Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙofar ta shiga kanta tsaye ta durfafi dakin baccin Audu. Hadiza na tsugunne tsakiyar falon tana gyara zaman abin karin data ajiye musu tana kuma dakon fitowar megidan dake ƙarasa shiryawa a ciki tajo an buɗe ƙofa ta daga kai taga Binta ce bata kalli sashen da take ba ta wuce kai tsaye abinta zata shigar mata ɗaki babu shiri ta daka tsalle kafin Binta ta kai ga ƙofar tuni ta cimmata ta tare mata gaba cikin yanayina babu yabo babu fallasa take faɗin "baiwar Allah daga ina?" Binta ta kalleta sheƙeƙe kafin tayi tsaki tace "Ban gane daga ina ba? Kanki daya kike mun wannan tambayar ko kuwa baki san ni wacece ba sannan baki san cewar nan ɗin dakin Mijina bane?" "Ɗakin Mijinki fa? da alamu kece kanki yake da motsi a ciki shiyasa har kika gaza tantance a inda kike, to idan ma ada nan din Ɗakin Mijinki ne a yanzu ba nashi bane mallakina ne, sannan ko ace har yanzu yana mazaunin Ɗakinnasa bakida damar ko shiga tunda ina ciki, kwana nane dole ki jira harse randa na gama uzurina na fita kafin ki shoga ki shimfida naki mulkin" Hadiza ta mayar mata da martani cikin lafazin dake nuna daidai nake dake. Binta ta lafta mata harara tareda da jan dogon tsaki ta kauce mata ta kama mabuɗin ƙofar tana cewa "Idan na shiga se ki fiddo ni waje isashshiya me ɗaki" bata ko gama rife bakinta ba kuwa Hadizan ya fizgota ta maidota bayaz Binta tayi taga taga zata fadi ta kama bango, data tabbatar ta daidaita a ƙasa ta shammaci Hadizan ta wats amata mari. "Bantan uba, kika mareni? Wlh kin jangwalowa kanki masifa da bala'i se kin san ni kika mara" Hadizan ta fada a haukace kafin tayi ƙasa, Binta na jira taga ko ramawa zatayi se ji tayi ta wawashi ƙafafunta kafin tayi wani yunƙuri ta kaita ƙasa. Dambe ne rikica ya sarƙe tsakaninsu, Binta nada garin jiki haka kuma tana da ƙarfi amma naci da dakiyar zuciyar Hadizan tasa take neman cin galaba akan Bintan dan tunda ta fahinci ƙafafunta nan ne Rauninta su take riƙewa ta watsar da ita a ƙasa ta hayeta ta kila idan ta mirgine ita ma ta sakata a Osi ta daka haka suke ta birgima a falon sun yi watsa watsa dashi labulen ƙofar dakin kansa yayo ƙasa sun rikito da ƙarfen. Audu na bandaki ya ringa jiyo kamar hayaniya kamar kuma ana dukan Bango, ya bude ƙofa ya leƙo da kunnensa dan son tantance daga ina hayaniyar take tashi idan ba gizo ba se yaji kanar daga Falo ne, ƙarar fashewar abu dayaji Tusss ta sakashi rarumar Kwangorinsa ya ɗaura din daya jikinsa duk kumfar da be gama ɗaurayewa ba ya fito yana goge ta fuskarsa, yana buɗe ƙofa ya tarar da dambaruwar da ake kwasa a falon, ƙarar dayaji kuma Talabijin dinsa suka rikito da ita ta fashe basu ma lura dashi ba, seda ya buga musu tsawar da ta saka dole suka shiga taitayinsu sannan kowa taja gefe tana sauke numfashi kamar Zakaru. "Wane irin hauka da dabbanci kuke mun a gida? nan ɗin sansanin dambe ne ko yaya? ke Binta me ma ya kawoki nan ma da farko?" Audu ya faɗa cikin tsananin fushi yana kallon Binta dataji jiki dan gar bakinta ya fashe yana zubarda jini. Cikin kuka tace "Bakaga abinda wannn mahaukaciyar daka