yanda Ubangiji ya wankeni itama ya wanketa ya bayyana gaskiyar duk wani mugun qulli da kukayi akanta" tana gama fadar haka ta gyara kwanciya ta jera yaranta a gabanta bayan ta bashi baya ta rufe ido zuciyarta na tafarfasa tsanar Audu me tsanani tana hudata.
Badan kar tayiwa Allah butulci ba da tace inama ya jinkirta bata wannan gwalalon kyauta a wani gidan inda yafi na Audu Alkhairi? Amma dukda haka ta godewa Allah ta sake gode masa bisa ni'imar da yayi mata.
Tamkar wanda lakarsa ta tsiyaye haka ya ringa jefa qafafu harya fice daga Asibitin, ya manta da Musbahu sukaje hakanan beyi tunanin mota ba ya ringa taka qafafunsa bude ido kawai yayi ya ganshi a qofar gidansa tundaga Asibitin Murtala, tafiya yayi wadda rabon da yayi irinta a qafa dai ze iya cewa tun Zamanin yana Audu qolo. Binta na zaune a tsakar gida da jama'arta da suka zo yi mata Sallama makwafta da kuma Turai da Mardiyya Wata sabuwar qawa da tayi babu dadewa.
Yanda Audun ya shigo ya saka duk matan binsa da kallo kamar ma be lura dasu ba haka ya tsallaka ta tsakaninsu ya wuce sama, Turai ta kalli Binta kafin tayi mata alama da ta bishi ta miqe tana murmushin yaqe ta sallami maqwaftan ya rage Turai da Mardiyya kafin ta haye sama gurin Audu.
Yana zaune akan kujera yayi irin zaman nan na balance ya bude qafafu da hannayensa kana kallonsa kasan da akwai abinda yake damunsa. Cikin salo da kissa ta bude firji ta dakko ruwan sanyi ta matsa gabansa ta tsiyaya masa tana cewa
"Lafiya dai ka shigo kamar baka cikin hayyacinka?"
Seda ya kwalwale ruwan ya miqa mata kofin kafin ya yunqura ya gyara zamansa yana kallonta dakyau yace
"Zubaida ta haihu"
"An ganta kenan, a ina? To mema ya shafemu da ita ko haihuwar ta? Halan gurin farkan nata ta je ta haihu acan ko?" Ta yi maganar tana yatsina fuska. Miqewa yayi ya nufi daki yana tafiya a hankali yace
"Ta haifi tagwaye duka maza, kamanninsu daya dani"
"Me kake nufi?" Ta miqe a zabure qirjinta na dukan dubu dubu kunnenta na mata amsa kuwwar Tagwaye Maza da ya fada, se ya waiwaya ya kalleta yace
"Karmu fara wannan maganar ma. Kin cuceni kin rabani da matata, waima meye dalilinki na sheganta mun Yaya Binta? Me yasa kikayi haka?"
"Ni na sheganta maka yaya? A yaushe akayi haka? Tsakaninka da Allah ni da kai mun taba magana nace maka cikin Zubaida shegene? Hasashena nayi na fada kai kuma tunda kasan da walakin goro a miya ka tabbatar haka ne to kuma se kazo kace na cuce ka dana maka me? Da kake wannan babatun ma me kake nufi ka karbi cikin kenan ko Yaya?"
"Ciki daman nawane" ya bata amsa yana shigewa ciki dan in ya tsaya din be san me zece mata ba. Gaskiya ta fada magana tayi me harshen damo shi kuma ya hau ya zauna daram wato ta tabbata ya zama wawa kamar yanda Yakubu ya fada Bintan ta karanci rashin tunani irin nasa shiyasa tayi amfani da wannan ta cusa masa tunani a kwakwalwarsa harta kaishi ga yanke danyan hukunci yanzu gashi tun ba'aje ko ina ba ya dawo yana dana sani mara amfani dan yasan ya rasa Zubaida ba zata sake yarda ta komo gidansa a matsayin matar aurensa ba.
