Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsakaninta da Iyayenta kuma yazo yana wulaqantata akan Matar daya hadu da ita daga baya tasan baya qaunarta tun sanda aka kashe mata Da amma be dauki matakin komai ba. Haka ya kwanta ransa duk babu dadi sedai da Asubahi da yar dagwas ta kaishi gari me nisa tuni ya manta da wata Binta da Emotional blackmail dinta. Tana can ta saki baki tana jiran ya bugo Asubanci yaci gaba da rarrashinta dan jiyan Data gama surutai bandaki ta shiga ta kulle yayi yayi ta fito taqi tace ya fitar mata a daki in ba haka ba zata kwana a ciki sannan ya tafi to ta dauka daya dawo masallaci ko kafin ma ya fita se shiga ya dubata amma taji muqus har gari ya waye tarwai se Tara saura na safe suka fito da Amarya yayi shirin fita, tana zaune kan barander dakinta Lantana na share tsakar gidan suka fito ta zube tana gaishe su. Kamar jiya yauma harda dan risinawar Zubaida ta mata ta gaidata, bata tanka ba ta zabga tsaki bata dai yi masifar data sababa shirun nata kuma se yaji babu dadi dan haka yacewa Zubaida yana zuwa. Falon Bintan ya shiga ya tsaya a tunaninsa zata bi bayansa amma shiru, ya leqo ya mata magana nan ma ci kanka bata ce masa ba wannan ya hasalashi ta wulaqantashi gaban me aiki dan haka ya fice fuu ko Adawo lafiyar da Zubaida take masa be amsa ba. "Zaki san ni ba sa'ar wasanki bace wlh yau se kin gane kurenki badai jiya ya ceceki ba? Yau naga ubanda ze kwaceki a hannuna" Binta ta fada tana miqewa bayan data tabbatar Audu ya fice daga gidan tabi bayan Zubaida data qarawa tafiyarta sauri jin abinda take fada, gudu ta saka ganin dagaske kamata take shirinyi tana fadawa daki ta turo qofa Binta ta saka hannu zata dannata ciki bisa tsautsayi ta datse mata yatsa da qarfi take ya fashe ya fara jini. Page 20 "Akan me zaki kulle qofa? Dukanki zatayi ko cizo da ze saka ki kulle qofa har ki hada da hannunta ki matse?" Audu ya fada cikin kaushi yana duban Zubaida dake durqushe gabansa kanta a Qasa Binta kuma na daga gefe tana yarfe hannu yatsanta data datse da qofa ya kumbura idanun nan sunyi fici fici da alamun tasha kuka ba kadan ba yau din. Audu na yin sallama Lantana da bata tafi ba ta zube a gabansa tana fada masa uwar dakin nata babu yanda take tana daki, hankali tashe ya doshi Dakota n nata can ya tarar da ita tayi zaman dirshan a qasa tana yarfe hannu tana kuka harda majina, shiri sukayi da Bintan akan hakan dukda dagaske take jin azabar ciwon yatsan amma tuggun da take so ta hada da faruwar hakan shi ya saka ta sake rakwarkwabewa ba iyakar zafin ciwon ba. Daya tambayeta ya akayi taji ciwon take ta gaya masa Zubaida ce, akan ta bita daki su sulhunta kamar yanda ya roqeta jiya akan tayi haquri ta kwantar da hankalinta su zauna lafiya to bayan tafiyarsa tayi tunani akan hakan kuma taga ya kamata ace tayi shine yau taje dakinta da niyyar ta bata haquri akan abinda tayi mata jiya a maimakon ta saurareta se kawai ta hau zaginta tace ta fitar mata a daki, data tsaya ta dafa qofar shine ta hada harda hannuta ta datse shi kuma kamar fulawar da aka zubawa Yeast ya shiga kumbura ya tafi fuuu ya kira Zubaidan nan gaban Binta ya titsiyeta yana tambayarta ba'asin dalilin rufe qofa. "Ni ba a sanina na bigeta ba kuskure ne" ta fada cikin sanyin murya, Binta ta zabura tace "Wlh qarya takeyi tana sane ai Lantana na gurin ka tambayeta kaji" "To