auro a matsayin mata tayi mun ba se tambayata kakeyi meya kawoni dakin Mijina?" "Wane ɗakin Mijin naki? Ai kinsan banida wani ɗaki a cikin gidan nan yanzu. Banda fitina da son tayar da zaune tsaye meya kawoki? ki maza ki bar nan gurin kuma wannan ya zama kado na ƙarshe da zaki sake tako ƙafarki zuwa saman nan muddin bame dakince ta baki dama ba, fice Malama" Audun ya sake mayar mata da bacin ran dayafi na farko, Binta ta kalleshi ta kalli Hadiza dake sakin murmushin cin nasara wani kuka me tafe da zallar baƙin ciki da takaici ya zo mata seta wuce tana yinsa wiwi dan tasan a yanda ransa yake a ɓacen nan idan ta tsaya zubar da mutunchin seyafi haka Hadiza ta bita da kallo. "Ke kuma akan me zaki kamata da dambe?" ya maida dubansa ga Hadiza se tayi ƙasa da kanta kawai ba tareda tace komai ba, yayi tsaki ya juya yaba ce mata "Ki Gyara gurin kuma ki samarmun wani abun da zanci tunda kun lalata wannan" "Yanzun kuwa in sha Allahu" ta fada tana duƙawa ta fara tattare barnar da sukayi ranta ƙal da beyi mata faɗa kamar yanda yayiwa Bintan ba. Binta kuwa seda taji kanta na barazanar fashewa kafin ta haƙura ta dena kuka. Fuska tayi luhu luhu ga kuka ga Kutufon data sha a hannun Hadiza. Har mamaki takeyi yanda Hadizan da take gani tafi ƙarfi ta lallasata tilas ta canza salo tunda dai a doke ita zata ji jiki to ita ma ta ƙarƙashin ƙasa zata bi mata kamar sauran ta hanyar tuggu da munafunci dan ta rantse ba zata zauna ba ɗayar ba zata shigo ta tarar da ita ba. Ta tafasa ruwa ta gargasa jikinta ta kwanta tana cigaba da ƙulle ƙulle a ranta. Audu kuwa fes suka karya da Amaryarsa suna raha da jin dadi ya mata sallama ya fice ba tareda yako leƙa ya gano halin da Binta take ciki ba. A haka yayiwa Hadiza kwana uku ya koma dakin Binta, a taƙin kwanakin nan kan Binta ta raina kanta domin duk wani tuggu da take jin ta iya Hadizan ta doketa ta shanye a kwana uku seda ta maodata abar tausayi a cikin gidan ta kankane komai ba ga me gidan ba hatta su Mairo se yanda tace dasu dukda daman Mairo bata da Matsala Lantana ce yar kwal uban kuma tun washe garin tarewar Hadizan ta saita mata zama data sakko da kwanuka Lantana na wanke wanake ta ajiye mata seta matsar dasu gefe bata wanke ba, bata kulata ba se da maigidan ya dawo har sannan kuma Lantana bata tafi ba taba daka dan yanzu ta zama ta hannun damar Binta da ita ake shawarta komai tunda basa haɗuwa da Turai suna zaune Audun ya shiga ya cewa Lantana ta fice masa daga gida an sallameta. Binta tayi tsugul zatayi magana ya yarfata yace idan ta sa baki se tabi Lantanar tunda gidansa ne akan me Matarsa zata sakata abu taƙiyi Lantana ta ringa tumami tana roƙon ayi haƙuri dakyar ya barta bayan yaja mata gargaɗi shikenan ta shiga taitayinta. Kamar yanda Audu ya faɗi kwanan Juma'a na zagayowa Iyalan Gidan Sarkin Ƙaraye wanda suka samu rakiyar Ahalin gidan sarkin Kano dan can aka ajiye Amarya masu yi mata danki ne sukayi gaba suka dirarwa gidan Audu. Unguwa tacika maƙil ana ta kallon su masu busa Algaitu natayi. A cikin gida kuwa yai din ba Binta dake neman haukacewa ba su Turai na danneta hatta da