ga wacce ta yi masa a ciki?
Yallaɓai ne ya yi dariya kafin ya ce"Ai Nene wannan ƙanin naki sai dai in yana da rabon samun Hurul aini ma'ana in ya mutu ya samu rabauta a shiga aljannah."
Nene ta aika masa da dakuwa ta na faɗin" Kawun na ka ne ka ke yi ma mugun fata? To bakin Tafida ya sari ɗanyen kashi Abba"
Sai lokacin ya yi mgana ya na zaune kusa da yayarsa yana danna waya.
"Na ƙyale su Nene. In cikin su akwai wanda ya isa gobe ya ɗaura mini aure "
Nene ta yi saurin cewa"Ba su ma isa ba. Amman dai mu mun isa Abba ka fara furfura fa"
" Lokacin ta ne Nene ban tsufa ba da saura na. Aure kuma zan yi in sha Allahu."
Nene ta amsa da Allahu ya sha kafin ta ce"To yau duka ba ka ga wacce ta yi maka ba? Ko yar uwan Sadiya?
Gabana har ya na faɗi na ji me zai ce kawai sai ya ce"Duka fa ba su da kamun kai. Nene wacce mace ce ta gari ce mai kunya za ta yi shigar bayyana sura ta na nuna ma namiji alamun tana son shi? Ni ba irin matan da na ke son aura ba ne Nene ki bar mganar nan."
"To ita wacce kuka ɗauko daga asibiti fa? An ce ka ba ta lambarka?
Kai tsaye ya muskuta kafin ya ce" Ita ma ta na cikin jerin su. Ita ta fara mini mgana kin ga kenan itama kunyar ta yi ma ta ƙaranci sannan kuma ni ba lambata na ba ta na Tariq na saka mata."
Me za mu yi in ba dariya ba sai aka bar Tariq da buɗe baki sai yanzu ya tuna domin da ya saka mata lambar sai ya ce wayar ba ta tare da shi tana gida a kashe.
Sai ta ce ta hannun ka fa? Sai ya ce ta aiki ne ashe shi ya gama ma aikin.
Ni da Yallaɓai muna ta dariya Nene ma sai da ta dara. Tariq dai ya ce zai rama ganin dare ya yi suka ce za su koma Nene ta ce su kwana Abba ya ce kamar wasu mata. Sanin halin su ya sa ta ce Abba ya gaida Innayi. Shi kuma Tariq ya gaida da Hajiya.
Tare muka fita har baby ta yi barci sai ɗaukan ta Babanta ya yi Jidda ce kawai idanuwanta biyu ta ga babaninta ta maƙale musu suna mata tambayoyin makaramta tana ba su amsa.
10k Kawu Abba ya ba ta shi kuma Tariq 5k ya ce ita da Baby su siya chaculate sai ta ki karɓa ta na kallon Babanta.
Uncle Abba ya kalli Yallaɓai kafin ya ce" Kai Tafida ko ba ka yi ma yar namu bayanin ko kana raye muna da iko a kanka da su gabaɗaya ba."
Yana dariya ya ce"Sai ku jira na mutu tukunna"
Ni dai ina jinsu ina ta dariya Sai da yace Jidda ta karɓa sannan ta karba ta wuto wajena ta ba ni na karba ina musu godiya.
Tariq ke faɗin" Abba mun kusa zama surukai fa. Ka ga Jidda da tsawon kafa."
Abba ya jinjina kai kafin ya ce"Zan fara neman aure ko domin kar azo neman aure tarihi ya zo uban jidda ya ji kunya." Daga Tariq har Yallaɓai na suka fashe da dariya nima na dara sanin halin su in sun haɗu. Na shige mota ina ce ma Tariq ya gaida Farida ya ce za ta ji.
Uncle Abba kuma ya ce" Ni kuma wa zan gaisar miki Sadiya?
Ina dariya na ce"Amarya mai jiran gado."
Yallaɓai ke faɗin" Su kawu Sa'adu ko matansu ba."
