Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
karshe na fice da gudu zuwa bedroom ɗin ina shiga kafin na rufe ƙofa ya cimmin karfi ba daya ba turani ya yi kan gado ya biyo bayana ya na faɗin" Duk wayon Amarya dai." Ina ture shi ko gizau sai ya fara min cakulkuli ina ta dariya kamar zan mutu ina faɗin" Yallaɓai cikina don Allah ka bari." Sai da ya ga numfashina na sama sannan ya kyaleni ya na faɗin" Gobe dai dole ki bari na yi shagalina tunda kin ga asibiti na bukatar samples." Ko mgana ban yi mishi ba ina maida numfashi shima sai ya yi rigingine ya na nishi, ina ganin haka na lallaba na haye kanshi na fara masa cakulkuli da ƙarfi tun yana daurewa har ya fara dariya yana hantsila kafa, karshenta dai muka yi biji biji da gadon fililluka duk a kasa in ya yi min cakulkuli nima na yi masa daga haraba ma za a iya jiyo dariyan mu. Har sai da muka gaji sannan muka koma muka kwanta muna hutawa. Karfe sha ɗaya Yallabai ya yi wanka ya fita ya ce zai je Gwammaja ne daga can zai ta fi office ya fita ba daɗewa Saude ta zo ita na bari da gyaran gida na kwaso under ɗin yallabai da nawa sai kayan barcin mu na fita can in da muke wanki na kafa kujera kayan ba su da yawa kuma ba su yi wani datti ba cikin lokaci na gama na shanya na saka abin matse shanya na kama dasu. Bayana sai da ya riƙe ina gamawa na yi wanka da ruwa mai zafi, sannan na gyara bedroom ɗin da muka yi kaca kaca dashi ni da Yallaɓai. Ina da sauran fulawa sai na tura Saude kasuwar ƴan kaba ta siyo min kayan miya har da kabeji, ƙuli kuma daman ina da sauran shi sai dai bai da yawa ne. Da ya ke ina son gurasa to ina yi da kaina lokaci bayan lokaci. Gurasa na yi mana. Ita kuma Saude ta niƙa min sauran kayan miyan a blander na saka su a cikin fridge bayan ta ci na saka mata guda uku a leda na ce ta tafi da shi gida. Da safen daman Yallaɓai ya yi mganar albashinta daman mu da kan mu mun kan je gidansu hannu da hannu mu ba ma mahaifiyarta haka tsarin ya ke,  sai na ce mata ƙila mu shigo zuwa dare. Su Jidda suna dawowa su ka ga gurasa na yi suna ta tsallen murna. Kayan abinci ko sai bayan mangariba suka kawo mana. Yallaɓai baya nan dole su suka kwaso su zuwa cikin gida. Ma sha Allah na furta a raina komai an kawo har da su maclean da kayan maggi, ni da Jidda muka gyara komai a muhallinsa na Nene kuma na cire mata nata kayan Tea ne sai sabulan wanka da na wanki sai katan ɗin taliya da maracroni sai coouscous, tun da ta na so, shi ma saboda ya saba siya mata duk wata ne a matsayinsa na Namiji amman abincin gidan gabaɗaya yana Wuyan Yaya Usman ne gaskiya duk da sauran duk suna yi, matan ma kowacce tana iya bakin ƙokarinta. Kayan tea ɗin ma gida uku ne Nene da Hajiya Iya sai Maman farko. Da Yallaɓai ya dawo sai na nuna masa ya kalleni kafin ya ce" Ba matsala dai ko? Sai na rumgumeshi ina faɗin" Ba matsala mun gode Yallaɓai Allah ya ƙara buɗi da wadata." Sai shima ya riƙe ni yana amswa da Amin Amin. Ni nasan na yi dacen miji, in dai Yallaɓai ya na dashi ba zan taɓa neman wani abu na rasa ba. A daran muka fita mu ka je Gwammaja mu ka kaima Nene nata ya ƙara mata da 20k tana ta saka albarka farko ma ta ce ba za ta amsa ba ni na ce ta karɓa. Sai ta saka hannu ta karɓa tana faɗin" Komai fa suna yi min Sadiya to kuɗin kuma na mene ne? Ina mirmishi na