ƙarshe shi ne Pap smears ne kuma har na karɓi result ɗin wannan satin da ya wuce na kai ma Dr Aisha cikin ikon Allah ta ce mini shima ba wata matsala.
In da na ke ɗan samu salama kenan kuma ta na bani hop ɗin duk da saura gwaje gwajen ba mu gama ba, ba ni da watsala lokaci ne bai yi ba in ya yi zan ƙara haihuwa.
Zuwa lokacin shiryen shiryen bikin Yaya Usman ake yi domin cikin watan da za mu shiga kafin azumi za a yi bikin na shi. Anan Gwammaja za a yi bikin tunda ɗaurin auran ma a kaduna ne. Yadda Yallaɓai ya faɗa mini gabaɗaya da Anty Zabba da yaran za su zo kamo sai an gama biki za su koma fatakot har da amaryan.
Har anko ƙannensa su Nasara sun fidda Atamfa ce mu ma duk mazajen mu sun yi mana mu da yara. Aure dai ya tabbata ba fashi amarya na dawowa daga london aka tsaida date ɗin biki.
A kuma tsuƙin ne na kirga za mu yi 15 years Anniversery da aure ni da Yallaɓai zuwa bayan sallan azumi da kwana shidda kenan. Ni kaɗai a raina na shirya za mu yi walima tun da tun na 10years ba mu kara ba lokacin Baby ta cika shekara ɗaya sai muka haɗe da birthady ɗin ta.
Ba mu kara yi ba sai wanman karon na ke fatan mu sake yi. Daman a gida ne daga ni sai shi sai yara muka yanka cake ɗin mu sha hotunan mu da ciye ciye washegari kuma Yallaɓai ya fita damu mu wajen wassani da sauran su. Tun tuni na so na yi masa mganar amman bai samun lokaci Alhamdulillah yana ta samu kwangila bayan gama gina gidan buredi a Rano dalilin haka ya samu kwangilan gina bayuka na wasu makaratun sakandiri a garin na Rano sai ya kasance zamansa a nan office ba sosai ba sai dai Musabahu ya zauna wani lokacin gidan bulo kuma daman sun ɗauki yara ma su kula da shi, shi dai Musabahu manaja ne kawai.
Abin da na fara lura da shi shi ne Gimbiya ta fara ƙoƙarin takura ma rayuwar aurena ta na daga can gidansu tana takaba.
Ni na san cewa Yallaɓai na zuwa ganinta tun da yana yawan zuwa Rano. Ban kuma taɓa nuna damuwata ba ko na nuna fuska ban ji daɗi. Sai dai na ga ba ta da hankali in ya dawo gida sai ta kira shi a waya ta ji wai yadda ya koma gida. Da safe kuma ta iya kiran sassafe tsirfa kala kala daga ta ce Anty Bahijja za ta ba da saƙo a kawo mata sai ta ce Nene sai ta ce Anty Maimuna wani lokacin ita ce ma za ta ce ya siya mata abu kaza ya taho mata dashi tsirfa kala kala ranar da bai je Rano ba ta riƙa kira kenan ta na korafin me ya sa bai zo ba? Abin da ke ba ni mamaki shi kuma sai ya na biye mata sau ɗaya na yi masa mgana da cewa wani lokacin ta na kiran shi a waya ba ta da abin faɗa sai kawai ya ce min abar tausayi ce kuma ga shi ta samu hawan jini dalilin rasuwar nan shi ya sa ba a son ana ɓata mata rai.
Na ga ƙoƙarin Yallaɓai da ya iya faɗa min haka amman kuma ta wanni fannin ban yi mamaki ba mun taɓa samun matsala da shi a baya tun ban haifi Baby ba akan Gimbiya muka yi faɗa da Yallaɓai na ce in son Gimbiya ya ke yi me ya sa ya aure ni bai aure ta ba saboda na ga bin binin ya yi yawa amman sai buɗe baki ya yi ya ce mini" In da bai haɗu da ni har Allah ya haɗa zukatanmu ba to ya ba ni tabbacin bashi da mata sai Saudatu."
Har Gimbiya ta yi aure ban daina fargaban wata rana zan ta shi na ga Yallaɓai ya auro min ita ba na huta da ta yi aure amman yanzu kam bayan ta zama bazawara ta sake dawo mini cikin rayuwata ta na yi min barazana.