Keyarsa ya tallaba ya na faɗin" Mara ɗa' a."
Tariq na gefe ya ce zai rama masa. Ni dai mun fi minti talatin a waje kafin su yi sallama su suka shiga mota suka ɗau hanyar Rano mu ma muka ɗau hanyar gida.
Muna hanya na kalli Yallaɓai ina faɗin" Dare bai yi ma su Kawu ba?"
Ya na tuƙi ya ce"To wallahi Abba har sha biyun dare ya kama hanyar rano."
Sai kawai na yi fatan Allah ya kai su lafiya.
Mun isa gida lafiya Yallaɓai ya dauki Baby zuwa ɗakin su na ce Jidda ta yi mata shirin kwanciya su sun ci abinci a gidan Nene, ni da Yallaɓai na zuba mana sauran tuwon da na yi muka ci muka ƙoshi. Sai da muka yi brush muka yi shirin kwanciya duk mun gaji sai barci sai da asuba ne Yallaɓai ya ja mu ka yi ta ɓarnan ruwa.
Da safen daman ban yi niyyar zuwa asibiti da wuri ba sai ga ma wayar Amina ta ce an sallami Alhaji sai na ce shike nan sai zuwa anjuma zan leƙo gidan.
Zan tsaya saude ta zo ta kama ma Jidda ta wanke Unfiorm ɗin su nima Yallaɓai na gida ba zai fita ba ƙila sai zuwa anjuma.
*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
09069067488.
08032773332.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
I just published "Page 12" of my story "TURKEN GIDA."::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68237857847ebcbfe6d205fe
*🅿️11*
*1994.*
*KATSINA. Ƙauyen Yashe dake ƙaramar Hukumar Kusada.*
Hajiya Dubu na zaune a dandamalin ƙofar ɗakin ta, ta na ɓanɓaran masara. Masaran gonar Aminu ce an kawo ta gida yar sauran da ta rage ba ta bushe ba ne aka shanya bayan ta bushe shi ne take ɓanɓarewa.
Daga ƙofar gida ta ji kamar hayaniya ba jimawa sai ga wani magidanci ya shigo riƙe da jaka a hannunsa bakinsa kamar gonar auduga saboda farin ciki.
"Hajiya Yaya Sule ne ya zo."
Haka ya faɗa. Itama sai ta washe baki lokaci ɗaya tana miƙewa kakkabe hannunta ta yi a jikin zanin jikinta kafin ta kalli yar yarinyar dake gefenta a zaune a rakuɓe wacce a shekaru iyakarta sha uku sannan ba za ta haura sha huɗu ba.
"Ke Asma'u kwashe mini masara ki kai cikin ɗakin can"
Haka ta faɗa kafin ta maida hankalinta ƙofar shigowa dai dai lokacin da aka yo sallama kamar wanda ya fara shigowa haka ya ke shima sai dai a akwai bambamci shi daga ganin shigarsa za ka fahimci daga birni ya ke. Shadda ce mai duhuwa ya saka da takalminsa sahu ciki kansa da hula amman fuskarsa duk ta yi ƙura saboda kuran hanya tunda shekarun da yawa ba titina a lokacin kuma akuri kura ce za ka samu in ka sauka a bakin hanya ta shigo da kai cikin Ƙauyen.
"Maraba. Lale da zuwan Sule. Kai ne tafe."
Safiya ce domin lokacin ba zai gaza sha ɗaya da wani abu na safe ba. Kuma da karfi ta ke yi masa maraba da ya sa matan gidan da ƴa'ƴansu fitowa daga ɗakunan su. Har ƙasa ya duka ya na faɗin" Mun same ku lafiya Hajiya?
