bakwai a Duniya Mahaifinsa Malam Lawan Me gari ya rasu wata hudu tsakani ya rage kwanaki goma Goggo Asabe ta fita daga takabarsa itama ta amsa kiran Mahaliccinta shikenan Tijjani ya tashi maraya gaba da baya riqonsa ya koma tsakanin dangin Mahaifinsa yau yana wannan gida gobe yana na can wanda gaba dayansu sunayi ne saboda tarin dukiyar qasar da Mahaifinsa ya mutu ya bar masa ba kuma sun bari ya girma ya samu komai ba se wata gona kwalli daya wadda itama wani qanin mahaifiyarsa ne yayi tsayin daka gurin ganin bata salwantaba se fili wanda gidan da iyayensa suka zauna ya kamachi a bashi amma Sabon me garin da aka nada wanda yake qanin Mahaifinsa ya gaje ya shiga ya zauna a ciki dukda cewar gadon Tijjani ne, badan ma suna tsoron tijarar Kawun nasa ba shine dalilin daya saka ya bashi wani fili daban yace ya gina.
Da wannan gona daya tsira da ita yaci gaba da kula da rayuwarsa ita yake nomawa abinda ya samu ya siyar yayi buqatunsa har yayi aure ya auri Fadi yar Kawunsa yayan mahaifiyarsa haka suka zauna tsayin shekaru cikin rufin Asirin Allah har tayi yaya biyar Maza uku mata uku Lawan da suke kira Baba se Hashimu, Maryam, Amina, Aminu da kuma Zulai. Bayan Baba da Hashimu sun tasa su suka cigaba da taimaka masa da gonar da ita kadai ce hanyar samunsu, abinda suka noma a ciki zaau cire abinci, ragowar a siyar a ringa buqatun yau da kullum wannan dalili ya saka rani damina koda yaushe cikin shuka yake musamman da Allah ya taimakeshi gonar tasa tana kusa da wata fadama dan haka bashida matsalar ruwa sabodan noman rani sannan tana da girma babu laifi shiyasa yake noma nau'ikan abici kala kala.
Suna zaune lafiya da Fadi lokaci daya ya bijiro da zancen son qarin aure bayan daya hadu da Hafsatu Farar bafillatana baquwa da sukazo qauyensu kawo Amarya Tijjani na ganinta yace tayi masa, be samu matsala da Fadi ba, inda ma yar tangardar take be wuce damuwar yanda al'amura zasu kaya musu ba idan ya qaro auran dalili da cewar lallaba rayuwa sukeyi ba shida wata hanyar samun kudi idan ba noman nan da yakeyi ba dukda rayuwa nada sauqi a wancan lokacin amma nauyi ze qarar masa idan yayi auran, rarar da suke samu ta amfani gona har a siyar bw zama lallai aci gaba da samu ba tunda wacce ze auro din itama haihuqa zatayi wata rana wannan Fadi taso ta fahimtar dashi amma ya nuna komai na Allah ne shi yake ciyarwa kuma yanda ya nufeshi da qarin auran ze hore masa abinda ze cigaba da kulawa dasu haka kuwa akayi ya auro Hafsatu zaman au gwanin dadi da Fadi tana bata girma sosai a matsayinta na wadda ta girmeta kuma tana sama da ita a gidan aure wannan ladabi nata yake qarawa Malam Tijjani sonta.
Shekara daya ta haifi Da Namiji aka saka masa Yakubu, shekarar biyu ta haifi Audu se Bilkisu, Aisha da kuma Muktar me sunan Babanta suna ce masa Baballiya.
