ke ji abu kamar cin tuwo na maida shi, ba na gajiya ni dai kawai a yi kuma da an gama sai na ji a lokacin nake son abin gaskiya ba zan so na samu ciki irin na Baby ba.
Haka dai Yallaɓai ya gama wanke wanke sai na ce ya cika ladanshi ya wanke wajen ya goge mini kitchen ɗin harara ta ya yi ya ce" Shi wannan ɗin ba ni da lada ne ko ba ki gode ba ne? Da sauri na ce" Na gode. Allah ya ƙara girma mai girma Tafidan Rano."
Kaina ya shafa ya na faɗin" Rayuwarki ta yi albarka ɗiyar ga."
Ni da shi muka saka dariya gabaɗaya. Haka nan ya haƙura ya tayani muka gyara kitchen ɗin muka goge sannan muka koma ɗaki Yallabai dai sai da ya aikata abin da ya ce wato mu ka haɗa wanka Musbahu na ta kiran shi baƙi sun iso amman shi ya na gida yana shagali.
Tare muka fita bayan mun shirya na rufe gida bayan na ɗaukan ma Baby dogon wando kawai suna da kayan sawa a gidan Nene domin wani lokacin in sun je sun kwana ba duka kayansu suke dawowa da shi ba, ni kuma ba na damuwa saboda irin haka suna wucewa daga makaranta ba ni da haufin kayan da za su sauya.
Yallaɓai na sauke ni a Gwammaja ko shiga bai yi ba ya wuce office ya ce mini sai ya dawo
A can na samu Hauwa Munnira ce ba ta kariso ba. Gida cike da dangin Maman Farko sannan a bangaren ƴaƴa kuma su Anty Zulaihat da Nasara sune kan gaba su da su Anty Bahijja. Anty Zuwaira kuma da ya ke yar sabga ce ba ta zo ba ƙila sai yamma. Suwaiba, Jamila da Hindatu duk suna nan Safiya ma haka Hafsat ce tana Abuja ba ta ƙariso ba matar Muhammad Sani an ce sai Jumma'a za su taho tare da mijin nata.
Ummu Salma ma da ke aure a Bauchi da wuri ta zo, na zo ba daɗewa Jawahir ta dawo daga makaranta sun samu hutun sati biyu.
A ɗakin Nene na sauka. Tunda nan ne ɗakin Uwar mijina. Ana mganar abincin da za a yi su Anty Bahijja suka ce a yi tuwo da shinkafa sai alale sannan za a yi zoɓo duk da akwai lemuka da ruwa da aka sauke sai Nama da aka ce za a kawo naman sa da na rago za a gyara a soya domin a yi amfani da shi ga baƙi masu zuwa. Sai can bayan azahar sai ga Muninira Halima ma sai bayan la'asar ta zo. Mu surukan gidan muka gyara wake tunda an farke shi ya fara ƙwari bayan mun gama an kawo kayan miya da yawa ni dai daman yar laushi ce su Hauwa na bari da gyaran kayan miya ni dai na gyara albasa Munira na yi min tsiya gyaran albasa kaɗai ne aiki a wajen? Na ce shi ne na ga zan iya. Hauwa dai an yi dama dama cikin gyaran kayan miya ina zan iya. Ba zan yi ba ada dai kam na yi amman ban da yanzu.
Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya zo muka koma gida washegari ma Alhamis mun koma ranar nama aka gyara aka soya sai kum an tafasa kayan miyan da aka nuƙo. A ranar baƙin Rano suka iso har da Gimbiya a ciki ban ɗauka ma za ta zo bikin ba amman sai na ji ana mganar har da cuku cukun transfer ɗinta ya kawo ta bikin.
Sai can da mangariba ne ma muka haɗu muka gaisa. Baby dai ta kawo mini chaculate ta ce Anty Gimbiya ta ba ta, ba tun yau ba tana son su Jidda ba kyauttukan da ba ta yi musu tun tana gida ko bayan auranta da suka je honeymoon da mijinta Paris ta siyo musu kaya masu kyau da yarari.
