Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amman ba dai ka ji bakin su ba. Shi ya sa na ce a gidanmu kowa da irin halin da ubangiji ya yi masa dai dai gwargwado da zai zauna da mutane. ****** *2000* *Ɗorayi* Hajiya Dubu ce ta ƙure Radiyo ɗin ta a tsakar gida tana sauraran gidan radiyon jihar kano ana karanto labaran yammaci. Zaune take saman tabarma daga can ƙofar ɗakinta. Gwaggo na gefen ta suna jin labaran jefi jefi Mama ma dake  can gefe tana tankaɗen garin masara a cikin farantani. Tana ɗan saka musu baki jefi jefi. Ina kwance a kan gadon Hajiya Dubu har wani ƙara nitsewa ne ke yi. Ba wanda ya san ina ciki saboda gadon mai rumfa ne. Kuma san da na shigo har Hajiya Dubun ba ta sani ba. Yau alhamis ba islamiya kuma ni ce ke da girki gabaɗaya na gaji. Da rana alkubus ɗin alkama na yi gabaɗaya a gajiye na ke daman kun sani yar laushi ba na son aiki kawai ina kwance bayan na idar da sallar la'asar ina hutawa Mama ta leƙo ta ce min na fito na ɗora miya a lokacin tura baki na yi kafin na ce. "Mama Tuwo kuma? "E." Haka ta faɗa tana kallona idanuwana har ya ciko da ƙwallah. Gaskiya dai na gaji kuma a ƙasa ƙasa sai da na ce na gaji Mama ta yi tsaki ta na sakin labule kafin ta ce"Ke daman ai ko kina kwance ne sai kin ce kin gaji. Malama ki taso kar dare ya yi kin kuma san Alhaji ya hana ku tuwon dare." Na fi mintina talatin kafin na taso sai da Mama ta ƙara leƙowa tama faɗin za ta make ni. Ni kaɗai ne a ɗakin Amina ta bi su Rahila yau wata yar islamiyan mu na aure ni daman ba na zuwa biki ban je ba ina gida amman daga baya na fara nadama da na sani na bisu sai na ga wanda zai tsaya har a ce ya yi tuwon dare. Shekaru wajen biyu kenan Alhajinmu ya ce aikin gidan da ya dawo kanmu ni da Rahila da Ma'u tun da alokacin mu ne ƴan matan gidan muna cikin shekaru na sha tara ne kuma muna zangon karatu na ƙarshe a matakin babban sakandiri a makarantar GGSS ƘAWAJI dake kwanar dakata a jihar kano.    Yaya Balki ma ta yi aure shekaru wajen huɗu da suka gabata. Yanzu a gidan daga mu sai Datti da ke ajin ƙarshe a ƙaramar sakandiri sai Amina dake ƙokarin shiga matakin farko a babban sakandiri. Sai Yaya Muntari da ya dawo gidanmu da zama shekaru uku yana karatu anan FEC KANO. Sai Hajiya Dubu da Alhajinmu ya ɗauko ta bayan mun tare a sabon gidanmu dake Ɗorayi. Domin Alhajinmu tuni likafa ta cigaba ya koma aiki da Hukumar KEDCO na jihar Kano. Sai Yaya Abubakar da ke karatu a jami'ar Bayero yana karantar Vitnary ya na shekara ta uku ne. Sun ɗaɗe a gida shi da Yaya Hamza kafim su samu su ci jarabawar babbar sakandiri a lokacin samun jami'ar ba ta wahala cin jarabawar sakandiri ne mai wahala wajen sau uku suna sake rubutawa sannan suka ci. Shi sai ya zauna a gida nan kano shi kuma Yaya Hamza sai ya lula Sokoto Usman ɗanFodiyo University Udus. Acan ya ke karantar accounting