Goron salla ai a gida ake ba da wa Anti. In kina son goron salla sai ki zo gidana ki karɓa. Yanzu ma kin makara salla ta wuce sai dai kuma ta layya in muna raye."
Ita Anti ba ta damu da mgana ta ba cikin dariya ta ce" Kai Anty Sadiya."
Nima ina mata dariyan na ce" Ƙwarai Anti. Salla layya in kina son goron salla ki zo gidana da wuri ni kuma sai na cika miki jaka da kuɗi."
Gwaggo na bakin famfo tana alwala ta na jin mu ta dai yi mirmishi ba ta saka mana baki ba.
"To Anty Sadiya in sha Allahu zan zo. Wannan salla a gidan Umma Ma'u na yi shi ya sa."
Ina mata mirmishi na ce" To ai shiken nan na ma san Ma'u ta cika miki jaka da goron sallah ba ki buƙatar tawa ko?
Har ga Allah ni a wasa na yi mganar kawai sai gani na yi Ya Murja ta bankaɗo labule ta fito da hijabi a jikinta da alamun ta idar da salla ne kallona ta yi daga sama har ƙasa nima ko cikin mamaki na ke kallonta sai kawai ta daka ma Anti tsawa ta na faɗin ta wuce ta je ta yi sallah sai yarinyar ta wuce ɗakin Gwaggo da sauri.
Kamar zan yi mgana sai na fasa na fara tafiya wajen famfo Gwaggo ta taso za ta shiga ɗakinta.
"Ke Sadiya.."
Ya Murja ta yi mini kira cikin gatsali sai na juya ina kallonta cikin mamaki. Ba ma ni kaɗai ba hadda Gwaggo.
"Me ya faru Ya Murja?
Na faɗa ganin kamar tana sakin huci kawai sai ta nuna ni da yatsa ta na faɗin" Daga yau in kina so ki yi min rashin kunya ki zo gare ni kai tsaye ne ba sai kin rakuɓe a jikin ƴa' ta kina gaya min mgana ba. Ba na son rashin kunya."
Galala na yi da baki ina kallonta kafin na samu zarafin mgana Gwaggo ta tsawarta da cewa" Murja me kuma ya kawo wannan mganar?
A fusace ta ce" Ba ki ji mganganun da ta ke faɗa ma Anti ba ne? Ta nuna kamar da gayya ne ban tura Anti gidanta ba na tura ta gidan maƙiyarta Ma'u ba. Duk na fahimci mganganunta."
Gwaggo ta yi tsaki kafin ta ce" To ni ban ji haka ba. Mganar su kawai suke yi na tsakanin uwa da ƴa."
Nan fa Ya Murja ta ce ita fa k a taufau da ita na ke yi. Ƙara nuna ni ta yi da yatsa kafin ta ce" Daman ba tun yau ba kin sha faɗan wai na fi son Ma'u da ke da ita kawai na ke shiri yayana ma gidanta suka sani. To yadda kika faɗan ne domin Ma'u ta fi ki ladabi da biyayya sannan ita ta ja ƴa'ƴana a jiki ke kuma da ba ƙi kaunar su ba ki ja su a jiki ba. Kin ga ko kar ki ga laifin su in ba su je in da kike ba. Gidan kuma Ma'u da ki ke jin haushin suna zuwa yanzu suka fara zuwa. Sai dai baƙin ciki ya kashe ki Sadiya"
"Murja me ye haka don Allah.?
Ya Aina bayan ta fito daga ɗakin Mama itama sanye da hijabi ita da Ya Balki da Rahila. Ma'u dai ba ta fito ba ni kuma tsabar mamaki ma na kasa magana.
"Ya Murja Alhajimmu na ciki fa. Gaskiya wannan ba girman ki ba ne. Sadiya fa ba da ke ta ke mganarta ba."
A fusace Ya Murja ta ce" Ba za ku gane ba ne. Ni na san ga in da ta dosa. To me ye na damuwa don ƴaƴana ba su je in da ta ke ba. Marwa da kika zaɓa kina so ita ai kin gayyaceta kuma ta je suma in kika nuna kina so su je ɗin za su je."
Sai a lokacin na fahimci haushina ta ke ji saboda Marwa. Kai wannan mata ta ɗoramin karan tsana.
