Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yan gidanmu na kanta kamar sun ga wata sabuwar hallitta. Ina ji Alhajinmu na kora bayanin wace ce Ma'u a garemu gabaɗaya. "Ɗiyar ƙanwata ce Hasiya. Mahaifinta ya rasu ɗan nan garin Yashe ne. Ta dawo hannun Hajiya da zama shi ne da na je na ganta na taho da ita za ta zauna da mu har abada." "Allah ya taya mu riƙo Alhaji." Gwaggo da Mama har suna haɗa baki wajen faɗa. "ƴar uwan ku ce Ina fata za ku kalleta a matsayin jini ɗaya." Yaya Abubakar ya amsa da in sha Allahu.   Yaya Murja ta yi karaf ta ce"Muna son ta Alhaji. Ga ƙawa ma na yi mata Rahila." A lokacin ƙankance ido na yi ganin ta haɗa hannun Rahila da Ma'u waje ɗaya. Saboda sun zauna daman a kusa da juna ne. Ita kuma Rahila sai mirmishi take yi a yayin da Ma'u ke kallon kowa da idanuwanta. Tun kafin zuwan Ma'u daman ni da Yaya Murja ba ma zama a waje ɗaya saboda ta na da faɗa ni kuna ina da baki ta bakin ta ta ce ba ni da kunya manya na mgana ina saka musu baki. "Har da Dubu ma. Saboda na ga za su yi tsara ya sa na samu karfin gwiwan ɗauko Asma'u." Alhajinmu ya faɗa sannan idanuwansa suka fara laluɓena sai ya ganni a can baya ina zaune. "Dubu..'     Ya kirani kamar yadda ya saba kirana sai na amsa. Sai ya ya fito ni da hannu na taso na zo gaban shi. "Dubu ba ki ga yar'uwan ki Asma'u ba ne? Na juya muka kalli juna ni da ita sai na kauda kaina kafin na ce" Na ganta." Ya na mirmishi kafin ya ce"To ga ta nan ke da Rahila na bar ma Amanan Asma'u. Ku yi ƙawa da ita kun ji ko? Ni dai kai na ɗaga Rahila  ce ta amsa har ta na cewa" Alhajinmu a saka ta a makarantar mu don Allah" Sai kawai na ji Alhaji na faɗin "In sha Allahu tun da daman Hajiya ta ce ta gama firamari sai na saka ta a tare daku har islamiya ma" Sai kawai Rahila  ta rumgume Ma'u tana murna. A lokacin Yaya Abubakar ya kalleni ya ga na haɗe rai sai kawai ya kalli Ma'u yana faɗin" In Sadiya ta yi miki wani abu kar ki raga mata ki rama kin ji ko? Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya yana nuna ni. Ana ta dariya har Alhajinmu. Amman ni ban yi dariya saboda ni ban ɗau abin da wasa ba. Mun ƙara kallon juna ni da Ma'u na wani lokaci sannan kowa ya ɗauke kansa. Yaya Murja har tana faɗin" Wallahi kuwa. In Sadiya ta ga sakenta ai ta shiga uku." Mutane biyu da suka fara bin bayan Ma'u tun kafin tafiya ta yi nisa. Suna faɗa mata abu mara kyau game dani.   A wajen kwanciya ma na ga abu. Mu uku muke kwana a karamar katifa a ƙasa ni da Rahila da Amina. Amman sai Rahila ta jajibo mana Ma'u ban iya shuru ba sai da na ce" Rahila a ina za ta kwanta? Ko ke za ki kwana a ƙasa ki bar mata wajen ki? Daga mgana sai aka ga laifina. Kawai sai Yaya Murja ta fara zagina su suna babban gado ita da Yaya Balki. Gwaggo sai da ta shigo ta raba faɗan da har Yaya Murja ta ce Ma'u ta dawo gadon su ta bar mun katifar sai Gwaggo ta ce Amina ta koma wajen su Yaya Murja mu kuma mu kwanta mu uku ban ji daɗin hukunci Gwaggo ba amman ba ni da mafita ni ta kafafunsu na kwanta Rahila na bari da kwanciya filo ɗaya da Ma'u.   