kasa komai gashi har lokacin jinin bai tsaya ba amman dai ba ya zuba sosai.
Da wuri Saude ta zo ta yi mini aikace aikace ta yi girki, sai wajen ukun rana na ba ta kuɗin mota ta koma gida, sukuku sukuku dai na yini Hauwa ma ta kira ni wai jiya ba ta san tafiya na ba, na ce ban jin daɗi ne, ta yi min sannu har ta na cewa ko zan leƙo can gidan Haliman? Na ce gaskiya a'a saboda ba na jin ƙarfin jikina ta yi min sannu sannan muka yi sallama.
Ni fa ko lafiyata ƙalau ba zan koma ba ko Rahila da ta haihu sau ɗaya na je sai ana gobe suna da ranar suna na koma.
Saboda yanayina tun ranar ban ƙara fita ba ina gida ina shirin tafiya Zariya. Na gama haɗa duka takardun gwaje gwajen da aka yi min a asibitocin kano da tests da sauransu waje ɗaya saboda kar na manta. Na ma kira Anty Khaleesat na faɗa mata ina nan zuwa, Yaya Hamzan dai na kira shi ban samu ba.
Ranar asabar da yamma muka je gidanmu tare da Yara na sanar da Gwaggo tafiyata Zariya ta ce Allah ya sa a dace. Na jira har Alhajinmu ya dawo shima na faɗa masa.
"Allah ya sa ki je a sa'a. Allah ya sa a samu abin da ake nema."
Na amsa masa da Amin Amin, mun daɗe a gidan sai wajen goman dare Yallaɓai ya zo ya ɗauke mu, shima baya samun zama a Rano ya ke yini, saboda ya samu kwangilan gina wannan gidan biredin, gabaɗaya ya kwashe kuɗin hannunsa ya zura a ciki.
Sai da muka dawo gida mun yi shirin kwanciya na ji suna waya da Uncle Abba, na ji kuma ya na faɗin bashi da kuɗi.
Sai da suka gama waya, ina gaban madubi ina saka Humra, yau ni amarya ce domin jinin ya ɗauke min yau da safe,shi kuma ya na zaune gefen gado daga shi sai ƙaramin wando.
"Wai an ya za ka samu rakani asibitin nan kuwa?
Na faɗa ina kallon bayansa ta cikin madubi, bai juyo ba na ji ya ce"Ina tunanin haka nima, saboda aikin nan kuma kin ga ana buƙata ta a wajen"
Sai da na gama fesa turaren na gyara gashina da na kasa kitso har yau, kuma na kasa wanke shi a gida na kuma kasa zuwa a sake wanke mini.
Gabansa na zagayo ina faɗin"In ba ka da lokaci ka bari gobe kawai na tafi, in na ga likitan zuwa jibi sai na dawo in sha Allahu."
Kallona ya yi kafin ya ijiye wayarsa a gefe, ya saka hannu ya jawo ni na zauna a saman cinyarsa ya zagaye hannayensa a kuguna muna kallon juna.
"Kin tabbatar da ba matsala in kika tafi ke kaɗai?
Ina yar dariya na ce"Haba! Kamar wata yarinya? Ba matsala Allah tunda aiki ne ya hana ka rakani."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce"Ga lambar Dr Fadil Abba ya turamin ya ce sun yi mgana in kika je asibitin shi za ki fara nema."
Sai na gyaɗa masa kaina gudun mantuwa sai ya ce na ɗauko wayata na kwashe lambar, tashi na yi na ɗauko ya faɗamin na saka na yi saving ina so na yi masa maganar kuɗi amman kuma sai na fasa na san Yusuf game da lafiyata in dai yana da shi ba abin da ba zai yi min ba, ni ina da kudi a hannuna 40k, na so na siya ma Halima turmi atamfa da rigan yaro amman sai na ga Yusuf ba shi da kuɗi ya saka a wannan aikin sai na dakata, in har bai ba ni da yawa ba sai na ɗauka na ƙara dashi.
A daran mun raba dare muna farantama juna rai.
Muna ƙamƙame juna, cikin shauƙi da kauna.
"I miss you Sadiya ta."
Mirmishi na yi ban yi magana ba. Shi ya ta shi ya fara yin wanka sannan ya tasheni nima na yi wankan Sannan muka dawo muka sake kwanciya sai asuba muka tashi, Saboda ina da tafiya a gaba na da wuri na tashi.
