da Baballiya ne kadai basa gurin se Hashimu da yace bashida lokacin saurar Soki burutsunsa ba kuma ze yarda dan da aka haifa a gabansa saboda yayi kudi ya zauna yana masa fadanci ba dan haka babu shi akayi zaman
Dukkaninsu sunyi matuqar farin ciki da Al'amarin kamar yanda ya tsammata ya san kuma Yakubu se yafi kowa jin dadin maganar har ya qagu yaga farin cikin da zeyi, ya bawa Yaya Baba kudaden daya ware matsayin na sadaki sannan ya sake ware wasu akan a bata tayi shirue shiryen da zatayi.
"Aa, wannan ai kai ya kamata ka bata hannu da hannu bamu ba" Yaya Baban ya fada masa amma ya dage akan su hada duka su kai saboda ya shiryawa ransa bazasu hadu ba harse an maida Auransu tukunna saboda gani yake zama ta rainashi idan yaje gurinta yanzu, amma idan yayi haka se abin yayi kamar yan uwansa ne ma suka tursasa dawowartata karma ta gane zumudinsa tazo tace zata rama abinda ya mata.
Dasu ka kai kudi kuwa ba'a tashi daga gun ba Mala Sadi yace a shafa fatiha kawai tunda ba sabon Aure bane, a karo na biyu Audu ya sake qullo Aure Binta bata sani ba se bayan daya koma ya fada mata maganar cikin Yaren da ya ke so ta fahimta a sannan cewar "Su Babangida zasu dawo nan da sati biyu".
Ta nuna jin dadi da murnarta a fili a zuciyarta kuwa dariyar mugunta takeyi tana shirya yanda zata kwarzabi rayuwarsu a ruwan sanyi kuma ba zata sake bari su koma Bechi ba balle Bara'atu taci Arziqinsa ta silarsu.
"Se a gyara musu dakin nan na tsakar gida ko, amma harda Abdullahi zasu dawo dukda dai ya nuna mun ni ba uwarsa bace tunda Bara'atu ta bar gidan nan ko hutu ne sake zuwar mana ba" Bintan ta fadi cikin kissa, Audu yayi murmushi yace
"Hardashi duk zasu dawo shi za'a gyara masa dakin tsakar gidan dai tunda yanzu ya zama saurayi su kuma su zauna dakin Mamarsu".
Bata kawo komai ba haka bata tambayeshi dawa zasu zauna ba to ina ruwanta?
Su zauna dakin su kadai ita bataqi ma wuta ta tashi cikin dare su qone ba kowa ya huta da lissafinsu.
Haka aka fara shirye shiryen gyaran tsohon dakin Bara'atu inda kuma Zubaida ta zauna, duk a salon kissa da kisisinar data qaro kwas yasa tayi shiru tana gani ana kankare kankare da liqe liqe har qofofi aka irin wanda aka canza na dakunanta da saman Audun babu jimawa sababbin shigowa na zamani se tayi tsammin ya canza ne saboda gidan duk yayi kala daya. Aka sake fente tsajar gida, ana ya saura kwana uku Bara'atu ta tare su Bilki da wasu yan uwan Bara'atu uku harda Hadiza qanwarta suka zo mata danki na neman magana.
Tarkacen kayan jere kadai suka taho dasu dan Audu ya fada musu ze saka mata Gado da Kujeru, Binta na daki tana baccin bayan Azahar suka iso Lantana da Mairo su na tsakar gida, Mairo na kai kawo tsakanin Kitchen da bakin famfo ita kuma Lantana tana daga jikin katanga inda Inuwa ta sauka tana zaro zance wanda duk gulma da tsegumin matan unguwa ne takeyiwa Mairon ita kuwa tafi ki mutu bata ce mata amma hakan be saka tayi shiru ba se zuba takeyi.