shima yana shekara ta huɗu ne. Yaya Auwal kuma yana Nasara state University  Keffi. A shekaran nan ya tafi shima. Mun zama ƴan mata duk wani tantanin budurci ya gama bayyana mana. Alhajinmu yana da burin in mun gama sakandiri mu yi aure. Ban san dai tunanin sauran ba amman ni ba ni da burin aure yanzu sai na gama jami'a na samu aiki saboda a lokacin Alhajinmu ya samu ƙarin girma manaja ne a hukumar wutar lantarki ta jihar kaduna kuma ya samu daman ƙaro karatu tun a zamanin baya. Ni ma sai na ji ina sha'awar haka. Rahila dai na san cewa ba ta da ra'ayi mai zurfi kamar nawa, Ma'u kuma har gobe ba jituwa a tsakanimu shi ya sa ni ban san me take ciki ba. Amman shekarun sun tura da ya sa na ƙara aminta da zargina na cewa Tana son Yaya Hamza shi kuma ba ta gabansa duka ɗaya ya ke ɗaukan mu. Shi kuma Yaya Abubakar a yanayin yadda ya ke kafa kafa da Ma'u son ta yake yi ita kuma baya gabanta ni dai ina gefe ina kallon komai ina tunanin ta yadda Ma'u za ta ɓullo ma lamarin ƴan'uwa guda biyu. Amman na ci alwashin ba zan bari ta zo gidanmu ta raba mana kan yan'uwa ba na san halinta ba ta da kirki kanta kawai ta sani. A yadda muka taso a haka muka girma. Ni da Rahila mune masu tsawon. Sai dai muna da bambamcin jiki ita Rahila ta fi ni kiɓa. Ma'u kuma muna da yanayin jiki bamu da kiɓa amman ita ba ta kai mu tsawo ba ta ɗauko tsawon mahaifiyarta ne Baaba dake can kura ta hayyaffa da wasu ƴaƴan bayan Ma'u. Amman kuma duk wanda ya ganmu ya san mu ɗin jini ɗaya ne. Ballatana ni ban cika yawo da Ma'u ba sai dai makaranta in ya zama dole a gida kuma ta shafa mini lafiya saboda ba na ƙyaleta. Sannan dawowar Hajiya Dubu gidanmu ya sa ba ma wanda ya isa ya taɓa ita da Yaya Abubakar sun sha artabu a kaina. Tun kuma da Hajiya ta dawo gidanmu na tattara kayana na koma ɗakin ta can na ke kwana sai in har na ga dama ne nake shiga ɗakin mu duk saboda kar na haɗu da Ma'u za mu kwana gida ɗaya mu tashi amman ba za mu yi ma juna mgana ba. In ko faɗa ya haɗa mu in na fara gaba da ita sai mu yi wata ba mu yi mgana ba sai in Rahila ta gaji ta kai ƙarar mu wajen Alhajinmu in ya yi mgana sai Ma'u ta ce in ta yi mini mgana ba na tanka ta. Sai a ɗora laifin a kaina amman thank god Hajiya na nan ita ce ke zama justice ɗina in dai akan Ma'u ne.   Bangaren Yaya Murja ma ba ta sauya zani ba. Ko bayan auran ta in dai za ta zo gidan da abun arziƙin da za ta kawo ma Ma'u da Rahila har da Amina ni kuma sai ta ce ba ni da kunya. Ni ma da na gane ko gidan zan iya kirga zuwana, na fi zuwa gidan Yaya Aina ko Yaya Balki in ma fitan ya kamani kenan. Har a lokacin ba ni da wata kawa da zan iya nunawa amman Rahila da Ma'u suna da ƙawayen su. Barin ma Ma'u ƙawarta din nan Shema'u har lokacin suna tare su Gwaggo duk sun santa ta na zuwa nan gida itama Ma'un ta na zuwa gidan su saboda su haɗu da Ma'u su yi ta munafunci  har can dakata tare suke a makaranta. Ni dai kamar yadda ban son Ma'u itama Shema'u ban ƙaunarta domin gabaɗaya halin su ɗaya. Za mu haɗu sau goma a makaranta sannu ba ta haɗamu da Shema'u amman in ta zo gida tana mini fara'a kamar ta Allah. Na daɗe da yarda da mganar hausawa da suka ce sai hali yazo ɗaya ake abota. To akwai mugayen hallayar Shema'u da Ma'u da suke kamamceceniya.   ****   Mama  ta shiga madafi ta ga na ɗora miya tana tafasa ko ƙashin miyan ma da Muntari ya shigo da shi ban saka ba sannan ban ko ɗora tuwo ba. Ba ta yi mamaki ba sanin halina sai ta fito tana faɗin" Sadiya me take son zama ne ni Rukayya? Gwaggo na zaune ta ce"Me ya faru hala? Sai ta kaɗa kai tana nufar ɗakin mu kafin ta ce" Ba ta ko ɗora tuwo ba. Kuma miya na ta dahuwa ko ƙashin da muntari ya shigo da shi ba ta saka ba." Lokacin ta ɗaga labulen ɗakin tana kwala min kira ina daga ɗakin Hajiya har na fara barci. "Ba ta fa a ɗakin" Hajiya hankalinta na wajen jin radiyonta ba ta ma jin su.  Gwaggo ce ta leƙo dakin Hajiya ta na kiran sunana na ji har gyara kwanciya na yi. Ban ankara ba sai ji na yi an ɗaka  mini duka a cinyata da sauri na miƙe ina sosa wajen sai na ga Mama tsaye a kaina tana huci. Cikin tura baki na ce"Kai Mama a cinya fa kika dake ni." "In ba ki tashi ba sai na mare ki a fuska yanzu." Ina jin haka na yi saurin saukowa daga gadon saboda na san halinta tana da saurin hannu. Ina fitowa na ga har mangriba ta yi Gwaggo ta kalleni ta na faɗin" Sadiya ho. Ke ko koyi da ƴan'uwanki ba kya yi. Su in dai suna da aiki akan lokaci suke gamawa." Haushin aikin dake gabana ya sa ban ko yi ma Gwaggo magana Hajiya ce ta kashe radiyon ta na faɗin" Me ya faru ne? Ke Dubu ina kallabin ki? Sai a lokacin na taɓa kaina ba ɗankwali ina tura baki na koma na ɗauko a saman gadonta da ya saɓule na ɗaura na fito dai dai Hajiya na faɗin" Dare ya yi ina su Asma'u ne? Su kama mata su yi girkin tare.' Jin haka sai na washe baki amman sai Mama ta ce" ƙyalata ta Hajiya. In na su aikin ne tana ɗaki kwance kauda kara ba za yi musu ba. Sai su ne za a ce su yi mata na ta aikin? Sai murnata ta koma ciki sai dai Hajiya ta sake ƙwatana da ta ce"Ita ai ba yanayin su ɗaya ba. Tun da sun fita zafin nama ai ba a zauna a zama ɗaya ba." Jin haka yasa na miƙe da karsashina saboda na san in su Rahila suka dawo sai Hajiya ta yi musu mgana sun tayani. Icce na haɗa na ɗora Tuwo Mama na ta faɗan in ina girki har jajjage ita ke yi mini kawai na fito na ɗora ina jin ƙyashi na duba har wanke wanke da sharan tsakar gida da Amina ce ke yi sai da ta yi kafin ta fita sai ni da in dai ina da aiki sai ran kowa ya ɓaci ina cikin madafi ina tura baki amman raina fes domin na samu raran kuɗin cefane Alhajimu 2k ya ba ni kayan Miya kawai na siya kashi daman yaya Muntari ya kan tura ma kuɗi in dai za a yi miya ya siyo. Kuɗin cefane ke saka ni farinciki in ranar aikina ya zagayo amman bayan haka yini na ke yi cikin baƙin ciki sai na ji gabaɗaya duk na gaji kamar mahaukaciya haka nake komawa a irin yanayin ana takata sai na yi sati ina gaba da mutum.   