Can da dare ma tare na ganta da su Jidda da yaran Naja'atu. Sai ranar jumma'a Ango ya iso gida. Sai ihun ango ƴan uwa ke yi masa yana kamewa kusan Soja da tsare gida a ranar ma Tariq ya zo shi da Faridarsa. Muhammad Sani da Nafisa tun da safe suka iso shi Jafar ma da matar shi Nauwara ma sun iso ranar duk da Kaduna za a ɗaura auran amma dai ya zo gida shima.
zuwa kuma yamma komai an kammale shi.
Za a yi waina amma an ba da ne a yi sai dai Tuwon da miyan anan gidan za a yi shi kuma Alalen Anty Bahijja ta ce namu ne mu surukai mu za mu yi tsakani ga Allah ta na son ɗora mana wahala. Hauwa da Muniira na bar ma jagoracin su da ya ke a nan gidan suka kwana ni kuma gidana na koma na kwana na ce musu in sun ga ban zo da wuri ba kar su jira ni su fara aikin daman sun san halina ba da wurin zan zo ba. Jidda nan ta kwana tare da yara sa'aninta ita kuma baby ta na tare da Gimbiya Yallaɓai ke faɗa mini ta kira shi a waya ta faɗa masa ta tafi da Baby gidan Naja acan za ta kwana.
Da safe sai da na sha barcina na gajiya. Yallaɓai ma a gida ya barni na dai shirya shi cikin wata dakakkiyar shadda mai ruwan ƙasa har da babban riga hula da takalminsa bakaƙe haka ma agogon fatan dake hannun shi na fesa masa turare na bishi da Allah ya kiyaye ba da motarsa ya je ba shi. Da shi da Tariq motar Uncle Abba za su bi zuwa Kaduna.
Motar shi kuma Muttaƙƙa zai tukata zuwa Kadunan shima ɗaurin aure 11 ne na safe tun takwas suka ɗau hanya.
Ni ina gida ma sai wajen goma da rabi na fita. Rahila ta kira ni ta ce za ta zo na ce sai ta zo domin ni ban gayyaci kowa ba Yaya Balki ma da ta yi mini mganar muna da biki ba gayya na ce ni ban yi gayya ba.
Sai dai in sun zo domin Allah Gwaggo daman ta ce sai bayan biki za ta je Allah ya sanya alheri.
Ma'u daman na san za ta zo balle Uwar ɗakin nata ne yan gaba gaba. Ko da na je su Hauwa sun gama alale Munnira na ta harara ta na ce su yi haƙuri na tsaya shirya Yallaɓai ne.
"Au to me Yallaɓai? Mu ma ai muna da mazajen da za mu shirya amman ba mu je ba sai ke mai Yallaɓai a 'a yallaɓiya"
Munira ta faɗa ta na mai ƙara ɓalla minibharara.
Ina dariya na ce" To ai ban hanaku ba. Da kun tafi kuma"
Hauwa ta ce" Mu tafi Anty Bahijja ta tsire mu ko? Daman da ba ki zo ba ta ce Munirra ta ɗau girman tun da ke ba ki daraja girman da Allah ya ba ki."
Ina dariya na ce" Ran Munirra ya daɗe. Zan zama mai yi miki biyayya."
Kafaɗata ta daka tana dariya. Hauwa ke faɗa mini Nafisa ba ta da lafiya ta na ta amai ba ta yin komai ba na ce yanzu haka ciki gare ta. Nauwara kuwa gidansu ta gudu har na zo ba ta dawo ba.
Shashen Marigayi Hajiya Karima muka gyara muka zauna tunda sauran duk ya na cike da jama'a Shashen Nene duk mutanen Rano ne Hajiyar Tafida ma da safe ta iso. Ni daman na yi wanka na a gida Jidda na nema na bata kayan da za ta saka da takalmi da mayafi saura na Baby ne an ce ba su dawo ba. Faridan Tariq kuma suna da ƴan uwa acikin gari can ta je ta kwana bayan ta dawo itama muna tare. Sameena ma sai a ranar ta so ashe ba ta nan ta je can Niger wajen dangin mijinta duk muna tare da su anan ɗakin.
Karfe sha ɗaya da mintina goma Nasir ya kira Munnira ya ce an ɗaura aure acan ma cikin gida an kira su Anty Bahijja sai suka fara guɗa suna ta iface ifacen murna. Sai wajen sha biyu muka sake wanka muka saka ankom mu. Ni na yi kitso amman ban yi ƙunshi ba saboda wacce ke yi min kunshi ta yi tafiya kuma wacce ta yi ma su Hauwa na ga kunshinta bai yi min ba sai ban yi ba.