"Barka barka, baqi mukayi a gidan? Daga ina?" Lantana ta fada tana miqewa sanda su Bara'atu suka shigo da ubannin buhubhuna da suka lodo su kwalla da Samiru. Mairo ma tayi musu sannu da zuwa, ta gane Hadiza a zaman da tayi a gida dukda ta dan qara jiki amma kamanninta basu bace mata ba sannan kuma ga kamannin me gidan a fuskar Bilki hakan ya ankarar da ita cewar daga Bechi suke.
"Bismilla ku shiga tana ciki Hajiyar" ta fada musu bayan data gaidasu a mutunce, kafin suyi magana Lantana tayi tsugul tace
"Ban gane su shiga ba? Ke haka akeyi kawai daga ganin mutane kice su shigar mata daki kina ganinsu yarkace yarkace da wasu uban buhunhuna kamar yan gudun Hijira qilama mabarata masu neman mafaka ko kinga sun miki kalar qawayen Hajiya balle kice su shiga daki kai tsaye?"
"Hayaniyar me akeyi ne haka? Lantana keda su waye?" Binta da subadadin lantana ya farkar da ita ta fada tana leqowa ta tagar uwar dakanta dake cikin tsakar gidan. Tayi sak ganin Bilki wadda suna hada ido ta tamke fuska tam.
"Kune tafe cikin ranar nan? Sannunku da zuwa aiko be sanar mun kuna tafe ba ku shigo" ta fada iyakar dauriyarta a qoqarinta na janyo su a jiki da kirki kamar yanda Turai ta bata shawara Bilki kadai ta sani cikinsu ko kuma ta gane tunda tasan Hadiza sedai sanin babu abinda ze kawota gidan yasa bata ma kawo a ranta ta santa ba. Dankwalinta ta shiga nema dan ta fito falo ta jiyo Bilki na cewa
"Da yake zuwan namu ba naki bane shi yasa be gaya miki ba, bari mu shiga can mun gode da tayi" daga haka suka ja kayansu zuwa dakin Bara'atun. Bi ta tabi bayansu da harara tareda sakin tsaki kafin ta daure kanta ta fito ranta na suya. Tsabar isa da samun guri ne yasa zasu kwaso jiki rabe rabe suzo mata gida kuma be gaya mata ba ko kuwa shima besan zasu zo ba sannan wadannan uban kwanukan da suke tafe dasu na menene ko daga Kasuwa suke? Take tambayar kanta harta fito tsakar gidan Lantana na tsaye guiwa tayi sanyi saboda yanda taji Hajiyar ta musu magana ya nuna mata sudin ba banza bane kamar yanda ta tsammata.
"Ashe baqinki ne Hajiya" ta fada tana sosa kai, Binta ta wuceta tana cewa
"Qannen megidan ne"
Seko ta dafe qirji ta zare ido, amma data tuna suda banza a gun Binta duk daya se ta dan saki ranta sedai mamaki ya kamata da har Binta tayi musu tayin shiga dakinta, to shiri suka fara haka ko kuwa duk cikin wasan kwaiwayon data fara ne?
Binta kitchen din tsakar gidan ta shiga ta tarar da Mairo na kwashe Shinkafar data gama dafawa Miyar na kan wuta tana idasa soyuwa.
"Idan kin gama akai musu abinci kafin nan a hada ruwa da lemo idan da Alkaki ki hada musu" ta bata unarni ita kuma ta amsa da
"Toh Hajiya".
Dakin da suka shigan ta wuce, sun shimfida tabarma cikin kayan da sukazo dasu Mata biyu na zaune Bilki na tsaye taba duban dakin daya qara kyau dalilin sabon fenti da qofofi harda Abun sak kwan lantarki duk aka canza se gurin ya qara haske da kyau.