Lahadi ne yara suna gida, shima Yusuf din ya ce mini sai azahar zai tafi Rano. Ni na yi mana Breakfast muka karya gabaɗaya sannan na yi wanka na shirya Yallaɓai ya ce na tafi da wuri baya son na yi yammah a hanya..
Kaya kala biyu na haɗa a karamar akwatina Baby na ganin na haɗa kaya ta fara rigiman sai ta je, Babanta ne ya zauna ya na lallashinta.
Na kira wayar Saude ban samu ba sai na kira na Balaraba mamanta, na faɗa mata zan yi tafiya Saude ta zo da wuri ta gyara gida ta yi ma yara abinci sannan in ba damuwa ta kwana da su kafin na dawo duk da nasan Yallabai zai kula da su ga jidda amman gwara dai na barsu tare da Sauden tun da shi sai dare yake dawowa Balaraba ta yi min fatan dawowa lafiya tace Saude ta je islamiya in ta dawo za ta zo in sha Allahu.
Yallaɓai ya saka mini duka Report ɗina na asibitin da na ta zuwa a baya a cikin ƙaramar jakata ya turamin 30k a acct ɗina lokacin muna hanya shi da yara za su kaini tasha misalin sha ɗaya na safe.
"Na ga 30k Yallaɓaina. Ina godiya."
Duk na san kuɗin sun yi kaɗan amman ban iya masa ƙorafi ba, ba halina ba ne.
Ya na tuki su Jidda na bayan mota ya waiwaya yana kallona ina sanye da hijabi, na saka abaya da mayafi ya ce na cire na saka hijabi sai na sauya kaya zuwa atamfa doguwar riga.
"Ki yi hakuri Sadiya ba kuɗi a hannuna in akwai kuɗi a hannunki ki cika duk abin da kika kashe ki rubuta, in an biya mu zan biya ki duka kudaɗenki in sha Allahu."
"To."
Kawai na ce masa, domin na saba jin in aka biyamu zan biyaki duka kuɗinki kuma an sha biyan shi ɗin amman sai ya manta da ni in na yi mgana sai ya ce kuɗin sun ƙare na yi hakuri a gaba zai biyani.
Ba su bar tasha ba sai da motar mu ta tashi, sit ɗin mutum biyu Yallaɓai ya biya min kada na takura, sannan ya biya kuɗin mota muka rumgume juna ni da shi, yaran ma haka suna ɗaga min hannu ina ɗaga musu motar mu ta bar tashan, sai bayam mun tashi ina ga shima ya tuka motar zuwa gida.
Muna hanya ma na sake kiran Anty Khaleesat, tunda da safe ta kirani ta ce yaushe zan ta so, na ce mata zuwa sha ɗaya na rana lokacin da na ce mata mun taso Yaya Hamza na gida har ya karɓi wayar ya na faɗin" Na ɗauka Yallaɓan na ki ne zai kawo ki?
Ina dariya na ce"Haka ya so, amman ya fara wani aiki kuma ka san ana bukatarsa sai na ce kawai ya yi zamansa ni na je na dawo"
Sai ya ce ai shikenan Allah ya kawo mu lafiiya. Na amsa musu da Amin sannan muka yi sallama.
Kafin mu sauka Zariya ban san sau nawa Yallaɓai ya kirani ba, na sauka ma a kwangila Zariya ya sake kirana na ce yanzu zan samu Adaidaita zuwa anguwan da Gidan Yaya Hamza ya ke. Gra kusa da bankin Gt Bank in da yake aiki.
****
Ina zaune a falon gidan Yaya Hamza rashe rashe ina cin abinci shinkafa da miyar Naman rago da Anty Khalesat ta yi min, ita ta na zaune a saman kujera ta ba ma Amna nono muna hira sai ga kiran wayata da ke saman kujera a cikin jakata tun da na iso na watsar da su saman kujera ban bi ta kai ba.
Na iske Yaya Hamza a gida amman ban daɗe da zuwa ba ya fita ya ce wani abokin aikinsa mahaifinshi ya rasu za su je Ta'aziyya.
Khaleesat ta fi kusa da jakar ita ta matsa ta ɗauko jakar ta, bude ta ɗauko wayar.
"Waye?
