Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ido idan bata ga dama ba zata mata ba idan kuwa zata kwana tana magana setaga dama zata ɗaga kai ta kalleta, da Binta ta buga ta buga taga babu riba seta saki lamarin Aisha ta koma kan Yayan gida wanda ruƙonsu gaba daya ya koma hannunta harda na Hadiza guda biyun ta saka an karbo su tun data yaye Aliyu an watsasu cikin yan uwansu. Riƙo take musu irin na jeka ka mutu, iya babu kwaba, abinci me kyau idan sunci a gidan to ranar girkin Aisha ne wadda iyakarta dasu kenan in ta dafa abinci ta basu. Sanda aka maido dasu Aminu tacewa Audu zata ɗauke su har ta kai kayan yaran ɗakinta Allah kaɗai yasan me suka tattauna da Binta washe gari yace ta mayar dasu cikin yan uwansu saboda baya so kansu ya rabu sannan duk abinda ya shafi wani yaro a gidan muddin ba ɗanta ba babu ruwanta a ciki ƙarƙashin kulawar Binta suke. Ita ɗin bata zurfafawa akan abubuwa dan haka bata tsananta ba ta maidasu kamar yanda yace ayi ba kuma ta shiga sabgar Yaransa muddin ba su suka kai kansu gurinta ba wannan zata musu duk abinda ya kamata sedai idan taga wani abun cutarwa ne take tsoma baki wani sa'ilin yaji ya sa a gyara wani lokacin kuma ya gwasaleta yace ai Yayansa ne ba kuma ta fishi sonsu ba, wannan halin sanyin nata da nuna ko in kula akan wasu abubuwan shiya janyo matsalar gidan bata tsaya iyakar kan Yayan tsakar gida ba ta shafi harda nata. Da Binta taga ta kasa cin galaba akan Aisha seta haƙura ta mayar da hankali gurin ganin ta sake kama Audu a hannu da gidan gaba ɗaya, kamar yanda Turai tace mata ta bar batun Aisha domin ba wata tsiya bace ba kuma wani ji da ita Audun yakeyi sama da ita ba ta mayar da hankali gurin gina gobenta data Yayanta. Abinda yake a gabanta yanzu shine tasan duk ta yanda zatayi ta cusa yayanta a zuciyar Audu ya zamana bashida wani tunani idan bana su ba sannan tayi duk me yuwuwa ta dakusar da ragowar a gurinsa, karta barshi ya shaƙu dasu ta hakane kawai Yaranta zasu zama sune kan gaba a kamai nasa hakan kuwa akayi babu Boka babu Malam seda ta san yanda tayi ta raba tsakaninsa da Yaran dukda daman shiɗinma ba wai yana ta tasu bane sosai domin tunda harkokin Arziƙi suka sake buɗe masa ya zamana bashida isashshen lokacim zama a gida ma balle yayi hira da yaran yasan matsalarsu. Duk wani abu na gidan a hannun Binta yake kama daga abinci, sutura harkar karatu da duk wata buƙata kome ya tashi ita zece a tambaya, Riƙo take musu na mugunta ga Azabtarwa, a gabansa takan nuna ta damu da yaran ta ringa kai masa sukar duk yanda take ƙoƙarin jansu amma basa sakewa da ita irin dai yanda ta ringayiwa iyayensu, yaran Zubaida dana Hadiza da suka tasa se suka fara gudu suna tafiya gurin iyayensu dan itama Hadizar tayi Aure tuni, akan wannan Bintan ta haɗasu da Audu ya musu mugun duka dan tace iyayensu na zugosu duk zuwan da zasuyi se sun dawo da sabuwar ɗabi'a ya kuma kafa musu dokar hanasu zuwan daga ƙarshe ma tasa aka kaisu makarantar kwana banda Nata Yayanso se na Aisha data cw bata yarda ba sunyi ƙanƙanta, idan zasu tafi a Arziƙi irin na ubansu Garin kwaki ne da suga se ƙuli ƙuli provision dinsu idan ya bada kudi yace ayi musu siyayya seta soke ba kuma su isa su faɗa masa ba domin izayar da zasu sha se sun gwammace basu faɗa ba shima ɗin kuma be zama lallai ya yarda ba. Yanayin matsatsi da damuwa da suke a ciki tasa cikin su shidan Hassan ne kaɗai se Aminu suke mayar da kai a karatu daman duk aji daya aka sakasu harda su Babannan da yaci ace sunkammala sakandire a sannan amma aka mayar dasu Aji daya na ƙaramar sakandire gaba daya. Banbancin da ake nuna musu ƙarara a fili tsakaninsu da sauran da iyayensu