Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya nemo masa ita. "Wlh sonta nake Bashir kuma da Aure" ya fadawa Bashir din. "Amma dai Audu baka da hankali, to ai koni da nake cikakken dan Bariki iyakata da Karuwa na biya buqata ta mu rabu a gurin duk matan da suke yawo a garin nan ka rasa wa zuciyarka zata so se Karuwa? Hauka kake ko shaye shaye ka fara?" Bashir ya fada cikin madaukakin mamaki. "Nidai idan zaka nemo mun ita kawai ka nemota Malam babu ruwanka ko Magajiya ce a hakan naji na gani kuma ina sonta in har ta amince kuma auranta zanyi" Audu ya bashi amsa cikin tsare gida. Bashir ya kunna sigarinsa yana zuga yace "Babu shakka Haqqin Bara'atu ya fara dabaibayeka tun ba aje ko ina ba, ka saki yar gidan mutunchi me Cikakken Asali zaka maye gurbinta da Karuwa to Allah ya kyauta ka shirya gobe muje Zariyan, da kace musu Yar Dagwas da tuni an nemo maka ita sedai kuma idan suna ta canza a can dan halin matan Bariki ne basa amfani da sunansu na Ainihi. Page 16 Kamar yanda Bashir ya fada suna isa suka tambayi yar dagwas se gasu a dakinta aka rakasu. Zubaidan na kwance kamar mara lafiya suka shiga, ta ringa kallonsu da mamaki dan bata gane Audu bama Bashir dai data fi waya shi ta gane. "Lafiya? Tara ko bashi?" Ta fada cikin tsiwarsu irin ta yan Bariki bayan data miqe tsaye. Audu dai se binta yake da kallo Bashir yace "Ai kya bamu gurin zama musha ruwa tukunna yar dagwas", tayi gatsine kafin ta dauki wani siririn mayafi ta yafa a kanta da babu dankwali ta fita tana tafiya a hankali. "Duk yanda akayi dan Hau ta hadu dashi ya lakada mata na jaki shiyasa ka ganta haka" Bashir ya radawa Audu. Wani duumm yaji a zuciyarsa, shikam So be kyauta masa ba ya rasa macen da ze zargo masa se yar bariki wadda jikinta bashida shamaki da Maza. Zuby ta dawo da kwalabe uku a hannunta, biyu na Giya is Coca cola daya ta ajiye a gabansu. "Ga naka nan wadannan nawa ne" Bashir ya fada yana tura masa Coke din. Seda ya zuqe kwalba guda kafin ya kalli Zubaida dake zaune daga gefe ta jingina tana kada qafa yace "Tafiyar ta Aboki na ce, kwanaki ma yazo yayi ta bulayi ni ban ma san ya akayi yasan sunanki Zubaida ba yazo haka ya koma ba tareda ya sameki ba, bari na baku guri na dan nemi inda zan rage lokaci" ya fada yana miqewa da dayar kwalbar a hannunsa. "Kaga jashi ku tafi ni ba lafiya ta isheni ba kuma ko qalau nake kasan tsadata ba haka nan ake fado mun ba kamar wata mara Aji" ta dakatar da Bashir din, se yayi murmushi yace "Al'amarin da yake tafe dashi yafi wannan kedai ki saurareshi kawai" daga haka ya fita ya barsu. Audu ya muskuta yana kallonta soyayyarta na qara huda zuciyarsa yace "Bakida lafiya ne" "Matsala aka samu nayi ciki, uban yace ze karba kuma naga kar daga baya yazo ya mun Akuya na zubar" ta fada masa kai tsaye kamar wadda ta aikata abin kirki, is ya kasa cewa komai ya zuba mata ido kawai zuciyarsa na bugawa. Ina jinka fadi abinda ya kawoka dan kwanciya nake so nayi" ta sake fada tana gyara zama, zaman shima ya gyara ya fuskanceta dakyau kafin ya shiga zayyano mata abinda yake cikin zuciyarsa dan ya gaza dannewa, "Kuma ni da Aure nake sonki, ina so ki bar wannan rayuwar ki koma gida gaban iyayenki wannan rayuwar bata dace da Mace kamarki ba, ki je kiyi Istibra'i zan aureki". A duk maganganunsa fadar ta koma gida gaban iyayenta ne ya jefata a wani hali ya tado mata da tsohon mikin dake zuciyarta nan da nana hawaye suka