rina. Ma'u na so ta haɗa mana yaƙi a gida Yaya na sonta ita kuma tana son ƙani.
Cikin lokaci kawai na ji ana mganar haɗa auran Yaya Hamza da Ma'u da kuma Rahila da Muntari. Yaya Abubukar kuma Alhajinmu ya ce fito da matar aure. Ba shi da mafita illah ya amsa Gwaggo ta so ta yi magana sai na ji sa yana roƙonta ta bar mganar shi da Hamza duk abu ɗaya ne. Kowa ya ji ba Yaya Abubakar ba ne sai ya yi mamaki saboda shi dai Yaya Hamza kowa ya san halin shi. Shi kuma Umarni kawai Alhaji ya bashi, shi kuma bashi da mafita. Amman kwata kwata bai taɓa hasaso da ya auri Ma'u ba. Da farko da aka sanya lokaci na yarda makaman yaƙina ganin har Alhajinmu ya ba ma Yaya Hamza umarnin dawowa gida ya ga Ma'u ya kuma dawo sun gana Ma'u ta yi ta rawan jiki ita a dole burinta ya cika. Sai dai me Yaya Abubakar ya kasa ɗaukan takwallalin ya haƙura da Ma'u ya fara rama a tsaye ga yawan ciwo ina tsoro kar rashin tausayin Ma'u ya kashe min ɗan uwan na yi ta kulla yadda zan yi na rasa mafita.
A wannan halin an saka ranar auran su da zaran mun ƙara zana jarabawar sakandiri a karo na uku. Yaya Muntari ya samu aiki da wani kamfanin sarrafa leda. Shi kuma Yaya Hamza ya fara aiki da bankin first bank a can ibadan ɗin. Ni ba kaina na damu dashi ba saboda ban samu miji ba daman kuma ni burina sai na gama jami'a zan yi aure.
Muna gabda gama zana jarabawarmu kawai Yaya Abubakar ya fara wani ciwo har da kwanciya a gadon asibiti ganin haka yasa na ce ba zan bari Ma'u ta kashe mini ɗan'uwa.
Ni na je na samu Hajiya Dubu na faɗa mata duk abin da na sani. Ita kuma ta samu Alhajinmu ta faɗa masa abinda ke faruwa ni na ba da shaidar Gwaggo ma ta sani da aka kirata sai ta amsa amman ta ce Abubakar ɗin ya ce a bar mganar kar kowa ya sani kuma itama tana ta tabbacin ciwon nan saboda Ma'u ne. Alhajinmu bai yanke hukunci ba sai aka sallamo Yaya Abubakar daga asibiti Alhajinmu ya taramu a gaban kowa da kowa har da masu auran da Yaya Hamza da Alhaji ya sa ya dawo garin.
A gaban kowa da kowa ya tsitsiye Yaya Abubakar sai da ya faɗi gaskiyan yana son Ma'u duk yadda ta yi ta masa inkiya da ido kar ya faɗa. Har Baaba an kirata tana wajen jin haka shima Yaya Hamza ya ce ya bar ma ɗan uwansa shi daman baya sonta.
Hankalin Ma'u da Baba ya tashi saboda Alhajinmu ya ce an maida auran Ma'u akan Yaya Abubakar kuma ya yi ta faɗan cewa ba domin na zo na faɗa ba da an yi auren kuma azo ana neman mafita. Ban manta kallon da Ma'u ta yi mini a wannan lokacin ita da Baaba. A kuma nan take ta fashe da kuka ta ce ba ta son Yaya Abubakar Yaya Hamza take so shi kuma ya ce a ƙanwa ya ɗauketa. Alhaji ya rasa mafita yace zai yi mgana da sauran yan uwanshi. Har sai da su Baba Aminu su ka zo garin. A ɗakin Hajiya suka zazzauna suka tattauna Hajiya Dubu saboda samar da masahala sai ta kalli Alhaji kafin ta ce
"Sule a shawarata kar ka matsa ma Ma'u ko Hamza. Tun da Hamza ya ce baya so. Abubakar ma yace ya hakura da ita to mu fasa wannan al'amarin kowanensu ya nemo mata itama ta nemo nata mijin mu aura musu sai na ke ganin kamar in muka yi haka za a samu mafita."