" Wata wai Sameena Tafida Rano."
Mirmishi na saki kafin na ce Allah Sarki da hannuna na hagu na miƙa hannu na karɓi wayar.
"Wace ce? Ƙanwar Yallaɓai ce?
Sai na girgiza mata kai, kafin na ce"E, a'a. Ɗiyar marigayi Tafidan Rano ce."
Ɗaga kiran na yi da fara'arta kamar yadda muka saba mace ƙwara ɗaya da muke mutumci sosai daga gidan Marigayi Alhaji Yusuf Tafidan rano, duk cikin su da ita kaɗai na saba kuma na ke zumunci ko Gimbiya da muke da lambar juna ba ma waya iyaka ta dai in mun haɗu a gidan Nene ko Rano gaisuwan fatar baki ce.
"Matar Baba."
Haka ta faɗa daga bangarenta ina dariya na amsa mata mu ka gaisa da tambayan yara. Da ta ce min ta zo sunan Halima na gobe ba ta ganni ba an ce ina Zaria. Daman na san za ta zo tunda Halimar ƙawar ta ce.
"E. wallahi na zo gidan Yayana zan kwana. Gobe ina da ganin likita a asibitin Shika in sha Allahu."
"Lafiya kuwa? Ko ba lafiya ne?
Da sauri na ce"Lafiya ƙalau zan dai ga likita ne kawai. Kin shigo garin kenan?
Sai ta amsa min ina ma jin hayaniya, daga karshe ta ce yaushe zan dawo na ce mata gobe in sha Allahu sai ta ce za mu haɗu ita sai jibi za ta koma Rano.
Sai da muka yi sallama na ijiye wayar a gefena.
"Ban ga ne wata Sameena ba. "
"Da wuya ki santa. Rahila ce ta san ta, ɗiyar wannan aminin mahaifin su Yallaɓai? Wanda ya rike tafidan rano lokacin ya na raye, amman bayan ya rasu an ɗora ƙaninsa, ita wannan da muka yi wayar autan su ce Sameena, kin ga kamar ƙanwa take a wajen su Yallaɓai."
"Oh na gane su, lokacin haihuwan Baby na ga duk sun zo na ji ana cewa iyalan gidan marigayi Tafida ne."
Ina gyaɗa kai na ce" Su fa, ai Yallaɓai na ya zauna gidan sosai tun yana matashi, kuma uwargidan Marigayi ɗin Hajiyar Tafida ƙawar Nene ce tare suka yi yarinta ƙawaye ne sosai. Yadda Yallabai ya faɗa min a bikin Nene marigayi Tafida ya ga Hajiyar ya ce yana so har ta kai su ga aure suka tara zuru'a. "
"Allah Sarki.."
In ji Khaleesat, ni kuma ina cin abinci na ce" To ita wannan da muka yi waya ɗiyar Amaryansa ce, Hajiya Kaltume."
Ita dai Khaleesat da ba wani sanin su ta yi ba sai dai ta bi ni da Allah Sarki kawai. Sai da na ci na koshi sannan na shiga ɗakin da aka sauke ni na yi alwala na yi sallar azahar da la'asar sannan na kira Yallaɓai bai ɗauka ba sai na kira Saude ta ba ni su Jidda muka yi mgana.
Daga nan sai na kira Dr Fadil, shima bai ɗauka ba sai na ƙyaleshi, ina duba wayar sai na ga ashe ma Hauwa ta kirani sai na kirata daga baya.
Daman na san za ta ce ba ta ganni gidan Halima ba na ce mata ina Zariya ba da ni za a ci wannan sunan ba, sai ta yi min fatan dacewa muna ma waya Dr Fadil na kirana sai na katse nata na ɗaiuki nashi.
Mun gaisa ko da na faɗa masa sunana sai ya ce ai ya gane ni Abba ya tura masa lambata. Na faɗa maaa na shigo Zariya ina gidan Yayana sai ya ce gobe da safe ƙarfe goma zai shigo asibitin na tabbatar da na shigo a wannan lokacin sai na kira shi, da haka muka yi sallama.
Ba gaji saboda zaman mota, gado na haye ina jin kamar ba zan iya tashi ba. Khaleesat ta leƙo ni ta ganni kwance sai ta ce na huta kawai itama tana ciki tana gyara kaya ne.
