ya kwankwasa kana ya murda handle din qofar. Fahimta da yayi a kulle take yasa ya zagaya ta window ta da yake a tsakar gidan ya zuge ya leqa ciki, kayana da ya gani barbaje suka fahimtar dashi bata nan, se abin ma ya bashi dariya a fili yace
"Yaji tayi kenan"
"Ki tafi na manta zataje zata fita yau ta fita da wuri ina bacci" ya fadawa Lantana, kamar zata fasa kuka haka ta ja qafa tana waiwayensa, kamar tace masa zata zauna ta jira tunda ko fita Bintan zata yi tana barinta tayi mata jiran gida gashi ta kwaso yunwar safe ta saka rai zatazo taci me kyau kuma ace bata nan.
"Alhaji Mairo tazo ne? Kuma zuwa yaushe Hajiyar zata dawo?" Ta fada tana sunkuyar da kai,
"Idan ta dawo zata saka a kiraki ba yau ba ba gobe ba, kija qofar ki tabbatar kuma ta rufu idan kin fita" ya bata amsa yana juyawa tilas ta fita taja musu qofar gidan. Audu kuwa kasa komawa bacci yayi, tunanin inda Binta ta tafi ya shigayi, qila ba zata wuce gidan Baturiya ba dan bata da yar uwa a Kano bare yace gurinsu zataje Baturiyar itace yanzu babbar Qawarta ko yace Aminiya indai ba gidanta taje ba to Kaduna ta tafi.
Zabura yayi ya miqe yana salati, idan Kaduna ta tafi ya Alhaji zero dauki maganar? Ze goyi bayansa ko kuma ze goyi bayan yarsa ne? Idan Alhaji ya goyi bayan Binta yace ya sakar masa yarsa ya makomarsa zata zama kenan dan dai Alhajin shine abin tunqahonsa, duk abinda yake ganin ya tasarma zama da bazar Alhajin yake rawa.
A gurguje yayi wanka ya shirya, kai tsaye gidan Ali ya fara zuwa suka hade a waje Alin na shirin fita ya kuma tabbatar masa Binta bataje gidan ba dan babu inda zata buya da ze kasa ganinta.
"Dan girman Allah kazo ka rakani Kaduna" ya roqi Alin
"Kai yanzu? Ina babu wannan magana, ai yanda ka tirko rigimarka se ka san ta yanda zaka kasheta. Amma fa ban taba dauka da gaske kaci kai ba Audu se yanzu, duk matan da suke garin nan yayan mutunchi ka rasa wadda ta burgeka se wannan yarinyar? Kodai Asirinsu tayi amfani dashi ta zarge zuciyarka?" Ali ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki kafin ya shige mota ya daga ba tare da ya bashi amsa ba
Yau dinma Musbahu yaje ya dauka suka tafi Kaduna, seda ya isa qofar gidan kuma ya fara tunanin me zece musu idan ya shiga? Seda sukayi sallar La'asar da Magriba da suka riskesu a hanya kafin ya saka kai cikin gidan. Ko ina tarwai da haske, Tun daga Get suka fara gaisawa da ma'aikatan gidan harya isa qofar falo. Ta ciki Munira ta hangoshi, ta kwasa da gudu tayi daki ta fadawa Binta da tunda tayi wanka taci abinci take rama baccin da batayi jiya ba.
"Wlh ko me za'ayi karki koma ai raini nema kamar ke ace a miki kishiya bayan duk fafutukar da daukar hakkin da mukayi muka fitar da waccen shine za'a dakko miki alaqaqai to babu wannan maganar" Muniran ta qara zugata.
Tun daga yanda Alhaji ya amsa masa gaisuwarsa yaji guiwoyinsa sun qarayin sanyi dama Mama tana musu iso a tsayw suka gaisa ta shige ciki, yau ko Kayan Alatun da ake tarbarshi dasu be samu ba Ruwa da Lemo ma Alhajin ne yayi magana aka kawo musu.
"Bansan ta taho ba Alhaji, na dawo daga sallar Asuba kawai na tarar bata nan" Audu ya fada bayan dogon shirun da sukayi kowanne kamar ya rasa abin fada.
Alhaji ya nisa yana kallonsa yace
"Me ya hadaku da har yasa ta baro gidan ba tareda saninka ba?".