Daga bakin qofar ta tsaya ta aika musu gaisuwa rai babu dadi kamar an mata dole suka amsa banda Bilki data shige daya daga cikin dakunan gurin, Binta tayi kyacci a ranta tana ayyana yanda zataci kan uwarta kafin ta kalli yar dattijuwar da ta fisu shekaru Qanwar Inna Hajara ce tace
"Bari a kawo musu ruwa, bamu san da zuwanku ba ai da an muku shiri me kyau"
"Ba komai yar nan hakan ma mungode" matar ta fada a ranta tana mamakin rashin kirkin Bintan da ake fada ita dai bata gani ba.
"Munafuka" Bilki ta fada bayan ta juya, matar da ake kira da Inna Habi tace
"Kai Bilkisu, niko banga abinda kuke fada akan matar nan ba. Yanzu wace macece zata tari dangin kishiya sunzo danki haka?"
Mairo ta aje Try data doro su ruwa da Lemo da kayan tabawa, seda ta zabura jin maganar Inna Habin ta kalli Bilki da tayi wata dariyar mugunta tace
"Karkiyi saurin yanke hukunci Inna ki dai jira kiga qarshen wasa dan in akayi wasa babu tabbacin ki fita da qafafunki daga cikin gidan nan muddin ta gano wacece ke".
Mairo ta hade yawu ta miqe tana gasgata zancen Bilkin tabbas Hajiya bata da wannan baqin Labarin, wato shi Alhaji baya gudun rigima ya ringa zuwa yana daura Aure matarsa bata sani ba dadi daya data ji da taga Alamar Bara'atu ce zata dawo dalilin ganin Hadiza.
A can daki kuwa Binta na zaune kan kujera ta harde qafa Lantana na daga qasa suna magana,
"Ku tabbatar da basu buqaci komai ba komai suke so a musu, so nakeyi idan sun koma dukda nasan waccen shegiyar ba zata taba fadar Alherina ba amma saura da yau suka fara zuwa dole dai suce na musu Kirki" Bintan ta fadawa Lantana ta miqe cikin rawar jiki tana cewa
"An gama Hajiya, kin san dama ni indai Ladabin Kule ne nan na fi kauri laka laka zanwa mutum kamar zan kwanta masa idan ina son abu".
Binta ta bita da kallo tana fassara maganarta a zuciyarta kafin taja tsaki a fili tace
"Kar nake kallonki ai karki dauka wawiyace ni kice zaki shammaceni".
Bajewa su Bilki sukayi suka kwashi Abinci abinsu, Hadiza ta tattaro kwanukan da suka gama dasu ta fito dasu waje gurin wanke wanke ta tarar da Lantana na wanke tukwanen da akayi abincin rana Mairo kuma na qoqarin dora na dare ta aje kwanukan hannunta tana musu sannu suka amsa Lantana ta qureta da ido tana si ta tuna inda ta santa bata tuno dinba Hadizan ta juya ciki. Haka taci gaba da wanke wanken tana ta qoqarin gano inda ta santa haka nan kuma ta tsaya mata a rai harta gama tana maida kwanuka ta kasa haqura ta cewa Mairo
"Nikam fuskar matar can batayi miki kalar sani ba?"
"Gaskiya Aa, ke kin santa ne?" Ta mayar mata da tambaya se ta tabe baki tace
"Oho nidai se na ga kamar nasan me kama da ita, qila kama ce to ko kuma a hidimar gidan nan muka taba haduwa da ita"
"Ta yuwu hakan" Mairo ta sake bata amaa tana cigaba da abinda yake gabanta.
Daga soro aka rafka sallama, muryar gardi ce Lantana da bata komai taja Gyalenta ta leqa taga Maza biyu da motar kayan katako a qofar gidan.
"Yauwa, kiyiwa Hajiyar magana kice ga kaya Alhaji yace a Kawo" wanda da alama shine Direba ya fada mata kafin ta bashi amsa Bilki da ta jiyo sallamar itama ta biyo sahu tana ganin kayan kuma ta gane nasu ne dan haka tace
"Ku sauke toh a shigo dasu, ga Almajirai nan su tayaku"
"Toh Hajiya" suka amsa mata kafin su fara kiciniyar kwance Belet din da suka zagaye kayan da ita.
