Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
siya ƙanwar wata mate ɗina ce da muka yi Buk ce ke  yi. Sannan na siya ma Yallaɓai gift wani agogo mai kyau 25k shima a wajen wacce muka yi BUK na siya daman kayan maza take saidawa na saba siyayya a wajenta in dai zan siyam Yallaɓai wani abu na gift wajenta na ke siya. Bayan mun idar da salla mangariba muka ƙara kawata falon a center table na ijiye cake ɗin sai muka zagaye shi da voul na nama da dambun nama cake, da donut sai lemuka da ruwa. wajen ya yi kyau muna gamawa na ce Jidda ta kashe hasken falon in an ji motar Yallaɓai yana shigowa sai a kunna daga nan na ce su je ta yi wanka ta yi ma Baby na ce su saka dogayen rigunan da na siya musu yan kati ita na Jidda riga da wando ne. Baby kuma doguwar riga ce kala ɗaya na siya musu mai kalan baƙi da fari. Nima na shiga bedroom ɗina na tuɓe na faɗa Tiolet na yi wanka amma a ƙasan raina ina tunanin ina Yallaɓai ya je? Ko kaduna ya je? Ya ce zai kirani amma shuru har na fito wanka ina wasi wasi. Daman na yo alwalata ana kiran isha'i na kabbarta salla bayan na idar ne na zo na zauna gaban madubi na tsantsara kwallya mai ƙayatarwa. Na gyara gashina na sake shi baya na yi ɗauri mai kyau ɗinki riga ds sikat ne sun kamani sun yi mini cif a jikina haka na yi ma kaina barin turaren humra ko'ina na gifta ina tashin kamshi na saka wani takalmina baƙi mai ɗan tsini kaɗan ina tafiya ya na ɗan ba da sauti kaɗan ƙwas! Ƙwas   Falon yara na shiga na gansu sun yi kyau suma. Jidda ma ta ce" Umma kin yi kyau" na ce na gode  sai na ja su muka yi ta ɗaukan hotuna sun ɗan yi ma duhu saboda dare tare muka zauna sun kunna cartoon ni kuma waya ce a hannuna ina ta kiran Yallaɓai wayarsa a kashe tun ina duba agogo ina saran dawowar Yallaɓai har na sare Baby ta gaji har ta fara barci ita kanta Jiddam ma barci ta ke ji. "Umma Abba bai dawo ba? "Yana kan hanya in sha Allahu." Na faɗa mata cikin karfin hali. Tashi na yi na fara zagayen falon ina yi ina duba agogon wayata. Tara da rabi ta yi shuru sai hankalina ya tashi na fara tunanin ba lafiya goma na yi na ce bari na kira Nene na ji ko yana can ai kuma ya san da ina gida ina jiran shi. Na latso lambar Nene kenan zan kira sai kira ya shigo mini na ɗauka Yallaɓai ne jikina na rawa na koma na zauna sai dai kuma sunan wacce ke kira ne ya sa sai da gabana ya faɗi Ras! Haka kurum na ji kamar ba alheri ba ne ya sa ta yi min wannan kiran karfe goma na dare. "Ma'u ce.'   Jikina sai ya kama rawa har ta katse ban ɗauka ba. A ƙoƙarina na kira Nene amma ba ta bari ba kawai sai ga wani kiranta ya ƙara shigowa cikin dauriya da shahada na ɗaga kiran "Ma'u." Na faɗa kafin ma na yi mata sallama. Sai ta amsa mini cikin yanayin muryanta amma cikin farinciki. "Na'am Sadiyar Yallaɓai." Yadda ta faɗi sunan ne sai na ji ban yarda da ita ba. Kafin na samu zarafin mgana ta cigaba da faɗin" Na san za ki ce kira cikin daren nan ko? . Da sauri na ce" E ina fatan lafiya." Sai da ta yi wata irin dariya kafin ta ce" Lafiya sumul. Murna cika shekaru sha biyar da aure na kira na yi miki sannan tare da ba ki wani kyakyawan albishir." Sai kawai na ji zuciyata ta tsinke amma sai na ɗaure cikin karfi hali na ce" Na gode. Ina jin ki wani albishir ne wannan da ba za ki iya jiran safe ba ki ka kira cikin daren nan? Tana dariyan nan na ta na mugunta ta ce" Ba na so wani ya rigani ne. Na fi so ki fara jin wannan albishir ɗin daga bakina." Juyawa na yi sai na ga Jidda har ta fara barci daga kan kujera sai kawai na miƙe na buɗe kofar falon Yallaɓai na shiga na maida ƙofar na rufe a cikin duhun nan na lalubi kujeran dining na ja na zauna ina faɗin" Uhm ina jin ki Ma'u." "Zan kashe wayata yanzu. amma ki kunna data ki hau whatspp na tura miki saƙo." Ko kafin na ce wani abu ta kashe wayarta.  