tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*
BARA'ATU
Gaba daya komai daya faru ya ringa mata tamkar fim, sanda ta samu labarin an mayar da auranta da Audu daga zuwa kai sadaki rasa tantance me zatayi tayi se kawai ta shiga daki ta kulle ta kwanta kan Katifa tayi shiru ta bar Inna Hajara da yan uwanta dake ta murna a tsakar gida.
Ita kadai take hangowa kanta makomar rayuwarta, su murna sukeyi amma ita tasan meta baro a gidan Audu wanda bata fatan ta koma ta tarar. Sannan abinda yake qara sanyaya mata jiki yanda har kawo lokacin bata saka Audu a ido ba dukda ta samu labarin yazo yana garin ta dauka kafin faruwar komai zeje su zanta yaji ra'ayinta taji nashi amma se kawai ta tsinci anmaida mata aure babu jin ta bakinta babu komai abinda ko sanda tana budurwa ba'ayi mata ba anya kuwa Audu ne yake son komen nan ko kuwa yan uwansa ne suka tursasashi maida ita? Tayiwa kanta tambayar.
Da yammacin ranar Kawunta ya kai musi kudin sadaki hade danashirue shirye da Audun yace a bata tayi, wannanya qara kassara mata jiki harta kasa daurewa ta fashe da kuka domin ta tabbatar da cewar ba ra'ayinsa bane na mayar da ita dole wani ne ya sakashi idan kuwa hakane ta tabbatar seta gwammace kida da Karatu gashi bakin Alqalami ya bushe ballantana tace a koma baya.
A sanyaye take komai ga sati biyun da aka saka na kwanakin tariyarta suna qaratowa har sannan kuma bata saka Audu a ido ba, da tayi maganar wa Yan uwanta Hadiza ce kadai ta fahimceta dan Inna Hajara fada take mata akan waita fiya saka damuwa a rai ai babu yanda za'ayi ace dole aka wa Audu ya mayar da ita tunda shi ba yaro bane ba rashin zuwan sa kuma bata san uzurinsa ba kuma dai duk tsiya gidansa za'a kaita idan taje can koma menene zasu tantance. A wannan gabar ita da kanta seda ta ga baiken Innar tata ta kuma fara yarda da abinda ake fadi a gari na cewar kwadayi ne yake Dawainiya da Innar tata.
Idanba kwadayin abin duniya ba kowacce uwa tana qoqarin siyawa yar tamutunci a gurin Miji amma ita wannan be dameta ba fatanta kawai ta koma gidansa duk irin rayuwar da zatayi bata sani ba. Cikin wannan zullumi da Taraddadi ta shiryi dawowa gidan Audu karo na biyu a matsayin matarsa. Tsirarun mutane suka rakota ciki harda yan gidansu Audun basu jima ba kuma saboda motar data kawosu yana tsaye ga kuma wadda zata maida su Bilki dan haka suka rankaya suka koma ana ta tsegumin Ina Binta ta tafi basu ganta ba.
Bayan sun tafi gidan ya mata shiru dan ita kadai ta taho yaran ance se ta kwana biyu a kawo su a cewar Hadiza tasha Amarci a tado da tsohuwar zuma tukunna, dariya ma maganar ta bata dan bata hango wannan Amarcin da suke fada muddin Binta na cikin gidan nan. Ta fita tsakar gidan ta tsaya tana qarewa ko Ina kallo, gidan na nan yanda ta barshi se yan canje canje na kwalliya da fenti da aka sakeyi masa yanda ko ina yake shiru cikin Aminci a ranta tayi fatan ina ma gurin ya dawwama a haka? Ina ma rayuwarsu ta baya sanda suke zaune a daki ciki daya a Bechi ta dawo?
