kanta ya qone dan shi kansa Audun tunda yaga canjin fuskar Yayan nasa yasha jinin jikinsa domin yasan baze wuce dalilin ganin Bara'atu ba amma ta yaya zeyiwa Yakubu bayanin halin Bara'atu ya fahimat? Ita din Majicin sari ka noqe ce babu me fahimtar ainihin halinta se wanda ya zauna da ita. Suna gama tsakurar Abincin Yakubu yace ze tafi Balaraba ma ta miqe wannan ya qara tabbatarwa da Audu tabbas Yakubun ya fusata dashi ne.
A qofar gida Bara'atu data bi bayansu ta fashe da kuka, tuni Balaraba ta shige mota dan tace ba zata iya magana da Bara'atu ba zuciya tana iya dibanta ta watsa mata mari ko ta daddana mata Ashar haba wannan mutuwar zuciya har ina ta zauna Kishiya da Miji su nemi kasheta da ranta.
"Dan girman Allah Yaya Yakubu ka taimakeni kai kadai nake saka ran zaka fahimceni a yanzu, bazan iya yi maka bayanin halin da nake ciki ba amma ina roqonka da kayiwa Allah ka shiga lamarina ka nema mun yanci a gurin Dan uwanka wlh na gaji, ban zata cewar wahalar data fi ta bayace take kirana zuwa gidan nan ba, ban dauka ya maidoni bane saboda ya qara biyamun karatun da be kammala a baya ba, ni dai na haqura ina fatan wahalar dana sha ta zame mun kaffara a rayuwata" ta fada cikin matsanancin kuka daidai nan Audu ya qaraso Soron ya kalleta ya kalli Yakubun daya daga kai sama yana kokawa da bacin ran dake taso masa.
"Me kikeyi a nan gurin Dallah wuce ciki" Audu ya fada yana zare mata ido ta juya cikin gidan bayan data sake kallon Yakubu irin kallon ka taimaka mun.
"Na zata anan zakuyi sallar Isha in aka idar da Tarawi se na maida ku gidan" Audu ya fada cikin inda inda, Yakubu ya juya ze fita yana cewa
"Babu damuwa zamu koma gida kasan muna tare da gajiyar hanya, idan ka samu lokaci kazo ina son magana dakai" daga nan ya sa kai ya fice daga gidan.
Masifa da Bala'i Audu ya ringa zazzaga mata bayan daya koma cikin gidan akan seta gaya masa abinda ta fadawa Yakubu dayace yana neman sa amma tayi shiru banda kuka babu abinda takeyi daya gaji ya fita gaba daya ya rikice dan be san me Bara'atun ta fadawa Yakubu ba, maganarta ta qarshe kadai yaji da tace wahalar datasha ta zame mata Kaffara wace wahala? Amma dai ba a gidansa take nufi ba? Ya ringa tambayar kansa. Sallar ranar dai yayita ne kawai ana idarwa kuma ya tafi gidan Yakubu.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Audu ya ringa Jijjiga kai yana buga qafafu haka nan zufa take keto masa kamar wanda yake zaune kan Kunama, bakinsa har kumfa yake saboda masifa Yakubu ya zuba masa ido yana kallonsa kawai, shi yanzu tantama yake anya Audu bashida wata matsala akansa kuwa kodai shaye shaye yakeyi be sani ba. Tambayarsa yayi akan me yake faruwa tsakaninsa da Bara'atu ya ringa zana masa maganganu marasa lissafi bare kan gado, a duk abinda ya fada masa babu guri daya dayaji laifin illa tsantsar Zalunci da Azabtarwa da ita suke mata, ya mayar da ita tamkar Baiwar daya siyo da kudi a cikin gidansa shin wai me Bara'atu tayiwa Audu ne a rayuwa dayake daukar fansa akanta yanzu?
"To Audu kasan dai Aure anayinsa ne bisa yarjejeniyar Mutum biyu Mace da Namiji, haka nan idan har ya zama da cutarwa kowanne bangare yana iya neman sauqi ta hanyar rabuwa idan har babu wata hanyar samun daidaito bayan wannan din, ni Ina ganin tunda dai zaman ku ya zamana da cutarwa ku rabu hakan ze fi Alkhairi akan kuci gaba da zama daya yana daukar Alhakin daya" cewar Yakubu.
Audu ya dago a fusace yace
"Wato ce maka tayi kasa na saketa kenan dazun?"
