shimfida suka kwanta. Washe gari aka tashi da hidimar daurin aure, shayi Bara'atu ta dafa mata da safe ta soya kwai dan an kawo Buredi tun cikin dare.
"Ko zakici Waina ko Tuwo a kawo miki?" Bara'atun ta tambayeta. Binta dake shiryawa bayan ta fito daga wankan da har bandakin ta kai mata ruwa tayi banza da ita ganin haka yasa ta fita itama ta shiga wanka. Daurin auran na safe ne, kafin goma gida ya cika danqam da mata harda Mazan ma masu shigowa yiwa Goggo Fadi Allah sanya Alkhairi. Binta tasha kwalliya da Leshi ta baza turare ta kafa kujera a tsakar gida tana kallon kowa daidai. Bara'atu bata daddara ba ta sake yi mata tayin wainar daurin Aure ko tuwo wannan karon tace ta bata.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Wainar Masara ce tayi kyau matuqa ta zubota ta ajiye mata ta tafi kawo miya. Ta rage miyar tuwon Jiya daman saboda Bintan dan ta san ba lallai ta iya cin wadda akayi ta taro ba, ta bincike Kitchen din inda ta ajiye babu miya se ganin kwanon tayi ma a wanke an ajiye bata da zabi dole ta debo mata ta Bikin.
"Ni zaki kawowa wannan miyar kamar ruwan wankin kan mahaukaciya ni zan ci miki wannan kawai kice kasheni kike so kiyi" Bintan ta fada a fusace sanda ta dire mata miyar, kamar me magana da Babarta Bara'atu tace
"Kiyi haquri, na rage ta tuwon jiya bansan waya juye ba. Ki gwada wannan dinma tayi dadi wlh zaki iya ci"
"Dama mana tayi dadi a bakin daya sbaa cin gabza dole kice wannan tayi dadi" Binta ta fada tana harararta, Bara'atu ta miqe jiki babu kwari mutane duk sun tsaya suna kallonsu ga Bintan bata magana a hankali, da qafa ta tunkuda kwanon miyar ya fallatsarwa Bara'atu a jiki tana cewa
"Zoki kwashe shiyarki banma san me kika zuba a ciki ba da kike ta nacin se naci".
"Amma kedai anyi yar marasa mutunchi, yanzu da miyar da zafi ta qona mata fata fa?" Hashimu daya shigo yana saba babbar riga ya fada, Binta ta kama qugu tana masa kallon banza, sedai ta gaza ce masa komai dan yanda yayi maganar cikin hayagaga ta tabbata ze iya rufeta da duka. Mata aka dauki surutu caaa kowa da abinda take fada. Hashimu nata bala'i yana qundumawa Binta da Iyayenta da basu san anyi ba zagi. Ya kalli Bara'atu dake hawayen wannan cin mutunchi data mata cikin taro, tacu kwalliyarta da Shadda Ruwan omo Bintan ta mata wankan Miyar taushe
"Ke kuma sakarya kin tsaya kina mata kuka, k wuce ki kwase me zafi a tukunya ki watsawa yar banza a wannan kodaddiyar fuskar tata" Hashimun ya sake fada daidai nan Audu ya shigo yana fama da tasa babbar rigar ya tarar dasu cirko cirko, Binta na ganinsa ta saka kukan zallar kirsa da makirci tana cewa
"Saboda ni ba yar cikinku bace shine zaku tsaneni? Me nayi muku? Wani abu ya taba hadani da wani a cikinku ne balle ku qwafeni kuke neman halakani"
"Wace irin magana ce haka babu dadin ji wa yake neman halakaki?" Audun ya fada yana qarasawa kusada ita. Ta sake rushewa da kuka tace