a tambayi Lantanar mana in har zata fadi tsananinta da Allah ko ita ta san ba ina sane na bige miki hannu ba, sannan ni bani na nace ki shigar mun daki ba bare har ki saka hannunki qofa ta datse ki" Itama Zubaidan ta katseta "Ke! A gaban nawa ma rashin kunya zaki mata? To bari kiji daga yau koda wasa karki sake kullemun qofa tunda dai gida nawane ba na wani ba, sannan dukanku matana ne babu wadda nayiwa shamaki daga shiga dakin wata a cikinku, yanzu kalli ciwon da kikaji mata ji yanda hannun ya kumbura fisabilillahi hakan da kikayi yayi kyau?" Audu fada yana zare mata ido, Zubaida sadda kai qasa saboda kukan dake shirin bada ita tace "Amma dai tsakani da Allah ba haka ya kamata kayi ba, seka tambayeni abinda ya hadamu tunda dai kaji daga bangarenta" "Ke zaki tsara mun abinda zanyi a cikin gidana? To banyi hakan ba nace banga damar yin hakan ba koda abinda zakiyi?" Ya hayayyaqo mata seta fashe da kuka saboda takaici tama rasa abinda zata kuma ce masa "Tashi kije" ya bata umarni yana wani dauke kai dan kukan nata ya tabashi amma shi a dole ta masa laifi shiyasa ya dauke kai. Cikin kuka guiwoyinta a sanyaye ta wuce dakinta. Zubaidan na fita itama Binta ta fashe masa da kuka tana cewa "Yanzu shikenan ta jimun ciwo taci bulus iyakar abinda zaka ce mata kenan sannan saboda makirci ta fita tana kuka kamar ita aka zalunta?" "To ya kike so nayi, so kike na rufeta da duka ko kuma na riqe hannunta ki rama abinda tayi miki? Ina kinji dai tace kuskurene?" Audun yayi kanta a fusace, yanda yayin yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba wato tuggunta be samu shiga ba so tayi ya rufe Zubaidan da fadan koma ya falla mata mari koya rufeta ma da duka amma dai ko banza hakan ma babu laifi tunda ya sakata kuka a gabanta da haka zata cigaba da nunawa Zubaidan ita din ba kowa bace a gurinsa Audu, kuma duk yanda ta dama haka za'a sha. Qarawa kukanta volum tayi babu ko dadin sauraro Audu yaja tsaki yace ta tashi suje gurin wani wanzami dake qasansu a duba hannun. "Wlh ba zani ba idan ba zaka kaini Asibiti ba sedai na zauna da hannun haka kuma gobe karka saka ran zaka fito ka tarar dani a gidan nan Kaduna zan wuce" ta fada cikin kuka. Wannan tasa ya kaita Asibitin suka bata magu gunan rage radadi bayan an mata allurar kashe kwayoyin cuta sannan suka dawo gida lokacin goma harta gota, seda taci abinci tasha magani kafin ya wuce dakin Zubaida. Tana zaune a falo ta kunna Tv amma hankalinta baya ga abinda ake nunawar tayi nisa cikin tunanin da tunda ta baro dakin Binta takeyinsa. Se taga kamar shari'ar ta Audu ba haka ya kamata ya gudanar da ita ba, tambayarta ya kamata yayi abinda ya hadata da Binta har wannan tsautsayin ya faru bawai ya dora mata laifin matsewa matarsa hannu haka nan ba kuma da yake maganar kowa tana iya shigar dakin yar uwarta babu shamaki a ina ake haka fusabilillahi? Yanda ya shiga fuska a daure haka tayi masa sannu da zuwa jiki babu karsashi guiwoyinta suka sake sanyi da Al'amarin Audun, to fushin na menene kuma? Ba an gama magana ta wuce ba? Ya gama uzurirrikansa data bashi abinci yace ya qoshi, bata sake tsinkewa da lamarin ba seda ya juya mata baya da sukaje kwanciya a ranta tace lallai abin babbane. "Kayi haquri in dai akan abinda ya faru jiya ne kake fushi wlh ba ina sane na matse mata hannu ba ita ta biyo ni tana zagina tace zata dokeni ni