wanke mata fuska. Kewar gidan da Mahaifanta ya taso mata se gani yayi ta hade kai da guiwa tana kuka wiwi. Hankalinsa ya tashi da kukan da take ya kuma shiga mamakin me ya sakata kuka, shidai ba wa'azi yayi mata ba balle ace tsoron Allah ne ya ratsata kawai ya gaya mata yana sonta ne ze Aureta amma take wannan kukan kamar wadda zata mutu take. "Ki dena kuka dan Allah" ya fada cikin rabewar murya. "Ka tashi ka fita" ta bashi amsa cikin bada umarni. Ya tsaya amma tsaqar data buga masa tasa dole ya fita cike da mamakinta ya zauna a qofar dakin. Zubaida kuwa tana kuka ta koma tunanin Baya, gida take tunuwa da mahaifiyarta tareda sauran yan uwanta da kuma dalilin daya fito da ita. Duk ranar da aka ambaci Iyaye ko Gida se tayi irin kukan nan, tana so ta sake ganin nata amma bata da hali. Kalaman Mahaifinta suka dawo mata sanda yake korarta daga gida. "Ki tafi, idan kika sake waiwayarmu Allah ya isa iyakar abin kunyar da kika jamun ya isa ki tafi duk inda zakije Zubaida na yafeki daga cikin Yayana". Cikin dare ya koreta, ba tareda yayi tunanin ina zataje ba wane hannu zata fada kuma ya gaya mata karta kuskura taje gurin danginsa kona mahaifiyarsu. Hatta da yan unguwa da suka tausaya mata suka so bata mafaka Tijara yayi musu yace ze hada duk wanda ya shigar masa hurumin gida da hukuma haka ya koreta se tasha taje ta samu mafaka duk akan dalilin Qaddarar data fada mata wadda shine sila. A dalilin kasa sauke nauyinsu da Allah ya dora masa na ciyarwa da sauran buqatu ya tilasta mahaifiyarta fara dora mata tallan shinkafa da wake tana kaiwa Bakin Kasuwa kuma a nan ne qaddara ta hauta wani Azzalumi yayi mata wayo yayi mata fyade, shekararta goma a sannan, ya gana mata Azabar data fitar da ita daga hayyacinta qarshe ta farka ta ganta a gidansu Kwance ga Mahaifiyarta na Kuka Mahaifinta kuma na Sababi kamar zeyi Aman wuta. Yana ganin kuma ta farka be duba komai ba yace ta tashi ta fitar masa daga gida, a fadar sa daman an sha gaya masa ana ganinta a shagunan Maza, ko a sannan din be yarda Fyade akayi mata ba, a yanda wanda suka tsinto ta suka gaya masa wai ciki ta zubar, wanda ya bata maganin ya gudu se ita suka tsinto cikin Jini a wani kango. Babu dogon tunani babu komai Mahaifinta ya yanke wannan danyan hukunci na korarta a cikin dare. Beyi tsinkayen cewa a sannan ko Al'ada bata fara ba ballantana ace ta dauki ciki, yayi mata korar kare cikin rashin Imani, Mahaifiyarta da qannenta naji suna gani tabar gidan shekaru goma kenan kuma kamar yanda ya fada bata sake koda taka qafarta a qasar Kano ba da Asuba tabi wata mata Mai siyar da Abinci a tasha daman ta santa idan ta kawo tallah tana gaisheta matar tasan abinda ya faru da Zubaidan dan haka data ganta cikin daren bata tambayi ba'asi ba kawai ta dauketa ta kaita dan dakinta na langa langa dake cikin Tashar. A nan ta gyarata tayi mata wanka ta kuma bata Abinci washe gari da Asuba suka hau mota suka bar Kano dan dama taga matar ta hada kayanta tsaf da alama zatayi Balaguro, bata tsinci kanta a ko ina ba se a Kwantagora, da fari Abinci suke siyarwa da giya a nan gidan daga matar ta ingizata zuwa ga wannan rayuwar da take nadama da dana sanin shigarta. Takanyi kuka tace me yasa bata tsaya ba Babanta ya halakata tunda yace idan bata fita ba seya kasheta? Data sani ta zauna ya kashe ta ta mutu tun sannan qila da tana Aljanna abinta da wannan qazamar rayuwar data jefa kanta a ciki. Audu