"Ina zaune kawai Bara'atu tayo kaina gadangadan da wuqa a hannunta, a garin na tureta ta taka kwanonmiyar nan ya fantsalar mata shine cikin su babu wanda yabi kadin ba'asin nufoni da tayi da wuqa sena miyar sata fantsamar mata suka hau zagina har wannan yayan naka yana cemun jinin shadanu" ta nuna Hashimu daya qame tsabar yau yaji wadda tafishi iya hada guri bashi kadai ba gurin kaf shiru sukayi suka daskare da mamaki, Audu ya kalli Bara'atu ya kalli wuqar dake yashe a gefenta ya sunkuya ya dauka yana nuna mata yace
"Me zakiyi da wuqa da kika nufota"
"Wallahi tallahi qarya take mun" Bara'atun ta fada tana saka kuka, Baba suwaiba wadda qanwace ga goggo Fadi ce tace
"Amma kedai wannan yarinya duk yanda akayi Abokanan wasa kuke da Shaidan, yanzu wuqar da ni kika tambaya na baki kika bare muruci shine zakice ta nufo ki da ita? Gaskiya bakya tsoron Allah yanzu ke ko kunyar idanun jama'a bakiji ba ki lafta wannan uwar qaryar da zata iya kashe Aure Allah wadaranki wlh tir da masharrancin harshe irin naki"
Nan aka sake daukar surutu kowa nayiwa Binta tofin Ala tsine. Audu ya kalli Bara'atun dake kuka kamar me sannan ya kalli Binta data sunkuyar da kai qasa kunya ta dabaibayeta kamar qasa ta tsage ta shige ciki takeji. Ta manta shaf a inda suke, Tsabar yanda idonta ya rufe tana neman dalilin da ze saka Audun sakin Bara'atu ya sakata hada wannan zancen da bata ma san sanda Dabarar tazo mata ba ta kwakwalwar kuma ta gaza kawo mata kalaman kare kai. Gaba daya sun kasa kunne suji hukuncin daze sauka akan Bintan da abinda tayi sabanin haka se ji sukayi yaja tsaki ya juya buguzun buguzun ya fice daga gidan.
"Kin shiga uku Bara'atu ke kuma taki jarabawar kenan a gidan Aure to Allah yasa ta zame miki kaffara"
"Bantan uba, yau naga abinda yafi qarfina ni yasu, Bara'atu dama haka kike zaune? Dole ki rame ai kinyi dakyau ma har yanzu kike cikin hayyacinki wannan makirci har ina?"
"Wlh bazan iya zama da irin wannan matar ba, dama ace Audun tsayayye ne da sauqi to da alama ta shanyeshi Allah sarki Dada Allah yayi bata da rabon shan takaicin suruka shiyasa ta mutu kafin a aurota dan wlh wannan tsaf zata raba Da da uwarsa kutusi"
Haka suka saka Bara'atun a tsakiya kowacce ta ringa surutunta, Binta kuwa jiki babu kwari kamar wadda aka kama da kayan sata ta shige dakin Bara'atun can qurya ta lafe a gado. Tana jiyo surutai ana zaginta amma babu damar tankawa ta rigada ta kwafsa. Haka ta wuni sir a daki ana ta shagalin Biki, Allah sarki Bara'atu, dukda abinda tayi mata haka ta zuba abinci da rana ta bawa Abdullahi ya kai mata bata daije da kanta ba. Bata ma sake shiga dakin ba dan ko kaya da zata sauya Bilki ce ta dauko mata ta kuwa yiwa Binta tatas kamar zata doketa dan bata gidan abin ya faru ta tafi gidanta ta dakko abu. Haka suka kwana.
Tun a daren ranar Abokanansa da matansu suka kai musu tsogwamin abinda ya faru suka tareshi da zancen,
"Gaskiya ka gyara gidanka Audu tun kana da hali. Wannan hanyar da ka dakko bazata bulle maka ba, idan baka dauki mataki yanzu ba kana ji kana gani gidanka ze ruguje, ba kuma iya matanka abin ze shafa ba harda yan uwanka seta rabaka dasu. Wlh banda qaddara ma wannan ba matar aure bace, mace babu komai a ranta se fitina da tada zaune tsaye? Wai me ka gani a gurin yarinyar nan harya rudeka Audu?" Shamsu Abokinsa ya fada. Audu yasha kunu yana kallonsu daidai dan kowa ya tofa ta bakinsa.
