abinda nake nufi ba kenan Goggo, nufina su Yaya suna da Iyalai mu kuwa bamu da nauyin komai kamar kuma yanda ya fada mu ba mazauna bane dan haka abincin zeyi mana yawa ku kuma ya muku kadan"
"To yanzu me kake so ayi?" Baba ya tambayeshi, Audu ya gyara zama yace
"Rabo za'a sake na gaskiya a fitarwa da kowa haqqinsa idan ma ta kama a kirawo su Liman da me gari su raba"
"To ba za'ayi hakan ba ubanmu, kai karfa kaga wai ka fara riqe yan kudade ka dauka kafi mu ko zamu bika to baka isa ba wlh da zaka zo kana yiwa mutane magana da sigar umarni. Bari ma kaji wannan rabon da kaga an baku dan dai Goggo ta saka baki ne amma da mu bamuyi niyyar baku kamar hakan ba saboda babu guminku ciki mu muka sha wahala muka noma abinci dan haka daga yanzu in har kuna son kuci abinda aka noma cikin gonar nan to sedai ku shiga ayi daku" Hashimu ya fada, Audu ya kalle shi kafin ya miqe yana cewa
"Amma dai muna da gado a cikin gonar ko?"
"Su kuma ai ba bayin ubanka bane da zasu sha wahala su noma kuna zaune su baku kuci" Goggo Fadi da se yanzun ta saka musu baki ta fada wannan ya tabbatar masa da cewar shawararsu daya dan haka ya fice yana cewa
"Ai kuwa in har haka kuka zaba sedai a raba gonar idan yaso se na gani in abinda kuka samu ze isheku ku noma abincin shekarar". Goggo Fadi ta hau tafa hannu tana salallami wai yazo har daki ya qare musu tanadi.
Audu kuwa yana fita dakin da suke kwana ya shige zuciyarsa na tafarfasa dan yasan idan ya koma dakin Dada ma fada zatayi masa ta bashi rashin gaskiya amma ya qudure a ransa kome za'ayi sedai ayi tunda ta haka suka zaba to su zuba su gani su waye zasu sha wahala. Kenan ita Goggo Fadi luf luf tayi musu sanda Malam na raye suke zaune lafiya da Dada shine yanzu daga mutuwarsa ko kwana sittin be cika ba fitina zata fara bullowa daga barayinta. Idan taqamarsu su suke noma gona ai su kuma suna da kaso a cikin qasar ya zama tamkar sun basu aro ne suna biyansu shikenan tunda dai basu hango wannan maslahar ba to za'ayita yanda suke so dan idan rigima ce kowa ya sani kaf karkarar bashida mahadi. Tun yana dan mitsitsi fada ne dashi kamar dage babu randa baz fita wasa ba tareda an kawowa Dada ko Baffa qarar ya daki wani ba shiyasa ma ya dena wasa da sa'anninsa ya shiga cikin su Yakubu amma ko su din idan kaga yanda yake a cikinsu seka dauka ya girme su kura ce tayi lafiya kuma tunda aka tabota kowa ze dandani kudarsa.
Yana kwance yana saqa da warwarar ta inda ze bullowa al'amarin, yanzu idan ya koma Birni Yakubu ya koma makaranta kenan zaman gidan in ba'ayi wasa ba gagarar Dada zeyi to kuwa baze taba barin haka ta faru ba. Yakubu ya shiga dakin rai a hade yace ya tashi su kwashe kayancan amma ko gezau Audu beyi ba, daya isheshi da magana yace
"Ka qyaleni baza'a kwashe ba se gobe tayi an sake Rabo sannan su kwashe nasu daga Rumbu tunda ai ba rabonsu bane ba"
"Audu kasan me kake so ka taso kuwa?" Yakubu ya fada yana zama a gefen qafafunsa Audu ya wuntsila ya tashi zaune yace
"Na sani, naje na same su sunce tunda bamu noma ba dan haka iyakar abinda zasu bamu kenan kuna daga yanzun ma muddin muna son Abinci sedai mu shiga ayi Noma damu"
"To ai gaskiya suka fada, shiyasa nace maka bazan koma makaranta ba na haqura da karatun zan zauna na kula da Dada dasu Aisha kai kuma ka shirya ka koma Birni kaci gaba da Buga bugar ka" Yakubu ya fada cikin sanyinsa, Audu ya galla masa harara tsabar takaici daya rasa me zece masa kawai yayi tsaki ya koma ya kwanta. Haka Yakubu ya gaji da masa maganar ya tashi su kwashe kayan qarshe se Aminu daya shigo gidan ne ya taimaka masa suka kwashe, shima seda ya tambayi Yakubun kayan menene wannan yayi shiru bece masa komai ba.
