Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Kuma fa na yi maka kunin tsamiya mai daɗi" Motsin fitowarsa na ji da na so na yi saurn ijiye masa wayar ne sai kuma na fasa sai da ya fito. Ya yi mamakin ganina tsaye da wayarsa sai da ya matso gabana sannan na miƙa masa wayarsa ya karɓa kafin ya samu sararin mgana na ce. "An tura maka saƙo."   Ina gama faɗin haka na fice na san kuma bayan ya duba saƙon ya ji nauyi domin ba na ce kunya ba tunda maza ba su san kunya ba. Har ya fito muka yi sahur jikinsa a sanyaye ni kuma sai na yi masa bariki ban nuna masa ko a fuska na ji haushi ba sai ya ɗan saki jikinshi amma a raina na kudiri niyyar koya masa hankali daga shi har Gimbiyar ta shi. Washegari ya tura mini kuɗin kayan salla nawa da na yara sai na su Nene da na Gwaggo. Daman yana yi musu kaya duk shekara. Dija collaction na tura ma kuɗin daman mun yi mgana na zaɓi komai har Marwa na yi ma kaya da Saude saboda mun yi waya a gida za ta yi salla in ta dawo sai kuma ta gama pratical ɗin ta za ta koma makaranta. Kuma daman ta turo mini kayan na zaɓa tuni suna wajen ɗinki kuɗin ne sai da ya tura mini bayan mun gama lissafi na tura mata.   Ni da yara kala huɗu ya yi mana. Leshi biyu atamfa biyu. Nene Atamfofi biyu su Hajiya Iya kowacce ɗaya sai Jawahir kala biyu Adanan kuɗi ya tura masa sai Gwaggo guda ɗaya Alhajinmu kuma shadda mai kyau. Sai ni mayafai guda biyu da Hijabi ni da yara sai takalman mu har Nene an siya mata takalmi da Hijabi gabaɗaya tun lokacin da a ka kawo kayan na nuna masa ya ce komai ya yi. Telanmu kuma daman na yi masa mgana kuma ga kuɗi har da na Nene na kai mana ɗinki tare da na Jawahir da Marwa Saude kuma na ta na bata mamanta na ɗinki ita za ta ɗinka mata. Gwaggo kuma da Alhajinmu na kai musu na su suna ta godiya duk da suma su Yaya Hamza duk sun yi musu. Nene ma na kai mata takalmi da hijabinta na ce kaya na wajen ɗinki ta na ta saka albarka. Ranar da muka ɗau azumi na ashirin da shidda Mimisco ta aiko da kaya yan kanti kala biyu biyu na jidda da baby. Anty Bahijja ma ta aiko musu da material a ɗinke sai Anty Maimuna itama kala biyu amma Bby uku ta yi mata har da wani riga da wando masu kyau da takalma. Gimbiya kuma Yallaɓai ta ba ma kayan ya kawo ma su, kayan kwalliya ne sai hijabai da mayafai sai takalma masu igiya sai abun hannu da ɗan kunne sai kwalban da ake kitso da shi kayan kuma ta ce suna wajen ɗinki duk Yallaɓai ne ya ke koramin jawabi nan yaran suna ta murna shima bakin shi ya ƙi rufuwa. Daga gani ya ji daɗi kuma har hakan ya nuna a saman  fuskar shi.   Ni dai ban nuna masa komai ba na yi godiya har ya na saka min kati a waya ta ni kuma na san na kiran da na ce zan yi ma Gimbiya na yi mata godiya ne. Kai namiji munafuki ne wallahi.   Ranar da muka ɗau azumin ashirin da bakwai ɗaure Yallaɓai ya yi saboda na zo tashin shi na ga Gimbiya na kiran shi sai kawai raina ya ɓaci ban tashe shi ba. Ni kaɗai na yi sahur saboda Jidda na ce ta huta jiya ta sha wahala. Yallaɓai bai tashi ba sai da aka fara kiran salla lokacin ina zaune na idar da raka'atul fajir, ya tashi ya na kalle kalle kiran sallar da ya jiyo ne ya sa ya kalleni cikin muryan barci ya na faɗin "Sadiya mun makara ne? Na ji kamar ana kiran salla? Sai da na kalle shi