"Ana magana kayi shiru kana muzurai da hada fuska, mu nan babu wanda fushinka ze tsorata dan kar muke kallonka kasan mu mun sanka tun muna yawo babu wando, kuma gaskiya ce se mun fada maka ka dauka ko karka dauka wannan ruwanka mudai mu fita haqqin zaman tare" Iliyasu daya fi sauran zafi ya sake fada se sannan Audun ya budi baki yace
"To me kuke so nayi ko nace? Dani daku fa duka labari mukaji babu wanda abin nan ya faru a gabansa balle ya fadi haqiqanin gaskiyar yanda akayi"
"Amma Audu baka tsoron Allah, ta yaya Mutum sama da Ashirin zasu hada baki su fadi qarya? Idan duka matan gurin sun goyi bayan Bara'atu kana tsammanin Hashimu ma ze bi bayanta ne?" Iliyasun ya sake taso masa, saboda a bar maganar yace musu
"Naji, zan mata magana"
"Daga baya kenan, ai take a gurin ya kamata ka nuna mata kuskurenta ba wai daga baya ba yanzu ai ka bata qofar da zata taka koma wane tunda ko zakayi fada badai a gaban mutanen data muzanta wancan ba. Wlh ni mamakinka nake Audu, a tasowarmu idan wani yace ko a mafarki ya ganka Mace tana juyaka wlh duk se mun qaryata se gashi a gaske da ranmu muna gani ka zama solobiyon banza a gaban wadda ma bata isa ba" cewar Musa.
"Ya isa haka, nace zan mata magana ko, nifa ba wai wani abu yasa nake daga mata qafa ba. Idan na duba matakin dana taka a yanzu Mahaifinta ne sila, shi kuma a duniya bashida abinda yake so kamarta ya gayamun babu abinda zan yi na saka masa irin na kula masa da Binta wannan ne kadai dalili"
"Ai shikenan" kusan dukansu suka hada baki gurin fada tsabar takaicin da maganarsa ta qunsa musu daga haka suka watse suka barshi da Muzammilu shine be gaji da magana ba.
Washe gari kuwa da farar safiya Audu yace su fito su tafi. Bata san da su Bara'atu zasu koma ba seda taga ana loda kayansu a mota tayi qwafa bata dai ce komai ba dan babu fuska a gurin Audun, tun jiyan dai bece mata komai ba haka kuma be sakar mata fuska ba. Bara'atu dai duk a darare take har suka isa Kano ta wuce sabon dakinta har tsalle seda tayi saboda murna tayi dakin yan gayu. Haka aka cigaba da rarrafa rayuwa, sauqi daya ta samu shine na aikace aikacen Binta saboda masu aiki har biyu data tarar ta dakko wanda taja musu kunne akan ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu da Bara'atun a bakin aikinsu.
Ko a jikin Bara'atu daman me zata saka suyi mata ita? Gaisuwa kuma babu dole a ciki ita a zauna lafiya babu ruwan kowa da kowa yafi mata. Lantana me share share itace Mara mutunchi a masu aikin ta kuma lura tafi fada a gurin Bintan sama da Mairo me mata girki wadda Bintan ta santa ta taba zuwa gidanta kitso sau daya can qasan layinsu take Lantanar ce bata san a inda ta kwasota ba. Matar sam batayiba, a suffa ma Astagfirulla kalar munafukai ne da ita kuma haka take a zahiri. Ita take zuba gishiri akan ciwon zaman su da Bintan. Yanzu da cikinta yayi nauyi ta kusa haihuwa tadan rage hayaniya da hayagagar da take mata shiyasa har take dan samun damar fita tsakar gida tasha iska.
Randa Lantana ta kunno Bintan kuwa ruwa ba zata barta ta hadiye da dadinrai ba, masifa zagi cin mutunchi da gori babu wanda bata mata, tun ba da Hadiza qanwarta tazo, ita take binta an mata aure shekara biyu baya zaman yaqi dadi suka rabu da Mijin nan ma babansu ya tasata gaba shine ta gudo gurin Bara'atun ta kwana biyu tareda Addu'ar ko Allah ze fito mata da Miji a Kano tayi aure ta huta da Fadan Babansu. Nan fa Binta ta samu nayi, gori da yana fita a jiki da bazasu samu sararin shan iska ba, sauqi daya da bata samu goyon bayan Audu ba da tace ya kori Hadizan, da haka zasu tattaro su cika masa gida to da yake har sannan ba a koma daidai ba tun abinda ya faru a Bechi dukda da fatar baki be mata magana ko fada akan abinda tayin ba kawai ya dan dauke mata wuta ne yanda yake rawar jiki yana mata abubuwa ya rage wannan ma na bala'in mata ciwo tadai barine zuwa ta haihu dan ta kanta take yanzun shiyasa ma take sararawa Bara'atun amma da zarar ta haihu zata qaddamar da shirin da tilas ta bar gidan da kareren qanwar tata data kwaso.
