min dariya, nima mirmishin na yi sannan na koma na kwanta na lulluɓa da blanket ina tuna sunan da ya kira ni da shi, ko a baya a gida in aka kirani da wannan sunan sai Alhajinmu ya yi sharia faɗan ke rabuwa, Allah ya jiƙan Mama da Rahama ita ta lanƙayamin sunan nan da har gobe bana kaunarsa.
Ƙara gyara kwanciya nayi, ina tunanin me kuma wannan karon aka je aka gaya ma Alhaji akan abin da ya faru tsakanina da Ma'u?
Wayata na zura hannu na ɗauko na shigar da kaina cikin blanket ina duba wayar tawa, Missed calls na Rahila ba adadi tun jiya take kirana ban ɗauka ba har Yaya Murja na ga ta kirani har da Ma'u, kai matar nan ba karamar makira ba ce, uban ta zan yi mata da ta kirani bayan sun haɗu ita da ƙawarta sun ci mini mutumci? Kwafa na yi ni kaɗai na buɗe data ina ganin saƙonni na ta tururuwan shigowa, abin da ya fi jan hankalina ganin group ɗina gidanmu na S. YASHE'S sai faman tagging ɗina ake yi ko shiga ban yi ba saboda nasan zagi nake sha wajen su Yaya Abubakar tunda an taɓo yar gwal wacce ba ta laifi a wajensu, su na ba ni mamaki ta ya ya za ka yanke ma bangare ɗaya hukunci ba tare da an ji bayani daga ɗaya bangaren ba? Na rasa gane wani irin tasiri Ma'u ke da shi a wajen yan gidanmu da suke fifita damuwarta sama da damuwar ni da nake ƙanwarsu jininsu.
Na ga Yaya Murja ta min Vioce note mai tsawo ko buɗewa ban yi ba, na ga ma mganar Yaya Abubakar naga dai a farko ya ce Sadiya ke wai ba ki jin mgana ko?
Sai saƙon Rahila rututu wajen ashirin na tsaki ma na kashe datan ta je ga ta ga Ma'un ta zaɓe ta sama da ni yar'uwanta da muke uba ɗaya, wulla wayar na yi can gefe na sake gyara kwanciya ina tunanin abin da zan gaya ma Alhaji, ba ni da damuwa da Yusuf saboda nasan halin mijina ɗan ba ruwan shi ne duk abinda na ce masa zai ce ya yi dai dai ne, mutum ne mai ƙoƙarin girmama duk wani abu da nake so da wanda ba na so duk da baya sanin wasu rigimgimun dake tsakanina da Ma'u amman shi shaida ne ni da ita ba ma ga maciji.
Rufe idanuwana na yi ina tuna abin da ya faru a shekaranjiya asabar wajen sunan ƴar ƴar'uwata da muke uba ɗaya Rahila wacce muka taso tare tun muna yara aure ma rana ɗaya aka yi mana. Tsabar baƙin ciki sai da na ji taruwan ƙwalla na yi saurin shanyewa, daga kan gado ina jin mganar Yusuf ta haraban gidan tunda window ɗakin na ta wajen haraba kenan su Jidda ya raka Salisu mai mashin ɗin da yake kaisu makaranta ya zo, ina kuma kwancen ba jimawa ya shigo ɗakin sai na yi luf kamar ina barci ina jinsa ya zo ya ɗauki wayarsa da laptop ɗinsa sannan ya kashe min hasken ɗakin ya fice bayan ya rufo min ƙofar. Sai na koma na ƙara lafewa na lumshe ido ina wani tunani a cikin raina ban sa na furta a fili ba sai da na riga na furta cewa" Ya Allah ka ƙara bani haihiuwa ko guda ɗaya ne na ƙara haifa."
Idanuwana suna yi wani luu kamar zan fashe da kuka in na tuna wautar da kuruciyar da na tafka a zamanin baya gashi yanzu abin da na aikata na neman ya zo ya dame ni.
