Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma shekarun sun haura goma sai dai tunawa da abin ya faru kawai a yi dariya ko nishaɗi.   Mun cigaba da hirar baya a tsakanin muna yi muna dariya cikin nishaɗi wata magana da Yallaɓai ya faɗa sai da na sauka ƙasan cafet ina dariya.   "Lokacin da kika samu cikin Jidda na faɗa ma kawu Abba da Tariq? Kin san me Abba ya ce? Bai ba ni zarafin mgana ba ya cigaba da faɗin" Cewa ya yi wai ashe dai da gaske ina son aure ashe ƙwan haihuwa ne kunshe a cikina da ba a barni na yi auran nan ba da Allah kaɗai ya san in da za kai wannan ƙwan haihuwan."   Ia riƙe da cikina ina dariya na ce"To sai ka ce musu me? Domin ni a baya bai taɓa faɗa mini sun yi haka da su ba. Shima ƙasan cafet ɗin ya sauko kusa da ni yana faɗin" Me kuwa? Na ce wallahi ai kun kyauta ma kanku da kuka yimin yaƙi kan aurena da Sadiya. Tariq kuma ya ce Allah ya shiryeka Yusuf ban san yaushe ka lalace haka ba."   Ina kallonsa na ce" Gaskiya nima na san ka lalace ni ba haka na aure ka ba." Kansa ya saukar mini a saman kafaɗata yana faɗin" Ke kika lalatani Sadiya. Kika koyar da ni abin da ban sani ba kika buɗe mini baki. Kin san an ce da Namiji ya san mace bakinsa ke buɗewa." Mintsinin hannunsa na yi ina faɗin" Ni kar ka mini sharri. Na koyar dakai ko ka koyar da ni? Na faɗa ina kallonsa sai ya ɗago shima ya na kallona kafin ya riƙe mini hannuna guda ɗaya ya matse cikin hannunsa ya na faɗin" To shike nan na ji mun koyar da juna shike nan? Sai na gyaɗa kai matsowa na yi kusa dashi na matse shi rabin jikina na kan jikinsa ina faɗin" Wai Tarig ɗin sun koma ne? Yana shafa bayana zuwa ƙuguna ya ce" Ina jin kamar sai cikin Weekend ɗin nan za su koma. Faridarsa ma ta ce na gaisheki ranar na sha'afa ne." Kai na jinjina ina gyara zaman kaina a saman ƙirjinsa lokaci ɗaya ina faɗin" Yallabai. Kayan abinci fa sun ƙare." Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Bari mu gani zuwa a shiga wannan satin. Sauran da ya rage zai kai mu lokacin? "A'a gaskiya. Ko su indomie duk sun kare lemun su Jidda na makaranta ba ko rabin katan bai kai ba."   Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Allah zai rufa asiri. Amman duk kudaɗen hannuna na saka su cikin aikin nan kuma ba a ma gama ba ballatana su yi mana payment amman dai na yi magana da su za su fara ba mu half ɗin in angama aikin sai su cika mana."   Ɗago kaina na yi ina kallon shi kafin na ce"To wancan payment ɗin na ku da suka ce tun wancan watan fa? Shuru har yanzu? Ɗan girgiza kai ya yi kafin ya ce"Wallahi kuwa. Kin san yanayin aikin namu ace yau a ce kuma gobe. Sai dai kawai ranar da muka gani ko jiya mun yi mgana da P.A ɗin kwamishina ya dai ƙara bani hakuri kin san sha'anin gwamnati sai haƙuri kawai."   Gyara zama na yi ina kallon shi kafin na ce" Allah ya sa su biya ku a wannan watan" ya amsa min da Amin Amin domin muna cikin bukatar kuɗi mganar asibiti na yi masa sai ya kalleni kafin ya ce" Ranar monday ne ko? Sai na shirya mu je taren ko? Sai na jinjina kai kafin na ce"Allah ya kaimu." Dukkanmu sai muka yi shuru hankalin mu kuma sai  ya koma kan TV ɗin da ya ke shi kaɗai tunda hankalimu ba shi a wajen gabaɗaya.   