Da sauri ta ce"Haba dai. Tashi tashi maza Sule. Kai Sani shigar masa da jakarsa ciki ka yi masa shimfiɗa ka zauna anan ai sai ka ɓata jikinka"
Sai da ya shiga ciki ƙaninsa Muhammad Sani ya yi masa shimfiɗa ya zauna sannan Hajiya Dubu ta shigo ita ma ta zauna a gefe suka gaisa. Sannan matar Sani ta shigo suka gaisa har yana karɓan yarinyar da ta ke goyo mardiya. Sannan yaran ma duk sun shigo sun gaishe shi ga su nan ɓutu ɓutu. Ba karatun boko suke yi ba saboda lokacin karatun bai yawaita har ƙauyuka ba sai dai in namiji ne a tura shi gona in mace ce kuma a yi musu aure masu rabo ne ma iyayensu kan tura su wani gari karatun allo.
Matar Aminu ma ta zo ta gaishe shi kafin ka ce me an cika gabansa da ruwa da fura. Har da abinci ma tun da su ƙauye ba ruwansu da wani lokaci ko da yaushe ka zo suna da abinci sannan sun iya karrama baƙo. Baƙon ma irin Sule da ba ko yaushe ya ke zuwa ba sai in ya samu sarari. Yaran gidan sun zagaye shi sai da Hajiya ta fattatake su amma ba su tafi ba sai da ya buɗe jakarsa ya ɗauko alewan da ya siya musu na tsaraba ya ba ma Babban cikin su Nura ɗan wajen Sani ya ce ya je su raba sannan suka fita suna murna. Shima Sanin fitan ya yi ya ce zai gangara gona ya faɗa ma Yaya Aminu zuwan shi.
"Ya wajen iyalan naka? Ina takwarata Dubu ina fatan duk kuna nan lafiya ko?
Hajiya Dubu ta faɗa tana gyara zama. Sai da ya kurɓi ruwa da cikin kwanon sha mai murfi da aka kawo masa sannan ya ce" Duk suna nan lafiya Hajiya. Rukayya da Maimuna duk suna gaishe ki. Takwaran ki kuma ta so ta biyo ni to sun fara zango karatun sakandiri na farko shi ya sa ban zo da ita ba. Sai dai ta yi jadadda mini saƙon gaisuwarta zuwa gare ki."
Hajiya Duhu ta yi mirmishin farin ciki kafin ta ce" Duka ina amsawa. Allah sarki ashe takawara an sake zama ƴan makaranta. Ina jiranta in suka samu hutu."
"In sha Allahu."
Sun fara taɓa hira sama sama ta na faɗa mai gidan su Maimuna ma an yi rasuwa jiya ƙanin mahaifinta ya rasu sakamakon ba wayar hannu a lokacin sai dai a tada ɗan aike ya je ya faɗa. Daman tana shirin aika Sani ne sai kuma gashi ya zo.
"Allah Sarki. Allah ya jiƙansa. Daman tana ta zencen sa ashe jinya ba na tashi ba ne. Allah ya yi masa rahama."
Ta amsa da Amin Amin. Shi kuma ya ce zai je ya yi musu gaisuwa kafin ya tafi gobe in Allah ya kaimu.
"Gobe gobe nan za ka koma Sule?
Kai ya gyaɗa kafin ya ce"Saboda wajen aiki Hajiya. dama na ga kwana biyu ban leƙo ba shi ya sa na ce bari na zo na duba ku".
Ya faɗa lokaci ɗaya yana buɗe jakarsa ya fiddo da ledojin guda biyu duk ya tura gabanta ya na faɗin" Sabulai ne da sai siga Hajiya. A yi hakuri ba kamar yadda na saba zuwa ba ne. Tsakiyar wata ne ba a yi albashi ba."
Ta jawo ledojin gabanta ta na faɗin" An gode. Allah ya yi albarka Allah ya raya maka zuru'a. Allah ya ba ka masu jiƙan ka kamar yadda kake jin ƙanmu. Allah ya ba ka aljanna sanadin wannan zumuncin naka."
Yana ta amsa mata da Amin Amin cikin jin daɗi.
"Hasiya dai na can lafiya ko?
Hajiya Dubu ta gyara zama za ta yi mgana kenan sai kawai ta ga inuwa daga saman kanta ta na ɗago kanta sai ta ga Asma'u tsaye ta na leƙen su. Shima Sulen sai ya kallo ƙofar ɗakin ya ga ana leƙe.