Rayuwa ta qarayiwa Malam Tijjani da iyalan sa tsanani saboda sun qara yawa kuma madogarar tasu dai guda daya ce wannan gona, qari da haka hatta da Maryo da Amina yayan Goggo Fadi da aka aurar mazajensu duk suma ba masu qarfi bane se ya zama har dasu ake noma gonar Malam Tijjanin abinda aka fitar a raba kowa yaje yayi ta jalautawa da iyalansa wannan matsatsin rayuwa ya saka Audu tashi da burin son yayi kudi saboda Baffansa ya huta da wahala. A lokacin farko shigowar Boko Yaro dayane a garin yake karatun Bokon Shamsu wanda yake dan Me gari shima ya kaishi cikin Kano ne yana zaune gidan wani Hakimi se shekara shekara yake zuwa gidan. Sa'an Yakubu ne amma duka Abokanai suke dasu Audu tunda tazarar shekarun ba yawa kuma tare suke karatun Allo kafin aka kaishi birni idan Shamsu yazo kuma zeyita bawa su Audu labarin Birni da Turawan da suke koya musu karatu har yace suyiwa Baffansu magana suma akai su dan Malamansu sun gaya musu idan suka dage sukayi karatu zasu samu aiki a ringa biyansu Albashi wadanda suka iya turanci kuma har Ingila zasu tafi dasu.
Zancen kudi da Audu yaji yasa hankalinsa ya tashi ya kuma quduri niyyar zuwa Birni Yakubu kuwa da tun qaraminsa ya tashi da Burin Zama Alqali, ko wasa akeyi zece shine Alqali ayita zuwa gabansa ana kawo shari'a shima Shamsu yace masa a birni da akwai Kotu ba irin yanda ake shari'a anan ba sedai aje gaban me gari. Audu yacewa Yakubu suyiwa Baffansu maganar zuwa Boko amma se yace Aa dan shi yana da sanyi ba kamar Audun ba yana gudun yiwa Baffan magana yayi masa fada dan lokacin da aka kai Shamsu be manta ba harda Baffansu a masu cewa an kaishi ze koyo yahudanci Audu beyi qasa a guiwa ba ya samu Mahaifiyarsu da suke cewa Dada da zancen tayiwa Baffa magana ya samu me gari idan Shamsu ze koma birni su bishi take kuwa ta nuna rashin amincrwa itama dai kamar Yakubu ta tuna masa da Mahaifinsa na Adawa da Karatun Boko da ya shigo daga nan aka bar maganar badan har zuciya Audu ya haqura ba sedai yayi shiru ne kawai zuwa wani lokaci saboda tunda yaji zancen kudi fa hankalinsa yayi kan Birni kuma kota halin qaqa dai se yaje shi.
Seda aka shekara kafin dama ta sake zuwar wa Audu a wannan Karon a gurin Malamin da yake musu karatun yaji cewar ze kai Yara Birni can tsangayar Malaminsa Gwani Musa a unguwar Kabara. Audu najin wannan batu yana komawa gida ya sanarwa da Dada a wannan karon itama bata ce Aa ba tasan kuma shima mahaifinsu baze hana ba inda zaa iya samun matsala be wuci yanzu da suka tasa ba suna taya sauran yan uwansu aikin Gona amma tasan hakan baze zama wani abu ba. Haka kuwa akayi ta damu Malam Tijjani da batun yayi na'am har yace ze samu Malam Tsalha malamin tsangayar tasu yaji kanun maganar, bayan duk shirye shiryen da suka kamata Audu da Yakubu suka bi tawagar Yaran Gari zuwa birni Almajiranci, dukda Malam Tijjani yaso iya Audu ya tafi Yakubu ya tsaya amma Audu ya kafe kaida fata se sun tafi tare saboda shirinsu na karatun Boko wanda Yakubu ya fishi buri akan abu shi neman kudi kawai yake so yaje yayi a Birni ba wani Karatun Allo kona boko ba.
