Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ya ni zaɓan kayan da zan saka. Mun daɗe gaban wardrop duk wanda na nuna sai ya ce a'a. Daga karshe dai ya tsaya kan wata super shi ya siya mini ita mai kalan green na ciro ta ina faɗin" Amman Yallaɓai mayafi zan saka ko? Hararata ya yi kafin ya ce" Asibiti gidan biki ne? Na marairaice ina faɗin" Don Allah fa. Atamfar nan ba ta kyau da Hijabi."   Jan gefen hannun rigansa na ke yi sai ya kalleni sai na marairaice ina faɗin" Haba My Yallaɓai na. " Wani kallo ya yi mini kafin ya duƙa ya na faɗin" In kin yarda mu sabunta wanka." Da sauri na ce" Bar shi na saka Hijabin." Na faɗa ina tura baki shi kuma yana mini dariya. Haɗe rai na yi ina faɗin" Ni ko? Ni ko ai shike nan." Sai ya ce to na saka mayafin amman sai na yi alƙwarin amjuna akwai ɓarnan ruwa ya na iya sai na ce na yarda sannan ya bari na ɗauko mayafin kayan takalmi ma shi ya zaɓa min wani flat mai ruwan ƙasa irin kayan shi ya na da jaka sai na ɗauki jakar ina jin Yallaɓai na faɗin" Wai ko dai ba Alhaji za ki je gaisarwa ba. Biki za ki je?   Ina dariya na ce" Kai Yallaɓai na. Wani biki kuma! Jinya zan je." "To ma su jinya." Share shi kawai na yi domin na san yanzu in na yi magana sai ya iya ɓata mini shiri shi ya sa na yi shuru ina bin sa da mirmishi. Muna nan sai ga Sabitu ya kira ya ce ya na waje sai ya ɗau kayan ya fita dashi ni kuma fita zuwa ɗakin su Jidda na ga sun shirya dogayen riguna suka saka na Abaya saboda halin Yallaɓai na ce su cire mayafan su saka Hijabi yanzu nan zai ce yara ma ƙanana ina koya musu saka mayafi. Yallaɓai ba wai yana da tsanani ba ne amman fa ya na da saka ido kan iyalansa. Wani lokaci zai yi mini tsanani wani lokacin kuma sauƙin kanshi har ya na yi mini yawa.   Jidda na ce ta ɗau kwandon abinci zuwa mota ni kuma na koma ciki ina fesa turare. Har na ɗan fesa kaɗan sai na tuna da Yallaɓai yanzu raina zai ɓaci. Da sauri na ijiye na koma ina shinshina kaina in ƙamshin ya fito na shiga uku da faɗan Yallaɓai. Hon kawai ya yi ta mini daga haraba ni kuma sai da na kashe duka wutar gidan sannan na fito na kulle ƙofar falo. Su Jidda na gidan baya ya na hira da su ina buɗe gaban mota na shiga ya juya ya na kallona kafin ya ce" Alhaji ki ka fesa ma turare ko likitocin ? Ya faɗa cikin haɗe rai. Da sauri na ce" A'a. Turaren kayan ne ina ga." Ƙura mini ido ya yi da sauri na ce" Da gaske ban fesa turare ba." Bai ce mini komai ba ya yi ma motar key sai na koma na jingina da kujeren mota ina maida numfashi. Mun ɗau hanya na ji ya na faɗin" Mu fara zuwa asibiti in na duba Alhaji sai na kai su gwammaja ɗin" Ni dai na amsa masa domin na ga ya wani haɗe rai ne. Mun isa asibitin wajen sha ɗaya saura ne. Amman na iske har Ma'u ta zo ni da Rahila ne kawai ba mu iso ba amman har su Yaya Auwal da matansu da