Akwai wata rana baƙin ciki kamar na kama Yallaɓai da duka da asuban fari fa, ya je sallar asuba bai dawo ba ta yi ta kiran wayarsa ina ganin an saka Daughter na san ita se sai ban ɗauka ba. Sau uku ta na kiran sa har wata zuciya ta ce na ɗauka sai wata ta kwabe ni sai da ya dawo na ce an kira shi a gabana ya ɗaga waya ya kirata bayan sun gaisa shi ya ma ɗauko ko wani abu ne ya faru ya na tambayanta ko akwai matsala ne ina jin muryanta ta cikin wayar tun da wayar da ɗan kara ta na faɗin.
"Daddy yau za ka shigo?
Sai ya ce ya na sa ran yau sai kawai ta ce" Ka taho mini da tsaraba."
Shi kuma ya ce me take so ta ce duk abin da ya ke so.
Tsabar takaici na kasa mgana.
Sai na shanye takaicina na kalle shi ina faɗin" Wai ta gama takaba ne?
Kai tsaye ya ce min" Cikin wata nan za ta fita in sha Allahu."
Sai kawai na girgiza kaina, ina so na yi mgana amman kuma sai na fasa saboda maganar ba ta da amfani sai kawai na yi masa shuru kuma ya je Ranon a ranar kuma ina da tabbacin ya yi mata tsaraba tunda bayan ya dawo gida muna tare ta kira tana yi masa godiya. Ƙarin abin haushin ma wani lokacin in dai ya kai dare a can abincina sai dai ya zama kwantai sai ya ce Hajiya ta matsa masa ya tsaya ya ci abinci. Kuma Yallaɓai na ganin ina nuna damuwar hakan a saman fuskata bai taɓa damuwa da ya ba ni haƙuri ba shi a wajen shi ba a yi komai ba sai kawai na koma gefe na na zura masa ido ina ganin gudun ruwan shi amman dai ni na san ko na ƙi ko na so ai ƙarshen alewa daman ƙasa ne.
*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
09069067488.
08032773332.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/FAtGNQc8Y8pB008TuxFJVo
Eaman ScholarSphere.
Where ideas Take Shape.
WHAT WE DO.
ASSIGNMENT
PRESENTATIONS.
ARTICLES
PROJECTS.
BOOK
AND MANY MORE.
CANTACT US THROUGH.
02347067793152
MOTTO:
"Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures"
*🅿️17*
Shirye shiryen biki Yaya Usman kawai ke kan layi yanzu saboda bikin ya rage saura kwana takwas.
Kuma da ya ke bikin anan Gwammaja za a yi ita kuma Amarya a Kaduna gidan kakkaninta wanda ya haifi mahaifinta. Shima tsohon Soja ne mai ritaya amman ya rasu. To nan za a ɗaura aure ranar asabar amma taron biki ranar jumma'a ne asabar da an gama ɗaura aure amarya da tawaganta za su sauka a Kano sai ranar litini ango zai ɗau amaryansa da iyalansa su hau jirgi zuwa fortacol
Kuma auran daman na yan boko ne lefe ma kuɗi kawai ya tura ma Amaryan aka ce ita ma uwargidan an ce ya ba ta kuɗi bayan ya biya mata Hajji shi da ita da Amarya bayan sallah da an fara tafiya za su ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki.
Zuwa lokacin hatta abincin da za a dafa Yaya Usman ya saka an kawo. Biki dai za a yi na masu da shi, ba talauci a ciki ba kuma ɓarnan dukiya dai dai ruwa dai dai tsaki.
