in na sauya waje da asibiti mai kyau da ke da ƙwararru kila za a iya gano wani abun har na nemi magani domin na samu waraka.
"Ki kwantar da hankalinki, sai mu je tare in sha Allahu "
Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce" Shi ke nan, Allah ya kaimu nan da kwana shidda kenan ko?
Sai ya amsa mini ganin duk na damu sai ya shiga lallashina, da cewa in sha Allahu ba wata matsala. Cikin yaƙinin da na ke dashi na ce" In sha Allahu."
Bai kashe wayar ba sai da ya ga na sake har muna hira da dariya sannan ya kyaleni.
Amman bayan mun gama wayar tagumi kawai na yi ina tunanin makomar rayuwata. Ina kwaɗayin na ƙara haihuwa, an ce komai na mahaifata lafiya kalau zan iya samun ciki kowani lokaci amman sai yaushe? Sama da shekaru uku tun ina saka rai har na fara gajiyawa? Ni kaɗai na yi ta kukana ina sharan hawaye kasa komai na yi kafin su Jidda su dawo makaranta jinin ya ɗan tsagaida sau ɗaya na sauya pampers, ban yi musu ko abinci ba cewa na yi su sha goldenmorn sannan in sun huta Jidda ta dafa musu ko farar taliya ne su ci da mai, ɗakina na koma kawai na kwanta ina jin kasala na rufe ni.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿️06*
Har bayan mangariba ina cikin ɗaki ban iya fitowa ba, na ci kukana har na ƙoshi na lallashi kaina. Baby ta zo za ta dameni da surutu na ce ta je Yaya Jidda ta kunna mata Cartoon. Ita kanta yarinyar ta lura da yanayina har yadda ƙasan idanuwana suka kumbura.
"Umma ba ki da lafiya shi ne kike yin kuka?
Sai da ta saka ni mirmishi, kanta na shafa kafin na ce" Lafiya ta ƙalau. Je ki wajen Jidda, kun yi sallah ko?
Sai ta gyaɗa mini kai.
Jin abin da na ce ya sa sai ta juya ta fice daga bedroom ɗin na bita da kallo tana fita na ƙara fashewa da kuka, ƴaƴa biyu gare ni su Allah ya ba ni, yanzu in ban ƙara haihuwa ba suka zo suka mutu fa?
Tuna haka kaɗai sai da ya sa na ji kamar jinina ya yi sama, domin ji na yi numfashina na barazanan barin jikina gabaɗaya tsabar tashin hankali da damuwa.
Daga ƙarshe suma sun gaji da zama a falo su kaɗai sun saba in ina gida tare muke yi salolli da azkar mu yi karatun Qur'ani sannan na duba littafansu na makaranta muna yi muna hira, su kaɗai gare ni domin a wannan rayuwar ƴan'uwanka ma suna gudunka, Mijin ma ba lalle ya zama mai amana ba, su ko ƴaƴa ko akan bola uwa ke kwana ba su isa su sauya ma tuwo suna ba.
Ganin har an yi sallar isha'i takwas ta gota ban fito ba sai ga Jidda ta kwaso mini Baby sun shigo har Bedroom ɗina, ina cikin bargo na dunkule suka hawo har saman gadon suna kiran sunana.
'"Sannu Umma? Kan ki ke ciwo?
Haka Jidda ta tambaya, sai na yi ƙoƙarin goge idanuwana na miƙe zaune ina faɗin"Na ji sauƙi, kun yi sallar isha'i? Jidda ta ɗaga min kai kafin ta ce"Har karatun Qur'ani mun yi na ƙara ma Baby na ta karatun"
Kanta na shafa kafin na ce"Allah ya yi miki albarka Jiddan Umma."
Baby ta ɓata rai tana faɗin"Ban da ni Umma? Sai itama na shafa kanta ina saka mata albarka, kantowa ta yi saman jikina, ni kuma sai na koma ina wasa da jelan kitsonta na 2step da akayi mata, da ya ke suna da tsawon gashi ni suka ɗauko duk da shima babansu da dangin shi gabaɗaya suna da cikar suma.
Jidda ta yi ta yi ta zubo mini abinci na ce ta bari in na tashi zan sha Tea. Wanka na ke so na yi ga kaya can da na ɓata ma ban wanke ba, Baby har ta yi barci a jikina sai na ce Jidda ta ɗauketa zan ta shi.