Amina ma ta iso daga kaduna. Mun gaggaisa da su har da Yaya Murja Baaba ta na nan ita da Gwaggo suma na gaishe su Baaba a dakune ta amsa ban damu ba. Yallaɓai kuma ya fara musabaha da mazan matan ma suka gaisa ga duka har ƙasa ya gaida Gwaggo da Baaba. Ma'u har da cewa" Yallaɓai barka da safiya.' Ya juya suna gaisawa su Jidda ma suka bi kowa ɗaya ɗaya suka gaishe su. Suna waje Alhaji na ciki ya na barci Yallaɓai ne ya shiga tare da su Jidda. Ba daɗewa ya fito ya ce za su tafi ni na raka shi har bakin mota muka rabu akan cewa sai anjuma za su zo tare da su kawu ina ɗaga musu hannu suka bar haraban asibitin Baby sarkin rigima jin wajen Nene za a kaita sai ta fara murna. Abincin da na zo da shi Gwaggo na ba ta karɓa ta na ta saka albarka. "Ba wacce ta zo hannu rabbana. Yadda kuke jin ƙan mu kuma Allah ya jiƙan ku wata rana." Aka amsa da Amin Amin Baaba ta na ta wani taɓe ba ki ni ko ba ta isheni kallo ba Mun gaisa da Ma'u da tambaya ya jiki daga nan na karisa saman darduman da Amina ke zaune ita da Laila da Khaleesat suna hira.  Sai bayan na natsa ne na tambayi Baba Aminu aka ce ya koma tun safe Baba Sani kuma ya koma gida ya huta sai anjuma zai dawo. Na kira wayar Rahila ta ce min ga su nan a kan hanya ba daɗewa ta iso itama da kwandon abincin ta. Kowa da wanda ya saba dashi ya zauna su Yaya Murja yan wajen Ma'u suna zaune waje ɗaya har da Zaitunan Yaya Abubakar. Yaya Aina ce ma ta ɗan zauna a wajen Rahila kuma daman kowa ya san kaf gidanmu na fi shaƙuwa da ita shi ya sa ko an gamu tare muna hira ba wanda zai bi ta kai.     Muna nan har bayan azahar Laila Yaya Auwal ya ɗauke ta zuwa gidan su. Alhaji ya farka wajajen biyu duk mun shiga mun gaishe shi da jiki ya ce ya ji sauƙi yau ma ya ce likita ya sallame shi.   Yaya Hamza ya ce ya bari ko zuwa gobe in ya ƙara jin sauƙi. Baaba na gefe ta ce"Gaskiyar Hamza ka ƙara kwana ka samu hutu sosai Yaya Sule." Shi dai Alhaji an fi ƙarfinsa kawai ne kawai shi ya sa ya yi shuru. Sai ya koma ya kishigiɗa bayan Gwaggo ta kara mai filo "Yara nan fa duk sun taho maka da abinci me za ka ci? Gwaggo ta faɗa ta na kallon shi. "Allah ya saka muku da alheri. Allah ya yi musu albarka na gode." Dukkanmu muka amsa da Amin Amin Abincin ya ce sai anjuma amma ya sha ruwa. Ni ya kallah kafin ya ce"Dubu yau ke kaɗai kika zo? Ina kika baro min uwargidana Hauwa'u? Ina dariya na ce"Ta zo ka na barci Alhajinmu. Yallaɓai ma ya zo amma anjuma zai dawo in sha Allahu." Sai ya jinjina kai kafin ya kalli Ma'u ya na faɗin" Asma'u ki yi ma megidanki godiya maimuna ta faɗa mini bai bar yaran nan sun kashe komai ba. Allah ya ƙara ma arziƙin sa albarka Amin." Ma'u ta amsa da Amin Baaba har ta amsawa da Amin Amin da karfi na kalle ta lokaci ɗaya ina taɓe baki. Ba mu daɗe a dakin ba muka fita waje saboda dokar likita. Muna asibitin nan har la'asar sai ga kiran Hauwa ta na ce min ga su a asibitin ita da Mutaƙƙa ina ne barayin ɗakin da aka kwantar da Alhajin? Ina jin haka ni na fita haraban asibitin na taho da su.    