Daren ranar Binta ta wuce Saudiyya cikin tashin hankali bayan sun rakaya dasu Turai sunje Asibiti sun ganewa idanunsu Tagwayen da akace Zubaidan ta haifa. Kuka wiwi ta ringayi kamar wadda kanta ya kwance wai ya za'ayi tazo a bayanta ta haifi tagwaye kuma Maza kenan yanzu ta fita kasafi cikin dukiyar Audu kenan. A Saudiyyan haka tayi Ibadar rabin Addu'arta ta Allah ya sa tayita haifar Yan biyu Maza ne bayiwa kanta wata kwakwkwarar Addu'a ba balle Yayan da take roqon a bata haka aka sauke Hajji ta dawo kamar yanda Audun yayi tunani daga ita se Kayan data tafi dasu yar tsarabar data yiwo bata kai kota kashi goma cikin uban kudin data tafi dasu ba.
Bayan dawowarta ta tarar da an kwashe kayan Zubaida wannan ya dan rangwanta mata damuqar data saka kanta a ciki. Daman daga Asibiti Zubaidan gidansu ta wuce kamar yanda Mahaifinta ya buqata Yakubu yayi iyakar roqon da ze iya amma Malam Hassan yace yayi haquri kawai. Ran Yakubun ya sake baci matuqa ya dauka Audun zeyi Nadama ya kuma nemi su sasanta ta koma dakinta amma seyaga akasin haka. Ya dai siyawa Jarirai kayan na Alfarma haka itama Maijegon ya hada da ita da Manya manyan Ragunan suna dana Qauri ranar kwana biyar da Yan Bechi suka zo wanda suma Yakubu ne yaje ya sanar dasu suka kai kayan Barkar.
Da aka kwana biyu har ya koma Ikko ya sake dawowa wata daya bayan haihuwar kenan ya sake tarar Audu da zancen ya suke ciki sun daidaita zata dawo idan ta yada wanka ko kuwa kai tsaye babu boye boye yace masa
"A gaskiya ni bazan iya zuwa nayi bikon wata mace ba, zan bata lokaci harta huce daga fushin da takeyi, idan ta nuna buqatar cigaba da zama a gidana se mu daidaita".
Yakubu ya rasa abin fada ya ringa kallon Audu kawai yana jin kamar ya rufeshi da duka. Ya dade yana ganin marasa hankalin mutane amma Audu leader ne, cikin tsantsar takaici yace
"Abinda ya hanaka ka maido da Bara'atu kenan tunda bata furta da bakinta tana so ta dawo ba ko?"
"Ka gane ashe, ai Allah ya kallo duk wani abu daya kamata ace nayi da ze nunawa Bara'atu ta dawo dakinta nayi. Kana kallo dawainiyar gidansu kaf har abinda be zama dole na ba yi musu nakeyi, duk wata se nayi mata aiken kudi da kayan abinci kuma idan naje Bechi ina zuwa naga Yaran to me kuma ya rage da zanyi ya nuna mata Biko nakeyi? Sena zubarda girmana na roqeta ta dawo bayan Alfarma zanyi mata naci gaba da zama da ita bayan laifin data aikata mun?
Itama Zubaidan ai koda ina da laifi nata yafi yawa a ciki, me yasa bata tsaya tayi mun bayani yanda zan fahimce ta ba amaimakon haka seta ringayin abubuwan da zasu qara tabbatar mun da zargina akanta ni kuma shine ya tunzurani na yanke hukunci. Kuma ai ita har haquri na bata da naje Asibiti tace babu ita babu ni kuma ta hanani taba Yayana shine kake so naje gidansu nace ta dawo salon ta samu damar rainani ko to ni bazan iya wannan aikin zubarda mutunchin ba" Audun ya fada cikin dagawa.
Mamaki, takaici hade da baqin ciki sukayiwa Yakubu rubdugu lokaci daya amma ya rasa kalmar da zeyi amfani da ita gurin zagin Audun dan haka ya kada kai kawai ya wuce ya barshi yana jinsa yana masa magana akan ya tsaya mana ina zashi be ko waiwaya ba. Duniya dai akace tafi bagaruwa iya jima, tabbas yana jiyewa dan uwansa randa muguwar Ta'adarsa zata bibiyi rayuwarsa.
Page 24
Rayuwa ta miqa, kwanan Binta Talatin da bakwai da dawowa daga Aikin Hajji ta haihu ta sake samun Da Namiji da yaci suna Naziru, yafi babu wai Agwai da baqin Da yanayin da ta nuna kenan domin ta gama sakankancewa da Addu'ar data ringa zagaye Ka'aba tanayi akan Allah ya bata yan Biyu Maza ta karbu to dayan ma babu laifi tunda yanzu sunyi kai daya su ukun gaba daya kowacce tana da Yaya Maza Biyu kenan, amma ba ta sare ba za kuma taci gaba da addu'a Allah badi war haka tayi yan uku ma ba biyu ba kuma duka Mazaje dan babu yanda za'ayi wata mace ya fita kaso a cikin Dukiyar da ubantane silar samunta.