Har akayi sallar Magriba babu Binta babu Audu, bayan tayi sallah ta gyara kwalliyarta, babu laifi ta qara jiki akan shekarun baya da take gidan dukda ba qiba tayi ta azo a gani ba amma ta murje, yanayin ta dai na Shiru shiru da sanyin jiki yana nan wanda halittace canzashi da kamar wuya, a bangaren wayo ko ace wayewar kai ma babu wani cigaban Azo a gani data samu domin shekaru kusan hudun a Bechi tayi su ta sake komawa duhun kan data baro, mutanen da taci gaba da mu'amala dasu sune dai wanda ta sani tun yarintarta babu wani sabon Ilimi ko wayo data qaro ita ba Makarantar Boko ta shiga ba balle Islamiyya kullum tana zaune a gida kwalliya kanta ba yi takeyi ba Hadiza ce tayi qoqarin ganin ta saitata tayi gyara ciki da waje a dan taqin kwanakin da aka saka na tariyar tata, ita da yake yanzu a cikin Kumbotso take aure babu laifi kanta ya waye fiye da Bara'atun dukda daman tun Asali ba zubinsu daya ba dan da ace Hadiza ce ta samu damarda Bara'atu ta samu ta auran Audu tabbas ba Binta ba kowacce Macece zata iya karawa da ita.
Seda aka fara kiraye kirayen sallar Isha'i taji motsin an shigo gidan, ta taga taga wucewar Bintan,gabanta ya yanke ya fadi har seda ta dafe ta shiga karanto Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, fargaba da razanin da ta ke shiga duk sanda ta ganta a baya irinsa takeji a yanzu ta rigada ta tsorata da Bintan Allahya sani. Tana cikin wannan halin aka sake shigowa wannan karon Audu ne shida Musbahu. Faduwar gabanta ta ninku tana jiyoshi suna magana dan bata iya leqawa ma ta ganshi ba harya sallami Musbahun taji alamun tafiyarsa yayi can gurin Binta kafin ta iya sauke numfashi.
Tana cikin sallar isha ya shiga dakin, ganin tana sallar yasa ya fita bayan ya fada mata sallahun ta sameshi a falon Bi ta idan ta idar haka ta ringa taraddadin taje ko kar taje bayandata idar da dallar daga qarshe dole ta miqe, babu wani sauran magana ta rigada ta dawo cikin gidan nan abu biyu ne kodai ta tashi ta kwatarwa kanta yanci ko kuma rayuwarta ta qare cikin tsoro da firgicin Miji da kishiya.
Tana tafe sallaf salaf a ranta tana kewar Balaraba, qila basu san ma an mayar da Auran nasu ba tasan da tana nan data qara mata qarfin guiwa dan duk sanda sukaje Bechi idan taje gurinta maganar kenan take mata ta tashi ta kwatarwa kanta yanci wannan sanyin Jikin babu inda ze kaita.
Da sallama ta shiga falon kanta a qasa bata zauna ba har seda ya bata umarni ta dan dofana kan kujerar data fi kusa da ita.
Maganganu yayi musu dan ba za'ace Nasiha ba wanda kusan duka jan kunne ne ga ita Bara'atun akan abubuwan da suka faru a baya da baya so a sake maimaita irinsu ya kuma tabbatar mata da cewar Binta da kanta ta nemi daya maido da ita har yana fada mata a wannan karon itace qasa da Binta dan haka ta bata girmanta na kasancewarta Gaba da ita a aure da kuma shekaru.
Yanda ya ringa maganar gaba daya se taji ta muzanta ta kuma gasgata tunaninta na cewarba ra'ayin kansa bane wani ne ya sakashi ya maido da ita amma me yasa duk cikin mutanen se Binta? Meta shirya? Wace kitimurmurar take so ta sake hada mata data nemi a maido da ita iyakar Taskun data sakata a baya be isheta ba kenan?
Ya gama maganarsa ya basu damar me magana tayi, Binta da kanta ya gama fasuwa da yanda ya nunawa Bara'atun ita ba komai bace yanzu a gurinsa, taji ina ma haka ta kwantar da kai lokacin daya auro Zubaida tabbas da martaba da qimarta a gurinsa ta zarce ta yanzu amma hakan ma babu laifi zatayi duk iyawarta ta sake kafa kanta.
"Nidai babu wani abu daga gurina, Bara'atu daman tun asali yar uwa na dauketa ba kishiya ba ina fatan kuma itama wannan karon zata saki ranta ta zauna dani zuciya daya, sannan kafin a kai ga maganar rabon kwanaki akankwana uku da zakayi mata na qara muku sati kunga kwana Goma kenan saboda kuji dadin Amarci sosai a tuna baya" Bintan ta fada cikin kissa. Wata dariyar Bosawa Audun yayi, Ita dai Bara'atu kanta yana qasa, to me zata ce musu kuma? Tana jinsu suna ta soki burutsunsu shida matarsa kafin aka rufe taro yace taje yana zuwa.