Ba na so na yi hayaniya saboda Alhajinmu kawai sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Ki yi hakuri Ya Murja na ga ƙin ɗau zafi har ga Allah ba da wata munafa na faɗi mganar da na faɗa ba. Amma in ta ɓata miki rai Allah ya baki haƙuri. Mganar Anti na zuwa gidan Ma'u ban taɓa sawa a kaina ba domin da ni da Ma'u duk ɗaya ne. Ke ma kuma ina so ki gane wani abu da Anti da Marwa ɗaya suke a wajena ba Bambamci."
Ina gama faɗin haka na juya na wuce wajen famfo ina taran ruwa a buta. Na san dukkansu sun yi mamakin sanyina har sai da Gwaggo ta ce" Shike nan Sadiya kin gama magana. Ke kuma Babba kwabo kin ji kunya tunda har yau Sadiya ta fi ki hangen nesa."
Ganin ban kulata ba ya sa ta koma ɗaki fuu. Kuma kowa ita ya ba ma rashin gaskiya a wajen. Sai bayan da na ɗauro alwala na shigo cikin ɗakin ne Ma'u ta ke ce min" ki yi hakuri Sadiya ki fahimci Ya Murja don Allah itama ba da wata munafa ta yi miki mganar ba.'
Kallonta kawai na yi ni kam wani makircin Ma'u ne ban gani ba sai kawai na ce" Bakomai. Ita za ki ƙara ba ma hakuri saboda na ga kamar ta ɗau zafi da ni."
Ina gama faɗin haka na saka Hijabi na ta da salla. Bayan na idar sai muka ci abinci na ga dai Ya Aina ta keɓe da Ya Murja na kuma san faɗa ta ke yi mata shi ne na ga ta ɗan saki ranta a raina na ce matar nan me na yi mata wai ta tsane ni ne?
Muna cikin cin abinci sai ga Ya Abubakar ya shigo ganin abinci kala kala muna ci ya sa ya ce"Kai. A ina aka samo abinci nau'i nau'i haka kamar an samu sabon restaurant?
Rahila ce ta faɗa masa kowaccem mu ta dafo abinci daga gidanta sai shima ya samu waje ya zauna ya na faɗin" To shi ne ana wannan shagali aka manta da ni? Ni ne fa the head of the family"
Ya Balki ta ce" Mun ɗauka Zaituna ta yi maka kyakyawan beta kafin ta fito gida"
Ta faɗa ta na kallon Zaitunan da ke ta cin abincinta jin an taɓo bangarenta ya sa ta yi saurin cewa" Laa shi ya ce in taho ba sai na tsaya na yi abinci ba."
Rahila ta ce" Ehem daman na san za a rina."
Yaya Aina ke faɗin" Ke kam Zaituna ban san yaushe za ki wayau ba. Ko mu kin ga mun taho ba mu yi girki ba? Ga shaida nan tunda gashi nan kina ci in da kin dafa kafin ki fito mijin ki zai zo ya na neman abinci?
Kanta na kasa ba ta yi mgana ba Yaya Abubakar ya wani girgiza kai kafin ya ce" Ƙyaleta Aina ta yi lokaci ne."
Daga haka kawai ya miƙe ya ce ya na ɗakin Alhaji a kawo masa abinci. Zaitunan Ya Aina ta tasa ta ce ta saka mai ta kai masa ta na fita Ya Murja ta ce" Mata kamar mai almatsutsai"
Ya Aina ta ce" Lafiyan ta ƙalau iskanci ne kawai da ta samu shi Abubakar ɗin mai sanyi."
Ni dai ina jin su ban tanka ba ina ta cin abincina ni shinkafa da waken da Rahila ta dafa na ke ci su kuma su Ya Aina sun ci nawa sun kuma ci na Ma'u ita waina ce da Sinasir. Mganar gaskiya duk cikin mu Mijin Ma'u ya fi kuɗi kowa kuma ya san haka amma duk da haka dukkanmu ba za a ce muna cikin halin rayuwa ba dai dai gwargwado mazajen mu na da rufin asiri. Mijin Ya Murja ne ma sai a hankali domin ya samu matsala can kwanaki an kore shi daga wajen aiki ya fi shekara uku a gida amma dai an ce ya koma shi ya sa Ma'u ta samu dama tana taimakonta ita kuma kwaɗayi ya sa idanuwanta ya rufe. Ni ba na kyautar ganin ido ko ka gode min in na yi niyyar yi maka alheri na yi, in ban yi ba shike nan ba zan yi domin duniya ko kai da zan mawa ka yabeni ba ita kuma Ma'u daman halinta ne ta yi alherin da duniya za ta sani a yabe ta a kuma san tana yi ɗin da son nuna ita fa mijinta na da kuɗi domin in dai Ma'u ta san za a zo gida a haɗu ƙarshen kayanta a kyau da tsada ta ke sakawa. A fuska ba ta nuna wani abu amma ga ni da na san halinta ni na san ta na da halin son a sani.