Su Baba Aminu ma sun aminta da shawaran Hajiya kuma ita Alhaji ya ɗauka aka warware mganar auran Ma'u da Yaya Hamza har da Yaya Abubakar ɗin bayan an ce kowannen su ya zaɓo na shi matar daga waje. Wannan lamarin shi ya ƙara rura wutar kiyayya tsakani da Asma'u.
Kwana biyu da faruwan lamarin na samu salama saboda ko banza itama ba ta samu abin da take so ba. Sannan Yaya Abubakar ba zai ga laifin Yaya Hamza ba. Ina kwance a saman gadon Hajiya ba ta ɗakin tana makewayi Ma'u ta shigo har ɗakin ta tsaya a kaina.
"Lafiya Ma'u?
Idanuwanta jajir ta kalleni kafin ta fara mgana cikin zafi."
"Wallahi na tsane ki Sadiya. Na tsane ki."
Nima kai tsaye na ce" To ai nima ba sonki nake yi ba Ma'u."
Sai kawai ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Tun da kika zama silan rasa burina Sadiya ina so ki rubuta ki ijiye na rantse da sarkin da ke busamin numfashi sai na kuntata ma rayuwarki sai na saka ki a uku fiye da yadda kika sakani ko kin samu farinciki sai na yi sanadiyar lalatashi zuwa baƙin ciki. Kamar yadda na saba cin nasara akanki haka zan cigaba da nasara akanki har ƙarshen rayuwarki.".
Kai tsaye nima na kalleta kafin na ce"To in kin fasa. Ta Allah ba ta ki ba. Aniyar ki sai dai ta biki. Kuma ban yi nadaman abin da na yi ba. Da ki ɓata mana zuru'a gwara ke ki rasa na ki burin na zalunci."
Sai kawai ta yi kwafa ta fice a ƙofar ɗaki suka haɗu da Hajiya tana kiran sunanta ta yi banza ta wuce da ta shigo sai ta tambaye ni ko mun yi faɗa da Ma'u ne? Ina komawa na kwanta na ce" Ni ina ruwana da ita."
Hajiya na faɗin" Sai hakuri ki rika kyaleta yanzu kin san ga abin da ya faru.'
Ina jinta ban tanka ba.
Tun faruwan lamarin bayan wani lokaci Ma'u ta warware Yaya Abubakar ɗin ma da sauƙi. Ta nuna ma kowa ba komai amman ni nasan ba ta hakura ba. Tsakanina da ita sai ya ƙara lalacewa. Ko da yaushe in ta fakaici idon mutane sai ta gaya min mgana nima sai na rama haka dai muka yi rayu cikin bata sona nima bana sonta. Jarabawar mu ta fito cikin ikon Allah ni da Ma'u muka samu ban da Rahila ba ta damu ba tunda aure za ta yi ni kuma ina ta murna zan fara jami' a.
Alhajinmu ya so ya hana Yaya Hamza ya matsa masa aka nema min gurbin karatu a jami'ar bayero a shashen tsumi da tattalin kasa economics. Ma'u kuma ta ce bording za ta yi sai aka nema mata Federal University Minna ko na ce ita ta nuna tana bukatar can ɗin.
Saboda lamarin da ya faru bikin Rahila da Yaya Muntari ba a ma ƙara mganar shi ba sai zuwa gaba in zukata sun huta.
Yaya Auwal kuma yana can keffi sai salla sallah ma ya ke zuwa ganin gida wani abun ma sai dai ya ji labari bai san faruwan shi ba.
