Ya fada yana kallonta, cikin iyakar gaskiyarta tace
"Na dauka zaka toshe qofar tsakiyar dakin nan seka huda mata qofa ta wajene mu tashi da falle daya"
Daya rasa abin ce mata kawai ya fashe da dariya, ya gama rubutunsa ya tattare takaddun ya fita.
Daya tuntubi Yakubu zancen gida ce masa yayi
"Ka sakata a bangarenmu kawai"
"To ku kuma fa?" Audu ya tambayeshi,
"Wannan ba matsala bane tunda kaga idan muka tafi yanzu se mun shekara ko fi kafin muzo, zuwa sannan se musan abinyi" Yakubun ya bashi amsa. Cike da rashin jin dadi Audu yace
"Wai dagaske kake ba zaka zauna ayi Bikinnan kuna nan ba? Wai me nayi da yayi maka zafi har haka ka qullaceni?"
"Bakayi mun komai ba Audu tafiya kuma ka sani ina shekarar qarshe ya kamata ace na ninka mayar da hankali akan Karatuna sannan itama Balaraba na gaya masa tana zuwa makaranta acan to sun koma kaga be kamatu daga farawarta kuma ta ringa wasa ba. Nidai abu dayane da yake damuna na rasa dalilin da sam auran nan be kwanta mun a zuciya ba, ina tsoron ka auro matar da zata wargaza maka zaman lafiya, ta gurgubtar da kyakykyawan tushen daka soma ginawa. Haka kawai nake jin baka dace da matar Aure ba Audu amma Allah shine masanin gaibu ina kuma yi maka addu'ar Allah ya kawai da duk wani abun qi daga hadinku".
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Biki ya rage saura wata daya, ba qaramin raraka Audu yayiwa jarinsa ba ya hadawa Binta lefe na yar gata aka kai, be bar Bara'atu a baya ba dan itama seda yayi mata lefen dukda be kai na Bintan ba, ya kuma bada aikin sababbin Gado da kujeru daze chanza mata. Yakubu sun kwashe kayansu wanda Bechi ya aika dasu Bilki ta dauki Gado Aisha Kujera ragowar tarkacen yan uwa suka raba sun rabu da Audu akan ze nemi fili nan kusa a tayar masa da wani gini domin siyan bangaren Yakubun yayi dukda Yakubu yace Aa ai gida gaba daya na Audu ne dan da kudinsa ya siyi fili ya gina amma shi yace ba haka ba koda shi ya gina kyauta ce yayiwa Yakubun dan haka yanzun siya yayi kuma in Allah ya yarda kafin su zo Kano ze maida masa da wani.
Ya tada gyaran gurin, anyi toshe toshe da liqe liqe, maginin gaske ya dakko Injiniya akayi masa aikin se ga guri ya fito fes an fitar da Sef cinten daki biyu da falo a tsakiya harda bandakin tsakar gidan aka shigar mata a daki se kitchen aka lailaye ko ina da Torazo gida dai ya fito na zamani a ganin ba za'a kushe ba dukda yasan dai a matsayin Bintan tafi haka amma ai ita tace taji ta gani ko a bukka ze ajiyeta zata zauna. Bara'atu ma ta samu arziqi an saka mata torazo a dakunanta dana su Abdullahi da tsakar gidan, Gadonta ta maida musu can aka saka mata sabon da Audu ya mata ga kujeru da kafet harda kayan Kallo se danqareriyar firiza duk a kayan fadar kishiya ita kuwa me ta manta?
Audu nata doki da murna sanda yan uwan Binta sukazo ganin guri se kuma murna ta koma ciki. Babu kara suka ringa kushe gurin da yada maganganu akan an asirce musu yar uwa banda haka me Binta zatayi dashi balle har ta yarda ta zauna a gurin da ko Boyis kwatan su Albarka. Basu kwana a gidan ba kamar yanda ya shirya musu otal suka kama washe gari suka juya sukaje can sukayi ta cece kuce da fadar maganganu abinda ya saka Mamansu magantuwa kenan saboda yanda suka fasakta muhallin Bintan abin yayi muni. Tayi tsammanin yanda ya zage yayi lefe haka ze qerawa yarta gida kodan ya rage mata radadin auransa da bata so yar tayi, meye amfanin Kudin da Ubanta ya sakar masa domin tana da labarin qanin Kyauta yake bashi mai, idan an kai masa tanka goma kudin Biyar Alhajin yake karba haka tsayin shekara daya bata taba jin yace ga kudi Kaza na Ribar Mai da Audu ya kawo ba amma shine zeyiwa yarta wani Akurkin kaji a sakata a ciki.
