daya".
Tirqashi, wasa farin girki
Page 15
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
"Allah ka gani babu saka hannuna a cikin wannan al'amarin, Allah karkasa haqqin baiwar Allan nan da suka dauka ya bibiyeni" Ummu ta fada bayan data gamajin abinda ya gigita mata tunani. Da safiyar sunan aka kirata daga gurin aikinsu, ita din yar jarida ce kasancewar ta dauki uzuri ta tafi Kano se kuma wani aiki ya taso dan haka manajansu ya kira akan taje a maimakon ace se an taso wani daga Kadunan yazo tunda tana tareda abin nadar rahoto da sauran abubuwan buqata shiyasa ta tafi bata san badaqalar da aka kwasa ba seda ta dawo kuma da ace tana nan tabbas da bata goyi bayan abinda suka aikata ba dan ita din itace Mahaifinsu sak gurin dattako. Ta Jinjina abin ta kumayi matuqar mamakin yanda yan uwan nata suka iya aikata wannan ta'asa.
Idanunta dauke da hawaye ta kalli Babbar Yayarsu sakina da duk itama abin duniya ya isheta yace
"Yanzu Yaya harda ke? Kika bada shaidar zur? Kuna tsammanin idan Dady ko Mama sukaji maganar nan me zasu ce? Wannan wane irin zalunci ne yau koda ace dagaske matar nan ta aikata abinda kuka ce ai wlh ku masu rufa mata Asiri ne idan yaso ku barta da Allah ya kamata da haqqin ran data dauka amma bataji ba bata gani ba kun laqa mata sharrin da ze bibiyrta har yaya da jikoki sannan kunyi sanadin datse mata igiyoyin aure wlh ku kuka da kanku ku kuma shirya ta inda haqqin ta ze bibiyeku domin kuwa Allah baya bacci se ya saka mata kuma. Ke kuma( ta juya kan Binta) tun kina da sauran dama ki koma ga Allah ki bar wannan turbar da kika hau dan wlh babu inda zata kaiki se filin Nadama mara amfani da dana sani. Yanzu ba se anjima ba ki tashi kije ki gayawa Mijinku gaskiyar magana ki warware wannan qullin da kika yi, karki bari Yarinyar nan ta bar gidan nan dan wlh Binta ina jiye miki rayuwar da zakiyi a gaba wuyanki daure da haqqin ta, Kizo ki tarar da mata a gidanta ki gallabi rayuwarta ki hanata sakat da Mijinta meye ribarki a ciki?"
"Dan Allah Yaya Ummu ki riqe wa'azinki abinda ya faru dai ya rigada ya faru zance kuma Dady ko Mama sedai idan ke zaki fada musu kuma idan kika janyo suka mana baki kema se Allah ya saka mana akanki dan haka gara mu rufe maganar nan a inda ta faru Allah ya kiyaye gaba" Munira ta fada ganin sauran sunyi shiru har Bintan da Alama maganar Ummu tayi tasiri a zukatansu wannan ya basu qwarin Guiwa itama Bintan ta karkace tana cewa
"Allah ne ya kawo mun hanyar fitarta cikin sauqi babu abinda zan fadamasa wlh". Da dai Ummu ta tabbatar sunyi nisan da ba zasuji kira ba dole ta qyalesu, a iya saninta iyayensu basuyi musu kalar wannan tarbiyyar ba ba kuma tasan a inda suka samo ta ba tana kuma musu fatan shiriya a gurin Allah domin basu hau kan layin da ze bulle dasu ba.
A bangaren Bara'atu kuwa duniyar ta mata zafi, har ta dangana da cikin dakinta bayan jefa qafa take kawai badan tasan ina take zuwa ba. Ta zauna dabas a qasa, Balaraba da labari ya iske ta dan bata je zamanba itama ta zama kamar wata mutum mutumi saboda mamaki. Suna haka Hadiza qanwarta ta shiga dakin ta shiga sauke kayan Bara'atun tana zubawa a Jakunkuna cikin tsananin fushi.
"Wlh se sunga sakayyar mugun abunsu a kansu, shi kuma in sha Allahu har ya mutu yana nadamar wulaqantaki butulu wanda be san Halacci ba" haka Hadizan ta ringa fada tana zuba kaya ta hade mata komai tas dan daman kayan nata ba yawa ne dasu yanzu ba ta kwashe da yawan suturunta ta kyautar kamar yanda ta saba duk sallah kuma zeyi mata dinkuna masu yawan gaske to Bana da abin yazo a zamanin binta kala uku ya mata se lokacin Bikin Saleh nan ma ya mata uku.