Hadiza tasha jinin jikinta ganin wadda ake shirin kawo musu a matsayin ta ukun ta tabbatar wannan duk abinda suke taƙama dashi ta damesu ta shanye, abun da ta sakawa ranta kuma suka shawarta da Yayarta shine ta zauna lafiya da Amaryar, babu ruwanta da shirginta muddin ba ita ta sanyota ciki ba domin fada da saraki babu riba. Se bayan Isha'i Amarya ta iso bisa da rakiyar Gimbiyoyin Kano da Ƙaraye da suka kawota. Dattijai ne na ƙwarai, dukda kasancewarsu sarakai sun san mutunci da darajar Dan Adam, sda suka shiga dakinBinta da kuma na Hadizan suka kai musu Amarya kamar yanda Al'adar Bahaushe take, kafin su iso Kano seda suka kaita Bechi gurin Dangin Audu suka kwana sannan suka dakko hanya washe garin suka iso Kano dan haka babu wanda yazo daga can. Amarya na lullube cikin Alkyabba yar ubansu Ƙwarjinin matan da suka rakota yasa su Turai suka kasa iya daga ido dakyau su kalle su bare su gano ya Amaryar take, Binta dai tana kwance dan ta gagara zama abin dai ba'a cewa komai aka gama musayar gaisuwa da Miƙa Amana suka wuce dakin Hadiza. "Dukda ban ga Amaryar dakyau ba gani nake yarinya ce ma babu wani abu da ze firgitaki akanta Binta" Turai ta faɗa bayan fitarsu. Binta tace "Hmmm" kawai dan baki ya mutu. An bar Amarya da kuyanginta guda biyu ragowar suka musu sallama suka wuce. Turai taso su leƙa Amarya tunda yan rakiyar sun tafi amma Zainab tace Aa, su bari sa dawo takanas su ganta kawai hakan sukawa Binta sallama suka tafi. Ranar Ango be kwana dakin Amarya ba, nan dakin tsakar gidan dai ya shige abinsa ya kwana. Washe gari kafin sha biyu Kuyangin Amarya suka ƙarasa mata gyare gyare sukayi mata sallama kamar yanda ta basu umarni su koma gidan sarki saboda Ango yace ayi masa uzuri base sun zauna ba da akwai masu taimaka musu da ayyuka har biyu anan gidan ya gayawa Yayanta Najibu kuma ya sanar da iyayensu suncr babu komai itama jiyan ya gaya mata shiyasa bayan sun kammala komai tace su wuce kawai. Tun la'asar sakaliya Ango ya shige dakin Amarya wadda bata leƙo tsakar gida ba balle mutan gida su ganta. Hankalin Binta yayi ƙololuwar tashi da jin Al'amarin daya auku, kasa zama tayi ta tafi tagar dakin Amarya ta dasa kujera ason jin me zasu tattauna daya shiga daki tun yanzu tsabar zirgilli se gashi ta jiyo wa kanta abinda yafi ƙarfinta ta ringa kuka a tsakar gida jin Audu yana yiwa Amarya kyaututtuka cikin fitar hayyaci yace har gidan da suke ciki ya bata. Hadiza dake girki ta ringa wa Binta dariya kamar zata kife, faɗi take "Allah ya ƙara, a garin gulma da munafunci zaki jiyo abinda ze toshe miki dodon kunne ki dena ji gaba daya" "Idan baki rufe mun baki ba senayi ƙasa ƙasa dake Hadiza" Bintan ta zaburo mata. Hadiza ta gyara tsayuwa ta dafe kwankwaso tace "Idan baki fasa ba Binta, ai kin san karon mu dake wancan da nayi miki kadan ne wlh yau sace ki zanyi tas dan naga wannan luhu luhun jikin naki yasa kike neman masifar mutane" "Zaki gane kurenki wlh dani kike magana" Binta ta maida mata tana shigewa daki dan ba hauka takeyi ba da zata sake gwabza dambe da Hadizan har yau bata gama jinyar ƙasusuwanta data tasamma karya