Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta saka Audu sallame sallar da yakeyi babu shiri ya fita daga daki da gudu, a bakin qofa sukayi kicibus da Yakubu da shima ya fito a rikice dan da gani ma daga wanka ya fito ya saka dogon wando ga rigarsa nan a hannu ko sanyin da ake busawa ma bayaji suka shiga turereniyar shiga dakin Dada inda Baballiyar yake qarawa Ihunsa qaimi matan kuma da duk suka fito suma harda Goggo Fadi sun tsaya daga waje kowanne abinda zuciyarsa ta bashi wuta ce tunda lokacin sanyi ana yawan samun wannan matsalar saboda Rushi da ake kaiwa daki dan aji dumi idan yazo da tsautsayi abinda ze iya kama wuta ya shiga ciki se kaga gobara ta tashi amma kuma basu hango jan wuta a cikin dakin ba ko kuma hayaqi to ko wani mugun kwaron ne ya cije shi? Yakubu ne akan gaba, burki yaci yana kallon Dada dake kwance idanuwanta a bude tana kallon rufin dakin hannunta daya na dafe da qirjinta dayan kuma ya saki ya sakko qasa, dukda cewar gawa daya ya taba gani ido muraran wato ta Malam amma baya buqatar a gaya masa cewar Dadan ta rasu. Lokaci daya wani kuka me cike da rauni ya kufce masa, ya durqushe gaban gadon Audu ya tsallake shi ya qarasa shigewa dakin dan be fahimci dalilin tsayuwar Yakubun ba ga Baballiya dabe fasa ihu yana kiran ya shiga uku ba. Hannun Dadan dake qasa ya daga ya maida kan gadon, sanyi qalau yaji shi, ya shiga jijjigata yana kallon fuskarta tareda kiran sunanta ganin ta zubawa guri daya ido Yakubu dake kuka kamar qaramin yaro, ashe Alhinin rasa mahaifiya ne ya hanashi sakat har seda ya kamo hanya ya dawo sedai an saba haduwar, bashida rabon zasu sake zantawa da ita rai yayi halinsa. Kama hannun Audu dake jijjiga Dadan yayi cikin kuka yace masa "Bari jijjigata ta rigamu gidan gaskiya" Ze iya cewa be fahimci abinda Yakubu yake nufi ba dan kwakwalwarsa gaza fassara hausar tayi dan haka ya shiga qoqarin dagata yana cewa Yakubun ya tayashi su fita da ita ya kaita Asibiti Yakubu ya miqe yana janye shi cikin daga sauti yace masa "Ka dena wahalar da ita Audu na gaya maka ta rasu" kalaman da suka fi duk wasu kalamai daya tabaji a rayuwarsa Muni, Dada ta rasu? Dadar da suka gama hira dazu daman duk wasiyya take masa? Kalaman Yakubu suka janyo hankalin su Goggo Fadi dake qofar daki take suka fasa kuka kafin kace me maqota sun jiyo aka fara shigowa rayuwa kenan tabbas dan Adam abin tausayi ne yanzun kaine qiftawar ido ana iya cewa babu kai. Duk wanda yaji rasuwar Dadan se yace jiya fa da La'asar sakaliya ya ganta a Mashin Audu ya dauke ta har sun gaisa, a masallaci ana idar da sallah aka bada sanarwar Jana'izar, kafin ko gari ya gama wayewa tangararau har an shiryata tsakanin Yayanta baka iya fidda wanda mutuwar tafi duka. Bilki suma tayi sanda saqon ya risketa Aisha tafita dauriya kuka ta ringayi Audu kansa duk taurin rai irin nasa ya koka hada kai sukayi da Yakubu suka ringa kuka gwanin tausayi. Bayan an kaita an dawo aka zauna zaman karbar gaisuwa, Goggo Fadi tayi wata zugewa lokaci daya, mutuwar Dadan ta daketa matuwa ta kuma yi nasarar maidata cikin hayyacinta. "Malam beyi sauri ba, nima zan bishi kuma kema kina tafe komai daren dadewa" kalaman Hafsatun na jiya suka ringa mata yawo a kwakwalwa ashe mutuwa Hafsatu zatayi? Da tasan haka da bata takaleta ba, data nemi yafiyarta akan abubuwan da ita da yayanta suka ringayi mata. Hashimu kansa yaji mutuwar amma da yake Dan Adam ne ana kwana daya ya ci gaba da sabgoginsa be