An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MATAR MUTUM BOOK 1
LABARI/RUBUTAWA
MARYAM FAROUK (UMMU-MAHIR)
Arewabooks@Maryamfarouk01
Wattpad@MaryamahMrsAm
Telegram @08142548705
Ko a tuntubeni a WhatsApp kan 07061838488
Littafin Matar Mutum na kudi ne, ki biya 500 ki karanta cikin salama
0709290797
Access bank
Maryam farouk Umar
NAGODE
Page 1
"Wallahi Allah shine shaidata bani da masaniya akan yanda akayi kudin nan suka bata. Kowa a nan ya gani ga lissafi nan na duk abinda ya shigo kuma ya fita saga duka companies dinmu tun farkon shekara zuwa yanzu. Idan har duka lissafin da accountants dinmu suka kawo daidai ne tayaya za'ayi ace yanzu an sake lissafi an rasa wasu kudade? Nidai ban ci ba sedai a sake lissafi tun daga qasa ta yuwu a nan aka samu kuskuren lissafi" AMINU BECHI ya fada cikin tsananin tashin hankali. Sati biyu kenan da al'amura suka rikice a BECHI GROUP OF COMPANY lokacin lissafin shekara yayi bayan daya gama hada komai a matsayinsa na AG lissafi yasha banban da abinda aka bashi a rubuce da kuma tsurar kudi da suke a qasa inda aka samu rarar naira na gugan naira har Miliyan dubu biyu da dari biyar (2.5Billion) wadda bayan bashi damar yayi bincike da MD da kuma Chairman sukayi yauce ranar da aka taru duk wani daya isa a company domin jin ta yanda akayi aka haihu a ragaya.
Alhaji ZAKARIYYAH BECHI dake ta jujjuyawa a kujerarsa yana wani miskilin murmushi da babu wanda ya tantance kona menene ya kalle shi yace
"To Aminu kaida kanka kace dukka lissafin da aka gabatar maka daidai suke kuma baka karba ka saka hannu har seka bincika komai ka tabbatar da haka yake. Sannan a iya saninmu ku biyu kuke da access da central account dinmu dakai da Chairman duk wani wanda ze shigar ko fitar da kudi bayan ku biyun seya samu approval a gurinku to tayaya kake zaton zamu yarda idan kudi ya bata kuma kace mana bakada masaniya akai kenan Chairman ne da kanshi ya kwashi kudaden ko kuma me kake nufi?"
Aminu ya kalli Chairman din da tun zamansu bece komai ba ya tallabe haba da hannaye biyu yana bin duk wani da yayi magana a cikin su da kallo, Dattijo ne da a qalla zeyi shekaru 70 zuwa sama, dukda a zaune yake amma kana kallonsa zaka san Zabgegen mutum ne Jindadin rayuwa yasa har yanzun yake da sauran kwarinsa. Aminu ya hadiye yawu muqut saboda yanayin fuskar Chairman daya gani, bashi da yawan fara'a daman amma kuma yanayinsa na yau ya banbanta da kullum kana gani kasan zuciyarsa a kusa take koda yake ai dole, batun kudi akeyi fa, kudin daya qare rayuwarsa yana nemansu ya tara ace lokaci daya wasu su ringayi masa zari daidai dole hankalinsa ya tashi.
Seda ya daidaita nutsuwarsa kafin ya kalli MD dake jiran jin ta bakinsa yace
"Nidai na gama magana, ban ci kudin nan ba ban kuma san wanda ya dauke su ba. Amma dai kamar yanda nace kowanne gida (sector) su sake turo mana da lissafinsu na shekara a qaramun lokaci zan sake bin komai daki daki zan zauna da duka Bank Managers dinmu in Allah ya yarda za'a gano duk ma inda kudin suka shiga" ya qarasa muryarsa na rawa kuma cike da roqo da yaqinin Alhajin ya yarda dashi ya bashi wannan damar. Idan ya rasa besab ina ze dosa ba, abu biyu ne dole daya ya faru, dukda kasancewar Dan Chairman na cikinsa a sabgar Company basa kawo wannan relation din, ya sani kodai yayi Aman kudaden nan tas Miliyan dubu biyu da dari biyar wanda ko an siyar dashi da matarsa da yayansa da abinda ya mallaka baza'a hada wannan kudi ba abu na biyu kuma in wancan be samu ba yasan garqameshi za'a yi a prison still kuma A siyar da duk abinda ya mallaka Company ya rage Asara maganar aikin sa daman tun ranar da kudin sukayi batan dabo ya rubuta resignation letter ya ajiye dan ko be bari ba korar sa za'ayi.
