Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
albarka Baby  ta ga yan biyu  sai wasa suke yi, ƙila babansu ya kira su su gaida baban na su, Jidda ba ta falon tabbacin ta koma ciki. "Sannun ku da zuwa." Na faɗa ina sauke ruwan saman center table ɗin da ke gaban Yallaɓai da Tariq. "Yauwa Sadiyar Yallaɓai. Ai ina nan ina masa tsiyan yau ko ba ya so mu ganki ne ya ɓoye ki? Ina dariya na zauna a kujeran kusa da Farida. "Haba dai ko ɗaya. Ina wanka ne lokacin da kuka shigo." Tariq ya jinjina kai kafin ya ce" yan hutu. Shi ma ai yanzu ya ke faɗa mini bai daɗe da tashi barci ba." "Shi ne ɗan hutu. Amman ni tun asuba ban koma ba." Farida na hararan mijinta ta ce" Shima ɗin ya na fin haka ma yana barci." Yallaɓai ya ce" to daman mana. Ni da suka raina ne suka saka mini ido shi da kawunsa Abba." Tariq na dariya ya ce" Tafida yarinyar  nan fa ta kirani. Ni dai kawun ka ya kusa kashe min aure. Madam fa ta ƙi yarda da rantsuwata shi ya sa na matsa mu zo ga ka ga Sadiya ƙila tafi yarda da mganar ku." Ina dariya Yallaɓai na dariya Farida ce ta haɗe rai kafin ta ce" To na sani ko sabuwar budurwa ya yi. Kira kan kira" Ina dariya ne amman ina auna wawancin Shema'u kina mace ki zama mai arha haka! Amman tuna wacece ita sai ban yi mamaki ba. "Maman biyu kar ki yarda. Tabbas ni ma kwanaki nan ban gane masa ba duk yadda aka yi ya fara neman aure a boye." Yallaɓai ya faɗa ya na haɗe ai sai Tariq ya kasa magana amman ya buɗe baki. "Uhm. To Allah ya ba shi sa'a." Farida ta faɗa kai tsaye ganin ta ɗan shaka sai na karɓi mganar ina faɗin" ƙyale Yallabai.' Nan na faɗa mata abin da ya faru a jiya duk da ta na nuna ba ta damu ni na san ta damu. "Ku kam ba abokan rufin asiri ba ne. Daga kai har tazurin kawun ka." Tariq ya faɗa yana ture hannun Yusuf dake saman kafaɗansa. Farida na dariya tana bamu labarin sun je gaida innayi sun haɗu da Uncle Abba shima dai tuburewa ya yi da bai san zencen ba shima Yusuf ga abin da ya ce. "Ai gaskiya ne. Mu ba mu san yadda aka haihu a ragaya  ba." Yallaɓai ya faɗa yana dariya sai Tariq ya miƙe ya na fadin" Madam lokacin mu ya ƙare anan fa." Itama sai ta miƙe tana rataya jakarta. Dukkanmu sai muka miƙe gabaɗaya ina faɗin daga zuwa sai tafiya. "To ai zuwan daman na a gaisa ne. Muna nan muna jiran ku ke da Yallaban na ki dai." "In sha Allahu." Na faɗa, muka bi su har waje ina yi ma yan biyu wasa. Kamar na sani na sako yar dubu ɗaya daga ɗaki shi na bama yaran ganin Farida ta zo ma da su Jidda bickit mai yawa. Sun shiga mota ina bangaren Farida ina yi mata sallama. Yallaɓai kuma suna bakin motar shi da Tariq suna mgana. "Man sai yaushe kenan? Tariq ya buɗe mota ya shiga lokaci ɗaya ya na faɗin" Ai ni ƙila sai ranar da tuzurin kawun ka ya samu matar aure in za mu je tambaya sai na shigo." Dariya suka yi har suna tafawa. Ni ko sai na ce" Kawun ku ke ma haka? To ai ba ku za ku yi masa tambaya ba." Tariq na dariyan mugunta ya ce" har auran ma za mu karɓa masa. Gaya min su wa za su je? To iyayen duk sun tsufa sun kare mu ɗin dai mune rufin asirin sa. Tafida ka bar gemun ka ya taru nima haka saboda na ga kamar kawun na ka ya fara maganar aure. Ko wani lokaci zai iya neman mu." Dariyan su suka sha suna tafawa nima ni da Farida muna ta ɗan dariya. "Sai mun yi waya. Allah ya kiyaye hanya." Yallaɓai ya faɗa