Ni fa na gama sakankancewa daman ba alheri Ma'u za ta nuna min ba. Amman ban taɓa tunanin ganin abin da na gani ba. Jikina na rawa na buɗe data saƙonni na shigowa amma ba ta su na ke ba Ma'u na ke nema ina ko ganin ta tura mini abu kamar hoto na faɗa hannuna na rawa na danna sama yana buɗewa. Wallahi tallahi yana buɗewa ne amma kamar yana buɗewa da gudun numfashina ne. Yana gama buɗewa na ji kirjina ya amsa. Kaina ya sara, hannunawana sun fara  ƙarkawa saboda jikina da zuciyata suna rawa ne a lokaci ɗaya a lokacin idanuwana sun firfito ba domin na ji mamakin abin da na gani ba ne. Sai domin ban taɓa tsammacin shi a lokaci kusa haka ba. Ina wannan rawan jikin da na zuciyan kiran Ma'u ya sake shigowa ban ɗauka zan samu kuzarin ɗaukan wayarta ba amma sai gashi na ja na ɗauka na kuma ƙarata a kunnina duk da yadda zuciyata ke gudu da sauri da sauri.   "Ina fatan kin ga irin kyakyawan albishirin ɗin da na ke so na gaya miki ko Sadiya? Runtse ido na yi zuciya na fat fat! Amma sai wata zuciyar ta ce Sadiya kar ki bari a ga gazawarki daman shi Ma'u take jira kamar an dake ni na dawo hayyacina sai na saki wani mirmishi wanda ya fi yin kuka daɗi na ce" Haba ai kin makaro Ma'u domin Yallaɓai ya riga ki yi mini wannan albishir ɗin' Shuru ta yi domin ni na san ta yi mamakin jin kalamaina. Ban bari ta ƙara mgana ba na ce" kin yi gaggawa Ma'u da kin jira da ni da kaina zan kira ki na faɗa miki Yallaɓai YA ƘARA AURE" Ban ƙara ba ta wata damar mgana ba na cigaba da faɗin" Walimar da na shiryama ma a gida saboda Anniversary ɗin mu ne da kuma taya shi Murnan ƙaruwan da ya samu na aure." Ina gama faɗin haka kit na kashe wayar saboda sai na ji kamar santsi na ja na ina shirin na sumulmiyo daga kan kujeran da na ke zaune. Sai na kama jikin kujeran da hannuna ɗaya na ƙanƙame jikina ba inda ba ya rawa. Zuciya ta da tunanina sun tsaya waje ɗaya cak na kasa yin ma wani tunani. Ji na ke yi kamar ina zaune ne amma jiri na ke gani shi ya sa na ƙamƙame kujeran da na ke zaune amma ban san lokacin da na ji na sulmiyo ƙasa ba.  Sai ga ni zaune a kan mazaunaina a ƙasan tayel ina kokawa da numfashina wayata ta yi zaman dirshan a kan jikina na saka hannunawa da suke rawa na ɗauka na buɗe na koma whatpps na shiga kan sunan Ma'u ina kallon hoton da ta tura mini sai a lokacin na lura da in da Ma'u ta ga hoton.   Sunan Anty Bahijja ne a saman sreenshoot ɗin da ta yi, sannan hoton na GIMBIYA CE(SAUDATU) tsohon hotona kamar ma a gidanta na Abuja ne kafin mijinta ya rasu. Tana tsaye a falon gidanta a lokacin ta na mirmishi ta saka wata doguwar riga ne a hoton. Abin da ya fi ɗaukan hankalina shi ne kalaman da aka yi amfani dashi a ƙasan hoton. "Allahu Akbar alƙawarin Allah ya tabbata. Congratulation Mrs Yusuf Muhammad(Tafida)." An ce wai ka yi ma hawaye rahama ne. Sai yanzu na amince da wannan mganar, na kasa jin kuka ya taho mini ma idanuwana sun ƙeƙashe. Shi kenan ta faru ta ƙare an yi ma mai dami ɗaya sata. Daman shi ne suprise da Yallaɓai ya ke ta faɗin zai ba ni? Lalle ko na karɓi kyakyawan suprise. Ban san lokacin da ya shigo gidan ba domin ban ji ƙaran buɗe get da shigowar motar sa ba ba.  