Barci ya kwashe ni sama sama ban daɗe ba na tashi saboda na ji karan ruwa a Tiolet kenan Yusuf ya shiga wanka sai na miƙe duk da ina jin kasala na saka takalma na tsakar gida mai taushi na fita daga ɗakin na buɗe kofar kitchen ɗina na shiga mai girma ne, irin kitchen ɗin zamani amman ya yi kaca kaca saboda manya sun yi aiki mirmishi nayi Jidda, ba ni ta biyo ba karsashinta irin na Babanta ne amman da ni ta biyo ba za ta iya taimakamin kamar yadda take taimakamin yanzu ba, ta yi ma Baby wanka ta shiryata sannan ta shirya kanta ta kuma yi musu abin karyawa da na tafiya makaranta sai in naga dama na ke fitowa na yi wani abun. Gyara kitchen ɗin na yi sannan na dora ruwan tea bayan na saka haɗe haɗen ganyen shayi. Nima doyar na fere na soya mana sai na yi mana yar source ɗin miya ta albasa.
Na kwshe komai zuwa dining kenan Yusuf ya fito cikin shirin fita, sanye da shadda mai ruwan ƙasa dinkin riga da wando tazarce da hula a saman kansa kuɓe takalmin kafarsa mai buɗewa ne baƙi
A falon muka haɗu yana ta tashin kamshi sai na tsaya ina kallonsa har sai da ya tsole min ido kafin ya ce"Kallon fa? Na koma miki saurayi ne?
Mirmishi na yi kafin na ce" Ko da yaushe Saurayi ka ke a idanuwan Sadiya Injiniya Yusuf, ina kallon ka ne kamar yau ɗin ne na fara ganinka a hanyar dawowata daga BUK a wata ranar laraba."
Na faɗa ranar ta na dawo mini a cikin tunanina a tare muka saki mirmishi, kujera na ja masa na dining ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin"Na ce ƴan mata doguwa sallamu alaikum ba, ki ka wani juyo kina min fari da ido kika juya kika cigaba da tafiyarki"
Ina dariya ban yi mgana ba ina tsaye ina haɗa masa tea shi kuma yana faman kallona, basarwa na yi ina faɗin" Yau sai ka shirya ba ka jirani na zo na shirya ka ba ko?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Na bar Sadiya yar laushi ta huta ne."
Da gangan na ɗiga masa ruwan zafi a hannunasa dake ɗaure da agogon fata baƙi, da sauri ya cire hannunsa a wajen ya na yarfewa ni kuma sai na haɗe rai ban ma kalleshi ba, cikin kallona ya ce"Sadiya bayan Tekwondon ɗin dare kin fara na safe ne? Kafarsa na taƙa dake cikin Takalmi da sauri ya janje kafarsa ya na faɗin"Akwai matsala kam."
Ina tura masa Mug ɗin tea
ɗin gabansa da Doyar da na saka masa amman ban kalle shi ba. Na juya zan tafi ya riko hannuna amman sai na ƙi juyowa daman raina a jagule ya ke, amman sai ya yi tunanin mganarsa ne ya ɓata min rai, tasowa ya yi ya rumgumeni ta baya yana faɗin"Kin ji haushi ne? To Allah ya baki hakuri Sadiya ta."
Mirmishi na saki ina riƙe hannunsa kafin na juyo da shi muna fuskantar juna, gemunsa na shafa zuwa sajensa kafin na ce"Ka ji ka wani haushi? Sadiya ce fa da Yusuf? Ka manta.? Sai ya duka ya sumabaci goshina tunda ya fi ni tsawo kafin ya ce"To ai na ga za ki tafi ki barni ni kaɗai ahalin ba haka muka saba ba."
Da sauri na ce"Ruwa zan ɗauko kasanni da shan ruwa"
Tuna haka yasa ya sakar min hannu na fice daga falon zuwa falo na biyu kitchen na koma na ɗauko karamin mug na koma wajen depenser na tsiyaya ruwa mai ɗan sanyi sannan na koma falon na ja kujera gefensa na zauna muka fara karyaawa.