Be boye masa komai ba ya bashi labarin Auran da yayi wanda yake ganin shiya tunzurata ta baro gidan, ya rufe da qaryar cewa
"Bansan cewa zasu daura Auran ba saboda tambaya kawai akaje".
Shiru Alhaji ya sakeyi yana kallonsa kafin yace
"Menene gaskiyar maganara data fada na cewar Yarinyar Karuwa ce?" Seda ya daga kai ya kalli Alhajin saboda kalmar daya fada din se yaga kamar tayi girma musamman ana maganar matarsa ne ina laifin yace tsohuwa, wannan ya tunzuro zuciyarsa ta raya masa ci masa mutunchi Alhajin ya tashi yi amma ya danne dan ko ya masa qarya bashida amfani tunda har magana ta fito amma a ina Binta taji wannan batun?
"Kayi shiru" Alhaji ya katseshi, kansa na qasa yace
"Gaskiya ne, amma ban aureta ba seda na maidata gaban iyayenta tayi Istibra'i kamar yanda shari'a ta tanadar"
"To akan me ka daki Mamana har kaji mata ciwuka a jiki?" Alhajin ya fadi ainihin abinda yafi damunsa a duk cikin maganar, se Audu ya daga kai da sauri ya kalleshi jin abinda ya fada.
"Wlh Mari daya nayi mata, shima kuma cin kwalata tayi a gaban yan uwana da sukazo fadamun an daura aure ta labe harta tsinci maganar shine ta shaqemun wuya nace ta sakeni taqi ni kuma zuciya tasa na mareta bayan nan ko yatsa ban nuna mata ba wlh" ya fada cikin kare kai. Alhaji bece komai ba yaja Intercom ya kira cikin gida kan Binta tazo, ba'a dauki lokaci ba ta fito tana jan qafa fuskar nan kamar dafaffen Kunu ta zauna kusada qafar Alhajin tana hararar Audu wanda ke kallonta yana mamakin abinda ya karceta a fuska kamar sunyi dambe da Mage.
Ce mata yayi ta maimaita duk abinda ta fada cewar Audu ya mata, tana kuka ta shiga shiryosu harma da abinda dazun bata fada ba na cewar daman Audun ya dade yana yawon ta zubar dinsa har kwanaki yake tafiya yayi acan in ya dawo kuma tayi magana ya zageta koya hada mata da duka qarshema tace idan ta fita har gidan yake kawo mata shidai kasa cewa komai yayi saboda mamaki, maganganunta kuma babu yanda za'ayi ace qarya takeyi tunda tabbas yana yawace yawaceb har yaje ya kwanan amma ai ba abinda take fada yakeyi ba sedai kuma waye ze bada shaidar hakan?
Shidai Alhaji na jinta yana kuma kallon Audu daya kasa rufe bakinsa seda tayi shiru kafin ya kalleta yace
"Kinaji ko Mamana, duk wani Aure da kika gani tattare yake da qalubale muddin kuma ba ma'aurata sun bude cikinsu ba bazaka taba sani ba dan haka kowa haquri yakeyi kamar yanda kika faro haqurin kici gaba dayi kuma tunda ya auro yarinyar da take dauke masa hankali a wajen ai magana ta qare se ayi fatan kuma Allah ya hada kanku ya bada zaman lafiya. Kaikuma abinda nake so na gaya maka shine ka tabbatar kayi na farko kuma kayi na qarshe da zaka dora hannu da sunan duka a jikin Mamana, zan manta da duk wata alaqa dake tsakaninmu na maka ka a Kotu domin bana hada kowa da yayana, ban daki yar kowa ba dan haka babu hujjar da zata saka wani ya dakar mun yata. Idan tayi maka laifin da ba zau iya sasantawa a tsakaninku ba ka kawo mun qararta nizan hukuntata amma bazan lamunchi duka ba ina fatan ka gane?"
Kunya, nauyi da takaici suka rufe Audu gaba daya ya rasa ma abinda zeyi, Alhaji yaci gaba da cewa
"Idan Allah ya kaimu gobe yanda kikazo da sassafen nan ki tattara ku koma aje aci gaba da haquri kuma na kashe maganar nan, Aure kuma dakayi Allah ya sanya Alkhairi ya baka ladan Jihadi"
"Wlh bazan koma ba, babu yanda za'ayi nayi zamab kishi da Karuwa Dady kawai kace masa ya saketa idan ba haka ba bazan koma gidan ba" ta fada cikin kuka tana bubbuga qafa.
