Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na ce"Gidanmu muka yini ranar asabar, lahadi kuma na ce su tsaya saboda shiryen shiryem makaranta, su goge uniform da homework lokaci ya ƙure shi ya sa sai na ce bari su bari wannan satin da sun dawo makaranta ranar jumma'a zan tsa yar mai mashin ɗin su, sai ya kai su in sha Allahu."   Miƙewa ta yi, lokaci ɗaya ta na rayata jakarta, kafin ta kalleni tana faɗin"Kina  da ƙulafucin ƴa'ƴan Sadiya. To ki yi zuciya ki sake haihuwa mana. Amman ace kamar gidan Yusuf shi da ke son yara a ce ƴaƴa biyu kaɗai gare shi kamar ba shi da wani zaɓi, yanzu in muka ce ya ƙara aure sai ki ji haushin mu ko? Ƙuramin ido ta yi saboda tana so ta ga yadda zan yi, sai ni kuma na nuna mata har yanzu ba ta gama sanin wacece Sadiya ba.   Dariya na saki har ta na fidda sauti kafin na ce" Jin haushi kuma Anty Bahijja? Ai aure umarnin Allah ne shi ya ba su damar ƙarawa, wallahi tallahi na sha faɗa ma Yallaɓai in zai ƙara aure ya ƙara domin ni ba ni da matsala da ƙarin auransa tun da ba akaina za ta zauna ba, kuma ko ta zo sai dai ta zo a ta biyu kin ga kenan ko ya ya dai na ke na amsa sunan Turken gida. Haihuwa kuma ta Allah ce, in ya tsara min ƴa'ya biyu zan haifa shike nan, kuma ni ba zan yi ma Yallaɓaina baƙin cikin ya ƙara aure ya sake haihuwa ba, duk wani abu da ya fito daga tsatson Yusuf abin so ne a wajena."   Kamar ba ta yarda da magana ta ba, domin sai ta ƙara kallona take yi, tana mirmishi, kallonta na yi domin har ta mirmishinta irin na Yallaɓaina ne. Ganin ta kama hanyar barin falon ya sa na miƙe na bi bayanta dai dai lokacin da na ji ta na faɗin"Ke fa kika tsaida haihuwan da kanki Sadiya kin ga ko, ko auran Yusuf ya ƙara bai yi miki rashin adalci ba." Ina bin bayanta na yi mirmishi amman ban yi magana ba.   Ni ce har haraban gida na rakata, ina ce mata"Ba ki zo da mota ba ne Anty Bahijja? Kai tsaye ta ce" Tana waje." Sai na gyaɗa kaina fulawowin gidan ta bi da kallo kafin ta ce" Fulawowin nan sun ƙara ma gidan nan kyau fa." Na biye mata ina cewa" Sosai ni ko ma da farko ban so Yallaɓai ya saka su ba sai bayan sun fara girma sai na ga sun yi ma wajen aiki."   Wani kallo ta yi min ta cikin likabinta  da ta saki kafin ta ce"To gidan ki ne? Da sai kin zaɓi abin da zai saka ma gidan shi? Dariya na yi kafin na ce" Gidana ne mana Anty Bahijja, ko kwatance za a yi gidan Sadiya za a ce ko Maman su Jidda, kamar yadda kema a ke kwatancen gidan mijin ki da gidan Malama Bahijja." Kallona ta yi ido cikin ido ni ko sai na waske ina dariya.   Sai ta bige da yin mirmishi kafin ta ce"kin samu dai kan Yallaɓai ta bakin ki kina yadda kika ga dama, to tunda ya yi miki gida saura mota ko? Ina riƙe baki na ce"Ni Sadiya? Ai ko kuɗin ya samu kuka ji zai siya mino mota hana shi za ku yi Anty Bahijja" Kai tsaye Ta ce"Tabbas. Gwara ya yi aure shima ya tara zura'a  kar ki manta a gidasu mata huɗu cif ne da kimanin ƴaƴa 21 ban da waɗanda suka rasu." Ni ko da gayya na ce"Allah ya bashi kuɗin da zai wadatamu. Sannan sai ya yo auran miye a ciki?   Anty Bahijja ta san halina ko Hajiya Maimuna ba na raga mawa, in suka faɗa min cuta zan faɗa musu mutuwa, duk da suna yayyen mijina, saboda suna da ƙananun maganganu sannan sun sakama rayuwata ido, a wasa ne za su yi ta faɗa minI magana Nima ko a wasa na ke maida musu martani. Anty Zuwaira ce kaɗai ba haka a tsakanin mu saboda ita tana kama girmanta, da yake yar boko ce ga isa da gadara ba ta da ma lokacin tsayawa ƙananun maganganu. Har makaranta private nata na kanta gare ta, sannan ita ma ta kai matsayin Principal a wata makaranta ƴan mata ta cikin gari, sannan uwa uba mijinta a Mininsty of education reshen jihar kano ya ke aiki.   