Amman ni ba wani ci nake yi ba sai juya cokali na ke yi yana ta min hira kan wani kwangila gina makaranta da aka ba kamfanin shi sun gina wajen shekaru biyu ba a biya su kuɗin aikinsu ba to daman an kira shi tun wancan sati ana saka ran payment ɗin shi ne ya ke ta mini surutu ba na wani fahimta gabaɗaya natsuwata ba ta tare da ni
Sai da na ji ya na kiran sunana.
"Sadiya."
"Sadiya."
Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalleshi idanuwana sun yi laushi kamar zan yi kuka.
Daƙatawa ya yi da cin abincin ya na mai ƙure ni da ido kafin ya kira sunana cikin yanayin da yakan kirani a duk lokacin da ya ga na shiga damuwa.
"Sadiya."
Na kalle shi amman ban amsa ba cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce" Me ke damun ki ne? Tun fitowata na lura da yanayin ki ya sauya."
Da sauri na yi mirmishi kafin na ce"Haba. Bakomai fa kawai ina tunanin kiran me Alhaji ke yi mana ni da kai?
Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya saka hannu ya rike min hannuna guda ɗaya yana faɗin"In dai kan wannan ne karki damu ba komai, ina tunanin kawai kila Alhaji na son ganin ki ne, kin san fa ke dubu ce."
Ya faɗa da sigan zolaya duk dai ya sakani dariya kuma sai da na dara, ya manta ko wancan satin ni da yara acan muka yi ni sai dare ya je ya ɗauko mu. Amman ba na son na kawo masa mganar Ma'u shi ya sai na bar shi a hakan na san halin shi in har bai ga na saki ba ba zai fita gidan ba ko ya fita to cikin damuwa ne shi ya sa na saki jiki muka karya muna mganganumu na soyayya da muradi kamar yadda muka saba.
Bayan mun gama tare muka koma ciki ya wanke bakinsa nima na wanke duk da ban yi wanka ba. Yana riƙe da hannuna har falo ya ɗauki laptop ɗin sa na karɓa da wayarsa na rike masa shi kuma da key ɗin motarsa a hannu na rakashi har haraban gida na saka masa kayan a gaban mota bangaren mai zaman banza shi kuma ya je ya buɗe get sannan ya dawo ya rumgumeni muka sumbaci juna sannan ya sake ni yana faɗin"Karki damu in na dawo gida da wuri sai mu je mu ga Alhajin ko?
Sai na gyaɗa masa kai, na buɗe masa gaban mota ya shiga ina ɗaga masa hannu yana ɗaga mini har ya fita daga gidan ya tsaya sai da ya fito ya rufe get ɗin ya ɗaga mini hannu nima na ɗaga masa a fili na furta"Allah ya dawo mini da kai lafiya yallaɓai na."
Cikin gida na koma na zauna a falo kawai rumgume da cussion ina tunanin rayuwa, na ɗan lokaci sannan na tashi na koma ɗaki na yi wanka na yi shigar doguwar rigar wani material mai maroon da baki sai na saka baƙar hula, ina cikin shiryawan na ji ana buga get daman na ce Saude ce ganin shuru ya sa sai ta kira wayata ina ɗauke da wayar na fita zuwa can haraban gidan na buɗe mata kofar, wata yar budurwa ta shigo tana a faɗin.
" Anty hala barci kike yi ne ina ta bugu ba ki ji ba?
Kai tsaye na ce"A'a na yi wanka ne ina kan shiri ne."
Gaisheni ta yi na amsa ina faɗin" Ya su Balaraban ? Ta amsa min da lafiyan lau suna gaisheni.