Mu aka bari da wahalan raba abinci shi dai na yi saboda Mimisco ce ta kirani da kanta ta yi mini mgana shi ya sa na yi abin da ta ce.
Kafin bayan azahar kowa ka gani ya ci kwalliya sannan wasu sun ci sun sha ko na ce ana kan cin da sha ɗin. Sai a lokacin su Baby suka dawo an saka mata wani leshi mai duwatsu dogowar riga sai da na natsu na fahinci anko ne irin shi ne a jikin Gimbiya da Naja'atu da ƴayanta sun kuma saka musu ƙananun hijabi a saman kansu har takalmin su baki mai igiya iri ɗaya ne. Baby na ta murna ta nuna mini na ce kaya sun yi kyau na kuma yi ma Gimbiyar godiya ta na mirmishi ta ce mini bakomai.
A she ban sani ba har da Jidda sai can wajajen La'aaar na ga Jidda ta sauya atamfa ta saka kayan itama tana murna ta ce mini Anty Gimbiya ta yi mata na ce ta gode.
Rahila da Yaya Balki ne suka zo min biki domin ba zan saka Ma'u da ƙawarta a lissafina ba. Ni fa ban ma san ta zo ba sai da Yaya Balki ta ce kafin su fito sun yi waya ta ce musu ta na gidan tun ɗazu na ce ni kam ban san ta zo ba sai da suka ci abinci na raka su ɗakin Maman Farko suka yi mata Allah ya sanya alheri daganan muka shiga ɗakin Nene nan na ga abin mamaki Ma'u da ƙawarta shema'u filet ɗin abincin su cike da kaji da nama sannan suna tare da su Gimbiya da Anty Bahijja ana ta hira ana shewa.
Tana ganin mu ta tsargu ni ko da gangan na kalleta kafin na ce" Su Ma'u manya maso bare kiƙi dangi. Kin zo amman ba ki iya nema na ba?
Sai ta fara kame kamen ta nemi ni ba ta ganni ba sai tana taɓe baki kafin na ce" Muna shashen su Jawahir tare da su Hauwa."
Nan dai muka gaisa ni dai na kai su ciki su ka gaida Nene da Hajiyar Tafida bayan mun fito na ga sun tsaya suna mgana da Ma'u da shirina na yi tafiya ta. Allah ya so mu ma Mimisco ta ce mu ɗiba komai saboda namu baƙin kuma daman ina nemanta saboda ba a diɓar mana na mazajen mu ba, mun yi waya da Yallaɓai duk da sun yi reception a can akwai bukatar mu ijiye musu abinci.
Anty Maimuna na tare da baƙin ta dangin mijinta. Sulaihat na gani na ce ina Mimisco sai ta ce mini tana bangaren Hajiya iya sai na kalli Anty Bahijja ina faɗin.
" Anty Bahijja muna bukatar nama sannan da waina."
Kai tsaye ta ce" Duk wanda aka ba ku fa?
Nima kai tsayen na ce" To na mutane ne wannan, shi wannan da na ke magana na mazajen mu ne da suka tafi ɗaurin aure ne na yi ma Mimisco ma mgana."
Sai gabaɗaya suka kalleni har da Gimbiya.
Sai Anty Bahijja ta riƙe baki tana faɗin" To ma su miji. Mu namu mazajen da suka tafi fa? Ba su da rai ne ?
Ina dariya na ce" Kowa na shi ya sani Anty Bahijja. Ba zan hanaki ki ijiye ma Baban Sulaihat ba. Amma ni kam sai na ijiye ma Yallaɓai duk abin da na ci."
Naja'atu ta buga guɗa kafin ta ce" Kin burgeni Anty Sadiya. Shi ya sa Kawu dai ya fara ajiyan tumbi."
Ina mata dariya na ce" Ai na iya kiwo ne."
Ta ce kwarai kam. Sai aka maida mganar dariya Anty Bahijja ta miƙe ta na faɗin.
"Muje mai Yallabai."
Ta faɗa tana riƙo hannuna sai aka kara saka dariya ni ko sai na rike ta muka fita daga falon muna tafe tana ce mini wai shi Yallaɓan nan ba zai ci abinci acan ba ne? Na marairai ce na ce zai ci amman akwai tafiya kar ya dawo ya na jin yunwa.