kafin na ce" Kai dai ka makara. Ni na yi sahur ɗina." Cikin mamaki da tuni barcin ya sake shi ya ce" Ban ga ne ba? Ni fa? Kai tsaye na amsa masa da cewa" Ba ka yi ba." "Me ya sa ba ki tashe ni ba? Sai da na yi shuru kafin na ce" Ban tashe ka ba. Saboda na ga wacce ka rabama girki da ita na kiranki sai na koma a tunanina ta tashe ka yau ɗin" Galala ya yi ya na kallona sunana ya kira na yi masa banza sai kawai na miƙe na kabbarta salla ganin haka yasa shima ya mike amma sai ya ya ɗau wayarsa ya duba sannan ya mike ya fita zuwa tiolet ya ɗauro alwala ya fita zuwa masallaci sanda ya dawo ina ji da na yi baricn ƙarya weekend ne yara ba makaranta sun ma yi hutu jiya jumma'a.   Na san mganar da na faɗa masa na cin ransa bai iya hakuri ba ina barci ya tashe ni da mganar wai bai gane me na ke nufi da ya raba mana girki ba? Da wa ya raba mana girki? Kai tsaye na ce" Da wacce ta ke yi maka girki kana zuwa ka ci ka biya tuƙwaici mana."   Wani kallo ya yi mini ni kuma ina shirin na juya na koma barci ya riƙo ni ya na kiran sunana. "Sadiya." Ido na sakar masa kafin na ce" Na'am Yusuf." Kawai sai ya girgiza kai bayan ya saki hannuna kafin ya ce" Sadiya karki fara abin da ba halin ki ba ne. Bincike mini waya kike yi yanzu saboda ba ki yarda da ni ba? Kai tsaye na ce" Allah shi kyauta. Kawai dai akasi aka samu na gani." Komawa na yi na kwanta ina faɗin" Karka damu ba wani abu fa." Miƙewa ya yi ya na kallona ni kuma sai na ja bargo har saman kaina. Hannu ya saka ya janye bargo ya na faɗin" Ki tashi mu yi mgana" Sai na ƙi tashi na riƙe bargon ina faɗin" Wata mgana? Ai mun gama mganar nan ko? Zura min ido ya yi kafin ya ce" E duk da haka na ce ki tashi mu yi mgana." Na ko ƙi tashi na juya zan gyara kwanciya a saman kaina Yallaɓai ya yi min tsawa. "Sadiya na ce ki tashi mu yi mgana ko? Kar ki bari raina ya ɓaci wallahi." Yadda ya yi mganar ne ya sa na gane ranshi ya ɓaci sai na miƙe na zauna a saman gado shima sai ya zauna ya na mai sauke ajiyar zuciya. "Sadiya wallahi ba komai tsakanina da Daughter fa. Kawai dai kin san am her favorite ne tun a baya. Kuma ni tana kira ne ba domin ta san ba ni da mata ko wani abu ba just normal na yan'uwan juna kin gane? Sai kawai na gyaɗa masa kai, domin ni na san kawai yana faɗa ne. "Kar ki ɗauke shi a wani abu don Allah. Ni ina mijinki haƙƙi ne a kanki ki tashe ni kamar yadda kika saba." "To ba za a ƙara ba." Na faɗa saboda na gaji da jin mgananunsa. "Kuma game da abinci in na je duba Nene sai ta yi mini ta yi in na ce ba zan ci ba sai Nene ta ce ko kaɗan ne na taɓa. Kin san dai ba zan yi ma Nene gaddama ba. Mganar tuƙwaici kuma wannan kyautatawa ce kema kuma ai ina yi miki ko? Ina ta kallon shi dai amman na kasa mgana. "Ba ki son kiran ne? Sai na ce mata ta daina Sadiya ta ba ta so." Wani kallo na yi masa kamar in yi dariya saboda na ga zai raina min wayau amma ban yi ba. "Zan faɗa mata ta daina kirana da asuba gashi yau ta ja mini yin ɗaure." Ya faɗa ya na yar dariya har yana shafa min kumatu. Yaƙe kawai na yi masa ban yi mgana ba. Hamma ƙarya na fara yi masa sai ya ce na koma na kwanta shi zai fita can falo akwai aikin da zai yi har ya ɗau laptop ɗin sa ya fice ina bin shi da kallon mamaki. Ajiyar zuciya na sauke ko ba komai a