Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kaina da karfi zan wahala sai kawai na saki na miƙa masa kaina tare da ragamar rayuwata bayan nima na saka duka hannunawa na zagaye ƙugun shi.   Mun daɗe muna sumbatar juna har sai da ya gaji sannan ya sake ni. Ya na maida numfashi ina maidawa. A tare muka kalli juna gira ya ɗagamin kafin ya ce" Amarya ta." Hararan shi na yi kafin na ce" Haka ake Ango kai duk ya fara furfura? Ni jarumi ne angona."   Na faɗa ina gyara zaman rigata da ya zame min. Wata dariya ya yi kafin ya ce"Bari in yi wanka yau ƙila da rabon har Gwaggo sai ta zo jinya ina ga."   Ina jin haka na ɗaga hannu ina faɗin" Yallaɓai na." Rigarsa ya cire yana yar ɗariya ya ce"Sadiya ta." Na san halin shi wallahi in ya so mugunta in na shiga hannu har sai na dawo ina magiya. Har mamaki na ke yi Yallabaina kullum kamar ƙara masa ƙarfi ake yi. Duk da mun yi aure yana tashen samartaka.  Amman yanayinsa na yanzu ya na ninka yanayinsa a baya ne.   Bin sa a baya na yi ina faɗin" Yallaɓai gajiyan tafiya ba ta sake ni ba. Ko na kwanta ne?   Tiolet ya shige ya na faɗin"Ki kwanta mana na hana ki ne? Gwara dai ki yi ma kanki faɗa ki ɗauko kazar amarcinki a fridge ki fara ci kafin na fito. Zan karɓi maiƙon kazata a daran nan in sha Allahu."   Nakwa nakwa na yi da fuska har lekoni ya yi yana dariya. Ba ni da mafita kitchen na fita na bude fridge ɗin na ga kazan dankwaleliya ce a faranti na sako mana kazar dai ta bakin shi ta sha maiƙo ga albasa da kabeji.   Ruwa na ɗauko mana da lemu bedroom ɗin na kawo mana ba daɗewa sai gashi ya fito daga wanka ɗauro da Babban Towel a ƙugunsa ya ganni zaune saman cafet da farantin kaza a gabana.   Ya kalleni sai ya saka dariya ni kuma sai na gimtse fuska cikin nishaɗi ya ce" Ke fa kika ce na taho da kazar amarci yau za mu tuna amarcin mu. Kin ga fa ke kika saka mini rai da kwaɗayi."   Shuru na yi kawai na fara gutsiran kazan ina ci, shima sai da ya shafa mai ya saka gajeren wando sannan ya zo ya zauna ya na tayani cin kazan tun ina share sa har na saki yana bani a baki ina bashi mun ci kaɗan ba da yawa ba. Sannan na kwashe komai na maida kitchen sauran kazan kuma na saka a fridge.   Wanka na shiga na gyara jikina. Bayan na fito na shafa mai na saka humra sai na saka wata rigar barcina ƙarama mai buɗewar gaba Yallabai na saman gado ya na jirana da na tsaya masa yanga ma tasowa ya yi yana faɗin" Kin san dai ina da karfin iya ɗaukan ki ko? Cak ko ya ɗaga ni sama amman sai da ya yi nishi. "Wai wai. A gaishe da Yusuf." Ya faɗa ya na jinjina nauyina ni kuma sai na kwashe masa da dariya na ƙara hantsila kafata da ya sa na gagari karfinsa mu ka faɗa kan gado. Bin sa na yi na danne ina faɗin" Wayyo karfin Yallaɓaina ya fara ƙarewa." Ya na jin haka ya mirgina ni na dawo kasan sa ya kalleni sai kawai ya girgiza kai ya sauka daga kaina. Gadon ma ya sauka gabaɗaya ya je ya kashe hasken ɗakin sanɗa ya fara yi in ganin duhunsa na yi gefe ina dariya ina faɗin" Yallaɓai wasa fa nake yi" Ban tsira ba sai da ya yi sufa ya dira kaina a saman gado. Ya turmusheni yana faɗin" Ƙarfin Yallaɓai ya ƙare ko? Ina ta dariya. Haka muka dinga mirgina daga kudu zuwa yamma kafin dai mu natsa sai da muka yi wassanin da muka saba. Ni da Yallaɓai muna da wasu abubuwan da in ba mu yi ba ba ma jin daɗi. Yallaɓai ya ɗauke ni a komai na shi haka nima, za mu yi ta wassani muna dariya kafin mu faɗa farantama juna, cakulckuli ya rika yi mini kamar zan shiɗe sannan ya bi ni ya danne ya haɗe bakin mu waje ɗaya.   