na qofar dakin yana jiyo kukan ta daga ciki, kasa daurewa yayi ya koma ya tsaya akanta yana ganin yanda take kuka har jikinta na jijjiga. "Dan girman Allah kiyi shiru, idanhar maganar so ko aure danayi miki ce ta sakaki wannan kukan na janye na haqura ke dena Kukan haka" ya fada cikin sigar lallashi. Bata bari ba, haka ya kai tsugunne ya ringa lallashinta da kalamai masu kwantar da hankali. Shida kansa yayi mamakin inda ya iyasu, be haqura ba har seda ta dena kukan tana ajiyar rai da jan majina. "Kiyi tunani akan maganata" ya sake fada mata ba tareda ya sare ba. "Ta yaya mutum kamarka me kamala, na fahimci ba halinka daya da Abokinka ba ya za'ayi kace zaka auri Karuwa kamata wadda bata da mutunchi ballantana daraja?" Ta fada hawaye na sake sakko mata. Audu ya zauna da kyau ganin ta sakko tana so suyi magana yace "Nima ban sani ba, amma na tabbatar qila Allah ne yaso dana zama silar fitar dake daga wannan rayuwar shiyasa ya doramun sonki. Sannan maganar Mutunchi ko Daraja, ban sanki ba bansan daga inda kika fito ba amma na tabbatar koma daga ina kike kin kasance Mace me Mutunchi da Daraja a baya, qaddara ce ta kawoki nan domin mata kadan ne suk shiga Bariki da son ransu, mafi aka sari Qaddara ce take afka musu wadda mutane suke kasa yi musu uzuri harsu ingizasu ga zuwa abinda yafi wanda ya same su a baya muni. "Duk abinda dan Adam yake aikatawa muddin be mutu ba yana da damar shiriya ya nemi yafiyar ubangijinsa, kema lokaci be qure miki ba. Ki bar wannan rayuwar da babu komai cikinta se qasqanci, ki koma gida wlh da gaske nakeyi zan aureki bada wasa nake sonki ba". "Mahaifina ya koreni, yace karna sake komawa gidansa idan har naje be yafe mun ba. Ina so naje, ina kewar mahaifiyata amma bana son na sake shiga wani fushin nasa akan wanda nake ciki" ta fada cikin sauti me ban tausayi. "Ke din yar wane gari ce? Kuma meya fito dake daga gida?" Audu ya tambayeta. Bata boye masa komai ba na daga labarin rayuwarta ta gaya masa gaskiya, yaji tausayinta kwarai dagaske ya kuma ga baiken Mahaifinta. Irin wannan qaddarar ta fadawa mata da yawa, idan da ace iyaye suna taya Yayansu karban qaddararsu a yanda tazo musu da an samu raguwar masu fantsama Bariki. Da yawan iyaye Sukan manta cewar Abin kunyar da suke tunqahon yayan sun jawo musu har yasa suka kada su duniya kadan ne akan rayuwar da suke jefasu suyi, ga dakon zunubi domin duk abinda suka aikata na barna tare za'a raba musu Sakamakon da iyayen saboda sune suka turasu zuwa ga barnar. A tunanisa da a ringa zunden mutum ana cewa yarsa ta zama Karuwa gara a kira shi uban wadda aka tabayiwa Fyade ko tayi cikin shege ya barta a gabansa ta shiryu har ya aurar da ita wannan haqurin da mutum yayi se ubangiji ya dubeshi ya shirya masa zuri'a amma korar yara akan wata qaddara mara kyau ba daidai bane, su kansu Iyayen sunyi bankwana da kwanciyar hankali daga ranar da suka kori Yayan nasu basa sake samun nutsuwa. Audu basuje Zariya da niyar kwana ba amma Alamun cin galaba akan Zubaida daya gani ya sakashi kwana a garin. Yayi mata alqawarin ze nemo mata mahaifinta muddin yana raye ze hada su kuma koya mutu ze maida ita gida gurin ragowar yan uwanta. Ya roqeta akan ta shirya su tafi Kano tare, ze bata mafaka har zuwa sanda zata daidaita da iyayenta amma taqi, tace dai yaje ba zata dawo idan har mahaifinta ya mata izini. Haka washe gari suka dawo Kano gaba daya Audu bashi da kuzari, Bashir