Gidan Yaya Hamza flat ne daidai na zaman mutum ɗaya haya suke yi amman yana gina nashi. Yayansu biyu duka mata, tana goyon na biyun mai sunan Mama Ruƙayya Amna(Tasleem) ta na gidansu Jawahir ɗin ta je hutu.
Har na fara barci na ji kiran wayata na ɗauka cikin muryan gajiya, da barci.
Jin na isa lafiya ya sa Yallaɓai ya ce na huta sai mun yi magana anjuma.
Ban tashi ba sai gabda mangariba, na yi wanka na saka riga da wando, ni daman kaya irin atamfa damuna suke yi, plazo na saka da T.shirt.
Daman na ɗauro alwala ina shiryawa na tada sallar mangariba, tun ina sallar ake kiran wayata sai da na sallame na ga wai Ma'u ne.
Tsaki na ja na ƙi ɗauka kira biyu sannan ta ƙyaleni, amman da na kunna data sai na ga saƙon ta.
"Ban gan ki a gidan Halima ba. Ina fatan lafiya ko?
Daƙyar na iya ce mata lafiya lau, daga haka ban ƙara ba sanin da na yi gulma ce ai na san ta ji labarin na je Zariya, tunda Yallaɓai ya ce ya faɗa ma Anty Bahijja ba zan je sunan Halima ba zan je Zariya ganin likita kuma ina da tabbacin Ma'u ta ji labari.
Ni da kaina na kira Rahila a waya muka sha hira na ce mata ga ni a gidan Yaya Hamza.
" Kai Sadiya, ko ki jirani mu zo tare in na yi arba'in"
Kamar tana ganina na harareta kafin na ce"A'a sai dai na tsaya ki yi hamsin"
Sai ta kwashe da dariya, zolayata take yi tasan ai abin da ya kawo ni.
"In sha Allahu Sadiya za ki ƙara haihuwa da ikon Allah."
Kamar zan yi kuka na ce"To Amin. Amman kin ji daɗin ki Rahila. Da ba ki yi planning ba, ba ki haɗu da side effect ba gashi nan kina ta haihuwanki yayanki huɗu bayan ma kin yi ɓari sau ɗaya."
Rahila ta yi saurin cewa"Ki daina cewa haka ko ba wannan dalilin in Allah ya kaddaro fa, ki dai kawai ki ce ya zama sanadi, mu yi fatan kuma ya zo karshe."
Ganin na damu ta yi ta lallashina sannan muka yi sallama. Ina nan zaune har aka kira isha'i na tashi na yi salla.
Ban fito daga ɗakin ba sai da na ji muryan Yaya Hamza sannan na fita muka gaisa.
"Ke lafiya na gan ki wani iri?
Sai na ce masa bakomai, Khalesart ta ce"Bai wuce damuwanta na haihuwan nan"
Ya na zaune gefen matarsa ya ce"Mi ye to abin damuwa? Ba ga su Jidda ba, ke ba na son damuwan nan ba wani abu in ma ba ki ƙara haihuwa ba ko?
Shuru na yi masa ban yi magana ba, shi daman ɗan kai tsaye ne.
Kifin hausa ya siyo mana mai daɗi, sannan ga shi akwai wuta ana kwana chasa'in sai na zauna afalon Yaya Hamza bayan ya gama cin kifinsa ciki ya shiga ya bar mu muna kallo muna hira. Muma ɗina wajen goma muka yi sallama na shige ciki na yi shirin kwanciya sai da na kwanta sai na ɗau waya na kira Yallaɓai ya ce min yanzu ya shiga gida yara duk sun yi barci.
"Har Sauden??.
Sai ya amsa min da e, hira muka yi kaɗan tun da shima ya gaji na dai sanar dashi yadda muka yi da Dr Fadil. Ya ce na kwanta da wuri saboda na tashi akan lokaci, mun yi sallama tare da kalaman soyayya sannan na yi addu'ar barci na kwanta.
*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
09069067488.
08032773332.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿️7*
Tun da na kwanta ban farka ba sai da na ji kiran sallar asuba daga can masallacin da ke baya kaɗan da gidan Yaya Hamza.
Na tashi da ƙarfin jiki, sannan ina jin wani karsashi a tare da ni, ina idar da sallar asuba ina zaune ina azkar sai ga Khaleesat ta leƙo ni, bayan mun gaida juna da kwana ina tambayan Amna ta ce min ba ta tashi ba, ita ta saka min ruwan zafi a kittle ya na tafasa ta ce na juye na yi wanka.