"Maganar wani lokaci ko a sake bincike duk bata taso ba dan a tsayin faruwar abun zuwa yanzu da da wani abu da zakiyi tuni kayishi, just admit it Aminu kai kaci kudaden nan ka dawo dasu baki alaikum base magana tayi tsayi ba" NAZIRU BECHI ya fada yana wani zazzare masa ido
"Nima dai abinda na gani kenan, idan kuma yayi taurin kai Maigirma Chairman ina ganin a barshi da Legal department suyi aikinsu nasan su zasu sna ta yanda zasu tirsasashi yayi aman kudin ko kuma su miqashi inda ya dace" Alhaji Zakariyya ya qarasa miyar gishiri, cikin Aminu ya kada, ya ringa raba ido tsakanin Alhaji BABANGIDA BECHI da kuma YAKUBU BECHI da yake matsayin mataimakinsa AAG wanda tun fara taqaddamar kamar ma baya gurin wayarsa yake dannawa kunnensa saqale da Bluetooth tabbacin ba jinsu yakeyi ba hakan yasa ya tsayar da idonsa kan Alhaji Babangida cike da roqon ya saka baki amma seyaga ya saukar da kansa qasa bece komai ba.
Dakin ya sake daukan shiru na wani lokaci kafin cikin murya me cike da Izza irin ta wanda suka ci suka tada kai Chairman, Alhaji AUDU BECHI ya fara magana yana cewa
"Duk naji bayanan ku kuma na duba takaddun da aka rigada aka gabatar mun tuntuni. Account general, ina so daga yanzu zuwa qarfe biyu ka gabatar da takaddar barin aikinka da kanka saboda idan muka koreka zamu bata maka career be zama lallai ka sake samun aiki a wani gurin ba, kudi kuma duk wanda ya dauka yaje dan kansa" yana gama fadar haka ya tsuke bakinsa yana kallonsu daidai.
Aminu ya sauke ajiyar zuciya me nauyi tamkar wanda ya hadiyi kunama, jiki da bakinsa suna rawa ya zame daga kan kujerarsa ya durqushe yana cewa
"Nagode Alhaji, Allah ya qara girma nagode nagode".
Naziru da Zakariyya wanda farkon maganar Alhaji yayi musu dadi, sun dana kuma ta kama suka kalli juna tareda yin signa akan idon Alhaji Babangida dake lura da duk wani motsinsu ya girgiza kai kawai. Bazeyi kaffara ba idan ya rantse cewar shirinsu ne saboda sun nuna baqin ciki qarara da kujerar ta Aminu amma baze saka baki a cikin maganar na domin rayuwar gidansu rayuwa ce irin ta kowa tasa ta fishsheshi shida Yan dakinsu. Tunda Aminu ya samu wannan matsayi qarara mutane da yawa a gidan suka nuna qyashi da hassada bayan rasuwar Mr Adekunle Balogun wanda shine AG na BECHI GROUP din tun kafuwarsa Alhajin bisa shawarar Legal Department da sukaga cancantar Aminun aka dorashi, shekaru biyu kenan tun kuma hawansa abubuwan da ba'a saba dasu ba suke faruwa amma wannan al'amari shine mafi girma wanda baze yuwu a dauke kai ba.
Cikin zafin ran dake nuna hassada qarara Alhaji Zakariyya yace
"Ranka ya dade (haka suke kiransa muddin sabgar data shafi aiki ce) naji kace yayi resigning kawai banji maganar dawo da kudi ba ko wani hukunci da za'a dauka akansa?"
