Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata ido banda Audu dayaja tsaki dan maganar tata ɓacin rai ta ƙara masa ya tuna da wani lokaci can baya sanda suna Yara tun Malam nada rai Goggo Fadi na ce musu yayan me farar ƙafa, a lokacin abinda ya dauka saboda Dada Farace tar duk jikinta abinda take nufi kenan kalar fatar ƙafarta shiyasa be taɓa gayawa Dadan ba se bayan daya girma ya san ma'anar abin sannan ya fahimci zaginsu takeyi shiyasa duk inda yaji an faɗa se ransa ya baci. Binta ta ringa kuka tana maimaita an Auro musu me farar Ƙafa shikenan zasu tagayyare su shiga wani hali yan jaje suka koma wasu na ganin salonta data saba laƙawa matan da yake aurowa sharrine wasu kuma sun yarda da abinda ta fada dan tun bayan Auran Audun abubuwa suka fara canzawa yanayin bunƙasar Arziƙin tayi ƙasa ba'a dai samu wani ibtila'i babba kamar wadannan ba. A hankali rayuwar walwala da jin dadin da akeyi a gidan ta fara juyewa zuwa ƙunci da tashin hankali dan zuciyar megidan a kusa take kullum ƙiris yake jira a taɓashi yayi zazzaga ga mata uku kowacce da ciki haihuwa kusa hatta da yanayin cima ta sauya dan samun ƙasa yakeyi ba sama ba. An kwashi watanni cikin wannan hali, Audu nada shirin mallakar rijiyar Mai tasa ta kasansa a kwankin baya domin har ya fara harhaɗa kudade sun gama tsara yanda za'ayi da Alhaji Zakariyya wanda ze siyar masa da daya daga cikin rijiyoyinsa sedai matsalar daya shiga a yanzu da harta girgiza masa jari ta tilasta masa karbo kudaden daya bayar matsayin kafin Alƙalami ya sakasu cikin harkokinsa na Noma da kiwo wanda anan Ibtila'in yafi sauka, Amfanin gonar da ya noma a shekarar sama da kaso hamsin ƙwari sun lalatashi haka dabbobinsa na gidan gona Kaji sedai a shiga basu abinci a tarar da au fululu a ƙasa sun mutu ko a hangi Sa ya Tirƙeƙen Rago yana kakarin mutuwa sedai a danne a yanka. Abu dai kamar wasa ana saka ran samu sauƙi se ya zamana kullum kamar Tiri ƙaruwa abubuwan sukeyi. Mutane da yawa sukace hannu aka saka masa, Asirine, jifansa akayi ya bazama shine waccen tsangaya ya kai sadaka shine waccen gidansa kuwa kullum cike yake da Gardawa anata saukar Karatun Alƙur'ani idan an gama ayi sadaka amma abin se godiyar Allah kawai. Ana wannan yanayi Hadiza ta tashi da Naƙuda cikin dare, Audu da Aisha ne suka fita kaita Asibiti dan Bibta cewa tayi Allah ya kasheta babu inda zataje da Aishar ta shiga kiranta Audu kuma tace masa Yara, be kamatu a barsu su kadai a gida ba. Haka kawai sun hau Titi suna tafiya mota ta tsaya, ya fita yayi yaj dube dube ya sake kunnata yana ja inji yayi wata ƙara Baammm mota ta cake kuma ko ba'a fada musu ba sun san Injine ya buga, tamkar Audu ya fasa kuka, ya fita nemo taimako Hadiza dai nan cikin mota ta haihu ta santalo danta Namiji ƙato. Wani mutum ne ya taimaka musu ya ƙarasa Asibitin dasu se safiya aka sallamosu bayan an tabbatar da ita da Jaririnta duk lafiyarsu ƙalau motar Audu kuma akaje da Janwe aka dauketa. Binta da taga Hadiza ta dawo gida da Da Namiji ba'a cewa komai, baƙin ciki kamar ta mutu ko zuwa tayi mata barka batayi ba har akayi sunan Aminu Hadizan ta koma gida saboda jikinta dayaƙi