mata ba. Haka Ango ya yiwa Amarya sati guda, rawar kan da ya ringayi ba Binta ba Hadiza kanta ranta ya sosu amma da yake ita tana da kissar zaman duniya seta shanye bata ko nuna a fuska ba wannan tasa Audun yake ta tata ya kuma hadata da Amarya a cewarsa ta zama ƙanwarta ta ringa kula da ita Binta kuwa data tayar masa da hauka fita yayi a sabgarta ta nemi shiga sabgar yar Amaryarsa da banda gaisuwa da murmushi babu abinda ke hadata da mutanen gidan nan ya nuna mata ya fita hauka. "Wlh ko bisa kuskure naji hannunki ya taba jikinta se kin gane baki da hankali" ya faɗawa Binta sanda tayi niyyar marin Aisha lokacin daya hadasu su ukun. Haka aka ci gaba dagurgura rayuwa, watanni uku Bi ta ta tayarwa da Audu zancen ya kamata a ɗebo yaran Bara'atu da Tagwayen Zubaida su dawo gida kodan saboda makaranta dan a yanzun ta dan rage abubuwa a ƙoƙarinta na son maido da darajarta data zube a idona Audun. Ya kuwa ji dadin maganar harya zanta da Hadiza da kuma Aisha. Hadiza tace zata riƙe su, zata karbe kayansu tunda daki daya ne da ita ba ze yuwu su ringa kwana can ba se su zauna nan dakin da Abdullahi yake amma Binta tayi tsallen Albarka tace ba'a isa ba. Ai ita ta tado da maganar a dakko su kuma ita ta zauna da uwarsu ita suka sani sannan itace babba a gidan dan haka ita zata riƙe Yaran. Daman ita Aisha yar kallo ce a tsakaninsu, idan ba an sako ta ba tafi ku mutu bata ce musu, seta wuni a daki in har ba ita take da girki ba shine zata fito Mairo tanayi tana kallo harta fara karban wasu abubuwan tana tayata dan a gida bata girki kusan yanzu ne ya kamata ace an fara sakata ire iren wadannan ayyukan se kuma Aure yayi mata sammako shi yasa koda suke rigimar waye ze riƙe yaran bata saka musu baki ba ƙarshe da Audun da kansa yace Binta ce zata riƙe yara haka kuwa akayi ya debo su suka dawo gidan, an musu nisa a makaranta wannan tasa aka sake maidasu baya Zakariyya ya wucesu se aka hadasu su biyar harda Naziru aka saka su. Zama yaci gaba matayen uku suka samu ciki kusan lokaci daya, Binta bata lura da cewar sauran biyun duk sun samu ƙaruwa ba domin a duk sallar da zatayi se tayi addu'ar Allah yasa duk su kasance juya basa haihuwa ita kuma Allah yasa duk shekara tayita haihuwar Yara Maza ta cika gidan dasu tana ta kaɗifiri da iyayi wai ita me ciki bata san su biyun ma sun rigata samu ba se randa zataje Asibiti ta fito ta gansu duk su biyun kowa da shirin fita, bata ta Aisha domin tunda ta ganta tace wannan me sauƙi ce Hadiza ce a gabanta dan haka ita ta harara tana cewa "Karma ki kuskura kice yau ma binmu zakiyi, ba zaki tashi fita ba se kinga zan fita da Mijina to se ki taka ƙafarki ko ki fita ki hau Bus" "To ai yau ba ranar girkin ki bace balle ki nuna mun isa da iko, Miji kuma namu zakice dan bake kadai kike dashi ba" Hadiza ta maida mata. Aisha na gefe tana kallonsu bata ce uffan ba sema lafewa datayi jikin katanga tana kallonsu sega Audu ya fito "Uhm Bismillahi zaku fara ba kudai se kace kajin hausa wlh baku da aiki se faɗa ce cacar baki Allah ya sawwaƙa muku" ya faɗa yana baza babbar riga. Binta ta tunzura dan ta tsani wannan