Hadiza ta gama hada kayan Bara'atu ta fara hade na yaran se a lokacin Balaraba ta iya bude baki tace
"Karki hada kayansu ki barsu a gidan ubansu babu inda zataje masa da Da"
"Bazan iya barin Yayana ba ba zata riqe su ba" Bara'atun ta fada tana fashewa da kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta. A mugun fusace Balaraba yace
"Ai ko kashe su zatayi se kin barsu, wlh ba zakiyi masa wahalar yaya ba yanda ya auro ki ke kadai ki tafi su zauna a gidan ubansu kuma dole ta wahalta musu, abinda tayi miki kuma Allah na gani seya saka miki ko ba dade ko bajima se taga sharrinta a kanta da ita da yan uwan nata gaba daya".
Haka aka kwana ana maida magana, washe gari Qarfe shida motar yan Bechi ta daga, Bara'atu kuma mota daban Yakubu ya nemo ta dauketa da kayanta tare dashi da Balaraba suka tafi banda yaran dan kamar yanda Balaraba tace ta barsu shima Yakubun da Asuba daya shiga yace a kira masa Bara'atun haka ya gaya mata ta zube masa Yayansa. Watsa watsa sukayi da Audu akan al'amarin, babu yanda beyi dashi akan ya janye furucinsa ba amma ya rantse akan baze maidata ba wannan tasa Yakubun barin gidan a cikin daren be kwana ba da Asuba kuma ya fita ya nemo mota aka balle kayan Gadon Bara'atun tas yasa aka lode su sannan ya samo qarama suka tafi a ciki zuciyarsa cike da baqin ciki da takaicin abinda Qanin nasa yayi. Ya kuma yi rantsuwar cewar babu shi babu duk wata sabga data shafi gidan Audu.
Abin seya zamarwa Bara'atu duka biyu domin kafin su isa wanda suka fara tafiya suna kai labari kamar wutar daji ya yadu cewar hassada tasa ta kashe jariri saboda yayanta kadai take so su gaji Audu. Mutane da abin mamaki wasu tamkar a gabansu akayi se kace wani hawan sallah haka aka cika qofar gidansu ana jiran aga ta inda zata bullo tunda ance ya saketa ta hado kayanta tana hanya, aiko da suka isa seda Yakubu ya hada da dura Ashar abinda ba halinsa ba kafin matan da sukayi dandazo suka watse da sabuwar gulmar cewa magana ta tabbata gata nan harda kayanta gaba daya da alama auran ya qare saki uku yayi mata.
Seda tayi matuqar dagaske kafin ta iya shanye wannan jarabawa. Yanda mata suke musu zuruftu suna yada musu magana ita da mahaifiyarta har ciwo ya kwantar da Innar tata. Babanta kuwa nasa bala'in yafi na kowa dan da farko ma cewa yayi ba zata zauna masa a gida ba. Duk kuwa sa Yakubu ya sameshi qafa da qafa ya gaya masa komai daya faru amma mutumin nan ya hau kan qarya ya zauna ya dora mata laifi har yana cewa uwarta ce ta sakata. Watanta biyu a gida Audu ya tattaro yaran ya aiko mata dasu, tana zaune se gani tayi ana shiga da kayansu da buhunhunan abinci ta tambayesu su dawa sukace Direban Babansu ne ya kawo su a cikin kayansu taga kudi, kudade masu yawan gaske se farar takarda da gajeran rubutu a jiki.
"Kiyi amfani dasu gurin kulawa da yarana duk wata zan ringa aiko musu da abun buqata Aminu ze kai su makaranta a nan" abinda takaddar ta qunsa kenan. Hawaye suka wanke mata fuska, wato dagaske Audu ya cireta daga rayuwarsa kenan baze bata damar wanke kanta ba tana roqon Allah daya bayyana gaskiyar abinda ya faru badan tana so ta koma gidan Audu ba aa sedan ya cire zargin kisan kai daya dora mata a ransa.