mata dadi tun bayan haihuwar Binta faɗi take ta tafi kenan ba zata dawo ba. Haihuwar Hadiza ta sake zuwar musu da sabon sauyin dayafi na farko dan Asara ce take afkuwa kan Asara duk abinda Audun ya taba seya lalace Binta ta samu nayi ta ringa kwakwazo ai damab ta faɗa ya auro me Farar Ƙafa beji ba. Yakubu ya samu Audu yake tambayarsa "Anya kuwa Audu kana fitar da zakka yanda take idan munyi lissafi?" Cikin tsananin damuwa Audu yake ce masa "Allah shine shaidata dukda bani da cikakken sani akan kasafin Zakka shiyasa ma bana fitarwa da kaina nake baka, kuma wlh Duk idan muka fitarda lissafin shekara yanda kace a fitar din nan haka nake cirewa da hannuna nake rabawa dan karma na bawa wani yayi ha'inci ya rage sannan ka san muna fitarda sadaka daban itama haka ake hadawa a rabar nidai na yarda wannan jarabawa ce kawai daga ubangiji ina kuma roƙon daya bani ikon cinyewa" "Hakane, na godewa Allah daya sa ka yarda cewa duk wani tsanani daga shine haka kuma sauƙi ma daga gareshi ne. Kaci gaba da Addu'a muma muna tayaka karka kuskura ka bari wata maganar banza tayi tasiri a ranka ace maka wani ya maka Asiri ko wani abu, ka ƙaddara Allahn daya baka Arziƙin shine ya jarabceka akansa". Kwanan Hadiza Ashirin da bakwai da haihuwa Aisha ma ta haihu ta samu Mace. A gida ta haihu daga ita se Bilki da kuma Unguwar zoman da aka kira dan Audu baya nan kuma babu mota balle a kaita Asibiti kuma Allah ya bata da sauƙi ta samu yarta Kyakykyawa me kama da ita. Binta na daki tana fama da kanta dan itama ta kusa Lantana ta kwaza mata zancen haihuwar, tayi wata dariya harda buga ƙafa tana cewa "Ita kuma da ƙafar hagu ta shigo kowa na farawa da Magaji shine zata haifo mace? Koda yake na godewa Allah, Allah yasa in ma zata cigaba da haihuwar tayita jera irinta" Lantana ta tayata sukayita izgilanci akan Ikon Allah. Da Audu ya dawo ya tarar da haihuwar, farin cikin jin Mace aka haifa ya wanke masa kaso hamsin na damuwar da yake kwana yana tashi a cikinta. Ya fita ya samo mota suka tafi Asibiti, su kadai yasa aka maido shi kuma ya tafi bakin Asibitin Nasarawa inda suke da zuwa Binta siyayyar Haihuwa dan rigar da aka sanyawa Jinjirar bashi ya siya ba be kuma san inda Aisha ta sameta ba halin daya shiga yasa duk ya manta da wai ana da buƙatar wasu abubuwan na haihuwa Hadiza ma se bayan data haihun ya basu kudi suka siyo abinda ya sawwaƙa tunda ta san yanda Al'amuran suke wannan kuwa cewa yayi a hada masa kayan barka na Alfarma, aka ware masa wanda ze tafi dasu lokacin ragowar yace a hade masa su ze turo wanda ze ɗauka ya wuce da sauran. Binta data tsammaci Audu bazeyi murnar samun ƙaruwar Ɗiya mace ba se taga akasin haka, murna sosai ya ringayi, kwanan Aisha uku da haihuwa ta tafi wanka gida wanda daƙyar Audun ya bari gida ya rage Shida Binta se yara. Binta ta shiga zullumi, tunda Aisha ta haihu walwalar Audu ta ƙaru haka bashida wata hira seta yar jaririyar me suna Amina taci sunan Mahaifiyar Najibullahi yayiwa kara, basuyi sati biyu da tafiya ba ya kwashi yaran duka ya kaisu su gano Laila kamar yanda suke kiran yarinyar wannan ya ɗaga mata hankali ta kuma shiga zullumin to kodai