kuma tsoron haka yasa na shigo na tura qofar bansan ta saka hannunta a ciki ba" Zubaidan ta fada hawaye na saukar mata sanda Audu ke shirin fita da safe ba tareda ya ko kalli kayan karin data jera masa ba. "Oh, bayan abinda kikayi shine kina da bakin sake magana harda sharri zaki mata a yaushe ta zageki harta biyoki zata dokeki?" Ya fada yana dakatawa daga fitar dayayi niyya. Hawaye suka balle mata na takaici, wato sharri tayi mata? Ita Bintan Allah kadai yasan abinda ta fada masa wato natane gaskiya se ita data fadi ainihin abinda ya faru shine zece ta mata sharri? Muryarta na rawar kuka tace "Akan me zan mata sharri? Sannan ai kaima zaka iya bada shaida akai dan ba shibe karo na farko data zageni ba ko tayi yunqurin dukana a gabanka ma anyi shekaran jiya ba kai ka kwaceni daga hannunta ba?" Ta fada tana tsare shi da ido. Yayi jummm alamar ya gasgata abinda ta fada din amma saboda qi fadi da rashin son gaskiya irin nasa se ya murje yace "Rashin kunya zakiyi mun har kina tsareni da ido kamar wani sa'anki? To bari kiji muddin kina neman zaman lafiya a gidan nan dole ki zauna lafiya dani da kuma matata. Mu bamu saba fadace fadace da kuka iya har ana fidda jini ba a gidan nan dan haka ki san a inda kike" daga nan yasa kai ya fita ya barta tsaye kamar ya dasata tana juya kalamansa. Ita da suwa suka saba fadace fadacen da zubar da jini? "A bariki mana yake nufi" zuciyarta ta bata amsa, dabas ta zauna dafe da kunci hawaye suka shiga mata tsere, wato abinda yake nufi kenan, a fakaice yana gaya mata cewar nan ba irin gidan daya dakkota bane kenan da suka saba Fada kamar Kaji suna jiwa junansu rauni Yau Audu da kansa yae goranta mata wani al'amari daya shude a rayuwarta kenan. Wannan abu yasa gaba daya jiki ta yayi sanyi, sararin data samu ta fara baje kolin sharholiyarta duk karsashin ya barta shima kuma be bi takanta ba yana ta tattalin Binta da hannu ya saka a gaba har ya saukar mata da zazzabi me zafin gaske seda ta kwana uku a kwance kullum kuma is Zubaidan ta shiga ta dubata safe da dare idan yana nan zata amsa cikin sakin fuska idan baya nan kuwa har Lantana samun damar yaba mata magana take suce mata mayya wai ta kama mata hannu to kurwarta kur. Ita Binta ko abinda take mata ma sam be dameta ba irin na Audun, qiri qiri yaba ganin gaskiya amma ya take yabi qarya shin wane irin mutum ne shi haka? Ya za'ayi rayuwa ta yuwu a haka ace duk abinda aka gayawa mutum walau shine gaskiya walau qaryane se ya hau ya zauna kuma idan ya gano gaskiyar daga baya girkan kai da izza su hana shi karbar kuskurensa ai ko baze furta da baki ya karbi gyara ba se ya nuna hakan a aikace amma shi babu daya daga ciki da yakeyi sedai ya dora fushi wannan ai ba daidai bane. Data lura da gaske fushi yake da ita kuma bashi da alamar sakkowa dan har ranakun girkinta da suka zagayo bacci ke shigar dashi dakinta safiya nayi ze fice dole ta sauke nata fushin ta sake samunsa ranar ta tattara duk wata wayo da dabarar da take dasu ta wanke kanta a gurinsa ta hanyar karban laifin da bata aikata cikin sani ba ta kuma tabbatar masa da ba za'a sake ba har da kukanta tace kuma ya rakata a gabansa ta baiwa Bintan haquri sukaje ta bata haqurin ganin idonsa yasa Binta tace ta haqura ai ita komai ya dade da wucewa a gurinta daman wannan tasa ya sakko daga fushin da yake suka koma zamansu lafiya abinda