Cikin fushi da tari Alhaji da maganar, takanas ya tashi Tunde suka tafi Kano kwanaki biyu bayan komawarsu su Salima a sannan Biki ya rage saura kwanaki goma se ganinsa kawai Audu yayi ba zata. Shidai Alhajin bega aibun gurin da suka ringa fada ba domin a abinda ta rasa a gidansu baze wuce girma da kuma taswirar gini ba dukda haka domin gujewa duk wasu surutai na matar tasa da bata taba qalubalantar wani hukuncinsa ba yasan tayi kawaici matuqa akan lamarin auran tunda har ta magantu yanzu tabbas abin ya kaita maqura dan haka yacewa Audu
"Me yasa baka sanar dani baka da gurin da zaka ajiye Mamana ba?"
Audu yaji wani iri, wato shima ya raina gidan kenan? Amma dai a qarfinsa sunsan yayi abinda ze iya harma ya zarta. Shiru yayi bece komai ba gudun kar zuciya ta kwashe shi ya gayawa Alhajin mara dadi dan be gama hucewa daga fushin cin zarafin da Yayansa suka masa ba daman.
"Ina ganin zan saka a duba gida ginanne idan yaso se a siya a sakata ciki ko ya ka gani?" Alhajin ya sake fada se sannan Audu ya daga kai ya kalleshi. Wato zancen Labahani gaskiya ne da yake cewa idan ka auri yar masu kudi rainin arziqi se abinda ka gani sannan su zasu ringa yi maka iko da gida to idan kuwa haka ne shi ba za'ayi akansa ba, baze bada qofa ba balle daga baya idan ya hana ace yayi Butulci.
"Kayi haquri Alhaji ba ina nufin raini a gareka ba amma maganar gaskiya wannan ne muhallin da nake dashi da zan saka Binta a ciki. Ka sanni ka san Asalina haka itama tun gabanin tafiya tayi nisa a tsakaninmu tasan komai a kaina kuma ta yarda da hakan zata zauna dani a kowanne. Kayi haquri ka barni na ajiyeta a inda Allah ya horemun a yanzu, ina fatan zuwa gaba na gina mata daidai da tsarinta amma a yanzu abinda ya sawwaqa kenan".
Badan Alhaji yaso ba gudun kuma karya takurashi yaga kamar ya masa kutse a cikin lamarin gidansa yasa ya haqura ya tafi kuma kamar yanda Audun ya fada ita Bintan taji ta gani dan ya zaunar da ita kafin a kawo kudin Aure ya tambayeta ta amice tace koda can Qauyensu ze kaita tana sonsa a haka zata aureshi.
Haka akayi Biki Amarya ta tare, iyayenta sun zuba mata abinda dakin ze iya dauka. Danma kuma babu laifi ginin an fitar da dakunan da baga dan haka sun dauke gadajenta Biyu kantama kantama yan Dubai. Kujerune dai seda aka canzo ainin wanda aka siya mata saboda falon ya matse ga Divida bango guda yar waje kujerun ma irin bajaj din nan ne 1 sitter su takai girman two sitter matsakaitan kujeru dan haka suka matse matuqa dole aka mayar aka canzo mata wanda gurin ze dauka. Kwana biyu yan uwanta sukayi suka juya dalilin seda suka kaita Bechi wanda basu kwana ba ko banda ruwan gora da aka basu babu abinda suka iyaci na daga abincin tarbar Amarya yamma lis suka tada jaraba seda aka kaisu Kano gidan Amarya dan sunce ba zasu iya bacci a garin ba wannan Abu ya qona ran Yan uwan Audu ya ku.a darsa tsanar Binta a ransu duk da ba ita ta musu ba amma sun ce itama haka halinta yake kenan tunda bata hana yan uwan nata yar musu da magana da izgilanci ba
Audu kansa ya qara hasala wannan karon dan haka babu wata sallamar Arziqi suka koma Kaduna suka yita fadar qarya da gaskiyar abinda ya faru na wai an aura masa ita buqata ta niya ya fara musu rashin mutunchi. Todai babu yanda suka iya aure ya qullu Amarya da Ango na son junansu sedai fatan a zauna lafiya.