itama ta haifi Mace ne saboda bata so ace wani Ɗa yafi nata shiga zuciyar Audu, amma da ta zauna tayi dogon Nazari seta watsar da waccen shawara, ita tana lissafine ne da abinda za'a mutu a bar mata, Yara Maza sune masu Gado duk wannan soyayyar da yakewa Lailan a banza tunda baze ɗauketa ya ɗora akan dukiyarsa ba da wannan ta watsar da tunanin haihuwar Mace taci gaba da lissafin zazzago Yara Maza. Tsiranta da Aisha kwana goma sha tara ta haihu a Asibiti ta samu ya mace kyakykyawa da ita tamkar Laila dan yarinyar na fadowa Nurse din data karbeta ta dagata tana cewa "Masha Allahu zankadi kin samu kyakykyawar yarinya da gani da Mahaifinta tayi kama dan ta fiki kyau" Nurse din ta gaya mata magana dan Binta ta gallabesu se dai idan bataje Awo ba amma tabbas se tayi faɗa da wata daga cikinsu. Zabura Binta tayi ta fizgi ƙafar Yar kamar wadda ta fizgi leda ko wani abu mara rai, tawara ƙafafun tana so ta tabbatar dagaske Mace ta haifa ko kuwa tsokanarta sukeyi data tabbatar din kuwa seta saki yar Nurses da basu gama dawowa daga mamakin fincikar da tayiwa ƙafar yarinyar ba suka dulmiya cikin na sakinta da tayi ba taredadamuwar zata faɗi a ƙasa ba. Kuka ta fashe dashi bayan data koma ta kwanta. Nurse ɗin data cafe yar ta kalleta cikin ɓacin rai tace "Amma kedai anyi yar ku*****ba, banda ke mahaukaciya ce dabba ki fizgi ƙafar Jinjira haka bakya ko tsoron ki ji mata ciwo sannan ki saketa a ƙasa? Wlh badan mu muka karɓi haihuwarki ba da nace sato yarinyar nan kikayi" "To kice mana, idan ma kina sonta ki riƙe na baki kuma karki sake zagina wlh dan na fiki iya tashanci" Binta ta hayayyaƙo mata, matar zata sake magana sauran suka tareta sukace ta barta da alama tana da taɓi a ƙwaƙwalwarta. "Sedai uwarku ce me taɓi a ƙwaƙwalwa bani ba" ta bisu da zagi sanda suka fita taci gaba da kukan ta. Haka suka tattaro suka dawo gida abin dai babu daɗi yanda Binta ta ringayi kamar me taɓin hankali duk saboda ta haifi Mace wannan fincika da tayiwa ƙafar Nazira ita tayi sanadiyyar Nakasarta wanda ba'a gane ba har seda ta kai munzalin tafiya sannan bayan dogon bincike likitoci suka gano wasu ƙananan jijiyoyin dake riƙe Sangalalen ƙafa da tafin ƙafarta ne a tsinke shiya nakastata ya zama ƙafar bata ɗaguwa sedai ta jata a ƙasa. Lokaci daya Hadiza da Aisha suka dawo, tafiyarsu lamuran Asare Asaren da Audu yakeyi ukayi sauƙi, suna dawowa tamkar an watsawa wuta fetur abu ya koma sabo farfaɗowar daya fara aka sake kwanciya rigijin harma abin yafi nada muni. Akace zuciya bata da ƙashi balle kuma irin ta Audu me cike da wasi wasi a hankali se famfon da Binta take masa akan ya auro masu fararen ƙafa ya fara tasiri a zuciyarsa. Ya fara tsangwamar Hadiza da Aisha domin a cikinsu ne yake ganin akwai silar taɓarɓarewar Arziƙinsa, kyara, hantara, wulaƙanci ya fara yawa, Hadiza bata shiru idan ya mata ramawa takeyi daman Binta bata isheta kallo ba dan tasan gamonsu Aisha ce take masa shiru dan haka diban Albarkar tasa yaso yafi yawa akanta musamman da Binta ke yawan cewa daman an fi samun masu farar ƙafar cikin mata masu shiru shiru kuma ai data tafi wankan gida abubuwa sun farfaɗo amma tana