Daya shiga gurin Goggo Fadi lokacin su Hashimu sun tafi gidajensu ya sake tambayarta nan ta wassafa masa qarya da gaskiya akan Audu, Aminu yayi shiru kafin ya kalli Mahaifiyar tasa yace
"Amma zancen gaskiya wannan ba Adalci bane Goggo, wannan hatsin da ake magana fa Malam ne ya noma shi a gonar sa mu duk mun tayashi aiki ne a matsayinmu na yayansa, kinga kenan duk wani Magajinsa yana da rabo daidai da kowa a ciki koda kuwa Jinjirine yau aka haife shi. Sannan maganar kuce idan basuyi Noma ba baza'a basu abinci ba bata taso ba saboda yau idan sukace a raba gonar nan kun sani Kason da zamu samu baze isa mu ringa noma abinda ze riqe mu ba, kuma ko cewa sukayi mu ringa haya muna biyansu bamu da abinda zamu basu. Nidai a ganina ayi maslaha koda kuna ganin ba za'a ringa raba daidai ba tunda mun fisu yawan Ahali a ringa fitar musu da abinda ze ishe su har su saida suyi sauran buqatu hakan duk taimakon kaine".
Goggo Fadi tayi kasaqe tana kallonsa kafin tace
"Babu shakka Aminu wato Hafsatu da Yayanta sun fimu a gurinka kenan ko?"
"Ba abinda nake nufi kenan ba Goggo, ni wlh kece ma kike bani mamaki gaba daya kin biyewa Yaya Hashimu yana doraku akan wata hanya ta daban dan Yaya Baba ma babu ruwansa sedai idan yanzu shima ya dauki hudubar tasa, har Malam yaja numfashin qarshe yana mana nasiha da mu hada kanmu kar mu bari baraka ta shiga tsakaninmu me yasa kuka zauna tsayin shekaru lafiya dasu se yanzu daya mutu sanda yafi buqatar mu hada kai mu cigaba da yi masa addu'a sanann ne kuma fitina da rabuwar kai zata bullo?
Kowa ya sani Dada bata da matsala kuma kome zakuyi ba zata daga kai ta kalle ku ba amma ai mutum ya kamata yasan daidai ba se an tunatar dashi ba ina amfani cikin danne haqqin wani wannan abun fa magana ake ta dukiyar marayu da wanda ya cinye kudi da kadarori daku da kuke shirin cin kwayoyin hatsi a gurin Allah baku da banbanci Goggo, nidai shawarata tun wuri ku farga karku bari shaidan yayi tasiri a zukatanku. Yanzu an fara rigima akan Gona gobe kuma se ace za'a raba gida shikenan zumunchin da Malam yake ta mana takarar mu riqeshi kinyi sanadin murqusheshi"
"Nice ma zan raba muku zumunchin?" Goggo Fadi da jikinta yayi sanyi da maganganun Aminun ta fada, ya miqe yana cewa
"Eh mana saboda duk fitinar da su Yaya Hashimu zasu zo da ita idan kika tsawatar musu dole su bari amma idan kika basu goyon baya kinga gaba zasu qarayi" daga nan ya fice ya wuce can dakinsu inda suke kwana dasu Audu.