Ko kaza bata zo mata barka ba daga Bechi balle suna haka sukayi bidirinsu da ita da yan uwanta se qawaye da makwafta shi kansa Audun tun bayan abubuwan da suka faru zamansu ya canza salo dan gaba daya ya daura mata laifin itace silar Rabashi da Zubaida ita kuma ta nuna sam ba haka bane ba. Da fari bayan dawowarta ta biyeshi zaman ya zama babu dadi sedai bayan da suka tattauna da Turai da kuma sabuwar mashawarciyar da suka samu wato Basira se abubuwa suka canza daga bangarenta.
Basirar ta qara tunasar da ita cewar muddin fa tana son biyan buqata seta kwantar da kai. Tilas ta maida kanta banza a gurin Audun, tunda har ta fahimci shi mutum ne me matuqar son girma da son a nuna ya isa to tayi amfani da wannan damar gurin kaishi matsayin da Allah be kaishi ba. Ta ringa nuna masa nan duniya babu yashi, duk kuma abinda ze fada karta kuskura ta musa masa ta barshi akan komai yayi daidai ne baya kuskure.
"Hajiya sufa Maza kamar qananan yara suke wlh, fahimtarsu kawai zakiyi me suke so menene basa so shikenan ku zauna lafiya. Kuma a yanzu abinda ya kamata ki mayar da kai gurin yi shine ta yanda zaki kafa kanki da Yayanki a gurinsa yanda zakiyiwa duk wata mace da zata shigo rayuwarku Zarra" Basirar ta fada taba durqusar da kai irin na shahararrun munafukai. Binta ta hura hanci tace
"Ai ba se kin fada ba, haihuwa dai an haifesu amma naci alwashin muddin ina raye yaya nane zasu zama kan gaba a komai na dukiyar Audu, baze tuna yana da wasu yaya ba bayan nawa, duk wanda yaci Arziqin Audu to ni naso"
"Ina yinki qawata fada da cikawa wannan aikinki ne" Turai ta fada tana bata hannu suka tafa. Haka suka yita qulle qulle da shiri na yanda za'ayi yanzu da nan gaba. A haka har lokacin haihuwar tata yazo bayan anyi suna da kwanaki Turai taje ta sameta da zancen rashin zuwan yan Bechi.
"Ni se nake gani ko dai babu dadi yaci ace kina sabga dasu, saboda dangin Miji ba qananan Munafukai bane, kinga idan suka kafawa mutum qahon zuqa Allah ne kadai ze kubutar dasu. Kina kallo dai yanda nake zaune da nawa duk sharrin mutum be isa yace na masa mugun abu a fili ba kuma na sani sun sani basa qaunata nima bana qaunarsu amma tunda ban bada qofar da zasu wulaqantani ba kinga qalau muke zaune dan haka kema dole ki gyarota dasu, ki jasu a jiki musamman ma naki da suke Fuqara'u Ahalin tsiya. Kamar kajine kina watsa musu tsaba na tabbata zasu biki ko wannan ma ze qara miki fada idan kika kame yan uwansa kinga koda ace kin samu tangarda dashi ba fata ba yan uwansa zasu zame miki makamin da zaki gyara komai" cewar Turai.
Binta ta numfasa tace
"Turai baki san yan uwan Audu ba musamman yan dakinsu. Yanda yake da wannan kafaffiyar zuciyarfa iwa ta mutanen farko haka suke. Bana tsammatar kudi ze saka su soni kina kallo ko shi din da yake musu shine jigon komai nasu akan Wannan shegiyar Bara'atun duk suka masa tawaye, yanzu an kuma na biyu sun nuna sunfi qaunar Karuwa akaina shiyasa duk suka qi zuwar mun Barka amma ai na samu labarin su sukazo suka kaikayan suna suna gidansu Zubaidan.
