Marigayi Alhaji Inuwa kamar shi sun yi ilimi sun kuma tsaya da kafafun su. Ba matan ba sannan ba mazan ba wasu sai sun gama karatun suke auren wasu kuma suna cikin yi suke auren sai su ƙarisa a gidan mazajen su. Yusuf dai ya yi karatunsa na fimari kaf a garin Rano ne a gidan Alhaji Yusuf Tafida tare da Tariq da kuma Abba. Sannan bayan sun gama ya nema musu makarantar kwana a kaduna mai suna. Federal Sceince and tecnical collage (FSTC) Kafacan Kaduna. Su uku tare suka yi makaranta tun daga matakin fimari har matakin gama babban sakandiri daga nan sai Yusuf ya tafi Abu zaria. Tariq ya tafi jami'ar Ibadan shi kuma Abba ya tsaya anan BUK ya yi karatun shi.
Sun gama degree farko kuma kowanne ya zaɓi in da ya ke so ya cigaba da karatunsa. Shi Tariq Jami'ar lagos ya koma ya yi masters ɗinsa shi kuma Yusuf ya dawo kano ya yin da Abba bai cigaba ba ya koma Rano ya fara kasuwanci da noma tunda abin da ya karanta kenan. Yawancin zaman Yusuf ba a kano ba ne ya fi zaman Rano shi ya sa akwai sabo na musamman tsakaninsa da yaran gidan Marigayi Tafida, kuma a gidan ba a kiran sunan shi sai dai Baaba. Ita kuma Hajiyar Tafida ta ce Tafida mutun ɗaya ce ke kiran shi da Daddy Saudatu(Gimbiya) ƙanwar Tariq ce. Kuma ta ci sunan gimbiya ce matar sarkin Rano a wancan lokacin.
Mganar aurena da Yusuf ta yi barazana domin yan'uwansa sun ce ba zai yi ba ya yi gaggawa sannan bai gama karatu ba kuma ba shi da sana'a mai ƙarfi sai buge buge. Kuma shi Yusuf Mutun ne da ba ya son zama a ƙarkashin wani ya fi son ya zauna in his on. Ban taɓa ganin mutun mai tsari irin Yusuf ba ya karanta abin da ya shafi zane zane amman kuma ya na da sani kan abin da ya shafi gini da sauran su. Tun kafin mu yi aure ya sha faɗa mini so ya ke yi ya buɗe kamfanin shi na kan shi ba ya ƙaunar aiki a ƙarkashin wani ya fi so ya cika burinsa na yadda zai gina kansa domin ƙara ma matasa karfin gwiwan kan dogaro da kansu. Bai taɓa faɗa mini yan'uwansa sun ƙi auran mu da farko ba sai daga baya saboda lokacin da suka ƙi sai ya kai su ƙara wajen kawun nan na su sna bangaren babansu da ke Rano su suka shige masa gaba akan mganar auran mu. Daga karshe da suka ga ya dage sai suka hakura suka bar shi ya yi. An saka rana ba lokaci mai tsawo ba sai aka sanya shi lokaci ɗaya da na su Rahila. Abu kamar wasa kamar mafarki sai ga shi abu ya tabbata kowa ya ji zan yi aure sai ya yi mamaki kamar irin su Ma'u da ba haka ta so ba sannan da ta ga Yusuf sai ta fahimci na tsere mata ko ba ta fada mini ba a fuskarta na ga hassada da kishina. Duk da rasuwar Mama ta saka an ƙara wata ɗaya kafin auran mu mutuwar da ta gigitamu har Alhajinmu da har gobe ya kasa manta rashin Mama. Da Gwaggo da ta daɗe cikin jimami shi ya sa a sha'anin bikin ba a yi wani taro sosai ba. Amma dai kayan ɗaki komai iri ɗaya ni da Rahila babu in da aka bambamta mu ni a anguwar Dakata muka fara zama ita kuma Rahila nan cikin anguwan Ɗorayi ne tana kusa da gida.
A tsarina ban taɓa tsara ma kaina fara rayuwa a gidan Haya ba. Amman sai gashi nan ne muka fara shimfiɗa rayuwarmu ni da Yusuf. Ya san ina karatu kuma ya yi alƙwarin barina har na gama karatuna. Mun sha amarcin mu sosai na ke jin daɗin zama da Yusuf in zan je makaranta wani lokacin har rakani yake yi in bai da wajen zuwa in shima yana da shiga makaranta sai mu jira juna mu koma tare. Yana samun kira haka in ana son zane sannan tun lokacin yana karambanin karɓan kwangila gini sai ya nemo ma'ikata da injiniya.