Yanzu ma muna cin abincin ta na ba da labarin Alhaji Mustapha ya ce zai ba ta jari na miliyan biyar ta fara kasuwanci shi ne take neman shawarammu wata sana'a za ta fara. kowacce na faɗin albarkacin bakinta nima sai na tofa nawa na ce ta saro dogayen riguna da takalma da mayafai na mata ta fara saidawa mu gani ko za su tafi. Sai Ya Aina ta ce yauwa ta ƙara har da atamfofi da kayan yara ni kuma sai na ce kayan yara ta jinkirta tukunna zuwa gaba ta fara da waɗanan dai ta gani yadda kasuwan za ta kaya.
Cikin mirmishi ta ce" Haka ma Shema ta ce. Da ya ke mun yi mganar da ita ta waya. Ya ce dai na tsaida shawara visa na fitowa Egypt za mu je a can zan yo sarin kayan nawa in sha Allahu."
Ya Murja ta washe baki tana faɗin" Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ƙanwata."
Ta amsa mata da Amin Amin. Ita kuma Ya Balki ta ce " Sai ki faɗa ma Gwaggo da Alhaji su suka albarka."
Sai ta ce za ta faɗa musu sai mata fatan alheri suke yi nima na yi mata ta re da fatan Allah ya sa a fara a sa'a ta amsa lokaci ɗaya ta na kallona kafin ta ce" Amin Sadiya. Amma fa kema ya kamata ki zo ki fara wata sana'ar zama haka ba daɗi."
Wani abu ya tsaya mini a maƙogawaro. Ma'u ta bala'in raina min wayau. Kuma kawai sai su Ya Balki suka amsa da wallahi kuwa Sadiya. Rahila ce ke faɗin" Ita fa Sadiya Shagon saloon da gyaran jiki take son buɗewa"
Ya Balki ta ce" To wannan ai lissafi ne me yawa. Ta dai yi tunanin fara wani abun kafin ta yi ƙarfin da za ta buɗe saloon ɗin."
Duk yadda na so na yi mgana sai kuma na kasa. Da na so na mayar mata da martanin mganarta ne sai kuma na yi tunanin ina yi magana za a ce ni ce fitinanniya Ma'u ta yi min mganar arziƙi na maida shi ta tsiya
Sai kawai na kalli Ma'u nima sai na mayar mata da martanin mirmishinta kafin na ce" Kar ki damu ki maida hankali kan naki. Nima soon in sha Allahu Suprise zan ba ku."
Sai ta ce Allah ya yarda ta na min wannan dariyan na ta na mugunta. Ya Aina ko sai faman mgana take yi ta na cewa sana'a ita ce mace ko da mijinki na maka komai to ka yi dogaro da kan ka ko domin wata rana.
Ya Balki ta ce" Har da ma rayuwa Ya Aina."
Rahila ma na ji tana fadin itama za ta fara awo a cikin gida Ya Aina ta ce kasuwanci mai kyau. ita Ya Aina tana saida kayan miya da kayan nau'in ɗanɗanon girki ita kuma Ya Balki tana saida gwanjuna. Ni ce daman ban saida komai sai Rahila Ma'u kuma daman tana nuna mijinta na mata komai sai yanzu ne ta zo da labarin za ta fara na ta kasuwamcin.
"Albishirin ku"
Na faɗa ina musu mirmishi. Na gama cin abinci tuni har na sha ruwa na yi gatsa.
"Goro fari ƙal."
In ji Rahila da Ya Balki har suna haɗa baki.
"Nan da kwana uku za mu cika shekara sha biyar da aure ni da Yallaɓai na. Haka ma Rahila da Ya Muntari."
Na faɗa ina musu mirmishi.
Ya Balki ta fara cewa" Ma sha Allah. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Kai ashe kun daɗe kamar jiya ne na ke ganin bikin ku fa ke da Rahila?
Rahila na dariya ta ce" Sadiya ta na lissafi ni fa mancewa na ke yi. Ko da muka yi shekara goma sai da na ga sun yi walima ne na ce ma Ya Muktar yau auran mu shekaru goma Cif."
Ya Aina ta ce" Shekarun suna gudu ba wuya. Allah ya ƙaro muku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya raya muku zuru'a."