"Ke Asma'u zo nan.."
Sai ga ta ta shigo ta na laɓe laɓe hannunta ta jawo ta zaunar da ita a gabanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ke kowa ya zo ya gaida babanku ke ba ki da hausan zuwa ki gaishe shi?
Sai ta kalle shi cikin yarinta kafin ta ce" Ina yini"
Cikin sanyin murya kamar za ta yi Sule ya yi mirmishi kafin ya ce"Ina kwana dai ko?
Ya faɗa ya na kallonta. Hajiya Dubu ta taɓe baki kafin ta ce"Haka ta ke. Tunda Hasiyar ta kawo ta wajen wata ɗaya kenan ta kasa sakin jikinta. Ga yara ƴan'uwanta ta kasa sakin jiki a cikin su sai ƙulafacin uwa."
Sai ya kalli Hajiya Dubu kafin ya juya ya na kallon ƴar yarinyar cikin mamaki ya ce
" Ƴar waye wannan Hajiya?
"Yarinyar wajen Hasiya ce fa. Wacce ta haifa da marigayi Hashimu."
Cikin buɗe ido ya ce"Dama ba tana hannun dangin babanta ba ne?
Hajiya Dubu ta ce"Uhm' kafin ta cigaba da faɗin" To Hasiya da ƙulafaci mana. Wai can Asma'u ba sa'aninta ba ta jin daɗin zaman gidan. Bayan ta yi auren nan ta amso ta ta tafi da ita to ashe dai zama bai yi daɗi ba sai gashi ta dawo mini da ita wai ta zauna a hannuna."
"Me ya sa?.
Ya faɗa cikin mamaki Hajiya Dubu ta amsa shi da cewa" To ta dai ce min yaran mijinta na ta sun ƙi karɓan Asma'u sai megidan ya ce ta maida ta dangin ubanta. Su kuma kasan duk mata ne ƙannen Hashimu wata ma ƙanwarsa da yake can ƙauyen gaba damu ta so ɗaukan Asma'u Hasiya ta hana shi ne ta bar ta a wajena ni zan riƙeta in har Allah ya aramin rayuwar."
Sai ya jinjina kai kafin ya kira Asma'u da hannun alamun ta zo. Hajiya ta tura ta gabanshi. Riketa ya yi ya ɗora ta a saman cinyarta ya na faɗin" Me sunan ki?
"Asma'u."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce"Ma'u ce" Sai ya ƙara kallonta kafin ya ce" Za ki bi ni can birni kano? Akwai abokan wasa kamar ki Rahilatu da Sadiya. "
Sai ta kalle shi kamar yadda Hajiya Dubu ke kallon shi sai Asma'u ta kalle shi kafin ta kalli Hajiya ita kuma sai ta yi mirmishi kafin ta ce" Ba ruwana. Kawun ki ne in za ki bishi shike nan nima na huta.".
Sai ta ɗaga masa kai alamun za ta bishi. Sai ya dawo da kallonsa kan Hajiya ya na faɗin" Hajiya zan ta fi da Asma'u na je na haɗa ta da su Sadiya na sakata a makaranta. Ba zan bari a kaita ƙauye a gurgurta mata rayuwa ba"
"Allah ya ba ka lada Sule. Daman Hasiya burinta Asma'u ta samu rayuwa mai inganci. Allah ya taya ka riƙo"
Ya amsa mata da Amin Amin sai ta ce to Asma'u ta tashi ta haɗo kayanta a wanke saboda gobe Sule zai wuce zai tafi da ita. Sai ta fice tana murna. Hajiya ta yi mirmishi kafin ta ce" Ja'ira itama tana son bin ka ashe."