"Yaya Hamza fa?
Sai ta ce min kar in damu dashi, akwai wani Kittle ɗin a Tiolet ɗin cikin ɗakin barcin su zai yi amfani dashi.
Ko kafin ƙarfe bakwai na safe na yi wanka na shirya, tunda goma Dr Fadil ya ce za mu haɗu a cikin asibitin akwai sauran lokaci, sai na zauna gefen gado na jawo wayata da niyyar in kira Yallaɓai.
Sai ma na ga ya kirani har sau biyu, ƙila lokacin ina wanka ne sai na kira shi, bai ɗauka ba sai da ta gama ringing ta katse sannan ya biyo bayan kiran nawa.
"Ina kwana Yallaɓan Sadiya."
Cikin yanayin maganarsa ya ce"Yallaɓan na ki na nan ya yi kewarki? Kin tashi lafiya Sadiya ta?
Na amsa masa da lafiya lau, ina tambayan su jidda, cikin ɗan sauya murya ya ce"Kya bari mu gama gaisawa. Amman hankalin ki na wajen yara, suna lafiya suma Saude na taimaƙa musu da abin karyawa sun shirya lokaci kaɗan zan kai su makaranta in sha Allahu."
Sai da na yi dariya kafin na ce"Afuwan Yallaɓai na. I miss u jiya fa dakyar na yi barci saboda rashin ka."
Na ƙarishe faɗa ina masa shagwaɓa dariya ya yi kafin ya ce"Jiya na kira wata, tana ta mgana cikin magagi kamar dai Sadiya ta ko?
Baki na rufe ina ƴar dariya shima yana ta ya ni.
"Allah da gaske na yi kewarka, duk in da na juya domin in laluɓoka sai na ji wayam."
Kai ya kaɗa kamar ina ganinsa amman saboda ni na san Yallaɓan nawa shi ya sa na fahimci abin da ya yi ɗin kafin ya yi maganar.
"Uhm ko dai kina kewar jikina, ba ki samu kin buga tekwondon ɗin dare ba ko? Kin ta buga kafa shuru ko?
Dariya na kwashe masa da shi ina faɗin"Laa Tafida kai ko? Shima dariyan ya yi, sannan muka cigaba da hira ya na ce mini na tabbatar da na fita da wuri, kar kuma na makara a samu matsala, sai na faɗa masa ai har na yi wanka ma ƙaryawa kawai zan yi na wuce in sha Allahu.
Kafin mu gama waya sai da ya ba ma su Jidda wayar muka gaisa. Jidda faɗi ta ke yi" Umma gidan duk ba daɗi da baki nan?
Ina dariya na ce"To ga babanku nan? Ko duk da haka gidan ba daɗi?
Sai ta yi dariya ina jin sa daga gefe yana faɗin" Wato mamanku ce, Turken gida in ba ta nan ku ce gidan ba daɗi, ni kuma in ba na nan gidan da daɗi ko?
Jidda ta ce"Abba kai ma in ba ka nan gidan ba daɗi." Uhm kawai ya ce ya karɓe wayarsa ya na faɗin" Ku ba ni wayata."
Baby ce ta saka rigiman ita ba ta yi magana ba dole ya ba ta muka gaisa ita har da neman yin min kuka.
"Umma yaushe za ki dawo? Nima ina so ki je da ni."
Saboda ina son na tsokani Yallaɓai sai na ce"Ga Babanku nan, sai na yi sati zan dawo" kawai sai ta fashe da kuka ta na faɗin" Umma ni na fi son ki dawo. Abba fa ba ya zama a gida."
Ina ta dariya san da na ji yana faɗin"Baby ki ji tsoron Allah, yaushe ne ba na zama a gidan?
Wayarsa ya karɓe ya na faɗin"Yau ba zan siya miki ice. Cream ba, ki bari in Umman ta ki ta dawo sai ta siya miki."
Ni diramansu ke ba ni dariya, domin ina jin sanda ta bishi ta na faɗin Abba ka yi hakuri to Umma kar ta dawo zamu zauna da kai ya ce daga baya kenan.