zuciyar Yallaɓai game da Gimbiya ita har gobe shi ne zaɓin ta tsoro  na ɗaya wannan karon mafarkinta zai iya zama gaskiya in dai ba wani ikon Allah ba tunda ba ta da shamaƙi da hakan ta kowanni fanni. Tun kuma daga mganar da muka yi ba mu ƙara tada mganar ba. Ita ma ta daina kiran asuba ina tunanin da gasken ya yi mata mgana sai na ji daɗi ko ba komai  ya nuna mata ni matarsa ina da daraja. daga nan nima sai na watsar da abin da ke cikin zuciyata na kishi na rumgumi mijina. Sai cefanen salla tare muka je kasuwan muka siyo komai sauran kayan miya kuma Musbahu ya ce ya ba ma kuɗi zai kawo minibana gobe salla nama kuma daman a can gida sa suke yankawa a raba gabaɗaya amma dai ya siya mana na kasuwa kilo huɗu sai kaji muka haɗa da shi ni kuma a gida na siya fulawa zan yi cincin da cake da donut ga masu tayani Saude da Marwa da ta zo mini salla duk tare muke ayyukan gefe ɗaya kuma ina ta mana shirin Annirvesary ko Yallaɓai bai san shirina ba da ya tambayeni nace masa kawai ya tura mini kuɗi suprise ne shima ya ce a ranar akwai suprise ɗin da zai ba ni ina ta murna har ina zolayanshi na ce Yallaɓai ko ka biya mini Umra ne? Yana mirmishi ya ce in sha Allahu za mu je Umra Sadiya ta. Da ni da yara duk mun yi ƙunshi salla wata Hajjaju ce maƙoyar su Rahila na kira har gida ta yi mana kunshi na biya ta. kitso kuma mai yi mana kitso ta zo gida ta yi ma su Jidda har da Marwa da Saude bayan ni na wanke musu kan na su a gida.    Ni dai ana gobe sallah na je shagon Amesty ta yi mini Saloon. Ban cika son yin kitso ba saboda Yallaɓai ya fi son in bar gashina a haka ta bakin shi ya ce ya fi mai daɗin taɓawa. *TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 09069067488. 08032773332. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *Janafty* *TURKEN GIDA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Kz6koexT4Yj4o2zO4xVzrU INA MATAN DA SUKA DADE SUNA NEMAN MAGANIN SANYI WATO INFECTION MAI KYU BASU SAMUBA, ANYI MAGANI ANYI MAGANI HAR ANGAJI, TOH KICE ALHAMDULILLAH, SABODA ALLAH YA HADAKI DA MAGANIN DA ZAI MAGANCE MIKI KO WANE IRIN CUTTAN SANYI WATO INFECTION DA YA KAMAKI CIKIN SATI GUDA DA YARDAN ALLAH. SHIGO GIDAN BUZAYE WAHALANKI TA YANKE HAJIYA💃💃 INA MAI NEMAN KAYAN GHARA ZAFAFA, MASU INGANCI, MASU KARFI, WANDA ZAI KANKARO MIKI MUTUNCINCI DA KIMARKI, WANDA ZASU DAWO DA HANKALIN ME GIDA GAREKI, SU SA YA MAKALE MIKI DA ZAZZAFAN SOYAYYANSHI, YA DINGA SAKE MIKI KI WARWASA YANDA KIKE SO💃💃 TO ER UWA SHIGO GIDAN BUZAYE KIGA IKON ALLAH DON KUWA ALLAH YA KAWO MIKI KARKEN MATSALANKI NA RASHIN DACEWA DABAKYAYI NA KAYAN GHARA😁💃💃 KUSHIGO GIDAN BUZAYE KU GYARA KUGA IKON ALLAH *🅿️19* Mun yi azumi ashirin da tara 29 ɗaya ga watan shawwal ya kama ranar asabar ne a ranar muka sallaci salla ƙaramar salla. Mun je idi mun sallaci salla tare da al'ummar Musulman duniya gabaɗaya ni da Yallaɓai da yara sai Marwa da ta yi salla tare da mu. Bayan mun dawo idi na saka Marwa ta dafa jallop ɗin shinkafa mai nama. Tun a daran jiya muka gama duka soye soyen mu Saude da Marwa sun taimaka mini ƙwarai shi ya sa jiya da Saude za ta tafi da daddare Musabahu ya zo gidan da shi na haɗa su na ce ya kai ta gida tunda akwai motar Ya Usman a hannun shi tun lokacin biki bai koma da ita ba. Na dibar mata naman salla da kayan fulawan da muka yi sannen na ba ta ɗan kunne da takalmin sallar da na siya mata sai pant da bara da na siya musu tare da Marwa sannan na diɓa mata shinkafa kayan miya kuma na ba ta kuɗi na ce ta kai ma Mamansu ta siya kayan miya su yi abincin salla tunda na wajen nawa an niƙa gabaɗaya na tafasa.   