wulaƙancin da yake mata a gabansu ya ringa nuna ita ba komai bace daidai suke da ita dan haka tace "Idan ma fita zatayi ka gaya mata ko ta taka ƙafarta ko kuma ta nemi Bus dan ba zata bimu ba" "Tunda motar takice?" Ya mayar mata ba tareda ya kalleta ba, ya juya kan Aisha ya dan saki fuska yace "Bismillah, muje ko?" "Kuje ina? Au itama fitar zatayi?" "Kinga Binta idan baki zuwa ki koma ciki suma duk Asibitin zasuje". Tana cika tana batsewa suka fita wajen tayi wuf zata shige gaba Audu ya dakatar da ita da cewa "Shiga baya, Aisha ce zata zauna gaba" Hadiza ta kwashe da dariya Binta ta sake ƙuluwa ta lailayo Ashar ta watsa mata ita dai ta shige mota tana cigaba da dariyarta. Bayan sun isa Asibiti tana tsammatar taga kowa ta kama gabanta dan a zatonta dubiya su biyun zasuje se gani tayi sun nufi bangare daya na yan Awo dan a waje ya ajiye su yace idan yaje kamfani Musbahu and juyo da motar ya jirasu ya mayar dasu gida. Binta ta ringa binsu tana jira taga abinda ya kawo su gurin Awon ciki sedai daga yanda taga suna gaisawa da Ma'aikatan gurin tasan da sanayya a tsakani suka zauna gurin jira ana bin layi bayan an karbi Katunansu jikinta har rawa ya dauka sanda taga kowa ta zaro kati daga jaka ta miƙa kenan duk cikine dasu bata sani ba? Yaushe akayi? Tana zaman me? Aka ringa kiran Binta Zakariyya ina bata ma jisu ba tayi nisa a duniyar tunani da zullumi karfa suma duk su haifi Maza dan taga kamar Audu bashi da ƙwan haifar ya mace. Matar da take musu awon ta kallera tace "Baiwar Allah tunanin me kikeyi haka duk kin firgice kalli fa har jininki ya ɗaga?" "Kedai kiyi aikinki ki sallameni ina da abinyi" Binta ta gwaɓa mata magana aiko matar ta harziƙo itama tace "Se nice banida aikinyi ko ai bacci kika ga ina yi yanzu ko rawa" "Kiyi haƙuri Sista" Hadiza ta tsoma musu baki aiko Binta tayi kanta da masifa ganin a waje suke yasa ta mata shiru se ma'aikatan ne suka haye itama Bintan kamar sa cinyeta Awon da ba'ayi mata ba kenan ta tattara ta fice ta haye Bus se unguwarsu Turai dan tana buƙatar su tattauna wannan matsala ta yaya za'ayi su biyu suyi ciki. Audu kuwa isarsa kamfani ya tarar da wani mummuman Labari, motoci guda biyar da suka dakko masa Mai daga kudu haka nan wuta ta tashi sun ƙone ƙurmus harda direba guda daya dayayi ƙundunbala saboda motarsa ce ta ƙarsher sun tsaya zasuci abinci Abin ya faru tamkar Tsafi kawai wuta ta kama motar tsakiya kanka kace me sauran sun dauka an hanashi amma ya kafe ya tafi a zatonsa ze iya janye motar kafin wutar ta cimmata se gashi yana shiga ta kama gaba daya se tokarsa aka tattare. Babban abin al'ajabi kamar yanda aka bashi labari ba iyakacin motocinsa bane a gurin mota tafi Ashirin da suka taho tare duk sukayi fakin suna cin abinci amma ibtila'in akan nasa suka sauka basu taba komai ba duk kuma iyakar ƙoƙarinsu na su kashe wutar abu ya gagara. Hankalin Audu ya tashi matuƙa domin ba ƙananan kudade ne suka narke ba sannan ga Rai da aka rasa. Gaba daya suka ɗunguma gidansu Direban daya rasu me suna Lawan sukayi musu Ta'aziyya, ya bawa Iyalansa kudade masu ɗan kauri da kayan abinci