"Da alama kunnenka ya soma samun matsala ko? To ka tambayi na kusa da kai su maimaita maka abinda nace, maganar wanda ze maye gurbinsa for now Yakub should take over kafin mu sake zama muga abinda ya dace da ayi ina ganin mun gama abinda ya taramu you can all dismiss" Alhajin ya fada ba tareda ya kalleshi ba. Alhaji Zakariyya ya hadiye yawun takaici ta wani bangare kuma yaji dadin cewar YAKUB BECHI ne zeyi taking over dukda sunso ace anyi confirming nasa ne take as the newa AG amma hakan ma nasarace sunyi nasu Hajiya zata qarasa aikin a gida. Shiya fara miqewa ya kalli Aminu dake harhada takaddun gabansa cikin izgili yace
"Dama anyi gadon farar qafa dole a tsammaci abinda yafi wannan, Allah dai ya sauwaqa ya kuma tsayar iya kanku kar a bata mana sauran iri da halin bera" yana gama fadar hakan ya juya ya fice daga gurin dukkan su kuma sunji abinda ya fada, Da daddaya suka ringa ficewa daga conference room din ya rage Alhaji Audu, Alhaji Abdullahi wanda yake heading bangaren Siminti kuma dane a gurin Alhajin Audun ma'ana dan Yayansa ne da suka hada uba se Mustapha Manzo, shugaban Legal department na rukunin kamfanunuwan Bechi. Alhaji Abdullahi ya kalli Alhaji Audu dayayi shiru da alama yayi nisa a tunani, cikin ladabin da yake masa tun usulan yace
"Gaskiya Baba a iya fahimtata da kuma binciken da nayi bana zargin cewar Aminu yana da saka hannu a cikin batan kudaden nan"
"Nima dai abinda zan fada kenan, nayi amfani da duk wasu measures da muke using gurin gano me laifi banga wasu alamu na rashin gaskiya a tattare dashi ba. Amma abinda yake bani mamaki shine tabbas kudi sun bata amma babu wata alama da za'a iya tracing a ga inda kudin suka tafi tunda ba transfer akayi ba and we don't deal with huge cash here ballantana ace cash aka debe su. Ni dai what I'm thinking is that kudin nan dama babu su, lissafin bogi aka bashi kawai kuma ina ganin matsalar badaga ko ina aka samota ba se daga Oil Sector. Tunda Naziru ya fara heading gurin nan ake samun runton lissafi Mr Obasaki yana yawan kawo mun qorafin idanna sanar maka Alhaji baka daukan wani mataki na sosai and i don't know your reasons for that. Ire iren wadannan abubuwan ya saka mutane da yawa basa mixing Family with business saboda abinda bare zeyi maka ka dauki mataki idan Jininka ne dole ka daga amsa qafa, amma maganar gaskiya idan ana so a ga daidai se an gyara saboda kowa yasan can ne bangaren dayafi kowanne kawo profit idan aka cigaba da irin wannan tafiyar ina tsoron kar wata rana a wayi gari babu uwar kudi ma balle riba" Mustapha Manzo ya fada, yanda yake maganar duk wanda ya saurareshi dakyau ze fahimci jirwaye yakeyiwa Alhajin me kamar wanka. Kai tsaye baya so ya dora alhakin batan kudin akan Naziru tunda bashi da hujja amma yana so Alhajin ya bincika da kansa ya tabbatar.
Alhaji dake sauraronsu a zahiri yana gyada kai amma a badini kanzil bazece yaji daga abinda suke ta babatu akai ba maganar farar qafa da Zakariyya yayi ce take masa yawo a zuciya wasu shudaddun Al'amura da suka faru a baya suka shiga dawo masa kamar auransa da Mahaifiyar Aminun, abubuwan da suka gidana a tsakani har zuwa rabuwarsu.
"Nidai Baba idan ze yuwu a janye maganar korar Aminu daga company nan, za'a iya suspending nasa na wani lokaci amma Yaron yana da matuqar qoqari kuma ya dace da gurbin da aka sakashi akai" Alhaji Abdullahi ya sakeyin magana se sannan Alhaji Audu ya dubeshi, kallon dansa na cikinsa yakeyiwa Abdullahin saboda shi ya fara riqewa kafin ya samu nasa yayan, haka kuma yana yi masa biyayyar da qalilan daga cikin wadanda ya haifa a cikinsa ne sukeyi masa irinta. Cike da Izzar data zame masa jiki yace
"My decision is final, idan shi Barrister Manzo be sani ba, kai kasan Hadiza ka kuma san dalilin rabuwata da ita dan haka bazan yi ganganci a matsayin kuskure ba" daga haka ya miqe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa datasha wani aiki irin na sarakai.