Ban bar jikin get ba sai da Anty Bahijja ta shiga motar ta ta tafi, ina ɗaga mata hannu bayan na ce ta gaida su Suhailat, sannan na rufe get ɗin na koma cikin gida a falon da muka zauna na koma na sake zama. Duk a cikin maganganun Anty Bahijja magana ɗaya ta fi tsayamin a rai. Wai da ta ce ni na tsaida haihuwa da kaina, tuni na ji kaina ya fara sarawa abin nan mai ɗaci ya tokaremin a cikin kirjina ya kasa wucewa, wani tuƙiƙi kawai na ke ji kamar zan shiɗe. Har yau na kasa aminta da ba Yusuf ba ne ya je ya kwance min zani a kasuwa a gaban ƴan'uwan shi ba, tunda ya na da wani hali na faɗi ba a tambayeka ba, sai sai Ma'u ita ce abin zargina na biyu saboda tana auran yaron mai bi ma Mijin Anty Bahijja ma'ana suna aure a dangi ɗaya duk wasu maganganu da suke samu a kaina ta bakin Anty Bahijja ne, ko sunan Sadiya yar laushi da ke bakinta ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba daga baƙin Ma'u ne.   Wannan yarinyar tun zuwanta gidanmu na san annoba ya zo cikin zuru'armu, idanuwan kowa ya rufe sun kasa gane tsabar makircin Ma'u da ta yi  gadon shi wajen uwarta Baaba Asiya ta tsotsa a nono, ban san ina hawaye ba sai da na ji danshin saman kumatuna. Baƙin ciki ya cika min zuciya,  me ya sa mutane suke kasa gane wani abu. Mace da Namiji waɗanda ke zaune ƙarkashin inuwa ɗaya ta ma'aurata tsakaninsu sai Allah, ba za ka ji bangare ɗaya ka yankema bangare ɗaya hukunci ba saboda Ubangiji ne kaɗai ya san mai ya ke faruwa tsakaninsu. Ƴan'uwan Yusuf suna ganin kamar komai na ke da shi sanadin ɗan'uwansu na samu Allah na tuba ba kyau tone tone in har da abin da nake dashi ya zauna a hannuna da yanzu na wuce matsayin da nake a yanzu, sun manta a yadda na auri ɗan'uwansu bashi da komai sai kwalin Degree da Masters sun manta gwagwarmayan da muka shafe shekaru sama da goma muna yi tare dashi rana tsaka saboda ya ɗan samu rufin asiri har ana tunanin ya ba ni duniya ina kwance a gida ina hutawa.   Hawayena na share ina jan ƙaramin tsaki, ni ba domin Yallaɓai ya hana ni aiki ba da tuni ba su ganni ina zaman gidan ba, amman in har ya biyani kuɗina da nake bin shi ina nan da tunanin buɗe shagon Saloon kamar yadda na ke buri. Suna alfahari da wannan gidan su a tunanim kamar ya gama mini komai tunda ya gina min wannan gidan sun manta tsawon shekarun da na kwashe ina zaman haya. Maganar auran sa ba ta gaba na ta lafiyata na ke, na riga na shafa faɗama Yallaɓai cewa ba zan taɓa baƙin ciki domin zai ƙara aure ba amman ya sani kafin ya yi tunanin ƙara aure ya yi tunanin mu ya wadatamu da komai na rayuwa da ni da ƴaƴansa ba kuma mu ba mu wadatatu ba, ya je ya ɗauko mata ta zo ita a wahale mu a wahale.   