Tun daga wannan ranar Ma'u ta zama yar gida ko na ce tafi ma wasu yan gidan sakewa tun da tama da masu tsaya mata. Da ya ke Rahila tafi mu girman jiki ni kuna siririya ce ina da tsawo ba can can ba amman yanayin fasalin jikin mu ɗaya da Ma'u. Mama ta saka na tsinta kayana na ba ma Ma'u saboda sune za su yi mata kafin Alhajimu ya siya mata wasu kayan saboda wanda ta zo da su duk sun yage an zubar. Sannan Yaya Murja ta yi mata tsifa suka rakata gidan kitso. Komai fa nuna mata suke yi ga shi ba ta cin Tuwo sai dai in tuwon shinkafa ne miyar ganye. Ba ta cin dambu ba ta shan fate tsirfa dai kala kala kuma an ɗaure mata gindi. Duk ranar da aka yi ɗaya daga cikin su sai dai a siya mata wani abun ko kuma a dafa mata wani abun ta ci ita yar gata. Islamiyarmu aka fara saka ta. Sai da aka yi albashi Alhajinmu ya saka ta a makarantar mu ta Goverment Girls Junior Secondary School Diso. Kuma abin mamaki da irin sunan da muke amfani da shi. ASMA'U SULAIMAN YASHE. lokacin da Yaya Abubakar ya kai ta makaranta za a saka sunan Babanta mahaifi sai ta kalli Yaya Abubakar ta na faɗin"Ba sunan Alhajinmu za a saka mini ba? Shi kuma Yaya Abubakar bai yi shawara da kowa ba ya sanya mata sunan Alhajinmu wanda dashi ta ke alfahari har gobe kuma har abada.   Sai da ya dawo gida ya faɗa Alhajinmu kuma bai ce don menene ba. Ba aji ɗaya aka sanya mu ba mu muna A ita kuma ta na B. Anan ne ta haɗu da Shema'u da daman halinsu yazo ɗaya. Rahila ce ke wani rawan jiki akan Ma'u amman ni sai na iya kirga ma maganarmu yadda ba ta mini mgana nima ba na yi mata kowa harkan gabansa kawai ya ke yi. Tun kafin kowa ya lura ni na fara lura da makircin Ma'u saboda ni ke kula da duka motsinta a gaban mutane saliha ce sai a makaranta in ka ganta tare da ƙawarta ba ka ce ita ce ba. Ban taɓa nuna ta a makaranta na ce ƴar uwata ba ce saboda ni ba ni ma da ƙawaye Rahila ce kaɗai na ke tare da ita. Amman ita Rahila mai jama'a ce kowa nata ne ni kuma ko ana son ƙawancen dani ba na ba da fuska ki gaji da naci ki haƙura ba islamiyan ba bakon ba.   Sai ya zamanto komai za a yi mana a gida guda uku ne tare da Ma'u. Ta zama yar gaban goshin Yaya Abubakaar shi ke koya mata karatu baya shigowa hannun rabbana sai ya yo mata tsaraba. Sannan Yaya Murja yadda take ƙaunar Ma'u ko ni yar uwanta ba ta sona haka. Alhajinmu ma gata yake nuna mata shi da su Gwaggo. Tun ina mamaki har na daina na sadakar da Ma'u ta samu tasiri mai yawa a zukatan yan gidanmu. Baaba Hasiya ta zo ta duba Ma'u bayan ta yi wattani huɗu a tare da mu. Lokacin tun ba mu gama zama cikakkun mata ba na ji Baaba na yi ma ƴarta huɗuba da cewa" Kin samu rayuwa mai inganci Asma'u. Ki kwantar da kanki ki yi ma Yaya Sule da Gwaggo biyayya domin ita ce matar Fari. Wancan Rukayyar ba ta gabana. Sannan ki samu cikin yaran nan na Yaya Sule  Maza wani ya yaba dake sai ki yi auran ki kin ji ko?   Ina laɓe ina jin su kuma ba niyyata na yi laɓe ba na zo shiga ɗakin ne na ji suna mgana na tsaya. Ban ankaraa ba sai ga sun fito. Baaba Hasiya daman in dai ta zo a ɗakin Gwaggo ta ke sauka ba ta sauka a ɗakin Mama na taɓa jin tana faɗa ma Alhajinmu a wani zuwa da ta taɓa yi wai Mama mai farar ƙafa ce tun da ya aure ta al'amarinsa ya ja baya tun da ga Lokacin na san ba ta ƙaunar Mama kuma mun taɓa zuwa Yashe a ɗakin Hajiya ta yi ma Mama rashin kunya har Hajiya Dubu na yi mata faɗa ina ƙarama a lokacin amman na ƙasa mantawa da abin. "Ke lafiya? Ko laɓe kike yi mana" Baaba ta katse ni tana hararata. Sai na kalleta kafin na kalli Ma'u sai kawai na ga ta yi mini wani kallo kafin ta ce" Daman Baaba ba ta sona. tun da na zo gidan nan." Sai kawai na saki baki ina kallon Ma'u Baaba kuma ta fara tafa hannu ta na faɗin" To ai sai ta kore ki. Shegiya mai mugun hali to Asma'u zama daram in ji mai naguda."   