Tun Asuba da suka fita masallaci Audu be dawo ba kaitsaye qofar gidan Liman ya tafi ya jirashi yana zuwa kuwa ya zayyane masa abinda ya faru dan ya rantse baze bar maganar ba, shirye shiryen komawa Birni yakeyi tayaya hankalinsa ze kwanta a can Alhalin an fara irin haka ga Yakubu yana maganar ze haqura da mafarkinsa saboda ya zauna ya kula da mahaifiyarsu shi kuma baze yarda ba shiyasa zeyi iyakar qoqarinsa yaga komai ya daidaita sannan su rankaya su koma Kano dan yayi rantsuwa muddin yana numfashi seya cikawa Yakubu burinsa na zama Alqali.
Liman ya gama jin bayaninsa yace yaje ze samu me gari daga nan za'a kira duka yan uwan nasa su zauna haka akayi kafin yamma duk an kai musu sammaci bayan sallar isha'i suka hallara gaban me gari Hashimu se muzurai yakeyi Baba dai fuskarsa kadaran kada han. Liman yace Audu ya maimaita abinda ya faru tsaf ya sake rattabo musu Yakubu se faman harararsa yakeyi aka tambayi su Hashimu sukace haka ne daga nan Liman ya fara musu shari'a ya karanto musu abinda Shari'a ta tanada akan rabon gado, koda ace wani da Guda daya shine kan ragamar juya dukiyar Ahali gaba daya, muddin dai wannan dukiya mallakin mahaifinsu ce duk randa ya mutu hatta da Jinjiri idan ya bari yana da gado a ciki, babu zancen kai kasha wahala ka tara dukiya tunda dai ba taka bace to ta kowace gaba daya. Liman yace gobe za'aje a fito da Hatsi gaba daya a rabawa kowa nasa idan yaso se su sake hadewa su ajiye duk inda suka ga dama.
Hashimu zeyi magana Baba ya hanashi, haka aka tashi rayuka babu dadi washe gari kuwa Liman da wakilan me gari sukaje aka sake rabon Hatsi dukda cewar a cikin daren Hashimu yasa an kwashe fiye da rabi an kai gidansa ya boye a hakan seda aka fiddo da huhunhuna hamsin da biyar, aka hada dana gurinsu Audu shida ya zama sittin da daya nan aka raba musu kowanne bangare suka tashi da Talatin, guda dayan kuma aka bawa masu rabo ladan aikinsu wanda ba shari'a ce tace a bayar ba tsabar son zuciya ya saka su karba.
Cikin zafin rai Hashimu yace
"Toh tunda anyi haka se a fadi yanda za'a cigaba da kasafin Abincin dan wlh babu yanda za'ayi musha wahala muyi noma suna zaune mu ringa raba komai daidai dasu. Audu yayi tsugul yace a raba Gona kowa ya dauki kasonsa. Yakubu ya zabga masa harara yana cewa
"Idan an raba kai zauna ka nomata?"
"Se mu bada haya, idan kuma su zasu karba ma bismilla ayi qiyasin abinda zasu ringa biyan mu duk shekara" Audu ya sake fada. Dada dai ta rasa abin cewa dan duk bata san tsiyar da aka qullo ba seda aka zo rabon abincin kiran da aka musu jiya da suka dawo babu wanda ya fada mata inda sukaje. Haka dai aka tashi a matsayar zasu bar musu barin gonarsu suci gaba da nomawa, ladansu duk shekara abinda aka samu za'a raba uku, su dauki biyu su basu kaso daya matsayin ladan hayar gona kowa yayi na'am da hakan dukda zuciyar Hashimu da Sama'ila Mijin Amina dan karere sunyi wani qullinsu na daban.