Gimbiya ta gama Takaba tsakanin bikin Yaya Usman saura kwana goma ne. An yi walima da taro a can Rano amman ni dai ban je ba. Na ga dai su Anty Bahijja sun ta ɗora ta a status suna mata addu'an Allah ya kawo wani mijin na alheri ya kuma ƙara mata dangana. A cikin hotunan akwai wanda aka ɗauke ta a ranar da ta fita takaban ta yi kwalliya amman ta yi rama duk da dai haka a raina na ce dangana ai ta riga da ta samu ko Yallaɓai bai mini mganar ba nima ban yi masa ba. Na kuma ƙara ganin ƴan'uwan suna yi mata addu'a a group ɗin iyalan Marigayi Muhammad Inuwa 02 wanda muke ciki gabaɗayanmu har mu surukan gidan da a can Ranon gabaɗaya amman kuma suna da wani wanda ba ma ciki shi kawai na iyalan gidan ne gabaɗaya shima na sani ne saboda ina gani a wayar Yallaɓai. Kuma shi wannan da muke ciki daga baya aka saka mu, sannan ba a cika ma mgana ba sai ta kama ina ga sun fi yin ɗan sirrin su a can ne saboda ire iren mu da suke gani kamar bare.
Yallaɓai kuma daman shi harkan chart ba wani damun shi ya yi ba. Yana yi ba wai ya yi ba ne, saboda harkokin shi da jama'a amman sai ya yi wata biyar bai saka status ba. In ma ya saka sai mutuwa ko in ya nishaɗu ranar Jumma'a ya saka salatin Annabi. Amman ni na san yana kiran Gimbiya a waya tun da ina yawan ganin sunanta a call long ɗin shi ba da kuma Niyyar bincike ba sai saboda wayarsa ba ta da shamaki a hannuna kamar yadda nima tawa ba ta da shamaki a hannunsa.
To a irin haka ne ranar da ta yi fitar Takaban wayar na hannuna da daddare Yallaɓai ya shiga Tiolet saƙon ta ya faɗo Allah na gani ban buɗe ba amman daga sama na hango godiya zuwa ga Daddy na, na gode bi sa ɗawainiyar da ka yi ta yi da ni. Daga nan saƙon ya yanke gudun shiga hurumin da ba na wa ba sai na kauda kaina ban buɗe masa saƙo ba saboda ba ni aka tura mawa ba da ya fito kamar in faɗa masa an tura masa saƙo sai kuma na fasa na ajiye masa wayarsa a raina na ce ai zai gani. Yadda na gani ban nuna na gani ba, nima kuma bai nuna mini komai ba, sai kuma da safe kafin ya fita na ji suna waya lokacin muna dining ina haɗa masa abun kari, alƙwarin da na yi ma kaina shi ne zan zura masa ido na ga iya gudun ruwan shi daga shi Gimbiyar. Amman abin na sukan raina ganin gabaɗaya idon ta na kan mijina kamar shi kaɗai ne a dangi?
Sai wata zuciyar ta tunasar da ni a lokacin." Kin manta ba namijin da ta yi ma so irin mijin ki? To ko dai angulu ne ke marmarin son ta koma gidanta na tsamiya?
******
LARABA."
Yau mun wayi gari ranar laraba. Kimanin jibi Jumma'a taron bikin a can Kaduna, mu kuma nan sai ranar asabar tunda mu za mu tarbi amarya. Ita kuma Anty Zabba ta iso kano ita da ya'yanta amma a gidansu ta sauka ta ce ita a can za ta yi nata taron biki. Mijin ta kuma ya amince shi ya sa ma kowa bai damu ba. Sai dai wanda ya ga zai iya bin ta can sai ya je, ni tun da na ji haka na ce me zai kai ka? Ai sai a ce ka je ganin gulma ne gwara mu tsaya nan Gwammaja in ta zo ma haɗu a gaisa.
Tun safe na tashi ina aikace aikace saboda mun yi da su Hauwa a Gwammaja za mu yi ni saboda aiki. Tun asuba da na tashi ban koma ba, tun watan da ya gabata hutu ya ƙare mini Yallaɓai ya cika alkwari ya saka Saude a makaranta wata private school ce mai ɗan sauki sauki a nan kusa da anguwar Ɗorayin ta ke da kafa ma Saude ke zuwa shi ya yi mata komai har uniform da jaka da takalmi an saka ta Jss2 saboda ta yi girma a jss1.
Tun da ta fara zuwa makaranta shikenan aikin gidana ya dawo kaina saboda ba ta samun lokaci sai biyu suke ta shi in kuma ta dawo da la'asar ta na zuwa islamiya. Sai alhamis da jumma take zuwamin in ta dawo daga makaranta tun da ba islamiya weekend kuma sai ta je Allo ta dawo.