Maganarta ya jawo hankalin su Mama da Gwaggo Ranar Lahadi kowa na gida. Baaba sai ta fara kuka tana faɗin labe ta kama ni ina yi musu ta na fitowa ta ganni shine ta fara min faɗa na yi mata rashin kunya har ina zagin Ma'u ina cewa ta zo cin arziƙi ba gidan ubanta ba ne"   Ban mantawa maganar har sai da ta kai kunnen Alhajinmu. Yaya Murja har ta na marina saboda ta dunguremin kai na ce Allah ya isa ta mare ni. Yaya Abubakar ya saka ni kneel down ban ji ba ban gani ba. Ni kuma ban ƙaryata su ba amman na yi ma Ma'u wani kallo ganin tana yi mini dariya. Alhajinmu ya yi min faɗa fata fata abin da bai taɓa yi min ba yana ƙara jadadda mini Asma'u ba bare ba ce ƴ'a take kamar kowa.   Ina ji ina gani Ma'u ta zo gidanmu tana mini iko. Sai ta takale ni da faɗa ni kuma ban gane makircinta ba sai na tanka ta shikenan in aka zo jin ba'asi sai ta marairaice ta fara kuka tana faɗin na ce mata in ta gaji ta koma gidan ubanta kafin Ma'u ta rufe shekara a gidanmu har gwammatina a wajen Alhaji ta hambarar da shi da makircinta kowa ba ya faɗin abu mai kyau akaina ko abu ya haɗamu sai ace Ma'u ce mai gaskiya ni ce mara gaskiya. Har Rahila ce mini ta ke yi" Don Allah Sadiya ki daina takurama Ma'u a cikin gidan nan. Ban ga abun da ta tare ki miki ba." Itama goyon bayan Ma'un take yi kenan daga lokacin na fahimci gwara na miƙe na kwaci kaina domin ba ni da mai goyon bayana ko Mama ce na je na faɗa mata sai ta ce ni ce ba ni da gaskiya ba mai cewa a tsaya a bincika. Mutum ɗaya ne bai taɓa goyin bayan Ma'u ba shi ne Yaya Hamza lokacin da ya dawo hutu mun taɓa wani dambe da Ma'u akan ina zaune a ƙofar ɗakin mu ina gyaran jakar makaranta ita kuma ta fito wanka. Ga hanya na bata amman da ya ke makira ce sai da ta ga ba kowa a tsakar gidan sai ta takani za ta wuce ni kuma na miƙe na jawota ta baya wajen ta tsaya sai kafartaa ta turguɗe sai ga ta a ƙasa amman yarinyar nan sai ta fasa ihu ana taruwa ta ce ni na saka mata kafa ta faɗi. Lokacin an saka ranar auran Yaya Murja ita ta saka mini hannu Yaya Hamza ya tsawatar   ashe ya na daga can ƙofar ɗakinsu ya na ganin abin da faruwa.   "Yaya Hamza Sadiya ta ɗora ma  Ma'u karan tsana tun daga ranar da Alhajinmu ya kawo ta gidan nan saboda ta ganta ba ta son tashin hankali."   Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce"Ita ta ce miki ta tsane ta? Ya za a yi ta tsane ta sai dai in akwai abin da take yi mata ne wanda ba ta so." Yaya Murja za ta yi mgana ya ɗaga mata hannu kafin ya ce"Ki daina ɗaukan bangare ɗaya a matsayinki na babba ki zama adala. Ina  can daga ƙofar ɗaki na ga abin da ya faru. Ke ce ba ki da gaskiya ta ba ki hanya amman saboda tonon faɗa kika takata ta miƙe ta jawo ki sai aka yi rashin sa'a kafarki ta turguɗe kika faɗi ko ba haka aka yi ba? Ya faɗa ya na tsare ta da ido. Duk rashin kunyarta sai ta sadda kai ƙasa ta kasa mgana shi Yaya Hamza akwai tsare gida ba irin Yaya Abubakar ba ne shi kamar wani mace yake jin kansa. Kai tsaye ya ce Ma'u sai ta bani hakuri dolenta kuma ta bani a kausashe ya kalleta kafin ya ce" Kar ƙi kara takalanta. Ni na san Sadiya ba ta faɗa ba a taɓa ta ba. Ku zauna lafiya da junan ku.'   