Bata tsammaci zuwansa da wuri ba se gashi ko minti goma bata rufa da komawa ba ya shiga da ledar kayan Marmari da kaza.
Washe gari haka ta tashi mamaki na neman kasheta, wato Namiji ko, Namiji duk wadda taci laya akansa ta shigenge.
Irin yanda Audun ya ringa mata rawar jiki yana fada mata kalamai jinsa kawai ta ringayi, haka da safe be fita ba, Binta da ta kusa hadiye zuciya cikin dare ta mutu saboda baqinciki da kishi amma tun farar Asuba ta tashi ta hau aikin da babu lada domin ba dan Allah tayi shi ba. Lafiyayyen abin kari tayi musu ta kai qofar dakin Bara'atun ta kwankwasa kafin ta ajiye dan ba zata iya shiga ba zata iya manta shiri takeyi ta bazara komai gayyar ta watse. Haka ta ringa musu wannan kabakin arziqi harna kwana uku kafin ta kasa cigaba, yanda Audun ke rawar jiki akan Bara'atun ya tassama haukatata.
Ita dashi yake ce mata daya san ze samu wannan kwanciyar hankalin da nutsuwa a gidansa da Bara'atu ya maido a maimakon ya Auri Zubaida har yana tambayarta me yasa bata kishi da Bara'atu amma lokacin Zubaida taqi kwantar da hankalinta?
Ta rasa amsar da zata bashi, ba abin ta daddana masa Ashar ba se kawai tace saboda ita Bara'atu a gidan ta tararda kuma Zubaida ba wai kishi da ita takeyi ba kawai Asalinta ne be mata ba da ace itama a gaban Iyayenta ya aurota tamkar Bara'atun da lafiya lau zasu zauna.
Ango Audu dai ya ci karensa babu babbaka ya murji soyayya yanda ya kamata shi da kansa ya tabbatar da akwai banbanci tsakanin Abinda zuciyarka ce take sonsa da kuma wanda wani dalili yasa kake tare dashi. Bazeyi qarya ba yana son Bara'atu, haka Zubaida da kansa ya ganta yaji yana sonta har kuma yanzun da da dama ze maidata itama suci gaba da zama yanda yake jin su biyun a zuciyarsa Binta bata kama qafarsu ba amma kuma ya rasa yanda akayi ta fisu tasiri a ransa, yafi girmamawa da daukar maganarta fiye da tasu menene dalilin hakan?
Seda ya kwana uku cif yana hutun Angwanci kafinya koma fita aiki a ranar kuma Binta ta sauke hau din data dorawa kanta ta yi mush girki ta bar Mairo taci gaba. Baqin cikin data qunsa a kwanakin Allah yayi yawa dashi tana nan kuma tana jiran ranar ramuwa kwanaki goman nan cif su ta bawa Bara'atun matsayin kwanakin farin cikinta a gidan daga nan kuma wasan ze canza salo.
Kamar yanda ta qudurta kuwa haka ce ta kasance kwana goma Audu yayi a dakin Bara'atu wadda zata iya cewa kwanaki goman nan sun zarce shekaru goma na rayuwarta dadi dominbata taba sanin dadin Aure ba a zaman da tayi da Audu kamar na wannan kwanakin. Ya shayar da ita madarar qauna tarairaya da soyayya ba'a magana gaba daya ya goge mata hadda ya kuma goge duk wani shakku da take dashi akansa na cewar ya dena sonta ko yana da wata manufa akan maidota da yayi, walwalarta ta qaru har wani kyau da sheqi ta qara kana ganinta kasan hankalinta a kwance yake Yanda kuma Bintan take sabgogin gabanta bata shige mata irin na wancan karon yasa ta fara tunanin da gaske ta aje makaman yaqinta zasuyi zamane na babu ruwan kowa da kowa wanda zata so hakan.
Randa Audun ze bar dakinta zuwa na Binta har kuka ta masa ya ringa rarrashinta akan kwana biyu ne kacal ze dawo sannan a qarshen satin zasuje su dakko su Babangida ma su dawo gida a saka su a makaranta dan Zakariyya ma za'a dawo dashi duka za'a hadasu a kaisu makaranta me kyau wannan yasa ta dan rage damuwa. Lafiya lau yayi kwanaki biyunsa dakin Binta randa ya dawo matasuka tafi Legas wanda tafiyar tazo mata a bazata ce mata kawai yayi ta shirya zasuje wani guri ta dauki kaya kala biyu farko ma ta dauka Bechi zasuje seda ta ganta a filin jirgi ta shiga zare ido, yau gata zata hau jirgi itama bata sake tsinkewa ba seda suka sauka yace mata Legas sukazo ta ringa tsalle kamar yarinya kamar wasa se gasu a gidan su Yakubu.