Audu be koma Kano ba seda suka tabbatar sun saita komai, sun siyarda wani kaso na abincin suka barwa Dada kudin a hannunta saboda laluran yau da kullum kafin ya tasa Yakubu a gaba kamar shine qanin suka koma lokacin tuni zangon karatu yayi nisa har ana shirin jarabawa dakyar aka karbeshi yaci gaba.
Audu yaci gaba da buga bugarsa a birni yana hada kan kudade, sana'a babu wacce baya gwadawa, idan kasuwar ta gusa seya saki ya koma leburanci, shine aikin gini shine zuwa gidan Burodi har sannan kuma yana zaune a makarantar Gwani Musa dan bashida wani guri da zeje ya ringa kwana idan ba nan din ba. Yana lissafe da su Yakubu sunyi hutun makaranta har an dawo wata rana ya shirya zuwar masa Visiting kamar yanda ya saba sedai bayan yaje makarantar aka shaida masa Yakubu be dawo hutu ba. Kwana biyu tsakani ya tasamma Bechi dan yaje yaga meya hanashi komawa makarantar, bayan isarsa ya tarar da Dada bata da lafiya,a yanda aka gaya masa wai Barayine suka diro tsakar dare suka kwashe musu abinci sannan suka farmaki dakinta suna neman Murjaninta da wata sarqar Zinare data gada gurin Mahaifiyarta da basu samu bane shine suka mata duka ita da Aisha har Aishar ta samu karaya a hannu.
Audu rasa abin cewa ma yayi, tunda aka haife shi a qauyen be tabajin ance barayi sun haura wani gida ba, ba wannan bama ace da suka shigo iyakar Rumbunsune ya tsone musu ido basu taba nasu Goggo Fadi ba sannan zancen Murjani tana dashi wanda ya taka na Dadansu a Daraja dan har shagube takeyi tace se Auran Aminu Autanta ya tashi zata bayar aje birni a siyar dashi tayi hidima duk basu bi sun dauka ba se na Dadarsu. Yayi niyyar tayarda balahira Dada tace Akul, ko bata sani ba idan yayi magana bata yafe ba wannan yasaka jikinsa yayi laqwas, tsanar da be taba zaton zeyiwa jininsa ba ta dirar masa domin yasan shirin sune.
Haka yayi sati daya ya juya dan Yakubu ya rantse masa baze sake komawa makaranta ba gaba besan abinda ze faru da su Dadar ba. Har kuka Audu yayi akan shi ze zauna Yakubu ya tafi ya qarasa karatunsa amma yaqi, yace to sedai su zauna duka nan Yakubu ya ringa lallabashi akan ya tafi shiya haqura da Boko haka Allah ya qaddara bakin abinda ze samu kenan ze zauna ya fara sana'ar dinki daya koya a zamansa a Kano yaci gaba da kula da mahaifiyarsu. Da banbaki ya yarda ya juya Kano da burin nema domin ya samu ya fiddo da mahaifiyarsa da yan uwansa daga Bechi suzo suyi rayuwa me kyau.
Page 4
Haka rayuwa taci gaba da garawa, iya wuya Audu ya dukufa gurin neman Halalinsa kuma ubangiji ya sanya masa Albarka a abun duk abinda ya taba nan da nan se ya karbeshi sedai kuma wani ikon Allah daya fara ganga ganga se sana'ar ta turgude sedai ya saketa ya kama wata wannan yasa aka koma yi masa laqabi da Audu sana'a Goma dan da yawa suna ganin kawai zafin nema ne ya saka komai seya taba. Wata shida shida yake kai ziyara gida idan kuma ya tashi tafiya haka ze hada tsaraba tuli ya kaiwa yan uwansa harda yan Dakin Goggo Fadi da tun abinda ya faru akan Gona aka koma zaman doya da manja idan ka cire Aminu shikadai ne suke mu'amalla dashi yayi Aure har matar ta haihu sun samu Abdullahi yaron idan ka ganshi se kace Audu ne ya haifeshi su Yaya Hashimu kuwa ana fama da baqin rai amma hakan be hana idan Audu yaje da kayayyaki ya basu babu kunya su karbe, a kwai zuwan da yayi Malam babban dan Yaya Baba yace ze bishi Birni Goggo Fadi tayi kicin kicin ta hana a cewarta baze tafi dashi ya koyo masa fitsara da rashin mutunchi irin nasa ba dukda Yaya Baban yaso hakan amma babu yanda ya iya Audu ya koma cike da baqin cikin Yakubu da duk zuwan da zeyi seya masa magiyar ya koma yaci gaba da karatunsa amma yaqi.