Seda suka shafe wata uku a tsangayar Gwani Musa suna kuma karantar birnin na Kano, basu san inda zasu nemi Shamsu ba balle ya kaisu makarantarsu, Audu a shige shigensa yayi Abokanai anan cikin Magashi suka shaqu da wani Yaro Sa'an sa Hayatu yaron gidan da Audu yake yiwa aikace aikace ne. Hayatu da sauran yan uwansa suna makarantar boko dan haka Audu ya nuna masa shida dan uwansa Yakubu suna sha'awar karatu kuma abinda ya fito dasu daga qauye kenan. Hayatu ya sanarwa da Mahaifinsa wanda a lokacin suna cikin mutanen da suka karbi Boko sosai yaji dadi kwarai da wannan abu dan haka ba tareda bata lokaci ba yaje da kansa ya samu Gwani Musa ya sanar masa da buqatar su Audu tayin karatun Boko. Da yake Malami ne me fahimta kuma shi kansa cikin yayansa akwai wadanda suke Bokon saboda yanda Sarakuna da masu kudi da suke samun damar fita Waje suke fada musu Alfanun Bokon be hanasu Audu ba, ya kafa musu sharadi dai na dole zasu cigaba da daukar Karatu, da safe suje bokonsu su dawo Yamma da dare su zauna a makaranta suyi karatun Qur'ani haka kuwa akayi su Audu suka fara zuwa makaranta shekara daya da haka yace shi ya gaji saboda Shamsu ce masa yayi idan anyi karatu za'a samu aiki a samu kudi shi kuwa kullum karatu ake dora musu bema ji ranar da za'a gama ba dan shekaru ake lissafowa Yakubu ne yayi ta tausarsa akan yayi haquri da sannu zasu kai matakin da suke buri.
Haka suka ci gaba, Yakubu na matuqar maida hankali ga Karatu yayinda Audu turanci kawai ya saka zuciyarsa ze koya saboda idan ta tabbata sun gama makaranta za'a kaisu turai kar yaje ya rasa bakin magana. A hankali ya faratiwa Makarar asha ruwan tsuntsaye, Sadi, da aka kawosu Almajiranta tare amma shi dan Bagwai ne shiya fara nuna masa hanyar Kasuwa. Da safe idan sun tafi Boko shida Yakubu ze zame ya tafi bakin Asibiti anan zeyi duk wani aiki daya samu, dako ne, aike, duk wani abu da zeyi a biyashi haka ya ringayi kan jiki kan qarfi dake ya saka abin a ransa kuma yana da zuciyar yi se gashi baya jin wahalar kowanne irin aiki indai ze kawo masa kudi.
Da Yakubu ya gane baya zama a makaranta yace ze gayawa Malam seya dakata da zuwa Kasuwa, cikin yan kudaden daya samu ya auno Aya da gyada ya kaiwa Matar Malam da suke kira Nene dayake suna shiri yace tayi masa gyada me gishiri da Aya me siga ya daura abarsa a Boko ya siyar a Allo ya siyar se gashi an gane shi a unguwa Audu me gyada da Aya kuma sosai yake ciniki abinsa. Seda suka shekara biyu kafin sukaje gida, a lokacin sun fara zama samari dan Yakubu nada shekaru sha biyar Audu nada Sha uku. Cikin yan kudaden jarinsa yayiwa Dada da qannensa harda Baffansu tsaraba.
Kowa yaji dadin yanda ya gansu, Dada ce ta ringa masa fada akan ina ya samu kudi yayi wannan siyayya be boye mata ya sanar mata da duk abubuwan da yakeyi harda zancen Boko da sukeyi shida Yakubu ya kuma qara da fada mata gaskiyar dama saboda ya samu damar neman kudi Yakubu kuma yayi karatu yasa sukace zasu Makarantar Allon. A wannan karon kafin su koma seda ta sanar da mahaifinsu gaskiyar komai gudun kar wata rana ya gane yace sun hada baki sun munafurceta, da fari ya ringa fada dan sosai yake Adawa da karatun Boko har yana cewa ba zasu koma Birnin ba se kuma daga baya basu san yanda akayi ya canza ra'ayi ba da kansa yayi musu shirin komawa ya kuma yi musu nasiha tareda gargadin su tsaya a turbar Allah karsu yarda masu jajayen kunnuwa su dorasu akan wata hanya sabanin wadda Addinin Islama ya dora mu akai. Ya sake jawa Audu kunne sosai akan banbance tsakanin Halal da Haram tunda yana zuciyar nema baze daku she shi ba, abinda ya janyo masa sakkowa harya haqura zasu koma dinma bayan sunyi magana da Hashimu dansa na biyu shiya nuna masa Alfanun abinda su Audun sukeyi tunda baya kaucewa shari'a bane.