A baya suka biyo shi duk rayukansu babu dadi har suka shiga Elevator Barrister Manzo yana so ya sake magana amma Alhaji Abdullahi ya hanashi. Tun kafin qofar Elevator ta gama budewa gaba daya suke jin hayaniya, Reception din cike da ma'aikata da sukayi cirko cirko se muryar Naziru dake tashi kamar ana yaqi. Cikin karadi da kwaroroto irin na Mahaifiyarsa yake cewa
"Wlh Babu inda zaka je se ka bude jakar nan mun cajeta, hauka ma akeyi kenan. A kamaka dumu dumu da laifin sata a koreka daga aiki sannan ka lullubo jaka zaka fita bamu duba munga meye a ciki ba salon ka kwashi sirrikan mu ka fitar ka saidawa Yan hamayya ko to baka isa ba" ya fada yana kiciniyar fincikar Bag pack din Aminu daya saka duk wani abu nasa me muhimmaci da yake a tsohon office dinsa tunda an sallameshi daga gurin.
Alh Abdullahi da Barr Manzo suka nufesu da sauri jin abinda yake faruwa, Alhaji Audu kuwa ko a jikinsa ya nufi qofar da zata fitar dashi daga building din. Daf da ze fita kunnuwansa suka jiyo masa wasu mata biyu ma'aikata dake saga gefe suna kallo daya tana cewa
"Nidai Safna da arziqi irin na wadannan mutanen gara talauchi da kwanciyar hankali, su fa basu san abin kunya ba, wlh Chairman dai bewa kansa tanadi na kwarai ba Allah ya baka arziqin zuria amma ka tarwatsasu babu soyayya bare shaquwa a tsakaninsu kowa so yake yaga kasawar dan uwansa yanzu idan baka sani ba wlh ba zaka taba yarda MD Oil and Gas da AG ubansu daya ba dan ko barene beci yayi masa irin wannan tozarcin ba ballantana jininsa."
Dayar tace
"Uhm kedai bari Halisa kinsan su CMD yayan Mowa ne shiyasa suke sharafinsu, bandama AG da MD Agric wa kika gani a yayan nasa yana aiki a nan se yayan yan uwa dana abokanai ragowar kina kallo duk wanda yazo baya zama yake neman hanyar da zata bulle dashi to ko nice wlh ba zan zauna ba Arziqin ubana amma a fifita wasu su zasu amfana ai dai idan Chairman ya sheqa be gyara kan gidansa ba to kuwa kwanciyarsa qalilan ce a kabari dan kullum se an tashe shi yaga tsiyar daya bari a duniya da ransa ma ji yanda suke akan dukiyar inaga an raba gado wani be samu yanda yake tsammani ba" suka tafa hannu suna cewa
"Allah dai ya kyauta.
Alhaji Audu ya daga qafa dakyar ya qarasa ficewa daga gurin bayan ya gama sauraron hirar tasu. Tunanin maganganunsu yakeyi a ransa, ba yau aka fara fada ba ko ya faraji wasu su fada masa akan idonsa wasu a boye suti gulma kamar dai wadannan kuma tun abin baya damunsa yana daukar sa ba a komai ba har ta kawo matsayin da shida kansa ya hangi illar da yayiwa kansa da rayuwar Ahalinsa gaba daya. A lokacin daya dora tubalin ginin sam be hango rashin ingancinsa ba, be hasaso ranar da ze iya ruftawa dashi ba seda lokaci ya qure masa akazo matakin da ko yana so ya gyara mawuyaci ne hakan ta yuwu.