Muka amsa da Amin Ya Murja ma ta yi addu'a muka amsa mata. Sai Ma'u da ta gyara zama tana fadin" Ma sha Allah. Allah ya ƙara ɗankon kauna Mrs Yallaɓai da Mrs Ya Muktar."
Ni ce na amsa mata Rahila ta na jin kunya Zaituna ce ta yi karaf ta na faɗin" Sadiya akwai walima ne?
Ina mata dariya na ce" Akwai amma ta iya ni da Yallaɓai ce da yara."
Ma'u ta ce" Allah? Ban damu kenan? Ina mata fari na ce" Ai kun gama na ku tunda kun yi addu"a.
Ya Aina ta ce" Shi ne ko babban mgana."
Zaituna na kallah ina faɗin" Tambayi Rahilan Hubby ƙila za su haɗa mana walima."
Duka ta ɗaka min a cinya ta na faɗin" Sadiya ban son wulaƙanci."
Kamar zan yi kuka na ce" Wai don na ce Rahilan Hubby shi ne har da duka? Rahila sai kawai ta balla min harara kunya duk ya kamata mu kuma gabaɗayanmu muka fashe mata da dariya.
Sai ta ji kunya ta tashi ta fita, ta na fita Ya Balki ta ce" Daga Rahilan har Muntari masu kunya ne."
Ya Aina ta ce" Wallahi ba su da hayaniya. Alhajinmu ya sha cewa tabbas an ijiye kwarya a gurɓinta."
Ranar yini muka yi ana ta hira a yi daɗi a yi tsiya bayan mangariba Gwaggo ta ce Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shiri ta koma gidanta yinin ya isa haka. Jin haka yasa muka fara shiri saboda tun da Alhaji ya yi mgana to dole fa kowa ta kama hanya. Ni dai Yallaɓai na kira sai ya ce bari a yi sallar isha'i sai ya zo mu tafi gida. Ma'u ta fara tafiya Alhajinta ya zo ɗaukansu ita da yara haka ya yi mana yayyafim kuɗi goron salla damu da ya'yanmu ban sam kuma nawa ya ijiye ma Alhaji da Gwaggo ba. Su suka tafi da Zaituna da ƴaƴanta za su sauke su a gida daga can na ji Ma'u na faɗa ma Gwaggo za ta biya gidan su Shema'u.
Kafin ya zo daman Ma'u ta sanar da Alhajimmu da Gwaggo mganar jarin da ya ce zai ba ta su ka yi ta masa godiya da saka albarka.
Nima da Yallaɓai ya zo mun je gaban Alhaji na faɗa masa nan da kwana kaɗan auran mu zai cika shekara goma sha biyar da ni da Rahila.
Alhajinmu ya yi mirmishi kafin ya ce" Ma sha Allah. Shekaru goma sha biyar masu albarka da tarin albarka zuru'a. Allah ya ƙara haɗa kawunanku. Haƙiƙa Yusufa da Muntari sun cika ƴaƴa tunda duk tsawon wannan shekarun ba su taɓa kawo min ƙaran ku da sunan kun yi musu wani abu ba hakan ma abin alfaharina ne. Allah ya yi muku albarka ya bar ku tare har jikokin ki."
Kan mu na ƙasa ni da Yallaɓai muna ta amsawa da Amin Amin.
Gwaggo na gefe ta na ta saka albarka kafin ta ce" Jiya ba yau ba. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Na tuna da Mama itama shekarunta a ƙasa kenan Allah ya jiƙanta ita da Hajiya gabaɗaya."
Muka amsa mata da Amin Amin da za mu tafi shima Yallaɓai ya ba ma yaran su Ya Murja goron sallah Marwa dai ta ce za ta bi Ya Aina zuwa gida amma jibi za ta dawo. Yallaɓai ya ba ma Alhajimmu kuɗi da Gwaggo amma ban sam ko nawa ba ne. Daga nan muka yi musu sallama ya ɗauke mu zuwa gida.
Sai da muka koma gida har mun yi shirin kwanciya muna rumgume da juna Yallaɓai na shafa gashin kaina ya ce.
"Sadiya ta."
"Yallaɓai na"
Na amsa masa cikin so da ƙauna. Sai kawai ya ce" Gani na ke yi kamar jiya jiya muka yi aure sai ga shi wai mun kusa cimma shekaru goma sha biyar da aure cikin yan kwanaki ƙalilan masu zuwa."