Ina gaba tana bin bayana har cikin gida falo na biyu na shiga bayan na kalli Saude ina faɗin"Akwai sauran abin ƙaryawa a dining ki ci sannan ki fara aikin"
Da to ta amsa min sannan na shige ciki na rufe ƙofa. Saude kenan mai zuwa tana mini aikacen aikacen cikin gida. A can anguwan mu na Ɗorayi ta ke, makota suke da gidanmu.
Saboda ba na son zaman shuru ya sa na kunna Tibin a tashar MBC3 ina ga Baby ta kunna sai ban sauya ba suna haska cartoon ina kallo saboda yara. Ya ɗan fara ɗaukan hankalina kiran wayata ya katse ni ina duba mai kira sai na ga RAHILANMU ce ke kirana.
Karamin tsaki na ja har sai da ta katse ban ɗaga ba sai da ta ƙara kira gabda za ta katse sannan na ɗaga bayan na saka a amsa kuwwa a fusace ina faɗin" Wai me zan yi miki tun jiya kike ta faman kirana?
Daga can bangaren Rahila ta ce" Kai Sadiya daman kina ganin ina kiran ki shi ne kika ki ɗauka? Kai tsaye na ce"To me zan yi miki?
Rahila ba ta ji haushi ba ta ce" Yi haƙuri na ga jiya ba ki dawo ba ne Sadiya."
Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" To na zo na yi miki mene Rahila? Ai Ma'u na nan za ta iya miki abin da ni ba zan miki ba ma."
Daga can bangaren Rahila ta ce"Haba Haba Sadiya wai ke abu ba ya wucewa a wajem ki? Jiya nan fa Ma'u har da kukanta ta ce ita wallahi ba ta ji daɗin abin da ya faru a tsakanin ku da shema'u ba a gabanmu fa har da yaya Murja ta kira ki baki ɗauka ba, me kike so a yi miki Sadiya.?
Karamin tsaki na ja kafin na ce" Munafuka kawai,."
Rahila ta ce"Don Allah Sadiya ki daina wannan ƙiyayar ga Ma'u. Yar uwanki ce fa."
Rahila ta magana kamar na kifa mata mari ta cikin wayar haka na riƙa ji.
Wai Ma'u ta na kuka a gabansu Yaya Murja, takaici ya hana ni mgana ina jin Rahila na ta wa'azin ta na fama akan na manta komai na rumgumi Ma'u.
A fusace na ce"Allah ya tsari Sadiya da ta rumgumi Ma'u. Kamar yadda ba na kaunarta itama ba ta ƙaunata amman kun kasa ganewa, shi ya sa har da Alhajimu kuka haɗa ni, ku kuka sani ga ku ga Ma'un nan tunda kuka zaɓe ta shikenan amman in dai ta na waje ina waje sai dai ɗaya ya hakura ya bar ma ɗaya."
Rahila ta ce"Ni ban gaya ma Alhaji ba sai dai in su Yaya Murja ne."
Baƙi na taɓe kafin nace"Koma waye ku kuka sani. Ai an taɓa yar gwal dole a je a kai ƙarana wajen Alhajin mu mana"
Rahila ta sauke kai tana faɗin" To ki yi hakuri Sadiya don Allah."
Kamar ba zan yi mgana ba sai can na ce"Uhm"
Rahila ta yi dariya kafin ta ce"Sadiyar Dubu tawa, ga naman sunan ki a hannuna fa."
Kai tsaye na ce" Ban so. Ki haɗa ma Ma'u duka ki aika mata."
Ban ba ta ma zarafin mgana ba na yanke kiran ina ƙara jin takaicin kaina da na tsaya ma ina sauraranta alhalin nasan Rahila ta fi shaidar Ma'u sama da ni da muke jini ɗaya.
Ƙwafa na yi a raina ina tunanin in muka je gaban Alhajinmu zan fito masa a mutum kawai gwara ya raba tsakani na da Ma'u kowa ya yi sabgarsa zai fi alheri.
*Janafty.*
*25/09/2024*
*11.03am.