nata yi masa shaqiyanci da cewar shima ya zama dan hannu dan tunda suka rabu basu hadu ba seda safe da zasu wuce Kano dan haka besan duk abinda ya faru tsakaninsa da Zubaida ba. A gida ya tarar da Binta cikin yanayi na neman tashin hankali dan yana shiga tambayar data fara jefa masa itace "Daga gidan uban wa kake?" A lokacin yanayin sanyin jiki da kuma martabar mahaifinta da ya wuce ya zageshi ya saka ya qi tanka maka amma kaitsaye zuciyarsa ta ringa raya masa ya gaya mata daga gidan ubanta yake ko da abinda zatayi akai. Bata haqura ba ta bishi har daki tana ihu da hargagi tareda fadar maganganu. Baturiya matar Ali ce ta gaya mata Audun sun tafi wani gari gurin Mata tareda Bashir itama tsintar zancen tayi a gurin Mijinta yana gayawa wani Abokinsa daya je gidan shine ta wanke qafa ta tafi gidan Binta ta gaya mata ranar bata iya runtsawa ba a tsaye ta kwana tana jiran taga ta inda ze bullo amma be dawo na se yanzun. Duk kalar rashin mutunchin data ringa zazzagawa be tanka mata ba ya shige daki ya kullo qofa ya shiga wanka. A ranar yake so yaje ya fara binciken iyayen Zubaida data gaya masa ita din haifaffiyar unguwar Alkantara ce, sanda ya fito Binta ta sauka daga saman harya fita kuma beji motsinta ba ya dauki mota ya bi kwatancen da Zubaida tayi masa besha wahala ba saboda sunan Mahaifinta data gaya masa Malam Hassan Na'ibi yana fada aka kaishi har qofar gidan lokacin qarfe biyar na yamma rana tayi sanyi a qofar gidan ya tarar da Malam Hassan din da wasu dattijai guda biyu kan tabarma suna hira. Ya ringa kallon mutumin, kamanninsa daya da Zubaidar, sedai yanayinsa ya nuna kamar bashi da lafiya saboda a kishingide ma yake be iya zama sosai. Audu ya qarasa kan tabarmar ya zauna suka gaisa duk suna masa kallon rashin sani. "Gurinka nazo Baba, idan babu damuwa ina so zamuyi magana ne" ya fada yana kallon Malam Hassan ganin haka ya saka ragowar suka gane baqonsa ne. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* "To ai babu damuwa samari ina jinka ka fadi abinda yake tafe da kai wadannan ba baqi bane Aminaina ne koma menene yake tafe da kai ka fada suji" Malam Hassan ya fada. Audu ya kalli mutanen da ya kira da Aminansa kafin ya sunkuyar da kai, bashida tabbacin basa cikin wadanda suka zugashi harta kori yarsa tunda yace Aminansa ne su dan haka baze fadi maganar a gabansu ba balle su hanashi karbarta. Qara qasa da kai yayi yace "Kayi haquri Baba amma daka daure munje gefe dan maganar da take tafe dani dakai kadai zan iya tattaunata" "Ka je mana Malam kaji abinda yake tafe dashi" daya daga cikinsu ya fada, Malam Hassan yayi shiru yana kallon Audu kafin ya yunqura ya janyo sandarsa dake gefe ya tashi, Audu ma ya miqe yabi bayansa yana kallon yanda yake tafiya a gicciye tamkar wanda ya taba samun ciwon mutuwar barin jiki". A soron gidan suka tsaya, Malam din ya kwalawa wata yarinya me suna Surayya kira ta fito da sauri, kamarsu daya da Zubaida dan seda gaban Audu ya fadi daya ganta. "Kawo mun kujerata" ya fada mata ta amsa da "toh Baba" kafin ta juya babu dadewa ta dawo da kujera me qafafu hudu irin ta qarfen nan doguwa Malam din ya dogara ya zauna akai yana nunaqa Audu wani tudu me kama da Dakali dake cikin zauren amma da Qaton dutse akayi shi. Audu ya zauna yana fuskantar Malam din. "Ina jinka samari, meke tafe da kai?" "Kayi haquri da abinda nazo maka dashi Baba sannan ina fata ka fahimce ni" "Ka tafi