Shekaru uku suka shude a sannan Audu nada shekaru Ashirin a duniya ya zama cikakken saurayi ta kowanne fanni, neman Kudi kuwa se abinda ya qarun masa, tuni an aurar da Aisha Yakubu ma yakai kudin aure a can rigar su Dada ya samo budurwa Balaraba kyakykyawar bafilatana har an tsayar da rana watan Azumin tsofaffi wata uku kenan masu zuwa shirin Auran yasa Audu ya qara qaimi gurin neman kudi, a cikin gidansu suka yanki fili Yakubun ya gina daki ciki da rumfa saboda gurin yana da yalwar tsakar gida kowa dai yasan yanda akw gini a zamanin da, mutum daya na iya faro gida yaya su tasa duk suyita yankar fili suna tada dakuna a ciki suma.
Hada qarfi sukayi shida Audu sukayi ginin dan shima yana taba Dinki kuma da yake yazo da zamananci za'ace ba kamar yanda aka saba a karkarar ba se ya zamana yayi suna har daga maqwaftan qauyukansu ana kawo masa dinkin. Tsaf suka gina daki dukda ginin qasane amma anyi Sumunti da daben qasa wanda daga Kano Audu ya taho da simintin haka dakin Dada ma an daga mata shi anyi dabe da fulasta, dakinsu da suke ciki a da wanda yake Rabon yaran Goggo Fadi ta zugasu sun karbe wai Hashimu ne yake ajiyar Hatsi dan yanzu ya siyi gona tasa daban yana nomawa kuma a tasun ma haka zeyi bake bake idan an girbe yafi kowa kwasa wannan dalili yasa Audu ya gyara Asalin dakin Malam wanda suka mayar na ajiyar shigi shima yayi dabe da fulasta ya zama gurin saukar sa idan yazo, da ana aikin ma so yayi da ayi katanga a raba gidan tunda har Bandaki sukayi dan Asalin na gidan a barayin Goggo Fadi yake sunyi wani tun rashin lafiyar da Dada tayi bayan rasuwar Malam akayi mata bandaki daga kusan dakunan ta yanzun ma kuma anyi a gefen dakunan Yakubu wanda Audu yace za'a dan kewaye masa bangaren saboda sirri.
Ya koma Kano da niyar se bikin Yakubu ya rage sati biyu ze dawo kafin nan ya sake roro abinda za'ayi hidimar biki. Da akwai Malam Mudan dan Bechi ne amma yana yawan shiga Kano dan baya rufa wata biyu beje ba ta hannunsa Audu yakeyin aike ko su aika masa daga nan.
Wata sabuwa ce ta bullo daga bangaren Bara'atu yarinyar da Audu yake mutuwar so yake kuma burin aure, tun dama dai Babanta ya matsanta matuqa akan ta fidda miji, duk sa'anninta an musu aure har sun fara haihuwa kullum ta Allah se yayi wannan mitar amma Inna tayita danneshi saboda ita tana son Bara'atun da Audu to wannan karon yace ya gaji duk danginsu babu yarinyar data taba shekara goma sha Shida a gida se a kanta kuma bawai bata da masoya ba dan haka seji kawai Inna Hajara tayi ya karbi kudin auran Bara'atun da saka rana wata uku kusan lokaci daya ze kama dana Yakubu kenan.