*Wednesday 07/05/2025*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY).*
*FATAN ALHERI GA AMINIYATA AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH), ITA ƊIN TA DABAM CE A WAJENA. NA GAISHE KI*
*NA GAISHE DA IYAYEN ƊAKINA*
*ZAINAB INUWA(AUNTYSIS)*
*HAJIYA LUBABATU MUSA*
*KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)*
*HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM*
*ANTY AISHA AHMAD IYA*
*ANTY ZAINAB ABDULWAHAB*
*HAJIYA HALIMA ƊALHA SHEHU.*
*ANTY HADIZA MAHE MUHAMMAD*
*ANTY HAIRI*
*ANTY FADILA KABIR*
*ANTY FIDDAUSI KABIR*
*FATAN ALHERI NA GODE*
*JINJINAN TURKEN GIDA ZUWA GARE KU*
*MARYAM JUMARE.*
*MARYAM(KITTY)*
*HAFSAT HAFNAN(SAHIBATU)*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z
*🅿️02*
Ina zaune a wajen Rahila ta ƙara kirana sai na danna mata busy. Ina mai ƙara sakin tsaki ni kaɗai ƙara miƙe kafata na yi a saman kujera mai zaman mutum biyun da nake zaune akai ina mai ƙara jin wani takaicin na ƙara cika min zuciyata. Rahila ba ta haƙura ba sai da ta ƙara kirana har wajen sau uku ina kashewa sannan daga ƙarshe sai ta turamin saƙo.
Na ba ma Hubby saƙon ki da zai fita, zai biya gidan Bulo ya ba ma Musabahu. Zai kawo miki ko kuma in ya haɗu da Yallaban na ƙi ya bashi ya kawo miki. Ki yi haƙuri."
Ba saƙon ne ya ba ni dariya ba sai Hubby da na ga Rahila ta rubuto mini shi ne ya sa ni tsintsirewa da wata dariya mai sauti wanda har sai da Saude da ke kichen ta leƙo tana faɗin"Lafiya Anty?
Ina dariya na ɗaga mata hannu ina faɗin"Bakomai Saude. Ci gaba da aikin ki."
Sai ta amsa min da kai ta maida ƙofar kitchen ɗin ta rufe ta bar ni nan zaune ina ta faman dariya. Wai Yaya Muntarin ne Hubby kai in na tuna da sunan ma sai na ji wata ƙarin dariya ni dai ban taɓa katarin Rahila ta kira shi da wannan sunan ba. Baban Islam na san tana kiran shi dashi ko Yaya Muktar ɗin da ta lankayamai amman yau shi ne karon farko da na taɓa jin ta kira shi da sunan Hubby.
Ina dariya ina tuna wani zamani a can baya ina jin na kasa riƙe dariyata. Har sake karanta saƙon na yi ina dariya a fili na furta" Tab! su Rahila masu Hubby manya."
Saƙon Rahila shi ya tafi da kaso mafi girman ɓacin rai na, har na ji zuciyata ta yi sanyi, ban jima a falon ba na miƙe dauke da wayata ta kitchen na bi saboda daga kichen ɗin akwai ƙofar da za ta sadani da ƙofar koridin Bedrooms ɗina.
Saude na gani a rakuɓe kamar wata bakuwa tana cin doya, a tsugunne ba ta san ma na shigo ba a saman kanta ta ɗago kawai ta ganni harara na ɓalla mata kafin na ce" Wai ban hana ki wannan ɗabi'ar ba Saude? Nan gidan baƙon ki ne? Cin abinci a tsugunne kamar an hana ki zama a in da kika ga dama?
Da sauri ta ɗago tana faɗin" Yi hakuri Anty, daman na ga ina sauri ne shi ya sa ban zauna ba." Ƙaramin tsaki na ja kafin na wuce ina faɗin"Ke dai kika sani, ki kuma cire hijabin nan saura na fito na ga kina aiki dashi kamar wata yar gudun hijira ki ga yadda za mu kwashe da ke a cikin a gidan nan."
