Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na koma cikin gida sai na ga Aneesa da wayata wai ana ta kirana ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne da sauri na ɗaga kiran. "Yallaɓai ka taho ne? Cikin wani irin murya ya ce min" Sadiya ta congratulation." Ina yar dariya na ce" Yallaɓai ka biya mini makka ne? Shima dariyan ya yi kafin ya ce" In sha Allahu ina saka ran haka, amman dai yanzu ina so na faɗa miki ne an biya ni half payment na aikin nan namu na Rano." Cikin murna na ce" Don Allah fa Yallaɓai" "Allah Sadiya ta. Yanzu kuɗin suka shigo sun kuma kirani sun faɗa mini." Ɗakin Mama na faɗa ina faɗin" Alhamdulillah mun yi kuɗi" Ya na yar dariya ya ce" In an yi mangariba zan fito sai na zo mu dawo tare" Da haka muka yi sallama, muna gama wayar na yi hamdala ina jin daɗi Allah ma ji roƙon bayin shi. Na ƙosa mangariba ta yi ma saboda murna, ina idar da sallar mangariba na shirya lokacin har Yaya Murja ta tara yayanta sun tafi gida ni da Ma'u kawai ne a gidan ita kuma tana tare da Baaba. Yallaɓai sai bayan isha'i ya zo, ya ƙara duba Alhaji sannan na yi musu sallama  muka tafi gida. Muna hanya ya kalle ni kafin ya ce" Yanzu da me zamu fara Hajiya ta? Ina dariya na ce" Mu je gida mana Alhajina." Sai muka kalli juna kafin mu kwashe da dariya, ni ko har ina dukan kafaɗansa kafin na ce" Ranka ya daɗe  mai girma Tafida." Shi dai ya na ta dariya ni kuma ina masa kirari "Angon Sadiya Ɗan gatan Nene, uban Jidda da Maimuna. Allah ya ƙara ja zamanin Tafida mai girma Injiniyan gine gine, mai muƙamin zane zane takawar ka lafiya" Ya na dariya ya ce" Me kike so Sadiya? Ina masa dariya na ce" Me kuwa na ke so? Yallaɓaina kaɗai na ke so." Gira ya ɗaga min kafin ya ce" Kin yi kyakyawan zaɓi kuwa." Muna tafe muna hira, har muka isa gida. Baby har ta yi barci, dole na tashe ta tana kuka tana komai na yi mata kitso, Yallaɓai na ta faɗan wai ban iya kitso ba ne na saka yarinya tana kuka. Baki sake na kalle shi kafin na ce" Au ban iya ba ko? Ya na kallona ya ce" To ni dai ban san lokacin da kika koyi kitso ki ka iya ba" Sai kawai na yi banza da shi Jidda dai lafiyan lau muka yi kitson mu, sai bayan na gama mu su ne na ce su yi shirin kwanciya Baby daman Babanta ya lallasheta har ta yi barci. Wanka na sake yi na yi shirin kwanciya Tea na haɗa mana muka sha sannan muka zauna kassafa kuɗi, abu na farko kayan abinci na yi masa mgana sai kuma na ce ya ijiye kuɗin makaranta yara tun da sun kusa fara jarabaawa. "A'a ki bari sai zuwa lokacin ai da sauran lokaci." Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda na san wataƙila zuwa lokacin ya zo babu, mun yi mgana ya cire wasu kuɗi saboda Gidan bulo da office sai na yi masa mganar Halima ta haihu ba a yi mata komai ba sai ya ce zai turamin 20k ya ce a siyi abin da ya kamata ina so na ce ya rage min ko kaɗan a cikin kuɗina amman ban yi ba kamar ya san me na ke tunani sai ya ce "Zan ba ki 50k ki rike a hannunki. Kuɗin ki kuma in gwammati ta biya mu sai na baki duka in sha Allahu." Ina yar shagwaɓa na ce" Yallaɓai buɗe saloon ɗin fa? Da sauri ya ce" Wannan ni na ce zan buɗe miki, kuɗin ki kuma haƙƙn ki ne zan biya ki in sha Allahu." Sai ya ga na yi shuru sai ya shafa kumatuna kafin ya ce" Kar ki damu. In sha Allahu duk za a yi." Sai na gyaɗa masa kaina. Mun cigaba da lissafi ya ce 30k na kayan maggi da kayan tea, sai na ce ai ya haɗa gabaɗaya cikin na kayan abinci tunda tare