suke a gidan dukda Yayan Aisha ma ba wai sun tsira bane banbancinsu dasu uwarsu tana a gidan kuma ita bata jiran Audu ko Binta da komai na gida yake hannunta a yanzu duk abinda ya tashi na yaranta zatayi musu wanda sauran basa fahintar hakan gani sukeyi su aka tsana aka ware wannan tasa suka washshi uban da matan uban da sauran yan uwansu gaba daya kowanne ya ƙudire wani abu daban a zuciyarsa. Haka rayuwa taci gaba da wullawa shekaru sun shude a kullum kuma rayuwar gidan Audu lalacewa takeyi a maimakon ta gyaru, ya saki komai a hannun Binta ya fantsama duniyar neman kudi kuma Alhamdulillahi rayuwar tana gara masa. Yanda ya faro tushen Arziƙinsa tareda Yan uwa da yayan yan uwansa wanda ba wani karatu me zurfi sukayi a wancan lokacin ba a sannu zamani yana canzawa sauye sauye suna zuwa a duniyar kasuwanci da akwai buƙatuwa ta mutane masu wata kwarewa ta musamman akan wasu al'amiran dole ya fara shigo da bare yana daukar Ma'aikata masu kwarewa ta musamman. Wannan ya zaburar da Binta, ta watsa yaranta zuwa ga fannonin da take da yaƙinin sune zasu riƙe manyan muƙamai a cikin Empire da Audu yake ginawa ta kuma cigaba da cusa masa su, ya zamana duk abinda zeyi ko kuma duk inda zashi tare dasu ne su su ukun nan Manyan su duniya ta sani a matsayin Magadan AUDU BECHI domin tun kafin Zakariyya ya gama makaranta Audu yake turashi ya wakilceshi a tarurrukan kuma a duk inda yaje ya kan gabatar da kansa ne a matsayin Babban Ɗan Audu Bechi, Yakubu yayi iyakar yinsa gurin ganin Audu ya daidaita amma abin yaci tura dole ya saki ya kuma zubawa sarautar Allah idanu domin a yanzun karan Audun ya aki tsaiko, ya isa, sunansa ya fantsama ya zaga ko ina Burinsa na zamowa ɗaya daga cikin mutanen da duk idan aka ambaci sunansu a faɗin Najeriya babbba da Yaro Mace da Namiji ya sanshi Allah ya cika masa wannan buri nasa. Ga dai zuri'a ta taru amma babu hadin kai, babu shaƙuwa babu jan juna a jiki balle jinƙai a tsakani kowa ya tashi ta kansa kawai yakeyi a gidan. Wadanda babu iyayensu sun girma cikin wani yanayi sannnan sun samu labarurruka na gaskiya dana ƙarya akan yanda zamantakewar Audun da kasancw da iyayensu, ita kanta Aisha da yanzu akw kira da Momy ba dadin zaman takeji ba. Itama ta tafka kuskuren da se a yanzu ta gano qautar da tayi, tayi saken da yaranta suka tashi akan tarbiyyar sauran yaran gidan, babu jitiwa a tsakaninsu kowa sabgar gabansa kawai yakeyi wata irin bahaguwar rayuwa tamkar a garin gwarawa haka ake a gidan Audu babu babba babu ƙarami kowa Tantirin kansa ne, tsakaninta da Binta har yau dai se a hankali dukda dai shekaru sunja kuma Bintan ta watsar da harkar kishi domin ta harba musu makamin da yayi musu illah sama da Hayaniyar zaman kishi, ta tarwatsa musu gida ta cusa muguqar Aƙidar yan ubanci a zuciyoyin Yaran gidan koda yake baza'a kira abinda sukeyi da yan ubanci ba domin ciki dayan ma kowa tasa ta fishsheshi akeyi sedai idan sabga ta haɗo tsakanin ɗan wani ɗaki da wani ba sannan ne sukan nuna haɗin kai kowa ya goyi bayan ɗan uwansa har kuwa Yayan Bintan dan abin yafi muni ma a tsakaninsu son kai da kyashi yayi tasiri a zukatansu. Ahmad da Jafar su kadai suka fita daban. Su biyun sun zama tamkar zakka a cikin Ahalin Audu, halaye da ɗabi'unsu sun fita daban dana sauran. Allah ya haɗa jininsu suna bala'in ƙaunar junanau yanda suke mu'amala ba zaka taɓa ɗauka ba uwa daya ta haifesu ba, Binta tayi masifar tayi Bala'in har Malamai ta shiga akan ta raba Jafar da Ahmad amma abu yaci tura, Jafar din duk cikin yaranta tafi jinsa a cikin zuciyarta, tana da burika masu yawa akansa sedai tun fara tasowarsa ta fuskanci kwata kwata Alƙiblarsa daban