A yanzu da yake cikin Shekara ta Saba'in da uku a duniya yaci ace yana kwance a gida yana hutawa da kuma shirye shiryen tarar da ubangijinsa ta hanyar yawaita tuba da ayyukan Alkhairi amma a maimakon haka tashin hankulan da be san suna wanzuwa ba a baya yanzu suke riskarshi. Bashida kwanciyar hankali a gidansa, tsakanin Matansa koda ace ba dukka kullum ta Allah idan ba safiya ba rana idan ba rana ba Dare se Binta ta tayar da tashin hankalin da ze kwana ya wuni cikin quncin zuciya. Ubangiji yayi masa ni'ima ta Yaya Maza zarata wadanda ya dora buruka da yawa a kansu sedai be gino rayuwar ta sigar da baze cimma mafarkin sa ba ya shuka barna yanzun kuma yana girbinta ne, yayan daya kwallafa rai akan zasu taimake shi a lokacin da qarfinsa ya tashi qarewa sedai sam hakan ta gagara a maimakon nutsuwa a kullum tukuicin tashin hankali yake samu daga garesu wanda shine silar komai ya sani ba laifinsu bane laifukansa na bayane suke farautarsa a yanzun.
Yayi zurfi cikin tunani har besan sun isa gida ba seda Driver sa ya bude masa murfin qofar bangaren da yake. Ya fita ya tsaya yana qarewa Tamfatsetsiyar harabar gidansa kallo ga motoci nan birjik kamar a gurin saida su. Gida ne daya amsa sunan gida wanda ko baka shiga ciki ba zaka iya wassafa tsaruwarsa, Get din gidan me kama da qofar Gari kansa abin kallo ne ga wasu shuke shuke da akayi a harabar na dogaye da gajerun bishiyoyi da suka qara qawata gurin se manya manyan Street Light jere da Zanqaleliyar Katangar gidan kamar ta mutanen Niger kana gani base an fada maka ba kasan idan dare yayi haske har yawa yakeyiwa Harabar. Gini ne Duplex a tsakiya yana kallo ka idan ka shigo nan ne kuma turakar Alhajin dakuna uku ne a sama da falo a qasan kuma kantamemen falo ne da aka zubawa kujeru saiti uku da bandakin baqi a gefe se kuma wani qarami Daga can gefen wanda fadar tsaruwarsa bata baki ne a nan Alhajin yake saukar baqinsa na Mutunchi Babban Falon kuma na Meeting ne tsaf yake dauke jama'ar gidan duk yawansu.
A cikin harabar akwai qofofi biyu dama da Hagu, ta hagun ce zata kaika cikin gida inda bangaren Matansa yake ta Dama kuma ta kasu biyu, daya ta inda dakunan samarin gidan yake ne dayar kuma dakunan masu aiki maza. daidai qofar da zata shiga dakai sashin samarin gidan ya hango Faisal yana tahowa da wasu kwaftara kwaftaran takalma a hannu irin na taqadiran Black Americans din nan yana waigen bayansa, baya tsammanin ma ya lura da tsayuwarsa ya giftashi yana cewa
"Dan kutumar uba da ka biyo ni mana da wallahi sena farke ka a gidan nan" ya fice abunsa ya bar Alhaji da zuciyarsa take tsalle da lugude, dawa Faisal yake fada da har yake furta wadannan munanan kalamai wai ze farke shi kamar wani Dan Daba?
Salim daya fito daga qofar shima kamar an harboshi yana kwalawa Issa daya daga cikin Buzayen da suke gadin gidan kira ya taho da gudu ya durqusa cikin maganarsa ta buzaye yace
"Gani Alhajji me kuke da buqata?"
"Ina Faisal?" Ya fada a fusace, Issa ya daga hannaye sama yana cewa
"Ya fita Alhajji yanzun ya fice ta qofa"
"Zonan Salim" Alhaji Audu ya fada ganin shima be lura da tsayuwarsa a gurin ba. Ya wani ja iska kafin ya matsa inda Alhajin yake, kadan ya rusuna yace
"Barka da Rana Alhaji"
"Meya hadaku?" Ya tambayeshi ba tareda ya amsa gaisuwar tasa ba wadda idanda ace a shekarun bayane ma tabbas seya kife shi da mari kan wannan gaisuwar rainin daya masa.