Baki shi ke yanka wuya. Domin da gaske amarcin aka sake maimaitawa. Ni fa har da su Mama na ke kira da asuba Yallaɓai na ta yi min dariya ko kallon shi ban yi ba. Dirza na sha a hannun shi har sai da na gane ba ni da wayau ta bakin shi ya ce ya goge reni ne ina tunanin ƙarfin sa ya kare har ce min ya yi ko mata goma ne budare zai iya da su a dare ɗaya ai sai na saki baki ina kallon shi. Domin ai Yallaɓai ya fi ƙarfina.   Ranar bai fita ba a gida muka yini tare. Kuma ta bakin shi maiƙon jikina duk sai da ya gama siɗe shi. Sai dare muka samu fita zuwa ɗorayi muka je na duba Alhajinmu daga nan na shiga gidan su Saude na yi ma Balaraba godiya.   Washegari na shirya ya sauke ni gidan Halima na ƙara gaishe ta. Tunda ban samu suna ba na kuma ɗan jima tun da har girki na yi mata ita kaɗai a gidan ga jego. Jawahir ce ke zuwa mata kuma ta koma makaranta sai ƙanwar mijinta itama kuma yau ɗin ba ta samu zuwa ba. Muna ta hira a bakin ta ma na ke jin wai Yaya Usman zai ƙara aure mijin Zabba'u. Na girgiza da jin zai ƙara aure. In na duba yadda Anty Zabba ta ke son mijin nan na ta bata iya haɗa shi da kowa ga ta da kishin tsiya. Halima na faɗa min saboda maganar auren bai faɗa mata har sai da aka saka rana ta yi ta tashe tashen hankula daga karshe ma ta yi yaji a mganar da ta ke gaya min ma tana gidansu anan kano.   Sai uku na rana na koma gida saboda girki. Saude suna da walima sauka a islamiyarsu ba ta zo ba. Ni dai na yini ina mamakin auran Yaya Usman ko alama Yallaɓai bai faɗa mini ba Hauwa ma ina ga ba ta sani ba. Munnira mun kwana biyu ba mu waya ba. Ita kuma daman Anty Zabba ɗin ba ma yi sosai iyaka in an haɗu a gaisa ne kawai tunda ba ma garin suke ba in ba wani sha'ani ko rashi ba sai mu shekara ba mu ga juna ba. Daman mutuniyata Hauwa ce sai Munniran da ba kamar yadda muke da Hauwa ba.   Mu da ɗan yawa mu surukan a gidan marigayi Alhaji inuwa. Mu shidda ne har da Amaryan muhammad Kabir da bai daɗe da yin auran ba. Shi likitan jini ne yana katsina yana aiki da medical center can ya ke zaune da matarsa. Ni da yake kowa ya san halina ba ni da shisshigi kuma in ma ka shige min ba lalle na iya mu'amala dakai ba sai in Allah ya haɗa jininmu to ballatana ma mai hali irin na Anty Zabba da shigen takama da ji da kai. Ko don ta na taƙamar mijinta na ta kuɗi sannan iyayenta ma wasu ne babanta tsohon alƙali ne a jihar kano mahaifiyarta kuma daga masarautar zazzau ta ke. Ni iyakata da ita in an yi wani abu da ya kamata na kira ina kiranta itama an aka yi min rasuwa ko rashin lafiya ta kan kirani ta gaishe ni. Ba sanayyar da zan iya kiran ta na ji labarin abin da ya faru ko Halima saboda ta na yar gida ce shi ya sa ta ji labarin.   Har wajen biyar na yamma ina ta tunane tunane na kasa ma tashi na ɗora girki. Na kira wayar Hauwa ba ta shiga na ji kanun labari in ta sani sai kuma ban same ta ba. Ni kuma ba na son kiran Munnira ko yaya ne ina ɗan rike girma na, ganin har su Jidda sun kusa dawowa makaranta ban yi girki ba ya sa na tube na shiga kitchen store na fara dubawa sai na ga gabaɗaya kayan abinci sun yi ƙasa shinkafa ba ta wuce tiya daman shine buhun ƙarshe sannan taliya kwara biyu macaroni ma ya ƙare indomie ma ina ga tun ina Zariya ta ƙare tun da daman ko da zan tafi ƙawayanni na bari.   