da tata yanda kasan an canza mata shi a Asibiti idan badan kamanni da yakeyi da ita ba tsaf zata ce ba ɗanta bane. Duk abinda Jafar zeyi seya shawarci Ahamd haka shima Ahmad ɗin, makwancinsu daya, a makaranta ajinsu daya hatta da kayan sawarsu basu banbantawa guri daya suke ajiyesu. Data rasa yanda zatayi domin tana so taja Jafar ta fara kitsa masa abubuwan da take so ya cimma tun da shekarun ƙuruciya amma abu yaci tura, Turai ce ta bata shawarar ta tura Jafar Makarantar kwana tunda Aisha bata ao bata taɓa tura Yaranta ba tasan bazata bar Ahmad yaje ba a haka zata janye Jafar sedai a banza domin tana tayar da maganar bata ma san anyi ba seda ranar tafiya tazo taga Ahmad ya shirya shima babu yanda ta iya ta barsu suka tafi akan zata sake shiri. Daga sama Allah ya aiko mata da mafita, Jafar yana son kwallo tamkar ransa wanda ita kuma bata so domin tana gabin Kwallon na ɗauke masa hankali ta hanashi karatu Rana tsaka Babban Yayansu ya kirata akam ya samarwa Jafar gurbin karatu a Acadami ta Ƙungiyar Manchester dake Ƙasar Ingila ta sanarwa da Audu idan ya yarda a fara shiri. Da fari taƙi, tana gani za'a cuceta a cutar mata Ɗa ita da take da buri akansa acw ya tafi wata makarantar Ball, amma da Yayanta ya kwatanta mata irin Kuɗin da yan kwallo suke samu take ta amince ta kumayi murna ko banza ta samu hanyar raba Jafar da Ahmad. Wannan tafiya ita ta raba Ahmad da Jafar, Ahmad baya bal Jafar kuma baze iya barin burinsa ba dukda a farko yaso yayi tirjiya akan baze tafi na se sun kammala sakandire idan Yaso Yaya Ahmad kamar yanda yake kiransa ya nemi Jami'a a can su tafi tare amma Ahmad ɗin ya ƙarfafa masa guiwa akan ya tafi basu rabu ba suna tare, hakan ko akayi shekarunsu goma sha uku a lokacin Jafar ya koma Ingila tareda kawunsa ya zama se Ahmad kadai a Najeriya, burin Binta ya cika na rabasu saura kuma na aiwatar da shirinta akan Jafar din domin ba wai kwallon ta kwanta mata bane har a rai Madarar kudin da Yayanta yace mata ana samu ne yasa harta yarda ta barshi ya tafin. Rayuwa taci gaba da gurgurawa abubuwa da yawa sun faru na dadi da akasin haka, anyi rashe rashe yan uwan Audu gaba daya sun kwanta dama ya rage dashi da Yakubu se Bilki data dade da dawowa gidansa da zama tunda suka bar Goron Dutse suka koma Hotoro GRA inda ya tamfatsa gida Gari guda me sassa babu Adadi lokacin ne kuma ya ƙara aure ya auri Rabi'atu yar Malam Haladu Shugaban Maroƙa na wannan shiyya. Malam Haladun shiya tallatawa Ausu auran yarsa a lokacin Audun nada niyyar neman Aure domin yana ganin yaci ace ya ƙara mata dukda ya auri wata Fa'iza a can yawon Ƙasashen duniya suka haɗu da ita amma bata kai ga tarewa ba auran ya watse dalili yace sedai tazo gidansa ta zauna ita kuma tana ganin da uwar kuɗinta da gidanta sedai ya bita har an daura da taƙi tarewa ya sallameta iyalansa basu sani bama se bayan da auran ya mutu wannan tasa ganin Rabi'a tayi daidai da tsarinsa kuma yayi tambaya gun Malaminsa domin tuni shima ya zama dan hannu a sabgar Malamai baya abu da ka kamar yanda suke faɗi aka tabbatar masa Rabi'ar hadinsu yayi daidai shikenan ya Angwance abinsa. Shekararta goma sha biyar kenan, da ace tana da zuciya koda yake ace iyayenta nada zuciya da tuni sun kashe Auran sun huta da gorin Binta. Bala'inta daya kwanta dama ta tattaro ta maido gaba daya ta ɗorawa Rabi'a, gorin safe daban na rana daban na dare daban yar matsiyata yar Maroƙa, tun ba data fara zuba Yaya tayi Namiji na fari daga nan hankalin Binta ya sake tashi, da tayi na biyu tagwaye mata se ta ɗan samu sassauci ana uku ma ta sakeyin Mace sannan ta dakata da haihuwar wannan yasa Binta data koma Hajiya a yanzu