Page 18
Ki bude kunnenki dakyau kiji abinda zan fada, dukiya da kike tutiya akanta ta Abdullahi ce, duk abinda nayi masa kyautace halak malak dan haka ko ki bishi ki koma, ko ki dage ya sake ki zabi ya rage naki amma ki sani sisin kwabo baze maidamun ba dan ya rabu dake ko wani abu saboda dama badan ya aureki na bashi ba, tashi ki bani guri karki qara mun ciwon kan da yake damuna" Alhaji ya dakatar da Binta dake ihun kuka.
Sanin halin mahaifin nata kaifi dayane yasa ta tashi ta koma ciki tana cigaba da kukan ta labartawa Mama yanda sukayi.
"Ahto seki shirya ki koma daman duk tsuntsun daya ja ruwa ai shi ruwa ze doka, ke kika zabe shi dan haka dole ki jure duk wasu tazgado dake tareda zama dashi kishiya kuma naga wata kika tarar kowa da halinta zata zauna ai ba kuma kanki ze ajiyeta ba" abinda Mama ta sake gaya mata kenan haka tana ji tana gani suka kama hanya da farar Asuba ba tareda ta hadu da sauran yan uwanta ba wadanda su ta saka ran zasu bata shawarar yanda zata yida wannan Al'amari, da Munira suka sake tattaunawa da dare ta qara masa karatun yanda zatayi ta hana Amaryar shigo mata gida dan basu hasko ma ta shigo balle ta zauna.
Haka suka sha tafiyar bata ko kula Audu sedai shine yake tankata lokaci lokaci daya gaji da yanda ta shareshi yayi shiru har sukazo Kano, yana Ajiyeta ya fita itama bata zauna ba jakarta kadai ta shigar daki ta fice gidan Turai.
"Wlh Turai ko a jikinsu, babu fa wanda ya daga maganar Asalin matar daya aura din kamar ma basu fahimta ba haka suka share zancen har a gabansa Dady yana wani jaddadamun duk kudin daya bashi ba Aro bane kyautace kuma ba saboda ni ya masa ba, wlh da na shirya rabuwa dashi amma wannan dalilin yasa na fasa. Babu yar iskar dazan tafi na barwa gida tazo ta wataya da kudin ubana".
Duk da yanayin jimamin da suke ciki seda Turai tayi dariyar maganar Bintan ta kuwa sake harzuqa tace
"Au ga mahaukaciya ko ina magana dariya ma kike mun"
"Ba haka bane, ke dince da abin dariya waini in tambayeki Binta tsakaninki da Allah Audu kike so ko kuma Dukiyarsa?" Turai ta fada tana kallonta.
Ta zabga tsaki kafin tace
"Duka gaba daya, kinga Audu yayi mun daidai da tsarin Mijin da nake burin na Aura cikas dinsa daya rashin wayewar Boko amma abinda yaja hankalina harna yarda na Aureshi saboda yanda Dady ya ke labarinsa na san gobensa zatayi kyau zeyi Arziqi. Turai ina son kudi ina so kuma na auri me Kudi, dukda nayi samari masu kudi yayan masu kudi abinda yasa na zabi Audu a cikinsu saboda shi be waye ba, zan iya masa wayo na samu abinda nake da buqata a gurinsa sannan na hana kowa rabar sa ya zamani ni kadai zan moreshi se yayana, ba qaramin takaici naji ba dana samu labarin yana da mata harda yaya kuma tun sannan na daura Aniyar seta fita ta barmun gidan, bayan nayi nasara sannan ga Arziqi nan yana qara habaka se kuma na bari wata tazo ta tayani ci? Wlh baze yuwu ba dole koda tsiya koda Arziqi matar nan ta koma inda ta fito babu yanda za'ayi na zauna da kishiya a gidan Audu".