Yallaɓai na gida bayan ya ci abinci da nama yana falo yana amsa wayar ƴan'uwa nima 5k ya saka min kati ya ce na kira barka da sallah. Na samu kiran wasu yan gidanmu waɗanda ba su kira ba ni na kira su Alhajinmu dai da Gwaggo su na fara kira Nene itama na kira ta yi musu barka da salla sannan na kira Inna Mariya da su Kawu Nafi'u na yi musu barka da sallah. Har Yaya Murja ni na kirata Ma'u ce dai ita ta kirani kafin ni na kirata. Amma na kira Baaba ban ji mamakin da ta ce ba ta gane ni ba. Domin ba ta da lambata sai da na faɗa mata sunana bayan ma na faɗan sai da ta ce. "Wata Sadiyar? Kai tsaye na ce" Ta Yaya Sulen." Sannan ta ce au muka gaisa sama sama su Jidda ta tambaya na ce suna lafiya daga nan muka yi sallama. Da ga ita na kira Baba Aminu da Baba Sani suma na yi musu fatan an yi salla lafiya. Da ga su sai Rahila sannan na kira Yaya Muntari shima na yi masa barka da sallah. Bayan dangina sai na kira dangin Yallaɓai daman bayan su Alhajinmu na kira Nene na yi mata barka da sallah. Sai Mimisco Anty Maimuna na sameta mun gaisa amma Anty Bahijja ba ta ɗauka ba sai daga baya ta kirani. Na kira Faridan Tariq sai su Hauwa dukkansu na yi musu barka da salla Anty Zabba mutanen fatakol ita ta kirani muka gaisa har ta ke gaya min yara na nan gwammaja sun zo sallah. Da ya ke lokacin ya yi kusa an haɗu da biki ba lalle wannan sallan yan nesa su samu zuwa ba. A ranar Yallaɓai sai yamma ya fita zuwa Gwammaja kuma bai daɗe ba ya dawo washegari lahadi ban je ko'ina ba saboda ƴan yawon sallah. An kawo min su Sahla sai yaran Munnira sannan Jawaheer ta zo tare da ya'yan Anty Zabba da suka zo daga fatakol. Daga ɓarayina ƙannen Marwa ne kaɗai su ka zo min yawon salla daman su sun saba zuwa ban saka rai da su Antin  Yaya Murja ba domin na san in da suke zuwa. Na ba su nama da kayan fulawa sannan na yi shinkafa da miya da salat suka ci da za su tafi da yamma na ba su kuɗin adaidaita sannan da kuɗin barka da sallah. Sun tafi kenan sai ga su Firdausin Anty Balki su biyu ita da ɗiyar ƙanwar babanta suka ce mini daga gidan Yaya Abubakar suke har ina yi musu tsiyan sai da yamma ne za su zo mini? Su bari sai gobe mana.   Suna dai sunne kai ba su ce komai ba, Allah ya taimaka bayan mangariba sai ga Musabahu da Adnan daman ina ta tunanin wanda zai kai min su gida tare da Yallaɓai suka shigo gidan. Ganin su ya sa na ce su jira su in za su tafi su a jiye min su a anguwansu ko daga bakin titi ne. Sai wajen tara na dare suka tafi tunda bayan sun ci abinci suna falo suna hiran su na ƴan'uwa acan falon shi. Amma sai da na kira Yaya Balkin na faɗa mata su Firdausi na gidana zan saka a dawo da su. Jidda da Baby daman a gidan Mimisco suka yi ni ta kira ni ta ce Direba zai dawo da su. Gwammaja kuma sai zuwa gobe za mu je can mu yini. Su Musbahu sun tafi da Firdausi ba daɗewa sai ga Direba ya dawo da su Jidda gida da Nama da yawa a leda da cake har da su lemuka