Ana kiran sallar mangariba su Rahila suka shigo. Gwaggo sai da ta yi musu faɗan da Alhaji ya shigo fa. Ma'u ce da yanayin mganarta ta ce" Mun taso da wuri Gwaggo rashin abun hawa ne." Ina madafi ina talge da fitila a hannuna ba wuta. Na gama kenan na rufe na fito nepa suka kawo wuta. Miya ta isa kaɗi har na kwashe ƙashin ina fitowa Rahila ta kalleni yadda na yi kaca kaca kafin ta ce" Wai ke ba ki gama tuwon ba daman?   Wani kallon tara saura kwata na yi mata na wuce ta. Ba domin ta matsa ba sai na bangajeta. Ma'u  wajen rijiya ta nufa bayan ta miƙa ma Amina Hijabinta ta kai mata cikin ɗaki wajen Hajiya na nufa ta miƙe tana kwashe tabarma tun da an kira mangariba raɗa na yi mata a kunne. "Hajiya ga su Rahila nan." Sai ta kalleni kafin ta juya ta na kallon Rahila wacce ke mgana da Ma'u. "Rahila da Asma'u in kun yi sallah ku kama ma Dubu aikin nan ta gama kafin Sule ya shigo." Rahila ta amsa da to amman Ma'u sai da ta kalleni nima na kalleta gwalo ta yi minibni kuma na ɗauke mata kai na koma kitchen. Gwara na kaɗa miyar da kaina na bar musu su ƙarisa tuwon. Sai da na kaɗa miyar na sauke sai na saka ruwan wanka ni kuma na je na yi alwala saboda ma ba na son mgana a ɗakin Hajiya na yi sallar mangariba na kuma yi zama na ƙarshenta dai Rahila da Ma'u suka ƙarisa tuwon Alhajinmu ya shigo gida bayan isha'i lokacin ina wanka a bayi daman ina ta Allah Allah na gama na fito kar ya dawo.   Ina fitowa yana tsakar gida an baza masa tabarma. Na so na yi saɗaf na shige ɗaki amman hakan bai samu ba sai da ya ganni.   "Dubu" Dole na amsa ina kallon shi faɗa ya fara min na wankan dare wannan karon ma Hajiya ce ta fito ta ƙwace ni.   "Sule ka ƙyale yarinyar nan. Yau fa a tsaye ta yini tana aiki har daren nan gwara ta yi wanka ko ta ji daɗin barci."   Alhajinmu ya yi shuru amma Mama sai da ta ce" To ta riƙa yin aikin ta da wuri mana. Sadiya son jikinta har bani tsoro ya ke in ta yi aure ban san ya za ta yi ba " Alhajinmu sai da ya yi dariya kafin ya ce" In ta ga ta samu ɗakin kanta za ta yi ne Rukayya. Nan saboda ta ga akwai su Asma'u ne in ba ta yi ba su za su yi." Ni dai na samu na shige ɗakinmu tunda nan ya fi kusa ina shiga na ga Rahila da Ma'u ana ta hiran bikin da suka je. Na yi kamar ban gan su ba mai na ɗauka na shafa ina da sauran kaya a ɗakin na buɗe jakar Rahila na ɗauko wata rigata na saka kafar Ma'u na wajen da gangan na taka ta saboda na ga ita ba makauniya ba ce ta na ganina a wajen ba ta janye ba. "Dutse kika taka hala? A sakarce na kalleta kafin na ce"Wataƙila." Ta yunƙuro za ta yi mgana Rahila ta hana ta da cewa" Kyale ta Ma'u. Ke kuma Sadiya don Allah ki koyi zaman lafiya." Na kalli Rahila kafin na taɓe baki ina faɗin" Sannu yar koran gimbiya." Haka na ke ce mata in na ga tana haƙiƙancewa akan lamarin Ma'u. Wani lokacin Rahila ba ta cika ban mamaki ba irin Yaya Abubakar bai ɗaukan lamarin Ma'u da sauƙi amman ina masa uzuri makauniyar soyayya ce ke damun shi.    