yayi mugun batawa Binta rai. A zaman tsamar da sukayi ba qaramin qara samun kan Audun tayi ba, a wayo da dabara take dada kwarkwarashi shi kuma dake kan keke ne ya hau daram ya zauna. Shiryawarsu da Zubaidan se ya zama silar warewar nata shirin musamman da taga kamar Zubaidan ta ganota duk irin tuggun data hada mata a gurin Audun ta dena musawa zata amsa laifinta ta durqusa har qasa ta bashi haquri tana hawayen munafunci a cewar Bintan shi kuma me son girma kansa ya sake fasuwa shikenan kome ta shirya ya wargaje. Tun daga wannan kuma Zubaidan ta hankaltu duk laifin da Binta ta dora mata zata amsa ta bashi haquri tunda ta fahimci abinda yake so kenan babu ruwansa da jin ainihin magana yanda take hakan kuwa da takeyi ya sama musu zaman lafiya se a dade ba'aji kansu ba idan ba kuma Bintan ta shammaceta ta tunzuro shi ta yanda harta gaza kare kanta ba. A haka aka kwashi watanni biyar da Auro Zubaida a kuma wannan yanayi ta fara laulayi wanda yazo mata da zafin gaske ga Amai ga Zazzabi lalurori dai iri iri ba qaramin Jiki take ji ba, wannan cikin ya sake gigita Binta, wato Zubaida zama tazoyi ma kenan tunda gashi har tayi ciki ita tana me haka ta faru yama za'ayi Mata suyita haihuwa a gidan Audu Bara'atu tayi biyu ita tana da daya kamar rai kuma a auro wata a bayanta tazo ta goga da ita wannan baze yuwu ba ta shiga takalar masifa kala kala fatanta Zubaida ta tanka mata ta samu dalilin lakada mata na jaki ta yanda cikin zebi rariya tun be gama samun gurin zama dakyau ba sedai bata samu hakan ba, Zubaida da ko a baya bata biye mata ba balle yanzun da take ta kanta. Abin ya hadewa Binta biyu dan Audun shima yanzu duk ya maida hankali kan Zubaidan sosai wannan yasa ta kasa jurewa ta fiddo haukarta fili take baje musu ita watarana ya tanka mata wata rana kuma ya qyaleta a haka abinda ya sassuta lamarin ganewar da tayi itama tana da shigar ciki saboda batan wata da tayi amma tayi shiru bata gayawa Audu ba sannan kuma cikin Zubaida yayi watanni uku a lissafinsu na daga sanda ta fara laulayi kenan ita kuma nata yana wata daya. Koda Zubaida sukaje Asibiti likita ya tambayeta yaushe rabon da tayi Al'ada ce masa tayi watanni uku, tayi lissafi da watan data fara laulayi dukda maganar gaskiya ba zata iya cewa ga lokacin da tayi al'ada ta qarshe ba tun zuwanta gidan sau daya tayi watanninbaya da suka biyo idan Al'adar tazo kwana daya ne kuma dan kadan ba kamar yanda ta sabayin kwanaki Bakwai ba kuma ba se qarshen wata ba ko yaushe tana iya ganinsa kuma ya dauke har ta fara zaton ko Sanyi ne ya kamata to tunda tasha magani kuma jinin be sake zuwa ba babu dadewa kuma ta fara laulayi. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Bayan tabbatar da lafiyarta data abinda take cikinta aka bata sati hudu ta dawo daga Asibiti, kafin zagayowar sati hudun nan tamkar wadda aka bugawa iska cikinta yayi wani girma na ban mamaki. A watanni ukun da tayi muddin ba wanda ya karanci yanayi na masu ciki ba shine ze iya tantance samuwar cikin a jikinta dan idan ka cire Laulayi babu wata halittarta data canza kota nuna samuwar wani abu tattare da ita. Cikinta na nan yanda yake be qara tudu ba haka nan batayi qiba ba se gashi a sati hudu cikin ya bude yayi girma haka jikinta da fuskarta duk sun sauya idan ka ganta seka dauka in kun rabu yanzu anjima za'ace maka ta haihu. Binta bata nan ta