"Haka tace, ta gaya mun ta gaji da cutar da ita da kakeyi kaida matarka dan haka tana neman sauqi ka sawwaqe mata auranka taje tayi rayuwarta ta samu wani can ta Aura wanda ze sota tsakani da Allah ya san darajarta kaje kaci gaba da zama da matarka da kake ganin tafi maka kowa" Yakubun shima ya mayar masa cikin daga murya. Se Audu ya miqe yana cewa
"Bazan saketan ba, ka gaya mata idan tana da qarfi tazo ta kwaci sakin ko kuma ta saki kanta"
"Ai kuwa idan baka saketa ta Arziqi ba zaka saketa ta tsiya dan wallahi maka ka zanyi a kotu qaryar taurin kai kakeyi Audu zan nuna maka jini daya ne yake gudana a jikinmu yanda kake jin ka gado Taurin kai seda na fara gada kafin ka samu ragowa, karka kawo mun takardar sakinta kafin nan da gobe kaga yanda zamu kwashe dakai" daga haka ya shige ciki ya bar Audu a tsaye yana tsuma, Bara'atu tace ya saketa? Ita da kanta ko kuwa wannan matar Yakubun ce ta zugata?
Kwanaki uku aka kwashe cikin wani yanayi mara dadi, kwana biyu da Audu yaje gidan Yakubu bayan ya dawo ya samu Bara'atu yayi mata cin mutunchi da tijara ya kuma jaddada mata sedai ta mutu amma baze taba sakinta ba washe gari da safe yana kamfani se ga magatakarda daga Kotun Musulinci an aiko masa da sammaci, ya karba ya duba kiransa akeyi daga kotu matarsa ta shigar dashi qara ya wuto gida Afujajan sedai be tarar da Bara'atu ba tun safe yana fita itama ta fice ta tafi gidan Yakubu tare dashi sukaje Kotun da kanta ta shigar da qarar bayan Yakubu ya sake tambayarta ko zata yi haquri ta bada lokaci su sasanta ta rantse masa akan wallahi ta gama zama da Audu muddin baso suke wata rana a wayi gari zuciyarta ta buga ta mutu ba su qyaleta jin haka yasa yace su tafi Kotun take kuma aka rubuta takadda aka kaiwa Audu.
Ranar Jajiberin sallah Bara'atu ta karbi takardar sakin igiya daya data rage tsakaninta da Audu, a ranar ya kamata suyi zaman kotu, tun Asuba daya dawo ya kulle kansa a daki yaqi fitowa, besan yanayin da yake ciki ba wani irin qunci da zafi zuciyarsa takeyi masa. Binta da duk abinda akeyi a kunnenta da idonta amma tayi biris tamkar bata san wainar da suke toyawa ba tana tsakar gida tana aikace aikacenta tana waqoqi Musbahu yazo, bayan sun gaisa yake ce mata gurin Baba yazo ta masa magana qarfe Goma ne zaman kotun nan gashi Tara da rabi tayi, dataje ta gaya masa beko waiwayo ba ya miqa mata farar takarda, duk yanda taso ta daure bayan ta karanta abinda yake ciki ta kasa seda ta rangada guda kamar wadda take saka Amarya a lalle. Tana bawa Musbahu takardar ta hau taka rawa a gabansa se ya rasa abinda zeyi kawai ya tsaya yana kallonta kafin jiki a sanyaye ya juya ya fice daga gidan ya kaiwa Yakubu saqon Audu.
Sanda takardar ta shiga hannun Bara'atu ji tayi kamar an mata bushara da gidan Aljanna, da Ajami ya rubuta dan haka ta gane komai abu daya daya dameta a ciki shine cewar da yayi karta tafi masa da Da ko daya, ta yaya zata barwa Binta yaranta? Matar data tsaneta kuma zata iyayin komai akanta da yaranta.
"Karki sakawa ranki damuwa akan yara babu abinda ze same su sannan kina nan a matsayinki na mahaifiyarsu babu abinda ze goge hakan komai daren dadewa kuma zasu nemeki. Ki fuskanci rayuwarki ta gaba, ki tashi kinemi ilimi ki tsaya da qafafunki in sha Allahu ubangiji zeyi miki sakayya a gaba da Mafi Alkhairi kinji" Yakubu ya tausheta.