kanka tsaye bana son wannan alayen me yasa kake son magana dani?" "Akan Zubaida ne" Audu ya fada yana kallon Malam din dan ganin yanda zeyi reacting aikuwa ya zabura tamkar ze fado daga kan kujerar Audu ya tare shi. Jikin Malam Hassan ya dauki rawa ya qanqame Audu yana cewa "Zubaida naji kace? Ina ka ganta? Kasan Zubaidata? Dan Allah tana ina daman tana tana raye?" Malam din ya fada cikin rawar baki tareda daga sauti abinda ya fito da yarinyar dazun da gudu kenan tana tambayar "Baba lafiya?" "Sunan Yayarku ya ambata, dan girman Allah ka gaya mun a ina kasan Zubaida tana ina?" Malam din ya sake fada babu tsammani se ganin hawaye yayi a fuskar Malam tamkar yanda Surayya ta fashe da kuka itama tana ce masa "Ina Yayarmu? Dan Allah ka gaya mana a ina ka santa?" "Kayi haquri Baba zan gaya muku amma se ka nutsu ka dena daga murya karka janyo hankalin mutanen waje" Audu ya fada yana zaunar da Malam din a kan Kujerar daya tashi. "Muje ciki Samari wannan maganar bata zau bace muje ka sanar mun inda kaga Zubaida" Malam ya fada yana miqewa, Surayya ta dauki kujerar jikinta na rawa suka shige ciki Audu ya mara musu baya. "Tausayin Malam da Surayya ya rufeshi ganin yanda suke kuka tamkar ransu ze fita bayan daya gama basu labarin inda ya hadu da Zubaida. "Allah ka yafe mun, wlh sharrin shaidan ne da zuciya ya ingizani na kori yarinyar nan. A sanadiyyar haka abubuwa da yawa sun faru. Baqin cikin rashinta ya saka mahaifiyarsu kwanciya jinyar da har tayi Ajalinta nima kuma na gamu da hawan jini har mutuwar Barin jiki na samu seda na shekara biyu ina jinya bayan rasuwar Habiba kafin Allah ya bani lafiya, wallahi nayi nadamar abinda na aikata babu inda kuma ban shiga ba a garin nan ina cigiyar Zubaida, har gidajen Mata masu zaman kansun na ringa zuwa ko Allah ze saka na samu wanda ya ganta amma ba'a dace ba se daga baya wani bawan Allah ya sanar mana wata Mata ce ta tafi da ita amma besan motar garin da suka hau ba. Tu daga nan na fawwalawa Allah na ke kuma Addu'ar idan har Zubaida tana raye Allah ya gama fuskokinmu kafin na koma gareshi kona nemi yafiyarta, dan Allah Samari tana ina? Ka kaini naga yata karna mutu da haqqinta a wuyana" Malam ya fada yana sake rushewa da kuka. "Kayi haquri ka kuma kwantar da hankalinka Baba, naso ace mun taho tare da ita amma taqi tace ba zata dawo Kano ba se idan har kai da kanka kace ta dawo dan bata so ta sake shiga wani fushin naka amma yanzu tunda anyi haka zan koma Zariya gobe idan Allah ya yarda a gidan nan Zubaida zata kwana" da wannan Audu yayi musu sallama tamkar Malam Hassan ze bishi haka ya ringaji, bayan ya fito daga gidan su Zubaida harya dauki hanyar gida ya fasa kaitsaye ya wuce gidan Mai. Full tank yayi, a nan ya tsaya yayi magriba ya dan ci abinci dan rabonsa da abincin kirki tun safiyar jiya kafin su tafi Zariya. Musbahu ya dauka, Dan Yaya Baba ne daya dakko ya sakashi a gidan Mai yace yazo ya rakashi a daren ya dauki hanyar Zariya. Musbahu ya ringa zare ido ganin inda sukaje, to me ya kawo su nan kuma. Zubaida na bacci taji bugun qofa ta tashi ta bude mamaki ya cikata ganin Audu. "Dama baka tafi ba?" Ta tambayeshi, ya kalli Musbahu kafin ya kalleta yace "Ki hada kayanki Asubanci zamuyi na je na samu Baba kuma ya yarda ki dawo gida" "Qaryane, yaushe kaje Kano har ka dawo nan?" Ta fada tana kama qugu, yayi gaba yana ce mata "Qanwarki Surayya ta girma kamanninku daya tamkar