ko sake zama gurin karbar gaisuwar ba ya bar su Audu dasu Aminu da idan ka ganshi zaka dauka mahaifiyarsa ce ta rasu. Su Audu kuwa ba'a magana duk sun sukurkuce bayasu ba baya matansu ba amma ya zasuyi haka aka share zama bayan anyi bakwai Abokanan Audu na Kano sunyi masa kara mota guda suka yi sukaje masa gaisuwa bayan da suka samu labarin rasuwar a bakin masu daukar kaya yan garinsu. Wannan karon tsakanin Audu da Yakubu rasa wanda ze lallashi wani ya koma bakin nemansa akayi. Seda Dada tayi sati biyar da rasuwa, Yaya Baba ya kirasu cike da Alhini bayan ya sakeyi musu gaisuwar rashin da sukayi kafin yace musu "Naga dukkanku baku da alamar komawa bakin neman ku musamman kai Yakubu da kuke tsaka da Karatu ka taho ya kamata kuyi haquri ku dauki dangana zamanku bashi ze maido da Goggo ba A yanzu Addu'a kadai take da buqata daga gareku sannan kuci gaba da jajircewa akan abinda take da burin ganin kun cimmasa". Maganar Yaya Baba tasa suka fara shiri jiki a sabule babu wani karsashi sun kasa sabawa da Rashin Dada, tunanin yanda rayuwarsu zata cigaba ba tareda ita ba sukeyi yanzu dawa zasu ringa barin matansu? Tunanin Audu kenan. Da dare ya samu Yakubu a bangarensu yana zaune shiru Balaraba na gefensa itama shiru duk ta fice hayyacinta tamkar Bara'atun sa ga tsohon ciki haihuwa ko wanne lokaci na iya zuwa shigowar Audun yasa ta cicciba ta basu guri. "Wata shawara nake da ita Yakubu" Audu ya fada bayan daya gyara zamansa. Yakubu ya kalle shi Audu yaci gaba da cewa "Daman akan Iyalanmu ne, kaga yanzu Babu Dada gaskiya hankalina baze taba kwanciya ace mu barsu a nan ba kaga dai halin da gidan nan yake ciki lokacin da ranta ma yaya balle yanzu da babu idonta" Yakubu ya jijjiga kai yace "Hakane, ni kaina ina wannan tunanin ga yanayin da suke ciki gaba daya kowacce na da buqatar kulawa ta musamman, amma kai menene shawararka me kake gani za'ayi?" "Dama dai tun zuwansu Ma'aruf na gaya mishi ya dauki kudi cikin cinikin da akayi a qarasa ayyukan da suka rage na gidan nan mu koma can kawai gaba daya da zama kaga hankalina zefi kwanciya na kuma tsaya a guri guda amma kai me kake gani?" Audu ya fada. Yakubu ya muskuta yana cewa "To wannan shawara ce amma kana nufin kenan zamu bar Bechi da zama gaba daya?" "To me muke dashi a nan da ze sa muci gaba da zama? Karka manta mun rasa uwa da uba dangi kadai suka rage mana kuma zamu ringa kawo musu ziyara lokaci lokaci musamman kaga Bara'atu iyayenta suna nan baze dauki lokaci me tsayi ba zamu ringa leqowa muna ganin dangin mu" Audu ya sake fada. "To gida kuma fa haka zamu barshi ya lalace?" Yakubun ya sake fadaz cike da qosawa Audu yace "Nidai na rigada na yanke shawara bazan iya cigaba da zama a gidan nan ba idan na kalli dakin Dada gani nake kamar zata fito daga ciki zuciyata bazata iya ci gaba da dauka ba" yayi maganar a raunane sukayi shiru baki daya kafin can Yakubun ya sake cewa "Ina ganin zan kama daki a Ikko da zamu iya zama da Balaraba zuwa na qarasa karatuna kafin muga abinda Allah zeyi" "Wannan shawara ce me kyau, amma kuma a halin da take ciki baze yuwu ka dauketa ba dole sedai a jira har seta haihu kuma kaga lokaci yana qara tafiya kamata yayi ka fara yin gaba kaje ka shirya duk abinda ya kamata idan ta sauka ta yada wanka se kazo ka dauke ta ku tafi ko ba haka ba?" Shawarar Audu. Yakubu yayi na'am da maganar tasa dan haka suka shiga shiri, sun sanar da matayensu abinda ake ciki haka yan uwansu da suke uba