Page 26
"Hajiya wasu Mazane da motar kayan katako, wannan me kama da Alhajin tace su shigo dasu gashi ana kaiwa wancan dakunan" Lantana ta sanarwa da Binta. Mamaki ya kama Bintan, kayan katako kuma na menene? Ta tambayi kanta, to kodai Bilkince zata dawo nan gidan da zama tunda ta samu Labarin a gida take auranta ya mutu? In ko haka ne da anyi tashin hankali da masifa kuwa, ita da gidanta bata san komai ba kawai taga ana shigo mata da kayan gado taqamar tana Qanwar Megida ko? To dashi da itan duk basu isa ba.
Fita tayi dan taji ba'asi, a tsakar gidan taci karo da Audu da batasan shigowarsa ba tana ganinsa tace
"Yawwa gara da kazo, ban fahimci zuwansu Bilki ba ga kuma wasu kaya da akw shigo dasu na menene?"
Fuska a sake ya dubeta bayan daya bawa Direban motar da suka kawo kaya kudi dan har sun gama saukewa yace
"Kayan su Babangida ne"
"Su Babangida? Su din ne aka siyawa kayan daki se kace na Amarya sababbin Gado da kujeru?" Ta tambayeshi fuskarta na nuna mamakin da take ciki.
Tafiya ya farayi zuwa dakin da su Bilkin keta kiciniyar hada kayan yana ce mata
"Amarya ce mana, ko bakya so a kwace miki kambunki?"
"Audu!" Ta kira sunansa a kausashe tana bin bayansa dan zuwa yanzu kanta ya fara qullewa bata fahimtar maganganunsa.
"Ina zuwa, bari mu gaisa dasu Goggo Ramma ki jirani a sama" ya bata amsa daga nan ya shige falon ya barta a tsaye tana saqa da warwara tana jiyoshi da Bilki yana ce mata
"Hajiya Bilki Tijjan Bechi"
"Kace na qulle jakata bana zan sauke farali" Bilkin ta mayar masa tana ajiye tsumman da take goge goge dashi, yayi murmushi yana tsugunnawa dan gaida Su Goggo Habi ya bata amsa da cewa
"Kusan haka, da dai layi za'abi se Yaya Mairo da Amina sunje sannanke amma yanzu kin san ance Albarkacin Kaza qadangare kansha ruwan kasko to kena Albarkacin qawarki bana zaku jera ku tafi tare in Allah ya yarda".
Bilki ta rangada gida wadda ta zama kamar saukar guduma a kwakwalwar Binta cikin karadi tace
"Nagode dan uwana Allah ya ida nufi, harna hangomu nida Bara'atu muna zagaye Ka'aba ya ubangiji ka nuna mun wannan rana" suka amsa matada Amin gaba daya.
A mutunce suka gaisa kafin ya fito ya ganta tsaye a gurin har sannan,
"To muje" ya fada mata se kuwa ta bishi kamar raqumi da akala zuwa saman nasa.
Zukudi tayi tana kallonsa tareda sauraron abinda yake cewa,
"Nasan ko a baya bakida matsala da ita, akasi aka samu akan abinda ya faru wanda da bakinki kika furta kin yafe har kika nemi dana dawo da ita kuma nayi matuqar jin dadin hakan, ina fatan zamanku ya canza salo a wannan karom dan zanja mata kunne sosai akan kar a kuma maimaita abinda ya faru a baya".