Sai ta gyaɗa kai. Ni kuma sai ya riƙe hannuna zuwa ɗakinsa yana lallashina. Tun daman akwai fahimtar juna a tsakanimu. Ina kuka ina faɗa masa makircin Ma'u sai abin ma ya bashi dariya cikin dariyan ya ce" To ke ma ki riƙa ramawa mana. Ki daina bari ta na samun galaba a kan ki." Shi mamaki ya ke yi ƴar Ma'u ta iya makirci tunda ya ganin ma idanuwansa.   Zaman Yaya Hamza a gida sai na samu lafiyan Ma'u. Tsoron shi take ji ko maganarsa ta ji yanzu za ta shiga taitayinta. In ya na waje ba ta iya wani motsin kirki har sai ya gama hutun shi ya koma tun kuma daga lokacin nima na gane in ta yi mini abu na rama kafin ta kai ga  haɗa min makircin ni Na haɗa mata amman ba ya tasiri tun da ni daman na yi ƙaurin suna sai ya kasance Ma'u ta riƙa cin nasara akaina ko a makaranta in na ganta tare da ƙawayenta suna nuna ni suna dariya barin ma wannan shegiyar ƙawar tata mai kama da biri Shema'u na tsane ta har acikin raina.   Mun je Yashe sau ɗaya bayan zuwan Ma'u gidanmu. Mun yi sati ɗaya har gidan Babanta mun je sai na ƙara raina mata kamar ma ba sa son ta. Domin ba a wani tarbe mu ba shi ya sa ita kanta ba ta zauna ba. Sai da muka dawo kano sai ita da Rahila suka shirya suka tafi kura in da Baaba ke aure ni kuma na ce ba zan je ba. Daga kuma lokacin in faɗa ya haɗa mu da Ma'u sai na yi mata gori da cewa in ta ji na dame ta Za ta iya komawa gidan tsoho a ƙauye nan dai gidan Ubana ne kuma ba ta isa ta hanani sakewa ba saboda na daina tsoro ko a gaban waye za ta kai ni ta fahimci makircinta ba ya yi mini aiki sai ta koma itama ramawa. Na samu sauƙi Yaya Murja ta yi aure a shekaran 1996. Yaya Balki kuma ba ta kai Yaya Murja zafi ba.    Sai da bikin Yaya Murja sannan na fahimci Ma'u ta ɗau huɗubar Baaba saboda Yaya Hamza ya dawo gida ya gama babban sakandiri shi da Yaya Abubakar duk suna gida jarabarwarsu ba ta yi kyau ba sai sun sake yi. A lokacin na fahimci in dai ta gan shi yanzu za ta fara gyare gyare lokacin muna Ajin biyun ƙaramar sakandiri ne amma har Ma'u ta san ta yi ma namiji karairaiya. Abin da na fahimta kamar tunaninta na kan Yaya Hamza shi kuma Yaya Abubakar tunaninsa na kan Ma'u ni ce na fara lura da ita da kuma abin da ke faruwa saboda ni ce daman idona ke kan duka motsinta.   Shi Yaya Hamza bai ma san ta na yi ba. Namiji ne mai tsare gida ba ya ɗaukan reni ba shi kuma da yawan sakewa mutane shi kuma Yaya Abubakar yana da sanyi ga arhan dariya shi fa kowa na magana dashi ga surutu ba kamar Yaya Hamza ba. Ga aji ga tsare gida mgana ɗaya bayan ɗaya cikin wayewa shi ya sa na ke ƙaunar Yaya Hamza na kuma saka acikin tunanin irin mijin da zan aura mai hali irin na Yaya Hamza ne sannan na ji a raina ba zan iya auran mai hali irin na Yaya Abubakar ba. Shi daman Yaya Auwal da shi da babu a gidan duk ɗaya. Sai a yi abu goma bai sani ba yana da ƙokari ko yau she yana ɗaki yana karatu in ba na boko ba na arabi. Kuma shi yana da ƙyaluwa ba kasafai ya ke saka baki a wasu abubuwan ba. Shi sai a shekaran ma ya zana jarabawar shiga babban sakandiri. *TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 09069067488. 08032773332. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *Janafty* *TURKEN GIDA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)* I just published "Page 12" of my story "TURKEN GIDA."::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68237857847ebcbfe6d205fe *🅿️12* Sulaiman Abubakar Yashe. Shi ne cikakken sunan Alhajinmu. Inkiyan Alhaji da ya samu ba yana nufin ya je ya sauke farali ba ne.   