da kuɗi da yawa sabbin yan ɗari ɗari suka ce Daada ne ya ba su wato mijin Mimisco daman sunan da ƴaƴan shi da ita kanta Mimiscon suke kiran shi kenan. Ranar litini ya kama ukun salla tun asuba na tashi ni da Marwa waina za mu yi saboda zan kai Gwammaja zan kuma aika da shi Ɗorayi da Gandun albasa. Saude na kira waya na ce ta zo da safe ta taya mu aiki. Saboda ina da mataya ko kafin sha biyu na rana mun gama toya waina duka miya daman tun safe na haɗa ta. Yallaɓai ya siyo mana manshanu daman na zuba a cikin miyan ga kayan ciki ga naman rago sannan ga ƙashi. Miya sai tashin kamshi ta ke yi Yallaɓai na sauri zai fita Rano zai je za su haɗu da Uncle Abba da Tariq da suka zo sallah sai na zuba masa ya ci ya na santi sannan ya tafi amma sai da ya ba ni goron salla ta na 10k sabbin yan 200 goron salla da kuɗin kwalliya domin na yi masa ado kuma ya burgeshi.      Muna gamawa su Marwa suka gyara gidan saboda rage kaya Yallaɓai na ce ya yi mini gaba da su Jidda zuwa Gwammaja da wainar su ni daga baya sai mu taho da Marwa. Saboda daman ranar a can muke yini sai washegari yinin salla na huɗu kowacce sai ta je gidan su. Saude ma kuɗin a daidaita na bata bayan na diɓar mata na su wainar sai kuma na bata na gidanmu a babban kula na waina sai ledan da na saka Nama da kayan fulawa na ce ta kai ma Gwaggo in ji ni. Ni kuma sai da na sake wanka na sauya kaya na saka leshin da Yallaɓai ya yi mini na yi amfani da mayafi da jaka da takalmi kalan adon leshin jikina na saka ɗan kunnayena masu kyau da yarari na fito na yi ras da ni na san duk in da na shiga ba wanda zai raina ni. Da muka fito daga gida ba Gwammaja muka fara zuwa kai tsaye ba sai da na biya Gandun Albasa gidan su Mama na kai musu abincin salla da Naman salla sai kayan fulawan da na yi ban jima sosai a can ba duk na ga su Inna Mariya da sauran yaran su muka gaisa na yi musu rabon barka da sallah daman duk sallah ina kai musu abinci kuma ina zuwa tunda ni kaɗai ce mace a kano Amina ta yi nisa sai in wani abu ya faru ta zo. Ni ɗin ce na ke ƙoƙarin sada zumunci suma kuma suna da kirki duk abin da zai faru damu suna zuwa sannan Ya Auwal ma in ya zo garin ya kan je ya gaishe su kuma taimako dai dai gwargwardo ya na yi musu abin da bai gagara ba.   A can Gandun albasa muka yi azahar sannan muka wuce Gwammaja. A can na iske su Hauwa da Munnira gida cike da ƴa'ƴa da jikoki. Domin kaf ɗin su yaran gidan sun zo sai dai waɗanda ke nesa irin su Jafar da Muhammad sani Yaya Usman daman sai yaran shi kawai ne suka zo. Su Anty Bahijja gabaɗaya suna nan da gayyarsu ban ga Gimbiya ba sai na ji Anty Maimuna na faɗin ta tafi Rano ɗazu da safe. Naja'atu ta zo amma ina gidan ta yi shirin tafiya gidan iyayen mijinta can za ta ƙarishe yininta Halima ma ta zo da yaranta ta yi kiɓa ita da jajariyarta mai kyau da ita har na ɗauke ta. Lokacin da na zo Nene ta kwanta sai da ta tashi muka shiga muka gaisa na kai mata Nama da kayan fulawan da na zo da shi ta yi ta saka mini albarka. "Sadiya Tafida ya kawo mana waina. Sannu da aiki Allah ya saka da alheri." Na amsa da Amin haka Nene ta ke komai sai ta yi maka godiya. Daman su Hajiya iya duk na shiga mun gaisa na kai musu na su Naman salla, tunda haka na ke yi duk shekara sai dai Yallaɓai