In na ce a zamana da Yusuf bai gatanta ni ba na yi ƙarya. Ya yi mini hidima da jikinsa da Aljuhunsa. Nene ta karɓe ni a matsayin surukarta. Amman ban da yayyen Yusuf da suke uwa ɗaya barin ma Anty Bahijjan sai bayan auran na ke sanin sun so hana auran mu a cewar su ya bari zuwa gaba sai ya auri Gimbiya. Sai daga baya na fahimci Gimbiya na son Yusuf soyayyar da ba ta iya ɓoye shi. Shi kuma ba ta gan shi a ƙanwa ma ya ɗauke ta. Suna son haɗa auren ne saboda amincin iyayensu amman kuma hakan bai yuyu ba. Farkon auran na yi musu biyayya kamar zan bauta musu saboda dai ina auran ɗan'uwansu. Kuskurena na farko shi ne na yi tunanin yin tsarin iyali saboda karatuna sai dai cikin Jidda shi ya zo ya shammace ni. Watanni tara da kwana huɗu da aurenmu na haifi Jidda da ta ci sunan Nene Hauwa'u.
lokacin ina aji biyu ne zan shiga uku na sha matukar wahala ga ciki ga karatu ga aure shi ya sa ina yaye ta na nemi shawaran Yusuf akan ina son in yi tsarin iyali shi kuma sai ya ba ni goyon baya muka je wani asibitin kuɗi na fara karɓan allura duk bayan 6 months har na shekara biyar. Daga wannan alluran sai ta zame mini matsala. Na gama karatun kuma ina son na ƙara haihuwa amman shuru ko domin goron su Anty Bahijja tunda suna ganin na daɗe ban ƙara haihuwa ba bayan Jidda sun ta zargin ko planning na ke yi amman ban faɗa musu ba tunda kamar na tona asirin kaina ne.
A kuma lokacin muka shiga rayuwa na halin babu. Yusuf ba aiki yake yi ba. Sannan aikin da ya kan samu ya ragu sai jifa jifa. Duk wani abin da na ke dashi sai da ya kare na zo da ɗan kunnen gold wanda na siya da sadakina amman sai dai na siyar da shi. Da cewar Yusuf in ya samu anam gaba zai siya mini. Saboda haka ya sa na nemi aiki a makaranta kuɗi anan kusa damu na fara koyarwa saboda mu rufa kan mu asiri. Ba zan raina ba in Yusuf ya samu na samu to amman yanayin aikinsa kafin ya samu fa? Kuma na yi na yi ya nemi aiki shi yaƙi a dole sai ya tsaya da kafafunsa. Ta ina za ka iya samar da kamfani baka da kuɗi?
Zan iya cewa renon jidda ma tare muka yi tun lokacin ina makaranta tare muke zuwa ya rike mini Jidda har mu fito daga karatu ko ya kai ta gida wajen Nene. Da na fara Koyarwa shi na ke barin ma a gida kafin na dawo ya gama duka aikin gida har girki ma ya yi. Kuma albashina ba na iya cin komai dashi ɓukatunmu na ke yi mana dashi. Sai dai yan'uwan shi duk ba su ga haka ba a tunaninsu na tsaida haihuwa ne saboda Yusuf bai dashi ni ma na fara damuwa sai na fara yawon private hospital ana ce mini ba matsala zan ƙara haihuwa sai da Jidda ta kai shekara Takwas da wattani na ƙara haihuwan y'a mace sai ta ci sunan Anty Maimuna muna kiran ta Baby zuwa lokacin kuma Yusuf ya samu buɗi tunda har ya siya fili ya fara gini muma kuma Alhamdulillah muna cikin ni'imarsa.