Yace masa "Baba idan ka dubi yanda rayuwa take tafiya a kullum abubuwa qara yi mana wahala sukeyi dan abinda muke nomawa ba wadatar mu yake yi ba balle har mu samu na siyarwa muyi sauran buqatu kuma ko a cikin karkarar nan idan ka duba masu fita fatauci Abokanan mu zakaga suna samun Abun rufin asiri har su taimaka mana muma, da ace tun muna qanana kamar su muma mun tashi da wannan tunanin qila da rayuwar ta mana sauqi amma yanzu tunda Allah yasa su sun himmatu zasuyi a barsu muyita rakasu da Addu'a Aminu ma da ze bisu suje can birnin yayi Bokon koya kama sana'a kamar Audu duk da hakan yayi".
To haka su Audu suka koma ba tareda Aminu ba dan yace ba zashi ba da yake Auta ne Goggo Fadi bata takura masa ba kuma shi kadai ya rage gabanta tunda duk an aurar da Maryo da Amina Mazan ma Hashimu da Lawan sunyi Aure. Rayuwa taci gaba da garawa Audu da Yakubu a birni, iya wuya Audu neman kudi yakeyi yana kuma riqe da hudubar Mahaifansa akan ya tsaya ga halal karya kuskura yaci abinda Allah be halasta masa ba kuma da yake a lokacin duniya na zaune lafiya cuta da bata gari basuyi yawa ba shiyasa abun yazo masa a sauqaqe. Tun yana Dako a kasuwa ko aikace aikace har ya fara kayi nayi, ze karbi kaya ya fita dasu ya siyar ya cire ribarsa har ta kai ya hada yar tireda yana kasa kayan koi gefe gida kuma ya ajiye Baro duk wani dan itace na marmari da ake yayi a lokaci ze saro ya ringa siyarwa yan kasuwar har mamakinsa suke ganinsa yaro qarami dukda yana da baragen girma amma zafin neman sa ba duk babbaba shiyasa yayi shura a bakin Asibiti babu wanda besan AUDU BECHI ba haka suke masa inkiya da garinsu.
Duk qarshen shekara suke zuwa gida kuma duk sanda zasu tafi haka ze hada tsaraba himili duk wanda ya shafe shi seya riqe masa wani abu ya kai masa dan badaga nan ba Audu akwai kyauta kuma a wannan yanayi Girma da Wahala suka fara kwantar da mahaifinsu dukda shekarunsa basu kai ace ya kwanta tun yanzu ba amma yanda rayuwar ta faro tun quruciya jiki yana wahalar data zarce abinda ze dauka shiya janyo masa ciwo yayi masa kwaf yau lafiya gobe babu haka yasa idan zasu je gida Audu ze siyi magungunan ya tafi masa dasu da irin mayukan zafi saboda qorafin ciwon jiki da yake yawanyi.
A wannan gantafalfala suka kammala Primary tareda Saukar alqur'ani ta biye wadda Audu dai ba zuwanta yake ba a sati befi ya leqa sau daya ba ita kanta Allon Karatun dare kadai yake zama Gwani yayi fadan yayi nasihar amma Audu ya toshe kunne, dadinta daya yana biya karatu daidai ya wanke Allonsa akan lokaci wannan yasa Gwani yake daga masa qafa Bokon ma idan ana jaraba zeje yayi kuma zeci ga turancin daya saka kansa ya iya radau dan ko Yakubu me qulafucin Bokon Albarka shiyasa Malaman suke ji dashi, Audu akwai rashin ji amma akwai kwakwalawar daukar Karatu.