A ranar suka tafi Bechi gaba daya dan dama can zasuyi sallah. Shiya kaita har gidansu ya kuma yiwa Inna Hajara bayanin komai, bayan tafiyarsa kuwa wuta ce kadai Inna Hajara bata hura ta jefa Bara'atu a ciki ba, ta kasa hango rayuwar da yarta take ciki da ta sa ta haqura da daular da ita hange, damuwarta kadai mutane zasuyi mata dariya, zasu rasa tallafin da suke samu a gurin Audun tunda ya kwace Yayansa, ita da take saka ran idan Bara'atun ta sauke farali Bana badi kuma a sakata a lissafi shine tayi mata baqin ciki shin Bara'atu wace irin yarinya ce ne? An gaya mata da akwai Auran da ake jin dadi dari bisa dari ne a ciki? Wace Macece zata samu Miji kamar Audu daula iya daula tayi wasa da damarta ai se sakarya irin Bara'atun gashi yanzu Auran ya mutu murus babu damar gyarawa.
An cinye watan Shawwal Mahajjata suka fara shirye shiryen tafiya qasa me tsarki, Audu ya rigada ya biyawa Bara'atu, Bilki da Aminu se Balaraba matar Yakubu, a hannun Aminun ya damqa duk wani abu daya kamata na Bara'atun, babu wanda beyi mamaki ba dukda sun san da ita cikin jerin matafiyan amma abinda ya faru yasa suka dauka za'a fasa tafiyar da ita sedai Audun ya basu mamaki. Lokacin tafiya yayi suka shirya sunyi bankwana da yan uwa da Abokanan Arziqi, dalilin su Bilki da Aminu ya saka Audu yi musu rakiya Iyafot dukda qasan ransa badansu yaje ba, haka nan zuciyarsa ta kasa nutsuwa a kwanakin, kullum ya kwanta se yayi mafarkin Bara'atun haka da rana wuni yake da tunaninta a ransa yana jin kamar ta cancanci ya nemi afuwarta koda har yanzun be yarda da cewar ya cutarda ita ba kamar yanda mutane suke fada amma kuma haka nan zuciyarsa take ingizashi ga neman afuwar da besan ta mecece yake da buqata ba.
A iyafot Mahajjata sun hau layin karban tikitin shiga jirgi, yana daga tsaye can gefe dan ya sake zama baqo a cikin danginsa tun da ya rabu da Bara'atu ya sake rasa karsashin sakewa musamman a gaban Yakubu yanzun ma ganinsa tsaye suna sallama da matarsa yasa duk ya kasa sakewa gashi yana so yayi magana da Bara'atu amma shegiyar zuciyarsa me masa hudubar tsiya tana gaya masa girmansa ze zube idan aka ga ya mata magana a nan gurin.
"Be kamatu na tafi muna riqe da juna a zuciya ba, ina roqon da ka yafe mun idanna maka wani laifi a zaman da mukayi da kai, daga bangarena na yafe maka, iyakar wannan Alkhairin da kayi mun ka zama silar da zan ziyarci ma'aiki ya wanke duk wani laifi naka da yake cikin zuciyata sannan idan ka koma gida ka gayawa Matarka in har taji tsoron Allah ta gaya maka gaskiya ta wankeni daga zargin data saka mutane sukemun na kisan kai na yafe mata idan ba haka ba idan harna mutu ko ita ta rigani mutuwa tabbas shari'armu sedai a qarqareta a gaban Allah dan bazan yafe ba bayan raina a ringa aibata Yayana ana jifansu da abinda ban aikata ba" Bara'atu da be san sanda ta dawo gurin ba ta fada tana kuma gama maganar ta koma cikin Ayari tana daga masa hannu, kamar wanda aka matsawa Remote haka shima ya shiga daga mata hannun, zuciyarsa ta ringa tsinkewa wata faduwar gaba da besan dalilinta ba ta saukar masa haka ya tuqa motarsa ya koma gida yana maimaita zancenta na matarsa ta wanketa daga zargin data dora mata.