Tsinanniyar Bilkin nan tun ranar sunan Dady na farko bata qara tako qafarta gidan nan ba gara Aishar tazo jinya kwanaki can Mazan kuwa tunda suka zo fadar Baqin labarin Auran Karuwa basu dawo ba hatta Baballiya tunda aka Auro ni sau daya ya tako qafarsa gidan nan sedai fa idan naje can Kaduna na ganshi ya samu guri ya baje kamar gidan ubansa yanzu nan Yakubu ne kadai yake zuwa idan cin mutuncibsa ya tashi kuma daman duk ciki Audun ma shi yake shakka shi kadai ne yake tsayawa ya gaya masa magana son ransa kuma ya shanye baze iya mayar masa ba a yanda ya tsaneni kuwa ko duniya da abin cikinta zan bashi baze qaunaceni ba haka Annamimiyar matarsa ni ko kamanninta bazan iya tunawa bama yanzu. Kai na tsani Yakubun nan iyajar raina wlh" ta qarasa tana cizon yatsa tsanar da tace tanawa Yakubu ta nuna qarara akan fuskarta.
"Dukda haka dai ance se an tsaga ake ganin jini, daurewa zakiyi ki cusa kanki cikinsu ko basa qaunarki ta hakane fa zaki ringa sanin wasu abubuwa da suka shafi shi kansa Audun, hatta da dukiyar tasa kince duk abinda ya samu acan yake narkata, filaye gonaki duk ya tattara acan to idan kika qwafe a nan kin bar musu komai can ta yaya zaki san me kuke dashi? Irin hakane kina zaune kina lissafin dokin Rano se anzo ranar kasafi kiji abinda ba haka ba ita Bara'atun da take cikinsu tsaya mata zasuyi taja rabo me tsoka ga wannan itama tunda sun nuna tafi musu ke duk mara musu baya zasuyi a barki da lissafi. Amma idan kika shige su ta yanda ba za'a layance miki komai ba kin sani shima kuma ki matseshi ta yanda duk abinda yayi ko zeyi seya gaya miki"
"Yana ma gayamun in dai ya siyi abu ze fada mun tunda wannan matsiyaciyar ta fita ne dai kinga yanda abubuwan suka koma"
"Se haquri ki kuma cigaba da lallabawa daman ai ba kullum ake kwana a gado ba dole wata rana a samu yanda ake so wata rana kuma aka sin haka sannan ba yanzu muke dubawa ba gaba zamu gina lokacin Jin dadib ai be ma zoba tukunna qawata kedai Allah yayi mana tsahon rai musha shagali" Inji Turai. Binta ta murmusa tace
"Ai ni dole ma nayi tsahon rai dan munyi Gadonsa"
"Ke karkiyiwa Allah gatsali wlh yanzun kijiki a rami" Turai ta fada tana zare ido, Binta ta rufe baki tace
"Uffararan Allah na tuba ba haka zance ba, dangin mu dai sunyi Gadon tsahon rai kinga nima zanyi" ta sake sakin wani shirmen Turai ta miqe tana cewa
"Bari kiga nayi nan iskancina be kai shiga hurumin Allah ba, to mutuwa dai ba ruwanta da gadon tsayin rai ko gajartarsa in lokaci yayi dole a tafi" da haka hirar ta watse saboda Binta tace kan me kuma ana hirar arziqi zata sako musu zacen mutuwa.
Bayan ta yada wanka ta cewa Audu zataje Bechi ta kwana biyu, wannan yasa ya sassauto daga daure dauren fuskar da yake fama dashi tun rabuwarsa da Zubaida. Ya shirya mata tafiyar Ado sabon Direban daya dauka yake jigila dashi ne ya kaita Bechin niqi niqi da kayan tsarabar data loda dan Hajji Kam taje tayo tsince tsincen su Zam Zam, Dabino Bagaruwa su kallo kallo na yara da sauran tarkacen tsaraba ta tafi.
Kadaran kadahan suka karbeta musamman da basu san da zuwanta ba dan haka babu wani tanadi da akayi mata ta bude dakinta ta shiga a ranta tana tsine musu babu wanda ya bita ko suce zasu tayata kimtsa guri sun dai karbi Naziru yana can hannun Sauda Amaryar Aminu. Ta gama kakkabe dakin ta kimtsa abinda zata kimtsa kafin ta bude jakar tsaraba ta shiga kasawa gida gida.