Na fara zuwa jami' a farkon shekaran 2002. Ma'u ma a shekaran ta tattara ta tafi Rahila kuma tana gida amman auran su da yaya Muntari ana tunanin karshen shekara tun da shima ya cigaba da karatunsa.
A kuma lokacin ne Allah ya yi ma Hajiya Dubu rasuwa. Rasuwan da ta gigitani matuka. Na yi kuka domin har daren da za ta rasu mun kusa raba dare muna hira sai dai mun wayi gari ba ta raye tabbas ni aka yi ma mutuwa. Rasuwar Hajiya dubu da wattani uku lokacin muna jarabawar semester farko a makaranta na haɗu da Yusuf Muhammad Inuwa(Tafida) kuma mun yi aure da shi a ƙarshen shekaran 2002 rana ɗaya aka yi bikin mu tare da Rahila da Yaya Muntari. Kuma ana saura kwana talatin da biyar auran mu Allah ya yi ma Mama rasuwa daga kwanciya barcu ciwon ciki dare zuwa asuba ta ce ga garin ku nan.
*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
09069067488.
08032773332.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿️13*
Tun ranar farko da na fara ganin Yusuf na ji a raina tabbas na haɗu da namijin da ya gama cika zaɓina. Sannan na san tabbas zai iya yin katanga da cikar burina na sai na gama Jami'a na samu aiki zan yi aure. Saboda in na bari ya suɓuce mini samun kamarsa zai yi mini wahala
Tun da gashi tuntuni ina tsumayen shi. Shi wanda ya dace ɗin amman ban samu nasaran haɗuwa dashi ba sai a wata ranar laraba. Daga cikin BUK na ke mun gama lacture tun safe har yamma na sha wahala ina tafe kamar zan faɗi, ba zan mata da kayan da ke jikina a ranar ba. Wata atamfa ce mai ruwan ganye hijabin jikina fari ne sai takalmin dake kafata mai saukaƙƙen tudu.
Daga bakin get ɗin jami'ar da na fito ni kaɗai ce. Ko anan ɗin ma ban yi wata ƙawa da na saki jiki da ita ba a dai gaisa kawai. Ina tsaye ina neman abin hawa ba ni da masaniyar tun a lokacin Yusuf ya ganni kuma Allah ya haɗa zuciyarsa da tawa a waje ɗaya.
Hauwa'u Jamilu ta fito tare da ƙawarta da tare na gansu Samira. Na gansu amman sai na ɗauke kaina kamar ban gan su ba, lokacin duniya na kwance sannan abubuwa duk ba su zama gari kamar yanzu ba. Ko wayar hannu nan sai wane da wane ke riƙe shi ko a ajinmu akwai ma su ita handset amman sai ɗaya ɗaya nima dai ina cikin mara shi.
"S. Yashe sai gobe."
Haka Hauwa'u ta faɗa sai na kalle su kafin na ɗan gyaɗa kaina. Ganin ina ta tsaye ban samu abun hawa ba sai na fara tafiya zuwa bangaren yamma su kuma su Hauwa sun yi gabas. Ina tafe ina sauri saboda yamma ta fara sauka biyar za ta iya gotawa a lokacin.
Ban san ya na bina ba. Saboda ban ji takun tafiya ba sai da na ji sallamarsa cikin muryansa mai zaƙi da haiba ta maza masu kyau da Aji.
" ƴan mata doguwa Salamu Alaikum."
Haka ya faɗa da farko ban yi niyyar na juya ba amman yanayin muryansa da salon da ya yi magana su suka rinjayi tunanina da zuciya na ɗan waiwaya na kalle shi yana daga bayana kaɗan ina juyowa sai kawai ya yi mini mirmishi irin mirmishinsa da na ke matuƙar so a tare dashi.
Na yi saurin ɗauke kaina na cigaba da tafiya amman na sauya takuna. Gaba na ta faɗuwa ban san so ba amman ina tunanin nima na fara son Yusuf a wannan ɗan kallon da na yi masa.