"Yanzu dai plan A ya ruguje se mu tafi ga shiri na biyu, kuma ina so ki kwantar da hankalinki qawata shi yaqi akace fan zambo ne, yanda kikayi da Bara'atu haka zakiyi da wannan ma koda ace ta shigo cikin gidan, yanzu abinda zakiyi, lambo lambo zaki masa ki nuna masa kinyi nadamar abinda kikayi ki bashi haquri kisan duk yanda zakiyi yabyarda dake ta haka ne zaki yi komai ba tareda ya zargeki ba, kamar dai lokacin Bara'atu ai kinga kin nuna masa kina sonta harta fita be taba sanin irin gallazawar da kika ringa mata ba" Turai ta fada
"Turai! Wannan fa ba Bara'atu bace, kefa kika ce mun kilaki ce ta ina zan iya goga kishi da yar Bariki Turai?" Bintan ta fada cikin yanayin dake nuna tabbas ta tsorata da Amaryar da Audun yayiwo mata. Turai tayi murmushi tace
"Dadi na dake Damusar takardace, ga tsoro ga ban tsoro, yanzu har akawai wata kisisina da matar bariki ta iya waddda mu bamu iyata ba? Meye a cikin barikin ne da har zata naki tsoro? Kinga fa yaqin nan dole se kin dage idan ba haka ba kina zaune zata shigo kuma ta kwace Mijin"
"Allah ya rufa asiri, wlh ko zan mutu bazan bari naga wannan rana ba" Binta ta fada tana fashewa da kuka Turai tayi dariya tace
"Bama zaki mutu ba sedai ita me shirin yi mana kutse ta mutu, yanzu dai kamar yanda na gaya miki kije ki lallabashi ku daidaita, da an kwana biyu kic zaki Bechi ki gaishe su a can zaki kwarkwance komai ki gaya musu wacece ita son samu ki fara sanar da Yayansa na Lagos nasan ko beji maganar na qauyen ba shi baze qijin ta tasa ba" da wannan shawara suka rufe ta koma gida ta yi matuqar qoqarin danne zuciya tayi duk abinda Turai tace.
Kuka wiwi ta ringayi tana bashi haquri da rantsuwar ba zata sake ba yanzun ma sharrin shaidan ne tayi iyayinta har seda ya sakko shima ya bata haqurin yanda Al'amuran suka kasance a qaryarsa wai besan za'ayi haka ba.
"Amma banji dadin yanda kika kwanceni a gaban Dady ba, na dauka ko abinda kika fada gaskiya ne ke me rufamun Asirice a ko ina" ya fada in relevant to zancen yawonsa data gayawa Dady. Kanta na qasa tana share hawayen kissa tace
"Kayi haquri, wlh bansan abinda ya shiga kaina ba kan yafemun Mijina kaji dan Allah"
"Ya wuce, Allah ya yafe mana gaba daya sannan in Allah ya yarda nan da kwana Goma Zata tare, ina so ki lissafa duk abinda kike da buqata da wanda za'ayi amfanin yinin Biki a can Bechi"
Wani abu ya caki ranta amma ta shanye tace
"Shikenan zan lissafa, yaushe zamu tafi Beechin toh?"
Da mamaki ya kalleta jin yau anyi zancen zuwa Bechi salin Alin ba ta fadi mara dadi ba, ransa ya qarayin fari yana qara gasgata da gaske tayi nadama dan haka yace mata se saura kwana uku zasu tafi da anyi yini yau washe gari au dawo gaba daya da Amarya ta amsa da Allah ya nuna mana a Ranta tana ayyana Bura'ubar da zata tafka a Bechi idan sunje.
Haka ko akayi, tana kallo aka ringa fenti aka shigo da sababbin kayan gado da kujeru aka saka a tsohon dakin Bara'atu baqin ciki kamar ya murqusheta ta mutu wato cikin dukiyarsu yayiwa Tsinanniyar Amaryar kayan daki, takaicin kanta ya sake rufeta datayi wautar cewa ya barshi bata buqatar komai duk a salon wanke kanta gurinsa. Ranar Laraba suka tafi Bechi ita da Direba daya hadata dashi tareda kayayyakin amfanin girkin da ba za'a samu a can ba, Juma'a za'a kai Amarya can ayi yini su Kwana Asabar su juyo.