dawowa ta dawo da tsiyarta. Abu dai gaba yakeyi kullum ba baya ba, idan yayi kamar yabi ta Binta yaje ayi masa istahara a fayyace masa wwacece silar rugujewar Arziƙinsa se kuma ya tuna nasihar Yakubu dayace jarabawa ce saga Allah idan yayi haƙuri a sannu komai ze zama tarihi seya kanne yaci gaba da Addu'ar neman ɗauki daga ubangiji. Cikin wannan yanayi aka cinye shekara guda wanda a kullum ta Allah abin zama yake jiya tafi yau, Audu da harya fara mance lissafin abubuwan daya mallaka se gashi a hankali ya fara ɗaga kadarorinsa yana siyarwa a ƙoƙarinsa nason farfaɗo da harkar Mansa dake neman durƙushewa baki daya ya saki komai ya mayar da hankali akanta domin itace ƙarfin tattalin Arziƙinsa. Binta ce takai wa mahaifinta rahoton abinda yake faruwa da Audun, shiri tayi ta kwashi kayanta domin tafiyar da tayi bata saka ran zata dawo ba, to ta dawo tayi me? Arziƙin da take zaman gadi yana shirin bin rariya wahala na doko musu sallama ita kam bada ita za'ayi wannan zaman ba. Alhaji Zakariyya ya tashi ɗan aike takanas aka kira masa Audu, sun tattauna amma a duk maganar da sukayi ya kasa gano musabbabin wannan Asara dake hawan Audu kamar wanda akayiwa Baki haka nan be bi takan shirmen Binta ba ya sake daukar Kudade masu kaurin gaske ya bashi yace kuma duk in wata matsala ta tashi karya jinkirta ya je gareshi, wannan karamci na Alhaji Zakariyya ya ƙara samarwa da Binta gurin zama a zuciyarsa domin ya sani Allah ne ya haɗa shi da Alhajin amma Auran Binta na daga abinda ya ƙara dankon zumunta a tsakaninsu kuma duk abinda zeyi masa zeyi dan Allah kuma saboda yana auran yarsa, wannan tasa ya ƙara kulla aniyar riƙe Binta dakyau domin bashida wata hanya da ze sakawa da Alhajin sama da hakan tunda duk sanda zwje gurinsa se yayi masa tanbihin ya kula masa da Binta karya dubi halinta. Wannan kudi da Alhaji Zakariyya ya bawa Audu basuje ko ina ba yana dawowa Kano wani Abokinsa yayi masa tallar Farin wake, a shekarar an samu ƙarancinsa acan wani ƙauye suka samoshi yace su siya da yawa su ajiye zuwa A kwana biyu idan farashi ya hau su fitar su siyar dashi su samu riba. Audu be taɓa yin irin wannan kasuwancin ba dan ko wani yaji ze siyi kaya ya ɓoye zuwa yayi tsada sannan ya siyar se yayi magana ya nuna masa rashin dacewar hakan amma a halin da yake ciki yanzu ta yanda ze farfado da jarinsa kawai yakeyi shiyasa ba tareda dogon tunani ba ya siyo wake aka jibge a suto, ba'a rufe watanni uku ba wake yayi muguwar tsada ya ninka kudinsa sau biyu akan abinda suka siyeshi lafiya lau Alhaji Mala Abokin Audu ya kwashe wakensa ya kai Kasuwa ana bude store din da kayan Audu suke aka tarar da wake dai babu na moro Ƙwari sun masa kaca kaca dayawa har ya fara yin gari tsabar yanda ya lalace kamar wanda ya shekara biyar a ajiye. Hankalin Audu yayi ƙololuwar tashi da wannan Al'amari, Alhaji Mala da Bashir suka sake jaddada masa tabbas idan ba Asiri ba to cikin matansa akwai me Baƙar ƙafa a tasu falsafar. Mala yace ya shirya ze kaishi gurin Malaminsa duk abinda ake ciki ze fayyace masa, yace Malamin yayi tafiya nan da sati ze dawo shima daman zeje dan akwai tafiya da zeyi yana so a bashi