Sati gudan da Audu yawa Amarya Binta an barji soyayya irin wadda ya dauka a fina finan turawa kadai ake irinta. Baiwar Allah Bara'atu aikinta ta dafa abinci wanda take qure duk basirarta da abubuwan da Balaraba take koya mata idan sunzo tayi musu takai musu idan sunci ta debo kwanuka safe rana dare haka take wannan Bauta tsakaninta da Audu kuwa da safe idan ya dawo sallar Asuba ze shiga ya duba su shikenan se wata safiyar ko idan taje kai musu abinci baya fita ko ina yana daki suna barzar Amarci a haka ya kwashe sati dayansa gurin Amarya wadda zuwa sannan ba zatace ta mata wani abu ba tsakaninsu gaisuwa ce tana da Fara'a da kuma son yara dan kullum zata kira su Abdullahi ta basu abin dadi ita Bara'atun cema wani lokacin take hana su zuwa saboda karsu takurawa Babansu da kullum yana daka.
Sati daya Audu ya tara su yayi musu nasiha sannan suka raba girki kwana bibbiyu kuma kowacce girkinta zata ringayi. Hakan yawa kowacce dadi, a falon Binta akayi zaman dan haka bayan ya sallame su Bara'atu tayi mata seda safe ta tafi. Yara duk sukayi bacci ta sake gyarawa tayi kwalliya da wasu kayan bacci da ta siya gurin Maman Kabir Maqociyarta saboda wannan rana. Tayi gyaranta daidai gwargwado na cikin jiki dana fata ga sabon kitso da lalle da tayi dukda kullum ta kalli Amaryar tata Da take Jajir ga jiki duk madara da tsoka se taji kamar Audu ba ze sake yi mata kallon Mace ba wannan tunanin ya sakata damuwa har tayi yar rama daman babu jikin se ta sake komawa yar yarinya firit da ita.
Tana nan zaune falo tana kallon Tv da tsumayen Audu har bata san bacci ya kwasheta ba. Motsin rufe qofa ya farkar da ita, ta kalleshi kafin ta kalli Agogo, sha biyu da rabi a saninta tun Tara da mintina take zaune a gurin kusan awa uku kenan.
"Bakiyi bacci ba?" Tambayar daya fara jefa mata yana shigewa cikin daki, ya gotata qamshin turaren Binta ya bigeta yanda kasan yanzu ya shafashi. Ta yunqura tabi bayansa tana cewa
"Ina zaune bansan bacci ya kwasheni ba" ta dakata ganin harya kwanta. A tausashe tace
"Har zaka kwanta bakaci abinci ba?"
Fuskarsa washe da murmushi me kama dana rainin wayo yace
"Au na manta qanwarki tace kiyi mata aikin gafara ta bani abinci".
Tayi zukudi tana kallonsa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta juya to me zatace?
Kwanukan Tuwon shinkafa miyar gyadar datayi wanda ciki ta dibarwa Bintan iyakar cikinta dan tun da safe yace a gurinta zeci abincin dare yanzu kuma ya canza shawara yaci a gurin Amaryarsa "to Allah yasa ya ishe su" ta fada a fili tana Adana abincin a cikin Fridge duk Balaraba ce ta koya mata tace a can miyar sati takeyi ta saka abarta a firinji sedai ta dumama idan zasuci haka sauran abinci duk adanawa takeyi shiyasa itama tunda ya siyo mata ta fara wannan dabarar da yake koda yaushe da wuta hankalinta kwance yanzu bata rasa abinda zata bawa yara kafin ta gama abinci.