Wai se ga Binta na bi gida gida daki daki na yan uwan Audu da sunan taje su gaisa abin dariya ita ce har gidansu Bara'atu. Duk gidan data shiga bata fitowa seta kwance Amaryar Audu ta fada musu tsohuwar kilaki ya auro, Bilki da tun sakin Bara'atu ta fita a sabgar Audu da gidansa farko cin mutunchin Binta taso tayi da ta je mata gida amma zancen data kai mata ya tayar mata da hankali. Me yake damun Audu? Wace hau ce ta haushi da ze auri Karuwa? Hankali tashe ta tafi gida ta samu su Yaya Babba duk sun tattaru dan kowanne na komawa gidansa da yamma ya samu saqon da Binta ta bari shiyasa suna idar da sallar Isha suka tattaro suka taho gidan gaba daya ita ko Binta tana masaukin su da aka qara gyareshi, rabon su duka ya siye banda na Yakubu dan nan yake sauka idan yaje se ya qara fadada nasan yayi dakuna manya da bandaki a ciki.
"Nifa tun ranar da mukaje neman auran kun tuna sanda na fita zagayawa a lokacin naji wasu suna qus qus din wai anya wadannan sun san labarin Yarinyar suka zo nema dansu aure? Basu dai fadi komai ba amma wannan magana tasu ta jefani a wasi wasi sedai tunda shi ma'auri wakilci kawai ya nadamu shi yasa nayi shiru bance komai ba" Yaya Baba ya fada, Aminu yace
"Haba Yaya, menene amfanin girman idan ba zaka ga abin da ba daidai ba ka gyara mana? Yanzi da kaji wannan magana ai ko a tsakanin mu seka gaya mana idan yaso mu basu kudin Aure mu tafi ba zamu yarda a daura ba har se an bincika munji dar din maganar halin nata, na tabbatar shima be sani ba yanzu ya za'ayi?"
"Amma ku kuna ganin gaskiya wannan yarinyar ta fada, kun manta sharrin ta kenan?" Hashimu da be manta kitimurmurar Binta ba ya fada. Bilki tace
"Bana jin qarya ne, tunda ga Yaya Baba ma yace yaji wata magana, yanzun dai mu jirayi Yaya Yakubu ya iso gobe idan Allah ya kaimu in yaso se mu san abinyi kafin Audun ya qaraso shima" inji Bilki, haka taron ya tashi, washe gari ko da Rana Yakubu da Iyalansa suka sauka Bechi. Binta batayi qasa a guiwa ba ta shige ko gajiya bata barshi ya ware ba yana aje haqarqarinsa a kujera ta zube a gabansa ko kallon inda take Bakaraba batayi ba taja yaranta suka shige daki.
Bilki tayi turus da kayan abinci a hannunta tana kallon Binta dake rusa kuka a gaban Yakubu tana masa bayani se ta fara jin anya maganar nan da gaske ce kuwa kodai wasan kwaikwayonta data saba ne ta hadashi?
"Yanzu saboda Allah ba zaki barshi ya ko huta ba zaki tasashi a gaba da wannan maganar?" Bilki ta fada taba harararta.
"Zauna Bilki" ya bata umarni kafin yaci gaba da cewa
"Menene gaskiyar abinda ta fada?"
"Yaya muma ita tazo mana da maganar, amma Yaya Baba yace..." Ta fada masa abinda Yaya Baba yaji sanda sukaje neman aure.
"Shikenan tashi kije, zamuji ta bakinsa idan ya qaraso"
"Dan girman Allah kar kuce masa ni na gaya muku"
"Dama ba zamu fada ba tashi kije abinki" da haka ta fita rai fes dan koda Yakubu beyi wata magana ba daga fuskarsa ta fahimci ya kadu da maganar.
Tana fita Balaraba ta fito daga daki tace
"Yanzu kun yarda da maganar wannan annamimiyar matar? Matar data laqawa wata sharrin kisan kai sena Bariki ne ba zata dorawa wata ba? Koda yake Allah ya kawoshi gara yaji abinda ta hada ko idonsa ze washe ya gane da wadda yake zaune ai".
Yamma Lis Audu ya isa Bechi, seda sukayi sallar Isha kafin Yakubu ya tareshi a wajen dan baya so sauran yan uwan su fara masa magana ta yanda laifin Binta ze fito. Cikin siyasa da kwarewar aikinsa ya saka masa maganar a baki, yana da labarin yawace yawacen da yakeyi da wannan yayi amfani yace an gaya masa acan ya hadu da Amaryar tasa.