bayan sun ƙara musabaha da Tariq. Shi ya bude musu get suka fita muna ɗaga musu hannu Allah ya sa baby ta samu biskit da ta yi rigiman sai ta je. Mun dawo cikin falo na kalli Yallabai ina faɗin" Duk abin da kuka faɗa akan Uncle Abba sai na faɗa masa." Yana ƴar dariya ya ce" To wai shi ne me? In ba ki da kati ki yi mini mgana sai na saka  miki." Kafaɗansa na kai ma duka ina dariya shima yana tayani. Mun zauna kan kujera ɗaya muna hira nan ne na ke gaya masa zan je Ɗorayi da wuri saboda yau su Yaya Auwal za su koma wajen aikin su. "Ok. Zan kai ki ne da kaina? "No. Ka bari dai sai ka je ka ɗauko ni" Sai ya gyaɗa mini kai sai na mike na wuce da farantin ruwan da na kawo ina faɗin. " Bari na je na wanke ma su jidda kan su." Da kai ya amsa min, sai na bar masa falon gabaɗaya. Kitchen na biya na sauke kayan hannuna sannan na shiga dakin su Jidda na ga sun gama tsifan har Saude ta ƙara share ɗaki. "Saude je ki wanke min sauran kofunan da suka ɓaci bari na wanke musu kai tare za mu tafi ɗorayi." "Umma ba kin ce za ki yi mana kitso ba? Jidda ta tambaya ne, sai na kalle ta kafin na ce" Sai na dawo ko zuwa dare ne." Mayafin jikina na cire na shiga tiolet ɗin akwai mayukan wanke kansu a ciki tunda daman rabi na kan raba na su da nawa. Kuma daman na iya ni nake yi ma kaina wankin kai ni da yayana a gida tunda ina da handrayer. Ruwa na tara mai ɗumi sannan na kira Baby na fara wanke mata sannan jidda a karshe, bayan na gama na fito na jona handrayer na busar musu da gashin gabaɗaya na shafa musu man kitso Jidda ita ta ƙara taje kanta ta daure da band ni kuma na yi ma Baby duk da ana yi ta na kuka har sai da Yallabai ya leƙo yana faɗin" To a kyaleta mana tun da an gama" Ina kallon shi kafin na ce" Za a dai gama amma ba a gama ba." Sai da na matse na samu na daure mata gashin. Yallaɓai ya ɗauke ta yana lallashinta lokaci ɗaya yana share mata hawaye, domin har da majina saboda kukan. "Ba ki son gashin ne? Yallaɓai ya faɗa duk cikin sigan lallashi sai ta gyaɗa masa kai, da sauri ya kalle ni kafin ya ce" Sadiya to a yi ma Baby aski ba ta son gashi balle ta rika kuka ko? Sai ya kalleta kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin" Ba na son aski." Yallaɓai sai ya kalleni kafin ya ce" To a bar mata gashin ta shi ke nan? Ya sake kallonta sai ta gyaɗa masa kai, rumgumeta ya yi, ni kuma me zan yi in ba dariya ba. Jidda ma ta na ta dariya Yallabai ya sunkunci Baby ya fice ya na faɗin" Tunda kun yi faɗa da Umma sai a ji da Abba ko? Bin bayan su na yi bayan na ce jidda ta ƙara share ɗakin saboda gashi. Ganin har an kusa azahar sai na bi Saude kitchen na ce bari kawai na dora farar shinkafa ina da sauran miya sai a ci da shi kafin mu tafi. Ni da na so fita tun bayan azahar sai gani har karfe uku sai da muka ci abinci na sauya kaya sannan na bar ma Yallaɓai amanar gidana da yarana ina ta ƙara jadadda masa. Sai kawau ya ce" Na ji mai gida. Kina ta mini kashedi megadi ne ni? Ina dariya na ce" Kamar haka! Tun da ko a ina aka je gida na Sadi baby ne." Na ƙarishe faɗa ina masa fari sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce" Hausawa suna cutar mu. Kai da guminka sai ka ji ana gidan Sadiya." "Ko gidan Maman jidda ba." Na faɗa ina yi masa dariya. "To ba a cewa na Baban jidda." Yadda ya yi mganar ne yasa har ina riƙe