Tagwaye" "Innalillahi dagaske kaje gidanmu, kaha Innata me tace maka?" Ta fada tana fashewa da kuka tareda bin bayansa da sauri seya dakata yace "Kije ki hada kayanki, mahaifinki na cike da zumudin ganinki na tabbatar yau baze iya bacci ba". Washe garin kuwa Asubanci sukayi, shidai Musbahu bakinsa fal da tambayoyi amma babu me bashi amsa. Har qofar gidan Malam Hassan ya isa da mota, tun daga nesa ya hangoshi zaune kan kujerarsa ya rafka tagumi gefe Aminan sa na jiya na tsaitsaye. "Ina ga shine wancan" daya ya fada yana nuna motar dake tun karo su, Malam Hassan ya miqe jiki na karkarwa, Zubaida ta fashe da kuka ganin da gaske Mahaifinta ne tsaye qofar gida yanayinsa kuma ya nuna ita yake jira. Audu kasa jure wannan yanayi na haduwar Uba da Ya yayi bayan wasu shekaru, be ko yi mata sallama ba yaja mota suka tafi. "Wlh idan naji zancen nan a bakin wani nida kai ne" ya fadawa Musbahu sanda ya sauke shi a Gidan Mai. Gida ya wuce, yayi tsammanin tarar da yaqi saboda fita daya sakeyi ya kwana amma se yaga akasin haka. Bintan bata nuna damuwa kamar jiya ba daya shiga wanka ya fito ya tarar ta shirya masa abinci ya zauna kuwa ya nadi abinsa dan a yunwace yake yana ci amma zuciyarsa da kwakwalwarsa suna kan Zubaida ko me takeyi oho. Binta kuwa abinda ya faru jiya bayan ya shiga wanka fita tayi ta tafu gidan Baturiya. "Bari kiji, duk matar da kikaga ta isa to wayo, dabara, kissa da kisisinarta ya kaita. Karki bata wayonki a gurinsa bayan kin rigada kin fara kafa gwamnatinki. Wannan ihu da hayagagar baze saka ya fasa abinda yayi niyya ba amma cikin salo da dabara se kiga kin rabashi da koma wacece dan haka ki koma gida ki bashi haquri da sannu ki gano bakin zaren sannan muyi qoqarin daukar mataki, sannan banda abinki ai da kishiyar gida gara ta waje. Kinsan duk Namijin daya saba zama da Mace biyu ma wuyaci ne ya iya haquri da daya dan haka in har ba so kikeyi ya aurota ya kawo miki ku zauna tare ba ki rabu dashi yayi sabgar gabansa" abinda Baturiya ta gaya mata kenan shiyasa ta dawo gida amma fa a zuciyarta bata jin zata iya jurewa kamar yanda tace mata amma zata gwada dauke kai dan kamar yanda Baturiyar ta fada tabbas da Kishiyar gida gara ta wajen. Kusan sati daya da dawowar Zubaida gidansu kafin Audu ya sake zuwa, har cikin gida Malam Hassan ya saka ya shiga. "Nayi ta neman inda zan zameka ashe itama ko sunanka bata sani ba, Yaro na gode, yanda kayi mun wannan Alfarmar ina fatan ubangiji ya jibanci lamarinka ya rabaka da iyayenka lafiya, nagode kwarai daka maidomun da Zubaida gabana, nagode daka zama silar barinta rayuwar barna" Malam Hassan ya fada daga nan ya basu guri shida Zubaidan dayaga tayi wani sanyi qalau tamkar ba ita ba. "Nagode da abinda kayi mun Allah ya biya maka buqatunka na Alkhairi" tace daga nan sukayi shiru kamar kowannensu ya rasa abin fadi shi ya gaji da shirun yace mata "Ina fatan abinda ya faru a baya ze wuce, ki cire komai daga ranki ki faro sabuwar rayuwa. Abinda ya faru qaddararki ce kuma Imanin mumini baya cika har se ya yarda da qaddara me kyau ko mara kyau sannan, ina fatan hakan ya zame miki kaffara. Sannan kuma ina nan akan bakana na neman yardarki, ina so da zarar kin kammala Istibra'i za'a daura mana Aure" "Kayi haquri bana zaton na dace da nagartaccen Namiji kamarka, nagode da abinda kayi mun kuma in Allah ya yarda zan yita yi maka Addu'a Allah ya baka mace daidai da kai" ta fada

Chapter 15 of 32