Sai da na ji lokacin da ya ke saka ɗan makulli yana ƙoƙarin buɗe kofar falon kamar an jani an mikar dani tsaye sai ga ni a tsaye a kan kafafuna. Wayata kuma tana jimƙe a hannuna. Ya buɗe kofar kenan ya shigo ni kuma sai na fara takawa ƙwas ƙwas ina ji jikina na rawa amma na daure na isa ga makunnin wuta na kunna dai dai yana ƙoƙarin ciro wayarsa daga aljihu domin haska fitila. Haske ya gauraye falon. Ya bi ko'ina da kallo dai dai lokacin kuma wasu daga cikin bloons ɗin da na saka afalon suka fashe ji ka ke yi tus! Tus! Sai da ya ɗan waiga sannan  ya juyo yana  sauke kallon shi a kaina dai dai ni kuma ina tsaye a gaban shi na harɗe hannayena a bayana. Na ƙasa takawa zuwa gare shi,  saboda sai na ga kamar ba Yallaɓaina bane kamar wani ne wanda ban saba dashi ba, sai na ke jin kamar wannan Yallaɓan yanzu akwai wata tazara da ya shimfiɗa a tsakanimu daga yau. Kafafuna sun yi sanyi kamar gara ya kama su in na ce zan cire ƙafa zan iya zubewa saboda firgici. Shi ma sai na ga ya tsaya yana kallona amma kuma bai tsawaita ba da sauri ya kauda kanshi. Mirmishi ya ke gayyato ma fuskarshi sai dai ban bari ya gayyato ma kanshi ba ni na fara gayyato ma kaina mirmishi lokaci ɗaya ina faɗin. "HAPPY 15 YEARS WEDDING ANNIVERSARY YUSUF MUHAMMAD TAFIDA." Na faɗa ina kallon ƙwayar idanuwanshi. Yadda ban je gare shi domin na rumgume shi ba. Shima bai yi saurin takowa gare ni ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana mai ijiye ledojin da ya shigo da su a hannun shi a ƙasa wanda ban san abin da ke ciki ba. Kafin ya ɗago kansa cikin ƙwayar idanuwanshi na ga rauni. Kasala tsoro da wani abu da na kasa ganewa. A kuma yanayin ya  kira sunana cikin wata irin muryan da ban taɓa sanin Yallaɓai  na da ita ba. "HALIMA." Zan iya kirga sau nawa Yallaɓai ya taɓa kirana da sunana Halima, a da in ya kirani ina jin kaina ya yi girma. Amma ban da yau domin sai na ji kamar ya kwarara min ruwan zafin a cikin jikina. Har ina jin tururunshi da hucin shi daga fatar jikina. Sai na ji kamar komai yana sauyawa kamar  duk wata kyakyawan alaqan da muka gina ta tare da Yallaɓai tana zangayewa tana komawa ruwa. Kamar kuma ruwan ya fara zuba a ƙasa ya na kwarara da ƙarfin gaske wanda daga ni har shi ba za mu iya tare shi ba. *Ƙarshen littafi na Ɗaya* _*Nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya na labarin Sadiya da Yusuf, ba zan ce komai ba domin kun gwadani kun gani, yanzu ma muka tsoma hannu a cikin labarin, ba mu fara komai ba gundarin Labarin na cikin littafi na biyu da na uku, kuma na sanar da ku a manhajar Telegram za mu yi 2,3 ɗin shi, in kuma tsarin VIP ne to mu haɗu a AREWABOOKS, zamu tafi hutu kamar yadda muka saba har sai mun samu adadin mutanen da muke so kafin mu fara, ku yi gayya, ku ba da labarin TURKEN GIDA, ku sanar da wanda bai karanta ba da ya fara domin za a iya barin shi a baya. Wallahi tallahi ina da kyakyawan yakini akan abin da na rubuta kuma ina mai ba ku tabbacin za ku samu labarin nan fiye da hasashenku a kaina, In sha Allahu ba zan ba ku kunya ba, ku biya kudin karatun ku, da zaran kun kai adadi za mu fara kuma ba jira har sai mun dire in sha Allahu. NA GODE*_ *TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU  #1k NE KACAL,  AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 09069067488. 08032773332. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *Janafty* *25 November, 2024* *17/May/2025* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 31 of 31