Kwanci tashi cikin Binta ya shiga watan haihuwa, lamari fa ya zarce nada dan kankat Audu ya tattara ya koma gurinta da kwana dukda daman kusan hakan ake, a girki hudu idan zatayi kwanaki takwas kenan da qyar ya kwana uku tareda ita dasun kwanta Binta zata doko qofa wai bata da lafiya daga qarshe ma tsakaninsa da Bara'atu sedai idan yana da buqatarta yaje da Rana ko da daren kafin lokacin kwanciya yayi daman saman sa Binta tace Turakarta ce ita kadai, daga qarshe dakin tsakar gidan aka gyarawa Abdullahi daya fara zama saurayi su Babangida kuma tare take kwana dasu a dakinta se dayan ya zama dakin Audun to a hakan ma ita bata damu ba tunda dai babu wata fitina ko a haka za'a cigaba da rakawa zata iya haqura.
Ranar da Binta ta haihu cikin dare naquda ta tasar mata, Audu baya nan ranar ya tafi Calaba dakko Mai a ranar dai suke saka ran dawowarsa amma har aka kwanta bacci shiru. Guraren sha biyu Ciwon gaske ya tasarwa Bintan, tun tana daurewa har abu yaci tura ta shiga kuka kamar yarinya. Abdullahi ne ya tashi fitsari ya fita tsakar gidan ya ringa jiyo kamar kuka daga dakin Bintan saboda darene guri yayi shiru kuma window dakin a tsakar gidan yake dan haka ya tafi da gudu ya bugawa Bara'atu qofa tana bacci taji bugun ta farka a gigice ta fito ya sanar mata da abinda yaji
Tunanin naquda take ne ya fara zuwar mata dan haka ta juya ta tafi dakko zani da Hajib idan yaso ta fita ta kirawo Baba Uwani maqociyarsu. Tana zuwa qofar dakin sukaci karo da Audu, bata gama mamakin sanda ya dawo ba tsaqarsa ta katseta.
"Ki kamata muje mota" ya fada rai a matuqar hade, jiki na rawa ta kama Bintan da tasan Azaba ce tasa ta yarda ta riqeta. Haka sukaje Asibitin murtala, kamar ana jira suna isa ko minti biyar ba'ayi ba Binta ta haihu ta samu Da Namiji. Yanda Audu ya ringa murna seka dauka haihuwar fari aka masa. A can suka qarasa kwana hardashi seda safe suka dawo gida Bara'atu ta ringa godewa Allah da zuwan Hadiza, shaf ta manta da batun Yara a gida seda sukaje Asibitin. Da ace Hadizan bata nan bata san ya zatayi ba qila sedai ta tako da qafa ta dawo dan ba zata barsu a gida suka kadai da daddare ba.
Kan jiki kan qarfi ta ringa hidima da Bintan da Jaririnta kyara da hantara kuwa babu wanda bata gani. Abinda yafi damunta yanda Audu ya shareta, ko magana ta masa a ciki yake amsawa hidima yake tayi da Matarsa da Jaririnsa kayan fitar suna ma ana saura kwana biyu Abdullahi ya shiga da qatuwar leda ta zazzage taga kayansu ne shida su Babangida ko dan kunne babu nata a ciki. Suna duba kayan ya shigo fuskar nan kamar hadari ya wuce dakinsa ta tashi ta bishi. Seda ta kai masa abincin dare ya gama ci kafin tayi masa godiyar kayansu Babangida da ya bayar ta qara da cewa
"Dan girman Allah idan wani laifi nayi maka kayi haquri ka sanar dani na gaji da wannan zaman gabar da mukeyi" ta tattara qarfin hali ta fada wanda Sadiya maqociyarta kuma qawarta guda dayace ta bata wannan shawarar ta cewa ta dena shiru, duk idan taga canji a gurinsa ta tuntubeshi suyi magana tunda tasan halin Binta baze wuce ta qulla mata wani abun a gurinsa bane koda ace baze yarda da ita ba in har ya gaya mata laifinta ta kare kanta shikenan ai ba makaho bane kuma ba kurma ba qin Allah ne ya saka idan an gaya masa abu yake hawa ya zauna ba tareda yayi bincike akai ba.