ce" ki rike a hannun ki Nene kina yin baki da ga Rano ko na sallamansu kya samu." "Haka ne. Na gode Allah ya yi albarka" Muka amsa da Amin Amin muna gidan sai ga Mimisco(Anty Zuwaira) ita da mijinta itama kayan abincin ta zo da shi da kayan tea, sai mganar zuwa ganin likita ga Nene, tunda nauyin asibitin na ta Mimisco ce ta ce a bar mata za ta iya. Mun gaisa  da ita kamar yadda muka saba ni dai ban taɓa samun matsala da ita ba. Tana da ilmi ta kuma san yadda za ta zauna da jama'a. Saboda zuwanta ya sa muka ɓata lokaci tunda Yallaɓai suna ta hira da mijinta. Sai wajen tara da rabi muka baro gidan bayan Yallaɓai duk ya shiga ɗakunan su Hajiya Iya ya ba su 10k kowacce suka karɓa suna godiya a hanya ne ma da za mu je Ɗorayi Yallabai ke faɗa, min Yaya Usman ya shigo garin  jiya amman bai kwana ba ya koma a ranar. "To. Ya zo biko ne? Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce" Ban sani ba. Na san dai ba zai rasa zuwa gidan su ba." Sai na jinjina kai kafin na ce" Hmm. Allah ya kyauta.". Saboda ina so na yi magana ina tsoron  kar Yallaɓai ya taso min shi mai ɗan uwa. Mun fara zuwa gidanmu muka sake duba Alhaji 20k Yallaɓai ya ba ma Alhajinmu. Gwaggo kuma 10k suna ta saka albarka. A bakin Gwaggo na ji labarin yau da safe Baaba ta koma na ce Allah ya tsare. Daganan mun shiga gidan su Saude 50k Yallabai ya ba ma Balaraba daman a wata 30k kuɗin aikinta amman Yallaɓai na yi musu ihsani kuma kafim mu baro gidan sai da ya yi mganar ya na so ya saka Saude a makaranta bai da ce a barta haka ba karatun boko ba, ta gama firamari ba ta cigaba ba. Mahaifiyarta har da hawaye tana ta godiya zaman amana ne da maƙotaka ya haɗamu har na ga Saude na ce ta riƙa zuwa tana kama min aiki saboda na taimaka musu. Daga gidan su Saude gida muka dawo tun da daman mun yi sallama da su Gwaggo muna hanya Yallaɓai ya ce na tura mai acct number Datti zai saka masa wani abu ina ta masa godiya. "Tsakanin mu ba Godiya Sadiya ta." Haka ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na yi masa mirnishi kafin na ce" Duk da haka dai zan gode maka. Yallaɓaina Allah ya sa a fi haka." Sai ya amsa min da Amin muna yi ma juna mirmishi. ***** Washegari da sasaafe, bayan Yallaɓai ya ja mun yi ta barnar ruwa ni dai ai nace dole zan kira mai kitso kafin Yallaɓai ya sa gashina ya sauke ƙasa saboda jiƙashi da na ke da ruwa. Sai bayan su Jidda sun tafi makaranta a gurguje muka yi abin da aka umarcemu mu kawo daga Lab. Saboda yadda ya jadaddamana cikin sauri muka yi wanka Yallaɓai ya kai ni asibitin na kai musu da sauri suka karɓa bayan na haɗa musu da takardan da suka ba ni shekaranjiya. Suna karɓa suka ce mu jira a waje za su ba mu result ɗin. Tare da Yallaɓai muka yi zaman jira ana ta kiran shi ma a office bai tafi ba sai da aka gama test ɗin suka kuma bamu result ɗin da cewa zan kaima likita ranar clinic ɗina. Daga nan Yallaɓai ya dawo da  ni gida ya ijiye shi kuma ya wuce office domin ya faɗa mini akwai kwangilan da ya samu na zanen wani kamfani da za a buɗe a kaduna ne. Na bishi da Allah ya ba da sa'a shi ya wuce ni kuma na buɗe gida na shiga. Ban san me result ɗin ya nuna ba tunda rubutun likitoci sai su sai na adata kafin ranar Monday. Ranar yini na yi gugan kayan under ɗin mu da na wanke mana na goge su tas na feshe da turare, na