ta ɗan ɗaga mata ƙafa kadan daga kwarzabar da take mata ta sake mayar da hankali ga Audu da dukiyarsa da kuma yanda zasu gaje komai ita da Yaranta. Babangida da Aminu su kadai suke aiki a ƙarƙashin Audu wanda suma sun shiga gurin ne bisa tursasawar Yakubu da ya zamewa Binta ciwon ido. Duk sanda wani ya mutu a gidansu Ausu se tace inama Yakubu ne ya mutu, ita dai ya tsare mata abubuwa da dama shi yake rage mata Tasiri yana kuma hanata rawar gaban hantsi. Sanda taso ta watsa duk wani Ahalin yan Bechi da yake aiki a ƙarƙashin Audu ta gama shirya yanda zatayi ta saka ya sallamesu Yakubun ne ya watsa mata shiri. Dukda haka bata saraya ba kuma a ƙalla taci riba domin tayi nasarar ɗora Yaranta a manyan kujeru na jan ragamar kamfanunuwan Audun. Zakariyya shine Manaja na baki ɗayam BECHI GROUP OF COMPANIES, Naziru kuma shine Shugaban sashin Manfetur da sauran Albarkatunsa ɓangaren daya fi kowanne samar da kuɗin shiga, Aminu shi aka dora a matsayin Akanta kujerar data so ace Yakubunta ne akai amma hakan bata samu ba se a yanzu suke saka ran faruwar hakan. A sauran Yaran gidan kuwa, Hassan ya zama Likita harta kai ga bude Asibiti na kansa wanda babu ƙwandakar Audu a ciki, be tambayeshi ba shima kuma beyi yakanar ya taimaka masa da wani abu ba yanda besan ya akayi yayi karatunsa harya kai wannan matsayin ba haka nan besan yanda yayi ginin Asibitinsa ba. Babannan harkar Noma ya kama domin shi dakyar yayi dipiloma ya ajiye boko ya koma Bechi ya cigana da Noma gonar da suka Gada gurin Bara'atu kuma Allah ya saka masa Albarka abun musammanda Babangida shima bangaren Harkar Noman ya karanta shiyasa ma Yakubu ya dage seda aka naɗashi shugaban sashin harkar Noma shi yake taimakawa Babannan ɗin da dabarun Noman zamani da Iri masu kyau dan haka sosai yake samun Alkhairi a sabgar ya siyi gonaki da yawa yana ta Noma abinsa acan Bechi Yayi Aure yake zaune da Iyalansa. Hussani shugaban masu taurin kai da kunne na gidan kenan, da fari yaso ya bi wata hanya ta daban, damuwa tasa yaƙi karatu ya fara bin Abokana banza yana shaye shaye, da Addu'a da Nasiha Zubaida data janye Yayanta da dabara ta samu kansa, be cigaba da Makarantar ba ya kama kasuwanci kuma yana da Nasibi kamar Audun sega harka ta buɗe masa dukda girma ya fara zuwa amma dai ba'a bar Yan bushe bushen duka ba shiyasa idan buyaginsa ta tashi babu me shiga sabgarsa a gidan dan ko Alhajin daidai yake dashi. Aliyu ma dai Injiniyarin ya karanta yana kuma aiki a wani babban Kamfani a Legas shigarsa Kano ma shi se sa'i da lokaci, cigaban da suka samu ya zama duk cikinsu babu wanda ya lalace ko yake aikata wani abu na Ashsha ba ƙaramin cin zuciyar Binta yakeyi ba, taso ace nata ne kadai suka ci gaba a gidan, taso rayuwar sauran ta tagayya ta yanda zasu zamana babu mamora se abinda suka yaga suka basu amma hakan ma babu laifi yanzu rayuwar ta fara. Yakubu ya zama Alƙali har seda ya kai ga zama Mataimakin Shugaban Alƙalan Najeriya kafin yayi Ritaya, rayuwar gidansa kishiyar rayuwar gidan Audu ce, Matarsa Ɗaya tilo har wayau Balaraba suna zaune cikin Amince da Yara Biyar data haifa masa Mata uku duk sunyi Aure se Maza biyu suka rage,Audu ya fishi, kudi, yawan zuri'a da kuma suna a duniya domin sunan Audun ba iyakar Najeria kadai ya tsaya ba a yanzu yana cikin jerin manyan masu Kuɗi a Africa duk wanda ya kwana ya tashi ya san da zaman Mamallakin BECHI GROUP OF COMPANIES wato ALHAJI AUDU BECHI sedai shi kuma yayiwa Audun zarra a gurin samun NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI TAREDA AHALI ME CIKE DA QAUNA DA KUMA SOYAYYA. END OF BOOK 1 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 32 of 32