Shi ya sa na ke son Hauwa in dai abu ya same ni ita ke fara zuwa ta yi mini jaje ko murna ita da mijinta. Mutaƙƙa ya shiga ya gaida Alhaji duk da ba lokacin dubiya ba ne na faɗa ma Alhaji ƙanin mijina ne ya na ta saka albarka. Mutaƙƙa ya zo da kayan marmari Hauwa kuma har abinci ta zo dashi kuma nan ya bar min ita karfe shidda ya ce ta koma gida. Na ji daɗi matuka ko da ganin sauran yan'uwana dangin mazajensu na ta zuwa gaida Alhaji. Ma'u har uwargidanta Hajiya Zainab ta zo da sauran ƙanensa.   Hauwa ta zo ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ni na yi mamakin ganinta har a cikin zuciyata na san ba domin ni ta zo ba illai Ma'u ce ta je ta taro ta. Hauwa ta saki baki ta na kallon su har da rumgume juna muna ji ta na faɗa ma Baaba matar Yayan mahaifiyar Alhaji Mustspha ne. Sai ta ɗago ta ga ina kallonta sannan ta ce"Kuma Yayar mijin Sadiya ne.".   Gwaggo na ta saka albarka da godiya ina ji Ma'u ta nuna Baaba ta na faɗin ga mahaifiyarta. Anty Bahijja har ƙasa ta duka suna gaisawa Rahila na in da muke Khaleesat ta shiga cikin gari gidan ƙanwarta Anty Aina ma ta koma gida Amina ma ta je gida ta huta. Yaya Murja ma dazu ta koma mu da Yaya Balki ne kawai mu ke asibitin. Daga zaunen da na ke na gaisar da Anty Bahijja sai lokacin ta kallemu ni da Hauwa. "To su Hauwa ashe a nan nan? Cikin rawan jiki ta ce" E. Ban daɗe da zuwa ba. Tare da Baban Sahla mu ke ya kawo ni sai ya wuce." Sai kawai ta wuce tana faɗin" Hakan na da kyau." Shiga ciki ta yi Ma'u na gefenta domin ta duba Alhaji. Sai da ta shige ne sannan Hauwa ta kalleni nima sai na kalleta amman ba mu yi mgana ba muna nan zaune ta fito har ta na ba ma Gwaggo 10k. Wai sai ga Ma'u ta juyo ta na ce min" Sadiya kalli Anty  Bahijja da ɗawaniya."   Mirmishi na yi kafin na ce" Allah ya ba da lada." Ma'u ce za ta rakata ni dai ko kafata ban ɗaga daga daga na ke zaune ba. Sai ta juya ta na kallon Hauwa kafin ta ce" Yanzu za ki tafi gida na yi miki lift? Da sauri na ce"Mutaƙƙa karfe shidda ya ce ta koma gidan" Sai ta wani kalleni kafin ta ce" Ya yi. Allah ya ƙara lafiya." Na amsa mata da Amin Amin har da Baaba a masu rako. Sai da suka bar wajen Rahila ta kalleni kafin ta ce" Ku ba ku yi rakon ba Sadiya" Kai tsaye na ce" Saboda mene! Ai ni ba na neman suna. Wacce ta zo domin ta ba ki ga har da uwarta arakon ba? Sai Rahila ta kasa mgana. Saboda ta san halina ta na ƙara mgana zan saki wata mgana kuma ga Hauwa a wajen sai ta tashi tsam da goyon yarta ta wuce wajen Gwaggo itama na rakata da harara.   