tafi Kaduna sanadin jikin Alhaji Zakariyya daya motsa harya kwanta a Asibiti dan haka suka tafi tareda Audu ya kwana biyu ya barota a can kuma zuwan yayi daidai da bikin yaye su Baballiya da akayi dan haka suka hada tafiyar harda Yan Bechi duk sunje sun duba jikin Alhajin kuma a gidansu Bintan aka musu masauki suka kwana biyu suka juyo tare aka baro Binta a can satin ta uku kafin ta dawo Kano. Ranar da Binta ta dawo ita kuma Zubaida bata nan taje gidansu yini se dare Audu ya dakkota koda suka shigo kuma bata ma san Bintan da dawo ba dan be gaya mata ba se da ya shiga tareda Zakariyya wai yaje mata sallama sannan ta sani ta kuwa cika da mamaki amma batace masa komai se fatan wayewar gari lafiya tayi kwanciyarta ita kadai. To washe garima bata fita ko tsakar gida ba dan a yanayin da take yanzun tafi ko yaushe buqatar samun hutu da nutsuwar zuciya bata shirya dibar hauragiyar Binta ba dukda tana so taje su gaisa tayi mata yame jiki amma ta bari akan se da dare idan yana zaune seta shiga ko ganinsa ze rage kaifin duk rashin mutunchin data so yi mata. Hakan kuwa akayi, bayan isha ta shirya taje Audu na zaune yana cin abinci tareda Zakariyya Binta na cikin daki tana buruntu tayi sallama ya amsa yana tsokanarta da cewa "Uwar biyu kin shigo?" Haka yake ce mata tunda cikin ya fara wannan girma me ban mamaki yace kodai yan biyu ne shi yasa wata hudu cikin ya ninka girmansa se tace masa to qilan tunda ita ba sanin ya cikin yan biyun yake tayi ba. "Baquwa mukayi?" Binta data fito ta fada tana zama akan kujera idonta akan Zubaidan, Audu ya murmusa yace "Baki ganeta ba? Kallarta dai da kyau kiga dawa tayi miki kama?" Ta zuba mata ido tana so ta gano wacece din kamar yanda ya ce, tai fici fici da ido se ko ta zabura sanda ta gama ganota ta nunata tana cewa "Ke..meye wannan? Me zan gani haka?" Yanda tayin ba Zubaida ba hatta Audu seda ya bushe da dariya yanda kasan wadda taga wata fatalwa haka rikice tana jera mata tambaya yace mata "Kinga abin mamaki ko? Yanda kika san cikin nan na jira ki tafi ya fara girma qila da baki dawo yanzu bama sedai kizo ki tarar ta haifeshi" "Au Namiji ma zata haifa?" Maganar ta subucewa Bintan, Zubaida ta kalleta Audu da be gane inda maganarta ma ta dosa ba yace "Yan tagwaye ma kuwa muke tsammata dan wannan cikin daga ke har Bara'atun ban taba ganin wadda tayi me girmansa ba" ya furta sunan Bara'atu a fili karo na farko tun bayan rabuwarsu da ita. "Zancen banza ma kenan, ita zata haifi yan tagwayen a gidan nan? Wlh baze yuwu ba" ta idasa kwancw qullin haukarta. Zubaida ta gyara zama ganin cin kan Bintan gaba yakeyi tace "Yaya ina wuni? Ya aka baro yan gida? Ya me jiki kuma? Ubangiji ya qara afuwa yasa kaffara ne" daga nan ta shiga yunqurin miqewa tsaye tana jin Bintan dake kallon Audu tace "Lallai ma wannan rainin wayo ne qarara kuma wlh bazan dauka ba, ni za'a mayar mahaukaciya cikin da be ko cika qata hudu bane zeyi wannan girman sannan saboda jaka ce ta raineni na yarda ai kuwa ba'a isa ba" Zubaida bata tsaya sauraronta ba ta wuce dan dai kamar maganar bata shafeta ba haukanta da bata gajiya dashi ne ya motsa ga Mijinta nan seta sauke shi a kansa amma ba ita ba ciki kuma dai ba mutum ke bayarwa ba balle tace zatayi fito na fito da wanda ya bata dan haka tana zuwa daki taci abinci tasha saiwoyin data jiqa jiya dataje gida Baba Zayya Amaryar