jera mana a cikin wardrope, ganin na samu natsuwa ya sa na ɗau wayata na kira Aisha lame na yi mata mganar ina son Body lotion, sau Face soap sai Fade cream sai showergel na wanka Sai ta ce mini za a kawo mini sai na ce kamar yadda muka saba zan tura mata kuɗin ta, Aisha Lame ba abin da ba ta saidawa na gyaran jikin mata. Kuma kayan ta suna da kyau da inganci su na ke amfani dashi shi ya sa kullum Yallaɓai sai ya ce ya na son taɓa fuskata saboda taushi da santsi sannan ba guraje, jikina kuma ya yi fresh ya yi taushi domin Showe gel ɗin ta ba baya ba yana bala'in gyara fata. Cantact Aisha lame. +234 703 666 2633 Tana aikawa da kayanta ko'ina a faɗin Nigeria Daga ita sai na kira Surayya Dee mai kayan gyara na BOJUWA ta dalilin Aisha lame na san Surayya. Kuma na yi amfani da kayanta na yaɓa da ingancinsu. Ni duk bayan wata uku na ke shan mganin sanyi sannan na ɗora da na gyara Ni macece da ta yarda da gyara shi ne har gobe ya sa na ke da matsayi a zuciyar Yallaɓai. Duk da har kayan marmari ba na wasa da su da duk abin da zai kawo mini Ni'ima amman kuma ban zauna ba ina gyaran jikina tare da can ainihin majalisar ɗinkin duniyan gabaɗaya. Maganin infection na ce ina so Surayya ta aiko minibda shi in na gama zan siya kazan uwargida tana ta dariya ta ce" Hajiyar Injiniya ba a dai gajiya da gyara." Nima ina dariyan na ce" Ba a gajiya Hajiya Surayya. Gyara shi ne mace da gyaran ya sa har gobe muke ƙyalli a idanuwan mazajen mu." Tana ta dariya mun rabu akan yau ɗin nan mai kawo mata kaya zai kawo mini tun da ya san gidana, tun da ba yau muke tare ba, sama da shekara ɗaya tun da na gwada kayanta na san ingancin su. Domin ke ma ki dace da ingantattun kayan gyara contact Surayya Halin yau on +234 803 277 3332. Kano Nigeria tana aikawa da kayanta ko'ina. Zuwa yamma sai ga saƙon Surayya Halin yau, a daran kuma na tura mata har kudin kazar da zan siya. Mayuka na bangaren Aisha lame kuma sai washegari da safe ta aiko mini dashi. Ranar jumma'a gidan Rahila muka yini  ni da su Jidda, Rahilar ba ta da lafiya zazzaɓi daga ita har Bbyn na ta sai dare Yallabai ya je ya dauko mu, mun sha hira mun yi tsiya mun yi daɗi ta ji sauƙi tun da har kitso sai da ta yi mini daman ta iya ta rufa mini asiri kafin Yallaɓai ya saka ruwa ya sauke mini gashi. mun rabu da Rahila ta roƙe ni ƙanwar mijin Ma'u za ta yi aure za ta biyo mini mu je tare kai tsaye na ce" In ta gayyace ni ba? In ba ta gayyace ni ba wallahi ba zan je gayyar soɗi ba." Rahila na dariya ta ce" Ki ji tsoron Allah Sadiya. Ke yanzu sai kin jira Ma'u ta gayyace ki." Ina hararanta na ce"Kwarai kuwa. Kawai tusa kai ba kwarjini in ta gaya min zan iya zuwa amman ba ta gaya mini ba sai dai na ce a sha biki lafiya." Washegarin asabar kamar ta san mun yi maaganar da Rahila sai ga shi ta tura mini katin biki sannan daga baya ta kirani. "Ina fatan za ki zo dai zo ko Sadiya? Sai na ce mata in sha Allahu tun da sati na sama ne. ****** Ranar Monday, na koma asibiti na ga Dr Aisha bayan na ba ta sakamakon ta duba cikin ikon Allah ta ce da ga ni har Yallaɓai sperm din mu suna active matsalan ba daga nan ba ne yanzu tun da an yi wannan an tabbatar da ba matsala za su yi focusing a kaina ne. Sai ta rubuta mini blood tests to look hormone levels. Na je na kai lap aka ɗibi jinina