Lokacin da na yi gaba ina ta fargaban Allah ya sa ya cigaba da bina ya yi mini magiya sai na yi masa kwatancen gidanmu. Har ɗan rage sauri na yi ina jinsa ya na cigaba da bina lokaci ɗaya yana sake faɗin.
"Haba ƴan mata. Ina ta mgana shuru"
Ɗan sake kallon shi na yi. Kai ya haɗu! Haka na faɗa a cikin raina ban wani saki fuskar da zai fahimci yanayina ba amman tabbas Yusuf ya shiga cikin zuciyata a karon farko da muka haɗu. Cigaba da bina ya yi yana min mgana amman ban tanka shi ba sai dai kuma tuni na gama haddace kamaninshi da kayan dake jikinsa. Tun a wannan ganin farko ni na san Yusuf ɗan gayu ne kuma yana da ilimi kuma shi ɗin daga ganin ɗan manyan mutane.
Yana sanye da ƙananun kaya. Jeans baki ne sai T. Shirt fara ta na da zanen baki a jiki amman ban iya ganin me aka rubuta ba. Takalmin ƙafarsa mai rufi ne sannan akwai wasu takardu a hannunsa. Ta gefen ido na gama ƙare masa kallo a cikin zuciyata kamar in yi ta tsalle saboda murna. Tsayawa na yi ina taran abun hawa shi kuma sai ya ƙara marairaicewa yana faɗin.
"Tafiya za ki yi ko muryan ki ba ki bari na ji ba?
Sai na kalle shi kafin na ɗan ɗauke kaina ina faɗin" Ya dace ka tari budurwa a hanya kana yi mata mgana?
Da sauri ya ce"Afuwan. to ki faɗa min sunan ki sai ki bani lambar wayarki sai na samu lokaci na zo gida mu yi mgana."
Kallonsa na yi sai ya yi wani sanyi kafin ya ce"Please."
Sai kawai na rausayar da kai kafin na ce"Sunana Halima. Amman ana kirana da Sadiya."
"Wow.! Nice name Sadiya ta." A karon farko da ya fa kirana da Sadiyarsa.
Sai na yi mirmishi ina so na tambaye shi sunan shi amman na kasa.
"Ba ni da waya. Gidanmu kuma na Ɗorayi in ka ce gidan Alhaji Sulaiman Yashe za a nuna maka."
Ƙuramin ido ya yi kafin ya ce" Sadiya kin tabbata zan same ki in naje?
Sai na samu kaina da ɗaga masa kai kafin na ce" In sha Allahu." Mirmishi ya yi mini nima sai na maida masa martanin mirmishi.
Shi ya taran min motar haya na hau sannan ya ɗaga mini hannu kafin ya ce"Bye. See you "
Ina so na ɗaga masa hannu amman sai na fasa sai dai na gyaɗa masa kai ina ɗan mirmishi.
Na koma gida a ranar cikin farinciki har sai da Rahila ta fahimci yanayina.
"Sadiya karatun yau hala ya fi miki daɗi ne?
Sai na kalleta lokacin ina tsaye ne a tsakar ɗakin mu ina mirmishi ni kaɗai ban sani ba har Rahila ta shigo ta kama ni ina ta mirmishi ni kaɗai.
"Me kika gani?
Na faɗa ina kallonta sai ta ƙara matsowa kusa da ni cikin raɗa ta ce"Ko dai?
Da sauri na matsa baya ina faɗin" Ko dai me! Ni matsa ki ban waje."
Na faɗa ina tureta ina mata dariya. Daga tsakar muka ji Gwaggo na gaisawa da Ya Muntari. Sai na ga Rahila na mirmishi a raina na ce daman haka ake ji in ka haɗu da wanda kake so. Sai na daina ganin laifin Rahila akan Yaya Muntari saboda na fahimci haɗuwar jini ce.