Seda ta gama kintsa komai ta dauke Babannan da bata san sanda Abdullahi ya kawo mata shi falon ba dan ya saka rigima a gurinsu ze kwanta dukda bata yaye shi ba ta kaishi daki abin mamaki har Audu yayi bacci, jiki a sanyaye ta kwanta itama ranta cike da saqe saqe. Washe gari da safe tana hada abin kari ta jiyo sallamar Binta. Tun daga cikin kitchen din take jn tashin qamshin turarenta, gabanta ya fadi sanda suka hada ido. Kwalliyarta kamar me zuwa zaben sarauniyar kyau. Har qofar kitchen din ta qarasa fuska dauke da fara'a suka gaisa daidai nan Audu da gama wankan sa kenan ya shiga yana shiryawa dan yau ze fita aiki ya leqo haqoran nan a washe yana cewa
"Aa, wa nake ji kamar Amarya da sassafen nan?"
"Nice, na zo bikon Ango naji shiru har gari yayi haske baka leqa mu ba" ta fada cikin wani salo da ya saka Bara'atu sakin baki kwan datake soyawa akan wuta ya fara qauri yayi baqi kafin ta ankare ta sauke. Abdullahi da Babangida suka fito daga daki suka gaida Binta, ta karbi Babannan tana masa wasa ta shige falon Bara'atun suka barta tsaye a kitchen. A sanyaye ta gama soya kwan ta fara shigar musu da abin karin. Ta jere komai a tsakiyar daki na Audu daban se nata dana yara daban. Abdullahi ta fara hadawa shayi shida ze tafi makaranta ta zuba masa wainar kwansa da Biredi ya dauka ya tafi dakinsu Babangida ya bishi dan haka ta zuba nasa ta bisu dashi ta bar Audu da Binta dake zuba hirar da bama fuskanta take ba dan rabi turanci sukeyi. Tana dawowa ta tarar sun baje suna karyawa tare.
Wani abu ya soketa amma ta daure
"Kin ganni da kwadayi ko?" Binta ta fada tana mata murmushi seta girgiza kai tana murmushin yaqe itama. Nata abin karin ta dauka ta shigar daki ta dawo ta dauki Babannan dake musu didifniya yana shirin zubar da shayi suka shige ciki. Binta na zaune har Audu ya shiga ya qarasa shirinsa kafin ta rakashi har qofar gida ya fita, ta rasa ma me zataji, haushi ko mamaki ko me?
Daga rakiyar Audu binta bata dawo ba bangarenta ta wuce. A sanyaye Bara'atu ta ringa ayyukanta saboda abinda ya faru daga jiya zuwa yau din. Da Asuba duk sun makara tashi shiyasa ma Audu be fita masallace ba. Daga gaisuwa wata magana bata hadasu ba ta fita hada abin kari shi kuma ya shiga wanka, tana Allah Allah ta gama idan sun zauna karyawar tayi masa magana Bintan tazo ta kasa ta tsare har seda ya bar gidan kudin cefane ma seda ta fito falo ta gansu a inda ya tashi ta daiji sanda yake ce mata gasu nan kafin ta fito kuma har sun bar falon to abinda take so ta fahimta shin abinda Bintana tayi da gayya ne ko kuwa dai tayine bada wata manufa ba?
Kasancewar Audu baya dawowa cin Abincin rana yasa se gurin uku ta tashi dora girki. Haka siddan Babannan ya tasa mata rigima, Babangida ya tafi makarantar Allo wadda akeyi nan cikin layinsu gida uku ne tsakaninsu qiriniyarsa tasa Audu kaishi dukda be cika shekaru uku bama sannan amma da yake yana da barage kuma bakinsa ya bude shiyasa seka dauka ya wuce shekarunsa. Ta rasa yanda zatayi da Babannan din ta goyashi yaqi ta aje masa kayan wasa duk a banza ga aiki ta dakko dan Funkaso take so tayi da miyar Tantakwashi se Zobo da Balaraba tace mata duk in tayi girki ta ringa hada masa Lemo ta kuma koyi kala kala su Jinja harda wani farau farau me dadi idan yayi sanyi.
Gaba daya kukan yaron ya hanata sakat gata ita bata iya aiki idan yaro yana mata rigima ba. Hijabinta ta zura ta dauki Babannan din da kayan wasansa ta doshi bangaren Bintan, qofar a bude dan haka ta shiga da sallama tana kallon wurin tana qara sha'awarsa, kullum tayi sallah se tayi addu'a Allah ya qarowa Audu budi itama ya maida mata da gurinta irin haka komai a ciki. Tayi sallama shiru ba'a amsa ba daga inda take tana jiyo tashin kidan turawa qila Tv ce qila radio ta kunna kusan sallamarta uku dan haka ta tura qofar falon da itama ba'a rufeta ruf ba ta shiga da sallama.