yace kafin su yanke abinda ya kamata suyi musu. Wannan damuwar tasa ya manta da matansa na Asibiti a can kuma bayan sun gama har bayan Azahar shiru Musbahun dayace ze zo ya maidasu beje ba Hadiza tace su tafi kawai ta yuwu aiki yasha kansa ya manta. Hakan ko akayi suka kamo hanya suka dawo gida, sun sauka a bakin titi Hadiza tacewa Aisha "Ko zamu ƙarasa gidan Yaya Yakubu dan naji Babansu Baba yace sunzo gari muje muyi Bikon Yaya Balaraba be kamatu ace bama zumunchi da ita ba gaskiya" "Amma bazeyi faɗa ba?" Aisha ta faɗa cikin sanyinta. Hadiza tayi murmushi tace "Haba dai gidan Yaya Yakubu ne fa babu faɗan da zeyi kuma tunda ba girki zamuyi ba kinga bamu da matsala da anyi la'asar se mu wuce gida idan ya dawo se mu sanar masa da munje". Faran faran Balaraba ta tarbesu daman ta dan wayi Hadiza sukan hadu idan tazo gidan Yayarta lokacin da suke can unguwar suma Aisha ce bata sani ba dan bataje gidan ba Yakubun dai yaje yaga Amare da yace suje tace Aa ai bata da sauran dalilin zuwa gidan Audu kuma. Se da sukayi sallar La'asar sannan sukayi haramar tafiya ta hada musu tsaraba cikin abubuwan data zo dasu, Dada da jininsu ya haɗu da Aisha tana ganin sun tashi tacezata bisu "Ki bari muje da ita idan yaso se Baffansu ya maido ta anjima da daddare" inji Aisha suka tafi da ita. Sun riga Binta komawa gida itace da girki kuma, sun tarar da yaran sun dawo daga makaranta Abdullahi ya tafasa musu taliya sunci da sauran miyar da yace ya gani a Kicin, shidin yana gida yanzu sun gama jarabawar fita daga sakandire da Audu yace ze fara zuwa kasuwa se kuma yace ya zauna ya huta dan ƙasar qaje yake da burin turashi idan takardar sa tayi kyau. Binta bata dawo na se guraren biyar da rabi ta shiga gidan tareda Lantana da alama ko ta biya ta gidan tane ta kirata shigarsu babu jimawa Mairo ma tazo ta fara shirin dora abincin dare. Shiru shiru har akayi Isha'i Audu be dawo ba, Binta ta sake cika tayi dam saboda ita keda girki shiyasa yayi zamansa a waje da waccen yar shilarce ai da tuni a gidan ma zeyi Magriba jikinsa na rawa se kace nata Matancin na Gwal ne. Har tara ta buga shiru babu Audu, Hadiza ta leƙa falon Binta dake zaune tana kaɗa ƙafa tana kuma ayyana tijarar da zatayiwa Audu yau idan ya dawo taji muryar Hadizan na tambayarta ko ya shigo. "Ke matarnan ki fita daga sabgata wallahi tallahi idan kika tiƙeni sena miki abinda bakiyi tsammata ba. Wato kunga gurin zama har kun bude mara kun ɗauki ciki to wlh ku kwana da sanin zaku haifesu a gidajen ubanninku kuwa" Binta ta faɗa tana miƙewa tsaye. Hadiza da fuskarta ke cike da damuqa tace "Ni ba tashin hankali ya kawoni gurinki ba, gani nayi ya zarta lokutan daya saba dawowa kuma idan ma zeyi dare irin haka yana sanar mana shiyasa hankalina ya tashi. Mijina na fari daga irin wannan fitar shiru shiru se bugamun ƙofa akayi na buɗe aka shigo da gawarsa" "Keta shafa wannan ni tsakanina da tsohon mijin naki ai Allah ya isa ce da be mutu ba ai da Mijina be kwaso mun ke kinzo kin addabeni ba, ki barmun ƙofar daki kuma Audun ai ba Ji njiri bane da za'ace ya bata" Binta na rufe baki sujai dirar mota