Na sha wahala a haihuwan Baby C.S ma aka yi mini daga nan kuma sai na yi ta samu matsaloli na zubar jini da kasala sai juwwa. Daga baya sai na fara ramewa sannan haihuwa ta zo ta tsaya mini cak sai na fara jelen gen zuwa ganin likitoci a asibitocin kuɗi suna cin kuɗina suna gaya mini ba matsala in sha Allahu zan ƙara haihuwa. Tun ina ɓoye lamarin har ya fallasa ga dangin Yusuf tsarin iyali na yi ya ba ni matsala shi dai ya ce bashi ba ne ya faɗa sai na yi tunanin Ma'u tunda itama bayan ta gama karatu ta dawo gida ba daɗewa ta haɗu da Alhaji Mustapha cikin wattani kaɗan suka yi aure sai wayan gari na yi na ga Ma'u tsudum a cikin dangin mijina.
Saboda sanin Yusuf a harkan kwangilan gine gine sunan shi ya ɓace daga Yusuf zuwa Injiniyan da ya yi ma haye. Sannan da tsarina da shawarata mu ka samar da sunan kamfanin shi. HM TAFIDA AND SON LIMITED." Hauwa' u and Maimuna kenan da sunana ya so ya saka saboda gudun mgana na ce mu saka na ƴaƴanmu.
A can zariya road ya kama office ɗin kuma ya yi ma kamfanin sa rigister. Ya taimaka kwarai wajen samun kwangiloli masu tarin yawa. Kuma balle ya san jama'a connenction ɗin shi da mutane yasa har Gwamnati na bashi aikin kwangila. Akwai kwangilan da ya samu na gina wata makarantan koyon aikin Jinya ta ƙanin marigayi Alhaji Yusuf Tafida. Wanda shi ne yanzu a matsayin Tafidan rano yana aiki a ministry of education. Yusuf ya samu alheri sosai da shi ya ƙarisa mana gini sannan na bashi shawaran ya buɗe gidan buɗo saboda yanayin aikin shi. kuma ya yi na'am cikin lokaci kaɗan ya buɗe gidan Buɗo. Mun tare a sabon gida bayan ɗaukan shekaru sama da biyar ana ginin shi. Tsarin gidan da komai tsarina ne Yusuf kuma ya yi zanen sanan yan kwangilanshi suka gina gidan da jagorancin.
Tarewarmu a anguwan lodge road. Yusuf ya hana ni aiki ya ce na zauna a gida na huta. Duk da ina da ra'ayin fashion na shiga makarantar koyon kwalliya da gyaran kai. Har zanen shagon da Yusuf zai buɗe mini ya zana amman har yau bai tabbata ba. Amman hidimdimu ba za su bari hakan ya samu ba. Tun da muka koma wannan gidan ƴan'uwansa suke tunanin ina can na samu daula kuma ban haihuwa sai kwanciya ina cin daula sun manta irin gwagwarmayan da muka sha a baya komai Yusuf ya samu ko ya mallaka tare da ni aka mallake shi. Ko bayan tarewarmu a sabon gida sun so ya ƙara aure domin Gimbiya ba ta yi aure ba har Masters ta yi. Da ta ga dai Yallaɓai na Sadiya ne ita kaɗai sai ta hakura ta auri wani tsohon sanata matansa uku ita ce ta huɗu. Ta na can Abuja kuma har ta samu aiki da NGO.
A shekaru sama da goma sha huɗu da wattani da aurena da Yusuf na san me ake kira aure da gwagwamarya. Ba zan ce ba mu taba samun matsala ba mun sha samu tun da ni ina da saurin fushi ga baki shi kuma yana da sanyi wani lokacin amma in ya yi fushi ba shi da kyau. Mun sha samun matsala akan ƴan uwan shi mussaman Anty Bahijja da Anty Maimuna. Daga karshe shi sai ya bi bayan ƴan uwan shi ya bani rashin gaskiya. Nene dai ba na ce ta taɓa nuna mini kiyayya ba. Ban taɓa samun matsala da ita ba shi ya sa na ke yi mata biyayya iya iyawata. Sannan akan zamantakewa ma muna samun matsala amma sai mu shirya kan mu a tsakaninmu. Amman matsalan da muka sha samu da ya yi ƙamari shi ne akan Gimbiya. Ban samu salama ba sai da ta yi aure. Yusuf ya samu kusanci sosai da Gimbiya itama kuma ba ta sakin jiki da kowa sai shi in na nuna fushi ko kishi sai ya ce ina da matsala ina da zargi. Kuma sai ta zo gidan Nene shi kuma in ya je ya biye mata ya kai dare har kwalliyan da na yi sai ya lalace in na yi mgana sai ya ce bai san lokaci ya tafi ba suna can suna hira da Gimbiya. Ban samu salama ba sai da ta yi aure sannan na ji hankalina ya kwanta amman fa da in na ji zai je Rano yini na ke yi zullumi.