Yakubu ya tafi makarantar kwana dan cigaba da karatun sa, burinsa ne ya zama Alqali Audu kuwa yace yayi sallama da Boko ya kama neman kudi kuma. Shi yayiwa Yakubu duk wani shiri na tafiya makarantar, haka kuma yana kai masa ziyara idan anyi hutu Yakubun Bechi yake tafiya yayi hutunsa acan Audu kuma ana Kano ana ta fafutukar rayuwa. Inda ya kafa yar tiredar tasa aikin fadada titi yabi ta gun dole ya tashi daga qarshe ya koma zuba kayan kolin nasa a Baro yayi ta zaga kasuwa yana waqa ta kiran customers yanda yake waqar abin dariya yake saka wasu siya badan ma sunyi niyya ba. Yakubu yana shekara ta uku a makaranta lokacin kuma aka aurar da Bilki wadda take bin Audu, ba qaramar Bajinta Audu yayi a auran nan ba dan dama ya dade yana tanadi saboda mutuniyarsa ce ko irin fadan sako da sakon nan basa yi da akwai fahinta sosai a tsakaninsu a kuma Bikin Bilkin ya dabbaqa soyayyarsa ga Bara'atu wadda tayiwa Bilki babbar qawa. Tun suna yan yara Audu yake sonta an dauka yarinta ce ashe shi har ransa ya riqe abun yanzun daya furta yana son ta da yawa wasa suka dauki abun saboda idan ka dubi a yanda akewa yara aure Bara'atu ta isa kaiwa daki dukda shekarunta sha biyu ne a sannan amma ga Bilki da take sa'arta an mata aure itama Audu kuwa yana shekara sha bakwai koda Maza suna saurin Aure a qauyen amma be isa ba tukunna, ga Yakubu me sha tara da Aminu me Ashirin da biyu nan basuyi aure ba bare Azo kansa haka dai ya ringa hurewa Bara'atu kunne da soyayyarsa seda ya tabbata ta mato ta yanda ko ya koma birni ba zata saurari wani ba zata jira shi kafin ya koma Birni ya bar Audu da suke hutun makaranta zasu shiga Aji hudu a sannan.
Satin Audu daya da tafiya jikin Malam Tijjani ya motsa kuma ciwon yafi na ko yaushe zafi dole Yakubu ya bazamo Kano neman Audu saboda Malam din da yake ta nanata a kira masa Audu gashi babu waya a sannan, kwanansa daya suka juya hankali tashe yanda ya tarar da jikin Mahaifin nasa ya tayar masa da hankali ya shawarci manyan yayyensu akan su tafi da Malam Kano a akaishi Asibiti amma suka qi a cewarsu anayin na gargajiya wai a yanda ya ganshi ma jikin da sauqi, cikin daren Ranar Malam Tijjani ya amsa kiran Ubangiji har yaja numfashinsa na qarshe kuwa be dena maimaita musu su tsaya akan gaskiya ba kuma duk rintai duk wahala karsu yada zumunchi suci gaba da hada kansu kamar yanda suka tashi.
Sunyi kuka sosai da jimamin rasuwar mahaifin nasu, daga Audu har Yakubu suka kasa komawa inda suka fito saboda mahaifiyarsu da mutuwar Malam din ta tabata sosai har itama ta kwanta jinya, ita din bata da kowa a yanzu se Malam dasu yayanta dan Iyayenta duk sun rasu Yayyenta biyu suma shekara uku kenan Babban Ya rasu me bi masa kuma be cika shekara da rasuwa ba shima yanzu ga Malam shima ya tafi. Seda sukayi dagaske suka qarfafa mata guiwa kafin ta dangana taci gaba da zaman takaba. Audu ya damu Yakubu akan batun komawa makaranta dan tuni hutu ya qare an Koma amma duk sanda yayi masa maganar se yayi shiru yaqi ce masa komai. Audu be fahimci dalilin Yakubu naqin komawa makaranta ba seda akayi sadakar Arba'in din Mahaifinsu, a ranar kuma dattawan qauyen suka zaunar dasu akan maganar rabon gado.