ciki wajen dariya. Mun rabu sai mangariba zai zo ya dauke ni bayan ya sake duba Alhaji. A daidaita muka samu zuwa Ɗorayi a kofar gida muka yi sallama da Saude bayan na ce  ta gaida mamanta. **** Ɗorayi. Ko da na je gida cike da ƴaƴa da jikoki. Domin kaf su Yaya Murja da yaransu suka zo tun da yau lahadi ba makaranta. Na iske har Ma'u tare da Zainab da su Alhaji ƙarami. Rahila ce kawai ba ta zo ba wai ba ta jin daɗi Mutanen Abuja dai sun riga sun tafi saboda nisa. Sai Yaya Hamza ne shi ma lokacin da na zo suna sallama ne za su ɗau hanya. Amina kuma za ta bi su su rage mata hanya daga zariya sai ta hau motar kaduna. Da ta ce sai gobe megidanta zai zo su koma tare to shima sai daga baya ya kirata ya ce suna da taro a wajen aiki da wahala ya samu zuwa. Ya dai yi ma Alhajinmu sannu ta waya. Tunda mijin Amina lacara ne a jami'ar kaduna. Kallon ta na yi lokacin da muka samu keɓewa a ɗakin Mama ina faɗin" Ke yanzu da sai ki tafi ba mu yi sallama ba? Ta na yar dariya ta ce" Ai na san kina hanya." Gyara zama na yi kafin na ce" Tun da Datti ya koma ya zo gidanki weekend kuwa? "A'a ya ce suna ta test ne. Zai zauna a cikin makaranta ya yi karatu. Ƙila sai sun gama zai taho.' Sai na jinjina kaina. Saboda Datti a farkon shigarsa jami'ar a gidan Amina ya fara zama amman sai aka samu matsala tun da akwai wani ƙanin mijinta a gidan da suka yi ta samun matsala da Datti har lamarin na neman shafan auren Amina tunda kowa kanshi ya sani. Sai Yallaɓai ya ba da shawaran gwara ya samu hostel ya koma can da zama, Allah ya sa ma akwai wani abokin shi ɗan nan kanon ne shi ya bashi waje a ɗakinsa suka yi sukwatin. Sai dai ya na ɗan zuwa wani lokacin ya yi ma Aminar weekend. "Mubarak ɗin ma ba ya nan yanzu. " Ita ta katse min tunani Mubarak sunan kanin mijin na ta. "Me ya faru? Har ya gama karatun? "Ban sani ba. Amma ina kyautata zaton kamar ya samu matsala ne duk da yayan na shi baya son faɗa mini. na san ya na Aji uku ne sai ya tafi can zuntu sama da wata biyu bai dawo ba gashi ana ta karatu sai na yi zargin wataƙila ya samu matsala ne a can makarantar." Sai na gyaɗa kai kafin na ce" Za ta iya yuyuwa. Ke dai tunda ba a faɗa miki ba. To ba ruwan ki." Tana dariya ta ce" Haba. Kamar ba ki sanni ba' Aiko na san Amina miskila ce kafi mahaukaci ban haushi, mun ɗan yi hira sama sama kafin Khaleesat ta leƙo ta na fadin ta fito su wuce ni na riƙe mata karamin akwatin ta muka fito suna falon Alhajinmu muma sai muka shiga can. "Na gode ƙwarai. Allah ya kai ku lafiya." Alhajinmu ya faɗa ya na ɗan kishigiɗe a saman kujera. Ya na riƙe da Amna Tasleem na kusa dashi. Khaleesat ta duka a kusa da Mijinta ta na faɗin" Allah ya ƙara lafiya Alhaji sai mun ƙara dawowa." "Allah ya sa. Na gode Allah ya yi muku albarka gabaɗaya." Muka taya su amsawa da Amin mune rakiyar har waje bakin mota gabaɗayanmu ba mu iyayen ba, sannan ba yaran ba. Sai da suka ɗaga muna ɗaga musu hannu suna ɗaga mana. Har sai da motar su ta ɓace ma ganin mu sannan muka koma cikin gida. Aneesa ɗiyar Anty Balki ce ta tambayi su Jidda na ce suna gida, a ɗakin Mama muka yada zango gabaɗayan mu tun da an ce a bar Alhaji ya huta ɗakin Gwaggo kuma ta ce Baaba na ciki tana barci kar a dame ta.   