muke siya a kasuwa a wani babban shago yana da lambar wayarsa list ɗin kawai zan rubuta ya tura masa da ƙudin har gida za a kawo mana kayan abinci. Har da sabule da omo, ni kuma sai ya ce zai ƙara mini 30k saboda siyayyarmu ni da yara su Unders da sauran kayan kwalliyan mata. Kuɗin asibiti kuma ya ce zai ware mini 50k saboda bamu san nawa za a nema ba sai dai goben in mun je mun gani. Sauran kuma ya ce zai yi amfani zai sallami sauran ma'aikata da shi ko da rabi rabi ne, ni na san har da kyatttuka sai ya yi in dai Yallaɓai ya samu kudi kamar suna masa kwaiƙwayi ni na yi masa mganar Nene, daman in za mu yi siyayya kayan abinci har da ita da kayan tea sai sabulan wanka sai ya ce na rubuta list ɗin gabaɗaya sai ya tura babban shago za a kawo kayan zuwa gobe in sha Allahu. Sai na ce to a daran na rubuta abin da na manta na ce zuwa da safe zan tuna. Saboda zuwana asibiti tun asuba na tashi na yi ma yara shirin makaranta Yallaɓai jiya ya siyo indomie da kwai , sai buredi sai na soya musu buredin da tea ɗin suka tafi da shi makaranta, ni kuma muka shirya daman tun safe na tura ma Dr Fatima saƙo sai ta dawo min da amsar za ta ƙara kiran Dr Aisha ɗin amman na je asibitin na siya kati za a kai ni gynea unit ɗin in ce dai Dr. Aisha na zo gani a shigar mata da Fayel ɗina za ta duba ni in sha Allahu. Tare muka fita da su Jidda muka kai su makaranta daga nan muka wuce Aminu kano. Da taimakon Yallaɓai nan da nan muka siya kati har aka yi mana hanya zuwa Gyea Unit da taimako  irin masu zirga zirga rarraba katina Yallaɓai ya yi ma ihsani, ya faɗa mai mun zo ganin wata Dr Aisha bukar ne. Wajen ta zai kai mini Fayel ɗina sai ya ce ba matsala ba ta ƙariso ba amman tana hanya. Sai wajen tara da wani abu likitocin suka fara zuwa. Muna zaune da Yallaɓai bangaren yan jira aka shigar da Fayel ɗin mu, Saboda ihsanin da Yallaɓai ya yi mishi sai ya shiga ciki ya yi ma Dr Aishan bayani sai ta ce eh ta na sane fayel ɗina daman a sama ya saka min ni ce ta farkon da aka fara kira na shiga ganin Dr Aisha Bukar kamar yadda ke rubuce jikin Office ɗinta. *Janafty* *TURKEN GIDA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Eaman ScholarSphere. Where ideas Take Shape. WHAT WE DO. ASSIGNMENT PRESENTATIONS. ARTICLES PROJECTS. BOOK AND MANY MORE. CANTACT US THROUGH. 02347067793152 MOTTO: "Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures" *🅿️15* Aminu kano Teaching Hospital. Gynecologist Unit. Ina zaune a kan kujeran da ke fuskarta wajen zaman likita. Idanuwana kir a kan Dr Aisha Bukar ina ƙare mata kallo. Ta fi Dr Fatima shekaru ita babbar mace ce gaskiya a kallah in ba ta haura 40 ba za ta tsaya a hakan ta na da kaurin jiki, ga tsawo ga kiba sannan ba ta da wani haske sosai. Tana zaune tana duba fayel ɗin gabanta gefe ɗaya kuma hankalinta na kan system ɗin dake gabanta da alama dai akwai abin da ta ke dubawa a ciki. Fuskarta da gilashi siriri sannan sanye take da rigan likitoci kanta kuma ta sanya ƙaramin breziya Hijab fari. "Sadiya Sulaiman Yashe" "Maa." Ba ta kalle ni ba hankalinta na kan system ɗin gabanta ta ce" Ke ce wacce Dr Fatima ta yi transfer ɗin ki daga ABU KO? Sai na gyaɗa mata kai lokaci ɗaya da cewa" Yes"  Saboda da turanci ta yi maganar. Tsayin mintina goma sannan ta ce" Ga Report ɗin ki da ta tura mini  ina kan dubawa." Da hausa ta yi mganar wannan karon kafin ta dawo da hankalinta kaina. "Sunana Dr Aisha Bukar. Zan cigaba da