Seda ya mula kafin ya fara magana yana cewa
"Wato badan Allah ya kawoni ba so kikayi ki bar Binta ta mutu ba zaki fita ki taimaka mata ba? Koda yake dama tasha fadamun kince se kinyi Ajalinta da ita da abinda yake cikinta ba zata haifeshi ba. Wlh mamakinki nake Bara'atu, yaushe kika zama haka? Ko kuwa dama hakan kike kin lullubeni ne baki fito da ainihin kalarki ba is yanzu?"
"Ni ya kamata nayi maka wannan tambayar yaushe ka zama haka Audu? A zatona kaine mutum na farko da zaka fara bayarda shaida akaina amma kuma se zaton nawa ya zama ba gaskiya ba, koda ace ba zaka shaideni ba Audu yaci ace kasan me zanyi da wanda bazan aikata ba. A Bechi tace na nufeta da wuqa ka yarda yanzu kuma tace ni nace zan kasheta da dan cikinta shima ka yarda wane mugun abu na aikata maka daya janyo irin wannan rashin yardar a tsakaninmu har takai ayi mun qazafin zanyi kisan kai kuma ka hau ka zauna? Nayi tsammanin ko Qadangarenta tace nace zan kashe zaka qaryata balle ran mutum ba dYa ba harda na Jaririn dabe iso duniya bama" Bara'atu ta fada cikinmatuqar qarfin hali hawaye masu dumi suna sakko mata.
Page 14
Hawayen ta suka qara gudu lokacin daya miqe ya fice daga dakin bayan daya antaya mata tsaki me qarfi. Ta dade zaune a gurin tana kuka, meta tsarewa Binta? Ita data shigo ta tarar batayi kishi ta tayar da hankalinta ba se itace zata yita hada mata tuggu da makirci a gurin Miji shi kuma sam babu bincike ya ringa zama kan magana da an gaya masa? Tana tsaka da wannan kukan Hadiza ta kwankwasa mata qofa, seda ta gyara fuskarta ta fita Hadizan ta gane tayi kuka amna tayi shiru bata tambayeta dalili ba kuka kuma ta gaya mata ta daura aure dashi tunda ba zata tashi tsaye akan wannan Kishiyar tata makira ba se ta zauna tayi musu kuka har hawayenta ya qare.
"Yace kije ga naman qauri can an kawo a gyara, banda rainin wayo ke zakiyi mata suyar qaurin ma ina yan uwanta sunzo? Dama ace zaman mutunchi kukeyi da sauqi amma keda bola banbanci kadan ne a gidan nan sann.."
"Ya isa Hadiza, muje ki kama min" Bara'atu ta katseta daga mitar data kwaso.
"Allah ya sauwaqe kedai da zaki iya bismillah" Hadizan ta fada tana zama akan kujera, tasan ba zatayi ba tunda ta fada dan haka ta fita rai babu dadi zuwa gurin gyaran Qaurin. Ta tarar da Mairo na hura ta dora yan ciki lantana kuma tana ware nama da qashi da alama hadosu masu gyaran naman sukayi.
"Barka da Rana Hajiya" Mairo ta gaisheta, fuska babu walwala sosai dalilin quncin zuciya ta amsa mata, Lantana kuwa ko kallon arziqi bata mata ba sema tahau waqar Habaici daga Mairon har Bara'atun babu wanda ya tanka mata daga qarshe ta nemi guri ta zauna dan Mairo tace ta bari zasuyi tana kallon Lantana nata jan qwafa da alama zataje tayi abinda ta saba na hadin masifa.
Suna kaskon qarshe yan uwan Binta biyu suka zo gurin ta gane Babbar ita tana dan zuwa dalilin akwai yan uwan Mijinta a nan Kanon me bi matan dai sau daya ta taba ganinta se yau na biyu. Dazu da suka sauka har ta fita zataje ta gaishe su suka hadu da Binta a tsakar gida tace ko barandarta ta taka seta mata rashin mutunchi shiyasa ta fasa dan hakan yanzun ta gaishe su suka amsa kadaran kadahan. Robar da aka zuba Nama suka dauke suna barwa Lantana sallahun idan ankwashe sauran a kai musu.