Dariya ta yi har ina jin sautin ta kafin ta ce" To Anty."
Ni kuma Bedroom ɗina na koma kan Dressing ɗin mirrow ɗin da ke ɗakin na ijiye wayata na koma na kwanta har da shigewa bargo. Har ga Allah na ji ana ta kiran wayata amman ban mai da hankalina ba, na ɗauka yan gidanmu ne kan maganar ƴar gwal Ma'u shi ya sa ban ko motsa daga cikin bargon da na ke kwance ba afili ma sai da na yi ƙwafa kafin na ce"Ku ci kan ku." Na ƙara shigar da kaina cikin bargo ina ƙara gyara kwanciyata.
Barci ya fara ɗauka ta domin har na fara wani mafarki mai ɗan karan daɗi, kamar daga sama na ji muryan Saude ta na kirana.
"Anty. Anty.."
A firgice na tashi saboda a saman kaina a can cikin barci na ji kiran sunan.
Saude na gani a cikin Bedroom ɗina daga can baƙin kofa, tana ganin na tashi zaune da sauri ta ce"Anty kin yi baƙuwa."
Yamutsa fuska na yi kafin na maimaita kalmar" Baƙuwa?
Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce"E. ta ce na faɗa miki Bahijja ce."
Shuru na yi ina tunanin wace ce kuma Bahijja, ido na ɗan waro kafin na yi saurin yaye bargon jikina na sauko daga kan gadon lokaci ɗaya ina faɗin" Tana can falo ne?
Saude ta gyaɗa kanta kafin Ta ce" E. tana can falon farko."
Kai na gyaɗa kafin na ce" Je ki ce mata gani nan zuwa Saude." Ta amsa min cikin ladabi sannan ta buɗe kofa ta fita ta barni ina sauke numfashi.
A gaban madubi na tsaya ina kallon fuskarta sai da na tabbatar da ba ni da wani abu da za ta kalla ta yi ƙorafi sannan na gayyato mirmishi da fara'a a saman fuskata sannan na zura takalmina mai taushi na zirga zirgan cikin gida, na zo zan gota ta jikin madubin sai da na ƙara tsayawa na kurama kaina ido ta cikin madubin ina jin gabbaina suna yin wani irin sanyi ƙalau, yanayin jikina na bi da kallo tabbas ina da son gayu da gyara ni macece da kana ganina kafin ma a faɗa maka wani abu akaina za ka sha shaida ina da son gyara, tun da ga kan gyaran fata na gashi da gyaran ƙasa na mace duka ba na wasa dasu bangaren gyaran fata kayan AISHA LAME +234 703 666 2633 na ke amfani da su, in kuma bangaren kayan ƙawa na gayu ne tun da ga kan atamfofi da abayoyi da takalma a wajen DIJA COLLECTION na kan yi siyayyata da ga ni har su Jidda shi ya sa kayana tare da na ƴaƴana muka fita dabam a cikin Dangi.
Numfashi na ja sannan na ƙara fesarwa, wayata na ɗauka sannan na fice daga ɗakin ba ta kitchen na bi ba sai ta bi ta korido tunda falon farko zan je, ina tafe ne ina latsa wayata na ji na tsorata lokacin da na ga cikin waɗanda suka kirani har da Anty Bahijja, lalle yau Allah ne kaɗai ya isa ya cece ni daga ƙorafi da ƙananun mganganu sai wanda kunnena suka iya ji, ina tura ƙofar falon lokaci ɗaya tare da sallamata da kuma tahowa da fara'a a saman fuskata.
+234 903 661 7473
Ta na hakimce kan kujera mai zaman mutum ɗaya, sanye da dogon hijabi mai ruwan kuka har da liƙabinta, kenan daga makaranta take, ta biyo ta nan ina nufarta ina washe baki lokaci ɗaya ina faɗin"Maraba da Anty Bahijja."