Da shekaru suka gangara haka sai nima na fahimci an gogi jigida. Na daina matsa ma kaina kan wasu abubuwan tun da na fahimci ni ba zan ga karshen su ba nima ba za su ga karshe na ba. Sannan irin wannan matsalolin ana samun su a kowani dangi. Sai dai na wata ta fi wata. Nene ce dole ne ita ne kawai ban daina yi ma biyayya ba amman sauran duk abin da na ga zan yi shi na ke yi. Na daina tsoron a ce na yi ko ban yi ba saboda shekaru sun gungura nima wuyana ya isa kaurin da na isa ga kaina. Shi ya sa na ke tafiyar da rayuwata da ga ni sai mijina sai ƴaƴa na. Sauran abin da ya fi ƙarfina na bar ma Allah ni yanzu abu ɗaya ne a gaba na. Ina son na ƙara haihuwa ko domin Yallaɓai mai son yara sosai.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWAR GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿️14*
Present.
Da safen tea muka sha gabaɗayan mu amman ban da Yallaɓai saboda kamar akwai gajiya a tare dashi. Tun bayan da ya dawo daga sallar asuba ya kwanta yana ta barci sai na ƙyale shi tun da na ga har wayarsa ma sai da ya kashe.
Da wuri Saude ta zo na saka Jidda ta fito da kayan na su. Daga kitchen ɗina akwai wata kofa dake fidda mutum ta can baya in da muke yin wanki ko shanya. Ko tara ruwan sama can na ce su je su yi wankin har da Baby da ta saka rigiman sai ta yi na ce a ƙyaleta ta yi.
"Umma ba fa wanki ta iya ba. Ɓata jikinta kawai za ta yi da ruwa."
Ina ɗakin na su ne a lokacin ina gyarawa saboda Saude ba za ta samu lokaci ba gwara ni na gyara gidan.
Kallon jidda na yi da ta shigo kawo min karan Baby.
"Bar ta yi. In ta jiƙa jikinta ai shike nan ta huta."
Haka na faɗa ina mirmishi saboda ni dai na san ina kamar ta ban so aiki ba amman tunda tana so ai ba zan hana ta ba. Wucewa Jidda ta yi amman ranta bai so ba sai na bi ta da kallo ina dariya.
Jidda akwai son aiki da karambani in da ta biyo ni da na shiga uku. Har yanzu da shekaru suka tura ba na son aiki barin ma girki, ko anan domin ya zame mini dole ne na ga ba mai yi mini. Saude daman in ta zo sai dai na saka ta yi ma yara. In da Allah ya so ni da Rahama Yallaɓaina bai da tsirfan cewa ga abin da zai ci duk abin da na kwaɓa na bashi yana maraba.
A baya kafin na samu Saude na wahala sai dai in Marwa ta zo mini hutu. Marwa babbar ɗiyar Yaya Aina ce. Lokacin da ta ke gida kafin ta samu makarantar koyin aikin jinya a garin tsafe na more ta saboda yarinyar tana matuƙar sona. Shi ya sa nima na ke son ta ina kuma kyautata mata. Ba ta zuwa gidan kowa hutu sai gidana in ta zo ba na komai sai dai na ci na kwanta Yallaɓai ya yi ta mini tsiyan daman haka na ke so na kwanta na yi ta laushi ni kuma na ce na ji ba komai.
Marwa ba ta da ƙiyuwa. In ta zo har wankin kayana da guguna tana yi min kayan su Jidda sai dai na fito na ga ta wanke ta shanya, budurwa ce mai kimanin shekaru 20 zuwa da ɗaya.
Duk da ni da uwarta ba sosai muke yi ba amman kuma Allah ya haɗa jinina da Marwa kuma ina daraja haka saboda yaran Yaya Murja ba sa zuwa gida na amman gidan Ma'u kam suna zuwa mata hutu. Har gwarama Firdausi ta wajen Yaya Balki ta kan zo wajena ban da su Anti. (Aina) sunan Yaya Aina a ka sanya mata sai ake kiran ta da Anti ita ce babba a ɗakin Yaya Murja ƙannenta huɗu duk maza ne. Ni bai dame ni ba domin kowa ya san halina ka yi da ni, ya ka ƙare ballantana ma ba ka yi da ni ma gabaɗaya.