******************************
A gidan Audu kuwa duniya sabuwa Binta ta bude ta kori Bara'atu ciwon idonta yanzu bata da wata damuwa ta samu gida ta samu Miji yanda ya kamata musamman wannan abin daya faru yasaka yake qara riritata yana lallabata da sunan tausayinta yakeji akan abinda ya faru. Da farko da taga an bar yaran bata damu ba dan ta qulle a ranta ta samu bayi sedai yanda taga Audun ya ninka kulawar da yake musu sanda uwarsu tana nan yasa hankalinta ya tashi dan haka tasan yanda tayi Abdullahi ya tafi makarantar kwana wanda daman an gama masa shirin hakan tafiyar Bara'atu tasa Audu yace an fasa nan ta san yanda tayi ya tafi daman tare suke kwana dasu Babangida shine dawainiyarsu idan Mairo tazo ta karba babu abinda Bintan take musu se Audu na gida dan haka Abdullahi bayan tafiyar Abdullahi makaranta ya zaman yaran su kadai suke kwana a daki, sun saba ana tashinsu suyi fitsari ko basu ruwa da sauran abubuwa yanzun basu da meyi musu cikin dare haka Babannan ze tashi yayi ta koke koke sedai Audun ya sakko yaji dasu tana kwance se ta fake da cewar nauyin bacci ne da ita bama ta jiyo su, randa aka samu akasi suka mata fitsari a kwance ranar wuni zatayi yana gana musu Azaba idan ya fita in ya dawo kuma ta ringa cewa ita ta kasa gane kan yaran nan, qana na dasu amma se nunkufurci tamkar uwarsu haka suke mata duk yanda take jansu sunqi sake mata.
Ya gasgata hakan saboda ko a gabansa ta jasu basa zuwa dalili kuwa Izayar da take musu idan baya nan kuma tace in suka fada seta yanka su, daya gaji da dawainiya dasu da dare baya samun bacci ya yanke shawarar a nemo me aiki da zata ringa kwana nan kuma tace bata yarda ba qarshe dai ya yanke shawarar mayarwa da uwarsu su tunda yasan itama ba a sonta ta barsu ba Yakubu ne ya tilasta mata wanda tunda ya koma a Lagos ko sau daya basuyi magana ba, fushi yake na gaske dashi shi kuma bega abinda yayi me girman da har Yakubu da sauran yan uwansa zasuyi fushi dashi haka ba. Basu dubi abinda ita Bara'atun ta aikata ba, idan daya bar Binta niyya tayi ta daga maganar zuwa Kotu sakin da yayiwa Bara'atu ne ya rage kaifin rigimar amma kowa be duba hakan ba laifinsa ake gani hatta da Alhaji Zakariyya Baban Bintan seda yayi masa fada sosai akan abinda yayi dukda ya fahimci da alama Alhajin be san musabbabin sakin ba.
Kwanci tashi har aka shekara da rabuwar Audu da Bara'atu a sannan kuma Binta ta sake haihuwa aka maida mata da sunan Babanta Zakariyya, rayuwa taci gaba da gungurawa, budi da Arziqi suna qara zuwarwa Audu a shekarar kuma yaje aikin Hajji tareda Yaya Baba babban Yayansu da Goggo Fadi, da Yakubu yaso suyi tafiyar amma yace ba zashi ba dan har sannan be sauka daga fushin da yayi da Audun ba, wannan dalili ya saka Audun bawa Yaya Baba kujerar ita kuma Goggo Fadi Yakubu ne yace ya biya mata, a cewarsa iyayensu Malam da Dada duk basuyi tsahon ran da zasuci arziqinsa ba dan haka yayi mata yasan zasuyi Alfahari dashi a inda yake ai kuwa taji dadi yayanta sunji dadi suka ringa masa Addu'a kamar me wannan abun da yayi ya saka Yan uwan zage jin zafinsa akan rabuwa da Bara'atu, dukda tafiyar ba'a son ran Binta akayita ba amma ba yanda ta iya tunda tana da danyan Jego a sannan haka sukaje suka dawo Audu ya koma Alhaji Audu.
Bayan dawowar Audu daga aikin Hajji ya tattara kudade daya dade yana tarawa tun bayan daya fara harkar mai. Kaduna ya nufa dasu ya samu Alhaji Zakariyya. Sanda Alhajin ya gama sauraron jawabinsa tsaf yana kallonsa yana murmushi. Shikam haka nan Allah ya dora masa qaunar Audun, tamkar sun hada jini ta wani gurin.