Sai da ya koma ɗaki a cunkushe ya ce"Ki dawo mai ƴa'ƴa kina ji sun zaɓe ki sama da ni."
Ya faɗa har ya na wani ƙwafa, ina danne dariya na ce"Sorry Yallaɓai Uwa uwa ce fa."
"Uba ma ai Uba ne ko?
Ganin in na yi dariya zan ƙara kunna sa sai na ƙyaleshi, ba mu jima muna waya ba ya ce bari ya yi wanka ya fita kai su makaranta zai wuce cikin gari akwai in da aka kira shi zai ga waje saboda zane, bayan mun yi sallama ina zaune ina mirmishi, ina son Iyalaina, na sha wahala kafin na gina gidana, yanzu kawai sai wata rana wata ta shigo a matsayin matar Yallaɓai ko?
Gabana ya faɗi, da sauri na kauda tunanin haka a raina saboda ban isa na hana shi aure ba in ya yi niyya, amman ina fargaban yadda wannan ginin da na yi shekaru ina gina shi, shin zai iya ɗorewa a haka? Ko zai rushe gabaɗaya?
Yusuf mutum ne na jama'a mai harkoki da yawa, shi ya sa ya na yawan samun ayyuka, a da sai na yi ta kallon ya na da son mutane da yawa, kowa na shi ne sai daga baya na fahimci sanin mutane ya na yi masa amfani saboda duk in da ake neman aiki irin nashi ya na zaune za a yi masa waya su ce wane ne ya ba mu lambarka muna son aiki kaza, tun a sanin da na yi masa mutun ne mai zafin nema da fafutuka.
Ina cikin wannan tunanin Khaleesat ta leko ta ce na zo mu yi breakfast, daman na riga da na shirya cikin wata doguwar rigar atamfata wata mai ja haka.
A dining muka haɗu gabaɗaya har da Yaya Hamza shima cikin suit ɗin sa na zuwa aiki.
"Ina kwana Yaya Hamza"
"Mun tashi lafiya Sadiya?
Na amsa masa da lafiya lau sannan na zauna muka fara karyawa, Tea ne da soyayyan biredi sai doya da miya. Tea ɗin kawai na sha da biredin. Yaya Hamza ya riga mu tashi 5k ya ijiye min a gabana ya na faɗin"Ki yi transport. Ina tunanin ko Khalee ta raka ki ne?
Da sauri na ce"Laa ba komai fa zan iya zuwa ni kaɗai. Ni fa ba yarinya ba ce Yaya Hamza."
Kai ya kaɗa kafin ya ce"Ke yarinya ce mana. Saurin aure kika yi, ki daina ganin kanki a babba domin kin haifi Jidda ta yi tsawon kafa."
Ni dariya Khaleesat ma dariya, shi dai ko a jikinsa ya ce mini ya wuce wajen aiki in ina bukatar wani abu zan iya kirashi, na yi masa godiya da fatan Allah ya ba da sa'a.
Matarsa ta tafi rakashi ni kuma na zauna na ƙarisa karyawa, bayan na gama na kwashi kuɗin da ya ba ni na koma ciki na kuskure baki, sannan na zo na saka mayafina takwas ta gota da kaɗan da ɗan nisa gwara na fita da wuri saboda na isa a kan lokaci.
Mayafi na ja na saka, sai na haɗa da bakar jaka da takalmi mai saukaƙƙen tudu.
Atm ɗina daman yana tare da ni da duka takarduna. Sai na saka 5k ɗin da Yaya Hamza ya ba ni a cikin jaka, ina shirin fitowa Khaleesat ta sanyo kanta ɗakin sai muka haɗu a kofar ɗakin..
"Har kin shirya wai?
Ina nuna mata jakata na ce" Ga shi ma kin gani. Gwara na tafi da wuri tun da kin san da ɗan tafiya."
"Haka ne. Amman a ina kika san asibitin?
Mun fita falo tare da ita lokaci ɗaya ina faɗin" Kin manta can Tasleem ta kwanta lokacin da kika haife ta?
"Oh! Kin ga har na manta kuwa."
Ta rakani har ƙofar gida ta na jaddadamin na samu Adaidaita zuwa pizzet daga nan sai na hau na Shika ɗin. Sai na amsa mata da toh, ta in ban gane wani abu ba na kira ta, ina dariya nan ma na ce mata in sha Allahu.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 31