A zamanin baya in mutum ya baro ƙayensu zuwa garin Kano a matsayin jihar ta cibiyar kasuwanci sai a riƙa tunanin ai ka zama Alhaji ballatana in ka samu rufin asiri to mutane da yawa kan iya sakaya sunanka da Alhaji. Sunan Alhaji ya bi sa har matansa da haka suke kiran shi har muma ƴaƴansa muka wayi gari da sunan a bakin mu. Alhajinmu haifaffan ƙauyen Yashe ne. Ita kuma ƙauyen Yashe tana cikin ƙaramar hukumar kusada. Ita kuma ƙaramar hukumar kusada tana cikin yankin Jihar katsina ce. Garin kusada manoma ne da makiyaya shi ne sa'arsu da shi suka yi kuɗi har suka arzuta wasu ma. Mallam Abubakar ya kasance kafin rasuwarsa matan auransa biyu Halima(Hajiya Dubu) da Balkisu. Kuma ya rasu bayan Balkisu ta riga su gidan gaskiya. Sai ɗawaniya da nauyin komai ya koma kan Hajiya Dubu. Kafin rasuwar Balkisu ƴa'ƴanta biyu ne kacal ta haifa sauran duk sun koma Sule da Hasiya. Sai riƙon su ya dawo hannun Hajiya Dubu da ta riƙe su tun suna kañana ba nuna bambamci. Ita Hajiya Dubu ƴaƴanta uku ne biyu maza mace ɗaya. Akwai Aminu sai Muhammad sani sai ƙaramar su Aina'u wacce ta yi aure sai ta rasu wajen haihuwa. Sulaiman a cikin garin kusada ya gama sakandirinsa daga nan ya yi tunanin haurawa garin kano domin ya cigaba da karatunsa na boko. tun da ya samu na addinin har matsayin sauka. Lokacin ba kowa ke saka ɗan sa a karatun boko ba amman shi Sule da kansa ya kai kansa makaranta saboda ya na sha'awar karatun sosai. Ya tafi kano neman ilimi bayan ya saida gonar da ya gada a wajen mahaifiyarsu. Ashe dalilin haka Kano za ta zame masa mafaka da sillar zama abin da ya zama. Diploma ya fara yi a can kano cikin ikon Allah kuma sai ya samu aiki a NEPA hukumar wutar lantarki na jihar Kano tun da lokacin ana iya ɗaukan masu takardan sakandiri aiki tun da tana da daraja. Samun aikin shi a wajen shi ya inganta masa rayuwa sannan gefe ɗaya ya na kiwo a gida ga Noma Aminu da Sani duk ba su yi karatu ba suna noma sannan suna kiwo.  Ya auri matarsa ta farko Maimuna yar nan garin Yashe ne maƙota suke ma. Sun yi aure tun shekarunsa ba su rufe talatin ba itama ta ƴar yarinya a lokacin ta fara zama a yashe kafin ya kama mata haya a anguwa uku ya ɗauketa suka koma can suka fara gina rayuwarsu. Farkon rayuwar ya fara ta ne da Maimuna(Gwaggo) sai dai kamar auran naTa ya zo masa da tarin buɗi. A shekarun biyun da suka yi aure ya yi noma kuma ya samu amfanin gona sannan ya saida kiwon shi ya siya wasu alherai sai bin sa suke yi da buɗe. Sannan ga albarka samun ƙaruwa ta ɗa Namiji wanda ya ci sunan kakanshi Abubakar. Bayan shi ba daɗewa ta sake haihuwan wani namiji aka sanya ma sa suna Hamza. Maimuna na da cikin Aina'u Sulaiman ya ƙara aure da Rukayyatu yar kano ce. Sun haɗu kuma Allah ya haɗa zukatansu waje ɗaya. Ya aure ta kuma Maimuna ta karɓeta hannu bibbiyu a matsayin abokiyar zama ba kishiya ba. A ƴan'uwansa ba wanda ya yi mgana kan ƙarin auransa sai Ƙanwarsa Hasiya balle da ta ga tun bayan auran shi kenan abubuwa suka fara lalacewa ko Sulaiman ya yi noma baya samun komai sai kiwon sa da ɗaya da ɗaya suna ta kasawa wasu ma sai dai a tashi a ga gawa shi kenan Hasiya ta ce