daya, Goggo Fadi ta fasa musu kuka sanda suka gaya mata shirin nasu tana cewa wai me yasa zasu ce zasu bar gidan kenan ita basu dauketa uwa ba ba zata iya kula musu da matansu ba? Daga Yakubun har Audu babu wanda ya kula maganganunta dan gani sukeyi ihu ne kawai bayan hari basu yarda wai har zuciya Goggo Fadin tayi tuba na gaske ba. A satin suka shirya tafi, sun tsara da gida ya kammala Audu ze kwashi Bara'atu da Balaraba duk su koma Kano da zarar Balaraban ta haihu kuma zata koma Wailari tayi wanka inda daga can zata bi Audu, da akwai Yayanta da yake zama a Ikkon shima Shanu yake kaiwa daga baya kuma yayi zamansa can matansa biyu ya kai daya can sunzo ganin gida zasu jima dan haka suka bari akana idan Yaya Iron ya tashi komawa zata bisu su tafi tare. Ana i gobe zasu tafi da maraice Balaraba ta haihu ta samu ya mace wannan karon Ubangiji ya bata da sauqi dan da tasowar ciwon gaske da haihuwar beyi awa daya ba, Audu ya fita qaraso musu siyayyar dan abinda zasu buqata kafin su koma Kano se dawowa yayi ya tarar da yar Baby me kama da Dadarsu sak haka ya kwasheta seda sukaje Asibiti aka tabbatar ita da yarta duk lafiyarsu qalau, farin ciki ba'a magana, Yakubu yayi mata hudu ba da Hafsatu zasu ringa kiranta Dada dan duk wanda ya gabta se ace Dada ta tafi Dada ta dawo. Haihuwar tasa suka qara kwana biyu, yan Uwan Balaraba suka dauketa zuwa gida wanka Audu ya wuce Kano tareda Yakubu daze koma Ikko. Wata daya bayan haka Audu da Bara'atu tareda Baballiya sukayi qaura Kano, qarshen zamansu a Bechi kenan. Ranar da zasu tafi mota guda ya dakko aka kwashi yan rakiya dan an kwashe kayansu daman tuni. Yan uwan Bara'atun uku Yayarta daya se Matar wanta da qanwar Babarta sauran sukace a hankali zasuje suga inda suka koma se murna suke tasu ta koma Birni suma sun samu gurin zuwa haka Inna Hajara har wani qafafa take tana yadawa wanda suka ringa Adawa da Auran Bara'atun da Audu magana ciki harda Babanta. Yan gidansu Audu ma kafataninsu su Bilki dasu Amina harda Matar Yaya Baba data Aminu da Amaryar Hashimu wadda se bayan sun tafi ya samu labari ya ringa tijara yana rashin mutunchi Goggo Fadi da tabi hanyar Allah tuni tun bayan rasuwar Dada batace masa qala ba, ita kanta taso zuwa amma ciwon qafa daya sakata gaba kwana biyu ya hana amma Audu ya mata Alqawarin da kansa ze dawo ya dauketa taje ta kwanar musu biyu kuma tafiyarsu ba tana nufin sunmanta dasu bane, basu da wasu dangi a duniya bayan su, su goman nan da Mahaifinsu ya haifa sune dangin Kansu. Yan Bechi suka ringa santin gida, kwanan su daya suka juyo Audu ya hado su da sha tara ta Arziqi qememe Abdullahi yaqi bin Babarsa Audu yace a barshi daman ai Abdullahi Dansa ne, uwar bata so ba dan daman ita ba wai son zaman da yake a gurin Bara'atun take ba kawai dai dan Aminun tsayayyae ne yasa ta kasa magana yanzun da Audu yace a barshi tace "Amma Babansa be sani ba zeyi fada idan aka koma babu shi" "Idan kin koma ki gaya masa ni Audu na riqe Abdullahi idan yana da jaa yazo ya dauke shi da kansa" ya fada mata zata sake magana Amina ta harareta tana cewa "Sedai kece zaki cr bakya son zamansa a nan dan dai Yaya Aminu ya dade da fadawa kowa ya barwa Audu Dan nan kuma wannan baqin ciki kikewa Danki ze zauna a Birni yayi Karatu me kyau ya tashi a waye" "Meye haka Yaya Amina?" Audu ya katseta, ta sake cewa "Gara na fada mata ai idan kuma ta ce se a bata danta gashi nan ta tarkata su tagi dana Koma zan hadowa Muzammilu