Tashin ta ta yi, domin ba ta iya ɗaukanta Baby akwai jiki a cure, bayan ta tashi ta kama hannunta zuwa ɗakinsu na ce ta tabbatar ta kaita tiolet ta yi fitsari, na ɗan ƙara samun natsuwa ganin jinin ya ɗan tsagaita amman bai ɗauke gabaɗaya ba. Wanka na yi, na fito kenan na ji buɗe get na san Yallaɓai ne.
Ba ni da wani ƙarsashi sai kawai na zura wata rigar barcina doguwa, kaina buzu buzu ko ta kan shi ban bi ba, haka na koma gefen gado na zauna ina tunanin abin yi? Sai na ji kamar ina rasa tunanina na wani lokaci saboda halin damuwar da na ke ciki.
Ina jin sa sai da ya shiga ɗakin yara ya gansu sannan ya ƙariso Bedroom ɗin mu, yanayin yadda ya ganni kamar ƙanwar mahaukaciya shi ya san ya yau ɗin fa ba lafiya.
Hannuwansa ya buɗe mini alamun in ta so amman na kasa tashi, kallonsa kawai na ke yi hawaye suna cika mini kwarmin idanuwana. Shi ko ganin naƙi tasowa ya sa ya tako gabana, hannunsa akwai brief case ɗinsa sai wasu takardu, sai da ya sauke su saman madubi sannan ya ƙariso gabana ya durkusa lokaci ɗaya ya na rike mini duka hannuwana.
Ina jin ya riƙe ni sai kawai hawayen da na ke ta riƙewa suka kwaranyomin a saman fuskata, marairaice fuska ya yi kafin ya ce"Haba Sadiya ta, ba na ce ki bar damuwa ba? Kin kuma ce min kin bari? To me ya sa kike kuka kuma? Kalle ki fa Yallaɓanki ya dawo amman kin kasa taran shi da irin mirmishinki da kika san ya na kwantar masa da hankali, sai ki tare shi da kuka? Alhalin kin san kukan ki dai dai yake da yi ma kwanciyar hankalinsa barazana?
Ya ƙarishe faɗa, ya na kallona ni kuma sai na ji raunina ya bayyaana share mini hawaye ya ke yi da tattausan hannayensa duka biyu, faɗi ya ke yi" Ki daina kuka, ki bar wannan kukan? Kina so na shiga damuwa ne?ko so kike yi nima na fara kukan? Uhm Sadiya ta?
Sai kawai na riƙe masa hannunwansa da duka hannayena guda biyu, ban san ma lokacin da na barƙe da kuka ba, kuka wiwi kamar Jidda. Daman a jikin Yusuf kawai na ke samun daman wannan kukan, ba ni da uwa da ace Mama na raye ita zan yi ma wannan kukan. Gwaggo kuma ba na zuwa gaya mata matsalolina ita da Alhajinmu ba na so su shiga damuwa, sannan duka ƴan'uwana ba ni da sakewa da kowa sai Rahila, itama ta na da ji da na ta auran ba zan ta zuwa ina damunta, a ɗakin mu Yaya Auwal ne kuma shi Namiji ne sannan ya yi nesa da mu, Amina kuma ƙanwata ce itama kaduna ta ke aure, Datti kuma yana makaranta sai in ya zo gida hutu.
Dole dai kafaɗan Yusuf ne abin jingina na in yi kukana shi kuma ya lalace wajen lallashina, har a raina ina jin ƙila watarana wannan kafaɗan da na ke kwanciya na yi kuka za ta iya yi min nesa da wat rana sai dai na yi kuka na a saman gwiwoyoyina ba zan iya samunsa a duk lokacin da na ke bukata ba, tunda ƙila ba lalle ya ƙare rayuwarsa da ni kaɗai ƴaƴa biyu kacal ba, ahalin ya na da yadda zai yi ya samu abin da ya ke so na mallakan yara da yawa.
Lallashina yake yi da duka iya kalamansa bakinsa, amman sai da na ji zuciyata ta rage kunci sannan na daina kuka na koma shassheka, rumgumeni ya tashi ya yi bayan ya zauna gefen gado, yana ɗan tapping ɗin bayana alamun lallashi.
Ɗagowa na yi ina kallonsa fuskata jage jage da hawaye, shi kuma sai ya saka haɓan hannun rigansa zai share mini hawaye da sauri na kauda kaina na saka hannu ina sharewa da kaina cikin muryan damuwa ya ce"Me ya sa kika hanani na share miki hawaye Sadiya?