mintina kaɗan ya shiga fuskar nan kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa be kulasu ba ya durfafi sama harya fara hawa meya tuna kuma ya sakko ya wuto Ɗakin Binta. "Au da hankalinka ya gushe can zakayi kenan an maka kiranye ka shigo kamar wanda aka jefo baka ko gani dakyau ai seka tafi can ɗin" Binta ta faɗa tana babbake ƙofarta. Hadiza tayi masa sannu da zuwa ya ɗaga mata hannu yana cewa Bintan "Matsa na shige" "Ai sedai ka koma inda da ka niyyaci zuwa" inji Binta. Tsaki me ƙarfi yaj ya juya ya haye saman Hadiza tabi bayansa Binta ta kwarma Ihu murya a sama tana kiran yau akwai tashin hankali a gidan ashe. A saman kuwa harya fara cire kaya Hadiza ta isa, a tausashe take cewa "Da alama gajiya tasa ka manta ba a nan kake na yau" "Ina sane, sedai in kema korata zakiyi se in tafi" ya bata amsa. "Ba haka bane, rigimar Maman Zakariyya ce bana so kana jiyowa gata can tana masifa bana son tashin hankali ko ƙo dazun a Asibiti seda aka ce mu guji yawan hayaniya" ta sake faɗa cikin taushin lafazi. Audu ya rafka tsaki, da matan nan sun san me yake ciki da sun ɗaga masa ƙafa. Rigarsa ya raruma ya sauka sukayi kiciɓus da Binta na hawowa ya raɓeta ya wuce ɗakin Aisha. Ganinsa ba yanda ta sababa yasa ta masa sannu da zuwa ya shige ɗaki ta bishi da ruwa, tana jiyo hayaniyar Binta dukda bata jin me take faɗi sosai. Abincinta ta kai masa beci ba yana kishingiɗe ya harɗe hannaye ya zurawa guri daya ido, ta ajiye, tana so ta tambayeshi ko lafiya amma ta kasa se kawai ta fita ga Dada da tayiwa mamarta alƙawarin za'a maidota hartayi barci yanayinsa kuma ya nuna ba lafiya ba balle tayimasa maganar. Tana zama Binta ta faɗo kamar jifa, ta mata kallo daya ta maida idonta kan Talabijin yanayin kallon Hadarin kajin da tayi matan ya saka Binta yin shiru dan kwarjini yarinyar ta mata, tabbas Sarauta ba Ƙarya ba. Ɗakin data san zata samu Audu ta tura ta shiga, Aisha bata san ya sukayi ba taga Binta ta fito sumi sumi ta wuce. Data sake leƙawa se taga kamar yayi barci dan haka ta shige dayan dakinta suka kwanta tareda Dada. Page 31 Seda aka kwashi sati daya cikin wani yanayi a gidan, Audu ba magana babu murmushi bare dariya duk kuma wadda tayi kuskuren shiga sabgarsa ta jawa kanta tijara. Basu san me yake faruwa ba se randa zugar Yan Bechi suka zo Bus biyu ranar befita ba kusan kwana biyu ma kenan be fita ba sedai yaransa dake ta zarya a gidan kuma sedai su fita can inda yake ajiye mota suyi magana ko Binta duk iya labenta bata tsinto abinda ake ciki ba har seda yan Bechi sukazo jaje. Ashe bayan motar Mai kwanaki Babbar Gonarsa da yake noman shinkafa ruwa ya shanyeta. Gonata ba yar ƙarama ba. Shinkafar kuma tayi kyau dan har an saka ranar girbi Dam din dake kusa da inda yake Noman yayi ambaliya gana ɗaya ya shafe gonakin dake kan hanya abindai ya munana ba'a cewa komai. Binta ta ringa kyarma jin Maƙudan kuɗaɗen da aka ce sun narke daga kan Mai zuwa shinkafar, "Shikenan, a garin kwashe kwashenka ka kwaso mana me farar ƙafa" ta faɗa hannu biyu aka jiki na tsuma hawaye suna sakko mata. Duk akayi shiru aka zuba

Chapter 30 of 32