Allah na tuba gari da yawa ai maye ba ya ci kansa ba shi ya sa ina yi ma Marwa abin alheri har ɗinkuna ina yi mata lokacin da ta samu makaranta tsafe siyayya na yi mata mai yawa kuma har da ni a masu rakata, sannan in dai ta zo gida hutu ko da ba za ta daɗe ba sai ta zo gidana ba ta daɗe ba ta yi mini sati ɗaya. Sau tari in zan siya abin mata na kwalliya uku na kan siya saboda Marwa. Ita tunda ta fara amfani da su bra da pad in dai na fita kasuwa siyayya ina siya mata na ijiye in ta zo hutu ko ba ta zo gidana ba ina aika mata dashi na ce Yaya Aina ta iijiye mata. Ban taɓa jin na damu da ta gode mini ba koma me na yi nima ai uwar Marwa na ke, kuma abin da ke tsakanina da mahaifiyarta ba zai taɓa shafanta ba.
Ko kafin in gama gyara gidan har sun gama wankin duk da bai da wani yawa daga uniforms ɗin su sai kayan barcin su. Ko daman ita Saude akwai ƙokari a shekaru iyakarta 17 ko ta gota da kaɗan ne. Na ɗan taya su shanya wajen sharce kayan. Bayan mun gama na ce Saude ta yi ma Baby tsifa ita ma Jidda ta kwance kan ta in wanke musu. Tun da ba su samu zuwa kitso ba sai in yi musu da kaina.
In kana da ƴa'ƴa mata koyon kitso ba zai zama wani abu mai wahala ba. Kuma daman ina da mai kitson tun ta can anguwan dakata da muka ta so bayan mun dawo nan tana zuwa gida ta yi mana ina biyanta ranar da kuma ba ta samu zuwa ba na kan kira Salisu ne ya zo ya ɗauki su Jidda ya kai su. wani lokacin in ta gama yi musu kitson yarta ke dawomin da su ranar da ba su samu zuwa ba na yi musu da kaina tun ban ƙware ba har ba ƙware kaɗan kaɗan.
Da na so sai la'asar zan je gida amman sai Amina ta sake kirana tana faɗa mini duk yau Yaya Hamza da Yaya Auwal za su koma sai na yi tunanin na tafi bayan azahar.
Yallaɓai bai tashi ba sai da na gaji har wajen sha ɗaya saura bayan na wanke tiolet na jiƙo hannuna na zo na tura masa a cikin ƙirjinsa da sauri ya buɗe ido sai a cikin idanuwana.
Ɗan ɓata rai ya yi irin na masu barci ni kuma sai na yi masa mirmishi.
"Yallaɓai a tashi haka nan. Kalli fa rana ta yi."
Na faɗa ina buɗe masa labulen window ɗin bedroom din. Ai sai ya kauda kai har ya na juyawa zai cigaba da kwanciya.
"Yallabai. Haba mana"
Na faɗa cikin yar shagwaɓa amman sai ƙara shigewa da kansa ya yi cikin bargo lokaci ɗaya cikin shaƙewar murya cike da barci ya ce.
"Sai azahar za ki tashe ni. Kin ji".
Ya faɗa ya wani ƙara sakin numfashi sai na saki baki kawai ina kallon shi na buɗe baki in yi mgana wayata dake kan dressing mirro ta ɗau kiɗa alamun kira sai na bar wajensa na isa wajen wayar.
"FaridaAisha."
Faridan Tariq ce. Haka na faɗa a fili kafin na juya ina kallon Yallaɓai lokaci ɗaya ina faɗin" Ka gani ko? Ƙila ma Tariq ke neman ka ka kama ka kashe waya kamar wanda ya kwana aikin gajiya."
Na san ya na jina amman bai yi motsi ba sai ni ce na taka zuwa gefen gado na zauna sannan na ɗaga kiran
"Maman biyu."
Daga can bangaren ta ce"Matar injiniya."