Jikina ya yi sanyin da na ƙasa tashi daga kan kujeran da nake zaune. Yallaɓai na kira domin na tuna masa maganar da muka yi na komawata ganin Gynea Asibitin ABU SHIKA. Ya sake kiran Uncle Abba mu ji yadda suka yi da wani abokin shi da ya ce zai kira a can Zaria zai taimaka mini. Amman ban same shi ba daman wani lokacin  wajajen office ɗin sa ba Network a yi ta neman wayarsa ba a samu. A shekarun baya wani babban asibitin kuɗi ma'ana private Hospital na yi ta wahala da jelangen zuwa ba wani cigaba sai cin uban kuɗi sai aka bani shawara na koma babban asibiti ko Aminu kano ko ABU Shika da ke Zariya. Yallaɓai ya so na zaɓi Aminu kano, ban san me ya sa tunani na ya fi karkata da gwara na fara ganin likita a Asibitin Shika ba. Shi kuma daman Yallaɓai ya na girmama ra'ayina da buƙatuna shi ya sa bai hana ni ba. Daga nan sai na sake buɗe data Group ɗin mu na BUK ya fara ɗaukan Hankalina saboda na ga ana ta massages da yawa kuma ni dai nasan tun da muka gama makaranta ba wani mgana ake yi sosai ba. In magana ta yi yawa to ɗayan biyu ne ko rasuwa ko an samu ƙaruwan aure ko na haihuwa.     Ina shiga ko sai na ga Hauwa Jamilu ce ta haihu ƴ'a mace, ƙawarta Samira Aliyu ne ma ta tura hoton Baby da sanarwan haihuwan, na ƙurama hoton Baby ido mai kyau da ita. Ina son haihuwa ina son na ƙara haihuwa har a cikin raina, ko a ina naga an yi haihuwa sai na ji dama ni ce ko da ace daga shi in na yi ba zan ƙara haihuwan ba.   Tagging na yi sai na yi mata barka a ƙasa kuma nace zan kira wayar ita Hauwan, duk da ban da wata ƙawa sanda muka yi BUK amman kuma ina gaisawa da mutane. Daga baya ma bayan mun gama makaranta na fi zumunci tun da in aka yi rashi ko ƙaruwa ko ban je na kan kira waya in kuma za a haɗa gudummuwa na kan tura nawa. Ina yin maganar Samira na Online ta yi min Reply. "Amin Amin. S Yashe ku kam dai kun gama ko?   Sai na ba ta amsa da cewa" Mun gama me Samira Aliyu? "Haihuwan mana, kin daɗe fa ba ki ƙara haihuwa ba ina jin" Emojin mirmishi na tura mata ban yi magana ba. Ina gani Maijidda Bala, ta yi tagging ɗin maganar Samira da cewa" Ƴan boko ne matar Injiniya guda ko matar Yallaɓai zan ce? Sai da na yi dariyan Sarari saboda ko username ɗina Sadiyar Yallaɓai ce a rubuce.   Kuma Maijidda Bala anguwanmu ɗaya, ta san gidanmu na san na su , duk halina na rashin son sakewa da mutane amman Maijidda na zuwa gidanmu saboda Rahila, to daman duk wanda ya zo gidanmu saboda Rahila ce ko Ma'u su ne masu jama'a. Ba zan taɓa mantawa da maganar Mama tun muna ƴan mata ta sha ce mini" Ke kam Sadiya da wuya ki ta shi aure ki ga jama'a. A yi mutum ba shi da son shiga jama' a kwata kwata." A lokacin dariya na kan yi kafin na ce"Shike nan sai ke da Gwaggo ku ci min ƙawayen amarya."   Allah Sarki Mama Allah ya sa kina aljannah. Ban biye ma mangaganunsu ba na sauka saboda kar na manta nan take na kira Hauwa na yi mata barka, har tana mini tsiyan ni na gama na ji daɗi na. Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba. Saboda ko me zan ce ba za ta gane ba sai da na ji tana faɗin"Nima daga wannan na faɗa ma Baban Afnan na gama wallahi. Allura zan je a yi min na shekara biyar." Da sauri na ce"Kul ɗin ki Hauwa. Karki yi wannan gangancin, in kika tsaida haihuwa na shekara biyar to za ki yi ta nadama har na shekaru ashirin ba ki daina ba. Saboda lokacin da kike son ki ƙara haihuwan ba za ki samu wannan damar ba."     Na faɗa ina jin raɗadin abin a cikin raina Hauwa ko cewa ta yi" Ko Sadiya? Sai kawai na rausayar dakai kamar tana ganina kafin na ce" Ku yi na gargajiya ko na musulunci Hauwa. Saboda haka ina gargaɗin ki in ba so kike yi ki ƙare a zuwa gaban Gynea ba." Hauwa na jin haka sai ta ce to shike nan za ta yi magana da Daddyn Afnan duk yadda ta so na yi mata wata mgana ban yi ba saboda ba close na ke da ita ba, rayuwa ai darasi ne  amman da zan buɗe mata cikina sai ta ji tunanin da ke cikin ranta ya fita ba domin komai ba sai tsira daga faɗawa irin halin da ni na faɗa.   