Tun bayan dawowar Hajiya kano rabon mu da garin Yashe amman dai su Baba Aminu suna zuwa duba Hajiya in kuma wani sha'ani ya tashi ƙwansu da ƙwarƙwatan su. Ma'u dai ta manta da gidan tsoho ba zuwa take yi ba. Kuma ni dai ban taɓa ganin wani daga cikin dangin babanta ya zo nemanta ba. Amman tana zuwa kura wajen Baaba itama Baban na yawan zuwa kuma duk saboda Ma'un ne. In ta tashi zuwa tare da Rahila suke zuwa ni ko in yi zamana a gida ban taɓa marmarin zuwa ba. Tun da na fahimci Baaba ba ta ƙaunar uwata nima daga ita har yarta ba na som su tun ballatana da na fahimci Baaba na da son abin duniya.   Ko irin a makaranta ƙawaye an sha zama kowa na faɗin irin ra'ayin mijin da zai aura ni ba na mgana saboda ra'ayi na ya bambamta da na kowa. A lokacin maza ba sa gabana duk da an sha tare ni a hanya ban taɓa maida kai ba saboda har a lokacin ban sami irin zaɓina ba. Rahila kuma daman na fara zargin suna soyayya da Yaya Muntari. Na daɗe ina mamakin shi so daman haka yake? Saboda Ya Muntari gajeren namiji ne kuma baki sannan yana da barkwanci ni dai ban ga abin so a wajen shi ba anawa tunanin kenan Ma'u ko an taɓa tare ta a hanya muna tare ta ce ita ta na da miji. Buɗe bakin Rahila tana dariya sai ta ce. "Yaya Abubakar ba. Na sani kun dace kwarai Ma'u." A lokacin Ma'u ta kasa yin gaddama amman yanayinta ya sauya ni kuma ina gefe ban ce komai ba a raina na ce maji ma gani an tura uwar amarya biko. Kuma gashi Ma'u da jinin masu kuɗi amman ba ta sauraran kowa ni dai masu cewa suna sona daga malaman islamiyamu sai na boko ita kuma Rahila gajerun maza kamar Yaya Muntari da ta sauya ma suna zuwa Yaya Muktar. Shekara ɗaya ta shafe tuni har mun zana jarabawar fita babban sakandiri a ƙarshen shekaran  2000 sai dai dukkanmu ba wacce ta ci sai mu ka dawo zaman gida. Lokacin Yaya Abubakar da Yaya Hamza sun gama karatun su suna hidimar ƙasa. Shi Yaya Hamza can sokoto ya yi zamansa yana hidimar ƙasarsa. shi kuma Yaya Abubakar nan kano wani ƙaramin asibiti na dabbobi kuma ya gamawa suka riƙe shi duk da yana ta cewa zai ƙaro karatu shi kuma Yaya Hamza bai tsaya ba tuni ya nemi gurbin masters a University of Ibadan. Sai dai in ya zo gida hutu bai ma cika zuwa ba bai wuce a shekara sau uku haka ba. Mun sake zana jarabawa a 2001 shima dai ba a dace ba. Ga shi su Baba Aminu sun fara mganar ya kamata Alhaji ya aurar damu. Tun da lokacin 15 16 ake aurarwa mu gamu sha tara muna shirin shi ga ta ashirin amman ba mgana ƙwaƙƙwara gwara ma Rahila mganarta da Ya Muntari ya kai gaban Alhajinmu kuma ya yi murna ƙwarai. Kowa kuma ya yaba da haɗin tunda su suka haɗa kansu. Ni ce dai haɗin ke ban dariya in ta yi ma Rahila dariya in na ga ta na rawan jiki akan Ya Muntari. To gwara shi ana son shi. Shi fa Yaya Abubakar yana yi ne amman kwata kwata kamar ba a son yana yi ba.   