Page 27
Da murna tayi musu yawa ita da Balaraban se kawai suka fasa kuka, Yakubu ko bakinsa ya kasa rufuwa, Audun ya shammaceshi dan besan duk abinda ya faru ba wannan abun da yayi kuma ya saka ya wanke duk fushin sa da yake damfare a ransa yaji matuqar dadin ganinsu ko ba'a fada ba kuma yasan hankalin kowannensu a kwance yake.
Aka ringa hirar yaushe gamo, A gidan sukayi kwanaki biyunsu dukda Audu yaso su kama Hotel tunda gidan qarami ne dakuna biyu ne daga nasu Yakubun se na yaransu amma Yakubu yace dole su zauna haka baquntar kwana biyu dai haka suka dawo Kano cike da kewa dan kwanaki biyun ba qaramin dadi yayi musu ba sun fita yawo har bakin ruwa sukaje aka musu hotuna Audu be taho ba seda aka wanke musu hotunan suka taho da kwafi dinsu.
A kwanaki biyu ba qaramin Ilimi Balarana ta zazzagawa Bara'atu ba da kuma wanda ta gani da idonta ta koyo, sun dawo ta qudiri niyyar tabuka abin kirki a wannan karon itama, zatayi amfani da duk dabarun data koya mata na riqe Miji, zatayi iyakar yinta yanda ba fata takeyi ba koda ace wani abu ya sake faruwa badai a zargeta da sakarci ko rashin sanin ciwon kai ne ya janyo mata ba.
Tafiyarsu Legas ta qara rura wutar bala'i a zuciyar Binta, dukda ya gaya mata kafin su tafi abin ya zafeta matuqa harta kasa jurewa ranar da suka dawo a dakinta ya sauka bata iya shanyewa bata amayar masa da abin da yake cikinta tas akaci sa'a be kulata ba domin shima ya qaro karatun zama da mata, ya san da akwai abubuwan da mace zatayi wanda Kishine yake tunzurasu babu yanda kuma zakayi da ita dole kayi haquri.
Watanni uku da dawowar Bara'atu, a hankali kyakykyawan zaman daya fara ginuwa tsakanin Ma'auratan ya fara samun tazgado, salon da Binta tayi amfani dashi a zamansu na farko da Bara'atu shita sake maidowa na cusguna mata ta hanyar bautar da ita da kuma zaginta tareda muzantata sedai a wannan karon ta canza salo ta kuma biyo ta hanyar da a qaramin wayo da Dabarar Bara'atu ba zata iya kaucewa Kaidinta ba.
Da farko ta dakatar da Lantana da Mairo daga zuwa aikinsu wanda tayiwa Audu qaryar Lantana sata takeyi mata shiyasa ta koreta ita kuma Mairo ta dakatar da ita ne kawai su ringayin girkinsu da kansu be kyautu ace abincin me aiki ze ringa ci ba bayan yana da mata har biyu sauran Ayyukan gidan ma duk bazasu gagaresu,
"Da ze yuwu mu zauna da Maman su Baba mu tsara yanda zamu ringa ayyukanmu kawai ba se wani ya taimaka mana ba. A gidan Yaya Aminu naga irin tsarin ya burgeni kuma hakan ya qara shaquwa da fahimta a tsakanin matansa kana gani duk gidanku babu Kishiyoyi masu fahimtar Juna kamar matansa haka yayansa kansu a hade baka ma iya banbance wannan na waye to nima irin zaman da nake so mu gina a gidan nan kenan duk abubuwan da suka faru a baya su zama tarihi mu tun kari gaban mu" abinda Bintan ta tsarawa Audu kenan cikin salo na zallar kissa da iya hada tuggu.
Audun yayi na'am da shawararta kuma yaji dadi, tabbas Matan Aminun abin kwatance ne yanda suke zaune tamkar Dadansu da Goggo Fadi kafin rasuwar Malam Tijjani, haka suka tashi gidansu aiki da komai tare su Dadan su keyi kwana a Turakar megida ne kadai ze nuna maka wadda take da Girki a cikinsu shiyasa shawarar tayi masa dadi yasan kuma Bara'atu ma zatayi Na'am da hakan itama.