Da fara'a muka gaisa sai ta ke ga ya min sun shigo garin ita da Tariq suna Gwammaja suna son ƙarisowa gidanmu amma an kira wayar Yallaɓan nawa a kashe
Da sauri na ce"Yau hutu ya ke ji tun da ya dawo sallar asuba ya kashe wayarsa. Amman ai yanzu yana jin mu. Za ku samu ƙariwan kuwa?
"E. Amman a tsaye gaskiya saboda daga nan sai kaduna in sha Allahu "
Ina buɗe baki kamar ta na ganina na ce"Kai. Yau kuma! Ba ku bari zuwa gobe?
Tana yar dariya ta ce"Mai gayya ne ya ce yau za mu tafi"
Ina dariya na ce"kuma an gama mgana ba."
Sallama muka yi ta ce suna tafe. Muna gama wayar na juya ina kallon Yallaɓai amman bai tashi ba sai na miƙe ina faɗin" Yallaɓai ga su Tariq nan da iyalansa don Allah ka tashi ka yi wanka ka ƙarya kafin su kariso"
Dakyar da soɗin goshi na samu Yallaɓai ya tashi. Hararan shi na yi lokacin da na ga ya miƙe ya na miƙa.
"Gajiyar duk ta mene ne?
Sai da ya sargafo hannayensa ta saman wuyana muna kallon juna kafin ya ce" To kuma me ye na tambaya? Duk tsawon gajiyar da kika tara min ne na wannan watan na ke safkewa"
Ya ƙarishe yana ɗage mini gira. Ture hannun shi na yi daga kafaɗata na wuce ina faɗin" Ni ban ce ka tara min gajiya ba sai kai?
"To ke wani ƙokari kike yi ban da abin ki. Ni ke fa aikin."
Ya faɗa yana biyo bayana. Juyawa na yi muka haɗa ido kafin na yi masa wani kallo sai kawai ya fara dariya ni kuma sai na rausayar da kai lokaci ɗaya ina faɗin"
"Au! Haka ka ce ko?
Na nuna shi da yatsa kafin na cigaba da faɗin" Kai nan har wani ƙokari gare ka? Ba domin ni ba Yallaɓai uhmm."
Na faɗa ina cije baki. Yana dariya ya ce" Sadiya ki ji tsoron Allah."
Na juya zan fita ina faɗin" Za mu haɗu ne anjuma zamu ga mai ƙokari da mara ƙokari "
Ta baya ya rumgumeni yana faɗin" Just a good morning Hug."
Dakyar na tura shi Tiolet ya yi wanka kafin ya fito na soya masa yar sauran doyan da ta rage sannan na dafa masa ruwan tea mai haɗin kayan shayi. Ƙananun kaya ya saka tunda yau ya na gida a saman dining na zauna har sai da ya gama karyawa.
"Yallaɓai daga yau in dafa sauran shinkafar nan komai namu ya ƙare na kayan abinci."
Na faɗa ina kokarin tattara kayan da ya yi amfani da shi.
"Kafin Anjuma ɗin Allah zai kawo mafita. In sha Allahu."
"Allah ya sa."
Haka na amsa ina mai fita daga falon zuwa kitchen. Na leka su Saude na ga Baby tana hawaye ana mata tsifa daman ita akwai zafin kai ita dai Jidda har ta tsife nata.
Ina dariya na ce"Baby ki bari a yi tsifa an juma Babanki ya ce zai si yo miki ice cream kin ji?
Jin haka yasa ta washe baki. Sai na ce to a daina kuka in ta na son shan Ice cream. Fita na yi daga ɗakin na rufo musu kofa duk da na yi wanka ina bukatar na ƙara tun da tun safe ne.
Ina wanka su Farida suka iso domin na ji lokacin da Yallaɓai ya fita ya buɗe musu get Tariq ya shigo da motarsa shi ya sa a gurguje na gama wanka na fito na shirya na saka riga da sikat na wani material sai ga Yallaɓai ya shigo.
"Ke sun fa ce suna kan hanya ne."
"Ga ni nan zuwa Sorry."
Sai ya juya ya fita ya na faɗn" Ki taho musu da ruwa."
Sai na amsa da to. Mayafi na saka na rufe jikina sannan na biya ta kitchen na ɗauko musu ruwan gora a fridge da kofuna guda biyu bayan na saka a faranti.
Ina shiga falon Farida ta zo ta tarbeni. Falon ya yi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 31