"Da gidan Mai, da jarin dana baka duk kyautace Abdullahi shiyasa hatta da filin da sunanka aka siyeshi haka nan na baka zabin sunan da za'a sakawa Kamfaninka. Ina fatan ya zame maka hanyar riqe kanka da Ahalinka gaba daya kuma Al'umar annabi su amfana da dukiyarka" Alhajin ya fada yana kallonsa. Haka Audu ya dawo Kano cike da mamakin karamci irin na Alhaji Zakariyya, wannan ya saka ya qara daura aniyar kulawa da Binta domin yana ganin babu wani abu da zeyiwa Alajin ya biyashi tamkar kyautata mata.
Yanayin Budi da sana'arsa ta sakashi haduwa da sababbin Abokanai matasa masu tashen kudi kamarsa a lokacin, kamar kuma yanda rayuwa take a kowanne fanni mutum yakan hadu da Abokanai na kwarai dana banza, ya rage a karankanka kayiwa kanka Alqalanci kabi wanda Tarbiyya da dabi'arku tazo daidai to hakan ce ta faru da Audu yayi sababbin Abokanai da suka kasance Yan cikin kwaryar Birni wayayyu kuma yan Boko sun fantsama cikin harkar Man fetur domin sannan itace harka data bullo da akeyin kudi da ita a dare daya.
Alhaji Bashir da Alhaji Ali sune mutum biyu da suka fi shaquwa da Audu saboda koda tafiya ta kamasu zuwa inda suke dakko Mai tare sukeyi sannan suna wasu sabgogin Kamar fitar Kayayyaki irinsu Cocoa da Qaro zuwa qasashen dake da buqatarsu. Wannan shawarar Audu ce dan tun yana zaman bakin rimi yakan tsince hirar ana zuwa daga waje ana siyan wadannan Abubuwa. A yawace yawacen kasuwancins yasan duk inda ake samunsu dan haka suna haduwa da Alhaji Bashir wanda shi kuma yana da kyakykyawar Alaqa da wasu Turawa dan a qasar waje yayi karatu nan da nan aka qulla kasuwancin se Ali ya shigo ciki shi kuma ya nemo musu masu siyan Qaro nan da nan Kasuwa ta bude musu Arziqi kamar ana ruwansa ta ko ina zubowa yakeyi.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Audu be tsaya iya nan ba yana Noma, manyan gonaki ya siya a Bechi sannan a Gadonsu da yake juyawa an fitar kowa ya siya masa tasa Bilki da Aisha sun bawa Mazajensu suna kula musu da ita shi kuma ya karbi hayar ta Yakubu data Baballiya yana Nomasu, babu abinda baya Nomawa haka nan be yada saide saiden Kasuwa ba Shagonsa na kayan yara da mata na nan ya qara bunqasa ya zuba yara suna kula masa dasu.
Alhaji Bashir shine me rawar kai a cikin guruf dinsu kuma shi ya fara diban Audu suna yawo a gari, shine rakashi gurin waccen yau gobe gurin waccan, tun yana zuwa rakiya kawai har ya zama shima ya fara kule kulen Mata. Dukda dai iyakar hirace take hadashi dasu sabanin Abokin nasa da yake taba shashanci da Matan. Ya kashe musu kudi su biyashi da Jikinsu bayan harkar mata har ruwa yana korawa kuma duk abubuwan da yakeyi yakan nunawa Audu hakan ba komai bane, a nan Nigeria ne ake daukarsu a wani Abu amma yej turai yaga rayuwa kuma menene amfanin neman da sukeyi idan ba zasuji dadin rayuwarsu ba?
Ali ma yana kula mata amma shima kamar Audun hirace kawai amma kuma su ukun ko da yaushe suna tare, duk yawon da Bashir zeje zasu rakashi su suka bude masa Ido da zuwa Hotels, su kama daki su wuni suna hira da yan mata a kashe musu kudi. A tun ana fitar rana har ta kai an koma ta dare. Idan ya dawo gida da Magriba ya gama uzurinsa ze salla wanka ya fita, Binta ta bararraje a gida hankali kwance ita kadai Babu Bara'atu. Bata wani damuwa da fitar tasa tunda tana samun duk wasu buqatunta idan ya zauna a gidan ma.me zeyi mata kuma a tunaninta be kawo mata cewar gurin Mata yake zuwa ba musamman data san yana harkoki da yawa yanzun.