suka ce na dawo nan da kwana biyu domin karɓan result. Tun ina hanya na kira Yallabai na faɗa masa likita tace matakin farko ba matsala yanzu dai sauran gwaje gwajen akai na ne. "Alhamdulillah. Suma sauran in sha Allahu ba matsala." "In sha Allahu." Na amsa masa cike da yaƙinin hakan A satin Hauwa ta zo gida na ta yini ita da yara a bakin ta na ke jin Anty Zabba ta koma amman sai bayan Yaya Usman ya koma ni ko sai na ce" Ya fi mata. Amma ba ta gina gidanta ta bar ma wata shi saboda kishi ba." Sai dare Muttaƙa ya zo ya dauke su. Washegari gidan Halima na je na kai mata Atamfar da na da siya mata a Dija collection+234 903 661 7473 Domin kayanta ta na ba da su ne akan farashi sari mai sauƙi. Sai na siya rigar yaro ssi pampers da na je sai na ɗora mata 5k na ce nawa ne kuɗin kayan kuma daga Yallaɓai ne tana ta godiya a gabana ma ta kira shi tana yi masa godiya ya ce ba komai. Ina shirin tafiya sai ga Anty Bahijja wai sun zo nan kusa ne ganin gidan da ƙanwar mijin Ma'u za ta zauna shi ne ta biyo wajen Halima. Da gangan na yi ma Anty Bahijja taɗin bikin ina dariya na ce. "Anty Bahijja ashe biki gare ku ba gayyata." Sai ta kalleni kafin ta ce" Ba ni ya kamata na gayyace ki ba Ma'u ce." Ina mirmishi na ce" Ai fa ta gayyace mu muna nan zuwa." Na ga ta kalleni da mamaki amman sai ta shanye ta ce sai mun zo ni dai anan na barta na koma gida da wuri saboda yara. Ranar asabar da wuri na shirya daman na faɗa ma Yallabai tun kwanaki ya ce ya ba ni izini. Shi na bar ma yara a gida na ce in zai fita ya kai su Gwammaja wajen Nene, ni kuma Rahila ta kirani ta ce wai mu a haɗu a Ɗorayi ni kuma na ce ba zan koma baya ba tun da na san gida yayar mijin Ma'un ta taɓa rasuwa muka je gaisuwa na san iyayin Yaya Murja ce za ta ce a haɗu a gida a tafi gabaɗaya tun safe Rahila ke kirana nace ina dalili su yi gaba sai azahar zan taho.   Ban ma samu zuwa ba sai bayan azahar ganin na yi rana kawai Yallaɓai ya ce na jira mu fita tare shima Alhaji Mustapha ya gayyace shi ɗaurin aure sai da muka kai su Jidda Gwammaja sannan muka wuce Maitama in da gidan iyayen mijin Ma'u suke, ko da na je su Rahila sun jima da tsufa da zuwa Ma'u har da rumgumeni can na ga su Anty Bahijja Hajiya sama Hajiya ƙasa tun da mijinta shine babba a ɗakin ita mahaifiyar Alhaji Mustapha kuma suna ji da shi, shi ya sa ita ke faɗa aji, ina ta mamakin yadda take ba da umarni a dangin mijinta an ce so so ne amman son kai yafi ita ta samu dama tana yadda ta ga dama amman idanuwanta na kan wasu kar su ji daɗi a gidan mijinsu sannan kar su zama masu faɗi a cika a dangi amman ita gashi tana yarda ta ga dama. Ma'u ta karrama mu ba zan raina mata ba. Shema'u sune yan gaba gaba Ma'u mijinta ne babba a maza duk da ya na da yaya mace, amman itama Anty Ma'u sama Anty Ma'u ƙasa sai abin da ta ce. Ina ta mamakin ina abokiyar zamanta Hajiya Zainab? Sai can na ganta ta ci kwalliyarta da kin ganta kin ga wacce ta gaji arziƙi ba haye ba. Ita ba ruwanta gaskiya ba ta son hayaniya ma Ma'u kuma da ya ke yar bariki ne duk ta siye dangin Alhajin da siyasar ta. Yaya Murja sai da ta yada mini mganar wai sai yanzu na zo biki da rana. Ni ko na ce Yallabai na gida tare muka zo dashi shima ya zo ɗaurin aure. Shema'u kuma ba ta mini magana ba ta yi wani ɗan iskan ɗinki duk ya kama