Sanda ya sanarda Bara'atu hukuncin da Bintan ta yanke na sallamar su Lanatana batace komai ba saboda daman ba ita suke yiwa aiki ba, sharar tsakar gida kadai abinda take mora a aikin nasu tunda ba Girki daya sukeyi ba kamar dai farkon zamansu ne me Miji tayi abinci dashi har gara Mairon tana kama mata wasu abubuwan idan tana girki a Kitchen din tsakar gidan Lantana kuwa kallon Arziqi ma baya hadasu balle aje a ga batun tayata aiki shiyasa sallamar masu aikin bata dameta ba.
Anyi kwana biyu da maganar ya tarasu falonsa domin tsara yanda zasu raba aikin gidan, Binta ce da girki ranar tana ta kai kawon hada musu abinci su duka gaba daya harda yaran dan sun dawo Abdullahi ma anyi hutun makaranta yana komawa gida ya samu labarin Innarsa ta koma Kano kwanansa biyu shima ya hado kayansa ya taho Audu da Binta suka ringa masa tsiya.
Seda aka qare cin abincin suka sallami yaran suka sauka qasa kafin suka nutsu cikin kujera dan yin maganar data tarasu din.
"Dan Allah ya kukaji abincin yau? Har wani dadi ya qara na daban saboda mun hadu Ahali gaba daya munci tare, gaskiya haka zamu ringayi daga yanzu saboda ni daman a gidanmu mun saba tare muke cin abinci gaba daya kaima ai ka sani" ta yi maganar tana kallon Audu se shima ya murmusa ya mayar mata da cewa
"Kwarai kuwa, ina fatan kuma wannan hadin kan ya dore"
"Nikam daga gurina babu wata matsala ai kamar yanda na gaya maka komai daya faru a baya ya wuce itama ina fatan ya zama haka a gurinta dukda har yanzu dai naga ta kasa sakewa se ta ringa darare jikinta kana kallo fa tunda muka zauna yanzu bayan gaisuwa babu abinda ta qara cewa ta barmu muna ta zuba kamar lalatattun Radiyo" Bintan ta soko Bara'atu wadda kanta ke qasa tana kallon lallen da tayi kwanaki biyu da suka wuce sanda ta karbi girki maganar Bintan kuma bata saka ta dago kota amsata ba saboda ita har yanzun ranta yaqi Aminta da wannan takun na Binta ba kuma taso ta saki jiki da ita ta sake shammatarta irin na wancan karon.
"Nikam matsalata dake kenan Bara'atu kin fiya qauyanci kiyi abu wani salo salo kamar mara jini a jiki tsakanin nida Bintan waye baqonki da ba zaki sake a cikinmu kiyi sabgoginki ba?" Audu ya fada yana gyara zama.
Seta daga kai ta kalle shi, kalmansa sun mata zafi dan har kwalla ce ta tarun mata a ido, bata da dauriyar zuciyar da zata jure cin mutunchi ko tozarci yanzu zata karaya ta fara kuka banda tsabar wukaqanci ita ze kalla yacewa Baqauya to ya suke shida itan? ai babu me gorantawa wani Asali dan tushensu daya koda yake shi daman be iya maganaba.
"Haba kai kuwa ya daga magana kuma zaka fara ce mata yar qauye? Koda yake kunfi kusa ai, Qauyawa biyu, yan Qauyen Bechi" Bintan ta zage su duk su biyun a wasance garan kuwa se ya hau dariya yana cewa shi ba baqauye bane ai baqauye wanda bashida wayewa kenan shi kuwa da yake fes ko haihuwar Birnin ba zasu gwada masa wayewa ba ai ita kuwa Bara'atu abun ya sake qular da ita amma ta hadiye bata ce komai ba sedai ta quduri niyyar yi masa maganar muddin suka kebe, zata gaya masa bata so, karya sake wulaqantata a gaban Kishiya (as if zata iya).