Cikin dakushewar murya na ce" Saboda kar ka ɓata kayan ka."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Kaya? Me nene kaya? Ban so kar ki sake hana ni share miki hawaye, domin ina fatan har ƙarshen rayuwata na zame majinginar in za ki yi kuka, sannan na zama mai share miki hawayen ki, ba na so na ji kamar na gaza miki ne Sadiyata."
Kai na girgiza kafin na ce"Ko ɗaya. Ba ka gaza mini ba Yallaɓai. Sai ma ni ce na gaza maka, na kasa ba ka farincikin da ka ke so, na kasa sake Haihuwa Yusuf, wallahi ina so na ƙara haihuwa ko ɗaya ne? Ko ɗaya ne ko? Ai kana so ko?
Haka na ke faɗa da sauri da sauri sai ya lura kamar ma na fara fita hayyacina sai ya yi ƙokarin rike mini hannu lokaci ɗaya yana faɗin"Shii. Kin manta muna da ƴaƴa? Ƴaƴan mu biyu Sadiya muna da Jidda muna da Baby? Me ya sa za ki yi ta damuwa bayan muma muna da ƴaƴa ba wai ba ki taɓa haihuwa ba ne"
"Ba za mu rayu da ƴaƴa biyu ba Yusuf, in suka zo suka mutu fa?
Haka na faɗa, ina jin har hannuna da ke cikin na Yusuf na rawa. Kallona kawai ya tsaya yana yi cikin mamaki kafin ma ya samu zarafin mgana na cigaba da faɗin.
"Ina ta tunanin me ya sa lokacin da na kawo shawaran zan yi planning saboda makaranta ba ka hana ni ba? Me ya sa ka biye mini? Me ya sa ka amince, da ka hana ni da ka bar ni, na yi ta haihuwa ai wahala ba ta kisa, ba zan mutu ba sai lokacina ya yi, me ya sa ba ka hana ni ba?
Haka na faɗa da ƙarfi sannan lokaci ɗaya ina jijjiga hannayensa, Kasa motsi ya yi sai kallona ya ke yi, yasan na fita hayyacina kuma ko ya yi magana ba zan saurare shi ba, sai kawai ya kamani ya yi mini wata irin rumguma da ƙarfi sai da na ji numfashina ya na barazana ɗaukewa dole na yi shuru amman fa na fashe masa da kuka.
Ƙamƙam ya riƙeni yana faɗin"Ba na so, me ya sa kike irin wannan tunanin? Ba za su mutu ba in sha Allahu ba yanzu ba."
"Yara suna mutuwa fa Yusuf? Ko Baby in ta mutu fa?
"Na ce ki bar cewa haka ko?
Ya yi min tsawa bayan ya ɗago ni yana mai ƙureni da ido.
Sai na sadda kaina kasa ina kuka.
"Kin yi nadama ne? Ko ba ki yi planining ba. In abin da Allah ya kaddaromana kenan Sadiya ba fa mu isa mu tsallake wannan kaddaran ba, kuma planning ba laifi ba ne domin kin nemi tazara saboda karatun ki, ko malamai ai suna mgana kan a yi tazaran haihuwa, me ya sa yanzu kike nadama? Ko an ce kina da wata matsala ne? Kin je asibitin nan an yi duk gwaje gwajen an tabbatar da lafiya lau mahaifanki. Side effect ne, kawai ya taɓa ki, kuma kusan daman komai na rayuwan yana da nashi amfanin da rashin shi, me ya sa za ki zauna ki rasa hankalinki? Har kina yi ma ƴaƴan mu fatan mutuwa?
Kafaɗata ya rike duka biyu, sannan ya kira sunana har sau biyu na amsa sannan na ɗago ina kallonshi.
"Kar na kara jin mganar mutuwa a bakin ki kin ji ko?
Sai na gyaɗa masa kai kawai ba tare da na yi magana ba, shi kuma sai ya koma ya na sharemin hawaye yana faɗin"In Allah ya so za ki kara haihuwa, in bai so ba duk som mu da haka ba za ki ƙara ba. Ubangiji ne ke iya tsara ma bawa rayuwarsa tun daga ranar haihuwarsa har ranar mutuwansa."