A can shashen Hajiya iya muka je ta diɓar min waina da naman na je na kawo kula ta saka mini tana ta min tsiya Mimisco ta kare min da cewa abin da na yi mai kyau ne mata da dama in ana sha'ani sai su manta da mazajen su.
Ni dai na wuce na barsu ina zuwa na ce su Hauwa sun ci sun ƙoshi suna sakin tusa sun manta da mazajensu to ni na yunƙura na samo ma mazajen namu abinci sai suka fara min dariya nace su gode minibko na fasa ba su Munnira ne wajen gaba gaban gode mini. Su Rahila da wuri suka tafi kafin mangariba Ma'u kam tana gidan tawagan masu ɗaurin aure da amarya suka dawo. A shashen Hajiya Iya aka safki amarya da tawaganta. Ana yin mamgariba na kira Yallaɓai na tambaye shi ko yana ina? Ya ce min suna cikin gida a ɗakin Musbahu da kaina na yi lulluɓi na kai masa abinci da ruwa da lemu na san daman shi da Tariq da Uncle Abba ne nama daman da yawa na diɓar musu sauran na bar ma su Munirra domin na ga su ba su damu da cikin mazajen su ba.
Yallaɓai sai da ya rumgumeni ya ba ni sumbata a baki kafin ya ce" Allah ga baiwarr ka nan Halima Allah ka jiɓanci lamuranta kamar yadda take jiblɓanta nawa."
Daman sun ce yunwa suke ji. Suna ma shirin tashi su fita su je su ci abinci a cikin gari ne sai ga ni, Tariq dai ba baka sai kunni ya fara cin nama Uncle Abba kuma sai ya kalleni kafin ya ce" Sadiya na ce wai ba ki da yar ƙanwa ne a gida?
Gabaɗaya suka saka masa dariya nima sai da na dara kafin na ce" Babu Uncle Abba kana so ne sai a duba maka a dangi?
Sai ya ɗau naman kaza ya saka a baki yana tauna kafin ya ce" Ina tunanin haka na gaji da wulaƙancin da yaran nan suke yi mini. Yusuf a gabana bai ji kunyar kama mace ba ina kawun sa."
Yallaɓai na cin waina ya ce" Ba fa Mace ba. Matata na kama. Kawu kuma ai ban hana shi aure ba ko?. In ka ji haushi gobe a ɗaura ko Tariq?
Ya faɗa ya na kallonshi Tariq ya gyaɗa kai sannan ya ɗaga hannu Abba ya zungure shi da ƙafa yana faɗin" Shege sarkin cin abinci."
Ni dai gajiya na yi na fita na bar su domin ba za su fasa ba sai dai idan ba su haɗu ba.
Farida dai na faɗa mata ba ta damuwa Tariq na tare da Yallaɓai. Su kuma su Hauwa suka ce wai na yi musu wayau na kwashe tsokoki na bar ma mazajensu kashi ina dariya na ce" To wai na hana ku diɓar musu ne da farko? Bana son son zuciya fa. Ku dai cigaba da zama."
Ranar ma ban kwana ba gida na koma amman tare da Farida da Sameena su Munnira ma gida za ta koma ta kwanta Hauwa ce na ga tana shirin ƙara kwana na ce ta je gida ta kula da mijinta tun da ban ga abin da za ta yi ba in ta kwanan
Uncle Abba da Tariq Rano suka koma suka kwana Yallaɓai kan gida ya dawo su Farida a ɗakin su Jidda na sauke su da safe bayan mun karya mun yi wanka muka koma Gwammaja.
Sai a ranar muka shiga muka ga Amarya. Doguwa ce baka mai jiki. A shashen da muka zauna ajiya yau ma nan muka zauna da farko ba mu yi niyyar zuwa gidan su Anty Zabba ba sai da ta kira Munnira ta ce tun da mun zama yan amarya ta yafe mu shi ne yasa muka shirya bayan azahar muka tafi can anguwarsu ta Rijiyar zaƙi.