Aiki duk ya yi min yawa rabo na da barcin safe har na manta da su Jidda sun tafi makaranta zan fara gyaran gida ina gamawa na je na tada Yallaɓai ya yi wanka ya zo mu karya to sai ya fita ne nake samun daman kwanciya na huta bayan azahar irin uku saura na miƙe na shiga kitchen na ɗora girki saboda yan makaranta.
Kibar da na fara yi saboda hutu duk ta zazzage ga shi daman ni ba gwanar aiki ba. Ina yi ina jin na gaji kai har gobe ba zan kaunaci aiki ba. Ga shi yanzu Yallaɓai ya lalace ba iya taya ni da komai ko da ya na gida ne sai dai ma ya yi ta mini dariya in ya ganni na yi shigar aiki na tsuke cikin Boom short da ƙaramar riga sai ya hau tsokanata.
"Sadiya ƴar laushi barka da aiki."
Ranar haka ya ke shan harara ba na ma tanka shi domin na biye masa sai ya ɓata mini lokaci shi kuma bai tayani ba, ballatana ya rage min wani aikin Ahalin na san ba abin da bai iya ba shima kuma ya san na san ya iya komai.
Yau dai aiki ya kacame mini ga wanke wanke jiya ban yi da yamma ba. Jidda ta so ta yi lokacin an kusan mangariba sai na ce ta barshi sannan ga shara na gama sai na yi mopping tunda na ɗan kwana biyu ban yi ba sannan na saka turaren wuta a burner gidan ya ɗau kamshi. Na riga na wanke tiolet ɗin su Jidda saura na mu shi na shiga na wanke ban gyara Bedroom ɗin mu ba Yallabai na kwance ya na barci har da minshari.
Falon yara na koma na zauna ina maida numfashi. Na huta kafin na tashi na yi wanke wanke. Amman na so Yallaɓai ya ta shi ya yi wanka ya karya sai na haɗa komai na wanke domin da na fara shara na fara jin jiri tuni na je na karya cikina ya cika to ina zan zauna shi ya na can kwance ni kuma ina aiki yunwa ta far min a ciki na faɗi a sume tuni na nema ma kaina mafita na karya na barshi.
Na yi hutun sama da minti talatin domin kallo ma ne ya ɗau hankalina wani film ɗin hausa da suke haskawa tashar Arewa24 na ga ya fara mini kyau sai na zauna ina kallo tuna ina hutun jaki da kaya a saman kaina ne ya sa na miƙe. Har na fara wanke wanke kuma sai na tsame hannuna a cikin ruwan omo na wanke da ruwa na fita zuwa cikin bedroom ɗinmu.
Tsaye na yi kawai a gaban gado ina kallon Yallaɓai ina sanye da wando baki plazo rigar jikina vest ce ta lame min jiki kaina ɗankwalin doguwar riga ne na yi gammo da shi a saman kaina.
Zuwa na yi kusa dashi, na fara jan bargon ina kiran sunan shi amman sai ya juya ya na jan bargon ina ja, alamun dai ba zai iya ta shi ba.
"Yallaɓai.."
Na faɗa ina dai dai ta saitin kunnuwan shi. A hankali ya buɗe idanuwansa da suka shige ciki saboda barci.
"Mene ne kuma?
Ya faɗa da muryan barci har ya na wani yamutsa fusaka ina ganin haka na saka hannuna na shafa kumatunsa sai ya ji sanyi da sauri ya ware ido yana kallona ni kuma sai na koma na riƙe kugu ina kallonshi rabi harara harara.
Ɗan tashi ya yi kaɗan ya na jingina da jikin gado kafin ya kalleni daga sama har ƙasa sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Me kuma na yi! ?
Baki buɗe na ce" Me ka yi fa ka ke tambayata Yallaɓai?
Ya na kallona ya ce" To ba dole na tambaya ba, kin ta da ni kamar yaƙi. Ga shi ke kuma kin riƙe kugu kamar mai shirin dambe."
Yana cewa mai shirin dambe na dunkule hannu na ware kafa ina masa gusha gusha sai na kai masa hannu kamar zan naushe shi. Dariya ya ke ta yi kafin ya ce"Oh yau tekwando rana za mu yi kenan! To ai na iya irin wannan ba ri ki gani"
Kawai sai na ga ya sauko ƙafafunsa ƙasa ya janye bargon sanin halin shi ya sa na yi saurin dawowa dai dai na riƙe masa hannu ya koma ya zauna na zauna a gefen shi na mararaice ina faɗin" Yallaɓai na."