Sun cigaba da hira har aka kira sallah ya yi alwala ya fita masallaci domin ya yi salla bayan ya idar ya daɗe a waje yana gaisuwa da mutane da aka kwana biyu ba a haɗu ba. Ya na wajen Aminu da babban ɗansa Muntari da Sani suka dawo daga gona rumgume ɗan uwansa Aminu ya yi yana murna da ganinsa Muntari ya duƙa har ƙasa yana faɗin.
"Sannu da zuwa Baba Sule."
Kansa ya shafa kafin ya ta da shi tsaye yana faɗin" Muntari ka ƙi zuwa dai na saka ka a makaranta tare da su Hamza ko? Ka gwammace ka yi ta zuwa gona da babanka ko?
Kansa na ƙasa ya na shafa ƙeya ya ce" Zan zo Baba in sha Allahu."
Sani ne faɗin ai yana yin makaranta gwammati na cikin garin kusada. Sai Sule ya ce hakan da na kyau in ya gama ya zo ya same shi a kano domin ya nema masa ta gaba da sakandiri saboda ilimi na da amfani sun ga misali a kan shi da ilimin da ya yi ya zama abin ya zama yanzu.
Cikin gida suka shiga gabaɗayansu kamar yadda suka saba in dai Sule ya zo a ɗakin Hajiya Dubu suke haɗuwa su ci abinci. To yau ma haka suka yi bayan sun gama cin abinci suka sake fita suka raka shi gidan su Maimuna ya yi gaisuwa da alƙwarin in ya koma ita za ta zo in sha Allahu.
Ranar dai ya yini cikin ƴan'uwansa har dare suna tare Hajiya ta faɗa musu zai tafi da Asma'u Aminu ya ce gwara haka ƙila za ta fi sakin jiki sannan can za ta yi karatu nan kuwa sai dai ta ta ƙara tasawa a yi mata aure.
A tsohon ɗakin su na zaure ya kwana gidan da ya ke ginin mutanen da ne na ƙasa ne da yaɓe. Da safe bayan sun karya ya yi wanka ya yi shirin tafiya kuɗi ya ba ma Hajiya Duhu ta yi ta saka albarka Asma'u an haɗa mata kayanta a kullen ɗan kwalli itama ta ci gayunta da takalminta ɗan madina da hijabinta da ya yi mata yawa.
Lokacin da Sule da Hajiya Dube suke sallama ya ce mata" Hajiya don Allah ki bari na zo na ɗauke ki in na gama gina gidana ki koma can da zama."
Hajiya Dubu ta ce"To Sule in na bika su na nan ai sai su ce na fi sonka ne ko?
Su Sani na wajen su ka saka dariya domin su san ba ta son barin garin kwata kwata.
Aminu ne ya ce" Hajiya da mu da Yaya Sule duk ɗaya ne. Mu ma za mu so ki samu rayuwa mai inganci da jin daɗi kafin wa'adi ya yi. Mu kuma ki bar mu anan mu ai ba yara ba ne muna da iyalai da yara. sai mu riƙa zuwa muna duba ki in sha Allahu."
Ba ta dai ce komai ba sai ta wani rausayar da kanta alamun ba ta amince ba shi kuma Sule ya shuru ne ya dai gama gina gidan na shi tabbas sai ya ɗauke Hajiya zuwa Kano domin itama ta samu chanjin rayuwa.
Har ƙofar gida Hajiya ta raka shi da zugan yara duk ya sallamesu da kuɗi sulalla ya ce su je raba a tsakaninsu Muntari ne ya ɗaukan masa jaka yana gaba tare da Asma'u shi kuma ya na baya tare da ƴan'uwansa suna tattauna mganar gonar shi da ake noma masa tana hannunsu ne tun da sune suke cikin garin.
Sune har zuwa in da ya samu akori kuran da zai ɗauke su zuwa babban hanya da za su samu motar kusada daga can su hau ta zuwa garin Kano.
*****
*KANO. Fagge.*
Ba zan manta ranar da Alhajinmu ya zo da Ma'u gidanmu ba. A wata ranar lahadi ne da yamma domin sanda suka iso ba ma gida muna isalamiya ni da Rahilaa mun dawo makaranta ne muka ga wata baƙuwar yarinya mai kallon mutane da idanuwanta a tsaye a cikin ɗakin mu.