Page 3
Malam dai sun sani Gona guda daya ya bar musu se gidan da suke ciki, aka raba musu komai yanda shari'a ta tanadar, ba'a samu wani surutu ko hayaniya ba saboda yawansu daya kowanne bangaren sunada Maza uku mata biyu se iyayensu mata. Zancen gida duk sun yarda akan kar a raba iyayensu suci gaba da zama ciki tunda kowa yasan bangaren da yake mallakinsa haka Gona sun yarda akan za'a ci gaba da nomata yanda aka Saba ana raba amfanin kuma lokacin daman yayi daidai dana girbi dan haka kwana kadan akayi girbi aka kawo amfanin Gona gida kuma daman abinda ake dan jalautawar yayi qasa banda ma Audu da ya zo da yan kudade shi yake ta hidima da gidan tun bayan Rasuwar Malam.
Su Audu sunyi zaton za'ayi rabo ne matsayin cewar kowa yana da gado cikin abinda aka girbe din amma se sukaga sabanin haka. Sanda akayi rabon baya gida yana gurin Bara'atu yaje tadi. Yakubu da akayi a gabansa kuma kanzil bece musu ba suka kacaccala kayan suka ware musu nasu wanda dama ba dukka aka fito dasu ba kadan aka yafito daga Rumbu aka zuzzuba musu Masara, Gero, dawa buhu bibbiyu Alhalin a shekarar an samu amfanin gona ko wanne launin Abinci yafi Buhu Hamsin amma abinda suka basu kenab se shinkafa da sukeyi wadda yawanci daman ita Siyarwa akeyi to bata isa girbi ba. SedaAudun ya dawo ya tarar da kayan a bakin qofar dakin Dada inda suka ajiye musu, duk da cewar Rumbun gidan a kasonsu ya fado amma su Hashimun sun kulle tulin abinci sun tafi da muqulli. Sanda Malam yana raye duk nan ake ajiye komai duk wadda zatayi girki ta shiga ta diba su kansu su Hashimun sedai su dibi wanda ze ja musu lokaci idan ya qare a kuma diba.
Audu ya gama kallon kayan kafin ya shiga dakin Dada suna zaune suna cin tuwon Dawa da Aisha ta tuqa musu suna hira jefi jefi ya ajiye musu qullin soyayyar karfasa daya taho musu dashi Dada ta saka masa Albarka tareda tura masa nasa kwanon tuwon da aka ajiye masa. Kai ya girgiza alamar ya qoshi dan yaci a gidansu Bara'atu, Innarta Da takeyi dashi shiyasa dui sanda yaje gidan seta tisa dole ya shiga in da darene se yaci tuwo tun yana kunya har ya sake dan ko beci ba zata hado shi dashi ya taho gida. Seda ya bari sun gama cin tuwon kafin yayi magana yace
"Dada naga Hatsi a qofar daki na waye?"
"Yawwa daman kai nake jira ka kamawa Yayanka ku shigar dasu dakin Malam (shima Rabon su ne) wannan uban sakalcin wai baze iya ba" ta nuna Baballiya dake rakube gefen gado wai bacci yake so yayi ita kuma ta hanashi tace se tuwon daya ci ya ratsa masa.
"Abinda ban gane ba Dada waya kawo Hatsin?" Ya sake tambayarta. Ta miqe tana cewa
"Rabon mune na amfanin gona da aka fitar dasu yayyenku suka raba, to kaga Rumbun nasu ne yanzu shiyasa nace ku saka a dakin Malam tunda nan babu guri"
"Wancan abun ne rabon mu rai shida a cikin sama da buhu dari da aka fitar, kenan buhu daddaya muka tsira dashi cikin gadon uban mu ba wai kyaimuta aka bamu ba?" Audu ya fada cikin zafin rai yana miqewa se a sannan Yakubu yayi magana yace
"Abinda suka ga ya kamata su bamu kenan kuma kar kace zakayi magana muje mu shigar dakin kamar yanda Dada tace"
"Wallahi Baze yuwu ba, banda ma tsabar rainin wayo roqarsu mukayi da zasu tsammana wannan abun ko kuwa? Dole a fito da komai a sake rabo me yasa ma da zasu fara baka kirani ba" yana gama fadar haka fuuu yayi waje Dada da Yakubu na kiransa amma beko saurare su ba yayi dakin Goggo Fadi.