"Nima haka na ke ji a zuciyata." Haka na faɗa masa na ke jin kamar jiya muka yi auran ashe shekarun sun tafi.
Ƙara kamkameni ya yi kafin ya ce" Har yanzu ba ki sauya daga Sadiyar da na fara sani yar shekara sha tara ba."
Nima ina mirmishi na ce" Kai ma har gobe baka sauya min a wannan gwarzon matashin da na aura a shekaru ashirin da bakwai ba."
Sai kuma muka kalli juna ta cikin duhun ɗakin da ɗan hasken da ya kan shigo ta window ɗin cikin bedroom ɗin kafin ya sumbaci goshina ni ma sai na maida masa martani na sumbaci kumatunsa kafin mu koma mu kwanta yama ƙamƙame dani kamar za mu koma abu ɗaya.
******
Wed.13 JULY 2015.
Rana ta ƙara zagayowa ranar da a irinta ne aka ɗaura mana aure ni da Yallaɓai a irin kuma ranar ne muka zama miji da mata. Jiya Yallaɓai ya dawo domin tun washegarin ranar da muka dawo daga Ɗorayi ya je kaduna sai jiya da daddare ya dawo. Kuma yau tun safe ya fita saboda Nene ta kira shi a waya tana son ganin shi. Bai ko tsaya a gida ya ƙarya ba ya fita wanka kawai ya yi. Su Jidda sun koma makaranta tun jiya sun tafi gidan ba kowa sai ni kaɗai Marwa ba ta dawo ba amma na kira Saude na ce ta zo ta ta ya ni mu gyara gidan.
Na ba da a yi mana cake babba sannan a gida na ce zan yi mana zoɓo muna da sauran naman sallah na ce kawai sai mu yi amfani dashi bayan haka na yi dambun nama da yawa ya na nan. Kawai dai yar walima ce daga ni sai mijina sai ƴa'yana.
Saude ta zo da wuri tare muka gyara gidan ko'ina muka turare shi da turaren kamshi. Saude na saka ta dafa farar shinkafa tunda ina da miya da na yi a frigde sai na koma ɗaki na ɗau wayata na kira telanmu domin na ɗinka wani material mai kyau saboda wannan ranar na tuna masa yau zan yi amfani da shi sai ya ce zai aiko min da shi anjuma kaɗan. Sauran kazar da na siya wajen Surayya Halin yau na ce Saude ta ɗumama ta kai mini falon yara ni kuma sai na kunna data na shiga ina ganin saƙonni.
Na ga group ɗin gidanmu ana ta tagging ɗina ina shiga sai na ga Ma'u ce ta sanar da Anniversery ɗin mu ana ta yi mana fatan alheri ni da Rahila da Ya Muntari.
"Mrs Injinya Allah ya ƙara dankon ƙauna."
In ji Yaya Auwal shi kuma Ya Hamza tagging ɗina ya yi kafin ya ce" Yallaɓiya an gangara a bautar ubangiji.. Allah ya zaunar da ku lafiya."
Haka suka yi ta ma Ya Muntari shaƙiyanci wai ɗankwali ya ja hula.
Nima na shiga ina amsawa cikin farimciki.
Na je na yi status amma ban saka hoto ba na dai saka Alhamdulillah!
Sannan sai na rubuta"
"Shekaru goma sha biyar cikin farinciki Alhamdulillah."
Duk da ban yi caption ba sai aka fara mini mgana ta private ana mana addu'a yawanci duk yan makarantar mu ne da muka yi BUK tare waɗanda na ke da lambarsu.
Sai Adnan ɗin su Yallaɓai da ya gani ya ce min" Ma sha Allah Happy Wedding Anniversery Mrs Yusuf Muhammad Tafida."
Musabahu ma haka ya ce mini" Ma sha Allah Allah ya ƙaro danƙon kauna ta Yallaɓai"
Duk na amsa su. Sauran dai su Anty Bahijja ban ga sun gani ba. Zuwa na yi na zaƙulo hoton Rahila a waya na ranar sunan ɗiyarta da aka ɗauka na saka a status ɗina na c
" Happy 15 years Wedding Annivesary Mrs Muntari Amini yashe(Hubby)"
Sai na ƙara da emojin rawa da murna da dariya. Ina ta dariya saboda na san in ta gani sai ta yi mgana Ya Hamza ya fara gani kawai sai ya yi tagging ɗin status ɗin da cewa.
"Ina na ki hoton?