A lokacin Yaya Aina ce kawai ta yi aure. Amman su Yaya Murja sune ƴan mata a lokacin ita da Yaya Balki tun da ba su da tsareyan haihuwa. Ita Yaya Murja ta na ajin kusa da ƙarshe a babban sakandiri ita kuma Yaya Balki tana ajin farko. Ni da Rahila ne muke tasawa a lokacin sai Amina da ke bin bayan mu a lokacin da Datti da ya ke namiji.
Lokacin da na shiga ɗakin mu na ga baƙuwa. Kallon juna muka yi cikin ido tun a wannan lokacin Ma'u ba ta kwanta mini arai ba idanuwanta kir suke a kan mutane. Rahila ce ta tsaya ta na tambayanta ita wacece, ni ina ko hijabin isalamiyata ban cire ba na fita tsakar gidaa in da Gwaggo da ke shanya kaya a igiya sai Mama dake cikin ƙaramin madafin da ke tsakar gida suna kuma hira jefi jefi da juna.
" Gwaggo Alhajimu ya dawo ne?
Na faɗa ina kallonta. Ba ita ta bani amsa ba Mama ce ta amsa min da E. Lokacin muna gidan Haya ne kafin mu koma gidanmu na Ɗorayi Alhajimu ba shi da bangare sai dai yana zama a ɗakin duk wacce ke da girki ne.
Ina so na tambayi wace ce na gani amman na kasa na wuce zuwa ƙofar ɗakin Mama na tsinkayi muryan Rahila ta na faɗin" La Gwagggo wannan wace ce? Alhajimu ya zo da ita daga Yashe?
Ta faɗa bakinta kamar kunne saboda na juya na kalleta. Sai na ji raina ya ɓaci ganinta rike da hannun yarinyar da na ji Gwaggo na faɗin" E sunanta Asma'u. Yarinyar Baabarku Hasiya ce. Anjuma dai Alhaji zai yi muku bayani sosai."
"Asma'u"
Na maimaita sunan a ƙasan raina. Kai na kauda ganin Rahila na tsallen murna to miye abin murna. Tana da ni to kuma miye na jin daɗi domin an kawo wata. Duk da akiyasin shekaru ba za mu girmi Asma'u ba tabbas sai dai mu zo tsara. Ni da Rahila tare iyayenmu suka yi goyon cikin mu kwana arba'in ne cif a tsakaninmu.
Lokacin da su Yaya Murja suka yo sallama suka shigo gidan suma da Kayan islamiyansu ni kuma na yi sallama a ɗakin Mama Alhajinmu ya amsa sannan na shiga. Sannu da zuwa na yi masa ya amsa ya na kishiɗen kan kujera ganina ya sa ya ɗan miƙe zaune ya na faɗin" Dubu. An dawo?
Na amsa ina gurfanawa a gabansa.
"Alhajinmu ina tsaraba ta? Ko Hajiya ba ta baka wani abu ka kawo mini ba?
Abin da na fara faɗi kenan kuma kamar ba haka ya dace na ce ba. Ƙila ya dace na ce ne" Alhajinmu wace ce ka zo da ita? Amman ban ce ba. Shi kuma bai damu ba yana yar dariya ya ce"Tsaraban ki ta gyaɗa ta nan. Sai da Hajiya ta jadadda mini ke kaɗai ce mai gyaɗar nan."
Ina jin haka na washe baki na zauna ina tambayan ya ya baro su Baba Aminu ya amsa da duk suna gaishe mu.
"Alhajinmu yaushe to mu za mu ce?
Saboda ina son garin Yashe ina jin daɗi in na je garin Hajiya ta na ji dani saboda sunanta aka sakamin shi ya sa ma Alhajinmu da su Gwaggo ke kirana Dubu. Sauran ƴan uwana kuma Sadiya.