Yara ne sukayita shelar zuwanta garin, Aisha ta biya gidan Bilki akan tazo suje yiwa matar Yayan nasu Barka da zuwa amma tace babu inda zataje. Haka ta tafi ita kadai ta tarar da Yaya Mairo da Yaya Amina da matan Yayyensu duk sunzo Goggo Fadi ta aika an gayo musu. Kamar yanda Turai ta fada kuwa duk wadda ta shigo fuska a murtuke dan ba a son ransu suka zo din ba dan dai bazasu tsallake kiran Sirikarsu bane amma data miqa musu qullin tsaraba se kaga sun hau washe baki suna godiya daga nan se a shantake a fara hira kuma wannan tasa Aisha ta tarar da dakin cike da Mata suka gaisa ta karbi yaron da daman shine maqasudin zuwanta bawai ganin Bintan ba tana tambayarta Yayansa tace mata Yana Kaduna tunda suka zo suna suka tafi dashi. Bata jima ba tayi musu sallama tace se gobe zata dawo.
Bayan Isha Jamila Uwargidan Hashimu ta sake dawowa da Langa tuwo da miya data sakowa Binta abincin dare. Tana daki bayan ta lallaba Naziru yayi bacci, qullin uban Nama ne a gabanta da damammiyar fura take ci Baballiya ne ya kawo mata bada jimawa ba tayi mamakin ganinsa a Bechi wato ya zo Kano amma koya leqa can gidansu da tayi masa tsiya yace mata ai yaje Kanon amma a Kamfani suka hadu da Yaya Audu dake ba jimawa zeyi ba anyi posting nasa can qasar Kudu yazo yiwa yan gida sallama ne shiyasa be shiga can gidan sun gaisa ba ya ajiye mata saqon ya wuce ta bishi da kallo tana mamakin girman da yayi, idan ba'ayi wasa ba zefi Audu tsaho da qirar qarfi yanzun.
"Sangangan kenan sudai sunyo gadon girmaz wai yanzu haka nawa Yayan zasu tashi kenan kamar dakarun yaqi? Allah yasa dai su kwaso hankalin wancan me baqar zuciyar Wan uban nasu dan ta nan ya banbanta da sauran" ita kadai take sambatu tana danna lomar Nama abinta Jamilan tayi sallama. Tsaki taja qasa qasa kafin ta amsa, babu damar ta boye abinda take ci dan ta rigada ta shigo dan haka ta hade fuska dan ba zata sammata ba.
"Aa, Hajiya irin wannan rabasha haka kice gashin Haladu aka kawo miki" Jamila ta fada tana kallon ledar kamar ta dumbula hannu yawunta ya tsinke dan qamshin naman ua cika dakin duka. Yaqe kawai Binta tayi ba tareda tace komai ba a ranta tana mamakin meya maido matar nan kuma? Yan cikin gidan ma sun barta ta huta kuma se ita zata kwaso jiki tazo ta isheta a daren nan daga zangar ta dan basu fuska dazu.
"Daman Tuwo na kawo miki, yo ahe ke tuni kin makari da babban yanka" Ta sake fada tana bude Langar tuwo da miyar data jere a qasa. Warin daddawa da kuka suka daki Binta a ranta ta danna Ashar tace
"Ni zanci wannan baqin tuwon da miya kamar yawun Kaza?"
"Zabuwa Babansu yace a yanka a zuba miki a miyar" Jamilar ta sake fada tana karkato mata da kwanon miyar dan taga Namomin da suke ciki wanda qarya takeyi ba Hashimu ne ya bada ba satar mata Zabo tayi tasa aka yanka tasan kuma da zarar labari ya isa kunnensa gobe akwai bala'i dan da tace masa Bintan tazo ma seda ya kora mata ashar yace ina ruwansa da wata Binta.
"Allah sarki aiko nagode, bari na ajiye da safe se a dumamamun nayi kari dashi"
"Aiko daman yafi dadin ci dumamen" Jamila ta sake fada tana gyara zama. Hira ta shiga sokowa Binta kamo nan kamo can, da taga bata da niyyar tashi dole ta bude naman ta mata bismilla aiko ta dirar masa seka rantse bata ci a gida bayan iyakar qoqari Mazajensu sunayi da wuya ayi miya lami a gida. Seda suka tada naman tas wanda Jamila ce ta cinye Rabi Binta ta janye Furarta gefe dan wannan kam ba zata bata ba.