Da muka ce ga in da zamu a gidan kafin mu tafi, sai da Anty Bahijja ta yi ƙorafin ne zai kai mu? Ita da Anty Zulaihat wai ai da gangan ta ki sauka anan a yi biki gabaɗaya Mimisco ta kashe bakin su da cewa" Ku bar su je yana da kyau haka a matsayin su na surukan gidan nan"
Dole suka yi shuru. Mun je ma Anty Zabba biki da muka je har tana cewa ta yi fushi nima ta ce ko waya ban kira ba na bata hakuri.
Anty Zabba har ta ɗan rame amman kuma ta yi gayunta tsab da ita itama ta yi taro gidansu cike da mutane yaran nata sai a ranar da za mu taho suka biyo mu zuwa gidan kakaninsu a daran kuma aka zagaya da amarya duka ɗakunan gida mu ma aka tara mu aka yi mata bayanimmu ɗaya bayan ɗaya.
Washegari litini da wuri Ango ya ɗau amaryansa da Rakiyan ƙannensa mata su Anty Nasara suka raka su gidan su Anty Zabba suka haɗa su suka yi musu nasiha daga nan sai filin jirgi suka ɗaga sai garin fatacol sai fatan Allah ya ba su zaman lafiya ya kaɗe fitina.
Shikenan gida ya watse baƙi da nesa da na kusa zuwa talata duk sun koma gidajensu Gimbiya dai ta na nan amman na ji Hauwa na faɗin daga nan Abuja za ta wuce an kira su kan mganar rabon gado. Mganar aikin ta kuma Yallaɓai ya faɗa mini an dawo da ita nan office ɗin NGO da ke reshen Jihar kano. Amman sai ta dawo daga Abuja za ta fara zuwa aikin.
A lokacin da ya ke gaya minibsai da na tambaye shi.
"A wajen Nene za ta zauna kenan?
Sai ya gyaɗa min kai har yana ce min" Nene ma ta karɓe ta. Ta ce sai kuma aure zai raba su."
"Uhm!
Kawai na ce a lokacin amman ban iya sake mgana ba.
Sai bayan bikin Yaya Usman na samu damar yi ma Yallaɓai tuni kan Anniversery ɗin mu ya ce wallahi ya manta gwara da na tuna mishi. To shima zai ba ni kyakyawan surpise a lokacin in sha Allahu ina ta murna ina cewa ko Hajji za ka biya mini? Ya ce Allah ya sa haka.
******
Bayan wata ɗaya da bikin Yaya Usman. Kuma a yanzu dai muna cikin watan ramadan ne har mun yi azumi takwas. Da azumi ya gabato Yallaɓai bashi da kuɗi a hannu ya samu kwangilan aikin nan na kaduna akwai kuɗin shi da ya saka a ciki, to kuma ya saba duk shekara ana yi masa kunin sadaka Maman Saude sannan yana rabama yaran dake ƙarkashin sa kuɗi ko kayan abinci.
Wannan karon ma da bai da kuɗi kayan abinci mu a ciki ya ce. A ɗibar ma Mutakka da gidan su Saude. Yaran shi na Office kuma kuɗi ya ba su, sannan gidanmu kuma 30k ya ba ni na kai musu da ƙwai da yawa da dankalin turawa wanda Uncle Abba ya kawo mana an cire ƙwai a gidan gonan shi Dankalin ma shi ya kawo mana buhu a ciki na dibar ma gidanmu da Muttaƙa.
Nene ma Uncle Abba ya kawo mata kwai da kayan gona muma ma mun shaida su kwaiba da mangaro har muna kyauta. Muttaƙa ma Hauwa ta ce ya samu alheri tunda shi kaɗai ne bai kai su karfi ba. Geron da Mijin Mimisco ya raba ma su Yallabai a ciki ya ce na diɓar ma su Gwaggo sauran kuma a ka kaima Balaraba na kunun Sadaka. Duk da daman a gidanmu ba mu da matsala komai akwai Yaya Hamza da Yaya Auwalu da suke da ƙarfi sun wadata su da komai, sai dai ihsani da kyauttawa namu amatsayin su na iyayenmu.
Mijin Amina ma ya aiko da kuɗi sauran alherin da aka samu ta bangaren su Yaya Balki an tura shi can Yashe wajen su Baba Sani. Ko Mijin Ma'u mota guda ya kawo na kayan abinci Baaba ai tana cikin alheri shi ya sa Yaya Aina ta ce a can kura Baaba ce yar gaban goshi to tana da ƴa tana auren mai kuɗi kuma ana aika musu da alheri. Ni Rahila ke faɗa,mini har dangin Babanta da azumin nan ta kai musu alheri.