"Sai kun samu hutun makaranta. Tun ga ma Asma'u in za ta je ganin gida ke da Rahila za ku riƙa rakata."
Kallonsa na yi kamar zan yi mgana sai na fasa. Sai kawai na bige da faɗin" Yaushe Hajiya za ta dawo gidanmu da zama?
Alhajinmu ya muskuta kafin ya ce"Sai na gama ginin gidana Dubu. Akwai ɗakin Hajiya sai na ɗauko ta zauna damu? Hakan ya yi ko?
Sai na gyaɗa masa kai ina mirmishi. Labarin makaranta ya tambayeni na gyara zama ina bashi labari sai da aka kira sallar mangariba sannan hiran mu ta katse.
Kowa ya yi alwala domin gabatar da Sallah. Alhajinmu shi da Yaya Abubakar da Yaya Auwal sai Datti suka tafi masallaci Yaya Hamza baya nan ya na Niger can ya ke karatun babban sakandirinsa. Shi Yaya Abubakar je ka ka dawo ya ke yi anan cikin garin kano.
Ina zaune a gefe ina ganin yadda ƴan gidanmu ke kara kaina akan Asma'u da Yaya Murja ta fara laƙaba mata sunan Ma'u da ya kashe Asma'un ma gabaɗaya. Kowa na rawan jikin tambayata abin da take so ta ci Rahila har tana ɗaukan kayanta ta na saka shi cikin jakar kayan mu na sawa tun da kayanmu na waje ɗaya ne. Ni dai ko magana ta fatar baki ba ta haɗa mu ba kusa da ita ma ban je ba. Har da Gwaggo da Mama a masu kai da kawo akan Ma'u.
Sai da aka yi isha'i su Alhajinmu suka dawo. Kowa ya ci tuwon da Mama ta yi amman ban da ni ba kuma ba na jin yunwa ba ne ina ji amman Rahila ce ta baƙan ta mini rai.
"Mama ki haɗa mana Tuwon mu tare da Ma'u ko Sadiya?
Tsabar haushi sai kawai na ce"Ni ban ci.".
Saboda na ga daga zuwan yarinya amman Rahila ta fifita ta sama da ni kawai sai na ce na ƙoshi.
Gwaggo ta kalle ni kafin ta ce"Me kika ci?
Sai na rausayar da kai kafin na ce"Bakomai."
Sanin halina na tsirfa wani lokacin sai Mama tace a rabu dani.
Ranar na sha mamaki domin Ma'u kasa cin tuwo ta yi tana ta jagwalgwalawa har su Alhajinmu suka shigo a ka shimfiɗa babban tabarma a tsakar gida ana zazzaune ana cin tuwo ni kuma ina daga gefe ina kallon kowa ɗaya bayan ɗaya.
"Bakuwar nan fa kamar ba ta cin Tuwo"
Yaya Abubakar ya faɗa duk sai suka kalleta. Haka ne ko ba ta ci sai wasa take yi da shi a hannunta.
"Ko ba ta cin Tuwo ne Alhaji?
Cewar Gwaggo. Mama ke ce tambayan Ma'u ko ba ta cin tuwo dai dai lokacin da Alhajinmu ya ce"Anya. Ban sani ba. Asma'u a siyo miki wani abun ne?
Sai ta kalle shi amman ba ta yi mgana ba.
"Za ki sha shayi?
Yaya Abubakar ya faɗa sai ta kalle shi sannan ta ɗaga kai alamun eh. Na sandare a zaune lokacin da Alhajinmu ya ciro kuɗi daga aljihunsa ya ce Yaya Abubakar ya je ya haɗo kayan haɗa shayi a haɗa ma Asma'u tunda ba ta cin tuwo. Da fitansa da sauri da tashin da Rahila ta yi ta ce bari ta sa ruwan zafi sai Mama ta ce akwai ma a saman tukunya a madafi.
A daran nan dai Ma'u shayi ta sha da buredinta. Ahalin har Alhajinmu tuwo ya ci. Gabaɗaya hankalin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 31