Bara'atu tasha kuka hankalinta ya tashi batayi qasa a guiwa ba tayi tattaki ta samu Yakubu dukda yar kunya da suke a matsayinsa na yayan saurayinta haka ta ringa masa kuka akan yaje ya gayawa Audu karya bari a aura mata wani ba shiba, yana komawa gida kuwa ya sanarwa da Dada tace yayi shiri ya taho Birni dan daman tasan za'ayi haka, duk sanda Audun yaje seta masa zancen ya kamata yasan me suke ciki da Bara'atu se yace mata ba yanzu ba yana so abubuwa su qara daidaitar masa akwai shirye shiryen da yakeyi.
Dole Yakubu yayi tattaki ya tafi Kano wanda rabon shi da zuwa tun hutun makaranta wanda daga shi be sake dawowa ba shekaru hudu kenan. Yakubu Kano be zarce ko ina ba se Tsohuwar makarantar Allonsu wato makarantar Gwani Musa dan yasan Audu bashi da wani masauki se can, sedai yayi rashin sa'a Malam ya sanar masa tuni Audu ya bar nan, ya kan dai kawo musu ziyara lokaci lokaci dan ba'afi sati bama yazo kuma Almajirai suna ganinsa a Kasuwar bakin Asibiti idan sunje yawo yace musu yanzu a Goron dutse yake zaune bedai san takamaiman wani guri a can din ba. Yana zaune a bakin Masallaci yana jira ko Allah ze kawo daya daga cikin yaran da sukace sun san inda yake zama a Kasuwa su rakashi sega Hayatu, yaron gidan da Audu ya yiwa aiki wanda Babansu ya kaisu makarantar Boko a lokacin.
Cikin mamakin ganin juna suka gaisa yace suje gida a can yaci Abinci yanata kallon Hayatun daya zama kalar yan gayu da gani ya fara jiquwa a Boko.
"Tunda ka tafi makarantar kwana shikenab bamu sake haduwa ba shekaru kusan takwas kenan amma banji dadi da Audu yace mun ka bar Boko ba, kaga ni yanzu haka ina shekarar qarshe a Jami'ar ABU zaria ina karantar Engineering da ace ka cigaba kaima yanzun ko baka gama ba kana kan hanya" Hayatun ya fada. Yakubu yayi murmushi kawai amma bece komai ba, duk wanda ze so masa da yayi Boko a bayan kansa ne dan mafarkinsa ne ya zama Alqali tun besan me hakan yake nufi ba. Ganin bazeyi magana ba yasa Hayatu cewa ya tashi suje ya kaishi inda Audun yake dan shi suna haduwa sosai har inda ya kama hayar shago yake zaune a can Goron dutsen ya sani.
A kasuwa suka samu Audu yamma tayi anata hada hadar kasuwa dan a sannan ma ake cin kasuwar sosai, kayan yaji yake siyarwa a sannan da sauran kayan qamshi zuwan Yakubu tasa dole ya tattara komai suka tafi masauki. Seda sukayi sallar Magriba da isha, ya rasa ma me ze ajiyewa Yakubun, ya kwaso Wasu yadika dinkakku kala biyu kowanne saiti uku a ajiye masa sannan ya sake dakko Shadda dinkin babbar riga shima guda biyu ya ajiye yana cewa
"Na Baballiya ne ba'a gama ba, daman Juma'ar nan nake cewa idan Malam Mudan ya shigo zan hada masa yayo mun gaba dasu kar kaya suyi mun yawa idan na tashi tahowa"
"Yanzu dai duk ka ajiye wadannan ka saurari maganar da nazo maka da ita" Yakubu ya fada yaba tattare kayan gefe, Audu ya zauna yana kallonsa se a sannan ma ya lura da cewar Yakubun bashida walwala dukda dai shi daman bame hayaniya bane sosai. A taqaice Yakubu ya bashi Labarin daya gigitashi jin cewar an sakawa Bara'atu rana da wani dan uwanta ya shiga share zuba dukda qofar Shagon a bude take ga iska na busowa amma Audu zufa yakeyi kansa ya shiga sarawa jin ze rasa Bara'atunsa macen daya gama kwallafa duk wani buri na duniya akanta. Shikadai yasan irin tanadin da yakeyi akan auransu shine yanzu Babanta zece ya bawa wani ita.