jagorantar matsalarki har zuwa lokacin da za ki samu waraka in sha Allahu." Ba ta jira jin ta bakina ba kawai ta cigaba ta faɗin. " A yadda na ga ɗan brief na matslar ki, kafin mu je kan matakan da muke ɗauka ga masu irin laluran ki, kin san abin da ke damun ki? Ko dalilin da ya sa ba ki sake haihuwa ba? Na ɗaga mata kai zan yi mgana kawai cikin zaƙin muryanta ta ce. "SECONDARY INFERTILITY"   Kai tsaye kuma ta cigaba da bayanin ta. "Kuma shi  Secondary infertility ( rashin samun ciki bayan mace ta haihu ko hayayyafa) yana faruwa ne lokacin da mace ta haihu sai kuma haihuwa ta zo ta ɗauke kwata kwata ayi ta nemanta ruwa a jallo amma bata samuwa wani lokacin har sai an dangana da asibiti. Mace a haihuwar farko ta san lafiyarta lau saboda ta samu ciki ba tare da neman taimakon likita ko shan magani ba, amma kuma daga nan sai haihuwar tayi ɓatan dabo." Nan ma sai ta ɗan dakata kafin ta cigaba da faɗin. "Yawancin abubuwan da ke haifar da secondary infertility sun haɗa da low egg quality(wato kwan haihuwar mace ya kasance baida karfin haihuwar) matsalar mahaifa, matsalar rashin karfin maniyyi, yanayin abinci da wasu abubuwan wanda suka danganci rayuwar mace kama daga yanayin cututtuka da uwa uba Family Planning" Ta ɗan ɗago ta kalleni ganin ina kallonta sannan hankalina na kanta ya sa ta ɗan gyara zama gilashin ta sannan ta sake cigaba da faɗin.   "Babban abunda ke kawo secondary infertility musamman a kasar hausa shine family planning wato tsarin iyali. Yawancin mata idan sunyi tsarin iyali yana haifar masu da matsaloli wanda cikin matsalolin nan babbansu shine sanadin family planning. Family planning na haifar da jinkirin rashin samu ciki da wuri saboda karfinshi da kuma aikin da yake a productive system na mace Kama daga hormones har zuwa Reproductive organs "Kuma kowani abu ya na da Siide effect, kuma shi planning yana ninka adadin shekarunsa sau ɗaya ma'ana zai iya haurawa da kashi ɗaya, wani lokacin har biyu, kamar ke ɗin nan kin yi na shekaru biyar amman ya haura ki har shekara tara ba ki haihu ba, sannan kafin ki samu ciki side effect ya taɓa ki kin ta samun matsaloli ko? Ba ta damu da na amsa ba ta cigaba da faɗin. "Secondary infertility kuma mace ta taɓa haihuwa sai ta zo ta hanyar planning ko kuma haihuwar ta tsaya mata chak, shine za ta je asibiti ayi aune aune sai a bata maganin da zai dakile karfin planning din nan da kuma wanda zai taimaka mata wajen buɗe mahaifar ta da hormones ɗin don a samu cikin, kamar irin problem ɗin ki kin gane? Sai na gyaɗa mata kaina alamun gamsuwa. Tana mgana da hausa ta na haɗawa da turanci a maganarta kawai na fahimci ita ɗin kanuri ce saboda ba ta da hausa sosai. Fayel ɗina ta jawo ta fara rubutu kafin ta ce" Kafin mu kai ga ɗora ki kan mgani Akwai bukatar sai kin yi wasu gwaje gwaje kamar yadda tsarin mu ya ke." Mintina sama da biyu sannan ta sake ɗagowa tana kallona kafin ta ce" "Muna da gwaje gwaje a kallah guda tara waɗanda sai kin yi su gabaɗaya ne za mu iya gano ta in da matsalar ki take, da kuma hanyar da zamu ɗora ki kan mgani." Gwaje Gwajen da ake sun haɗa da 1.A semen analysis (mace da namiji zasu tara, sai a tara sterile container a debi sperm din daidai lokaci  da namiji ke kawowa, da gaggawa ake yin awon sbd kada sperm cells din su mutu kafin ayi awon wanda hakan zai iya lalata sakamakon da ake bukata a wannan awon ne ake gane cewa sperm din namiji na active zai iya haihuwa ko aa. 2.Blood tests to look at hormone levels (zai nuna level din hormones, suna over secreting ne ko under secreting) 3.A transvaginal ultrasound  4.A hysterosalpingogram, a type of X-ray that allows your provider to see your uterus and fallopian tubes( wannan da x-ray machine ake yin shi,zai nuna cikin mahaifa da kyallemun mahaifa duka honestly speaking its painful) 5.Blood tests. Samples of your blood can be tested for a hormone called progesterone to check whether you're ovulating. ... 