kayansa a kawo maka shi ga Yaran nan tuli a dangi har wanda zaka riqr ze gagara ne?" "Audu yayi murmushi kawai jin abinda tace ya tashi ya fita bayan ya Ajewa Aminar saqon maganin ciwon qafa yace ta kaiwa Dada, haka suka koma Bechi aka bar su Bara'atu a sabon guri. Sannu sannu rayuwa taci gaba da tafiya, Balaraba ta yada wanka har taje Bechi daga nan tayo Kano ta kwanarwa su Balaraba Biyu kafin suka kama hanya da Audu daze rakata dan Yayanta Iro ya tafi da Shanu matarsa kuma tana da ciki ta kusa haihuwa wannan yasa Iyayensu sukace ta zauna ta haihu tukunna ta koma. Seda Audu yayi sati ya dawo rayuwa taci gaba. Sosai kasuwancinsa yake garawa. Kudin gonar su da suka siyar ya qara jari da shekara ta zagayo sun ninka kansu wannan yasa ya shawarci Bilki data kawo musu ziyara akan me ya kamata suyi, sun yanke cewar su nemi qananan Gonaki a ringa siya ta yanda a hankali kowa ze mallaki tasa aci gaba da juya kudaden kamar yanda yakeyi yana kuma fitar da riba yana bawa kowa saboda buqatu, gidansu ma Bilkin cewa tayi suyiwa su Hashimu tayi ko zasu siya dan ya mayar da gurin Rumbu kayan gonarsa yake ajiyewa a ciki Audu yace mata Aa su barshi saboda idan sunje su samu gurin sauka ze dai saka a gyara gurin a hankali. Page 9 Ranar wata Talata Bara'atu ta sauka a Asibitin Murtala inda Audu ya yankar mata katin Awo tun bayan dawowarsu Kano ta samu Da Namiji murna gurin Audu dasu Baballiya ba'a magana, wata maqociyarsu Baba Larai da suke mutunchi da Bara'atun tun tarewarsu ce tayi mata biqin kwana biyu kafin Audu ya tattarasu suka tafi Bechi, se ganinsu sukayi da jinjiri aka ringa murna a gidansu ta zauna seda akayi suna yaro yaci sunan Malam wato Tijjani suke kiransa da Babangida, Raguna biyu manya Audu ya yanka haka ya mata kayan barka irin na Birni duk inda ka shiga a Bechi labarinsu akeyi, lafiya lau tayi wankanta kwananta Hamsin da Haihuwa suka dawo Kano rayuwa taci gaba da garawa cikin ludufi da Amincin ubangiji. Kasuwancin Audu kam yana habaka dukda dai har sannan yana kan canje canjen sana'a dalili da duk wadda ya fara tabawa da an kwana biyu se abin ya fara sakin hannunsa tilas yake sake cafkar wata sana'ar ya dora wannan dalili yasa yana da ido acin kusan duk wata sana'a da ake juya kudi a samu riba, ba babbab ba qarama duk yana tabawa ita kanta Bara'atu be barta a zaune ba ya sakata tana taba sana'oi na mata na cikin gida kuma tana samu babu laifi ga Kitso da daman ta iya shima tanayi shiyasa idan suka tashi zuwa Bechi Sallah, Biki ko suna bayan abinda Audu ze bata haka itama zatayi ta Alkhairi wa yan uwanta da nasa, gida su kuwa baya rabo da dangi duk wanda ya samu dama ze zo Kano ya kwanar musu biyu ya koma. Yakubu na Ikko abinsa tunda Balaraba ta bishi seda suka shekara biyu kafin suka zo lokacin ya rage masa shekara daya ya kammala karatunsa kenan. Daga shi Har Balaraba idan kalle su seka qara, Yakubun ya waye ya zama wani baqin Bature hatta shigarsa ta canza zuwa coat baqa da farar yar ciki irin dai shigar su ta masu karatunshari'a ita kanta Balaraba Turanci har ya kama bakinta saboda suna tsakiyar wanda zo in kashe ka basu sani ba da Hausa. Ga Dada data jima da yayewa tayi kubibi abinta fatarta me haske irinta uwarta har sheqi take saboda zama cikin lullumi ga cin naman ruwa da suke se tsohon cikin da take dashi haihuwa ko wanne lokacin dalilin dawowar tasu ma kenan. A Kano suka sauka suka ringa yiwa Juna tsiya ita da Bara'atu da itama take dauke