Murmushi yake yi irin rai fes din nan harya gama maganar, Binta data zama kamar wata hoto se idanu ke motsi suna yawo tsakanin fuskar Audun da bakinsa, so take ta lailayo Ashariya me maiqo sannan ta tambayeshi a gidan kut***r uban wa tace ya maido da Bara'atu sannan dawa yake zaton za'ayi zaman lafiya sedai bakinta ya mata nauyi, bata iya koda motsawa ba seda ya miqe yana mata sallama kan ze koma Kamfani, takun saukarsa daga matakala ne ya farkar da ita daga suman zaunen da tayi ta zabura ta miqe sedai kafin ta kai ga sauka harya fice daga gidan dan tana kaiwa soro taji qarar Motarsa ya bar qofar gidan.
Zaman dabaro tayi ta dora hannu biyu a kai ta zunduma ihu kamar wadda aka aikowa da mutuwar Mahaifinta su Lantana da Mairo suka zaburo dan ganin menene, a dakin Bara'atu ma goggonninta biyu sun niyyaci fita banda Hadiza da Bilki da suka san za'a rina Bilkin ce ta dakatar dasu tana dariya ta cewa Goggo Habi
"Kinga abinda nake gaya miki ko? To yanzu aka fara, Hadiza rufi mana qofar nan dan ba hankali ne da ita ba se ta fado mana be kuma kamata mu biye mata ba dan ko gaban shari'a akaje mu za'a bawa laifi saboda gidanta muka zo"
"Hakane" Hadizan ta fada tana tura qofar ta rufe kamar kuwa sun san nan ta nufo dan zabura tayi kamar zakanya ta durfafi dakin tana kuka tana koro ruwan Ashariya tamkar zararriya ta shiga jijjiqa qofar da niyyar cirera sedai ko Gezau.
"Wallahi tallahi na rantse da girman Allah in baku bude qofar nan ba sena babbake ku a ciki, sena nuna muku ki qananan yan iska ne, ni za'ayiwa haka?" Ta fada cikin qaraji tana cigaba da bubbuga qofa. Dattijai biyun suka tsure, Goggo Habi fadi take
"Me gado a bude qofar nan karta qona mu kinji abinda take cewa"
"Kyaleta Goggo duk kurarin banza ne baki ne da ita babu abinda zata iya a aikace wanda zeyi abu ai baya fada" Hadiza ta bata amsa, Bilki dai bata tanka ba se jera samiru takeyi abinta tana yan waqoqi tamkar ma bata jiyo hauka da Tijarar da Binta takeyi a tsakar gida.
Iyakar masifa, bala'i da duk kalar Ashar wata ma a Bakin Bintan goggonnin Bara'atu suka fara jinta yau seda kamar yanda Hadiza ta fada kurarin banza take dan data gaji da buga qofar gefe ta zube tana kuka kamar me tana maganganu da cin Alwashi kala kala. Mairo data ga abin bana qare bane ta koma kan aikinta ranta duk babu dadi da wannan al'amari, ita kuwa Lantana tana nan tsugunne daga gefenta tun bayan data samu tsarabar hambari a qoqarinta na riqeta ta gwabje mata fuska daga nan ta matsa gefe amma taqi tashi daga gurin se fadi take
"Kiyi haquri Hajiya, ki tashi mu koma can daki kisha ruwan sanyi"
"Se naci "gi***n du***in uwarki Lantana idan kika sake cewa nayi haquri, Allah ya tsinewa haqurin kema Allah ya tsine miki" ta fada dole Lantana taja baki ta kame tana sosa fuska dan inda ta mangaretan har sannan be dena mata zafi ba tsabagen neman gurin zama da iya gulma yasa take zaune a gurin har sannan.
Binta na kuka wiwi kamar Jifa se ga Turai ta shigo gidan ita da wata mata, tun daga qofar gida ake jiyo ihu da kururuwar Bintan dan haka cikin sauri suka shigo dan ganin me yake faruwa.