Gimbiya ta dawo wajen Nene da zama saboda aikinta. Sun je Abuja tare da ƙanin mahaifinta Tafidan Rano an raba gadon dukiya ta samu gida biyi anan Abuja da kuɗi masu yawa na tumanin takaba dukkansu huɗun rabon su kenan. Su gwara su da ƴaya ita bayan tumin takaba ba ta samu komai ba. Yallabai na ji suna waya kan tana son a saida gida guda ɗaya a siya mata a fili anan kano kuɗin ta kuma Mota ta ke son siya. Da ya ke komai sai ta yi shawara da shi abin da ya ce kar a yi ta bar shi kenan wanda ya ce a yi kuma shi take yi. Ta ɗan yi facaka da ƙudin bayan Mota ta siya manyan suturu da gwala gwalai, har su Jidda ta siya ma Takalma da dogayen riguna daga Dubai oder ma ta yi, sai yan uwa suka yi mata faɗa suka ce ta fara tunanin kasuwancin da za ta fara tunda kuɗin gado kamar ruwa su ke za su ƙare ba tare da ta yi komai da su ba.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/FAtGNQc8Y8pB008TuxFJVo
Eaman ScholarSphere.
Where ideas Take Shape.
WHAT WE DO.
ASSIGNMENT
PRESENTATIONS.
ARTICLES
PROJECTS.
BOOK
AND MANY MORE.
CANTACT US THROUGH.
02347067793152
MOTTO:
"Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures"
*🅿️18*
Azumi ya raba tsakiya, mun gama goma na marmari mun shiga goma na wuya kamar yadda hausawa ke faɗi.
Yau in muka kai azumi mun kai sha biyar kenan, a duka shekarun da muka kwashe da aure ni da Yallaɓai na saba duk watan ramadana Yallaɓai ba ya kaiwa dare a waje a gida ya ke yin buɗe baki tare damu haka ya sabar mana kuma nima haka na saba.
Amma wannan azumin sai al'amarin ya ɗan sauya. Saboda ya samu kwangila gina ma'aikatan nan na kaduna gabaɗaya ma'aikatan shi suna can kaduna shima yana zuwa har ya kwana ma kafin ya dawo sai ya zama na in baya gari sai dai mu yi buɗe baki tare da yara. Ranar da muka kai azumi na sha uku ya dawo daga Kaduna na yi masa har kunin tsamiya da ya ke matuƙar so, amman bai shigo gidan ba sai wajen tara na dare. Na kira shi a waya na ji ko bai dawo daga kadunan ba ne? Sai ya ce mini ya dawo ya na Gwammaja da ya faɗa mini haka har a cikin raina ban yi zargin wani abu ba, sai da ya dawo na kawo masa abin buɗe baki bai ci abinci ba,kunin ma kaɗan ya sha ya ce mini cikin shi ya cika a lokacin sai da na yi mamaki sanin Yallaɓai ba ya iya cin komai a waje sai ya dawo gida barin ma da azumi saboda ya san ina gida na shirya masa abin buɗe baki kamar yadda na saba.
"Ka ci wani abu ne a can Gwammaja?
Tambayar da na yi masa a lokacin kenan. Shi kuma kai tsaye ya ce mini Nene ce ta matsa masa sai da ya tsaya ya yi buɗe baki. Na ɗan yi mamaki saboda hakan bai taɓa faruwa ba ai Nene ta san ya na da mata me ya sa za ta ce sai ya yi buɗe baki a wajenta? Amma sai wata zuciya ta kitsa min kyakyawan Niyya cewa ita ɗin uwa ce a gare shi ta na da wannan damar kuma abu na rana ɗaya. Sai ko a fuska ban nuna masa damuwata ba na basar da komai ya wuce sannan ya faran tamin rai da ya ce da Asuba na ɗumama masa kuninshi ya na so ya yi sahur da shi.
Haka ko aka yi da asuba bai ci komai ba kunin na ɗumama masa ya sha da buredi ni kuma da yara muka sha tea sai na soya mana ƙwai muka haɗa da shi. Ranar kuma da wuri ya dawo gida muka yi buɗe baki tare ana kiran sallar isha'i ya yi alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi sallar tarawihi kamar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 31