Shinkafa tuwo ce kawai ta rage da ɗan yawa. Na yi tagumi ina kallon store ɗin ko kayan su maggi robobin sun yi ƙasa na tuna suma tun watan can da ya gabata ba a siye su ba. Kayan abinci kuma daman in Yusuf ya samu kuɗi ya kan siya da yawa haka in shinkafa ne buhu biyu uku haka taliya da macaroni katan uku ko biyu da yawa dai yadda za mu daɗe ba mu nema ba. Ina tunanin gashi kayan abinci ya ƙare kuma Yallaɓai bashi da kuɗi. Ajiyar zuciya na sauke kawai a raina ina fatan kafin komai ya ƙare Allah ya kawo wata mafitar. Tunanin yin Tuwo ya kawo mini acikin raina sai na duba naga ina da kuɓewa ɗanya da Gwaggo ta ba ni wacce ta taho da ita daga Yashe ne sau ɗaya na yi amfani da ita tunda Yallabaina ba ma'abocin cin tuwo ba ne sai bayan lokaci lokaci haka.   Ban yi kai tsaye ba sai da na koma ɗaki na kira Yallaɓai na na ce masa yau Tuwo na ke so na yi ko yana so na dafa masa wani abincin ne?   "Sadiya na daɗe ban ci tuwo ba. Ina marmarin shi." Amsar da ya bani kenan. Sai na yi mirmishi kafin na ce"To zan ɗora tuwon yanzu. Ka taho min da ƙashi ko Nama wanda zan yi miyan dashi." Sai ya amsa min da toh, tunda yau ba Rano ya je ba Office ya je.   Da ƙarsashina na koma kitchen na ɗora ruwan Tuwo a saman Gas. Yara kuma na yi tunanin su sha wani abun kafin na gama girkin, ina cikin tunanin su sai na ji buga get na san sune tunda shidda saura a lokacin. Ni na je na buɗe musu kofa har Salisu ya tafi bayan ya sauke su. Tare muka shigo cikin gida da su ina tafe riƙe da jakar Baby da lunch box ɗin ta.   Bayan sun sauya kaya na ce su zo su sha ko goldemorn ne tunda corflex ya ƙare shima sai kwali kafin in gama abinci Baby ce ta biyo ni kitchen ɗin ta na faɗin" Umma me kike dafawa? Kai tsaye na ce"Tuwo." "Tuwo?   Ta faɗa ta na kwabe fuska. Sai ta bar ni ina ta mata dariya daman na san ba ta son tuwo sai na lallasheta na cewa ina da sauran miya zan ce ma Yallaɓai ya taho da buredi sai ta ci dashi jin haka yasa  ta yi tsallen murna. Ko kafin mangariba na gama Tuwo tunda na shinkafa ne har na mulmule a leda Jidda ce ma ta taya ni ɗaurewa a ledan muna yi ina nuna mata in da ba ta yi dai dai ba ta na gyarawa.   Miyan na ɗora daman na yi greting ɗin kayan miya daddawa daman ina da dakakkiya ban mantawa Inna Mariya ta aiko mini dashi. Sai na ɗan zuba ruwan da yawa saboda ban san lokacin da saƙon Yallabai da zai iso ba. Tare da yarana muka yi sallah a ɗakinsu na zauna muna karanta azkar tare sakamakon na daɗe ban yi musu karatu ba ya sa na ce kowacce ta ɗauko Qur'ani mu yi karatu.   Na biya ma Jidda na ta Baby ne muke yi lokacin da Yallaɓai ya shigo ɗakin na yi mamakin ganinsa yau da wuri haka. Ya na tsaye bakin kofa sanye da wani farin yadi kansa da hula ta zanna mai kalan aikin jikin yadin. Mirmishi a saman fuskarsa ga leda a hannunsa ɗayan hannun kuma key ɗin mota da sai wayarsa. "Sannu da zuwa."   Na faɗa ina kallon shi lokaci ɗaya nima ina maida masa martanin mirmishin. Baby ce ta tsshi ta isa wajensa ta na masa oyoyo Jidda kuma daga zaunen ta ce"Sannu da zuwa Abba." Ya amsa lokaci ɗaya yana ce ma Baby" Kar ki ɓata jikin ki." Ya faɗa ya na nuna mata ledan hannun shi. Miƙewa na yi na isa wajen shi ina faɗin" Ban ɗauka za ka dawo yanzu ba. Na ma za ta Musabahu za ka aiko."   