jikinta fuska da jiki sun sha mai ta yi wani fayau saboda in rama wulakancin da ta mini sai da na bari ta shigo ɗakin da aka saukemu sannan na kalleta ina faɗin "Shema'u ranar da muka sauke ki a gidan Nene Tariq ke faɗin wai kin karɓi lambar wayar Uncle Abba." Ba ita kaɗai ba gabaɗaya waɗanda ke wajen sai da suka kalleni daman na yi alƙwarin yadda ta yi min cin mutumci a gidan Rahila sai na rama. Ina mirmishi na ce" Wai kin roɗa ne? To gwara ma ki bi wani sarki shi Uncle Abba mata har ƴayan sarakuna daga Rano an yi masa talla bai ɗaga kai ba ballanta ke, na san dai zuwa yanzu kin ma san ya fi karfinki tunda lambar wayar ma ba tashi ya baki ta Tariq ne." Ƙur ta yi min da ido, ni kuma sai na gauraye fuskata da mirmishi Rahila na ta mini sigina na yi kamar ban gani ba har Yaya Murja mai baki ta kasa mgana. Shema'u kuma dakyar ta iya yaƙe kafin ta ce" Oh. Wannan daman na karɓi lambarsa ne saboda na ga ya yi min kama da wani sai daga baya na gane bashi ba ne, ni fa Sadiya ɗan'uwan mijinki ya yi mini tsufa kaf ma a dangin sa ba wanda zai iya dai dai da Shema'u.' Ta faɗa cikin danne yanayinta ina dage mata gira na ce"Da gaske? Cikin renin wayau Anty Aina ce ta yi mgana. "Sadiya ki bar mganar don Allah." Sai na yi dariya kafin na ce" An barta." Shema'u na yaƙe ta fice amman ni kaina  na san ta ji abin da ake ji in ka tozarta wani  a cikin jama'a sai da ta fita Yaya Balki ta ce ya aka yi ne na gyara zama  ina faɗa musu yadda aka ƙare. Yaya Balki na dariya ta ce" Wannan akwai ɗan jaka da rabi. Zai haɗa fada." Ina dariya na ce" Kaɗan daga aikin Uncle Abba kenan." Rahila ta ce ta gane shi ta taɓa ganin shi a gidana Yaya Murja ba ta ce komai ba sai daga baya ta ce" Ko ma dai menene ba kyau cin fuska a cikin jama'a." Kai tsaye na ce" Ba cin fuska ba ne. Ai naga nan duk ɗayan ne ko? Ta kalleni na kalleta sai kuma ba ta ƙara mgana ba. Ma'u ba ta ɗakin amman na san za ta ji labari Zaituna kam duk muna tare da ita amman ta ci abinci har da guzurin alale, ni da mangariba muka tafi ni da Rahila da Zaituna Yaya Murja ta ce sai ta kai Amarya amma Yaya Aina da Yaya Balki ban ji suna zencen ba amman dai can muka bar su. Na dawo gida da Waina da sinasir Ma'u ta matsa dukkanmu sai da muka taho dashi Shi na ci na sha ruwa tunda mai siga ne sai dare Yallaɓai ya je ya ɗauko su Jidda suka dawo gida. Su sun ci abinci Yallaɓai ne na dafa ma Indomie da ruwan tea ya ci kafin ya kwanta. Washegari Lahadi da asuban fari sai ga wayar Tariq Allah ya yi ma mijin Gimbiya rasuwa. *Janafty* *TURKEN GIDA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Eaman ScholarSphere. Where ideas Take Shape. WHAT WE DO. ASSIGNMENT PRESENTATIONS. ARTICLES PROJECTS. BOOK AND MANY MORE. CANTACT US THROUGH. 02347067793152 MOTTO: "Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures" *🅿️16* Mutuwa ɗaya ce haƙiƙa na tausaya mata ganin ko shekara biyu ba ta rufe da auran ba. Yallaɓai a ranar suka tafi Abuja tare da Uncle Abba da Nene, da Anty Maimuna Anty Bahijja za ta taho daga baya. Sai Hajiya iya Maman farko kaɗai aka bari a gida. Can suka kwana Tariq da Farida daga kaduna suka tafi. Ni kuma ranar litini na je ganin likita sai ranar na je lab na karɓo sakamakon test ɗina na kai mata shima ta ce lafiya lau ba wata matsala. Sai muka je matakin gaba