6.Chlamydia test. Chlamydia is an STI that can affect fertility 7.Pap smears 8.FSH follicle Stimulatiing Hormone 9.LH Luteinizing Hormones All these are the most common primary and secondary fertility tests for women." Ta na gama yi min bayanan ta miƙo mini takardan mai tambarin sunan asibitin a jiki, hannuna biyu na saka na karɓa ita kuma sai ta maida hankalinta a wajen system ɗin gabanta. "Ki je lab ki kai musu, za su yi miki cikakken bayanin a can" A sanyaye na ce" Yanzu Dr? "Yes. Ki je yanzu a can za su ƙara miki ƙarin bayani da yadda za a yi." Sai na miƙe ina mata godiya. "Sai an baki result sai ki dawo mun da shi , on Monday ranar da zai ma ranar clinic ɗin ki." Na yi mata godiya sai kawai ta gyaɗa kanta. Ina fita na nufi Yallaɓai ya na ganina ya taso, sai na bashi takardan ina faɗa masa yadda muka yi da ita sai ya ce mu je lab ɗin. Tare muka je lap ɗin amman shi bai shiga ba ni ce na shiga na ba su takardan, laboratory ɗin da ya karɓa ya duba takardan sai ya ce. "Muna bukatar ki zo da mijin ki " Haka ya ce mini wani ɗan baki ne, kai tsaye na ce" Tare mu ke yana waje." Sai ya ce na je na shigo da shi, bayan mun dawo tare sun bamu wajen zama, sai wani lap tecnicial ɗin ya fara mana bayanin gwajin da za mu fara yi a matakin farko wato Semi analysis na sperm ɗina da na Yallaɓai." "Ya za mu iya kawo muku samples ɗin? Yallaɓai ya tambaya sai ya kora mana jawabi a tsanake, yanzu dai ya ce za mu fara yin bucking ko gobe ko jibi za mu iya kawowa amman mu kawo shi cikin gaggawa.  Kafin mu tafi sai da ya bamu sterile container  ya ce mu yi amfani da shi, kafin mu baro asibitin har kuɗin test ɗin sai da muka biya suka samu takardan da cewar sai jibi in sha Allahu za mu kawo ya yi ta jadaddamana da kar mu ɓata lokaci ana son a yi awon da gaggawa ne. Mun fito daga asibitin muna hanya sai kawai na yi tunanin bari na tsaya a kasuwa na ƴan siyayya ta daga nan na tsaya in yi saloon kafin na koma gida. Nan take Yallaɓai ya tura mini 50k kuma ya ijiye ni a kasuwar Wambai. "Yanzu sai ina? Na faɗa ina ƙoƙarin buɗe motar na sauka bayan mun iso shagon da na ke zuwa gyaran kai kusa da kasuwar Wambai. "Office zan fara zuwa akwai mutanen da zan gani." Sai da na fita sannan na leƙa ta window motar ina faɗin" Ka tura list ɗin ga babban shago saboda su kawo mana da wuri" Sai ya gyaɗa min kai kafin ya ce" Kin tabbata ba abin da za a buƙata daga baya? Jin abin da ya ce ne ya sa sai na buɗe motar na sake shiga na karɓi wayarsa na dubo list ɗin da na tura masa. Kallonsa na yi kafin na ce" Ina jin su kenan. Amman za ka iya ce ko zai duba wancan list ɗin? "In ya na da shi ba" Ina ƴar dariya na ce" Ya na da shi mana. Ai suna ijiye rocord saboda babban shago ne." Sai ya jinjina min kai kafin ya ce" ƙarfe nawa za ki koma gida? Ina gyara zaman mayafin jikina zuwa saman kaina na ce" Da na gama siyayya zan koma gida in sha Allahu" Hannuna ya riƙe ya sumbata kafin ya ce" Take care. Ki koma gida da wuri." Ni kuma sai na sunkunya na sumbaci ƙuncinsa ina faɗin" Allah ya ba da sa'a." Daga nan muka yi sallama ya sauke ni ya wuce, shagon wata Amesty ne anan na ke zuwa gyaran kai tun da daɗewa.  