"Ko me zasuyi dashi se Allah, a irin arziqinsu ai wlh nama dai yaci ya gunduresu yanzu amma Allah sa suma ba jida zasuyi su tafi dashi su aje qulli qulli a firiza yanda Hajiyar nan takeyi ba su basu ci ba su basu bawa wani yaci ya musu addu'a ba kai Hajiya Binta fa akwai Rowa alqur'an" Lantana ta shiga jero zance babu kai babu qafa. Yanda Bara'atu bata tanka ba haka Mairo kamar bata gurin, wannan nadaga abinda yasa take qara ganin girman matar. Ba ruwanta ta shiga sabgar da bata shafeta ba, aikin daya kawota gidan kawai take yi idan tazo da safe ta gama musu kalaci da wuri take dora na rana wata rana ma sha biyu ta gama data gama ta karbi rabonta zata tafi se kuma gurin qarfe uku ta dawo ta dora na dare shima tana saukewa zata tafi se kuma gobe da safe musamman yanzu da Binta tasa aka hade girkin tun zuwan Hadiza a yanda ta cewa Bara'atu ta dena girki da kanta, kwadayin Nama da Kazar daya kawo qanwar tata seta koma haka idan anyi girkin zata tsaya a raba ta kwashe duk abin arziqi ta hadasu da qasan tukunya ita bata ci ba ita bata bari wani yaci ba ta bakin Lantanar, ba kamar Mairo ba ita lantana idan tazo tun safe seta kai Taran dare har se Audu ya dawo Bintan ta fatattaketa sannan zata tafi yanda kasan bata da Miji balle Yara.
Haka suka gama suyar ko dandanon gishiri a harshenta ta koma daki. Washe gari tun sassafe aka ringa shigo da kayan cefane, guraren Goma Binta ta aiko kiranta, A falon Audu na sama ta sameta tasha kwalliya abinta ba zakace jego take ba. Ta gaidasu ta zauna tana satar kallon Audu da tun maganar jiya be sake ce mata komai a gidan ba dubasun da yake da Asuba ma beje ba yau. Kudi ya tura mata murya a daure yace
"Gashi nan, ki duba cefanen da aka kawo, abinda babu se a siya sannan su Bilki suna hanya bansan ko su nawa bane ki gayawa Mairo a saka abinci da yawa"
Tayi shiru a ranta tana mamakin yau kuma ita aka bawa kudin cefane sannan ita ake cewa ta fadawa Mairo a qara abinci abinda ko ran girkinta Binta ke fadar abinda za'a dafa.
"Shikenan na sallameki" ya sake fada seta miqe ta dauki kudin tana jin Binta cikin kissa murya qasa qasa tana ce masa
"Ko kaifa, ai ya kamata dai itama ta ringa jin matar gida ce ba wai ace komai sedai taga anayi ba kaga kar suzo a qara tafiya dani a baki ace na kankane komai"
Ta tafi tana mamakin Bintan a ranta, wato matar nan ko wagainiya Albarka shiyasa wani sa'ilin bata ganin laifin Audu saboda Bintan tamkar me rufa ido take. Bata taba mata Tijara ko cin mutunchi a gabansa ba, idan yana nan nunawa take nan dunita tafi kowa son su zauna lafiya da Bara'atu amma ita taqi bata hadin kai, da hakan take kanainayeshi kullum tana nuna masa laifin Bara'atu ne ita ce bata so su zauna lafiya, Bara'atu ce take fadawa yan uwansa mugun abu akanta shiyasa kowa baya sonta, Bara'atu ta tsaneta bata da buri illa na taga bayanta sannan ita kuma tayi ta nuna bajintarta da son jan Bara'atun da yayanta a jiki a gaban idonsa idan yana nan har kyautar abubuwa take kai mata ko yara yana fita tabi ta karbo abinta ta dora da Tijara shiyasa baze taba ganin cutar da take mata ba.
Maganar girkin kanta da farko ta hana ko gaidata masu aikin suyi da kuna ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 32