sa'a. "Ai Ba'a zama haka Alhaji Audu yanda mutane suka ɓaci da jefw jefe wani ido kawai ze saka maka kaga komai naka ya tasamma lalacewa idan kayi sake magauta se sun kaika ƙas wlh kana kallon dai yanda abubuwa suke tafiyar maka kai base an ce maka da wani abu a ƙasa ba, idan ka biye ta wannan Yayan naka kana ji kana gani sedai ka koma jiran wa wani shago ana sammaka na cefane sunanka ya tashi daga sahun matasan masu kudi ka koma layin yan karayar Arziƙi" Inji Mala. Yana komawa gida ranar Binta ce take da girki, damuwa ta masa yawa yanzun shiyasa abu da yawa ba s an tambayeshi ba yana zaune zeyita rattabo zance kamar wanda kansa ya kwance. "Ina za'a jira har nan da sati ai ka tashi kawai kaje nan gurin Malam Salisu Mijin Lantana, ba tuntuni nake gaya maka ba amma kaƙi jin ta tawa ai yanzu da aka faɗa maka a waje ka yarda. Bari kaga inje in gano maka idan yana nan ai ba'a bori da sanyin jiki wlh gara asan abinda ake ciki" Binta ta faɗa tana saɓar Hijabi. Audu bashida zaɓi a wannan gaɓar ruwan kashe gobara kawai yake buƙata shiyasa be hanata ba, Hadiza na zaune tsakar gida kan tabarma tana cin Abinci garin da dan zafi zafi ga tsohon cikin da take dashi ya ƙara mata jin zafin Binta ta wuceta tana cewa "Maza kici gobe sedai kici a gidan me dattin hula". Can ta samu Lantana suka gama ƙulla yanda za'ayi Lantana ta shiga ta zayyanewa Malam Salisu yace babu damuwa duk yanda tace hakan za'ayi. Seda sawu ya fara daukewa Sha daya saura kafin Audu ya tafi gidan Malam kamar wani munafuki, Malam Salisu ya tambayeshi sunan sa dana Matayen nasa gaba ɗaya ya gama zana ƙasarsa yana jan wani kwandalelen carbi se muzurai yake da ido yana motsa baki yayi zane ya share yafi sau biyar kafin ya kalli Audu yace "Gaskiya Alhaji akwai gagarumar matsala, wai ma ya akayi haka wannan Aure babu bincike?" "Kamar yaya? Anyi bincike mana" Audun ya bashi amsa yana kallonsa a wani ɗage, Malam Salisu ya murmusa yana cigaba da zanen sa yace "Ba binciken halayya ko Asali nake nufi ba, Aa burujin ƙasa. Ya kamata ace in za'ayi Auran Alhaji a ringa bincikawa aga taurari matar ya suke zasuyi daidai da naka ko kuwa? Kamar dai yanzu kaga ita ta farin Fatsuma Binta kace sunanta ko? Wannan mahadin Arziƙi ce. Kaga kai Tauraronka wuta ne, ita kuma Iska ce, ya kaga wuta a lokacin bazara yanda iska take fifitata inta ringaci balbal ai Allah kadai ke iya kasheta to haka ne hadin naku taurarinta suna ingiza Arziƙinka zeyita hauhawa ne to kuma se akayi rashin dace ita Aishatul Humaira taurarinta na Ƙasa ne, wuta kuwa da an yafa mata ƙasa ai mutiwa takeyi to me kankat kuma Hadizatul kubura ita taurarin ruwa ne shiyasa da suka hadu su biyu se ƙarfinsu ya danne na fatsuma suke neman nakastaka kuma in har ba'a dauki mataki ba gaskiya Alhaji abin bazeyi kyau ba dan abinda ƙasar nan take nunamun idan ba'ayi da gaske ba har rigar sawa ka fita seka wayi gari baka da me kyau abinci kuwa wata rana se an kwana ba'a ci ba sannan yawan haihuwarsu yanwan Talaucin da zasu cigaba da saukar maka a gida". Ranar kwana zaune Audu yayi yana ƙullawa da kwancewa, Binta bata tambayeshi yanda sukayi ba domin ita ta tsara komai