A irin wannan yawaye yawacen Bashir ya kwashe su gari ya gari har kwantagora, basu san inda zasu ba seda suka gansu tsulum a gidan Karuwai, wai Ashe Ajo za'ayi shi kuma Bashir din da yake babban kwastoma ne kusan duk wata Karuwa data amsa sunanta a Kano yasan da zamanta to dalilinsa na zuwa kenan harya kwashi Abokanansa suka tafi tare. Ashe qaddarar Haduwa da Zubaida Yar Dagwas ce takai Audun Kwantagora, kyakykyawar yarinya Baqa me matsakaicin jiki yana ganinta Bara'atu ta fado masa a rai, idan yace be damu da rabuwarsu ba yayi qarya amma yakan danne zuciyarsa da cewar tayi abinda ya cancanci ya rabu da ita.
A yanda ya fahimta ko a cikin Karuwan Zubaida me Aji ce domin daga shigarta zuwa yanda take kamewa a gefe tanawa kowa kallon be isa ba ga Maza nata zuwa suna mata magana amma taqi koda yi musu kallo arziqi balle ta karbi tayinsu, bayan an tashi daga Ajo Bashir ya wuce sharholiyarsa Ali da Audu na zaune a dakin da suka sauka. Babu irin macen da Bashir be tura musu ba amma Ali ya kore su.
"Bana fatan na daukarwa Ahalina bashin zina dan ban san wanda ze biyashi ba, iya abinda mukeyi Allah ya yafe mana shima ina masa fatan ya shiryu ya dena abinda yakeyi" Ali ya fadawa Audu sanda yaga shaidan yana qoqarin ingizashi ya karbi tayin wata Kilaki datazo kansu tana duk wani abu data san zeja hankalin Namiji gareta, Alin ya mata korar kare.
"Nifa Ali da akwai yarinyar dana gani, kuma wlh ba sha'awarta nake ba ji nayi kamar sonta ya kamani a kallon farko" Audu ya fadawa Ali abinda yake zuciyarsa dan tunda ya zauna Tunanin Zubaidan yakeyi duk kuma macen data shiga se yayi fatan Allah sa idan ta fita ita ce zata biyo baya amma be ganta ba.
"A nan kaga macen da kake so? Ko kuma kawai kace mun kaima zaka fada ruwa" Ali ya fada yana gyara kwanciyarsa.
"Wallahi dagaske nakeyi, baka kuka da ita ba? Wata yar baqa haka ta saka jan kaya, dana kalleta se na ganta kamar Matata ta farko da muka rabu tunda na zauna a nan nake tunaninta" Audu ya sake fada. Ali ya juya masa baya yana cewa
"Lallai ka haukace Audu" daga haka yayi shiru. Audu kuwa be iya runtsawa ba se gabanin Asuba, tunanin Zubaida ya addabi ransa. Jin ta yakeyi a zuciyarsa kamar wadda ya shekara da sani abin tamkar Asiri a dan baccin da yayi kafin gari ya waye ma har mafarki ta yayi.
A daren ranar sun shirya washe gari zasu taho dukda Bashir be so ba sedai gari na wayewa Audu yacewa Ali su bari se gobe su tafi"
"Sedai na tafi na barku a nan dan ni banga abinda ze saka na qara kwana a gurin nan ba" Alin ya bashi amsa.
"To ka rakani na gwada sa'ata, idan ta kulani shikenan ko yau din zamu iya tafiya" cewar Audu. Kallonsa kawai Ali yayi dan lamarin Audun ya fara bashi tsoro. Ya tsoron kar maganar Hausawa ta tabbata da sukace zama da madaukin Kanwa na kawo farin kai, idan Audu ya dauki Halin Bashir to in beyi da wasa ba shima zasu jashi ciki dan haka ya kakkabe rigarsa ya fice daga dakin yana cewa shidai ya tafi ze hau motar Haya.
