta.
"Falalu ya fara tara da zancen a gurin zaman makoki da suka hadu a maimakon ya bashi amsa se kawai yayi dariya yace me ya hadashi da shirmen Mata a bakinsu yake jin wani Kwantaccen ciki amma shi be yarda da akwai shi ba. Shaidan ya rigada ya samu abinda yake so yayi kane kane a zuciyarsa haka nan ya jefa masa wasi wasi kala kala, sam ya kasa nutsuwa shiyasa daya fita salkar Magriba kai tsaye ya wuce gidan Bilki dukda ba shiri suke a yanzu ba tun bayan abubuwan da suka faru amma da yake buqatarsa ce yau ta tashi se gashi a gidanta. Tasna Yazo Bechi dan tun rana Labari ya isar mata ta bar gidan raauwar babu dadewa su kuma suka shigo daman kuma Audu na shiga Bechi labari ze karade ko ina kafin Alkhairin kyautar sa ya isa gida gida wannan lazim duk zuwa zeyi rabon abinda ya samu wa jama'ar gari musamman a baya zamanin da suke tare da Bara'atu sunfi zuwa garin sosai yanzun yakan jima beje ba amma duk in ya shiga dai zeyi Alkhaiti daidai yanda hali ya bayar.
A dakin Bilki ya zauna ya rafka tagumi yana sauraronta bayan da yayi mata tambaya akan gaskiyar ana iya kwantar da ciki tsayin wani lokaci sannan a tayar dashi sanda ake so?
"To zancen gaskiya anayi dukda dai ban tabayi ba kuma ban taba ganin wadda taje akayi mata ba amma na samu labarin mutane da yawa da hakan ta faru dasu, kaga babu nisa nan gidan Malam Ado ai kasan Ila Abokin Baballiya ta shima ba'a jima ba anyi irin wannan dambaruwar gidansa yayi Aure matar watanta shida ta haihu. Yar Umarawa ce ya aurota daman dai tun lokacin bikin aketa surutai akan yarinyar kamar magana ta dakko shine iyayenta suka tada auranta babu shiri, hatta dakin da ya sakata fa ubanta ne ya bashi kudi ya qarasa ginashi saboda yace be shirya Aure ba basu karbi Lefe ba kuma karka so kaga uban kayan garar da aka hadota dashi bana tsammacin sun qare har yanzu.
To a yanda Zainabu dai take cemun (kishiyarta) kasan Qanwarsa ce yayan Maza suke wai Amaryar watanta biyar sega Ciki ya fito qato kamar zata haihu gobe, kuma sunce sudai lokaci daya sukaga wannan abun mamaki da fara laulayinta da girman cikin befi watanni ba tofa ciki nayin qato daman akwai qanwarta da aka hadota da ita ta shirya ta tafi can garinsu satinta daya sega Babarta tazo ganinta wai ya akayi ya akayi ta tattarata suka tafi gida wai bata da lafiya za'a nema mata magani ba'a rufa wata ba akace ta haihu, su Zainabu sunje sun gano yar ance musu bakwaini ce to tace Aradun Allah wannan ya idan ka kalli idonta ma zakace ta shekara a ciki kuma qatuwa da ita tabarakallah in taqaita maka zance dai anyi wata uku da haihuwar yanzu Auran yake da wata tara tana can gidansu har yanzu bata dawo ba".
Wannan labari na Bilki ya sake bashi tabbacin maganar da Binta ta fada ana haka kenan, amma wace hujja ze kama ta cewar Zubaida ta shigo gidansa da ciki? Sannan wane tabbaci yake dashi akan kwantar da ciki tayi ta shigo masa dashi gida? Dole ya tsananta bincike ya gano koma menene amma yanda al'amarin ya kasance lokaci daya ciki yayita girma kamar na Aljanu ya bashi mamaki shi kansa. Be gayawa Bilki dalilin tambayar ba duk nacin data yi masa ya tattara ya tafi amma ya kasa komaqa cikin gidan can wani guri ya samu ya zauna yana ta lissafin ya zeyi idan ta tabbata da ciki Zubaida ta shigo masa ba nasa bane ba?
Seda yaga dare ya farayi ya koma gidan ya rigada ya cusawa ransa wani abu na daban shi yasa ya kasa koda kwana daki daya da ita ya bude dakin da Binta take sauka ya kwana a ciki. Har mamakin kansa ya ringayi yanda ko sau daya be taba tunano rayuwarta ta baya yaji ya qyamaceta ba ko ya kasa mu'amalantarta amma yanzu yaji ta fita a ransa akan abinda be gama tabbatarwa ba. Haka suka dawo Kano nan kuma zamansu ya dauki sabon zama ya fita a sabgarta tsakaninsa da ita ya ajiye mata kudin cefane idan ya kwana a dakinta kenan in tayi abinci bayaci gaba daya ya birkice saboda rashin nutsuwa daya sakawa ransa.
A bangaren Zubaida kuwa gaba daya ta maida hankalinta gurin Ibada ne da kuma kula da lafiyarta data abinda yake cikinta tayi matuqar qoqari gurin ganinbata bari damuwar Audu tayi tasiri a ranta ba haka duk iskancin da Binta zata mata bata daga kai ta kalleta yanda kuma be sake mata tambayar da yayi mata randa sukaje Bechi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 32