Rukayya ce da ya auro mai farar ƙafa sai da Hajiya Dubu ta tsawarta mata. Lokacin Hasiya ta yi aure anan garin Yashe amman dai Allah bai bata haihuwa da wuri ba. Ana ta raɗe raɗen wanda ta aura ne baya haihuwa kwata kwata sai da aka raba auran ta sake auran wani saurayi Hashimu shima dai kusan shekaru huɗu shuru ba wani labari. Cikin wannan halin  sai kuma a ka fara rasa wasu abubuwan na dukiya. Sai kuma aka yi ta samun ƙaruwa Gwaggo ta haifi Murja ita kuma Mama ta haifi namiji an saka masa suna Auwalu. Sai dai bai yi sati biyu ba Allah ya yi masa rasuwa. Sun tashi daga gidansu na anguwa uku ya kama wani a gandun albasa. A can aka haifi Balki da ta ci sunan kakarmu. Sannan Mama ma ta sake haihuwan Namiji sai aka maida mishi sunan wanda ya rasu Auwal. A yadda Gwaggo ta faɗa mana sun samu cikin mu a Gandun albasa ita da Mama amman kuma ba su haife mu a wannan gidan ba sai a gidan da Alhajinmu ya sake kama musu da ke Fagge shi ya fi girma ne sannan ga iyalai sun fara yawa. Kuma su Baba Aminu suna kawo masa ziyara ba shi da wajen safkarsu.   A yadda labari ya zo mana a bakin Gwaggo. Tsakani na da Rahila kwana arba'in ne. Rahila aka fara haifa, ni kuma sai ranar da Rahila ke cika kwana arba'in sannan aka haife ni. Ni na ci sunan Hajiya Dubu ita kuma Rahila ta ci sunan marigayiya mahaifiyar Gwaggo da ta rasu ba daɗewa a lokacin. Tsakani na da Amina ko shekara biyu bai kai ba shekara ɗaya ne da wattani daga kuma kan Rahila Haihuwa ta tsaya ma Gwaggo. Amman Mama ta yo auta Abdulsalam ana kiran shi Datti. A ƙiyasu mu goma ne cif a gidanmu. Ta bangaren Mama mu huɗu ne ta bangaren Gwaggo kuma su shidda ne sau zuwan Ma'u da muka zama mu goma sha ɗaya. Mun ta so cikin gata saboda Alhajinmu ya na ta samun ƙarin girma a wajen aiki sannan kuma har gobe bai daina noma da kiwo ba. A gidanmu kowa da halin shi misali kamar ni ina da tsiwa sannan ga taurin kai ina da nacin magana. Za ka ganni kamar ban san me na ke yi ba nan kuwa ina ankare da motsin kowa tun taso wata Allah ya yi ni da son jiki har suna Mama ta saka min Sadiya yar laushi. ina da sakin jiki amma ga ƴan'uwana ba ni da sakewa da mutane ba kuma tsoro ba ne kawai ni haka Allah ya halliceni ban cika son mutane ba sosai shi ya sa bayan Rahila da muka yi damben kuruciya tare ban taɓa wata ƙawa ba. Sabanin ita Rahila mai sanyi ce ga hakuri sannan tana da faram faram da mutane kuma kowa na ta ne shi ya sa in yara sun zo gidanmu tabbaci wajen Rahila suka zo ni ko mutm ya so mu saba ba na barin haka ta faru sai na janye jikina. Kamar ta bangaren Yaya Abubakar da Yaya Hamza ne. Shi Yaya Abubakar ba shi da zafi shima dai akwai sakewa da mutane ga surutu saɓanin Yaya Hamza da bashi da wasa ƙwata ƙwata. kamar misalin Yaya Auwal ne shi kuma wannan ɗan i dont care ne. Abu goma za a yi a cikin gida bai ma san an yi ba shi fa rayuwarsa kawai yasani sai ko in ya ji yunwa ya ci abinci. Yaya Aina itama ba ruwanta ba ta da faɗa amman Yaya Murja ta fi kowa shegen shisshigi da shiga abin da ba ruwanta ga sa ido sannan ba ta da haƙuri kamar zawo ta ke. Shi ya sa ba mu taɓa shan inuwa ɗaya da ita ba ita faɗa ni kuma rashin kunya. In aka duba Amina da Datti. Gwara ma Datti ita Amina miskila ce irin Auwalu sha'ani ko an saka su aciki ma ɓata lokaci ne abu nawa zai faru a cikin gidan suna nan

Chapter 17 of 31