Ina shiga ta na ganina ta tarɓeni saboda mun saba da juna har lambar  wayar juna gare mu. "Hajiya zuwa ba waya? Ina zama kan ɗaya daga cikin kujerun dake cikin shagon na ce" Ba da niyyar zuwa na fito ba. Daga asibiti na muke sai kawai na ce Yallaɓai ya sauke ni anan, daman ina ta wa ƙen zuwa." Yaran shagon na ta gaisheni, ina amsawa ita kuma sai ta je ta ɗauko min ruwa. Ba musulma ba ce amman in ka ganta sai ka rantse musulma ce hausa a bakinta kamar jakar Kano dressing ɗinta irin na hausawa ne. "Na gode." Na faɗa lokacin da ta ba ni ruwa na karɓa na sha kaɗan saboda ina jin kishi. Amesty na zaune gefe na tana faɗin" Ina su Jidda kwana biyu? Ina Baby mai kuka." Ina dariya na ce" Duk suna makaranta." Saboda ba ko yaushe na ke yi musu gyaran kan ba, amma na fi kawo su lokacin salla ko biki saboda ba ni da lokaci tsayawa na yi musu. "Me za mu yi? Wankin kai ko Saloon? Sai na zare mayafina na tuɓe ɗankwalina na zame ina nuna mata kaina. "Saloon ko? Kamar wata biyu kenan ban yi ba." Ta na dubawa sannan ta kalleni ta na faɗin" Gaskiya. Bari mu yi Saloon ɗin" Daman in dai na zo da kanta ta ke yi mini saɓanin sauran da yaran ta ke yi musu, ni kuma muna yi duk abin da na gani ina mata tambaya saboda ɓarayina ne, na iya wankin kai Saloon ɗin ma na iya, Amesty na dariya ta ce" Hajiya wannan shagon na Saloon sai yaushe za a buɗe shi? Nima ina mata dariyan na ce" Yallaɓai ya ce Soon in sha Allahu.". Sai ta ce Allah ya nuna mana. Na yi awa ɗaya da wani abu a shagon Amesty, kafin a gama min Saloon kaina ya yi kyau. Ba ni da kuɗi a hannuna sai na ce zan tura mata ta banki in na koma gida da haka muka yi sallama ta rako ni har waje. Daga nan na samu Adaidaita zuwa cikin kasuwar Wambai akwai shagon da na ke siyan su bra da pant da kananun gajerun wanduna na yara nan na fara tsayawa na siya ma su Jidda pant da vest sai sikat na yara da ƙananun wanduna sai na siya ma Jidda da Baby dogayen wanduna baƙaƙe saboda makaranta. Har da safuna na siya musu farare da baƙake, nima na siya ma kaina pant da bra sannan na siya ma Marwa, daga nan na wuce shagon Musa mai kayan costimetic na siya irin su shampoo sai sabulin da su Jidda ke wanka, sannan na siya Veet da kayan wankin tiolet sai Moneyfresh saboda Mopping, na yi siyayya sosai na amfanin gidana har man kitso na siya mana. Saboda siyayya shago biyu ne kawai shi ya sa ban wani daɗe ba na dauki drop ɗin Adaidaita zuwa gida a ƙofar gida na ga Saude ta na jirana. "Shi ne ba za ki kirani ba?! In ban dawo da wuri ba fa." Kanta na ƙasa ta ce" Na kira ki ba ki ɗauka ba. Yanzu na zo fa daman." Sai da ta ce ta kirani sannan na tuna wayata na can cikin jaka, key na saka na buɗe gidan Saude ta taya ni ɗaukan kayan zuwa cikin gida duk na ji na gaji, ga cikina kamar an yi yasa kamar ban karya ba kafin na fita sai da na haɗa tea na sake sha sannan na dawo dai dai. Sai da na natsu sannan na kira Farida na yi mata ban gajiya da yadda suka koma gida. Sannan sai na kira Amina ba ta ɗauka ba sai na kira Khaleesat itama na yi mata ya hanya. Lailan ma Yaya Auwal mun yi mgana da ita. Da rana tuwo na yi tun da shinkar tuwon kaɗai ya rage mana. Saude sai wajen uku na rana na bata kuɗin mota ta