da ciki na Biyu watannin Babangida goma sha daya ta samu ciki sati daya kenan Inna Hajara ta dauke mata shi tunda ta kusa sauka amma ba bisa son ran Audu ba. Seda suka kwana biyu suka huta kafin suka tafi Bechi gaba daya niqi niqi da tsaraba daga can Balaraba taje garinsu su kuma suka juyo Kano seda ta gama kwanakinta ta dawo. Zamansu gwanin dadi, idan safiya tayi Mazajensu suka fita Kasuwa inda Yakubu yake bin Audu Baballiya da Abdullahi su tafi makaranta duk wadda ta riga gama aikin bangarenta zata shiga gurin yar uwarta, nan ma girki daya suke kowa ta dibarwa iyalanta. Wannan karon ma Balaraba ce ta fara haihuwa ta sake samun Mace kwana biyar tsakani Bara'atu ma ta haihu ita kuma Namiji wannan Dalili yasa Audu da Yakubu da duk sukace babu wadda zataje gida aka hade taron suna, ranar kwana bakwan Balaraba akayi mata yanka yarinya taci suna Maimunatu amma taro seda da dan Bara'atu Yusuf dayaci sunan babanta ya kwana bakwai akayi Yan Bechi sunzo da dangin Balaraba an sha buduri sosoi taro ya watse se yan zaman wanka da kowacce aka kawo mata daga gida Yakubu ya koma Ikko saboda makaranta haka suka cigaba da wanka Balaraba na yada wanka taje garinsu da Bechi tayi musu sallama Audu ya kaita tasha da Yayanta suka bi Yakubu Bara'atu kuma taci gaba da rainon Babannan da Babangida wanda Audu ya kafa kwarzaba seda aka dawo masa da Dansa ga kuma Baballiya da Abdullahi abinsu gwanin Dadi suke zaune. Bayan Baballiya sun rubuta jarabawar kammala sakandire wadda tsallaken Aji akayi masa saboda girmansa akayi sa'a kuma yana gane karatun daman yana Aji Takwas suka baro Bechi dan haka suna zuwa Kano Audu yasa aka kaishi Aji biyu na babbar Sakandire, ya dage akan shidai aikin soja yakeyi, tun Audu baya daukar abinda muhimmanci har nacin Baballiyar yasa shi tambayar yanda ake shiga makarantar sojojin. Wani Maqocinsa a Kasuwa ya tambaya dan yanajin yana fadar da akwai qaninsa daya tafi aikin soja, shiya gaya masa qanin nasa yana makaranta a Kaduna shima wani Dan uwan mahaifiyarsu ne dayake zaune a can ya samo masa kuma ance daya gama ze fito a babban soja ne ba kurtu irin wanda mutanen mu a wancan lokacin suke zuwa suyita wahalar banza ana kashe su a yaqe yaqe ba. Wannan dalili ya saka Audu shirin tafiya Kaduna kai Baballiya makaranta. Yace masa ya shirya kayansa kala hudu zuwa biyar a jaka ya kuma hada takaddunsa, Bara'atu ta ringa musu dariya tana cewa "Dukda dai bamyi karatu ba amma nasan ba haka taka ake kai mutum makaranta ba dole se anbi matakai ka nemi gurbi idan ka samu kafin ka tafi ko?" "To ai nima ba cewa nayi zan kaishi kaitsaye ba, zuwa zamuyi can muji yanda tsarin komai yake saboda ban gsu da bayanan Labahani ba besan takan komai ba kawai shirme yake gayamun gara muje kinga idan abin babu wahala kinga ba se anyi jeka ka dawo bazan baro shi can kawai" Audu ya bata amsa. A daren tana hada masa nasa kayan Babannan dake wasa ya zubo da wata jaka da Audu ya cukuikuye takaddar kammala sakandirensa ya jefa a ciki da takaddun gonakin da suka siya a Bechi, ta tattare ta mayar tana masa fadan ya fiya qiriniya, Babangida ne ya daga wani qaramin kati ta bata ankare dashi ta mayar ba ya fita dashi. Audu na qofar dakin inda ta baza musu tabarma saboda zafi suna Hira dasu Baballiya da murna tasa ya kasa bacci. Abdullahi Babangidan ya kaiwa katin hannunsa, ya haska da yar fitila yana karanta abinda aka rubuta a jiki kafinya miqawa Audu yana cewa "Baba ga abinka