Kai ya girgizamin kafin ya ce"Kawai na ga ba wani aiki ne shi ya sa na ce bari na dawo gidan kawai.' Ya faɗa ya na miƙamin ledan na karɓa lokaci ɗaya ina kallon Baby da ke riƙe da hannun babanta."   "Je ku gama karatun Baby."   Kumatunta ya shafa kafin ya ce"Je ki. In an gama karatu ki zo ki karɓi tsarabanki." Jin haka yasa ta wuce da gudu ta na dariya muka bita da kallo gabaɗayanmu cikin ƙauna gaban Jidda ta koma ta zauna ta ɗauki Qur'aninta ta na karantawa da karfi. Ni da Yallaɓai muka fita ina gaba ya na bin bayana shi ya rufe musu ƙofar.   Tare muka shiga har kitchen ina buɗe naman. "Ko da na je duk sun gasa sai wannan na samu na 3k ne zai isa? Yallaɓai ya faɗa ya na sunkuyo da kansa ta ɓarayin wuyana. Kai na jinjina kafin na ce" Zai yi mana. Miya ce ba yawa sosai."   Sai da na saka naman duka a cikin miyan ina juyowa Yallaɓai ya rumgumeni ta baya lokaci ɗaya ya na faɗin" Yau ko ɗan hug ɗin oyoyo ba a yi min ba ko? Ina mirmishi na ce"To ka jira ka ga ban yi maka ba ne? Na faɗa ina wucewa wajen sink in da na buɗe famfo na tara hannuna ina wankewa shima sai ya sunkunyo da kansa ta wajen wuyana lokaci ɗaya ya zuro hannayensa duka biyu ya kama nawa yana murzawa a tare ruwa na zubar mana. "Nima a wanke min hannun mana Sadiya ta."   Ya faɗa cikin raɗa sai na yi yar dariya na karɓi hannun ina murza masa na wani lokaci kafin na kashe famfon ƙaramin Towel ɗin da ke kitchen na ɗauka ina goge masa hannunsa. Nima na goge nawa hannun sannan na yi masa rumgumar da ya yi min ƙorafi shi kuma ya ɗago ya sumbaci goshina.    Ta falo muka fita na ɗauko masa wayarsa da key ɗin mota muka wuce cikin ɗaki. Wanka ya ce zai yi amman da ruwan sanyi saboda garin akwai zafi zafi mun fita damina an fara zafin nan na fiddan dawa. Shi ya shiga wanka ni kuma sai na koma kitchen ina duba miyata da na saka mata kalolin maggi. An kira isha'i Yallaɓai bayan ya fito wanka ya saka Jallabiya ya tafi masallaci ni kuma da yara muka yi a gida. Da zai shigo ne ya shigo da ice cream ɗin da ya siyo ma Baby ita kuma Jidda wani bickit mai madara mai ɗan karan daɗi lokacin har na kaɗa miyata na gyara kitchen ɗin ina jin shigowarsa na faɗa wanka.   Har na gama shiryawa yana falo tare da yara. Ni kuma sai na tsuke cikin riga da wando. Wando ya kamani ta sama amman ya na da buɗewa ta ƙasa rigar ma tana buɗewa ta ƙasa. Wandon baki ne rigar fara sai na yi amfani da bakar hula a kaina ban fesa turare jiki kuma na shafa humra har da jan baki na saka na yi ɗas da ni ina fitowa falo wajen ya ɗauka da kamshi. Jidda na kira ta tayani ɗaukan kaya zuwa Dinning. Baby ta samu ice cream tuni ta manta da mganar Biredi ni kaina na manta ban kira Yallaɓai ban ba a lokacin.   Gabaɗayanmu muka haɗu a saman dining ɗin ban da Baby da ke can falo ta na kallo. Da kaina na saka ma Yallabai guda biyu na zuba masa miyar da ta ji naman rago Jidda ma ta saka ɗaya ta ce ya isheta nima dai ɗayan na saka saboda na ci abinci a gidan Halima. "Sadiya ta. Kin yi kyau.'' Haka Yallaɓai ya faɗa yana kallona da mirmishi a saman fuskarsa. Fari na yi masa da ido kafin na ce"Thank you Yallaɓan Sadiya." Jidda na cin tuwon ta ba ta ɗago ba amman ta yi mirmishi. Yallaɓai ya kalleta kafin ya ce"Hajiya Nene ko Umma ba ta yi kyau ba? Da sauri ta ce" Ta yi kyau sosai Abba." Ya na ƴar dariya ya ce"To ai shi ne na yaba kuma sai na ga kamar ta cancanci tuƙwaici ko?   