Qarfe goma suna tsaye bakin mota gaba dayansu, Bashir sunyi fada da Karuwar daya kwana da ita har taji masa ciwo da kwalba ya mata dukan mutuwa wannan fushin ya saka ya fasa qara kwanan da yayi niyya yace su tafi shi Ali daman harya fara cigiyar inda ze samu motar Kano yaga sun fito. Bashir na sallama da jama'ar sa Audu har ya shiga mazaunin Direba dan shi ze jasu saboda ciwon hannun Bashir sega Zubaida ta fito daga gidan taci kwalliya daurin nan kamar ze fadi saboda yanda ta tsikara shi hannu ta riqe da jaka madaidaiciya da zata ci kala a qalla Kala uku se qaranar jakar mata a daya hannun da alama wani gurin zataje kuma tafiyar kwana ce.
"Yar dagwas, an sauka daga sarautar kenan" Bashir ya fada yana kallonta, tayi far da ido, cikin yanga da iyayi tace
"Eh, ina kayi? Naga kamar tafiya zakayi ko?"
"Kano na nufa, kefa na ganki da jaka da alama balaguro zakiyi"
"Zan sauka a Zariya" ta fada tana wucewa motar, ta aje jakarta akan Boot ta wuce ta bude gaba ta shige kai kace motar tace. Bashir ne ya saka mata motar a Boot haka suka kamo hanya, duk yanda take daurewa seda ta biyesu ta shiga hirar, sun tsaya a hanya zasuyi sallah Audu ya samu damar yi mata magana shida ita.
"Kaga malam, nifa ba irin sauran masu Arhar da kuka saba tayawa bace" ta bashi amsa tana farfara ido ta wuce ta barshi a gurin yana murmushi kamar wawa. Dagaske sonta yake, irin soyayyar nan ma me zafi. Har qofar gidan da zataje suka sauketa a Zariya dukda tace su ajiyeta tun akan hanya.
"Nan ne sabuwar maboyar taki kenan? To sena rako Abokina" Bashir ya tsokaneta, ta harare shi kafin ta Audu tana taunar cingam qas qasa tace
"Nagode Samari, se wani jiqon"
"Shege Abokina wlh ka samu shiga, kasan uban nacin da nayi akan yarinyar nan kuwa amma taqi bani fuska? Kai bani kadai ba kowa mararinta yakeyi amma yarinyar nan yanda kasan kudi wahalar samu ne da ita, daga qusoahin gwamnati se Sarakuna take kulawa" Bashir ya fada yana dukan kafadar Audu.
Ali yaja tsaki yace
"Wlh kayiwa kanka fada karka kuskura ka bari shaidan ya maka ingiza me kantu nidai babu ruwana daga yau ma in sha Allah bazan sake binku fita irin wannan ba"
"Nifa na gaya maka sonta nakeyi dagaske" Audu ya fada bayan sun hau titi. Bashir ya ringa dariyar iskanci yana cewa
"A sannu dai duk zasu hau saiti, wato ina gaya muku dadin duniya a sha ruwa ga mata, kai Allah ka yafe mana kurakurenmu".
Haka har suka iso Kano.
Ba'a rufa sati ba ya kama hanyar Zariya ba tareda ya sanarwa da Abokanansa ba saboda yanda tunanin Zuby ya addabeshi, yaje gidan da suka ajiyeta wanda se sannan ya gane nan ma gidanmata masu zaman kansu ne, ya rasa ta inda ze fara nemanta. Har gurin Magajiyar gidan aka kaishi tace babu Zubaida a gidan haka ya haqura ya dawo Kano da qunar zuciya sedai duk yanda yayi akan ya yakiceta ya haqura da tunaninta abin yaci tura. Gaba daya ya shiga damuwa ya zaman har walwalarsa ta ragu. Da Binta ta matsa masa da tambaya se ya ce mata Asara yayi, aiko ta si ta fishi shiga tashin hankali ma dan Binta na son kudi, dukiyar Audu kuwa jinta take kamar tsokar jikinta a kullum zancenta Duk abinda yake dashi nata ne tunda itace sila shiyasa take baqin ciki idan yayi Alkhairi wa wasu, ta bangarenta kuwa duk abinda take dashi ko take samu babu me ci, hatta a karan kanta mugunta takeyiwa kanta dan da wani ya mori abu tareda ita gara ta haqura da abun itama.
Wata biyu Audu ya kwashe yana dakon soyayyar Zuby, dayaga abin baze fita daga ransa ba tilas ya samu Bashir ya roqeshi akan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 32