Hauwa ce ta kalleni cikin mamaki kafin ta ce" Wai ya kuke da Ma'un nan ne Anty Sadiya?. Kai tsaye na ce" Ina wanan tsohuwar da kika ga sun fita tare? Sai ta ɗaga mini kai. Kau tsaye na ce" Ita ce mamanta. Ita ɗin Baabar mu ce ƙanwar Alhajinmu ce da suka haɗa uwa ɗaya uba ɗaya."   Sai ta jinjina kai ni kuma sai na ƙara mata da cewa" Baban Ma'u ya rasu tun tana ƙarama sai da Baaba ta yi wani auran Alhajinmu ya ɗauketa shi ya sa ta tashi a gidanmu." Hauwa ta yi sakate kafin ta ce" Ikon Allah." Sai na kalli Hauwa domin na san akwai mgana a bakinta. Cikin sauri na ce"Me kika gani hala! Ko na ce kin ji wani abu ne a kaina daga bakin ta? Shuru ta yi ni kuma da sauri na ce" Don Allah ki faɗa mini Hauwa. Ba lalle kin san ba shiri tsakanina da Ma'u ba kina gani da idon ki yadda take shigema Anty Bahijja kuma dalilina ne tunda ai ba Musbahu ta ke aure ba. Balle kusan ta yi musu yawa haka."   Ƙasa ƙasa Hauwa ta ce" Ranar sunan Halima na ji suna mganarki." Sai na yi kwafa kafin na ce" Ai ba za ta sauya ba. Munafuka ce makira." Sai Hauwa ta riƙe min hannu tana faɗin" Ta so mu je ki ji wata mgana" Barayin muka bari gabaɗaya mun haɗu da su Ma'u a hanya za su dawo. Har ta na ce mini Hauwa za ta tafi ne na ce mata a'a da gayya na ce mata za mu yi mgana ne ina gani ta yi tsam daga ita har uwarta ni ko na ja Hauwa muka wuce abin mu.   Can haraba muka fita a babban falo muka samu kujeru muka zauna ina mai kallon Hauwa na ce"Me kika ji munafukar ta ce akaina? Hauwa ta ce" Ni fa ina ta mamaki na san ƴar uwanki ce amman me ya sa za ta biye ma su Anty Bahijja suna kushe ki?   Raina har ya fara ɓaci da sauri na ce"Me ta ce wai? Hauwa tasauke numfashi kafin ta ce" ita da Anty Bahijja da wata ban san ta ba tare da Ma'un suka zo." Kai tsaye na ce" Shema' u ce ƙawarta ce." Hauwa ta cigaba da faɗin" da Anty Maimuna ma awajen ana mganar haihuwa Anty Bahijja na ta faɗan wai kamar Tafida zai ƙare rayuwa da ƴaƴa biyu. "Buɗe bakinta sai cewa ta yi" wai daman tun farko ke ba ki da burin tara ƴa'ƴa da yawa. "   Ido na har wani ƙyalli bala'i ya haska a fusace na ce" Ita Ma'un ta ce haka don ubanta? Da sauri Hauwa ta ce" Ni fa ba na faɗa miki saboda na haɗa faɗa ba ne. Na gaya miki ne saboda ki sani ne"   Ina sassauta fushina kafin na ce" Ba zan yi ba Hauwa." Kallona ta yi kafin ta ce" Kin tabbatar? Sai na gyaɗa mata kai sai ita kuma ta gyara zama ta cigaba da faɗin" Ita fa Ma'un ta ce haka aiko Anty Maimuna ta ce ba ki isa ba kin auri ɗan dangi saboda haka in ke baki son haihuwa za su aura masa wacce za ta zo ta cika masa gida da ƴa'ƴa." Idanuwana har sun tara ƙwallah zuciyata na zafi. Na kalli Hauwa kafin na ce" Ban yi mamaki ba. Tun zuwan Ma'u gidanmu na san ita din ba alheri ba ce. Na kuna san watan wata rana sai ta zame mini matsala da damuwa. Amman ta je Allah ya fita ni dai ban taɓa bin ta da sharri ba in tana tunanin abin da ya faru na fasa auranta da Yaya Hamza take rike da ni a cikin ranta ta makara har gobe ban yi nadama ba. Da na bari ta auri Yaya Hamza da tuni ta haɗa mana yaƙi a cikin gidanmu."   