Har na sha'afa da mganar sai na tuna da sauri na kalleshi ina kiran sunan shi. "Yallaɓai na" "Uhm" "Ashe kuma Yaya Usman aure zai ƙara? "E. " Haka kawai ya ce mini ba tare da ya kalleni ba. Hankalinsa na kan kallo ni kuma sai na ƙara gyara zama ina faɗin" Shi ne ba labari kuma? "Labarin me? "Auran mana. Ko kai ban ji a bakin ka ba." Sai a lokacin ya juyo ya kalleni kafin ya ce"Bikin ya zo ne ba ki ji ba? Sai na girgiza masa kai jinjina kai ya yi kafin ya maida hankalinsa kan kallon shi lokaci ɗaya yana faɗin" Ba ma yanzu ba ne. Ina jin sai nan da wattani huɗu sai yarinyar ta gama karatun ta ta dawo tukunna za a yi bikin." "Au daman yarinyar ba anan take ba? "E. Ɗiyar ogansa ce a wajen aiki. Tana london ta na karatun masters ɗin ta amman ta kusa dawowa in ta dawo ne za a yi bikin." Ƙara matsan Yallaɓai na yi domin ina son na ji labari kai tsaye na ce" Ikon Allah. Kuma ya na sonta? Wannan karon wani kallo Yallaɓai ya yi mini da ya sa na yi shuru ina yar dariya kai ya girgiza kafin ya ce"Ban san wannan ba. Shi kaɗai zai iya amsa miki wannan tambayar.".   Ina dariya na ce"Kai ma za ka iya." Bai ƙara mgana ba sai na kwantar da kaina saman kafaɗarsa ina faɗin" Na yi mamkin da na ji zai ƙara aure. Duk irin yadda suke son juna shi da Anty Zabba'u.'' Yallaɓai dai ya lura da mgana a bakina sai bai biye mini ba sai kawai ya kallleni kafin ya ce" Uhm" Ina shafa kirjinsa na ce"Wallahi. An ce fa ta yi yaji ta na kano yanzu haka. Gaskiya ban ji daɗi ba. Kuma har yau shi Yaya Usman bai zo biko ba ya kyauta kenan?   Yallaɓai ya muskuta kafin ya cire ni daga jikinsa yana kallona cikin buɗe ido ya ce" Sadiya a ina kika ji wannan maganar? Kai tsaye na ce" Yau da na je gidan Halima ta ke faɗa mini fa. Ko ba a yi ba ne? Kai ya girgiza kafin ya ce"Ban sani ba. Domin ni a bakin ki ma na ji wannan mganar." Da sauri na ce"Au wai ba ka sani ba? An ce ko ba ta a fatakol. Ta dawo kano domin Halima ta faɗa mini bai faɗa mata mganar auran ba sai da aka saka rana da ta ji shi ne ta tada hankalinta ina ga dalilin yajin kenan." Ƙura mini ido ya yi yana kallona nima ko ina kallonsa ban damu ba na cigaba da faɗin" Gaskiya Yaya Usman bai kyauta ba. Bai kamata ya yi ma Anty Zabba haka ba an zama ɗaya an tara iyalai yayansu biyar fa aurensu sama da shekaru ashirin a ji Anty Zabba ta yi yaji saboda zai ƙara aure ai wallahi sai an zage shi duk da ban sani ba ai na san ba ta rage shi da komai ba. Wani lokacin ku Maza ba ku da adalci in za ku ƙara aure a ƙokarin ku sai duniya ta fahimci mace ta gaza ne ya sa kuke son ƙara aure" "Shi ya ce miki saboda Zabba'u ta gaza ne ya sa ya ke son ƙara aure? Ya katse mini mgana nima ko na taso masa da cewa" E mana saboda ya yi munafunci miye a ciki in ya na son ƙara aure da ba zai faɗa mata ba sai da mgana ta kamkama bayan ma an saka rana? A hankali ya ce" To ai Ogansa ne ya bashi yarinyar kuma akwai girmamawa a tsakaninsu shi ya sa ya karɓa". Mamakin Yallaɓai ya kamani yadda ya zauna ya na kare ma ɗan'uwansa..   "Duk da haka dai ai yana so ne ya karɓa shi fa namiji ba a yi masa dole Yallaɓai na. Kuma tun da har ya amsa me ya sa bai zo gida  sun tattaunawa da matarsa ba? Tsakani ga Allah bai kyauta ba a ce sai da aka saka rana ya ke gaya mata ko ni ce zan yi abin da yafi nata. Yanzu ta koma gida in an zauna ana mgana sai a ce saboda mijinta zai yi aure ta tada hankalinta ta kasa zaman gidanta ahalin abin ba haka ba ne shi ne bai kyauta mata ya yi mata rashin adalci bai kuma kalli zaman auren su na tsawon shekaru ba"   Yadda na ɗau zafi kamar ƙanwar Zabba'un abin ne ya ɓata mini rai ganin Yallaɓai na nuna abinda ya yi ɗin dai dai ne. Kallona kawai ya ke yi ya ina ta faɗa sai kawai ya juya ya jingina da kujera ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa amman bai yi mgana ba sai ni ne da na gaji na kalle shi ina faɗin" Yallaɓai ba ka ce komai ba? Kai tsaye ya ce" Me zan ce! In yi mgana ki ce ina kare masa saboda yana ɗan'uwana ko in ce ita ba ta kyauta ba ki ce sabo da ni Namiji ne ko? Baki kawai na saki ina kallon Yallaɓai ganin kamar ya ɗau lamarin da zafi. Ban gama mamaki ba na ji ya na faɗin" Ke ba ki san abin da ya faru ba kin bi kin zauna akai har kina zargin wani bai kyauta ba a mata da miji ba ka jin bangare ɗaya ka yanke hukunci shin shi kin ji na shi ne! Kin san me ya faru tsakaninsu da ya sa ta yi yajin? Kuma ban yarda Yaya Usman bai faɗa mata ba sai dai in ita ce ta ƙi amincewa tun farko daga baya da ta ga abin da gaske ne sai kuma ta sauya labarin. Mganar yaji kuma ita ce ta ji kunya miye na ta na yin yaji? Auransu shekara ashirin ko sakin ta Yaya Usman ya yi gidan nan ya zama nata. Hakan da ta yi ta nuna cewa ba za ta iya rufa ma mijinta asiri ba ta gwamace ta koma gida ta fallasa komai domin a san halin da suke ciki a yi musu dariya kuma wallahi kanta ta rage ma ƙima in ma tana tunanin ta yi ne domin samun wata daraja ko ɗaukaka in ta yi hakuri wallahi tallahi wata ba za ta zo ta fita ba ba kuma ina kare masa domin yana ɗan uwana ba sai domin na san halin shi adali ne kuma jajircettace ai yana sonta ya aureta ba zai zama domin ta gaza ba ne zai ƙara aure sai domin auran na cikin kaddaran Rayuwansa"   Idona a kan Yallaɓai ganin yana ta rattabo mgana. "Hmm " Kawai na ce kafin na yi shuru shima shurun kawai ya yi yana cigaba da kallon shi ban sake mgana ba ina auna mganarsa a zuciyata ba wani saboda yana ɗan'uwansa sai kuma domin ya na Namiji amman ko Anty Zabba na da laifi shima Yaya Usman ɗin ya na da laifi ni ko kwana za mu yi anan wajen maganganun Yallaɓai ba za su sa na daina ganin laifin Yayansa ba. Haɗe rai na yi har ina matsawa can nesa da shi kallona ya yi kafin ya yi ɗan mirmishi ya na faɗin" Ni ban kare masa ba. Gaskiya na faɗa miki. Sannan ki cire wannan tunanin na in namiji zai kara aure wai gazawar ta gida ce ba haka ba ne saboda shi aure da mutuwa duk ɗaya ne ba ka sanin lokacin in Allah ya kaddaro maka ne ba yarda za ka yi amman ba nufin ta gida ta gaza ba."   Taɓe baki na yi kafin na ce" Haka kuke nunawa shi ya sa muka ɗauka haka ɗin ne." Na faɗa har ina hararan shi sai kawai ya yi yar dariya kafin ya ce"To ke miye naki a ciki! Tun da ba ni ne zan ƙara auren ba." Ina mele baki na ce" Da nawa a ciki tunda mace ce ƴar uwata kuma muna aure a zuru'a ɗaya." Kawai sai ya fara mini dariya na kalle shi ina faɗin" Na zama abar dariya ne? Hannu ya ɗaga sama kafin ya ce"Ko ɗaya gani na yi har matsawa kika yi daga kusa da ni. Ni ne Yaya Usman ɗin? Tabe masa baki na yi sai ya fara matsowa kusa da ni yana faɗin" Yanzu dai Yaya Usman bai yi ma Zabba'u adalci ba ko? Mata ban san me namiji zai yi ya iya muku ba. Auran su sama da shekaru ashirin bai yi tunanin ƙara aure ba sai yanzu. Da ace ya ce zai yi a farkon auren su sai a ce daga yin aure zai ƙara mata kishiya in ya bari sai ta ɗan sha miya sai a ce sai da ya ga ya sun gama wahala tare ya yi kuɗi zai saka mata da kishiya in kuma ya bari ta manyanta sai a ce ya ga ya gama moran ƙuruciyanta zai ƙara mata kishiya. Mara adalci butulu duk kalaman ku ne. Na rasa ko wani yanayi ne na kishiya zai taɓa zama dai dai a wajen ku.' Kafin ma ya ƙariso na yi saurin miƙewa ina faɗin"Ba wannan yanayin domin ba macen da ke son zama da kishiya. Ko a gidan Annabin Rahama matansa sun yi kishi ballatana mu."   