A kusa da Yaya Aina na zauna ina faɗin" Wai su Marwa ba su samu hutu ba ne? Kai tsaye ta ce mini" Sun kusa fara jarabawa. In ta dawo za su fara pratical a asibiti to babanta ya ce ta dawo gida ta yi kawai." "E. Gaskiya ai yafi. Ni ko wai ba ta da waya ne kwanaki ina ta kiranta a kashe " "Ta lalace tana saka layinta a wayar wata ƙawarta ce." Sai na kaɗa kai kafin na ce" Haba shi ya sa ba na samunta. Ta dawo sai a gyara in ba ta yi sai a siya wata amman ba ta zauna ba waya ba." Yaya Balki ta yi karaf ta ce" Tun da tana da uwa Sadiya ba" Sai na fashe da dariya kafin na ce" Kwarai kuma matar Injiniya ba." Yaya Aina na dariya amman ba ta yi mgana ba. Yaya Murja na zaune waje ɗaya da Ma'u sai da suka jiyo suna kallon mu, sai na yi kamar ban gansu ba muka cigaba da hiranmu da su Yaya Aina. Muna nan zaune sai ga Zaituna ta shigo fakam fakam kamar an jeho ta. Yaya Balki ce ta yi mata mgana da cewa" Daga ina? Ɗazu mijin ki ya fita ya na cewa ba ki zo ba? Ruwa ta ce a bata sai da Aneesa ta kawo mata pure water biyu ta shanyen su tana maida numfashi. "Wallahi na ɗan je barka ne. Wata yayarmu ce ta haihu." Daga ji ƙarya take yi saboda sai wani faman kifta ido ta ke yi kamar wacce ta yi ma sarki karya. "Za ki ci abinci ne? In ji Yaya Murja ai da sauri ta ce" Wallahi kamar kin san ina jin yunwa. Can anguwa uku ne ba mu samu abin hawa ba sai da muka ci uban tafiya duk abincin da na ci ya gama zazzagewa." Su Ma'u na dariyanta ni ko ban yi dariya ba saboda ban ga abin dariya ba. Kallonta na ke yi kamar wata mahaukaciya ta hana kanta zaman lafiya saboda shegen shige shigenta ta kuma hana ɗan uwan mu ya huta. Firdausi a ka kira ta zubo mata jallop ɗin shinkafa da wake ta zauna ta na ci hannu baka hannu ƙwarya da Yaya Aina ta ce ta ci a hankali sai ta fake da cikin goyo tunda a lokacin ta na da goyon mai sunan Yaya Hamza. Ba ta lura da ni ba sai da ta ci ta koshi sannan ta ganni. "Sadiya daman kin zo? Yanayin maganarta sai ya yi kama da ta renin wayau. Amman ta juya ta na yi ma Ma'u magana. Sai na ji ya kamata na rama na nuna mata matsayinta, sai kawai na kalleta kafin na ce" To daman ina za ki ganni kin shigo kamar an koro ki" Na faɗa ina kallonta. A raina ina faɗin Yaya Abubakar ya haɗu da jarabawa na auran wannan matar, iyayenta talakawa ne ba su da komai Yaya Abubakar ne ke tallafe da su, yayanta namiji sai shaye shaye ƙannenta sai bin yan iskan anguwa amman ba ta duba haka ba ita ce yau cin bashi ita ce kafa adashe ta cinye ta sha shiga rigima Yaya Abubakar na fidda ta ina tsoron wata rana kar ta ɗauko abin da zai gagare shi ta saka a ɗaure shi. "E na shigo ban ko gani na shawo tafiya" Kai tsaye ina kallonta na ce" Wata tafiya? Ko dai yunwa domin daga ganin ki yunwar ce ke ɗawainiya dake daman." Yaya Balki na yar dariya ta  ce" Da alama kam." Ita kuma sai ta wayance da cewa" Ban tsaya a gida na yi abinci ba ne, kuma can ɗin na kaɗan na ci kuma ga tafiya cikina duk sai ya zazzage" "Ke kam Zaituna me zai hana ki tsayawa a gida ki yi abinci? Shi ya sa Yaya Abubakar da ya shigo ɗazu ya ce a zuba masa abinci ashe da yunwa kike barin shi." Yaya Balki ta faɗa tana kallon ta kafin ta samu zarafin mgana Yaya Aina ta karɓe da cewa" To ta ina ma mace na da miji da ƴaya  za ta fita ba ta yi girki ba? Ai ko fitar sassafe ce ka yi dai ko fara ba mai ne kafin ka fita." Ina gyara zama na ce" Ta saba ne. Ita fa Zaituna ba ta son komai ba