Cikin mamaki Hauwa ta ce"To daman da jiƙaƙƙiya a tsakaninku? Kai tsaye na ɗaga kaina kafin na ce"Akwai kam. To sai aka yi yaya? Hauwa ta cigaba da faɗin" Kawai sai wacce suka zo tare da kika ce ƙawarta ce ta na cewa shi ya sa kika yi tsarin iyali kenan ga shi ya ja za miki matsala kina son haihuwan kuma  ta ƙi samuwa. Nan take Anty Maimuna ta ce sai dai ke matsala ta ƙare a kan ki Tafida aure zai ƙara in sha Allahu."   Mirmishi kawai na yi a cikin raina ina jin kamar in na ga Ma'u na shaƙe mata wuya. Sannan ido na idon shema'u wallahi tallahi sai ta raina kanta Hauwa na faɗin wai na kwantar da hankalina ba su isa su saka Yaya Tafida ya yi aure ba. Kallonta na yi kafin na ce" Sun isa mana tunda ƴan'uwan shi ne kuma suna gaba dashi. Ni bare ce ko yau ya sake ni gidanmu za ni su kuma ai ba shi da kamar su. Hauwa na rantse da Allah ba zan hana Yallaɓai ya ƙara aure ba, ya ƙara ta zo ta ci duk abinda suke tunanin ina ci ƴaƴa kuma ta tara masa duniya ni kuma biyun da Allah ya bani Allah ya raya min su." Na faɗa ina ƙokarin maida kwallar da ta kawo min. Hauwa ta dafa kafaɗata ta na faɗin" Ki yi haƙuri. In sha Allahu ke ma za ki ƙara haihuwa. Ba kin je asibiti ya kuka yi da likitan? Ina sauke numfashi na ce" Ta dawo da ni nan asibitin Aminu kano. Jibi zan fara zuwa in sha Allahu."   Hauwa ta yi ta mini fatan dacewa na kalleta ina ƙaƙaro mirmishi. "Na gode Hauwa." Mun daɗe a wajen ta na ba ni baki na dai nuna mata bakomai ne amman ni kaɗai na san halin da zuciyata ta ke ciki. Amman na yi ƙoƙarin nuna ma Hauwa ba komai. Saboda haka ne na kalle ta ina faɗin" Kin ji Yaya Usman zai ƙara aure?   Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Na ji fa. Duk ranar sunan na ji ana tattaunawa. Shi kuma can bakin ƙannen shi na ji su Nasara suna ta zagin Anty Zabba wai so ta ke yi shi Yaya Usman ɗin ya zauna da ita kaɗai? Ko ya yi ma Ogan shi gaddama yaƙi karɓan auran. Sai zaginta suke yi suna faɗin kar Allah ya sa ta koma ɗin." Cikin mamaki na ce"Ikon Allah. Mutane sai Allah yau kuma ita Anty Zabban suke zagi? To Maman farko ba ta yi mgana ba?   Hauwa ta ce" Oh na ji dai kamar an ce ta kira shi a waya ta ce ya bar komai ya ke yi ya zo ta na son ganin shi " Sai na gyaɗa kai kafin na ce"Uhm. Allah dai ya kyauta.". Ta amsa da Amin ni na cigaba da faɗa mata yarda muka yi da Yallaɓai ya haƙinƙan ce. Ta na dariya ta ce" Ni ai ban yi ma Muttaƙa mgana ba. Kar ya ce ina son jin gulma amman na san shima bayan ɗan uwansa zai bi" Dariya muka ɗan yi gabaɗayanmu. Muna wajen Munira ta kira waya ta. Ta na tambayata jikin Alhaji? Na ce da saúƙi a ina ta ji ta ce Nasir ya