Baba ne ya dauko" Audu ya karbi katin ya haska shi tunaniya tafiyi na menene, duk sonya tuna kuma ya kasa, Kaduna daya gani a Address din dake jiki ya sakashi bawa Abdullahin yace ya miqawa Ummansu ta saka masa cikin jakar da ze tafi dashi, komana wanene yana da yaqinin zeyi masa amfani tunda zashi Kaduna. * MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na *GHT wato good health treatments *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri * *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* *Seda suka hau mota har sun wuce Zariya kafin katin ya fado masa take kuma ya tuna inda ya samo shi, wannan Alhajin daya taba taimaka ya basu Mai shekaru kusan uku kenan nasa ne. Farin ciki ya kamashi, a ransa ya ringa Addu'a Allah yasa yana raye kuma yana Kadunan idan sunje ze neme shi su sada zumunchi. Ikon Allah kenan, qila rabon su sake haduwa yasa Babangida binciko katin dan ko da kudi bazece ga a inda ya ajiyeshi ba, zaton sa ma ya fadi tun a ranar. Haka suka sauka Kaduna, Baballiya nata dan banzan raki wai tafiyar Nisa ya gaji Audu ya balbaleshi da masifa yana cewa a haka zeje aikin sojan qato dashi amma se ragonci kamar Mace. Ganin yana nema yayi masa kuka ya sakashi neman gurin me abinci a cikin tasha ya siya masa, suna zaune yana tunanin ta ina zasu fara, gashi la'asar harta kawo kai dan motar da suka hawo se a hankali kamar sun hau Jaki. Wani akwatun waya ya hango wanda ake biya ayi kira ya miqe yana laluba Aljihunsa inda ya saka katin Alhaji Zakariyya ya tafi gurin. Ya bada lambar aka kira masa, kiran farko ba'a daga ba seda akayi na biyu muryar mace cikin harshen turanci ta ratsa kunnensa. Gyara nasa harshen yayi suka gaisa kafin ya shiga tambayar mamallakin lambar wanda a katin yaga an rubuta Zakariyya, "wa za'a ce masa?" Ta tambayeshi yace mata "Kice masa Audu Bechi ne" Audu ya fada duda yasan babu tabbacin Alhajin ya gane tunda ba gaya masa sunansa yayi a wancan lokacin ba idanma ya tuna ya taba haduwa da shi kenan. Matar tayi shiru kamar me tunani kafin tace ya riqe waya tana zuwa. A can bangaren sakatariyar Alhaji Zakariyya ce ta dauki wayar wadda take a cikin ainihin office dinsa, ta sani lamba ce da yake magana da mutane masu muhimmanci dan haka duk wanda ya kira tabbas yana da muhimmanci gurin Ogan nata. Kwankwa qofa tayi, Alhaji Zakariyya ya bata damar shiga. A taqaice ta sanar masa da kiran daya shigo din, sunan Bechi data fada kawai ya sakashi zabura kamar wanda akace anga Dan uwansa daya bata. Fuskarsa a washe har haqoransa sun bayyana cikin son tabbatarwa yake tambayarta "Kikace BECHI" "Yes sir, haka yace sunansa Audu Bechi" ta bashi amsa. Alhaji Zakariyya ya daga kan wayar dake ajiye kan teburinsa wadda take a hade da ta teburin sakatariyar, Audu nacan saqale da waya a kunne cikin jiran tsammani yaji sallamar Alhajin kamar daga sama har wata Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga gaishe shi. "Har na fitar da rai da zaka kirani, kullum da tunaninka nake kwana nake tashi, na kasa manta Alkhairin dakayi mun" Alhajin ya fada cikin tsananin murna. Audu yayi murmushi yace "Haba dai Alhaji dan wannan abin ka kasa mantawa tsayin shekaru?" "Kai kake kallonsa a qanqanin abu, badan Allah ya kawo ka ka taimakemu ba a wannan rana bansan ya zamuyi ba. Ya bayan saduwa ya Kano? Kasan tun wannan ranar ban sake zuwa Kano ba amma duk idan naji wani zece sena bada sallahun a dubamun kai a wannan hanyar

Chapter 7 of 32