"Uhm kin ji muryan Yaya Muntari kin kasa sukuni."
Sai ta harareni tana faɗin" Ya Muktar dai ko Sadiya?
Ta faɗa ƙasa ƙasa. Ni ko ina ta dariya da gayya na fita tsakar gida dai dai zai koma can waje in da ɗakunsa suke da sauri na ce" Ya Muntari ina yini."
Sai ya juyo yana amsawa kafin ya ce" Sadiya yan makaranta an dawo."
Sai na amsa masa ina kallon Rahila ta cikin ɗakin mu tana faman harara ta. Ni kuma ina dariya. Yanzu saboda makaranta an ɗauke mini aikin gida sai in ranar weekend ne. Rahila ce da Amina ke yi tun da Ma'u na Minna sai an yi hutu ta ke zuwa ganin gida.
Haɗuwata da saurayin da ban san sunan shi ba sama da sati ɗaya bai zo ba kuma ban ƙara ganin shi ba. Har in na fito daga cikin Jami'a. Na yi ta tsayawa ko da yaushe ina hasashen zan ƙara ganinsa amman shuru sai na fara damuwa. Ko ya zo ne bai gane gidan ba? Ko kuma dai! Na kasa iya fassara yanayin da na ke ji amman na rage walwala da fara'a kamar dai ina so na bayyana damuwar haka. In na kwanta sai na riƙa mafarkin shi tabbacin dai ya samu matsugunni a cikin zuciyata.
Har na fara fidda rai domin an fi kwana goma da haɗuwarmu . Kamar wasa ranar da ya fara zuwa kofar gidanmu muka san juna sosai ranar laraba ne da yamma da wuri na dawo daga makaranta bayan na yi sallar la'asar na ci abinci sai na ɗan kwanta amma ba barci na ke yi ba. Na ji dai yaro ya yi sallama amman ban maida hankalina a wajen ba.
"Wai Sadiya ta zo in ji wani a waje"
Haka na ji an faɗa. Kamar an jeho ne sai gani a tsakar gida ina faɗin" Waye?
Haka na faɗa ina kallon yaron Rahila na kan kujeran tsakar gida tana gyaran wake Gwaggo da Mama suna can ƙofar shashen Alhajinmu suna hira Amina na bakin ma zubar ruwa ta na wanke wanke. Gabaɗaya suka juyo suna kallona cikin mamaki.
"Ni ma ban san shi ba."
Sai da na juya ina kallon su Gwaggo sannan na dawo hayyacina. Sai kuma na yi sanyi na kasa motsi.
"Je ka ce tana zuwa."
Mama ta faɗa tana kallon yaron. Ya juya ya fita amman ni na kasa motsi daga in da na ke tsaye..
Rahila na dariya ta kalleni ta na faɗin" ki koma ciki ki ɗan gyara mana! Ko haka za ki fita?
Sai na dawo hayyacina na koma ɗaki da sauri na sauya hijabina na duba madubi na gyara fuskata duk ina tunanin shi ne ko ba shi ba ne? Sai dai zuciyata na ta rawa. Na saka takalmina na fito tsakar gida bakina na rawa na ce" Zan je waje."
Gwaggo ce ta tanka ni Mama ba ta ma a wajen ta shiga ɗaki.
"To Sadiya. Amma kar ki daɗe saboda Alhaji."
Sai na amsa mata na juya na fita Rahila na yi mini dariya ganin yadda na yi wani sanyi ina tafe kamar ba na son tafiyar.
Lokacin da na fita na ci karo da shi a tsaye a ƙofar gidanmu yau ya yi shigar manyan kaya ne. Yana tsaye ya na fuskantar ƙofar gidanmu hannayensa harɗe ƙirjinsa. Na ji lokacin da zuciyata ta ta yi tsalle ta dawo waje ɗaya lokacin da na ganshi. Sannan farinciki ya bayyana a saman fuskata lokacin da muka haɗa ido ya sakar min mirmishi nima na maida masa martanin mirmishinsa lokacin da na ke tafiya zuwa in da ya ke tsaye ya na kallona.