Bintan na kwance kan kujera Idonta akan qofar ga Tv na aiki a ciki ake waqar da take jiyowa. Ta sake maimaita sallama tana fadada fara'arta, ba yabo ba fallasa bintan ta yunqura ta zauna tana kallonta ba tareda ta amsa sallamar tata ba. Kujrar dake dabda ita ta nufa da niyyar zama yanda Binta ta zaburo mata tana cewa
"Karki zauna mun a kujera" ya saka ta dage da sauri har tana shirin yarda Babannan tayi saurin dafeshi tana kallon Binta data miqe tsaye fuska a hade tamkar wadda aka aikowa da saqon mutuwa.
Page 12
"Karki zauna mun a kujera" ya saka ta dage da sauri har tana shirin yarda Babannan tayi saurin dafeshi tana kallon Binta data miqe tsaye fuska a hade tamkar wadda aka aikowa da saqon mutuwa.
Kallon kujerar tayi dan ta gani ko wani abun cutarwa ne akai da ya sakata hanata zama amma bataga komai ba seta sake kallon Bintan dake jifanta da wani kallo data kasa fassarawa. Cikin kaushin murya tace
"Meya shigo dake dakina?"
Mamaki da Al'ajabi suka cika Bara'atu, ita Binta take tambaya me ya shigo da ita dakinta? Matar da idan tazo kawo musu abinci take nacin ta zauna suyi hira itace take ganin rashin dacewar zaman musu ta tafi amma yau take mata magana haka cikin zafi da gatsali, tsawar data sake buga mata ta maidata hayyacinta, Babannan ya fasa kuka dan shi baya son Hayaniya tamkar Yakubu ne ya haifeshi. Qofa ta nuna mata tana cewa
"Fita, kuma wannan ya zama karo na qarshe da zaki tako qazaman qafafunki ki shigo mun daki, wato kinzo ki shafamun tsiya da talauci har da zaman mun a kan kujera? Wlh karki kuma idan ba haka ba sena banbance miki tsakanin aya da tsakuwa fita" ta qarasa cikin sigar bada umarni. Kamar kazar da qwai ya fashewa a Ciki Bara'atu ta fita daga dakin tama rasa tunanin da zatayi, to me hakan yake nufi?
Haka ta goye Babannan yana kuka da komai ta shiga aikin Jiki babu kuzari ga rigimarsa ga mamakin Binta Allah ya taimaketa yayi bacci taje ta shimfideshi dukda yamma tayi taci gaba da aikin girkin. Bata samu ta gama ba seda aka kira sallar Magriba, su Abdullahi sun dawo dan haka shi ta hadawa wanke wanke yayi mata ita kuma ta kama Babangida da Babannan tayi musu wanka itama tayi, seda ta idar da sallah kafin ta shiga kwalliya. Tana zaune da yara suna cin abinci ita kuma ta zuraww Tv ido tana tunanin abinda ya faru tajiyo sallama daga tsakar gida, mamaki ya sake tiqe ta to me tazo yi mata kuma? Ko kuwa Tijarar da ta mata dazu ce bata isheta ba ta sake biyota nan?
Tsoro da fargaba ya kamata, ta san idan dukane tsaf Bintan seta babballata ta zubar ita bama zata iya takalar fitinarta ba kamar yanda tace karta sake shigar mata daki in Allah ya yarda anyi na farko anyi na qarshe to akan me kuma ita zata biyota.
Bata gama tunanin ba Binta ta daga labule ta shiga Falon, tayi kwalliya ta kece raini da Leshi ga qamshi tana bulbulawa fuskarta washe da fara'a ta sakeyin sallama.
Kasa amsa mata tayi se kallonta da takeyi a dan tsorace harta zauna akan kujera Abdullahi ya gaisheta sannan ta kalli Bara'atun tace mata
"Ina wuni Maman Baba? Ya yaran yau duk basu shigar mun ba"
Tsabar mamaki Bara'atu seta hangame baki ta kasa ce mata komai, Binta na shirin sake magana suka jiyo sallamar Audu a tsakar gida, Yaran suka fita da gudu tararsa Binta ta sake qyara zama Bara'atu kuwa tama rasa ya take har ya shigo dakin. Fara'arsa ta sake fadada ganinsu duka a gurin, ya zauna a kan two sitter kusada Bara'atun yana cewa
"Aa kace Uwargida da Amaryar duk suna nan me kuke tattaunawa haka?"