Jikina ya yi sanyi, shi na ke kallo kafin na ce" Kai fa? Haka za ka zauna. Na san kana son yara a kallah dai ko ba da yawa ba kamar biyar haka."
Bai yi min mgana ba sai da ya gama gogemin fuska tas da haɓan rigan shi, ya na kauce ma mganar ne, ya mikar da ni yana faɗin"Mu je ki yi wanka"
Kai tsaye na ce"Na yi wanka fa" muryata a shake, shima kai tsayen ya ce"Ba irin wannan ba, irin wankan da kika saba mini"
Ban san lokacin da na yi mirmishi ba, har cikin tiolet ya kaini, ya duka ya sumbaci bakina sannan ya fice ya barni, na ɗan samu natsuwa shi ya sa na ƙara tuɓewa na sake yin wanka lokacin da na fito ya na ɗakin shi ya taya ni na shafa mai na shirya, kwalliya ya ce yana so na yi masa ina shagwaɓewa na ce"Wani kwalliya kuma da daren nan Yallaɓai na?
Hararana ya yi kafin ya ce"Bashi za ki biya, ki yi mini abin da kika saba na more kallon ki kafin na kwanta,."
Ganin na yi shuru ya sa ya marairaice ya na faɗin"Ko ba ki so na samu natsuwa daga kallon ki ne?
Ina jin haka na yi saurin girgiza kaina. Kwalliyar na yi masa na saka riga da wando. Wandon mai ɗamewa ne, rigar ma haka shi ya tayani na gyara gashina na saka rebon zan saka hula ya ce na bar mai kayansa ahaka, to kayansa ne shi ya sa bar masa kayansa.
Na faɗa masa ban yi girki ba, taliya ne Jidda ta dafa, sai ya ce kar na damu ya siyo mana kaza. Falon farko muka fita ya ɗauko mana kazan muka baje a saman cafet muna ci, ya na bani a baki ina bashi muna hira haka sama sama sannan jefi jefi muna kallo.
Na leƙa su Jidda har sun yi barci daman guda biyu ce muka ci ɗaya muka saka musu ɗaya a fridge, bayan mun gama ci muka ɗora da sanyayar maltina Yusuf ya kwashe komai da muka gama ya gyara wajen, ya kawo mini tissue ya goge mini hannuna da bakina shima ya goge na shi, kujeran mai zaman mutum ɗaya muka zauna ni na kwanta saman jikinsa, shi kuma ya saka hannu ya rumgumeni yana wasa da gashin kaina, muna hira sannan muna kallo a tashar Mb2 ne ana wani film ɗin Horror ina ta cewa ina jin tsoro amman Yusuf ya ƙi sauyawa wai ba wani tsoro.
Mu ne har 12 na dare sai da film ɗin ya ƙare, sannan muka kashe komai muka koma ɗaki. Yusuf ya yi wanka sannan muka kwanta muna rumgume da juna, dukkanmu mun yi shuru muna jin bugun zuciyan juna.
"Yallaɓai na"
"Uhmm"
Sai na gyara kwanciya a saman ƙirjinsa ina faɗin" Ka yi hakuri, na gaza ba ka dukkan farinciki ta bangaren ƴa'ƴa. Na san kana son yara domin tun kafin mu yi aure in ka zancen wajena sai ka yi ta faɗin Sadiya ko ƴaya goma kika haifa min ba za su isheni ba, na daɗe da sanin kai mai so ka ga gidanka cike da yara ne, bayan haka kuma ƴan'uwanka ma son ka haihu da yawa Nene ma haka, uwa uba ƙannenka da suka yi aure bayanmu duk sun fika yawan ƴaƴa na san ko yaya ne kana jin ba daɗi a ƙasan ranka, ka yi hakuri ba ni da wata mafitar ne."
Na faɗa muryata na yin ƙasa,. Kamar ba zai yi magana ba na ma ɗauka yana barci ne. Sai da na ɗago ta cikin duhun ɗakin akwai ɗan hasken dake shigowa ta window, na ganshi idanuwansa a lumshe, na fahimci ba barci ya ke yi ba da ya ƙara rumgumeni ƙam a samam kirjinsa. Ajiyar zuciya ya saki kafin ya ce" Ni ba ki taɓa gazamin ba,kin ba ni dukkan wani farincikin da ko wani namiji ya ke bukata. Kin zame min matar rufin asiri, da me kika rage ni? Ba ki rageni da komai ba mganar ƴaƴa na faɗa miki in biyun Allah ya bar mana mun gode in ya ƙara mana mun gode, mganar ƴan uwana kuma wannan na su ra'ayin ne, ba wanda ba ya son ya tara kyakyawan zuru'a Sadiya. Ita kuma Nene ki daina maganarta jikokinta nawa? Me ya sa sai nawa ne za ta damu domin ban haifa da yawa ba?