Cikin qunquni Salim din yace
"Takalma na ya diba kuma na rantse da Allah sena masa dukan mutuwa idan muka hadu" babu tsoro ko shakka a muryarsa ya fada. Alhaji ya qara tsumewa dukda cewar zuciyarsa tsinkewa take ta ciki akan al'amuran dake wakana dashi yace
"Me yasa kuke haka? Saboda dan uwanka ya dauki takalminka shine zaka fito kana daga murya kuna zubar da mutunchinku a gaban masu aiki kamar wanda ya daukan maka wani abu me muhimmanci? Bana son haka kar kuma na sake ji, shi ya wuce yana zage zage kai kana cewa zaka masa dukan mutuwa me kukeyi hakan"
Salim ya daga kai ya kalli Alhajin da wani irin duba kamar wani sa'an sa yace
"Shi daya wuce ka tsayar dashi kaji ba'asin zage zagen da yakeyi?"
"Ban tsayar dashi ba saboda.."
"Base ka fada komai ba saboda shi dan so ne basa laifi, nida ya daukarwa abu nayi magana nine mara gaskiya to se a biyani kudin takalmina idan ba haka ba kuma na rantse da Allah sena kwantar da yaro" Salim ya datse Alhajin babu dar bare shakka tsabar mamaki kallonaa kawai Alhajin ya ringayi ya kasa cewa komai. Shi Audu ne yayi lalacewar da Kalan Hanji a cikin yayansa ze ringa mayar masa da magana?
"You are very stupid Salim Alhajin kake gayawa wannan maganar saboda baka da hankali?" Ahmad da shigowarsa kenan ya tarar dasu ya fada, Salim ya kada qeyarsa ya juya yana cewa
"Ai gaskiya na fada Yah Ahmad da ace ni na daukarwa Faisal din abu da yanzu an hada Family meeting ance mun barawo shi kuwa tunda dan gaban goshi ne kaga ni ya bawa laifin ina masa hayaniya a gida a biyani abu na kawai a zauna lafiya" daga haka ya barsu tsaye kamar sokaye saboda mamaki.
"Kayi haquri Alhaji gaba dayansu se na bata musu zan zauna dasu" Ahmad ya fada cikin girmamawa, Alhaji ya jinjina kai irin na wanda Idea ta qarewa kafin ya juya ya shige Falonsa maganganun daya sha yau suka masa rufdugu a kwakwalwa tabbas makomar gidansa tana cikin garari, idan kuma beyiwa tukfar hanci ba za'a samu gagarumar matsala.
Sama ya haye dakinsa ya zauna bakin gado bayan daya rage babbar rigar jikinsa ya qara gudun Ac, tunanin baya ya shigayi, so yake ya gano bakin zare ta inda ya kuskure ko Allah zesa ya samo hanyar gyarawa. Kamar Film ya shiga hasko rayuwarsa tun daga tushe.
Page 2
ABDULWAHAB TIJJANI Shine Asalin sunansa, AUDU da mutane da suka sanshi dashi yasa ake daukar cewa ABDULLAHI shine sunansa kamar yanda duk inda kaji Audu a gurin bahaushe tunanin na karkata da cewar Abdullahi ne sedai shi Alhaji Audu ya samu sunan ne ta dalilin wata kakarsu tun suna yara ya tashi da bala'in son kudi, da sallah idan ya samu yan silallarsa na barka da sallah ya ringa yawo dasu kenan a aljihu yana karkadawa suna qara idan ka tambayeshi menene se yace
"Kudina ne tara su zanyi se sunyi yawa sosai" shikenan take kiransa da Audu kudi tun befi shekara biyar a duniya ba kuma sunan ya bishi aka manta da Abdulwahab sedai Audun kawai har girmansa kuma wannan dalili ya saka koda Yaransa suka Shiga makaranta Malamai sukayi musu register da ABDULLAHI TIJJANI BECHI a cewarsu Audu ba suna bane.
Alhaji Audu haifaffen wani qauyene da ake kira Bechi cikin qaramar hukumar Kumbotson Jahar Kano. A yanda labari ya iske su kakansu daya haifi Mahaifinsu Tijjani wato Malam Lawan shine me garin Bechi na farko ance seda suka shekara Talatin da matarsa Asabe kafin Allah ya basu haihuwar Tijjani hakan yasa suka dauki son duniya suka dora masa sedai Allah beyi zasuyi doguwar rayuwa tare ba domin kuwa shekarun Tijjani
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 32