se dariya take a cikin bargo dan ta saddaƙar gobe daga Hadiza har Aisha kwanan gidajen tsoffinsu zasuyi. Washe gari da duku duku ya mata sallama yace ya tafi Bechi, be ko bi takan sauran matan ba, yara da suke gaidashi ma be iya amsawa ba ya fita burinsa ya isa Bechi ya samu Hashimu domin wannan sabgarsa ce shine yasan takan Malamai. Ya isa Bechi be zarce ko ina ba se gidan Hashimun yayi rashin sa'a baya nan amma inji Jamila ba dadewa zeyi ba dan yace a aje masa abincin rana. A tsakar gidan ya zauna kan Turmi tsabar halin da yake ciki ya gagara shiga turakar Hashimun da tace ta masa shimfiɗa ta aje masa ruwa da fura. Seda akayi Azahar Hashimu ya shigo, an gaya masa anga wucewar Audu amma be yarda ba dan har can gida ya ratsa be ganshi ba se gashi ya tarar dashi a tsakar gida kan Turmi fuskarsa ta gama bayyanar da tashin hankalin da yake ciki. A taƙaice ya masa bayani babu bata lokaci ya goyeshi a mashin suka tafi wani dan ƙauye dake gabansu kadan. Bayanan Malam Salisu sunyi kamanceceniya da juna sedai an saɓa lamba a wasu guraren kamar Taurarin Aisha da Binta dashi bafulatanin yace masa taurarinsu iri daya ne da nasa dan haka babu matsala a hadinsu Hadizan dai itace me matsalar kuma akasin da aka samu Taurarinta nada matuƙar haske shiyasa ta tasiranci duka su ukun suke karbar gashi. Bala'un da Dan fulani ya jere masa je afka idan ne rabu da ita ba sun zarce na Malam Salisu, Hashimu yace "Dama a garin aure aure tun mutum na kwaso Arziƙi harse ya ɗebo tsiya gashi dai ka gani ai se ka san abinyi tunda wuri dan duk abinda Malam Sallau ya faɗa da wuya kaga be faru ba, seda ya hanani Auran Saude naƙi gashi ko ina karbar sakamakona" "Aishi ba Allah bane bare kace duk abinda ya faɗa seya tabbata" Audun ya bashi amsa. Hashimu yayi dariyar rainin hankali yace "Na fika sanin haka, amma tunda muka yarda dashi har muka zo tambaya gabansa ai magana ta ƙare, ya rahe naka ka ɗauki matakin daya dace" a gurin sukayi sallama Audu ya juyo Kano zuciyarsa fal wasi wasi. Ya daukarwa Yakubu Alƙawarin baze sake sakin wata mace ba gashi kuma yanzu dole ta saka zeyi sakin kuma ya san duk ta yanda zeyiwa Yakubu bayani baze taba fahimtarsa ba. Maganar gaskiya kuma baze zauna yanaji yana gani ya rasa komai nasa dalilin wata mace ba. Page 32 Bayan daya dawo a ɗakin Hadizan ya sauka ta karbi girki, ya ringa kallonta ga Aminu dake da shekara daya da watanni biyu ga ciki da ko yau ko gobe zata iya haifeshi. Tausayinta ya kamashi duk da halin da take ciki amma tana ta kaida kawowa tana hada masa abinci. A zamantakewa Hadiza bata da laifi, mace ce ta gaske dan ze iya cewa a duk matan da ya aura babu tsayayya kamarta. Ta iya kula dashi haka tsakaninta da sauran Matansa tana mu'amalantar kowacce da sigar data zo mata. Duk bala'in Binta ta sarara mata sedai tayi a bayan idonta amma ya zeyi? Shidai baze cigaba da zama da ita ba domin ko ita idan zata masa Adalci inta san itace matsalarsa yaci ta nemi rabuwa dashi da kanta kawai su haƙura da juna ze saketa badan baya sonta ba sedai dan hakan shine maslaharsu baki daya ze kuma cigaba da daukar nauyinta har iyakar rai ze cigaba dayi mata