"Yanzu dai muyi abinda ya taramu dare yanayi" Audun ya dakatar da wasan ganin Bintan na nema ta wuce gona da iri a wasan nata ta fara tabosu tana cewa wai kaf garinsu banda Yakubu waye yayi Karatun zamani dan shi kansa bata yarda yayi sakandiran ba
"Ke kuwa nasan dakyar ma idan kin taba shiga Aji" ta sake takalo Bara'atu wanna yasa ya dakatar da ita danshi basa shiri da raini.
Bintan ce dai tayi magana akan tsarin da take ganin zasuyi, Me girki ita zata dafa abinci wa gida gaba daya, zasu hade girkin kenan sabanin da da kowa takeyin nata sauran Ayyukan gida kuma shara da wanke wanke wadda bata da girki tayi harda sharar dakunan junansu sedai idan da wani uzuri ko lalura to dayar na iya daukewa dayar aikinta tsarin Binta kenan.
Maganar sharar dakunan Junan tayiwa Bara'atu banbarakwai dukda take Baqauyiya mara Ilimin amma tasan ko a karkarar da suka fito Kishiya bata sharewa kishiya daki sedai idan da lalura ina laifin iya tsakar gida? Tana jira taji Audun yace wani abu akai amma shiru sema jaddada hakan yayi da yace sannan ya juya kanta wai yana tambayarta ya mata ko tana da magana? Taga to me zata ce musu? Ta ce be mata ba su samun abun magana daga shi har matar tasa kenan se kawai tayi shiru suka gama abinda zasuyi ta musu sallama ta wuce se bayan data koma dakinta kuma abin yayi ta damunta, Balaraba ta gaya mata karta ringa barin magana a ranta muddin akan abinda ze cutar da itane, koda za'a ce bata kyauta ba gara ta fada a gyara akan ta bar abin a cikinta ta cuci kanta da kanta to amma tana gudun tayi magana kuma su canza mata ma'ana saboda muddin bada zuciya daya Binta tayi wannan abin ba to tarko ta hada mata so take tace wani abu ta ruftata ciki, haka ta kwana tana saqe saqen me zatayi?
Ta yarda da wannnan tsarin ko kuwa dai ta gwada sa'arta gurinnusar dashi rashin dacewar hakan? Bata son fitina ba kuma tason abinda ze sake janyo mata matsala da Binta ko Audu, a baya shiga dakinta na qasa da Minti biyar ya janyo har aka laqa mata sharrin kisan kai inaga yanzu taje shara?
A bangaren su Audu kuwa Bara'atun Binta ta gyara zama tana tsiyaya masa Zobo a kofi tace
"Se naga kamar Bara'atu bataji dadin maganar da akayi ba"
"Kinsan ta ai ita ba'a fiya gane ina ta dosa ba tunda kikaji bata ce komai ba hakan ya mata itama kenan" ya bata amsa bayan daya kurbi zobo. Ba haka taso ji ba dan haka ta sake kalailayewa tana cewa
"Uhm haka dai kace amma ni yanayin fuskarta na karanci kwata kwata maganar man bata zauna mata ba, idan lura kuma ai tunda kuka dawo daga Legas din nan tsumewarta tafi tada, kafin ku tafi ai tana dan sakin fuska idan mun zauna irin haka amma yanzu fa sedai tayita sunkuyar da kai tana irga yatsunta kodai har yanzu ta riqe abinda ya faru a baya ne a ranta?"
"To idan maganar abinda ya faru a baya ne ai ke ya kamata ki qullaceta ba ita ba tunda ke akayiwa laifi ko?" Cewar Audu, se tayi narai narai da fuska tace
"Nima dai hala na gani, nida aka cuta na dubi Allahmace na yafe amma kuma tazo tana so tayi zaman gaba dani idan fa ba a gabanka ba ko gaisawa bama yi bana so ina kawo maka maganarta ne kaga kamar wani abun nake so na hada shiyasa amma wlh sam duk yanda nake so na jata mu zauna lafiya taqi sakin jiki kayi mata magana in dai akan abinda ya faru take tunani dataqi sakewa dani wlh na yafe kuma na manta komai ta saki ranta mu zauna lafiya abinmu mu kama ka ram yanda ba zaka sake hango wata ba balle wannan karon ma ka sake kwaso mana Kara da kiyashi".
"Allah sarki Zubaida, aiko kin tunamun gobe idan Allah ya kaimu zanje na dubo su Hassan dukda dai nayi musu aike cikin satin nan amma gara naje na ganosu da kaina" Audu ya fada dan maganarta ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 32