A karon farko ya tambayi Binta gaskiyar abinda ya faru? Ya akayi tasan Bara'atu ce ta kashe mata Da? Bintan dake cike fam da tafiyar Bara'atun tayi tsaki kawai ta tashi ta bashi guri. Bara'atun nema take ta zame mata qajaga, ta tunkudeta amma ba zata bar zuciyarta ta huta ba kenan? Abu daya ke sanyaya mata rai idan ta tuna aure ya qare tsakaninta da Audu duk Bala'i dole su haqura sannan ga Yayanta nan zube a tsakar gida suna watangaririya iya rabata dasu da tayi tasan zuciyarta ta quntata, jira takeyi Tagwayen Zubaida su shekara biyu suma tasa ya karbo su subi sahun yan uwansu domin tasha Alwashin babu wata mace da zata mori Audu bayan ita, yaya dai da suka haifa sun samu sedai su jira idan ya mutu su yafici abinda suka samu amma badai a yanzu da yake raye ba.
An kammala aikin Hajji lafiya Mahajjata nata lissafin kwanakin daya rage musu su dawo gida haka nan yan gida nata shirye shiryen tarbar yan uwansu, kwanaki biyu ya rage Jirgin su Bara'atu ya sauka, a daren ranar da zasu tafi Jidda inda daga can za'a maido su Nigeria suna shirye shirye dan sun gama daure kayansu cikinta ya fara murdawa, kamar wasa tun tana jinsa kadan kadan har ta kai ga ta kasa zama cikin abinda be gaza Minti talatin ba da fara ciwon cikin rai yayi halinsa Bara'atu ta amsa kiran Mahaliccinta. Mutuwarta ta girgiza yan tawagarsu gaba daya bama su Bilki kadai ba.
Wata mata ce take fadin
"Dazu take cemun tun da muka hau jirgi tayi addu'a idan har ta kammala aikin Hajjinta lafiya kuma ibadarta ta karbu tana fatan ubangiji ya karbi ranta a binneta a qasar Ma'aiki tace tsoro takeji anya kuwa tayi Hajjinta daidai ashe lokaci yana tafe ubangiji ya karbi shahadarki Bara'atu Yarinyar kirki yarinyavme haquri Annabi yasan da zuwanki" haka akayi jana'izar Bara'atu da Asuba a masallacin Harami aka binneta a maqabartar da ba kowa yake samun wannan Alfarma ba se me tsananin rabo shikenan rayuwar ta qare ta tafi ta bar Binta a duniyar da take ganin ba zata qare ba.
Dawoqar Mahajjata a maimakon murna se Al'amari ya juye na koke koke da Jimami, duk wanda yaji mutuwar Bara'atu seya girgiza hatta da Binta da da take ganin idan aka bata wuqa zata iya dabawa Bara'atun se gashi sanda labarin mutuwarta ya rsketa zuciyarta seda ta tsinke ta kuma girgiza.
Munira qanwar Binta da tazo Kano tun Bayan qaramar sallah dalilin takurar da Mama take mata akan ta fitarda Miji bayan kamar wadda aka sakawa hannu Sauro be taba tsaida ita ba bare yaje gidansu da sunan zance shiyasa ta tattaro ta taho gurin Bintan saboda ta samu sauqi kuma qila ta samu Mijin a nan sanda taji zancen mutuwar Bara'atun kuka ta fasa ta dora hannu tana tumami
"Mun shiga uku Yaya Binta matar nan ta mutu bamu nemi yafiyarta ba wlh inaga haqqintane ya kamamu gashi naqi Auruwa Anty Sakina haka siddan aka koreta daga gurin aiki duk irin hanyar Dady da mutanen daya sani ta kasa samun wani aikin ga Mijinta ibtila'in daya fada masa daman da aikin nata suke lallabawa da tallafin da Dady yake bata to ta rasa aikin ita kanta Yaya Salima cikin garari take masifar yau daban ta gobe daban gashi yanzu ta mutu balle mu roqeta ta yafe mana qazafin da muka mata shikenan haka rayuwarmu zata qare a balbalce ni kenan bazan taba yin aure na na shiga uku na lalace wayyo ni Munira kaicona dana biyewa shedan muka laqabawa Baiwar Allah sharrin kisan rai bata ji ba bata gani ba" magana take cikin ihu da kururuwa wanda mutanen da suke tsakar gida Yan Bechi da sukazo tarar su Bilki duk sun Jita, Audu na kan Baranda dan jiri ne yake neman kadashi tun sanda labarin mutuwar ya riskeshi shiyasa ya zauna a gurin ana masa fifita se ga wata sabuwa yana jiyowa daga dakin Binta.