Dada da Yakubi sunfi Audu sanin yanayin zaman gidan a yanzu saboda kusan shekara bakwai kenan daya fara zaman birni idan yazo yan kwanaki yakeyi ya koma kuma duk sanda zezo da abin hannunsa dan haka kowa haba haba yake dashi. Yakubu kuwa tunda ya fara makarantar kwana nan yake hutunsa dan haka yasan duk wata kitimurmura dake faruwa tsakanin Goggo Fadi da yayanta da yawan qorafin da sukeyi akan Abinci wanda a cewarsu su suke wahala su Noma Hafsatu da Yayanta sedai kawai suci harda Bilki da ake aikawa dukda shi Mijinta babu laiifi yana da rufin asiri dan haka be shiga cikinsu ana noman tare ba amma in akayi girbi se Malam yasa an loda itama an kai mata acewarsa tana da haqqi cikin gonar.
Iyakar qoqari Malam yayi gurin ganin cewar kan Ahalinsa be rabu ba kuma har ya mutu yana musu wannan nasihar wadda kuma sunyi qoqarin boye taciki sun hada kai a gaban idonsa to amma yanzun basa jib zasu cigaba da bautawa Hafsatu da yayanta shiyasa suka fara da haka a ganinsu ma sun musu Adalci da suka basu wannan din ladan Aikin da Malam yayi kafin ya kwanta dama.
Audu kuwa da sallama ya shiga dakin Dada yana qoqarin danne bacin ransa, suna zaune ita da Baba da Hashimu suna hira. Ya tsugunna daga gefe ya gaidasu suka amsa fuska a sake kafin sukayi shiru gaba daya. Seda ya saisaita muryarsa ta yanda zasuyi magana cikin risilama kafin yace
"Yaya Daman naga hatsi a qofar mune dana tambayi Dada se tace mun wanda aka rana aka fitar mana ne"
"Na'am, haka akayi" Hashimu ya fada yana karkacewa dukda cewar shi Audu da Baba yayi magana, shiru suka kumayi ganin da yayi basu da niyyar tanka masa dan Goggo Fadi ma wata hira take neman jefo musu tana tambayarsa yaushe ze koma Birni dan haka yace
"Yaya tambaya fa nakeyi shi wancan abun ana nufin shine rabonmu mu biyar da Mahaifiyarmu kenan?"
"Ga amsa ka bawa kanka Audu me kuma kake da buqata?" Baban ya magantu sannan yaci gaba da cewa
"Ko yayi yawa ne? Tunda kai ba mazauni bane Yakubu ma Makaranta ze koma Innartaku daga ita se Aisha da Baballiya Aisha ma jiya na hadu da Hayatu yake roqar arziqin a basu ita tadan taya Bilki zama inaga an samu qaruwa ne ko yace bata da kafiya dama yanzu nake so idan zan fita na leqa nayiwa Goggon maganar to gaka ma seka shaida mata idan ka koma kaga wannan abinci ai ya isheta ita da Baballiya".
Ran Audu ya qara baci amma ya daure murya a daure yace
"Amma dai Yaya koda ace cikin Dada ne ita kadai kamata yayi a raba komai kai daya yanda shari'a ta tsara tunda dai muna da gado a ciki wannan ruwan mune bisa Adalci mu qara muku tunda kun fimu buqatar abincin"
"Babu shakka rashin kunya zaka manq Audu mu kake kallo kana cewa mun fiku buqatar abinci wato ga mayunwata ko?" Goggo Fadi ta fada tana tafa hannu. Ko a jikinsa yace
"Ni ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 32