faɗa mata ya ce Tafida ya saka a group ɗin su na gida. Ta tambaye ni wani asibiti ne na faɗa mata sai ta ce min ƙila gobe ta shigo. Ina dariya na ce ma ai ga Hauwa ta zo tun ɗazu. "Kai Hauwa sannu da ɗanwaken zagaye ko ki kirani mu taho tare." A speaker na saka Hauwa ta maida mata da amsa da cewa" Ke ni fa mijina ya kawo ni. Goben ki saka mijin ki kema ya kawo ki." Munira na dariya tace" Au gorin miji da kin ga Habibi ba ya gari? To na san hanya kin ji ta Yallaɓai gobe ina nan tafe." Na ce Allah ya kawo ta lafiya daga nan muka yi sallama. Ganin shidda har ta gota yasa Hauwa ta ce bari ta je ta yi ma su Gwaggo sallama ta wuce gida. Muna zuwa na ga Shema'u ta zo har ga Allah na so na daure amman na ƙasa ta kalleni ta na mini mirmishin munafunci irin na ƙawarta amman ni ta ga irin kallon da na yi mata. Ba domin muna asibiti ba ne. Kuma da ba uba na ne ta zo dubawa ba wallahi sai Shema'u ta raina kanta baƙar munafuka. Tana min magana na yi kamar ban ji ba sai da Ma'un ta ce" Sadiya ba ki ji Shema na mgana ba ne. Ba ta gari ne ɗazu ta dawo ta na zuwa, ke ta fara tambaya." "Oh." Haka kawai na ce na juyar da fuska ta domin na kasa iya ɓoye abin da ke zuciyata. Hauwa ta yi musu sallama kularta kuma aka juye abincin na riƙa mata har bakin asibiti ta samu adaidaita muka yi sallama. Ba domin Yallaɓai ya kirani ya ce bayan mangariba suna tafe tare da su Uncle Abba  da har na gaji na ce tafiya ta gida zan yi. Rahila ma ta koma gida wai za ta yi abinci da ga ni sai Ma'u da kawarta Gwaggo ma Yaya Hamza ya maida ta gida kiri ƙiri Baaba taƙi bin ta wai ta je za ta zo. Can suka keɓe da yarta suna da ƙuskus ni ko dagani sai Yaya Balki itama mijinta take jira Zaituna kuma ta koma gida saboda yara a cikin raina ina fatan Allah ya sa a sallani Alhajinmu gobe na gaji da zaman asibitin nan Waya ta na ɗauko na kunna Data na kwana biyu ban hau ba. Sai na ga an yi min mgana har da Yaya Maimuna ta na tambayan jikin Alhaji. Hindatu kuma ta ce ta kira waya ta ba ta samu ba.  Har da matar Muhammad kabir ma na ga maganarta. Kuma na ji daɗi na amsa su sama sama saboda an fara kiran sallar mangariba. Yaya Balki kawai na faɗa ma zan je sallah sai ta ce na tsaya mu tafi tare. Muna masallacin kafin mu fito Yallaɓai ya ce ga su sun iso asibitin. A haraban wajen muka haɗu suka gaisa da Yaya Balki ta yi gaba ta bar mu ina gaisawa da Aminan mijina guda biyu. Uncle Abba da Tariq. Sun yi min ya mai jiki na ce da sauki muna gaba ni da Yallabai suna baya zuwa in da ɗakin da Alhaji ya ke ciki. "Me ya faru na ga kamar ranki a ɓace? Yamutsa fuska na yi kafin na ce" Na gaji ina son na koma gida." Sai ya kalleni da saurin na ce" Zan bika yanzu ko za ku je wani waje ne? Kai ya girgiza kafin ya ce" A'a Gwammaja muka yi. Sai mu wuce taren su ma daga can za su wuce."   