tafi gida, ni kaɗai a gidan jin an kira sallar la'asar sai na yi sallah sannan na kira Yallaɓai nan ya ke faɗa mini ya na Rano ya je duba aiki. Ni kuma daman na manta ne ban faɗa masa mganar a saka drinks ɗin yara na makaranta ba da kayan kamshin girki tun da shagon babba ne a can kasuwar Singer ba abin ba sa saidawa. "Ai na tura masa na ce kuma ya saka duk abin da ya kamata." Sai na ce ya dai sake kiran shi ya faɗa masa sai a manta wani abun sai ya ce to. Sai shidda saura su Jidda su ka dawo, na so na yi wanki gajiya ya sa sai na ce bari na bari zuwa gobe sai na yi wankin. Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya dawo gidan yana tambaya ta ba a kawo kayan abinci ba? Na ce ba su kawo ba nan ta ke ya sake kiran shi manager ɗin sai ya ce a ba' a gama haɗa kayan ba ne sai zuwa da safe in sha Allahu. Da wuri muka kwanta su Jidda daman ko da Yallaɓai ya dawo sun kwanta. Ina kwance a saman ƙirjinsa sai na kira sunan shi. "Yallaɓai." "Uhm" "Ba ka ga Saloon ɗina ba ne" "Na gani mana"   Ya faɗa ya na ƴar dariya duk da ba na ganin fuskar shi amman ina jin sautin dariyan shi. Baki na tura kafin na ce" Shi ne ko ka ce ya yi kyau? Hannunsa ya kai ya zare mini hulan kaina ya na mai tura hannun shi a cikin gashin sannan ya kai hancinsa ya shinshina ya kuma sumbata da baki kafin ya ce" Kina da gajen hakuri. So na ke yi daman na baki kyakyawan tuƙwaici." Na ga ko kyakyawan tuƙwaici a daran nan sai da Yallaɓai ya saka ni jiƙa kai gabaɗaya kamshin Saloon ya bi ruwa ina tura baki na ce" Yallaɓai wannan tuƙwaicin naka ban yi maraba da shi ba." Yana min dariya ya ce" Saboda mene? Hararan shi kawai, na haye gado na shige cikin bargo ina tura baki, sai da ya tsane kanshi da danshin ruwa sannan ya hayo gadon ya na min dariya ni ko ko busar da kan ban samu na yi ba na dai tsane shi da towel. Har da asuba sai da ya ƙara jiƙa mini kai, lamarin yallaɓai ya ishe ni har sai da na tsare shi ina masa tambayoyi. "Yallaɓai ka faɗa mini gaskiya me kake sha ne a bayan ido na? Na faɗa ina mai tsare sa da ido. Muna dining ne bayan mun gama karyawa su jidda sun tafi makaranta. Wani kallo ya yi mini na bangane ba kafin ya ce" Kamar na me fa? Ina haɗe rai na ce" Ko ka siya manpower ne ka fara sha a ɓoye ban sani ba? Sai ya buɗe baki yana kallona kafin ya rufe ya na dariya. Ni ko ban yi dariya na tsare shi da ido ina faɗin" To Yallaɓai gwara na sani. Kana samu ɓarnan ruwa da yawa yanzu." Haɓa ya riƙe kafin ya ce" Fisabillahi Sadiya kamar ni na yi lalacewan da sai na sha wani abu za mu yi barnan ruwa? Kai na kaɗa kafin na ce" shi ne na ke tambaya." Miƙewa ya yi a kaina sai da ya yi mika sannan ya sunkuya dai dai kunnina na dama kafin ya ce." "Ke ba ki san muna girma  ba ne muna ƙara sanin daɗin abin da darajarsa ba" Kallonsa na yi sai ya dage mini gira kafin na samu zarafin mgana ya sumbaci wuyana da sauri na ture shi na miƙe ina hararanshi. "Miye haka? Saboda na ga ya na ƙokarin riƙo ni kuma yana min wani kallon ƙasa ƙasa. "Allah zan busar miki da gashin da kaina." Ya faɗa ya na ƙokarin jawo ni ai da sauri na warce na fara zagayen dining ɗin ina faɗin" Bar shi kawai na yafe. Ina da hannu" Shima sai ya fara bi na ya na faɗin" Kai Sadiya ta. Guduna kike yi yau kuma? Ya faɗa har yana marairaicewa. Na san halin shi cikin sauri na ce" E wallahi yau na guje ka." Dariya ya yi min ni ko na haɗe rai, haka muka dinga zagayen falon nan daga

Chapter 22 of 31