Ina nan zaune ina ɗan duba wayata amman ban shiga group ɗin gidanmu ba sannan ban shiga na ɗaiɗaikun su da suka yi min magana ta private ba saboda nasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Fita na yi zuwa Instergram ina kallon kwalliya domin  ni Allah ya yi da son abu fashion. Domin har certificate gare ni akam koyon kwalliya ba ma ɗaya ba sannan ina da na koyon saloon da gyaran jiki, shi ya sa wayata cike suke da ire iren su.  Ban san na ɗau lokaci haka ba sai da Saude ta zo ta ce mini ta gama da ciki za ta gyara falo sannan na ba ta waje, bayan na ce in ta gama ta ɗora min ruwa a gas ta dafa taliya fara tunda ina da miya a firiza.   Bedroom na koma na yi zama ma ina ta kallon Videos ɗin yadda ake kwalliya da na ɗaurin ɗan kwalli a istergram daman ni can na fi auki, kiran sallar azahar ya tada ni na ijiye wayar na je na yi sallah lokacin har Saude ta tsane taliyan da na ce ta dafa guda biyu, ni na karɓe ta na ce ta shiga ɗakin su Jidda ta yi sallah ni kuma sai na fito da miyar na ɗumama. Na saka ma kaina sauran kuma na bar shi a cooler.  Ƙaramin falo na koma na kunna kallo sai na sauya tasha zuwa Mb2 na iske a wani film mai kyau sai na barshi, filet ɗin abincin na kan jikina ni kuma na miƙe kafata saman cafet ina cin abinci ina kallo har Saude ta fito sai na ce ta ɗauko kofin ta tsiyayo mini ruwa a Dispenser.   Sai ta kawo mini sannan na kalle ta ina faɗin" Ki ɗiba abinci ki ci sai ki zo ki wuce gida kin san kina da makaranta." Da toh ta amsa min ta wuce kitchen ta diɓo taliyan ta zo ta zauna a kasa ta na ci, ba hira muke yi ba sai ni ce ma ke mata tambayoyi. "Babanku ya dawo? Sai ta ce min a'a sai na girgiza kai kawai, lagos ya ke zuwa kwadago in ya tafi sai ya yi rabin shekara bai dawo ba ya bar iyalansa da wahala. Ni na riga ta tashi, na tafi da filet ɗin hannuna da kofi zuwa kitchen na saka a sink ɗin wanke wanke. Leda na samu na buɗe drower ɗin cabinet ɗin kitchen ɗin na auna mata shinkafa tiya biyu sai taliya da maracaroni da na diɓar mata tunda nima abincin nawa ya yi ƙasa.     Bedroom na koma na ɗauko mata 2k daga cikin jakata sannan na dawo falon lokacin ta gama cin abincin sai na ce ta wanke hannu ta zo. Ina zaune ta zo ta zauna gabana ta na faɗin" Ga ni Anty" Ledan na tura mata gabanta lokaci ɗaya ina mika mata kuɗin hannuna ina faɗin"Ki kaima mamanku kin ji ko? Ta karɓa tana faɗin"An gode Allah ya saka da alheri." Na amsa da Amin ina faɗin"Ki yi sauri ki hau mashin ne biyu ta kusa." Sai ta amsa minI, tare muka fita saboda zan rufe gida tana fita na maida gidan na rufe na dawo falo ina kallo, film ɗin horror ne ya ɗauki hankalina sai da aka gama shi amman za a yi part 2 ɗin shi. Uku na rana na koma ɗaki na kwanta sai barci ban ta shi ba sai huɗu da rabi, sai na yi alwala na yi sallah na ga tunda huɗu ta wuce sai kawai na ce bari na yi azkar ɗina.   