Jai ta gyaɗa masa ta na mirmishi ina jin su ban ce komai ba sai da na ji ya ce"Kar ki damu zan ba ta kyakyawan tuƙwaici" Ɗagowa na yi ina hararanshi kafin na saka kafata na taka masa kafa sai ya janye yana dariya. Jidda dai ta gama cin tuwonta ta ɗauki filet ɗin ta bar mana Falon sai da ta fita na kalle shi kafin na ce" A gaban Jiddan ka ke mganar tuƙwaici? Kai ya gyaɗa kafin ya ce"To miye a ciki? Ai ba ta san irin tuƙwaicin da kike karɓa ba madam" Wani kallo na yi masa da ya sa sai da ya ƙware yana shan ruwa na yi masa gwalo ina dariya amman sai da na saka hannuna ta bayansa ina shafawa ganin ya sarƙe da yawa. Wani ruwan na sake zuba masa na bashi ya sha sannan ya ɗan lafa masa.   Kallona ya yi kafin ya ce" Ki riƙa bari sai mun shiga ɗaki sai ki yi mini wannan kallon kin ji ko? Ina dariya ban yi mgana ba shi kuma ya ce" Saboda tsaro ba."   Murguɗa masa baki na yi shi kuma sai ya kaɗa kai kafin ya ce"Murgaɗa da kyau za ki yi bayani ne yarinya in na fara gyara miki service ɗinki har da garambahul." Marairaicewa na yi ina faɗin" Mai jan mota ya tokare boda yau Yallaɓai." Kai tsaye ya ce"ko jan jirgi ne yau sai na gyara miki service ɗin ki." Dariya na yi shi kuma yana faɗin" Yi dariya da kyau." Ni ko na ce to kuka zan yi? Ya na min wani kallo ya ce" A'a shi wannan ki bari sai anjuma."   Kafarsa na taka ina faɗin" Yallaɓai cikin shagwaɓa " Da sauri ya miƙe yana faɗin" Yau wannan shagwaɓar taki ba amfanin da za ta yi miki " Tiolet ɗin falon ya shiga ya wanke bakin shi da hannunshi bayan ya fito ya wuce kan kujera ya zauna ya dauki remot ya kunna TV ni kuma sai na tattara komai na maida kitchen ɗin ina gyara wajen daga can zaune Yallaɓai ya ce. "Ki zo mu yi hira. Hiran saurayi da budurwansa." Ina mirmishi na ce"Sadiya da Yusuf ɗin ta ba." Kai ya jinjina kafin ya ce" ko dai Yallaɓai da Sadiyarsa? Na ce ai duk ɗaya. Sai da nima na wanke hannuna da bakina sannan na leƙa su Jidda na ce tara ta yi su kashe kallon nan su je su kwanta in suna da aikin makaranta su ɗauko su yi kafin su kwanta. Jidda ta amsa min da toh sai na rufe musu kofar na dawo wajen Yallaɓai shi kuma sai ya miƙa min hannu na taho ya yi min mazauni saman cinyarsa ina zama ya kishingiɗa nima sai na lafe kaina saman ƙirjinsa ina wasa da tsillin gashin wajen tunda ya cire jallabiyar daga shi sai dogon wando shi kuma sai ya cire min hula yana wasa da gashina gefe ɗaya kuma yana min susan kunni dukkanmu mun yi shuru muna jin bugawar zuciyan juna ga ƙaran tibi da iskar fanka na ƙaɗawa. Wani farinciki na ke ji. Zuciyata na bugawa da sauri da sauri kamar yadda shima na shi ke bugawa. "Yallaɓai na." Na kira sunan shi cikin wani salon da na san ya na kunna shi. "Uhm." A saman leɓensa ya amsa min. "Ina son ka." "Ina ƙaunarki Halimatuna." Haka Yallaɓai ya faɗa lokaci ɗaya yana ɗago kaina. Bakinsa na nufa shima sai ya sunkuyomin a tare muka tarbi juna muna sumbatar juna cikin wani shauƙi da muradin junan mu. *Janafty* *TURKEN GIDA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *SADAUKWRWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA (MOMMY)* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. *🅿️09* Mun daɗe muna sumbatar junanmu cikin wani shauƙin da a cikin zukatanmu kawai muke jin tasirin yanayin. Mu ka saki juna lokaci ɗaya kuma muka bi juna da kallo muna sauke numfashi a jejjere.   