Sai a lokacin ta ɗago kanta daga duba wayarta da take yi, sai da na kariso gabanta na zauna saman kujera mai zaman mutum ukun da take gefenta ina faɗin" Ina kwana Anty Bahijja."
Sai a lokacin ta iya ɗaga likaɓin ta sama fuskarta ta bayyana.
Cikin yanayin maganarta ta kalleni daga sama har ƙasa ni kuma ina ta faman yi mata mirmishi.
"Barka dai ta tashi gimbiya ko na ce Sadiya yar laushi ba"
Wani abu mai ɗaci ya taho daga cikina ya tokare a saman ƙirjina. Shi ya sa har abada ba zan taɓa ƙaunar Ma'u ba, kuma ni da ita ba za mu taɓa zama a inuwa ɗaya ba. Amman ban nuna mata ba sai ma na ɓige da yin wani kayattacen mirmishi kafin na ce"Kai Anty Bahijja, ki yi haƙuri kin kirani ban ji ba. Na ɗan kwanta ne."
Baki ta taɓe kafin ta ce"Ai fa aikin kenan barci, kina ciki kin kwanta yar aiki na yi miki aikace aikace"
Kai tsaye nima na ce" Saude ai tana zuwa tana taimaka mini ne, kinsan aikin gida da yawa Anty Bahijja."
"Ina wani yawa a aikin gidan nan Sadiya? Kawai daman kin saba da hutu shi ya sa kike kallon shi a matsayin aiki."
Ni ko sai na yi mata mirmishi duk da maganar ta na sukan zuciyata amman sai na ɓoye hakan a saman fuskata. Kai na kaɗa kafin na ce"Hutun ne ya zo Anty Bahijja amman karki manta a baya nima na yi aikin."
Ta san magana na gaya mata shi ya sa ta yi mini wani kallo, ban bari ta samu damar magana ba na cigaba da faɗin" Kuma Anty Bahijja laifi ne in mace ta samu hutu ta huta a gidan mijinta? Kema fa kina da yar aikin nan sannan ki na fatan nan gaba in su Sulaihat suka yi aure suma su samu gidan da za su huta ko ba haka ba ne? Ba fa wanda ba ya son jin daɗin nan fa."
Na faɗa ina kallonta saboda na ga kuma wata magana za ta ƙara faɗa mini, sai na ga ta juyar da kai ta na faɗin"Ba irin na ki ba Sadiya."
Ban yi magana na nima sai na kauda kaina ina ɗan mirmishi, na rasa wani hutu suke hangomin a cikin wannan gidan? Sun manta a baya komai na gidana da mijina da ƴaƴana ni nake yi ma kaina? Saude ba ta fara zuwa mini aiki ba sai bayan mun tare a wannan sabon gidan amman gabaɗaya ƴan'uwan Yusuf gani suke yi da kuɗin ɗan'uwansu na ke walwali ina haskawa sannan na samu duniya ina ta jin daɗina.
Ban ƙara ce mata ƙala ba, amman ita sai faman kalle kallen falon take yi tana wani taɓe baƙi, ba yarinya ba ce tunda Yayar Yallaɓai ce, daga ita sai shi tana da manyan ƴaƴa amman ba taba aurarwa ba suna karatu ne.
Can ta ga ji da zaman mulkinta ta kalleni ta na faɗin" Su Jidda suna makaranta ko?
Sai na gyaɗa mata kai, kafin na yi magana ta rigani da cewa" Kuma sai satin nan ba ki kai su gidan Yaya Maimuna ba? Me ya sa ?
Daman na san rashin zuwan su gidan Anty Maimuna sai ya zame min abin magana, zama na gyara kafin na fara faɗin" Ba su samu zuwa ba. Amman weekend ɗin nan in sha Allahu za su je."
Anty Bahijja ta ƙara faɗin" Me ya sa na ke tambaya?
Kai tsaye
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 31