sai shigen yawo da shige shige. Ko mu nan da kika ganmu sai mun yi abinci muke fitowa daga gidajenmu ballatana ke." Na faɗa ina kallonta sai tafara kame kamen wai ita ina ta ke zuwa karaf ko Yaya Murja ta ce" A a Zaituna. Kina da shigen yawo kullum ba ki iya zaman gidan ki. Na rasa gidan wa kike zuwa da ya fi gidan mijin ki? Har ta na rantsuwan wai ita ba in da ta ke zuwa ko da yaushe tana gida ba domin rashin lafiya Alhaji ai ta fi sati ba ta fita ba, Ma'u na dariya ta ce" Ko ana gobe rashin lafiya Alhaji kin biyo gidana kika ce daga anguwa kike hanya ta biyo da ke? Ko ba a yi haka ba? Ta faɗa tana kallonta ganin an ƙure ta sai ta wayance da cewa ta tuna sun je gaisuwa can ɓarayin su Ma'u shi ya sa ta biya ta gidanta. Ganin ta na neman sauya hirar ya sa na kalleta ina mai kiran sunanta. "Zaituna kenan. Ki daina ma karya kowa ya san halin ki nan kwanaki na ji an ce kin cinye kuɗin adashen mutane har da yan sanda suka dauko miki, to ni dai ba zan ce ki bari ba amman in kika ɗauko rigimarki ki riƙa tsayar da ita a kan ki ko akan dangin ki, ki bar ɗan uwana ya huta duk kin tsufar da shi kin saka shi a uku, kar ki kashe mini ɗan'uwa gwara ma ki daina abin da kike yi." Sai ta kasa mgana Yaya Balki ta ce gaskiya ne Yaya Abubakar duk ya fara tsufa saboda wahala da rashin kwanciyar hankali. Yaya Murja sai ta taɓe baki kafin ta ce" Ai Allah ya bashi wasu kudaɗen sai na ce ya kara aure ita kuma ta je can ta ƙarata, ka rasa abin da take siya da kuɗin da ta ke rigima komai dai dai gwargwado ya na yi miki zaituna me kika nema kika rasa? Ganin mun yi mata taron dangi ya sa ta fara kuka tana murza idanuwana. Yaya Balki ke faɗin" Me ye na kuka? Domin fa muna sonki ne ya sa muke gaya miki gaskiya da wasu dangin ne wallahi sai dai  ki ji wata maganar, to ki ɗauka mu muna sonki ne shi ya sa muke faɗa miki gaskiya domin ki gyara." Yaya Aina ta karɓe da faɗin" Kwarai da gaske in wasu dangin mijin ne ita kanta ta san ba za su ɗauka ba. Faɗan ke so kan ki muke yi miki ki gyara saboda ke ba yarinya ba ce kin san abu mai kyau da mara kyau, in kika bari ya yi zuciya ya ɗau wani mataki akan ki ba za mu saka baki ba to kafin akai ga haka ki sauya rayuwar nan da kike yi, ki zauna a gidanki ki fita daga shiga rigima tunda ba abin da mijin ki ya rage ki da shi' Kowa na ta tofa albarkacin bakin shi, Yaya Murja dai ta ƙare mganar da cewa" Ke ko koyi ba za ki yi da su khaleesat  da Laila ba? Dube su kowacce tsaf ita da ƴaƴanta, kuma suna rawan jiki akam mazajensu suna tattalin su amman ke ba wannan a gabanki sai shirme, to ki fara gyara kanki da gidanki in kuma ba haka wata rana za ki yi nadama."   Ma'u ta saka baki tana faɗin" Ki rika kwalliya Zaituna. Haba kamar ba mace ba, ba ki gyara balle ki gyara ƴayan ki? Namiji fa na son gyara kuma in kika gyara wallahi sai ya ji daɗi" Nima na yi mata nasihan ta daina zama kaca kaca ta zauna a gidan ta gyara kanta tana kuka tana mana godiya tare da alƙwarin ta daina muna mata fatan haka daga nan sai muka saki maganar muka shiga wata hira ana mganar Baba Sani zai tafi gobe su Yaya Hamza sun bar kuɗi a ba su Yaya Aina ta ce in muna da wani abu mu haɗa masa ko in akwai mai sabulai da omo mu kawo ni dai na ce ina da sabulai zan aiko da safe Ma'u ta ce za ta ga abin da za ta aiko, har da kaya ma Yaya