Shima miƙewan ya yi yana yar dariya kafin ya ce" To wai an ya ni za ki bari na ƙara auran nan? Wata uwar harara na wurga masa kafin na ce" Ai na san ka na da ra'ayi. Allah ya ba da sa'a. Ta zo mana tunda ba kaina za ta zauna ba "    Na yi wucewata na barsa nan tsaye sai ya biyo ni yana dafani kamar irin yadda ƙawaye ko abokai suke yi "Ba yanzu ba. Sai na zama mai kuɗi lokacin kin zama Gwaggo sai na auro yar shilla mu ƙarishe rayuwarmu tare ko? Da gwiwan hannuna na tokare masa ciki ya yi gefe yana dafe cikinsa fita na yi daga falo ina mai buga masa ƙofa. Bai biyo ni ba sai da ya tsaya ya kashe kayan wuta gabaɗaya ni daman ɗakin yara kawai na leka na ga sun yi barci sun bar wuta akunne Jidda ta bar littafanta nan ƙasa barci ya ɗauke ta. Ta shin ta na yi ta koma saman gado ni kuma sai na kwashe littafanta na ɗora mata saman drower ɗin su na tashi Baby ta je tiolet ta yi fitsari sannan ta dawo na kwantar da ita na sake tofa musu addu'a na kashe musu wuta na rufo ƙofar ina fitowa muka haɗe da Yallaɓai na dauƙe kai na ƙarisa wajen makashin wuta na kashe duhu ya bayyana. Na ji takunsa ta baya na ban anƙara ba na ga ya ɗagani sama yana nishi nishi. Wuntsila kafa na fara ina faɗin" Ni ka sauke ni"   Na faɗa ina tura masa baki,  shi kuma ya na faɗin" An ki ɗin" Wuntsila kafa na yi da sauri muka yi baya kamar zamu faɗi shi ya sa ya sake ni yana dafa bango. Dariya na saka masa saboda akwai duhu har bayansa na bige bango. "Wassh.." Haka ya faɗa, ni kuma sai na kwashi gudu ina jin sa ya na faɗin" Sadiya ki tsaya anan wajen." Ƙofa na buɗe na gudu bedroom ɗin mu ina faɗin" In kana da karfi ka kamani.".   Ina shiga na kashe hasken ɗakin duhu ya bayyana ya na shigowa ya fara kiran sunana ni kuma ina danne dariyata. "Yarinya in na kama ki za ki sha wuya fa." Motsina ya ji ya fara laluɓata ina gudu muna zagayen gado daga karshe mune har saman gado. A ƙarshe dai Yallaɓai ya yi nasaran kamani ina ta dariya gabaɗayanmu muka baje kan gado muna sauke numfashi. Muna kuma kallon juna acikin duhun ɗaki ni ce na ganganra na hau jikinsa na rike masa duka hannuwansa biyu na duka ina sumbatar bakinsa. Shima ya na tayani daga karshe. Da ya ke ya fini karfi tuni ya ƙarbi ragamar lamarin ya mirgina da ni na dawo ƙasan sa shi kuma ya kama ni a hannu tuni muka lula cikin irin ta mu kyakyawan duniya ta ma'aurata irin mu masu marmarin juna da muradi a kullum.    ***** Washegari ta kama jumma'a ne. Yara sun tafi makaranta Yallaɓai kuma an kira shi ya fita office tun safe sai ni kaɗai a gida. Tara na safe Saude ta zo yau gyaran kitchen na ke jin yi sai na ce ma Saude ta gyara sauran ɗaku nan ni kuma sai na gyara kitchen. Ina can ina gyaran wayata na ɗaki ana ta kira ban sani ba. Da ya ke Saude iyakarta gyaran falon farko da na biyu sai ɗakin yara da kitchen sai wanke tiolet ni na ke gyara ɗaki na da kaina sai haraban gidan bayan kwana biyu ko uku haka. Ni na ce ta shiga ɗakin da na ke sauke baki da ke kallon Bedroom ɗina ta gyara mini sai ta ji kamar ana ta kiran wayata sai ta ruga kitchen ta na cewa" Anty na ji kamar ana kiran wayarki a ɗakin ki." Sai na sauke Towel din da nake goge gogen na nufi cikin ɗakina sanye na ke da riga doguwa amman iyakarta gwiwata da kaɗan kwalliyar safen da na yi ma Yallaɓai ne kafin ya fita. Ina zuwa na ɗau wayata da ke saman gado na yi mamakin ganin kiran Ya Auwal har sau uku shi da kira ɗaya ya ke yi shi da Yaya Hamza in kin zo kin ganni sai ki kira su daga baya ganin kiran sa har uku sai na ji tsoro ina shirin bin bayan kiran shi sai kuma ga kiran shi ya sake shigowa da hanzarin na ɗaga.   "Yaya Auwal" Haka na faɗa cikin fargaba daga can bangaren da sauri na ji ya ce"Sadiya kina asibitin ne? Ya jikin Alhajinmu na mu? Cikin mamaki da rawan baki na ce" Wani asibiti ku. Kuma? Alhajinmu ba shi da lafiya ne? Cikin mamaki ya ce"Ba ki sani ba! Dazun nan Yaya Abubakar ya kirani ya ce Gwaggo ta kira shi a ruɗe Alhajinmu ya faɗi. To mun sake mgana ya ce ga shi sun isa asibitin mun rabu kan zai sake kirana amman shuru kuma na yi ta neman layin sa ban samu ba." Cikin tashin hankali na ce"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Wallahi ban sani ba. Ba wanda ya kirani Ya Auwal." "To ki yi maza ki shirya. Ki kira ki wayar Gwaggo ki ji asibitin da suke kin ji ko? Sai na amsa masa shima ya ce daman suna shirin tahowa ne da ya bari sai gobe asabar amman tunda ga wannan matsalan suna nan tafe in sha Allahu. Muna gama mgana hankalina tashe na kira wayar Gwaggo ba ta ɗauka ba sai na kira ta Yaya Abubakar amman ba ta shiga ba sai na kira Rahila ita na sameta abin mamaki suna asibitin tare da Ya Muntari shi ta ba ma wayar ma ya faɗa min asibitin da suke. Hankalina duk ya tashi Alhajinmu na da hawan jini amman ya daɗe bai tashin masa ba sama da shekaru biyar. Bayan rasuwan Mama ne ya kamu da hawan jinin. A gaggauce na yi wanka na shirya na kira Yallaɓai ina faɗa masa ya ce gashi a hanyar Rano amman zai dawo da wuri mu haɗu a asibitin. Saude na bar ma gidan na ce ta dafa musu sauran taliyan da ta rage ita da su Jidda. Ta kuma tsare min gida har in dawo Alhajinmu ke asibiti ba lafiya. Cikin yar damuwa ta ce" Sai kin dawo Anty. Allah ya bashi lafiya" na amsa mata da Amin tsabar sauri sai da na fita na tuna jakar da na ɗauka ba kuɗi a ciki sai da na koma na sauya wata jakar fitar ta sauri ce kayan jikina doguwar rigar atamfa ce sai na saka dogon hijabi Jalbab. Adaidaita na tara zuwa asibitin na kuɗi ne ban ƙara razana ba sai da na kira Rahila ta ce suna Emergency a firgice na tambaya aka kwanta ta mini Duk da ina cikin firgici na yi mamakin ganin kaf ƴan gidanmu a wajen kowacce da mijinta har da Ma'u Alhajinta da su ake shiga ana fita. Yaya Aina ce kawai ba mijinta a wajen amman har da Mijin Yaya Balki da na Yaya Murja. Yaya Abubakar da zaituna suna wajen. Ga Rahila ga Ya Muntari. A ƴan ɗakin mu ba kowa tunda Amina na kaduna ƙila ba ta sani ba ni ce kuma a cikin su ba wanda ya kirani amman sun iya kiran Ma'u saboda tsabar munafunci.    