"Sirri muke nida Yayata" Binta ta fada tana fari da ido, Bara'atu kuwa a salube ta zame qasa tana masa sannu da zuwa tare da gaishe shi ya amsa cikin walwala. A fakaice Binta ta galla mata harara, ta gani amma idon Audun be kai ba yana qoqarin ciro alawa daga Aljihunsa ze bawa Babannan. Cikin yauqi Binta tace
"Barka da dawowa Ango, akwai idon yara da nayi maka maraba ta musamman"
Wani abu ya sako qirjin Bara'atu, shi kuwa kamar wani gaula haka ya bita da kallo yana cewa
"Allah ko, to ki ajiye mun bashi".
Hawaye taji sun zubo mata tayi saurin sharewa tareda miqewa ta fice daga falon dan kawo masa ruwa. Wannan ai cin fuska ne, a dakinta a kuma ranar kwananta zasu ringa irin wannan maganganun daman haka akeyi ko kuwa nata Mijin da kishiyar ne suka raina mata wayo?
Ta hado Ruwa da Zobo a Try daidai zata shiga dakin taji Bintan na ce masa
"Ai nan na wuni, can din yayi mun shiru da yawa shiyasa na taho muka sha hirar mu ina tayata ayyuka se dazu babu jinawa na koma nayi wanka"
"Kai amma naji dadi, Allah yaci gaba da hada kanku" Audun ya fada daidai nan ta kai ajiye Ruwan a gabansa mamakin Binta na neman ya sumar da ita. Tana ajiyewa tsulum Binta ta sakko tana cewa
"Bari na tayaki" ta zuba masa Ruwan a kofi daya ta zuba zobon a wani kafin ta dauka duka biyu tana kallonsa da murmushi tace
"Wanne zaka fara sha?"
"Bani ruwan" ya fada ta kai masa Bakinsa babu shiri Bara'atu ta miqe daga durquson da tayi tunda ta ajiye kayan tabi bayan yaran da Abdullahi ya hada kansu suka fita, yaron nada hankali da tsinkaye. Baya taba zama ya tisa su gaba sedai idan ita ta kirashi ko Audun.
"Haka fa ta ringa mun duk qoqarina na ta saki jiki dani taqi, ni kadai nayita surutu kamar lalatacciyar Radio se naga kamar bata jin dadin shigowar da nakeyi" Binta ta fada. Audu daya bi Bara'atu da kallo cikin ransa yana jin babu dadi ya kalli Bintan yace
"Haka take bata da yawan magana, kije dakinki zan shigo idan na dawo"
Yanayinta ya nuna bata ji dadin amsar daya bata ba amma da yake uwar kisisina ce seta wayance ta miqe tana cewa
"Shikenan, da wai zan jira muci abincin dare tare kaga ci da yawan yafi dadi amma bari naje ko shayine na tafasa nasha kawai daman ba yunwa nake ji sosai ba"
"To ki zauna idan munci abincin se ki tafi" Audu ya sake fada kafin ya miqe ya fita tsakar gida inda Bara'atu ke zaune daura da Kitchen ta zabga uban tagumi kamar wadda innarta ta rasu.
"Nan kika zauna kuma? To ina ruwan wankana?" Ya fada yana tsayawa a gabanta. Ta miqe a sabule ta shiga Kitchen, ruwan sata jona ta dauko ta kai masa bandakin. Yabi bayanta suka shige uwar daka kamar Binta ta bisu kota fizgo Bara'atun haka taji, a ciki kuwa duk qoqarin Audu nason ta hada ido dashi taqi. Ta dauko masa Jallabiyyar da yake shiga wanka da ita da tawul din goge jiki ta ajiye kan Gado ta dauki kwandon sabulunsa ta fita dashi ba tareda ta kalli inda Binta ke zaune ba.
"Nazo na tayaka?" Bintan ta fada cikin salon cusa takaici, taji diran abun amma bata tsaya ba seda ta dangana da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 32