Balki ta ce tunda wancan zuwan da suka yi Matar Baba Sani ta mata zencen kayan yara haka suna so. Yau dai zaman gwanin daɗi ba faɗa ba bakar magana kowa ya binne abin da ke ran shi, Yaya Aina ce ta kalli Ma'u lokaci ɗaya tana faɗin" Ke ko Ma'u dangin babanki na neman ki yanzu? Sai ta yi shuru kafin ta ce" E. Muna waya da wasu daga ciki can kwanaki ma wata wacce da mamanta da babana uwar su ɗaya uba ɗaya ta zo wajena har ta yi kwanaki. Ni dai na daɗe ban je ba amman Alhaji ya ce in ya samu lokaci za mu je mu gan su." Yaya Murja ta yi karaf ta ce" Ba dole su neme ta ba. Sun ji labarin ba ta wulakanta ba. Ta na da abin duniya." Yaya Balki ke faɗin" To daman ai sai an san kana da amfani ake nemnka. Lokacin da suka san su za su wahala da ita ai ba su damu ba. Sai yanzu da suka san za su more ta. Ba komai abin da ta ke dashi ta yi musu ba shike nan ba." Ni ko ina gefe na ce shiken nan kuwa. In kana da shi ka yi in baka dashi ne in baka yin ba matsala. Ita dai sai gyaɗa kai ta yi tana faɗin in sha Allahu. Sallar la'asar ya tashe mu a wajen, bayan mun idar da sallah na shiga ɗakin Gwaggo na gaida Baaba ta amsa kamar yadda ta saba amsa mini. Daga nan ɗakin Mama na yi shigewata ina duba wayata su Firdausi ne a tsakar gida suna shara wasu na wanke wanke su Yaya Murja na baro su ɗakin Gwaggo. Tun da su sun rigani zuwa karfe biyar Yaya Aina ta yi sallama ta wuce gida bayanta Yaya Balki tare suka fita da Zaituna ni ma sai na yi shirin tafiya har Ma'u na fadin ta ɗauka sai dare zan tafi, da haka na so amman sai na tuna zan yi ma su Jidda kitso ba zan zauna jiran Yallabai ba. "Tafiya zan yi. Na yi ma su jidda tsifa zan kama musu kai gobe makaranta." Yaya Murja na gefe ta ce" Da kin zo da su Firdausi ta yi musu." Sai na ce mata ban yi tunanin Firdausin za ta zo ba ne, ina shirin tafiya Munirra ta kirani a waya ta na tambayan muna asibitin ne ko gida? Sai na ce mata muna gida sai ta ce mini gata nan zuwa ita ta tsayar da ni na jirata har sai da ta zo na rakata falon Alhaji ta gaishe shi. "Matar ƙanin Yallabai ne Alhaji" "Allah ya yi mata albarka. Na gode.". Har da kankana ta kawo masa Gwaggo na ta godiya,  mun dawo ɗakin Mama sai ga su inna Mariya sun zo duba Alhaji ta ce Amina ce ta faɗa mata jiya shi ne ta ce bari ta zo ta duba shi, dalilin haka yasa na daɗe a gidan tun da sai bayan sun tafi tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u, sannan ita Munnira ta ce min ba daɗewa za ta yi ba na fito rakata har bakin gida bayan ta yi sallama da su Gwaggo ta ke ce min. "Ke na taɓa ki da alheri matar Yallaɓai. Kin ji Yaya Usman zai kara aure? Ban samu zarafin mgana ba ta cigaba da faɗin" To yanzu ma mganar da ake yi Anty Zabba na gidan su. " Cikin nuna mamakin na ce"Wai har yanzu ba ta koma ba? Munnira ta ce" Ina fa ta koma, a bakin Nasir na ji wannan satin mai shiga Yaya Usman ɗin zai zo, na so kiran Anty Zabba sai na fasa kar ta ce ina da son jin gulma" Ina mata dariya na ce" Wallahi haka za ta ce." Munnira ta kama haɓa kafin ta ce" Shi ya sa ban kira ba. " Na ce gwara hakan itama Munira ta na faɗin ba ta ji daɗi ba, koma mene da ta yi hakura ta zauna tunda matar na shi ba akanta za ta zauna ba. "Uhm ke dai Munira Allah dai ya kyauta ya dai dai ta su." Ta amsa min da Amin Amin daga nan muka yi sallama

Chapter 21 of 31