Bayan mun gaisa ina noƙewa kai tsaye ya fara faɗin" Sunana Yusuf Muhammad Inuwa. Ni anan garin aka haife ni amman mahaifina da mahaifiyata mutanen Rano ne. Na yi karatuna har matakin Masters ranar da kika ganni ma a Buk na je ganin supervisor ɗina ne akan project ɗina. Sadiya da gaske na ganki kuma sonki sannan ina son in mun gama fahimtar juna iyaye su shiga ciki domin maganar aure."
Bayan takaitaccen bayanin da ya yi min ban ja aji ba na bashi dama mun ɗan jima muna hira har Yaya Abubakar ya dawo ya ganmu suka gaisa da juna. Daga wannan lokacin ba a ɗauki wata biyu ba hatta Alhajinmu ya san da Yusuf sannan in ya zo zence a wajena a cikin gida muke yi. Zuwa lokacin kuma ni da shi mun gama shaida muna son juna sannan mun aminta mu zauna kan inuwa ɗaya ta aure. Na gama mutuwa a kansa kamar yadda shima ya gama mutuwa a kaina, kowa dake gidanmu na gidajen auran su da mazan gabaɗaya su san labarin YALLAƁAI da tun a lokacin na laƙaba masa wannan sunann tuni na watsar da tunanin sai na gama Jami'a zan yi aure ba zan iya jira ba gwara na yi auren sai na cigaba da karatuna a ɗakin miji.
Ban taba sanin daga ɓarayin Yusuf zamu fuskanci barazana daga dangin sa ba. Duk da ya sha bani labarin gidansu da yan uwan shi na san suna da yawa tunda mata huɗu babanshi ya yi kafin rasuwarsa. Lokacin da muka haɗu da Yusuf a shekaru iyakarsa 27 to 28 ni kuma ina cikin shekarata ta ashirin na kuma san ya karanta Architecture ne masanin zane zane bai samu aiki ba amma yana buga buga. Mutum ne mai sabgogi da yawa da kuma ƙoƙarin neman na kansa.
Yusuf ya turo magabatansa daga Rano. Ya ce mini ƙanin mahaifiyarsa ne da ƙanin mahaifinsa sun zo sun gana da su Baba Aminu an ba su damar dawowata ta gaba za a tsaida mgana. A wannan gabar ne Alhajinmu ya gudanar da bincike a hakan Yusuf har na samu cikakken bayanin waye shi da asalin shi.
*****
Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa kafin rasuwarsa ya yi aiki a Ministry of Agriculture and natural resources. Ya rasu a shekaran 1999. Ya bar mata huɗu da tarin ya'ya guda 21. A kimanin ƴaƴan da haifa ashirin da takwas ne bakwai sun rasu.
Sannan bayan rasuwarsa da wattani matarsa ta huɗu ta bi bayan shi Hajiya karima.
Ɗan boko ne da ya yi shura tun a zamanin baya da boko bai yawaita ba. Sannan sun shiga gwamnati an dama da su sosai ta sanadin wani amininsa Alhaji Yusuf wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Rano. Shima ya rasu tsakanin shi da abokin nashi shekara ɗaya ne shima ya rasu ya bar mata biyu da yaya maza da mata.