Ni kaɗai a gida kamar mayya na matsu su Jidda su dawo sai shidda suka dawo saboda biyar da rabi ake tashin su kafin ya je ya ɗauko su shidda ta yi tunda makaranta boko da isalamiya ne. Dawowarsu ne ya sa na fito falo suna bani labaran makaranta suna cin abincin, Baby ce mai surutun Jidda irin Babanta ne tana da sanyi sosai ba kamar Baby ba. Suna gama cin abinci suka sauya kaya zuwa na gida. Unform ɗin Jidda ta ce za ta wanke na ce yamma ta yi, tunda suna da guda biyu ta bari zan wanke musu gobe da safe   Tare muka yi sallar mangariba, muna idarwa a ƙaramin falo muka fara karatu. Jidda na suratul maryam ne Babby kuma tana ƙasa ƙasa sai da suka biya na jiya na ƙara musu sannan muka yi azkar tare. Muna gamawa sai muka miƙe muka yi isha'i tunda an kira. Muna idarwa na bar su a falo suna kallo ni kuma na shiga kitchen na dafa ma Yallaɓai tea daman na dafa masa farar shinkafa tunda shi taliya ba ta dame shi ba, ina gamawa na shiga wanka ina wankan ma na ji shigowar motar Yallaɓai.   A gurguje na shirya cikin riga da wando, wandon plazo ne mai buɗewa ta kasa. Rigar kuma Top ce mai wuya ta kama jikina sai na gyara gashin kaina na tufke a tsakiya na saka wata hula mai love a saman kaina kalan pick .  Tsakiya babu komai, kwalliya na yi kamar yadda na saba na saka jan baki na kamar yadda na saba. Na ji ƙaran bude ƙofa ganin bai shigo ba ya sa na san ya shiga tiolet ne. Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ina zaune a gefen gado ina bin shi da mirmishi bayan na amsa sallamarsa.   Hannuwana ya buɗe minI na tashi da sauri na faɗa masa ya rumgumeni. Nima sai na ƙamƙamesa ina fadin"Barka da dawowa Yallaɓai na." Ya na shinshina ƙamshin humran dake jikina ƙasa ƙasa ya ce" Uhm. I like it."   Ɗagowa na yi muna kallon juna kafin na ce'Me? Yana mini wani kallo ya ce"ƙamshin ki mana." Far na yi masa da ido kafin na ce"All is yours" Kumatuna ya shafa kafin ya ce" Allah ya yi miki albarka." Na amsa da Amin. Ruwan wanka na ce zan haɗa masa ya yi wanka sai ya ci abinci. Shi kuma sai ya ce"E. sai mu ta fi wajen kiran Alhaji ba"   Gyaɗa masa kai na yi ba tare da na yi mgana ba. Sanda ya shiga wanka ni kuma na je haɗa masa abinci bayan ya fito ya sauya kaya zuwa wani yadi riga da wando ɗinkin zamani. Falon farko mu ka je saman dining ya ci abinci su Jidda kuma suna ƙaramin falo Bayan mun gama ba mu tsaya ɓata lokaci ba ya ce na saho hijabi mu ta fi, daman na fito da Hijabin jalbab mai ruwan ƙasa har ƙasa sai na saka takalmina iri ɗaya da wanda Yallaɓai ya saka daman tare ya siya mana.   Na ce musu Jidda su kula da gida za mu je gidansu Gwaggo mu dawo. Baby taa saka rigiman sai ta je Babanta ya tsaya yana lallashinta da zai siyo mata ice cream sannan ta yarda na ce in za su kwanta su kashe komai za mu fita da key da toh Jidda ta amsa da yi mana a dawo lafiya. Sai da muka fita da motar sannan Yusuf ya koma ya rufe get ɗin Sannan ya dawo muka kama hanya mun ɗauki hanya kenan na kalle shi kafin na ce" Na gwada kiran ka yau ban same ka ba." Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Nima na kira ki ban same ki ba." Sai ya kalleni kafin ya ce"Me ya faru? Kai tsaye na ce"Kan mganar komawata Abu shika ne, Uncle Abba bai ƙara kiran ka ba? Sai a lokacin ya tuna ya ce"Kash! Ya kirani amman shaf na manta ba mu yi mganar ba. Amman bari yanzu zan kira shi."   Ni ya miƙa ma wayar ya ce na kira shi, Kawu Abba daman ya saka masa da na kira sai na saka a speaker har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. "Kawu barka da dare." Shuru bai yi mgana ba. "Uncle Abba barka da dare" Wata murya a dakushe ya ce"Yusuf in ma bashi kake nema na kuɗi ba ni dashi wallahi. Wanda ma nake binka EFCC ne za su ƙwatar mini haƙƙina."   