Idanuwana suka kawo kwallah kafin na ce"Saboda kai ne Tafida. Kowa ya shaida kai ɗan gatan Nene, ne ta sha yi maka addu'an ka gaji mahaifinka wajen tara zuru'a mai yawa. Sannan ka manta burin ka na sake haihuwata domin na yi ma Alhajinku takwara?
Numfashi ya saki ya fesar kafin ya ce"Ban manta ba. In kin sake haihuwan zan yi ma Allah godiya in ma ba ki sake ba duka godiyar zan yi masa, ai bar ni haka ba ya bani biyu, ina waɗanda suke nema har yau ko ɗaya ba su samu ba? Ko ban yi ma Alhajinmu takwara ba, ƴaƴan sa nawa ne suka yi masa? Masu sunan Alhaji ai ba su da adadi ballatana in sha Allahu za ki sake haihuwa bayan Alhajinn Gwammaja har Alhajinmu za mu yi ma takwara in sha Allahu."
Kansa na ɗago na sumbata kafin na ce" Allah ya amsa" ya amsa min da Amin, ƙara shiga jikin juna muka yi, ya na so ya yi barci ni kuma ba na jin barci.
"Sadiya ta"
"Yallaɓai na."
"Barci na ke ji,"
Haka ya faɗa mini a saitin kunnena, sai na yi mirmishi kafin na ce"Saura magana ɗaya ta rage, in muka gama sai mu yi barcin ko?
"Umh"
Kawai ya ce ba tare da ya yi magana ba, ni kuma sai na yi shuru saboda ina ƙoƙarin iya faɗin abun da ke cikin raina.
"Yallaɓai."
"Ina jin ki"
Haka ya faɗa ya na tusa hannunsa a cikin rigata, wani sanyi na ji a cikin raina nima sai na kai hannuna saman kirjinsa ina shafawa kafin na ce.
"Yallaɓai na, kana son ka ƙara aure ko?
Ya ji ni, amman bai yi mgana ba ina wasa da gashin ƙirjinsa cikin wani salo, mirginawa ya yi kaina ya kama bakina ya na kissing, nima sai na tallafi kanshi, daga nan mu ɗan birkita juna da salon wassani kafin mu koma muna maida nunfashi, tunda mai jan mota ya yi bakare a ƙofar boda ba halin shiga kuma ba halin fita.
"Ƙarin aure hukunci ne na ubangiji. In Allah ya kaddaromin zan iya ƙarawa, amman ni a yanzu ba ni da ra'ayi domin duk abinda namijin kwarai ke nema a wajen mace ina samu a wajen ki, me zan nema kuma a wajen wata macen?
Raɗa na yi masa a kunne sai ya zille ya na dariya kafin ya mirgina ni na dawo saman shi ya ɗaga ni na zauna a saman cikinsa yana kallona ya ce" Ina samun natsuwa a tare da ke, har ina jin ba Namijin da ya kai ni morewa ma aure. Ko wata na aura an ya za ta kai ki a wajena?
Ina dariya na ce"Oho. Amman dai ni nasan halin maza ne, kun ce ba kwa ta cin shinkafa ba sirki ba, gwara ku sirka da taliya ko macaroni"
Dariya ya fashe dashi ina taya shi.
"To ni ke ce komai na, Taliyar macaronin tuwon duka kowani nau'in"
Kafaɗa na noƙe ina faɗin"Ba na son yaudara da daɗin baki"
"Sadiya ni zan yaudare ki? Yusuf ɗin ki ne fa?
Sukuwa na yi a kansa ina faɗin"Daɗin bakin maza ba, shi ne yaudaran"
Nishi ya yi kafin ya ce"Ba dadin baki fa a tsakanin Yusuf da Sadiyarsa. Allah da gaske na ke yi ke ce duka kayan daɗi na."