"Haka ne, amma ban aureta ba seda na maida ita gidansu tayi Istibra'i tukunna" ya bashi amsa kai tsaye. Yakubu ya ringa kallonsa ya gaza cewa komai, dakyar ya iya bude baki yace
"Amma yanzu na tabbatar da Audu baka da tunani sam, duk matan duniya ka rasa macen Aure se karuwa ko kuma asiri tayi maka?"
"Ni babu Asirin da tayi mun kuma ka dena cewa Karuwa tunda ta tuba ta bari sannan babu inda Shari'a ta haramta Aurena da ita tunda dai tayi tsarki sannan ni ina sonta a haka kuma nasan har a gurin Allah nayi aikin alkhairi jihadi babba nayi" Audun ya fada cikin yanayin ko in kula,
"Haka ne" Yakubu ya bashi amsa daga nan yasa kai ya shige gida ya bar Audun a tsaye.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
Tabbas yasan wannan lokacin zezo shiyasa yake yawan nunawa Dada rashin amfanin baiwa Audu damar yanke duk hukuncin da yayi masa ba tareda ya shawarci kuwa ba. Ita ta bashi wannan damar, shi a matsayinsa na babba bata taba daukar Maganarsa da muhimmanci ba domin a sannan tana ganin Audu ya fishi wayewa da sanin rayuwa, yasha gaya mata hakan bashida kyau domin idan ya yanke hukuncin daidai qata rana ze yanke akasin haka kuma baze taba ganin cewar yanayin abinda ba daidai din ba tunda ya saba cewar akoda yaushe shi yake bada shawara ba dai a bashi ba, yau da ace ta gina su akan turbar su shawarci junansu sannan su yanke hukunci akan duk wani al'amari na rayuwarsu ya tabbatar koda Audu na da taurin kai da kafiya tilas a wani bangaren yayi yanda ake so, gashi yanzu yana yankewa kansa danyan hukuncin da idan ba'ayi wasa ba se yayi nadamar su a gaba.
Tamkar dai Yakubun dmsanda su Yaya Baba suka tareshi suma tabbacin gaskiyar maganar ya basu be kuma saurari komai daga bakinsu ba ya shige daki inda Binta ta kasa kunne tana jira ta jiyo magana ta tashi amma shiru, washe gari Juma'a yan uwan Amarya Zubaida suka yiwa Bechi tsinke, su biyar se ita ta shida, dayan dakin dake kusada na Binta aka shigar da ita Mata nata turuwar zuwa ganin fuskar Amarya amma babu dama dan a rufe take daman gulma da munafunci ne kawai ya kaisu suga fuskar tsohuwar Karuwa. Binta na cikin Dakinta a kwance abin duniya ya isheta ta kasa fita har sanda aka fito da Amarya tsakar gida inda akayi shimfidu aka zaunar da ita Bilki ta shiga ta kira Bintan saboda Al'adace za'a danqa amanar Amarya a hannun uwargida.
Daurewa tayi ta qara barbada hoda, daman Leshi tasa me kyau daya qara fitar mata da suffar ta gaba gaba ta tura dauri gaba ta fita tana qoqarin danne shadan dake raya mata data fita ta cakumi Amaryar ta mata dukan mutuwa. Haka ta ringa yaqe har aka gama komai aka bude fuskar Amarya, ganinta tayi yar yarinya da kadan ta fi Bara'atu cika amma kyakykyawace kwarai duk da baqace, kaso ashirin na fargabarta taji ya ragu dan ta saka ran ganin matar da idanunta kadai zasu firgitata amma se ta raina zubinta.
"A haka dai gata kamar salaha amma wai tsohuwar kilaki kai jama'a Allah ka tsarkake mu ka tsarkake mana zuri'a" wata da bakinta bashida birki wadda kuma ta fita danyan kai ta cafe tana cewa
"Kedai bari Tsahare, aini abinda yafi bani mamaki ma Audun daya dakko wannan aba, anya ba juyar masa da hankali tayi ba dan dai wannan al'amari beyi kama da na wanda yake cikin hayyacinsa ba sedai aikin sihiri" seka rantse su kadai ne a gurin yanda sukayi maganar hankali kwance babu wata damuwa tattare dasu kamar wadanda aka saka maganganunsu kuma sun isa kunnen kusan duka mutanen gurin, Zubaida ta sake sadda kai qasa kuka na neman kwace mata, abinda take gudu kenan wanda ta tabbatar da seya faru, shi yasa bata tsarawa kanta yin aure ba koda ace ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 32