Alhaji Muhammad Inuwa da Alhaji Yusuf Tafidan Rano sun fito daga jiha ɗaya ne. Wato Rano sai kuma suka haɗu a makarantar kwana ta Barewa collage dake zariya. Ajin su ɗaya sannan ɗakin kwanan sy ma ɗaya ne. Daga lokacin suka fara aminta bayan sun gama sun nemi jami'a ɗaya ta Usman ɗan fodiyo University. Kowanne ya karanta bangaren da ya zaɓa shi Alhaji Inuwa sai ya yi karatunsa kan harkan Noma da tattalin ƙasa shi kuma Alhaji Yusuf Tafida sai ya kan harkan sanin Siyasa. Bayan sun gama karatun su sun samu manya ayyuka. Shi Yusuf a matsayinsa na jinin sarauta na Tafidan Rano yana da hanyoyin isa ga Gwammatin kano a lokacin. Dukkansu kowanen su ya je ya ƙaro karatu kuma dalilin Alhaji Yusuf Tafida rano Alhaji Inuwa ya tsinci kansa a Ministry of Agriculture na gwammatin Jihar kano a wancan zamanin.
Alhaji Muhammad Inuwa ya fara aure da Hauwa'u(Nene) wacce haifaffiyar Rano ce kuma duk an san juna. Kuma a sha'anin bikin ne Alhaji Yusuf Tafida ya haɗu da ƙawar Nene Aminiyarta Fatima Binta(Hajiyar Tafida)
Sai Aminan junan suka aure ƙawayen junan. Dalilin haka sai zumumcin su ya ƙullu a tsakaninsu mai ƙarfi. Kuma ya samu kafuwa har zamanin ƴaƴan su.
Shi dai Alhaji Yusuf Tafida kafin rasuwar ya ƙara mace ɗaya Hajiya kaltume. Ita ce ke da jibi da masautar kano kuma har ya rasu ƙaton gidan shi na nan a Rano. Amman dai yana da gida a cikin garin kano shi kuma Alhaji Inuwa a cikin garin kano ya gina ƙaton gida a gwammaja mai shashe da yawa daga nan Nene ta fahimci Mijin nata yana da ra'ayin zama da mace sama da ɗaya. Ya kuma tabbatar mata tun da sai da ya yi mata huɗu jeras sannan kuma dukkansu matan sun haifa masa zuru'a.
A bangaren ɗakin Nene Zuwaira ce Babba sai Maimuna. Sannan ta yi Bahijja. Sai da ta yi mata uku sannan ta samu namiji sai Alhaji Inuwa ya cika burinsa ya sanya masa sunan Amininsa Yusuf suna kiran shi( Tafida) a kuma a tsukin Hajiyar tafida itama ta sauka an samu namiji itama sai kawai shima Alhaji Yusuf ya saka masa sunan Amininsa Inuwa suna kiran shi(,Tariq) a kuma lokacin a gidan su Nene mahaifinta matan shi biyu mahaifiyar su Nene Innayi ta daina haihuwa amman abokiyar zamanta Hannatu( Inna) ta haifi ɗan ta Namiji sai ya ci sunan mahaifinsu Abdulmu'iz sai suna kiran shi da Abba shi ne kuma auta a gidan su Nene sai ya kasance waɗanan mazan guda uku sun tashi tare sun girma tare sun kuma ba da misalin kyakyawan zumunci juna a tsakanin su.
Bayan Yusuf sai Muttaƙa sai auta Halimatu.
Sai Maman Farko(Hajiya Saliha) ita yar kano ce ita ta ɗan fi Nene yawan ƴa'ƴa domin ƴaƴanta bakwai ne.
Usman shine Babba wanda Zuwaira da Maimuna ne ke gaban shi a tsarin manyan gidan sai shi. Bayan shi sai Nasaratu ita sa'ar Tafida ne sai Nasir sai Jafar sai Suwaiba da Jamila autar ta mai suna Hindatu. Daga ita sai Hajiya Zaliha(Hajiya iya) ita ƴaƴanta huɗu ne.
Hafsat ce babba sai Saffiya sai Muhammad kabir sai Musbahu.
Sai ta huɗun da ta rasu Hajiya karima ita ƴaƴanta uku ne. Ummu Salama sai Adnan Jawahir ce ƙaramar su. Kuma bayan rasuwarta riƙon su Jawahir ya koma ya koma ƙarkashin kulawar Nene.
Kaf ƴaƴan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 31