Daga ni har Yusuf sai da muka kyalƙyace da dariya. Ni ce na ce"Haba Uncle Abba ba amana yanzu sai ka kai mini Yallaɓai EFCC? Jin muryata ya sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce" Sadiya?  daman kina kusa? Na amsa masa da e, sannan muka gaisa dashi. Shi kuma sai ya bige da faɗin"Yallaɓan nan naki ya ci bashina kamar gadon ubansa yaƙi biyana. Gwara babbar hukuma ta shiga ciki, in na je gaban manya sai a saka sanayya a ciki gwara a kame shi ko amansu ne sai ya yi." Yusuf na dariya ya ce" Na ci fa halas, abin da ya yi Nene shi ya yi ka fa Kawu Abba." Kai tsye ya ce"Ko? To ai ko ita Nenen ta ci kuɗina sai ta biyani ballatana kai." Ni dai ina ta dariya ganin sun sarƙe da gaddama shi Yusuf ya na faɗin ya ci halas kawu na fadin shi ba ƙanin Uban shi ba ne na uwarsa ne bashi da gadonsa. Zungurin kafar Yallaɓai na yi sannan ya yi gyaran murya yana fadin"Sadiya ta ce a yi maka tuni ka yi mganar da Dr Fadil ɗin? Kawu Abba dagacan bangaren ya ce"Kash na manta. Amman bari na kira shi na ji yadda muka yi zan kira ka."     Sai ya kashe wayar, dai dai Yusuf na faɗin" Kina ganin komawarki can da ganin likitan ba damuwa? Sai na gyaɗa mai kai ina fadin"E, ba matsala can ma ƙwararru ne. Tunda na yi ta nan ban dace shi ne aka ban shawara na gwada can ɗin." Sai ya jinjina kai, bai yi magana ba sai ni ce na cigaba da faɗin"In ina da appoitment na ganin likita tun ana gobe zan je zariya na sauka gidan Ya Hamza bayan na gama ganin likitan sai na dawo."   Kai tsaye ya ce"E  hakan ma ya yi. Allah ya sa a dace." Na amsa masa da Amin. Mun shiga anguwan ɗorayi kawu Abba ya sake kira ya ce sun yi mgana da abokin nashi Dr Fadil shi likita ne a bangaren zuciya amman ya ce ya yi ma wata Dr Nayami mgana musulma ce amman ba bahaushiya ba ce, ya ɗan yi mata brief na matsalata ta ce zuwa sati mai zuwa za ta iya bani appiotment in har ya tabbata zai kira Kawun ya sanar dashi.   Jin haka ya sa sai na ji daɗi kamar na je ta shaida mini zan iya sake samun wani cikin haka na riƙa ji.  Daidai lokacin Yallaɓai na gyara parking a kofar gidanmu da ke anguwan Ɗorayi. *TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU  #1k NE KACAL,  AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 09069067488. 08032773332. *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE* *Janafty* *03/10/2024* *TURKEN GIDA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z *🅿️03* Gidanmu na nan a farko layin shiga anguwar Ɗorayi. Yanayin fasalin gidan babba ne sannan tun daga waje za ka fahimci tsarin gidan na tsohon ɗan boko ne. Domin Alhajinmu  kafin ya yi Ritire(Ritaya) sai da ya riƙe mukamin babban darakta na kamfanin wuta na jihar kano(KEDCO). Bayan kasancewarsa manomi. Kuma gidanmu na da ga cikin rukunun gidajen da suka daɗe a anguwar tun da sama da shekara ashirin duk da ko mu kanmu muna da wayau lokacin da muka dawo gidan tun a wancan lokacin zamani na kwance. Sai dai yanzu lokaci bayan lokaci yana samun ƴan gyare gyare da kwaskwarima daga su Yaya Hamza.   Ni na fara fitowa daga Motar. Yallaɓai na kuma an kira wayarsa ya tsaya a mota ya na mgana. Kofar gidan namu tar da hasken wuta gabaɗaya ma anguwa akwai hasken ƙwakwayen da suke kofar gidajen wasu mutane dake cikin rukunin anguwan ta Ɗorayi. Gidanmu na ke kallo ina tuna wasu shuɗaɗɗun al'amura da suka faru damu a cikin

Chapter 3 of 31