na A transvaginal ultrasound. Ta ba ni nan da kwana shidda na dawo. A ranar su Yallaɓai suka dawo daga Abuja kwanan su ɗaya amman an bar Anty Maimuna acan tare da Nene da Hajiya Kaltume sai an yi uku za ta dawo. Ranar talata muka je Abuja gaisuwa. Ni da Hauwa da Munnira sai Jamila da Hindatu, Hafsat daman ta na can Abujan ne, sai Mimisco da direbanta ne ma ya tuƙa mu. Mun iske gidan Gimbiya cike da yan uwa da abokan arziƙi. Kaf yayyenta mata da matan mazan suna nan, Hajiya kaltume da Nene ne tare da ita a matsayinsu na manya. Har Sameena a can na ganta ta ce tun ranar da da aka yi rasuwar ta zo sai an yi bakwai za ta koma. Tariq ma na nan shi da Farida da yara. Amman dai shi ya ce min da zaran an yi sadakar uku zai koma gida. Ba Gimbiya ke bin Tariq ba akwai wata mace sannan ita a shekaru ba za ta gaza 33 ba ko na girmeta bai wuce da shekara ɗaya ba. Lokacin da nake yi mata gaisuwa ta yi matuƙar ba ni tausauyi ta yi kuka idanuwanta sun shige ciki, ba ta mgana sai dai ɗaga kai ba ta ci ba ta sha sai an yi da gaske ta ke tsakura da kuma ta ci sai ta amayar dashi. Ta rame sai farin fata da dogon hanci gabaɗaya sai ta bani tausayi har araina ina yi mata addu'an Allah ya ba ta dangana. A bakin Sameena na ke jin Alhajin na gidanta ne lokacin da ciwon shi ya tashi. Ashe yana da ciwon hanta a Egypt ya ke ganin likita a daran su ka kai shi babba asibiti a nan Abuja da niyyar kafin a fita dashi waje, da asuban ranar Allah ya yi masa rasuwa. Allahu akbar. Allah ka sa mu yi kyakyawan karshe. Mun je gidajen duka matan shi mun yi musu gaisuwa tun da dukkansu suna anguwa ɗaya ne asokoro. Kuma gidajen su ba nisa bai wuce ka ga gida uku a tsakani ba. Yana da manyan ƴaƴa ba shi da ƙananu da Gimbiya ta haihu ne zai iya samun yara. Ba kuma yaro ba ne don ko da ta aure shi ya yi shekara 60 Allah na tuba a lokacin har ina ma Hauwa gulma me za ta yi da tsoho mai mata da ƴaƴa haka? Ashe zaman ma ba mai tsaho ba ne. Duk da na zo garin da Yaya Auwal ya ke ban je ba. Saboda gaisuwa muka zo kar a ce daga zuwa ina yawo. Sai dai na kira Lailan na faɗa mata mun shigo garin, sai ta ce in da sarari za ta shigo ta yi musu gaisuwa. Yallaɓai na bari, a gida shi da yara amma mun yi mgana ya ce gobe ranar uku za su dawo sai na ce kawai in sun dawo daga makaranta ya faɗa ma Salisu ya kai su gidan Rahila tunda ya ce za su kwana washegari sai a haɗu gabaɗaya a koma kano. Shi ya sa na kira Rahila na ce, za a kawo mata su Jidda su kwana a wajenta kafin mu dawo tun da Salisu ya san gidanta. Saude kuma Yallaɓai baya nan ban taɓa kwatantan barin ta ita kaɗai da yara a gida ba. Duk anan gidan Gimbiyar muka kwana. Abinci sai dai a kawo shi a dafen shi komai ga shi. Saboda ya na da kuɗi dan kwangila ne ya tara abin duniya kuma a baya ya yi siyasa. Washegari ranar da aka yi sadakar uku da wuri su Yallaɓai suka iso shi da Uncle Abba da su Kawu Sa'adu sai Anty Bahijja. har cikin gida kuma sun shigo an yi ma juna gaisuwa. Ni ina can ɗakin da muka kwana ba mu haɗu ba sai can yamma ma. Mun dai yi mgana ta waya da daddare kuma sun ƙara shigowa, a bakin Munnira na ji ta na faɗin wai Tafida ne ma ya matsa ma Gimbiya da lallashi har ta amince ta sha tee ɗin da yawa kuma sannan sai yau aka ji ta taɓa buɗe baki ta yi mgana amman ga

Chapter 23 of 31