Raina ya ɓaci da haushi shi ya sa daga su har mazajen na su ba wanda na ce ma sannu. Ina ji Rahila na kiran sunana na wuce zuwa in da Gwaggo ke zaune na duka ina gaisheta ta amsa min cikin kulawa da casabaha a hannunta. "Ya jikin Alhajinmu Gwaggo? Kai tsaye ta ce" Da sauƙi sun ce jininsa ne ya yi sama sosai nunfashin dakyar ya ke fita amman sun saka masa Oxygen yanzu ba daɗewa." Ido na zaro ina faɗin" Innalillahi." Sai tadafa kafaɗata kafin ta ce"Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu Alhaji zai tashi."   Sai na jinjina mata kai ina maida kwallar da ta kawo mini mutuwar Mama kawai na ke tunawa. "Gwaggo shi ne ba a samu wanda zai kirani ya faɗa,mini ba? Yanzu ɗin ma ba domin Yaya Auwal ba da ba zan sani ba kenan? Cikin lallashi da damuwa ta ce" Ki yi hakuri hankula a tashe suke. Abubakar kawai na kiran suma yan'uwan na ki ki yi musu usuri sun shiga ɗimuwa" Sai ban ce komai ba amman a raina na ce a dimuwan aka kira wanda ake so.   Ba bari a shiga in da Alhajinmu ya ke Yaya Abubakar ne kaɗai da su Ya Muntari ke zirga zirga. Zama na yi kusa da Gwaggo ba wacce ma na kallah balle in yi mata sannu har Yaya Abubakar ban gaisar ba sabida ya bani haushi har da ya ganni ya na ce min" Ke sai yanzu kika iso? Cikin gatse na ce" E. Sai yanzu aka faɗa mini" Hankalinsa ya yi can bai ma jini ba Rahila ce ta zo ta zauna kusa da ni muka gaisa Yadda ta ga na haɗe rai ne ya sa ba ta jani da magana ba. "Hala Yallabai baya nan ne? Kai tsaye na ce"Lokacin da na ji labarin abin da ke faruwa ya fita" Sai ta yi shuru kafin can ta ce"Ki yi hankuri ni kaina hankalina ya tashi na manta da kiran ki." Wani kallo na yi mata amman ban iya mgana ba. Muna nan zaune jugum jugun har wajen azahar sai da aka cire ma Alhajimmu iskar Numfashi tun da sun ce numfashinsa ya daidai ta. Sannan suka maida shi ɗaki na musamman da Mijin Ma'u ya biya duk na ji Yaya Abubakar na faɗin Yaya Hamza ya turo kuɗi shi da Yaya Auwal amman kuma mijin Ma'u ya biya komai. Ina kallo suna ta yi masa godiya su Yaya Murja har tana faɗin" Allah ya saka masa da alheri ba domin alherin Ma'u a gare shi ba yaushe har zai riƙa yi mana Hidima haka? Ma'u ƙi kara yi masa godiya kin ji ko" Sai ta amsa da toh kawai. Ban yi wani mamaki ba sanin halin su balle Yaya Murja akwai son abin duniya ita kuma Ma'u in ta fahimceka ta san yadda za ta riƙe sosai. Sai bayan an kai shi ɗaki na musamman ne aka bar mu muka shiga yana barci amman Alhajinmu duk ya rame ya faɗa. Daga gani ya daɗe da ciwo a jiki bai faɗa ba an ce mu bar shi ya samu hutu sosai sai muka fito dukkanmu zuwa kofar ɗakin muka zauna saman kujerun wajen. Mijin Ma'u ya yi ma Gwaggo sallama zai tafi ita kuma ta tafi raka shi. Sai bayan sun wuce ne Ya Balki ta kalleni taba faɗin" Sadiya ya gida? Ɗazu kin zo hankula ba a kwance suke ba ba a gaisa ba." Sai na ɗan saki fuska muka gaisa buɗe bakin Yaya Murja sai cewa ta yi" Duk da haka ta ganmu amman ta fi ƙarfin ta ce mana sannu." Nima sai na kalleta kafin na ce"Saboda me zan ce muku sannu? Kun ware ni a cikin dangi ba wacce ta iya kirana ta faɗa mini halin da ake ciki sai Ya Auwal dake Abuja ne ya kirani ya faɗa mini. " Yaya Balki ta ce"E ba a kyauta ba to ki yi hakuri. Nima Ma'u ce ta kirani ta faɗa mini ta ce itama Yaya Murja ce ta faɗa mata.'   Shekeƙe na kalle su kafin na taɓe ba ki na ce"Ai da ya ke Ma'u ce ake son ta sani an kirata an faɗa mata ba shikenan ba." Rahila na taka min kafa wai in yi shuru cikin masifa na ce"Sai kin ƙi faɗan gaskiya!

Chapter 13 of 31