Na faɗa har ina masa fari, ina zan yarda ya yi wasan chinese da ni. Lokacin ina amarya sai ya ce mu yi daga karshe dai na gane ni ce ke shan wuya ya fi ni karfi awasa duk ya naushe ni in na yi shagwaɓa na ce da zafi sai ya ce wai saboda kashina ya yi ƙwari kuma nan gaba ya koya min faɗan kare kai. Daga baya na ce ni wallahi ba na so shi ya sa muka daina amman ina amarya ba wasannin da ba mu sha yi ba. Ko dawowarmu nan gida in ya na da lokaci muna yar gudu ni da shi da yara ranar weekend muna da kayan jugging. Daga baya na daina fita saboda na gaji ban iyawa shi kuma ya ce wai na tara kitse ne shi ya sa. Sai dai ranar da ya so ya na fita tare da jidda da Baby ya na kuma gaya musu motsa jiki na ƙara lafiya a jikin ɗan adam.
Yadda na yi masa farin ne da yanayin maganata ya sa ya san akwai abinda na ke so.
Cikin mirmishi ya ce" Me kike so ne Sadiya? Domin in za ki cuce ni haka kike yi."
Hannuwansa na riƙe cikin nawa na marairaice ina faɗin" Haba Yallaɓai na wani rin cuta kuma? In miji ya taimaki matarsa sai a kira shi cuta?
"Kamar wani taimako kenan?
Ya faɗa ya na mai tsare ni da ido da sauri na marairaice kafin na ce" Yallaɓai na yi shara na yi mopping na wanke Tiolets baya na duk ya kage to kuma ga wanke wanke can ba a yi ba."
"To shi me? Wai na je na yi wanke wanken?
Ya faɗa yana kallona da sauri na ce" Ni ban ce ba."
Sai kuma na saki hannun shi na miƙe ina tafiya daƙyar kafin na ce" Ka tausaya mini Yallaɓai Allah bayana ke ciwo."
"Kina da ciwon baya ne ban sani ba?
Ban juyo ba na ce" To ni dai ina tunanin tun lokacin haihuwan jidda na goce. Kasan kuma sai a hankali a hankali ya ke tashi."
Da iya gaskiya na faɗa domin wani lokacin in na yi aiki bayana sai ya rike amman sai Yallaɓai ya ce" Ba shakka. To sannu."
Yanayin mganar na shi ya sa na san bai yarda ba sai na juya ina faɗin" Fisabillahi Yallabai yanzu ka lalace sam ba ka son aiki."
Me Yallaɓai zai yi ba dariya ba, ni ko sai na tsaya ina kallon shi da gaske fa haushi ya ke ba ni, ya na gida ace ba zan more shi ba.
Sai kawai na tura baki kafin na ce" Ko a da ka fi tausayina ne! Yanzu kuma ka daina tausayina ko?
Ganin yana kallona yana dariya yasa na fara matsan kwallar karya ina faɗin" Ko dai ka daina sona ne Yallabai?
Na tsare shi da ido har lokacin fa bai daina dariya ba. Sai kawai na fashe da kukan da ba hawaye ina faɗin" Na shiga uku Yallaɓai na ya daina so na"
Ya na dariyan ya ƙariso ya rumgumeni yana faɗin" Mamaki na ke yi da har yanzu ba ki san aikin da nake yi mai muhimmanci a cikin gidan nan ba?
Sai na ɗago ina kallon shi kafin na ce" Wani aiki ne? Barci ko?
Sai kawai ya kai hannun shi saman ƙirjina ya na shafawa ina kallon shi na ga ya dage min gira ai da sauri na kwace jikina ina faɗin" Ai daman anan kafi auki ba za ka zo ka tayani aiki ka motsa jikin ka ba."
Na faɗa ina tura masa baki. Yana dariya ya ce" Ai abin da nake yi shi ne babban misalin motsa jiki."
Sai kawai na jinjina kai kafin na ce" Kuma kana taimakon kanka ba."
Sai ya daga hannu saama kafin ya ce" In ji wa? Taimakon kai da kai dai ko?