"Uhm bari na tashi dare ya fara nisawa, nace da safe in Allah ya kaimu nazo na rakaki ki gano gidan ummarsu Babangida ko?" Jamila ta fada yana miqewa tsaye da shirin tafiya.
"Wace Ummarsu Babangida kuma?" Ta tambayeta cikin rashin fahimtar wa take nufi.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
"Au, Bara'atu zance miki ko zaki fi ganewa. Juma'a idan tazo mako uku kenan da tarewarsu, kinga gida badai gida ba tamkar naku ba Birni, ai gaskiya Alhaji Audu yayi karamci ya kuma kyauta saboda dangin uban nan nata tasamma ci musu mutunchi sukayi wlh, kinsan basa son uwarta ta fa daman akace. To yana mutuwa suka tada bala'i wai gidan da yake ciki gadonsu ne su goma ya hana a raba ya ke zaune ciki dan haka se su fitar musu a gida a raba sannan su san kasonsu, kinga dan taqin da akace sun cire musu a matsayin rabon baban nasu? Ai badan Alhaji Audu ba a garin nan bamu san Ina Inna Hajara da yayanta zasu tsoma ransu ba shine fa ana gaya masa ya aiko aka far....."
"Ya isa haka dan Allah, kije Allah ya kaimu goben se kizo ki rakani" Binta ta dakatar da Jamila daga zubar da takeyi tamkar famfon daya lalace. Jamilar ta fice bayan ta mata sallama tana dariya kamar wata wawiya tana fita Binta ta mayar da qofa ta rufe, wani kalar tashin hankali ke rufzo mata dukda yanayin garin babu zafi amma ita zufa ce take keto mata ta kafofin gashin jikinta. Ta ri ga safa da marwa a dakin tana huce ita kadai tama rasa ta ina zata fara tunani, Audu ya ginawa Bara'atu gida yaushe akayi haka bata sani ba kuma akan me?
To kodai sun maida Auransu ne bata sani ba tana can gaho? Ta jefawa kanta tambayar seta zabura a fili tace
"Kut**uba kenan ma ai kuwa da anyi yaqi duniya ni za'a yaudara a ninke baibai?"
Kukan da Naziru ya sakane ya ankarar da ita hayagagar da takeyi ta daukeshi taci gaba da zaga dakin tana jijjigashi, wato mutanen nan anyi qungurumayen munafukai, ashe da Jamila bata gaya mata ba haka zata gama zamanta ta tafi ba tareda ta samu wannan mugun labarin ba aikuwa zasuga tatura, seta nuna musu ta fisu iya tashanci wato uta zasu hadewa kai?
Tabbas Turai tayi gaskita da tace tana can Bihim zasu rabe komai a barta da zare ido gashi kuwa an fara.
Daren ranar bacci barawo ne ya saceta dakyar aiko tayishi da mafarkin wai Audu ya mutu an kwashe komai an bawa Yayan Bara'atu da Zubaida ita bata samu ba. Da safe kuwa dakyar ta iya zama jiran Jamila da ace tasan gidanta ma da ba zata iya zaman jira ba gara taje su wuce daga can. Wadanda suka dawo washegari son zuciya ganin yanayinta yasa suka watse dan a dare dayan ciwon qyashi da Hassadar data dorawa kanta ya zabgeta kai ka dauka kwana tayi tana gudawa.
Jamila bata zoba se bayan La'asar dalili kuwa Hashimu na gida ranar bayan ya gama Tijarata akan Zabonsa data dauka tayiwa Binta Miyar da ko dandanata batayi ba da safe da Sauda ta kai mata kayan Karin Kumallo tace ta dauke tuwon a bawa Yara. Seda ya fita kafin ta samu ta kammala duk abinda zatayi gudun kar sukai Magriba kafin ta fito. Tinqis tinqis se gasu a sabon gidansu Bara'atu Jamila nata zuba mata dan banzan Surutu ita ko Ruhinta da gangar jikinta suna ga su isa taga gidan da Audu ya ginawa Bara'atu.
Tun daga qofar gidan yanda aka lailayeta da fulasta tasha fenti yanayin tsari da taswirar ginin kai ba zakace a cikin Bechi yake ba. Wani abu me daci da maiqo ya taso mata har seda ta dafe qirji tana kallon qofar gidan dake garqame da kwado alamar basa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 32