Page 29
"Ke Munirah meye haka? Baki da hankaline kike daga murya baki san bamu kadai bane a gidan nan?" Binta ta fada a rikice tana qoqarin toshe mata baki Muniran ta fizge tana cigaba da cewa
"Ki barni Yaya Binta abin kukane ya sameni dole nayi, daman Yaya Ummu seda ta fada, tace akwai ranar da zamuyu kuka muyi Nadama, seda tace tun muna da sauran lokaci mu kwance qullin da muka daura a lokacin ban dauki maganarta da muhimmaci ba, haka kawai muna zaman zamanmu muka jazawa kanmu masifa ta hanyar shiga haqqin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba muka bata mata suna kuma mukayi silar mutuwar Auranta gashi yanzu ta mututu ta bar mu a duniyarda nauyin haqqinta a kanmu nidai Allah ya isa tsakanina daku kun cuceni wlh" ta sake fada muryarta a sama tana rusa kuka.
"Alhamdulillahi! Dadina da gobe saurin zuwa, Allah nagode maka daka matsi bakin Azzaluman bayinka suka tonawa kansu Asuri, kaiconku wlh, kaicon Zuciya me cike da Mugunta da Zalunci irin taku. Yanzu ai ga duniyar nan gaba daya bama gidan Audu ba ta tafi ta bar muku se ku shinfida tabarma ku cigaba da zama kuna kasa abinda kukaga dama a cikin duniyar, amma ku sani wlh cutar da kukayiwa Bara'atu bazata barku ku zauna lafiya ba, yanda kuka saka rayuwarta cikin qunci da takura harta koma ga mahaliccinta da yardar ubangiji haka zaku qare taku" Bilki ta fada idanunta na tsiyayar da hawaye, ta waiwaya ta kalli Audu daya runtse ido kamar yayi bacci a inda yake zaunen tace
"Baka da banbanci kaidasu, yanda zasu qare rayuwarsu suna girbar sharrin da suka shuka kaima haka zaka qare taka kana Nadamar zamanka da Bara'atu"
"Ke Bilki menene haka? Da wanne kike so yaji dan Allah?" Aminu ya katseta. Bata kulashi ba taci gaba da kukanta. A cikin daki kuwa Munirah na gamsheqar kuka Binta na tsaye akanta ta harde hannye gaba daya kanta ya qulle ta rasa abin da zatayi a lokacin, ji take kamar ta rufeta da duka shegiyar yarinya ta kwance mata zani a Kasuwa yanzu da wace kalma take so ta gyara kwabar da tayi mata?
Tana jiyo sanda su Aminu suke fadawa Audu zasu wuce saboda kar suyi dare a hanya.
"Ka daure ka shiga daki ka kwanta, rayuwar kenan daman farkonta da qarshenta dan taqin kadan ita dai Bara'atu tata ta qare kuma In sha Allahu munayi mata kyakykyawan zaton tana Babban masauki addu'a kadai zamu cigaba da bibiyarta da ita kafin tamu tafiyar ta riskemu Allah yasa kuma abinda ya faru a baya ya zame mana darasi a rayuwarmu gaba daya" Aminu ya sake fada masa daga nan suka fara haramar wucewa Bechi.
Cikin yanayi me ban tausayi Audun ya miqe, dakyar ya iya ce musu Allah ya tsarw hanya ya daddafa ya haye samansa a falo yayi zango ya kwanta rigingine a qasa wani zafi da radadi yake ji daga can cikin zuciyarsa, numfashinsa ya ringa fita da sauri da sauri tamkar wanda yayi gudu a, a sannu ya baiwa Idanunsa damar fitarda abinda suke muradi, hawaye ya gangaro ta gefen idanunsa zuwa cikin kunnuwansa, tamkar me tsoron wani ya jishi ya saki kuka kamar mace, kuka me tafe da abubuwa da yawa a cikinsa. Cikin muryar da bata fita yake cewa
"Dana san mutuwa zakiyi Bara'atu da ban rabu dake ba, inama ina da damar maido da baya, dana canza zaman da mukayi zuwa mafarkinki, dana san rayuwarki ba zatayi tsaho ba da...da...." Ya kakare yama rasa abinda ze fada se kawai yaci gaba da kukansa a hankali kewar Bara'atun me nauyi tana dirar masa. Kalamanta na sallamar da tayi masa suka ringa dawo masa kamar sannan take maganar, tace ta yafe masa amma bashida tabbacin Allah baze kamashi da laifin cutar da ita ba wai meya shiga kansa shi? Meyasa ya kasa tantance gaskiya da qarya a zamansa da Bara'atu? Me yasa ya gagara yi mata uzuri ya ringa Muzguna mata yana tozartata? Yanzu gashi ta tafi ta bar masa duniyar dai, tayi masa nisan da baze taba taddota ba.