"Shiyasa kullum Dada take maka magana akan kasan me kake ciki saboda gudun haka, ban dama Inna Hajara tana tataka ai kasan tuni Bara'atu ta dade a daki Bilki da suke sa'anni kana gani da ciki yana tsaya mata ai tayi yaya biyu ko uku yanzu tunda dai ga Aisha nan da ciki Auran bana se ita kake so tayita zama har se sanda ka gama shirinka duk sa'annin ta sunyi Aure har an fara zundenta a gari " Yakubu ya fada. Audu dai bece masa komai ba haka suka kwanta amma fa be iya bacci ba, cikin daren ya hada yar jakarshi, Asubar fari suka dauki hanya dan yace baze tsaya ganganci ba dole yaje a san me ake ciki amma da ransa baze bari wani ya auri Bara'atu ba.
Bayan dogon tirka tirka da yayyensu daga qarshe suka yarda zasuje tambaya masa Auran Bara'atun, sunje da fari Babanta yaso yayi gardama akan shi ya rigada ya amshi maganar wani ya basu haquri suka taho gida Hashimu har yana Allashi qara ai gara haka, seya koma can Birnin da ya liqe yagani idan ze samu macen da zata aure shi babu wanda yasan saga inda yake kujifa. Kwana biyu tsakani Audu na kwance yana jinya tunda yaji cewar baza'a bashi Bara'atu ba sega dan aike daga gidansu akan Babanta yace ya turo yau a daura musu Aure ashe wai Rijiya ta durfafa dagaske zata fada idan ba'a fasa auranta da wancan ba, harta tsoma qafa daya babanta yaga dai dagaske bata hayyacinta shine yace ya janye amma fa sedai Audu ya turo yau a daura Aure dan muddin aka kai ranar daya saka da wancan tofa sedai ta mutu shine Innarya ta tashi Yayanta ta aikoshi, Audu najin batun ya miqe beyi wata wata ba ya kama hanyar Gona inda su Yakubu suke can suna gyaran kunya kamar wani yaro ya zube yana basu labarin abinda akace.
Daga qarshe dai Yaya Baba da wasu Abokanan wasansu biyu ne suka sake zuwa dan Hashimu yace ba inda zeje, an samu Baban Bara'atu ya haqurq da zancen daura aure ranar aka tsaida magana akan rana daya dana Yakubu. Da wannan farin ciki Audu ya koma Kano, dukda ba haka yaso ba. So yayi ace se yayi gida a Kano sannan zeyi aure dan biki yake so yayi irin wanda akeyi A Kano yayiwa Bara'atu lefw na yargata wanda ze zama abin tarihi a garinsu harda kewaye, amma yanzun ma bata baci ba, zeci gaba da qoqari kuma ko ba yanzu ba seya biya bashin duk abinda ya qudurci yi mata. A haka kwanakin Biki sukazo, a zatonsa za'a daura aurene kawai tunda kowa yasan bashida Mahalli yayi qoqari ya siyowa Bara'atu kayayyakin fitar Biki daga Kano aka dinko harda takalma da mayafai kala hudu yayi mata na yan birni. Ana saura kwana hudu daurin Aure ya tafi Bechi bayan yayi sallama da Abokanasa na kasuwa dana unguwa dukya shaida musu zeyi aure, amma biki ba yanzu ba suka hada masa gudummawa kuwa sosai har seda yayi mamaki, koda yake shidin ba daga baya ba gaskiya bashida rowa ko kadan, haka Biki, suna, ta'aziyya sedai idan beji ba suma duk sun masa Alqawarin idan biki ya tashi zasuje tunda yanzu abin yazo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 32