"Na shiga uku ni Amina, me ya faru? Waya mutu Binta?" Turai ta fada tana nufar qawar tata da ta ke nan zaune kamar kayan wanke ta miqe qafafu kanta ya tuje dan tun fara Tijarar tata dankwali ya cire. Qoqarin kamata ta shigayi danta miqe amma ta kasa saboda yanda ta saki jiki ita aba ba kadab ba ganin Turan kuma yasa ta sake sakin wani kukan me ban takaici kamar wata yarinyar goye tana fadin
"Na shiga uku Turai Audu ya kasheni, wai Bara'atu ya mayar be gaya mun ba"
"Har naji sanyi a raina ashe ba mutuwa akayi ba, dan Allah kama jikinki ki miqe, Zainab zoki tayani mu dagata" Turai ta fada jin abinda Binta tace. Dakuar da sidin goshi bayan sun hadu su uku harda Lantana suka kai Binta daki se sannan ma suka tuna da Yaron da suka baro a daki ya fado daga Kujerar data kwantar dashi yana ta tsala kuka gwanin Tausayi.
"Dauke shi Dan Allah kuje waje ki rarrashe shi" Turai ta fadawa Lantana, ta dauke Nazirun tayi waje dukda ba haka taso ba, so tayi taji komai dukda ta tsinci kan zancen amma zata so ayi komai a gabanta yanda zata fi jin dadin bata labari idan ta fita.
"Yanzu saboda Allah me kikayi haka? Akan wata baquyiyar Bara'atu shine kika kwanta tsakar gida gaban masu aikin ki kina tumami kamar wadda ta kwace daga Turu wani irin abin kunya ne wannan Binta?" Turai ta fada cikin fushi. Binta dake kuka tace
"Ki qyaleni, saboda ba'a taba miki kishiyar nan bane shiyasa duk abinda nayi kike daukarsa shirme ke kinsan zafin abin ne balle ki gane yanda nake ji?"
"Koma menene, kome kikeji be kai ki zauna kina zubarwa da kanki mutunchi ba a samu abin fada akanki, wannan haukan da kikayi wlh Allah yasan inda ze tsaya dan wannan munafukar me aikin naki kina kallonta kinsan nadar rahoto takeyi. Allah na tuba ba Bara'atu ba ko mata uku Audu yace ya daura aure dasu ya kai ki kwanta kina kuka akai balle Bara'atun da ko kashin jikinki ya fita a gurinki, har meye abin tashin hankali a matar da kika san idan kinga dama ko ruwa ba zaki barta tasha da dadi a cikin gidan nan ba.
Kika kara da Zubaida ma kika koreta balle Bara'atu karan kada miya? Dan Allah karki bada ni mana, a gaban Audun kikayi wannan haukar ai kuwa kin kashe kanki kin ruguza duk wani shirinki na baya da wanda ya kamata muyi a gaba wlh murus kin kashe kanko a gurinsa".
A hankali ta fara rage kukan da take tana kallon Turai alamar sonjin qarin bayani, ta yaya ta kashe kanta a gurin Audu ta ruguza shirinta ma baya dana yanzu?"
"Wai ma tukunna, ta ya akayi har ya maida ta baki sani ba?" Turai ta jefa mata tambayar, taja Dankwalinta da aka tsinto mata a Soro ta face majina kafin ta shiga bawa Turai Labarin yanda sukayi kan zancen maido da yara sa dalilinta nayin hakan har zuwa kan zuwansu Bilki da maganar da sukayi dashi dazun.
"Tirqasa, au yanzu suna cikin gidan nan kikayi wannan abin kunyar gaskiya Binta baki haduba kwakwata kin bada ni wlh sauqinta daya be ga wannan qaramin haukan naki ba dan wlh da ace yana nan kikayi shikenan kin gama yawo babu wata fankama da zaki sake yi masa ya yarda" Turan ta sake fada kafin ta muskuta tayi qasa da murya taci gaba da magana.