Ya faɗa ya na saka duka hannuwansa cikin rigata ta ƙasa, ya fara matsa min ciki da karfi, ina bige hannunsa ina cewa ya bari yaƙi, sai da na mirgina ya bina ya hau kaina yana ta matse mini ciki ina ta dariya har da hawaye sai da ya ga zan shiɗe sannan ya ɗagani yana faɗin"Ba daɗin baki Yusuf ke yi ba ko?
Ina dariya na ce"Yallaɓaina ba ya daɗin baki."
Sai ya koma gefe ya na faɗin"Good. Girl."
Kafa na saka na shure sa ina faɗin" Sai na rama"
Yana dariyan keta ya ce"To taho mana, zo ki rama."
Ya faɗa yana ƙokarin kamoni na matsa baya ina dariya na san halinshi, yanzu sai ya yi min mugunta, bi na ya yi yana faɗin taho ki rama mana Allah ba komai,
Na haura ƙarshen gado ina faɗin" Ina ga na yafe maka." Dariya saka irin ta nishaɗin nan, sai da na tabbatar da ya ce ba zai min komai ba sannan na dawo jikinsa muka kwanta muna maida numfashi.
"Ka matse min ciki, in ka kashemin ƙwayayon haihuwata fa?
Ya na ƙokarin mikewa ya ce" Mu ga ni? Ni fa na san in da na matse."
Hannunsa na bige ina faɗin" Wato su ƙarishe mutuwa ka samu hujjar ƙara aure ko? Na faɗa ina yar dariya shi kuma ya daina dariyan ya koma ya kwanta kawai na fahimci baya son maganar yasa na koma na lafe saman kirjinsa ina faɗin.
"Ka sa ni ko aure ka ƙara ba zan taɓa juya maka baya ba. Saboda duk abin da ka kake so nima ina so, sannan ina son ka tara zuru'a kaima, amman abu ɗaya na ke so, don Allah kar ka yi hakuri ka ji a ranka saboda ban cike maka wani gurbi ba, mun kusa cika adadin shekaru sha biyar da auran mu, har ga Allah ban sa a raina zamu dauwama mu kaɗai ba, amman ina fatan lokacin da za ka yi auran ka wadatamu ka wadata kanka kada ka ɗauko aure ba tare da ka shirya ma hakan ba ka ji ko Yallabai na?
"Na ji."
Haka kawai ya ce, na san halin kayana sai na fara shafa fuskarsa zuwa gemunsa ina faɗin" Ka yi fushi da ni ne?
Hannuna ya riƙe kafin ya ce"Ko ɗaya. Na ji maganarki amman ina so ki sani ko mata nawa zan aura a bayanki ne, kin zama Turken gidana ke ce tsanin duk matakin da na taka arayuwata. Ki bar ni da maganar auren nan."
"Mu kwanta mu yi barci"
Haka ya faɗa ganin ina shirin yin magana, dare ya yi domin ɗaya ma ta gota. Lafewa na yi saman kirjinsa shima haka tun muna jin bugun zuciyar juna, har barci ya kwashe mu gabaɗaya.
Sanin halin da na ke ciki ya sa Yusuf bai ma tashe ni ba, ko da na tashi har su Jidda sun tafi makaranta. Yusuf ya yi musu abin karyawa da na lunch box, sannan muma ya dafa mana Tea ya soya mana ƙwai, ina ta shi ya ta sani tiolet ya ce na yi wanka ko da na fito ya zubomin tea a mug ya ce na sha sannan shima ya shiga wanka, ban yi mamakin Yusuf ba sanin halin shi, ba shi da ƙiyuwar aiki, ya kuma iya komai yanzu ne ma aiki ya yi masa yawa amman zamanin farko farkon auran mu ai na mori Yusuf sosai. Shi ya yi zaman Bording School, shi ya sa aiki ba ya gagaran shi na tuna haihuwan Jidda na farko a gida na haihu kafin Gwaggo ta zo har ya gama wanke duka kayan jinin nan, haka zan tafi makaranta ban gyara gida ba sai dai na dawo na ga ya gyara gidan ya yi mana abinci, lokacin nan har makaranta ya ke rakani ya ɗaukar min Jidda, kafin ya samu aikin nan na shi ya kankama mun gina wata rayuwa ne mai wuyar mantawa.
Har ya bar gidan nan bai barni na ɗauki ko kofi ba. Sai da na raka shi ya tafi sannan na je na wanke kayana na jiya da na ɓata na fita haraba na shanya, na ɗaga waya na kira wayar Saude na ce yau ta zo da wuri, kasala na ke ji na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 31