in ya je ya ji suna masa godiya nima haka suka yi ta min godiyar waina, Suwaiba har tana min tsiyan shi ya sa Yaya Tafida ya fara ijiye tumbi ashe daɗin girki na ne ina ta mata dariya. Maman farko ta ce ai ta diɓa ta boye za ta ɗumama ta ci da daddare wainar ta yi mata daɗi. Da ya ke shekara biyu kenan ban yi waina ba wancan shekaran tuwo na yi musu da miyar agushi wannan ne na ce bari na yi waina saboda a sauya baki. Kowa ya ganni tare da Marwa sai ya ce Sadiya ina kika samo yar budurwa mai hankali da kunya haka? Saboda da yara sun ɓata ɗakin Nene za ta ɗauko abun shara ta share. Ga shi ta na son yara goye take ma da ɗiyar wajen Halima har Nene sai da ta yi mgana na ce ɗiyar Yayata ce Marwa na tuna ma Nene ai ta na zuwa gidana hutu kuma na sha zuwa da ita gidan nan.   Nene cikin mamaki ta ce" Allah Sarki girman ɗan mutu ba wuya. Ita ce ta girma haka? Ina dariya na ce ma Nene wallahi ita ce. Nene ta yi ta saka albarka Anty Bahijja ta saka mana baki da tambayan a ina take karatu na ce a tsafe makarantar koyin aikin jinya sai ta taɓe baki ba ta yi mgana ba ni kuma ban damu ba sanin halinta akwai son ta ji ƙwaf kuma in an faɗa mata ta nuna kamar ba ta so ta ji ba. Ganin ɗakunan su Nene cike da ƴayansu zuwa jikokinsu sai mu surukan gidan muka tsame kan mu zuwa ƙasa shashen su Jawahir ba ta nan ma tun safe an ce ta tafi can gidan kakaninta na bangaren uwa ita da Adnan. Da ni da Hauwa da Muniira muka zauna acan muna ta hira muna shewa. Muna ƙara ma junan mu sani kan abin da bamu sani ba. Muna mgana kan kayan gyara ne Munnira ke faɗin rabon ta da wani gyara tun haihuwan Mufeedan ta. Cikin mamaki na kalleta kafin na ce" Ke kam Munnira me ya sa me ki? Mufeeda yanzu ai ta shekara uku ko Hauwa? Na faɗa ina kallon Hauwa wacce kafin ma ta bani amsa Muniiran ta karɓe da faɗin" Shekaranta uku da wata biyu." Jinjuna kai na yi kafin na ce" Ki ce waje duk ya yi tsatsa. Gaskiya ba ki kyauta ma Nasir ba." Na faɗa ina hararanta ita kuma tana dariya kafin ta ce" Ke ni fa gani na ke yi duk ba sa wani yi asara ne. Kuma ni in dai ba shi zai ba da kuɗin a siya ba sai na ke ƙyashin fidda kuɗina na siya wallahi."   Mamakin Munnira ya kamani daman har yanzu akwai mata masu tunani irin na Munnira? Ko dai ta yi ma kalmar gyaran mummunan fahimta kamar yadda wasu matan suka yi ma kalmar. Ban samu zarafin mgana ba Hauwa ta karɓe mganar da cewa" Haba Munnira ke da kan ki ma? Mata ai yanzu sun waye kowa ta san abin da za ta sha ya gyara ta ba wai kuma wanda zai zama cuta gare ta ba. Kuma kin manta hausawa na cewa in kana da kyau sai ka ƙara da wanka? Kina da yaƙinin tun gyaran da kika yi da haihuwan Mufeeda ya na nan a jikin ki? Haba ai yakamata dai ko yaya ne ki ɗan ƙara gyarawa ko dai baki sha komai ba yan kayan marmarin nan da za su ƙara miki cika da Ni'ima."   Daga ni har Munnira baki muka saki muna kallon Hauwa. Sai da ta gama bayaninta ta ga irin kallon da muke yi mata sai ta ji kunya ta kauda kai tana faɗin" Me ya faru kuke kallona? Ko ba gaskiya na faɗa ba." Ina ɓoye mirmishina na ce" Kin faɗi gaskiya Hauwa uwargida a gidan Mutaƙƙa shi ya sa har gobe bai kallon kowa sai ke ashe sirrin da kika riƙe kenan? To mu ma a ɗan gaya mana sirrin mana ko Muni? Na faɗa

Chapter 28 of 31