Seda yayi kuka me isarsa kafin ya tashi dalilin kiran sallar Azahar da ake tayi yana layi kamar wanda ya shawu ya dauro Alwala, baze iya sauka ba dan haka a nan yayi sallarsa addu'arsa gaba daya ta nemarwa Bara'atu Rahmar ubangiji ce, yana nan zaune yayi zuru zuru kamar wanda ya kwana zawo, motsin hawowa saman ya jiyo, ya waiwaya ya kalli qofa daidai nan Binta ta shigo da Try a hannunta ta doro kulolin abinci jikinta sanye da Zurmemen Hijabi har qasa fuskarta tayi jaa ta kumbura kamar wadda tasha kuka ta qoshi.
A gabansa ta ajiye Try din ta zauna se ji yayi ta fashe da kuka tana hailala da salati, yayi zukudi yana kallonta kawai.
"Mun shiga uku mun lalace Ashe Bara'atu mutuwa zatayi daman? Me yasa yarinyar nan bata haqura munyi zaman lafiya anyi rabuwar arziqi ba?" Yeeee ta sake rushewa da wani kukan.
"Binta" ya kirata cikin kaushin murya, tayi dif daga kukan munafurcin da takeyi ta kalleshi, cikin sautin daya fi na farko ya sake ce mata
"Zan sake tambayarki menene gaskiyar abinda ya faru ranar sunan Zakariyyah?"
"Wace gaskiya kuma wai kake buqatar sani bayan abinda nida yan uwana muka shaida maka tun a waccen ranar? Allah ya jiqan Bara'atu kawai ni daman tun tuni ai nace na yafe mata idanma wannan kake tunani" ta bashi amsa ba tareda ta kalli idonsa ba babu tsammani kuwa taji saukar yatsunsa a kuncinta irin marin nan na bazata seda ta wantsala gefe tana zare ido kafin ta taqarqare ta fasa qara tana kiran
"Ka mareni"
"Na marekin, kuma dukan tsiya zanyi miki yanzu muddin baki bani amsar abinda na tambayeki ba sa'innan na koraki gidanku" ya fada yana miqewa tsaye PPP ll ya razana Bintar bata taba ganin ya birkice haka ba, Bay's play llp ta fara ja ganin yana neme neme da alama abinda ze doketa dashi din yake nema hakan yasa tace
"Zan fada maka wlh, nidai na shiga bandaki ina fitowa kawai na tarar da ita ta zauna akan Jaririn"
"Har yanzu kina da bakin yimun qarya ko?" Ya fada yana nufota da wayar Radion daya zare, ta yunqura zata gudu Hijabin jikinta ya tadeta ji kake timm ta fadi a qasa be ko bata damar biqin radadin faduwar ba ya shiga zabga mata Bulaliya ta ko ina a jikinta. Dukanta yake kamar ya samu qato dan uwansa yana fadin "ba zaki fadamun gaskiya bako?"
Dadai ta tabbatar da gaskiyarta ce zata kwaceta a hannunsa dole ta fada,
"Wlh sune, basu fadamun daman ya mutu tuntuni ba se bayan da aka gama mana shari'a wlh ba laifi na bane kayi haquri ka kyaleni".
Be barta ba seda hannayensa suka gaji zuwa sannan ko motsin kirki bata iyayi ya mata lilis fatar jikinta duk ta fashe nan ya watsar da bulalar ya shige daki ya barta tana jan numfashin wahala dan kukan ma ta kasa cigaba da yinsa. Wanka yayi ya fito ya tsallajeta yayi waje abinsa, Munira na bakin qofar, tunda ta jiyo ihun yar uwar tata ta taho sedai tsoron karta shiga ya hada da ita yasa taci burki a gurin.
"Kar na dawo na tarar daku cikin gidana daga ke har itan" ya fada mata. Ta sauke ajiyar zuciya da be taba lafiyarta ba, seda ya sauka daga qasan kafin ta shiga, yanda taga Bintan ta tsorata ta kamata Binta ta fashe da kuka saboda Azaba ta ko ina jikinta radadi yakeyi mata.
Hudu ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 32