Balla masa harara na yi na kama hanyar fita ina faɗin" Kai dai ka sani."
Ina jin sa ya biyo bayana yana faɗin" Ciwon bayan ya warke ne?
Sai na tuna da sauri na riƙe kugu na sauya tafiya ina cije baki. Yallaɓai dariya har tana sauti na yi masa banza na fice ina faɗin ai sai ya yi ta kwanciya.
Har na dawo zan cigaba da wanke wanke ya leƙo ya ce na zo na bashi abin karyawa. Dole na koma falo na haɗa masa tea na zuba masa ɗumamen tuwon da na yi jiya da daddare miyan allayu zama na yi sai da ya gama ci muna yi muna hira bayan ya gama na tattara komai zuwa kitchen sai ya biyo ni ya na faɗin" Je ki huta bari na yi "
Ina jin haka na daka tsalle na rumgume shi na bashi sumba a baki kafin na ce" Yaron kirki Yallaɓan Sadiya."
Kaina ya dankwanfar ya na faɗin" Sai na fasa."
Da sauri na ce" Na tuba ranka ya daɗe ka yi mini rai."
Yana dariya ina dariya ban kuma iya zuwa na huta ba saman cabinet ɗin kitchen ɗin na haye na zauna yana wankewa ina karba ina jera su a muhallinsu.
Anan ne ma ya ke ce mini yanzu ya girma iyalai sun fara taruwa ba girman shi ba ne a ka ga yana aiki
Ni ko sai na buɗe baki na ce" To mi ye a ciki? Ko ƴayan ka sun gan kana aiki ba abin kunya ka yi ba ka na koyi da sunnar ma'aikin mu ne kuma daman da shi muke koyi "
"Uhm daɗin baki ko?
Ya faɗa ya na kallona da sauri na ce" Haba Yallabai ai tsakanimu ba daɗin baki sai dai gaskiya da gaskiya."
Na faɗa ina masa yar dariya sai kawai ya kalleni ya girgiza kai kafin ya ce" To ke ina wani aikin da kike ta zuzutawa? Tun auran mu tare muke aikin nan ban daɗe da daina yi miki girki kina kwance ba."
Sai na buɗe baki ina kallon shi, ban rufe ba ya cigaba da faɗin" Kuma hatta renon su Jidda tare muka yi shi to ina aikin da kike ta kira?
Sai na rufe bakina na kasa mgana sai da ya yarfa min ruwan wanke wanken da ke hannun shi yana faɗin" kin kasa mgana ne?
Sai na kauda kai ina faɗin" To na ga abin ya koma gori ne gwara a bar mganar."
Dariya ya yi yana ƙokarin sake mgana na yi saurin cewa" Yallabai yau ba za ka fita ba ne?
"Zan fita mana. Zan je office akan mganar aikin nan na kaduna ki yi min addu'an Allah ya sa ta faɗa za mu samu alheri in sha Allahu.'"
Da sauri na ce" In alheri ne Allah ya tabbatar in babu Allah ya kawo na alherin."
"Amin Amin Abar ƙauna ta."
Ya faɗa ya na min wani kallo sai nima na tsume ina masa kallon soyayya. Sai kawai Yallaɓai ya ce a hankali" Ko mu je mu yi ɓarnan ruwa ne mu dawo?
Da sauri na ce" A'a. Fita fa za ka yi nima zan je Gwammaja."
"To mu haɗa wankan mana ba shikenan ba."
"Ba ko shiken nan ba.'
Na faɗa ina haran shi, dariya ya fara yi min kafin ya ce" Me ke damun ki ne? Allah kin fara zama raguwa."
Ko magana ban yi masa duk irin ƙokarin da nake yi wai na fara zama raguwa.
"Na ƙosa ki sami ciki irin na Baby. Ko banza ki yi ta nema na ni kuma da sunan taimako ina shan Shagalina."
Kafaɗansa na kaima duka ina faɗin" Ba Amin ba."
Shi kuma ya na min dariya har ya na maƙale murya yana tsokanata.
"Yallaɓai na. Uhm
Uhm.."
Kunya ta kamani na saka tafukan hannuna ina rufe fuska shi kuma ya na mini dariya. In na tuna lokacin har kunyar kaina na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 31