da Malam Hassan Babanta yayi watanni biyu kenan ta hado mata saiwoyi wai na taimakon sauqin naquda ne da rage zaqi a yanda Baba Zayyan tace wai cikinta ya nuna alamun ta kusa haihuwa ta ringa dariya tana cewa Baba Zayyan kace a kanta za'a fara haihuwar hudunni kenan ita kuma tace mata to su daura tsakanin su za'a me gaskiya dan bata yarda da lissafin Asibiti ba ko makaho yaga cikin Zubaida yasan ya haura zuwa watanni bakwai ko takwas. "Idan kika lissafa watanninki a daki ai cikinki ya kusa isa haihu ina watan Sallar Tsofaffi akayi Bikin wata na takwas fa kike ciki yanzu ai dab kike da ki haihu" Baba Zayya ta nanata mata. Ita dai bata dauki batun da muhimmanci ba, wata hudun nan shi take lissafawa kanta dukda girman cikin da motsin da takeji abin dubawane, ba wannan ne cikinta na farko ba ciki biyu tayi a rayuwarta ta baya sedai dukkansu baau kai matakin da aka busa musu rai ba ta ciresu dan haka ba zata dorar da komai game da yanayin girma ko sanda yake fara motsi ba. Ta dafe cikin da hannu biyu tana jin wani yanayin nadama mara misaltuwa yana shigarta. Yanzu fa Al'umma zasu iya ringa jifan abinda zata haifa da rayuwarta ta baya ko? Washe gari Audu na fita Binta ta fice itama, daren jiyan basu kwashe shi qalau ba, Bintan da tayar da bala'i babu rufa rufa tace Audu ya raina mata wayau, watau ciki yayiwa Zubaida a waje can gurin tambadarsu shine ya aurota dan su rufawa kansu Asiri kenan ko to billahillazi ba zata yarda ba seta bankada kowa yaji wannan aika aikar da sukayi baze gurbata musu zuri'a ya hada yayansu da yan uba Shegu ba ta ringa masifa tana bala'i seda ya zabga mata mari ya korata dakinta kafin ya samu sa'ida hayagagar da take masa akai da safe kuwa ko leqata beyi ba dan tayi bala'in bata masa rai akan maganar tata Zubaidan kanta daga bakin qofa suka gaisa ya fita shine Bintan najin fitarsa daman ta shirya itama ta tafi gidan Turai. "Yanzu ke meye abin daga hankali a nan yanzu? Wannan ai abinda zaki koma gefe kiyi dariya kisha kallo ne idan ma da cikin ta shigo ke ai gaba ta kaiki dan magana na fita dayan biyu ne dole ya sawwaqe mata ta tafi ta nemi uban cikinta idan ma nasa ne dai ta saku tunda dai ba'a Aure da ciki to ai gaba ta kaiki gobarar Titi a Jos Qawata" Turai ta fada bayan da taji bayanin Binta. Ta numfasa tace "Zancenki gaskiya ne amma ta yaya kike tsammanin haka zata faru? La shakka idan cikin ba nasa bane wannan kuwa na san ze iya sakinta amma muddin na sane kema kinsa babu inda zataje kuma zama sunyi auran ne daman saboda kauda idon mutane da kuma zargi" "Banyi muku katsalandan ba Hajiya amma watan auran nan da kuke magana akai nawane tukunna?" Barira me Aikin Turai dake ta goge goge hankalinta na kan hirar su Bintan ta fada. Turai ta harareta tace "Wai sau nawa zan hanaki tsoma mun baki idan ina magana da mutane? Aiki kikeyi dama ko kuwa zaman gulma shiyasa kika maqalw gaban Tv tun dazu kin kasa gama gogewa kenan?" "Kiyi haquri hajiya ba gulma bace ba maganar gaskiya ce wanda a ganina duk abinda zaku shirya dole ya zamani kunyi akan saitin da ba za'a ruguzaku ba. Akwai hanya me sauqi da zakubi ku heganta cikin nan kona Alhajin ne tunda dai an samu tangardar lissafi girman ciki ya zarta watanninsa" Barira ta sake fada bayan ta saki duster da take goge goge da ita ta juya ga abinda tafi iaywa wato hada tuggu da

Chapter 19 of 32