Se bayan sallar Isha'i su Turai suka bar gidan bayan sun tattauna batutuwa da yawa da Bintan tareda matar da suka zo tare, jan kunne tayi mata sosai akan abinda suka tattauna ta fito ta rakosu zuwa sannan zuciyarta ta danyi sanyi kadan. Ta kalli dakin Bara'atun ta ciji yatsa, ta ci Alwashin seta gwammace mutuwarta da dawowa gidan Audu, zaman da sukayi a baya sharar fage ne yanzu ne zata nuna mata Asalin ita din wacece ta shayar da ita ruwan azabar da ko kallon inda Audu yake aka ce ta yi ba zata yarda ba.
Tana tsaye tsajar gidan bayan ta rakosu Turai Bilki ta fito sukayi wa juna kallon tara saura ta wuce Abinta bakin famfo ta bar Binta da jan qwafa. Kaf setaci uwarsu wlh a sannu zatayi maganinsu. Se yanzu kam taga baiken kanta data kasa riqe kanta tayi shirmen dazu ai su Bilkin zasu qara rainata su tafi da ita a baki amma ta gode Allah da batayi a idon Audun ba. Tana hawa Barander yayi sallama, ji take kamar ta qunduma ashar a maimakon amsa masa amma ta dake iya dakiya ta amsa sedai bata iya ta tsaya ba balle ta juyi ta masa sannu da zuwa ta shige daki tana jiyo shi suna magana da Bilki kusan minti biyar kafin yabi bayanta.
"Uwargida ran gida ko Amarya zance?" Ya tsokaneta yana zama akan kujera tace
"Uhm" kawai tana cirewa Naziru Nafkin.
"Yau sarautar ta motsa kenan?" Ya sake sako mata wasa ta daure ba tareda ta kalleshi ba tace
"To kai ya ka gani?"
"Ras" ya fada kafin ya laluba Aljihunsa ya zaro wata Farar Embelop me dan girma ya miqa mata se sannan ta kalle shi ta saka hannu ta karba tana budewa, Awarwaro ne guda hudu a ciki na zinari, ta hadiye yawu Aljanunta na son abin duniya suka motsa.
"Tukuici ne, ko ince sadakin fadar kishiya ne" Audun ya fada.
Maganar Turai ta dazu ta fado mata da tace
"Ki kwantar da hankali kiyi masa laka laka irin yanda kikayi sanda kika shigo gidan, kina kallon dai wahalar da kikasha lokacin daya Auro Zubaida ta isheki ishara kisan tashin hankali ko masifa ba zata biyar da Audu ba sedai lallashi da kwantar da kai ta hakane zaki moreshi sannan ki samu biyan buqatarki to tabbas ta fara ganin gaskiyar hakan.
Dake taga abin duniya se gashi harda yi masa murmushi tace ta gode. Ta goye Naziru suka wuce dakinsa tare, ya shiga ciki ya watsa ruwa kafin ya fito ta shirya masa abinci a ranta tana lissafin abubuwan da zata nemi yayi mata yanzu da yake neman shiri da ita. Yana cin abinci yana mata zancen ai jibi Bara'atun zata tare kuma su Bilki zasu zauna nan harse tazo kafin su koma Bechi haka ta ringa daurewa tana yaqe duk a qoqarin ta na amfani da hudubar Turai na karta bari ta canza masa tunani akan wanda yake mata game da Bara'atu ta hakan ne zata sake korata a ruwan sanyi ba tareda ya zargeta ba.
Kwanaki ukun da su Bilki sukayi a cikin gidan sun zamar mata kwanaki mafiya baqi da muni a rayuwarta. Idan ta tuna wai Bara'atu ce zata dawo mata gida se taji kamar ta shaqe kanta ta mutu kawai ta huta da takaici, ranar da zata tare din kuwa tun farar safiya yana fita itama ta fice gidan Turai dan bata da sama da ita a Kano wuni guda suna qulle qullen sharri na yanda za'ayi bata komo gida ba se bayan sallar Magriba lokacin ta tabbatar da su Bilki sun tafi idan ma Bara'atun tazo da yan rakiya duk suma sun koma inda suka fito.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 32