In da ma su Gwaggo suka fahimci yana son Ma'u bini bini sai ya je Kura gaida Baaba da ɗan siyayyan shi itama kuma ta fahimta. Magana dai ta yaɗu a tsakanimmu amman ba ta je wajen Alhaji ba. Su Yaya Murja kar a ji labari tana faɗin tuwona maina ne za'ayi ita ƙanwar ango sannan yayar Amarya. Ban taɓa tunanin Ma'u da Baaba za su iya tunanin abin da suka aikata ba. Domin Yaya Abubakar kafin ya kai mganar Ma'u wajen Alhaji ya yi magana da Gwaggo sai ta tambaye shi ko ita Ma'un tana son shi sai ya ce a'a bai bayyana mata ba sai ta ce ya nemi yardan Ma'u.     Abin da ya sa na san haka ya faru. Ranar wata asabar da daddare Yaya Abubakar ya kira Ma'u zuwa zaure na fito daga ɗakin Hajiya na gansu sun wuce shi ya sa na bi bayansu a lokacin ne na ji yana faɗa mata yana sonta ya faɗa ma Gwaggo ga abin da ta ce. Ma'u ba kunya ba tsoron Allah ta buɗe baki ta ce ma Yaya Abubakar ya yi haƙuri ita a matsayin yaya ta ɗauke shi ba da wani manufa ba tun da aka kawo ta gidan nan Yaya Hamza ta ke so. Ina laɓe ina ganin har duƙa mata ya yi amman Ma'u ta fara kukan munafunci sai ya ce shikenan saboda ita muguwa ce sai ta ce wai ya taimaka ya rufe mganar ba ta so Alhajinmu ya ji shi kuma ya ɗau alƙwarin ba wanda zai ji Gwaggo ma zai san abin da zai faɗa mata. Kafin ta taho na shige ɗakin Hajiya ina maida numfashi ta na kwace sai da ta ce" Dubu lafiya? Ina sauke numfashi na ce" Ba komai Hajiya." Ranar ko barci ban yi ba ina tunanin mafita ko da ba shiri tsakanina da Yaya Abubakar jinina ne. Na ji tausayin shi da ya sa na fara tunanin yadda zan ɓullo ma lamarin. Washegari na je gaida Alhaji sai ga Ma'u bayan sun gaisa ta ce wai in Alhaji ya bar ta za ta je kura wajen Baaba. Ina jin haka na ji a raina akan Yaya Abubakar ne. Saboda lokacin wayar hannu ba ta daɗe da shigowa ba sai wane da wane Alhajinmu kaɗai ya mallaketa. Ina jin sanda ya ce shikenan sai ta shirya cikin ni ko Rahila wata ta rakata ina jin haka na yi karaf na ce" Alhajinmu ni zan rakata."    Ba Ma'u ba har Alhajinmu sai da ya yi mamaki. Ma'u kam sake baki tayi kawai tana kallona. "Lalle Hasiya na da babbar baƙuwa." Haka Alhajinmu ya faɗa ni ai ban tsaya ba na koma ɗakin Hajiya ina haɗa kayana Hajiya ta ce lafiya na ke haɗa kayana.? "Ma'u zan raka kura wajen Baaba." Da mamaki Hajiya ta kalleni ba ta da wani karfi kwana biyun nan ba ta da lafiya ta na fama da zazzaɓi sai da aka kaita ma asibiti. Maida kanta ta yi ta kwanta lokaci ɗaya ta na faɗin" Yau kuma? To Allah ya tsare." Kowa