duk abinda ya kamata tamkar tana gidansa. Da daddare harsun kwanta ya tashi zaune, cikin nutsuwar dashi kansa besan yana da ita ba ua shiga yiwa Hadiza bayanin halin da ake ciki. "Kuma ka yarda? Tamkar fa kayi shirka ne Audu ka tara sani da Allah. Ya za'ayi ace maka nice silar Karayar Arziƙinka kuma ka yarda shin Allah baya jarabtar mutum haka nan dole se wani abu ya zama sila?" faɗa hawaye ma zubo mata. Audu ya murtuke fuska, yasan gaskiya ta fada to amma magana ta ƙare tunda har aka gaya masa kuma ya yarda dan haka yace "Kinga muyi haƙuri kawai nidai na rigada na yanke hukunci na sakeki saki biyu, kina da zaɓi na kici gaba da zama a gidan nan ba se lallai mutane sun san na sake ki bama". Kallon kayi hauka tayi masa kafin ta miƙe tana kuka ta shiga haɗa kaya, se yayi fakare kuma yana kallonta duk yaji babu dadi, da ace da wata hanyar da ze magance matsalar sa ba lallai seta rabuqa da Hadiza ba daya bi amma babu yanda ya iya. Washe gari ta bar gidan, Binta ta ringa rawa tana shewa, satin Hadiza ɗaya da tafiya ta haifi Aliyu, tayi maza biyu kenan sunyi kankan kan da Binta wadda keda cikin da na biyar Aisha nada na biyu a sannan. Tun Binta na saka ran Aisha zata bi bayan Hadiza har suka haihu wannan karon ma kusan tare tsiran kwana goma tsakaninsu Binta ta fara haihuwa ta samu Yakubu takwaran Alƙali, seda Babanta ya shiga maganar kafin ta haƙura da wannan takwara da aka mata da babban maƙiyinta Aisha kuma Abdullahi suna kiransa Sarki Al'amuran Audu kuma suka fara daidaita sannu a hankali Arziƙi yaci gaba da bunƙasa harya fi nada. Aisha da Binta sukaci gaba da jera haihuwa, bayan su Yakubu Binta ta haifi Aisha wadda Audu yayiwa ƙanwarsa takwara ta rasu wata daya kafin haihuqar Bintan itama yarinyar watanta hudu ta koma a lokacin kuma Aisha ta haifi Ahmad shekararsa daya cif Binta ta haifi Jafar se suka sake jera haihuwa Binta ce ta fara ta haifi Faisal Aisha kuma Salim, shekara biyu suka sake yin mata duk su biyun Binta ta samu Hafsa suna kiranta Hajiya Ƙarama ita kuma Aisha Khadija. Daga nan Binta haihuwar ta dan tsayawa Binta har seda Aisha ta haifi Maimuna da Aslamiyya sanan Binta ta sake haifar Bashir da Lawal, burinta ya cika, ta tara yaya maza zarata har guda shida tafi kowa Kaso cikin dukiyar Audu. Tsakanin Binta da Aisha zaman dai ba'a cewa komai, Binta bata fasa halinta ba ita kuma Aishar seta zame mata ƙarfen ƙafa domin dukta inda ta buga babu riba tayi tuggun tayi munafurcin amma abun yaƙi yaci. Audun da take taƙamar data san Lagonsa se Aishar ta fita bin yanda yake so domin zama tayi tamkar ruwa a cikinsu, hannu idan an saka mata ba zata ciza ba, duk abinda Binta zatace tayi idan ta titsiyeta ba zata musa ba koda batayin ba zata bashi haƙuri ta kuma baiwa Bintan ta yanda in Binta ta sake tada maganar daga baya a maimakon yaga laifin Aisha se faɗan ya juya kanta yace ta fiya son tada zaune tsaye. Halin Aisha kuma ba Munafurci bane ko Kissa irin ta Binta Aa haka Allah yayita da sanyi, sedai nata sanyi ya zame mata Alkhairi ba irin na Bara'atu na haka ita bata ɗauki wargi ko rainin da har Binta zata bautar da ita ba kallo

Chapter 31 of 32