Mirmishi ya yi mini nima na mayar masa da martanin mirmishinsa. Tallafo kuguna ya yi ni kuma sai na ƙara maƙale hannuwana a a saman wuyansa jawo ni ya yi na sake lafewa a saman ƙirjinsa ina jin yadda ya ke ɗan sauke numfashi kaɗan kaɗan kamar wanda ya yu gudun tsare.   "Yallaɓai.." Na kira sunan shi bai amsa ba sai ya kalleni kafin ya lakace min hanci da hannunsa guda ɗaya yana faɗin" Uhm" Hannuna na kai saman Sajensa ina shafawa har zuwa ƙasa wajen gemunsa da ya fara fitowa domin yana yawan askewa yana dai barin kaɗan haka ina shafa gemunsa zuwa sajensa ina faɗin. "Ka san kai ne namiji na farko da ka ruguza dukkan tunanina. Kowa ya san burina na sai na gama jami'a na samu aiki zan yi aure. Amman tashin farko ina haɗuwa da kai ina yar aji ɗaya a jami'a ka susuta tunanina da ya sa na amince da kalamanka na aure ka bayan na yi fatali da mafarkina da burina gabaɗaya."   Na ƙarishe faɗa ina kallon shi. Shima ni yake kallo kafin ya yi mirmishi ya ce" To ni ɗin wasa ne? Kin ga zangaɗeɗen saurayi jikan mutanen Rano. Kin san in kika bari na suɓuce miki samun kamata ai da wahala shi ya sa kika yi amfani da maganar hausawa da suke cewa in dama ta zo maka ka yi amfani da ita saboda wataƙila in ta suɓuce maka har abada ba lalle ka ƙara samun damar ba" "Allah ko?    Na faɗa ina kallonsa da ƴar dariya. Shi kuma sai ya ɗaga min gira kafin ya ce"Kema kin san gaskiya. Samun jarumi kamata a cikin maza ai da wahala shi ya sa kika yi wuf da ni da sauri kafin ki makara. Ko wata ta yi miki ƴar kafa ba."   Ina dariya ina jan gashin sajensa ya yi shii alamun zafi ya na ƙokarin riƙe min hannu na ce" To me ya sa ka yi ta mini na ci sai da na yi maka kwatancen gidanmu? Kai ma ai kasan in ka bari na subuce maka samun kamata da wahala." Na faɗa ina masa fari, bakina ya sunkuyo ya sumbata lokaci ɗaya ya na faɗin" Ɗan bakin nan na daga cikin abin da ya fara jan hankalina a kanki. Da yanayin mganarki da takun ki. Kai kin iya jan Aji kin ba ma bawan Allah wahala ranar da na koma gida daƙyar na iya barci. A time ɗin bani da burin aure har sai na samu aiki na gina gida na gina kaina amman tun ranar da na fara ganinki kika ruguza mini wannan tunanin. Ke ce silan da ya sa na yi fito na fito da kowa akan aure saboda ai suna ganin ban kai ba me na tara me na ke da shi sannan a tunaninsu na yi yaro a lokacin ba su san a halin da na ke kwana ba ne shi ya sa.'   Ya ƙarishe faɗa yana wani sauke nunfashi ni kuma sai na ƙyalƙyace dariya taya ni ya fara yi yana cewa" Allah. Azumi fa na ke yi duk litini da al'amis ai ya kamata su gane ina son aure. Daga karshe dai na fito musu a Mutum na ce ina son na yi aure saboda ina da karfin sha'awa kuma ina tsoron faɗawa halaka. Nene na jin haka tace ku bar Tafida ya yi auran nan Zuwaira shi ne alherin mu gabaɗaya."   Shi ke tuna labarin a bakinsa amman ni kuma ina hasaso lokacin a cikin idanuwana. Tabbas lokacin an sha gwagwarmaya sosai kafin auran mu amman gashi komai ya zama tarihi. Mun yi aure har da albarkar ƴa'ƴa biyu

Chapter 12 of 31