ya ji zan raka Ma'u sai ya yi mamaki har Rahila sai da ta ce"Allah ya sa Sadiya kin sauya kenan." Ni ba na ta kanta ni na san abin da zai kai ni. Ma'u ba ta da yarda za ta yi ta na ji ta na gani na shirya kayana Alhajinmu ya bamu kuɗin mota mun bar gidan ba ma mu haɗu da Yaya Abubakar bawan Allah shi kaɗai ya san abin da ke damunsa. Har muka isa kura sannu ba ta haɗamu da Ma'u ba. Mun isa gidan Baaba ita kanta ta yi mamakin ganin mu tana da abokiyar zama. Zaman dai ba wani daɗi ita kanta ta yi mamakin ganina tare da Ma'u cikin mamaki ta ce" Yau kuma wannan ce ina Rahilan? Ma'u ce ta amsa da cewa ni ce na rakota wannan karon. Duk da ban samu tarban da ya kamata ba ban damu ba Zainab ce kawai ƙanwarta ta kulani duk da ta na ƙarana ne sai sauran ƙannenta maza. Bayan mun yi salla mun ci abinci Ma'u na son keɓewa da Baaba amman ba hali tun da na hana ina wajen. Sai daddare sun ɗauka na yi barci suka ƙule cikin ɗaki ba su san ina kwance laɓo ina dakon su ba. Ina ganin sun shige ciki nima na tashi saɗaf saɗaf na laɓe ta jikin labule a daga nan na ke jiyo muryan Baaba ƙasa ƙasa. "Shi wai Abubakar ɗin ya ce ya na sonki? Ma'u ta ɗaga kai cikin damuwa saboda ina hangosu ta jikin labulen ƙurwan ɗakin Sai kawai Baaba tayi tsaki kafin ta ce" Shi ma dai da rigima ya ke. Ai ke matar manya ce duk da ban raina Abubakar ba. Sai dai tunda Hamza kike so shi ne zaɓina kuma ba kin ce yana can yana cigaba da karatu ba? Nan gaba Allah kaɗai ya san abin da zai zama." Ma'u ta kalli Baaba kafin ya ce" Baaba ya zan yi? Har fa ya faɗa ma Gwaggo. Kuma su ma yan gidan sun fara gane yana so na ba na so Alhaji ya ji labari Yaya Abubakar ya yi min katanga da abin da na ke so.' Baaba ta kama hannun ta lokaci ɗaya tana faɗin" Kwantar da hankalin ki. Gobe da safe ku koma gida ni kuma cikin satin nan zan shigo. Da ikon Allah ke rabon Hamza ce." Sauri na yi na koma wajen kwanciya a falo a saman katifa na yi kamar mai barci sai can bayan wani lokaci Ma'u ta fito ta dawo ta kwanta a gefena. Ta kwana mutsu mutsu nima haka a cikin raina ina tunanin ta wata hanya zan hana Baaba aiwatar da kudirinta? Har muka koma kano ban samu mafita ba. mun koma mun iske Yaya Abubakar na kwance ba lafiya daga ni sai Ma'u muka san dalilin ciwon shi. Zazzabi da ciwon kai har dai da Yaya Muntari ya raka shi asibiti ya ga likita.  Na ɗauka Ma'u za ta tausaya masa amman sai na ga kamar ba ta da tausayi ban samu mafita ba har Baaba ta zo gida ta kuma tara su Alhajinmu ta kawo mganar Ma'u tana son Hamza tun tuni ganin abin na gida ne yasa ta zo da mganar Alhajinmu na jin haka ya fara murna ya ce kuma zai aurama Ma'u wanda ta ke so. Gwaggo ta na so ta yi mgana amman Baaba ta san me za ta ce sai ta datse ta. Bayan an gama zaman a ɗaki Hajiya Dubu ke faɗa mini abin da ke tafe da Baaba. Daman na san za a

Chapter 18 of 31