Tun da Gwaggo ba ta nan da Baaba suka gaisa sai su Ma'u sannan na raka su ciki suka duba Alhajinmu ya ma tashi Baba Sani ya ƙariso zai taimaka masa ya yi alwala ya yi sallah. Ya ji daɗi ya na ta saka musu albarka da godiya ba dadewa suka yi masa sallama dukkansu kuma sun aje masa kuɗi ya na ta saka albarka. "Alhajinmu Allah ya ƙara lafiya zan bi Yallaɓai zuwa gida sai gobe." Alhaji ya jinjina kai kafin ya ce" Shi kenan mu kwana lafiya Dubu! A gaida min da Hauwa kuluta." Na amsa masa ina mirmishi,  sun rigani yin gaba ina fitowa na ce ma Yaya Balki zan bi Yallaɓai sai gobe ta ce ai ya kamata na je gida tun safe fa. Daƙyar na iya yi ma Baaba sallama ta amsa sama sama. "Sadiya Gwammaja za ku je? Na juya ina kallonta Shema' u ce. Kamar na ce a' a sai kuma na ce mata eh. Sai kawai na ji Ma'u na faɗin" To ki je mana Shema. Sadiya itama Gwammaja za ta je gidan kawunta."   Juyawa kawai na yi ban ko yi mgana ba ina ji ta na yi ma Baaba sallama. Ina zuwa na ce ma Yallaɓai za mu rage ma kawar Ma'u hanya. Ya ce to ba matsala Ma'un ce ta rakota abin mamaki tana ganin motar su Tariq dabam sai kawai Ma'u ta kalli Yallaɓai ta na faɗin" Yallabai bari ta bi wancan motar ko ba waje ɗaya za ku je ba? "Can za mu je gabaɗaya. Ta je ta shiga." "Tariq..." Ya ƙwalama sa kira ya na waya ne tsaye a bakin mota Uncle Abba ya riga ya shiga bangaren direba tunda motarsa ce. ''Ga ƙari na samo muku itama Gwammaja za ta je" Ya faɗa ya na nuna Shema'u dake tsaye ita da Ma'u. Sai ya ɗan ɗaga masa hannu alamun toh sai ya ce ta je ta shiga. Ni dai tuni na shige gaban mota na zauna Ma'u ta leƙo ta na fadin sai da safe na ce mu kwana lafiya. Muna tafe amman acikin raina ina tunanin me ya sa shema'u ta ke son bin motar su Uncle Abba? Tabbas da wani abu a ƙasa. Kafin ma a kai gidan su Yallaɓai ta sauka domin suna bayanmu ne mu dai muka yi gaba. Har ma mun shiga mun gaisa da Nene ta na tambayata Tafida ya ce Alhajinmu ba lafiya ya jikinsa? Na ce da sauƙi ta yi masa fatan samun lafiya.   Tariq ne na ji ya na yi ma Uncle Abba tsiya yau ko ya shafa kwalli ne ƴan mata sai kawo hari suke yi. Shi kuma bai ce komai ba Nene ce ta ce"Me ya faru? Tariq ya ce"Nene ɗazu fa a gidan su amaryan abokin mu yan mata shi kawai suke kawo ma hari. Yanzu ma da muka ɗauko wata yar uwan Sadiyan Tafida daga asibiti har lambar wayarsa sai da ta tambaya."   Ya faɗa cikin dariya. Ina zaune a cikin raina na ce a biri ya yi kama da mutum daman kawu ta gani kenan ta ƙyasa. Mirmishi na yi na ce lalle za ta sha wahala wallahi ko  ya na sonta ba zan taɓa bari ya aure ta ba. Ba wai ina dariya da daɗewan da ta yi ba ta yi aure ba ne. A 'a ba ta da hali mai kyau ne. Sai kawai na shiga hirar da cewa" Ba ƴar'uwanmu ba ce ƙawar Ma'u ce kawai." Nene ce ke faɗin" To Allah ya sa dai ya

Chapter 15 of 31