Ina dariya na ce ni ban da hoto ya ce ban isa ba. Kowa sai ya ce wai ina hotona da na Yallaɓai tunda na saka na Rahila. Ganin sun dameni ya sa dauko hoton da ranar idi ne ma Marwa ta ɗauke mu da wayata ni da Yallaɓai yana tsaye ni kuma na jinginar da kafaɗata a saman kafaɗarsa. Shi waya ma ya ke yi bai san ana hoton ba ni kuma ina mirmishi. Hoton ya yi kyau sosai yana sanye da farar shadda mai babban riga sai dai ya cire babban rigan. Ni kuma na saka leshi mai ruwan haske akwai zanen marun a jikin leshin sai ya haskani gabaɗaya.
Ina mirmishi shi kuma Yallaɓai ya ɗan sunkuya yana kallona aka ɗau hoton shi na saka a kasan hoton sai na saka.
"Barka da shekaru goma sha biyar cikin Aminci, soyayya, sadaukarwa a gare ka ya amintattace na. MRS HALIMATUSADIYA YUSUF MUHAMMAD (YALLAƁAI NA)"
Na ƙara da gayyar emoji kafin ka ce kwabo duk yan gidanmu sun ce na tura musu a group ɗin gida na tura hotunan tuni har sun sakamu a status daga ni har Rahila ni a bayan wannan sai na saka hoton Jidda da Baby shima da wannan sallan aka yi musu na yi mgana a ƙasa da cewa.
" A shekaru 15 da auren mu ga albarka da Ubangiji ya yi mana nan. Allah ya raya ku HAUWA'U YUSUF MUHAMMAD(Jidda) DA MAIMUNATU YUSUF MUHAMMAD(Baby)."
Kowa sai addu'a ya ke yi. Har ta Ma'u sai da ta ce na tura mata itama ta saka ta yi mana addu'a na amsa mata ko da bai kai zucci ba.
Na duba Yallaɓai ba ya online na kuma kira layin shi ba ta shiga. Sai kawai na tura masa test massages.
"Happy Wedding Anniversy Yallaɓai na"
Na jira na jira amman bai turomin amsa ba sai na yi tunanin ƙila Network ya sa bai shiga ba. Da ya tafin na kira shi na ji ko Jikin Nenen ne ya tashi sai ya ce mini yanzu ya iso gidan lafiyanta ƙalau sai hankalina ya kwanta.
Na yini cikin farincikina ina ta amsa wayoyin yan' uwa da abokan arzuƙa har mutanen fatakol Anty Zabba ta kirani ta na min fatan alheri Haka Munnira Hauwa dai wayar ta ya lalace ba ta sani ba.
Amma har Nafisa Muhammad Sani mun yi mgana da ita, sauran yan gidansu Yallaɓai duk waɗanda suka ga status ɗina mun yi mgana hatta da Halima Autar su Yallaɓai amma ban ga Anty Bahijja ko Anty Maimuna sun gani ba Mimisco dai tana online amma ba ta duba ba.
Ban damu ba, na cigaba da harkokina. Saude sai wajen uku ta tafi gida ni kuma salla kawai ke ta da ni a inda na ke Yallaɓai har lokacin bai dawo ba na kuma kira shi ta shiga bai ɗauka ba na ƙara kira shuru sai can ya turamin saƙon zai kirani ya je wani waje ne ni kuma sanin sabgoginshi sai ban damu ba.
Na cinye sauran kazar hadin uwargida duka na sha gumba sannan na sha kayan marmari ranar ko abinci ban ci ba har Jidda suka dawo makaranta daman na gaya musu in Yallaɓai ya dawo da daddare za mu yi walima Jidda ta ce" Umma waliman mene?
Ina mirmishi na ce" Na cikar mu shekaru sha biyar da aure ni da Abbanku."
Da ya ke ta na da wayau sai ta ce" Umma Allah ya bar ku tare." Na amsa da Amin Baby kuma sai tsallen murna ta ke yi, ko kafin mangariba har ɗinkina an kawo min daman kunshin sallar da na yi bai fita kitso kuma daman bai dameni ba ƙara gyara kaina kawai na yi, na saka Jidda ta ƙara gyara gidan ta kunna turaren wuta. Ina da bloons na ma Baby ne jidda ta kama min muka hura su na ɗaura su a falon mu wajen guda ashirin kala kala. Sai falon ya yi kyau sai bayan mun yi sallar mangariba sannan mai cake ta aiko mini dashi da kwatance sai gashi a gidana ta online na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 31